yana juya wayar Jaleela tafin hannun sa. Despite all the burika dayaci yanda zaiyi making life nata he'll, bazai ignore na kyau da sukayi ba ita da Anees. Yana son ya yi finding out y'ar waye wannan. Yarinya is so beautiful to be true. Tsintar kansa ya yi da shiga gallery nata ya cigaba da kallon hototun nan su ko Allah zaisa yaga wani clue da zai nuna uban Anees. But baiga komai sai hoton Jaleela kawai da Anees. Baya son zarginsa ya zama gaskiya. In dai kuwa har Anees bata da uba, oh life na Jaleela is about to get much worse. Wani irin zafi zuciyar sa yaji tanayi hakanan kawai. Abubuwa da suka shude shekarun baya suna masa yawo cikin ido. A fili yace
"She's a liar. Duk son Allah nata da Manzon sa. Har take iya kiran wasu da sunan y'an iska. At the end ita ce y'ar iskar ashe?. What a snake"
" you will pay for what you did. Just wait am coming for you miss Aleeyna "
Smirk daya saki sai ya matuk'ar bawa mutum tsoro. Bodyguards nashi mai suna James dake zaune gefen zaman mutum banza ya had'iye yawu kutt yana shivering.
Haka ya yi ta bincike a wayar . Duk wasu mutune da take hulda dasu ya d'auke su cikin d'an k'ank'anin lokaci.
To Jaleela da rawar jiki ta shige gida bayan Lami ta buɗe k'ofar. Mamaki ya cika Lami ganin yanda ta shigo a firgice babu takalmi bare d'an kwali. Hankali a tashe ta fara karanta Auzubillahi da dukkanin wasu ayoyi da suka zo bakinta. A tunanin ta ko Jaleelan tayi gamo ne. Yaraf Jaleela ta zube k'ofar d'akin ta. Had'a kai tayi da gwiwa tana wane irin kuka mai ban tausayi. Sai a lokacin Lami ta sauke ajiyar zuciya saboda wani irin tsoro daya rufeta. D'an nesa da ita kad'an ta tsaya a tsorace tace
"Hajiya lfy? Wani abu ya faru ne?"
Jaleela ta kasa cewa komai sai kuka kawai da take. Jikin Lami ya yi sanyi sosai a hankali ta matso ta durkusa kusa da ita. Rungume ta tayi tana d'an buga bayanta. Da ace tabbas Jaleela na tare da uwarta tasan cewa tabbas abunda take buƙata kenan. Aikuwa ta shige jikinta ta cigaba da kuka sosai tana kiran Ammi kaman wata k'aramar yarinya. Jikin Lami ya k'ara sanyi sosai. Menene ya yi sanadin daya sa Jaleela ta bar gida?. Sun d'auki sama da minti goma a haka kafin Jaleela ta janye ta yunƙura ta miƙe tsaye ta shige d'aki. Kai tsaye gadon da Anees ke kwance tayi ta jata ta matse a k'irjinta kaman wani zai kwace ta. Sosai take fad'a da zuciyar ta. Wani sashen nace mata ta gaggauta barin garin Abuja tun baiyi tracking d'in ta ba, wani sashen na cewa. And so what kuma. Ya kamata mu daina zama so weak. This is our chance to fight. Yanzu ya dace mu sashi regret na kangi rayuwa daya jefamu. Mu daina nuna masa weakness namu. Saboda shi muke ta guje-guje. Enough is enough. Allah shi kad'ai yasan ikon sa daya k'ara had'amu bayan mun fidda ran sake ganin sa. Yanzu ya dace shima ya d'and'ana d'acin daya saka mana a baki. Ya yi kuka kaman yanda mukayi shekaru d'ai-d'ai har bakwai. We have to show him we are strong and ready to fight, just like before.
Numfashi ta sauke da wannan tunanin ta yanke hukunci. Zatasan duk yanda zatayi bazai gano Anees ba. Tana tsoron ya kwace ta. Anees ita kad'ai ce duniyar ta a yanzu. Tana kuma rayuwa ne saboda ita kad'ai. Duk da begen ta nason komawa gida wajen iyayenta, bazata iya ba. Tana kunya ta koma musu bayan shekaru da yawa. Addu'arta a kullum Allah yasa su yafe mata ko inta mutu ta samu saukin cikin kabari.
Tunda Lameen ya fice ya yi zurfi cikin tunani. Wai wacece ne wannan yarinya ne?. Me yasa duk wanda ya had'u da ita baya iya rabuwa da ita ne?. Yasan waye Lameen and what hid capable of doing. Sosai yaga interest na yarinya cikin kwayar idonsa. But shima yana da interest a kanta and he's going to have her. Hoton ta daya gani yanzu ya k'ara jefashi cikin wani yanayi. Yarinya is so beautiful. To amma wannan y'ar way'e?.Numfashi ya fesar mai zafi ya ciro wayar sa ya dannawa Kainat kira.
Tsawon kwana biyu Jaleela tayi mak'ale a gida. Daga ita sai Anees. Ko k'ofar gida bata lek'o ba. Sam bata damu da motarta ko wayarta data bari ba a club d'in. Ita damuwarta karta sake had'uwa dashi. Yau ya kama Monday k'arfe bakwai suka fito ta gama shirya Anees. Yarinya tayi kyau sosai cikin uniform nata na kamaranta. Yar doguwar riga data tsaya iya kugu sai wata a ciki mai necktie. Kanta hulace da Jaleela ta nannade gashin kanta ta turashi kaman gammo. Bayanta jakarta ts makaranta ce peach mai gashin kaman ta mage. Lunch box nata da jakar kalansu d'aya. Ita kuma Jaleela duguwar rigace a jikinta mai fad'i wacce aka raba daga kugu. An tattare ya matse kaman sket. Rigar darka blue ce da mayafin ta data rataya a wuya. Duda cewa batayi kwalliya ba, tayi kyau sosai. Hannu Anees ta riƙe suka fito tana riƙe da Lunch box d'in. Saida ta tofeta da Addu'a sannan suka fito. Bakin gate suka tsaya saboda layin nasu akwai kwalta. Motoci na wucewa sosai na haya. Wata arniyar BMW M5 2025 ce wajen gudu biyar fake daga can d'aya b'angaren d'an gaban gidan kad'an. Jaleela sam bata kula dasu ba ta tari keke nape daya shigo layin da wasu mata. D'aya daga cikin motar aka buɗe masa ya fito in all his glory sanye cikin bak'ar suit daya dura musu katuwar coat ash colour. Gashin nan yasha gyara sai shining yake. Tsayawa ya yi yana kallonta gefen bakinsa a d'age da smirk. Suna can suna magana da mai nape sam bata lura ba sai da Anees taja hannun ta tana cewa
"Mummy kinga wani mutum mai kyau?"
K'irjin Jaleela ya wani irin harbawa, da sauri ta kalli inda Anees ke nuna mata. Saida zuciyar ta ta kusa tarwatsewa sanda idonsu ya had'u. Wani irin fisgar Anees tayi ta fad'a cikin motar a guje tana cewa muje malam. Ai tuni mai adaidaita da matan dake ciki cikinsu ya duri ruwa. Irin wannan abun da suke gani a American films na Mafias da suke sace mata suna sana kaisu prostitution ko wani abu makamci haka. Shine suka tunanin yake shirin faruwa a zahiri. Don duk wanda yaga Lameen da irin shirgar sa ga Bodyguards nashi da suka rufe titin dole kayi tunanin wani Mafia boss ne. Malam bahaushe da tsoro. Da yawa motoci sunci birki daga can nesa sun kasa k'arasowa kowa tsoro ya kamshi ganin turawa sun danno musu gari haka. Mai nape bai jira ta k'ara cewa su tafi ba ya tashi mashin a guje zasu hau titi Bodyguards nashi suka rufe titin. Tuni ciki ya d'uri ruwa. Jaleela ta zuba masa ido kaman yanda shima ya kafeta da nashi black eyes d'in. Sosai k'irjint yake bugawa amma fuskarta ta hana nuna wannan tsoron ya nuna. Blank take kallonsa kaman yanda yake mata. Murmushi ya k'arayi da dimples nashi suka lotsa ya fara takowa a hankali cike da izza.
Zagayowa ya yi inda take zaune ya d'an sunkuyo abunka da mutum mai tsayi. Anees dake ta kallonsa tana murmushi ya kalla kafin ya maida ido kan Jaleela data k'ara matse Anees kan cinyarta tana rufe mata fuska da hannu.
"Hmm. What with the rush?"
(Menene na saurin?)
Shiru tayi bata bashi amsa ba sai mugun kallo data watsa masa tanaji kaman ta kifa masa mari. Murmushi ya k'arayi ya kalli Anees.
"What is your name Beautiful?"
A hanzarce Anees tace " Baby Anees" ita kanta ta rasa farin ciki me takeyi haka. Hannu ya mik'a mata da d'an murmushi yace
"Come. Zona kai ki makaranta ko Baby?"
A guje Anees ta kai hannu zata kama nashi, Jaleela ta wani irin buge hannun saida Anees ta saki kuka. Rai a bace tace
"Me nace miki akan kula wanda baki sani ba?"
Tana kuka sosai Anees tace " Sorry mummy ". Mugun tsaki Jaleela taja ta kalli mai nape da mugun b'acin rai tace "malam mu tafi " mai nape dai tsoro ya hanashi tafiya ya kalli Lameen daya kafe Jaleela da ido Allah kaɗai yasan abunda ke ransa. Kwayar idonnan ta kara zama wani irin black.
"Kinga Hajiya kawai ki sauka"
"Eh wlh ki sauka kawai, kar ki shafa mana kashin kaji bamuji bamu gani ba"
Matan dake zaune cikin motar suka saka baki. Baki Jaleela ta cije kaman tayi bindiga. Wota yanzu ana cikin wani yanayi da ba'a taimako. Koda yake bayau ne ta fuskanci irin wannan kalubale ba. A fusace ta fito daga motar Lameen ya d'an ja baya yana kallonta da wani irin creepy smile kan fuskarsa. Mai nape tuni yaja mota a guje yabar gurin. Da azama ta juya zata koma gida ganin babu wasu motoci dake k'ok'arin shigowa. Batayi tunanin zai biyota ba saida ta kama k'ofar ta buɗe tana k'ok'arin shiga ta juyo taga mutum tsulum bayanta kaman zai shige jikinta. Wani irin ihu tayi tayi tsalle ta koma gefe taja k'ofar da sauri ta rufe bata shiga ba.
Kama Anees tayi ta b'oye bayanta kaman mai shirin rufeshi da duka tace da k'araji.
"Uban menene ka ke bina kuma?"
"Language. Kinsa yanda na tsani zagi"
"Naci uban Language d'in na bishi da gudu. MENENE ka ke bina?"
Ta fad'a da k'arfi da kaf compound d'in saida ya d'auka. Ido ya zuba mata cike da nazari sai kuma ya saki y'ar dariya yace
"Har yanzu kina nan da wannan feistyness naki. After all shine sanadin komai "
Kaman bashi ne ya yi dariya ba lokaci d'aya ya wani irin had'e fuska kaman bai taba dariya ba. Ita kanta Jaleela duk kurinta saida tasha jinin jikinta. Wani k'aramin card ya fito dashi ya mik'a mata. Wulaƙantaccen kallo ta watsawa hannun nasa da katin bata karb'a ba. Gira ya d'aga kafin yace
"Take it or you will not like what am going to do next "( ki karb'a baza kiji dad'in abunda zanyi ba idan ki ka k'i)
Yanda ya yi magana saida wani tsoro ya ratsa ta . Ka kalli fuskar ta maida ido kan Anees dake kallon su. A guje ta warce katin kaman mai k'arban kashi. Murmushi ya yi ya d'an ja baya kad'an yace
"Ki same ni wannan address bai 7pm Sharp. Don't be late"
"Who the he'll are you da ke ke tunanin zaka bani unarni nabi"
Wani irin kallo ya yi mata taji kaman ta saki fitsari.
"Do not come. And see what happens "
K'arasa maganan ya yi da kallon Anees. A guje ta k'ara b'oye ta a bayanta. Ya d'ago ya kalleta da murmushi kan fuskar yace
"Exactly"
Daga haka ya juya ya bar gurin. Da ido Jaleela ta bisa k'irjinta na wani irin suya. Tsana, kiyayer sa sunyi mata katutu a rai har makogaro take ji. Tana kallo ya shiga mota suka bar gurin. Ga mamakin ta sai ga motar ta an shigo da ita an faka. Wani Bodyguards nashi ya fito daga cikin motar bai kalleta ba ya juya ya fice. Tsaban takaici ji tayi kaman ta saki ihu. Numfashi kawai ta fesar mai zafi ta kama hannun Anees suka shiga motar ta kaita makaranta. A mota tayi tayiwa Anees fad'a na kulashi da tayi harda gaya masa sunanta. Ji take kaman ta rufe yarinya da duka tsabar takaici. Data dawo gida kuwa taita ihu tana jifa da kaya kaman mahaukaciya.
'Sai kayi dana sanin kara dawowa rayuwata a karo na biyu. Mu zuba nida kai shege ka fasa. Ahhhhhhh"
Ta suri filon kujera tayi jifa dashi.
𝗚𝗨𝗗𝗨𝗡𝗔
𝗔𝗞𝗘 .
𝒜𝐬𝐡𝐚𝐧𝐭𝐲 𝐥♡︎𝐯𝐞.
Masu tambayar books nawa akwai.
SULTANAAH
SAUYIN LAMARI
MULKI
KAIDIN MACE
ZUBAR HAWAYE
Da sauran su.
Mutanena a dinga share na GUDUNA AKE sauran groups da ku ke pls. I can't do this ni kaɗai kullum sai kayi share from the beginning. Pls a dinga share fisabilillahi 🙏🏻👌🏻
31/35.
Shabiyu da rabi daidai ta d'auko Anees daga makaranta. Tunda daga safe har zuwa wannan lokacin ta kasa yanke hukunci kan taje kaman yanda ya bata umarni?, ko ta share shi?. Haka zatayi ma bai isa ya yi mata abunda Allah baiyi ba don haka baza taje ba. Idan ya isa shi wani ne yasa azo a fito da ita k'arfi da yaji. Magriba nayi ta gark'ame gida ta ko ina. Window da kofofi. Tariga da tasan Kainat ganinta yanzu kuma sai sanda Allah ya yi don bata ma nan garin Abuja tana can Emo wajen wani Sugar Daddy nata soja. Duk yanda take nuna jarumta kan fuskarta amma zuciyar ta abun yasha banban sosai. Tana cikin fargaba duk sakan d'aya daya wuce idonta nakan agogo tana irga lokaci. Lokacin da agogon ya nuna k'arfe bakwai daidai saida k'irjinta ya harba. Tsoro sosai ya darsu cikin ranta. Tabbas tasan koma wanene wannan mutum hatsabibi ne na gaske. Saboda lokaci kad'an yasan inda take har yasan kuma motarta data bari a club d'in. To in har yasan hakan tabbas babu abunda bazai iya aikatawa ba. Wai shin shidin waye ne?. Me yasa ne tun farkon had'uwar su babu alkhairi ne a ciki?. Numfashi ta fesar mai zafi ta gyarawa Anees da tayi barci kusa da ita kan kujera kwanciya. Fuskarta ta shafa ta k'ara tofeta da Addu'a. Ajiyar zuciya ta k'ara saukewa ta maida hankali TV da take kallon wani series na Korean, QUEEN OF TEARS. Duk yanda take tsananin son kallon series d'in gaba d'aya batajin dad'in sa. Kallon kawai take amma bata da nutsuwa koya taji motsi zata kalli k'ofa ko window. Gani take kaman zai aiko d'inne a fita da ita k'arfi da yajin. Tanan nan zaune har k'arfe gome babu wani motsi. Sai a lokacin ta sauke wata katuwar ajiyar zuciya ta miƙe ta suri Anees sukayi d'aki. Wanka ta shiga bayan ta kwantar da ita ta fito sanye da rigar wanka data tsaya mata a gwiwa sai d'an k'aramin tawol da take goge gashin kanta dashi. K'aramar riga tasa mara nauyi ta barci. Saida ta feshe jikinta da turaruruka taja hijabi ta shimfiɗa dadduma. Sallan isha tayi da nafila. Ta jima tana Addu'a da neman tsari wajen Allah na wannan mutum kafin taja Qur'ani ta fara tilawa. Daran ranan dai Jaleela haka tayi barci da ido d'aya. Washegari a daddafe ta shirya Anees suka fito zata kaita makaranta. Sosai gabanta ke fad'uwa tunda suka fito. Koda suka shiga mota ma tanayi tana waige waige. Kusan kaff week en Jaleela tayi shi ne cikin fargabar abunda zaije ya dawo. Sannu a hankali kuma komai ya wuce had'uwar su ta k'ara zama kaman labari. Ganin har an d'auki wannan lokacin bata k'araji motsin basa, ta tarkatashi ta ajiye a gefe. Sannu a hankali ta soma dawo da rayuwar ta. Waya ta sake mai kyau k'irar Samsung. Tana buɗeta ta fara kiran Kainat. Saida kunnenta ya yi ciwo saboda ihu da hargagi da Kainat d'in ta dinga yi mata cikin wayar. Bata tsaya sunyi wata doguwar magana ba ta kashe wayar. Kai ta girgiza tana kallon tsirarun mutane dake ta wucewa k'ofar makarantar su Anees. Agogon hannunta ta kalla baifi saura minti biyu su tashi ba. Lokaci na cika kuwa aka buga k'ararrawa. Shiru-shiru Jaleela na jira taga bullowar Anees amma shiru ka ke ji kaman wacce ta aikate garinsu. Tana kallo yara nata fitowa iyayen su na d'aukan har suka k'are sai malamai. A yanzu wani irin zufa ta fara had'awa cikin motar. Jiki na wani irin rawa ta buɗe motar ta fito tayi cikin makarantar. Sama ko k'asa babu Anees bare labarin ta. Jaleela tun tana ganin abun wasa sai gata ta zama kaman mahaukaciya tana neman Anees lungu da tsako na makarantar da kiran sunanta. Sauran malamai da suka rage a makaranta aka bazama ko ta shiga wani gurinne. Ana cikin neman nata saiga malamar su da data fito daga office na principal. A guje Jaleela tayi kanta tana ihu
"Ina Anees, ina Anees ina ki ka bari ta tafi ba'a tashi ba?"
Da tsananin mamaki Auntyn tace
"Yanzu abunda ya fito dani daga office na principal kenan. Yau tsawon sati guda kenan Anees batazo makaranta ba"
Idan kaga yanda idan Jaleela ya fito sai ta baka tsoro ta wani irin dafe k'irjin tana cewa
"Ban gane abunda ki ke cewa ba? Anees d'ince tayi sati bata zo makaranta ba? Wa nake saukewa kenan nake d'auka idan an tashi?"
Tayi maganan kaman zata rufeta da duka. Da sauri malaman dake kusa suka shiga tsakani suna bada hak'uri. Jaleela ta cigaba da bala'i
"Wane irin maganan banza. Yarinya da nake kawowa kullum nake d'auka kice tayi sati batazo ba. Ciwon hauka ne ya kama ki ko makamcewa ki ka yi. Ina y'a take?
Haushi ya kama Auntyn itama a zafafe tace
"malama kinga kar ki cimin mutunci. Saboda me zanyi miki k'arya?. Biyana akayi na kula da y'ar ki na bata ilimi mai kyau. Kulawa na d'aya daga cikin abunda nake bata, badon kulawa da nake ba bazan damu da rashin zuwanta ba bare har na kai office. Saboda haka babu abunda zaisa nayi k'arya. Yau sati guda kenan batazo ba "
Dumm k'irjin Jaleela ya buga. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Hannu ta d'ura aka ta rushe da wani irin kuka da ihu.
"Wayyo Allah na shiga uku"
Ihuce-ihucen yaja hankali mutane suka shigo makarantar harda shi principal ya fito. Yanda take ihu ana bata hak'uri sai abun ya baka tausayi. Gaba d'aya ta fice daga hayyacin ta. Sosai tayi musu bayani kullum sai ta kawota ta ajiye kuma idan an tashi zatazo ta d'auke ta. Ya akayi babu wanda yake kula da zuwanta da kuma fitarta?. Wannan abu dai akwai d'aure kai. Kaman wacce aka tsikara ta miƙe da bala'in sauri daga kasan da tayi zaman dirban. A guje ta fito daga makarantar. Turus ta tsaya bakin k'ofar kaman wacce aka kafe a guri ta zubawa Motar dankareriyar Motar PRADO dake fake gefen ta ta motar ido. Ba motar ce ta sata tsayawa ba sai wanda yake jingine jikin motar. K'ananan kayane a jikinsa blues Baggy Jean's da wata ashe d'in riga data kwanta jikinna ta kamashi tsam kaman baya iya numfashi. Ya d'ura mata jacket irin ta Biker's d'in nan Leather bak'a. Gashin sa ya tufke tsakiyar kansa yan silli sun zubo gefen fuskar sa dake d'auke da farin glass. Wayyo kyawun da ya yi abun bazai kwantatu ba. Komai na Jaleela tsayawa ya yi chak bata ganin kowa da komai sai shi. Zuba masa manyan Brown eyes nata tayi k'irjinta na wani irin boiling kaman wacce ake zubawa tafasheshshen ruwan zafi.
Wani irin karkatar da kai ya yi gefe yana k'are mata kallo tun daga sama har k'asa sai kuma ya saki Smirk. A hankali ya kama murfin motar ya buɗe. Y'an k'afafuwan Anees suka fara fitowa daga cikin motar ya mik'a hannun ya d'auko ta . Numfashi da Jaleela ta sauke kai k'arfi shima saida yaji k'irjinta ya wani irin harbawa kaman an kwad'amata guduma har saida takai hannu ta dafe tana wani irin haki. Wani iri relief ya saukar mata da wasu hawaye masu matuƙar zafi suka biyo kuncinta. Jiki na rawa ta nufeshi ta fisge Anees daga hannun sa da k'arfin gaske. Kafin ta gama sauke ta daga jikinsa ta d'auke shi da wani mahaukacin mari saida fuskarsa ta koma gefe. Haka ya tsaida fuskar tashi yana kallon gefen bai juyo ba. Allah ne kad'ai yasan irin zafi da zuciyarsa take. He was so piss off da kwayar idonsa a take ta rikid'e ta koma jaa. A karo na biyu ta k'ara maimaita thesame mistake.
Yanda ya juyo ya watsa mata manyan idonsa da sukayi jazur kaman garwashi saida ta tsorata taja da baya. Amma zuciyarta dake zafi da tafarfasa baisa tayi backingdown ba ta fara zagga masa masifa tana zagin sa da gaya masa dukkanin wani abu daya zo bakinta. Uffan baice ba saida ta gama ruwan bala'i ta k'arasa da cewa
"InshaAllahu yanda ka shiga rayuwarta ka hanani samun nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali, sai Allah ya jarrabeka da kwatancin uk'ubar rayuwa daka jefani. Duk wani hali dana shiga kaine sanadi kuma bazan tab'a yafe maka ba. Ka fita daga rayuwata dana y'ata "
Leb'ensa na k'asa ya wani taunewa yana kallonta da wani irin strange look. Menene take ta babatu haka? Shine ya yi sanadin shigar ta me?. Fuu ta juya ya bita da kallo da jajayen idonsa. Saida ta saka Anees cikin mota ta zagaya zata shiga ta tsinkayi maganan.
"You just make thesame mistake da ki ka yi before. So watch out for me"
Sosai maganansa ya bata chill har cikin bargon jikinta, bata juyo ba ta fad'a cikin motar da sauri ta fisgeta a guje ta bada masa kura da sauran mutane da suka tsaya kallo. Yanzu wannan mutumin tsoro yake bata. Maganan gaskiya bazata iya cigaba da zama nan ba matsawar yana nan. Mutum kaman aljani. To wai taya yake iya shiga yake d'auke Anees da zarar ta ajiyeta? Kuma yake dawowa da ita ta d'auke ba tare da kowa ya lura ba?. Anya kuwa mutum ne?. Numfashi ta k'ara saukewa ta kalli Anees dake rungume da wata katuwar pink Teddy Bear. Yarinya tayi wani irin shiru kaman mara lafiya da alamun bataso rabuwa da Mutumin ba. Bazaiyiwu ba dole ma ta gaggauta nesanta Anees dashi. Tanaji tana gani bazai kwace mata yaba. To yanzu ina zataje?. GIDA . Zuciyar ta ta bata amsa. Hawaye suka wanke mata fuska ta k'ara maimaita GIDA kan leb'enta hankali .
Shikam ya jima a tsaye kafin ya buɗe motar ya zauna a baya. Jingina ya yi kujera ya maida idonsa ya lumshe yana wani irin numfashi a hankali.
'InshaAllahu yanda ka shiga rayuwarta ka hanani samun nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali, sai Allah ya jarrabeka da kwatancin uk'ubar rayuwa daka jefani. Duk wani hali dana shiga kaine sanadi kuma bazan tab'a yafe maka ba. Ka fita daga rayuwata dana y'ata '
Maganganun ta suna tayi masa yawo a kunne. What did she mean by that?. Zain dake zaune wajen direba ya juyo sosai yana kallonsa. Yau daga shi sai Zain ne suka zo saboda ya sasu suna investigate na wasu da yake tunanin suna bibiyar Jaleelan da bata sani ba. Target d'in nasu kuma yaga kaman kan Anees ne. Abunda Jaleelan bata sani ba tun ranan dukkanin wani motsin ta a tafin hannunsa yake. Yasan dukkanin wani abu da ita kanta Jaleelan bata sani ba. Wasu mutane ya gani suna binta kullum zata kai Anees makaranta. Idan ta sauke ta zasu faka motar suna tunanin yanda zasu shiga su karbo Anees. Ranan daya tabbatar da zarginsa ya shirya Plan nashi perfectly. Da zarar ta sauke Anees kafin kowa ya ganta yaronsa da yake ciki yana jiranta zai fito masa da ita. So she kansa baisan why yake protect na yarinya daya tsani uwarta ba. But he can't help the feeling da strange connection da yake ji duk sanda yaga Anees ko ya yi kusanci da ita. Ya barwa kansa yana protect nata ne saboda yarince dake so innocent and pure koda kuwa bata hanyar Sunna aka same taba. Jan numfashi ya yi ya kai hannu a hankali ya shafa fegen fuskarsa data mara.
'But hannun ta is so soft '
'What?, dude no'
Murmushi ne ya kufce masa jin yanda yake fad'a da zuciyar sa shi kad'ai.
"King ka sani a duhu. What is going on ne ? Dama ka santa ne har ta iya daga hannu ta mareka and you did nothing?"
Idonsa dake lumshe ya ware su kan Zain dake kallonsa cikin rashin fahimta. Zubawa juna ido sukayi yana karantarsa sosai yake hango damuwa cikin kwayar Zain d'in. Kaman bazai bashi amsa saida ya maida idonsa ya lumshe sannan yace
"She's that girl 7years