Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
jefa kanta cikin wannan halaka? Kai ta girgiza ta miƙe ta shige d'aki da Anees ke kwance. Saida ta k'ara gyara mata kwanciya tayi shimfiɗa nan kasan kafet ta kwanta cike da tausayin yarinya da irin rayuwar da uwarta take. Don ma taga Jaleelan na sauke dukkanin wani nauyi da Allah ya d'ura mata na uwa .itace uwa itace kuma uban. Tana kuma yin bak'in k'ok'arin ta wajen ganin ta ginata bisa tarbiya mai kyau. Har yau bata tab'a kawowa ranta cewa Anees bata hanyar sunna aka same ta ba. Sha d'aya daidai tayi fakin motar ta harabar club din. Tun daga wajen sa mutane keta kai da kawo kace safiya ce. Club din yau a cike yake tam da manyan yara,maza da mata. Kota ina fitilune kaman rana. Guri ta samu wajen su dank'ara-dankaran motoci da ganin irin su a nan sai a kashashen waje. Haka nan kawai taji k'irjinta ya d'an buga tana k'arewa motocin kallo. Juyawa tayi yaga yanda da yawa duk ji da kuɗin su motocin suke kallo suna musu hoto, babu wanda ya iya matsawa jikin su saboda wasu shegun Bodyguards dake jikin motocin da suit a jikinsu fuskar su rufe da mask ,baka gani komai sai idanuwansu. Harta hannunsa bakaken safe ne. Kana ganinsu kasan ba hausawa bane don yanda suke a murde. Idanuwan su kad'ai ya isa ya saka fitsari a wando saboda yanda suke jefan mutane da wani deadly glare. Kana gani kasan wannan Bodyguards abun tsoro ne. Ji tayi kaman ta juya,amma ita tana daga cikin mutanen nan da suka d'auki alkwari da muhammaci. Numfashi ta fesar a hankali ta buɗe murfin motar ta fito. Ai kuwa ido ya yi caa a kanta bata bari kallon ya dameta ba ta taka a hankali ta shige club d'in. Saida ta fara zuwa gurin Bartender ta nuna masa katin. Da d'an mamaki ya nuna mata hanyar da zatabi ta wuce mutane dake kallonta. Wasu na rawa ,wasu na zaune suna shaye-shaye. Y'ar corridor tabi mai dan tsayi sai gata ta bullo wata k'ofa da samanta aka rubuta VIP LOUNGE. Babu tunanin komai ta kama k'ofar ta kutsai ciki. Abu na farko daya fara dukan fuskata shine wani irin kamshi da tsananin sanyi daya ratsa ta. D'akine hadadden gaske da aka kwata da kayan more rayuwa. Kana ganin d'akin kasan ba kowa ke iya book nashi ba sai d'an wane da wane shima sai ya kai ya wuce. Da d'an mamaki take bin d'akin da kallo sam bata kula da wasu tsumammun deep black eyes kaman midnight da suka kafeta ba. Baki ta d'an buɗe da mamakin ina mutanen kuma nan babu kowa. Sannu a hankali ta fara yin k'asa da idonta har suka sauka kan wannan black eyes d'in daya d'aga gira cikin matuƙar confusion yana kallon ta. Dukkanin wani noti dake kanta kuncewa ya yi numfashi ta ya tsaya cak lokacin da idanuwan su suka sarke da juna. Idonta ya yi wani irin buɗewa so wide da sai ka tsorota. Kace mutuwa ta gani.Shima nashi b'angaren matsanancin mamaki ya rufesa yana kallonta. Da wani irin mugun slow gefen bak'in sa ya yi wani irin coiling da wani irin creepiest way ya saki Smirk. Cikakkayar girar sa ya d'aga guda d'aya murya so ,so deep and husky yace "You" ...... 😁finally ooo. Kina so a tallata miki Hajar ki @ affordable price?. Chat me up 👇 08140754777 𝗚𝗨𝗗𝗨 𝗡𝗔 𝒜𝓀ℯ . 𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮 21/25. Yanda ya kira ke d'in sai tsigar jikin ka ta tashi kaji kaman ka buga kai jikin baango tsaban creepiness. Jaleela bata san sanda ta juya da wani bala'in gudu ba har tana yarda wayarta da jakarta dake hannun ta. A guje ta fice wani irin kuka ya kwace mata. Yanda ta fito kaman mahaukaciya ya bawa mutane mamaki suka bita da kallo. A guje ta fice daga club d'in ko takan motar ta bata bi ba. Haka tayi ta shek'a gudu kan titi tana kuka kaman hauka sabon kamu. Duk wanda ya tsaya don taimakon ta idan yaga yanda duk ta firgice sai ya tsorata ya kasa mata magana. A guje zasuja motar su. Da yawa ma suna tunanin ko gamo sukayi. Gabas kawai ta saka a gaba bata tsaya ba saida ta ganta k'ofar gida. B'angaren wannan mysterious mutum wani irin miƙewa ya yi majestically ya tako inda ta tsaya. A hankali ya sunkuya ya d'auki jakarta data yasar yana juyata cikin tafin hannun sa dake sanye da safa. Sunkuyun da ya yi lallausan gashin kansa ya zubo ya rufe masa ido. Mugun smirk ya saki murya so husky yace "So..... finally after all those year, we meet?. Who could have thought The world is too small" ya k'arasa yana wani irin chuckling. K'ofar banɗakin da aka buɗe yasa ya d'aga ido a kasalance ya watsawa Zain daya fito yana goge hannu da d'an k'aramin tawol. Gira ya d'aga yana kallon Zain ta gefen ido. "What?" Zain yace yana k'ok'arin zama. Wani irin chuckling ya yi ya miƙe rike da pose d'in ya dawo ya zauna kusa da Zain yana kallon sa. "Your Babe. She just left" "What?" Zain yace yana zare ido ya yi saurin warce jakar daga hannun sa. A hanzarce ya fice daga d'akin ya bishi da manyan black eyes nashi yana mugun murmushi. Da saurin Zain ya fito har harabar gurin amma ko kurar ta bai gani ba. Baki ya cije rai a b'ace ya koma lounge nasu. Yanda ya barshi haka ya same shi zaune lazy kan kujera ya d'ura hannuwansa kan kujerar ya kafe k'ofar da sexy eyes nashi. Mugun kallo Zaid ya watsa masa "Me kayi mata?" Y'ar gira ya d'aga kafin ya saki y'ar deep dariya da dimples nashi suka lotsa. Oooh wannan mutum is a very sight to see. Baza kasan sanda ka ke dilalar yawu ba idon kana kallonsa. Da deep voice nashi yace da hausar da bata fita sosai "Ni kuma? Ask her mana. Me yasa daga ganina ta tsorota ta gudu, kaman wacce taga wani mugun abu? " Smirk d'in daya saki zaka san akwai meaning bayan maganan da ya yi. Numfashi kawai Zain ya sauke. Duk lokacin daya d'auka yana jiran wannan rana in the blink of an eye komai ya wargaje. Zama ya yi gefen sa yana kallon yanda ya koma ya kwanta ido a lumshe, har zuwa lokacin da murmushi kan fuskar sa. Tunanin abunda ya kawo shi Nigeria ma yau d'in nan yake. 2 DAYS BACK . kwana biyu da suka wuce. ABU DHABI. Kaman yanda Malika tasa ayi shela, hakan ne ta kasance. Cikin d'an k'ank'anin lokaci labarin auren LK da Aafiya ya baza Abu Dhabi. Da yawa suna cikin jimami da tunanin yanda makomar Aafiya ita ma zata koma. Kaman sauran matan da Lk ke aura, itama Aafiya gagarumin biki Malika ta fara shiryawa. Dukkanin wasu dangi na b'angaren Aafiya da Lk sun hallara cikin wannan katuwar masarauta. An fara shagali bikin irin nasu na larabawa ta ko wanne fanni. To amma shi wanda ake abun domin sa yana can MALIBU baisan abunda aka be. Sai bayan an d'aura aure Malika ta tura kannan sa da suke twins. Aizak da Aryan suka je suka tisoshi a gaba. Bai san da zancen bikin ba sai da daddare ya kebe cikin d'akin sa. Had'addiyar black suit dake jikinsa yake cirewa a hankali cike da kasala. Wani irin ingarman namiji ne majiyi karfi. Koya ya motsa jiki sai kaga damtsen nan sun motsa. Dogon gashin sa dake tufke a tsakiya kansa ya kai dogayen yatsun sa ya cire band d'in. Kaman ruwa gashin ya biyo ya kwanta wuyansa luf mai tsananin laushi da tsantsi gashi bak'i sid'ik. K'ofar d'akin sa da yaji an buɗe alamun an shigo baisa ya juyo ba saida ya kama farar rigar dake cikin suit d'in ya fara cirewa. Jin shirun ya yi yawa ya wani irin juyowa a hankali yana balle ragowar botirin rigar da ya yi saura. Numfashin Aafiya ya wani irin tsarkewa lokacin da kwayar idonta ta fad'a cikin midnight Black nashi. Kut ta had'iye yawu. Hak'ika waya da labarai basa masa adalci sam. Don yanda ta gansa haka a zahiri , Sam ba'a kwatanta irin matsanancin kyau da Allah ya bashi. Mutum kaman shi ya yi kansa. Jan wani irin numfashi tayi sanda kwayar idonta ta sauka fatar cikinsa dake uban shining ga wasu uban 8packs kace zanasu a kayi. Kut ta k'ara had'iye wani yawun. Sannu a hankali ta ke yawo da idonta dukkanin wasu sassan jikinsa kafin idonta ya sauke kan kyakkyawar fuskar dake d'auke da wani irin full lips pink masu matuƙar shek'i. Hancin nan kaman biro tsaban tsayi ya tafi da manyan idanuwan da ko ita Albarka. Tsananin bak'in kwayar idan nasa da girman idon nasa idan yana kallon ka sai kaji kaman mai kallon ruhin ka. "Min ant?" Taji kakkausar murya sa kaman saukar aradu. D'an firgita tayi saboda yanda tayi nisa wajen bege. Saida ta lashe leb'en ta daya bushe kamas ta buɗe baki zatayi magana , kaifin idonsa da yanda ya kafeta da manyan idanuwan sa, fuskar nan babu wani emotion yasa taji fitsari na neman kwace mata. Had'iya ta k'arayi ta k'ara buɗe baki amma ko kalma d'aya ta kasa fitowa. Gaba d'aya a firgice take da tsananin kyawun sa da kuma kwarjinin sa . Dif,dif ya nufota kaman wani bijimi. Aafiya batasan sanda ta juya da wani bala'in gudu ba tayi waje. Turus ya tsaya inda ta bari ya kafe k'ofar da ido. Wacece ne kuma wannan harta samu ikon shigo masa d'aki haka kai tsaye. Duk cikin masarautar nan ansan yanda baya son mata suna masa aiki. Why Malika zata turo masa ita don yasan bazata wuce wata Baiwar ba. To amma anya Baiwa ce? Yanda ta chaba ado haka. In har bai manta ba harda gwala-gwalai ya gani a wuyanta da hannun ta. Wacece ne wannan?. Kafin ya sake wani yunƙuri an sake buɗe had'addiyar k'ofar tasa an shigo kai tsaye. Wacce ta shigo yasa ya d'an saki ajiyar zuciya yana binta da kallo. Sanye take da alkyabba da aka Chab'awa ado da zinare. Alkyabba mai hula ce data rufe fuskatar ta ruf kaman rariya. Sannu a hankali ta maida k'ofar ta rufe saboda bayinta dake bakin k'ofar. A hankali ta juyo ta tako har inda Lk ke tsaye. Hannu ta kai ta yaye hular alkyabba data rufe mata fuska. "RAINHA" (ma'ana Sarauniya da harshen PORTUGAL). Kyakkyawan murmushi tayi masa ta d'ago hannun ta daya sha ado da gwalgwalai ta shafa fuskar sa. Tsananin kyawun ta saiya firgita duk wanda ya ganta. Saboda haka ne take rufa fuska. MATILDA baturiyar k'asar Portugal ce. Sanadin had'uwar ta da Sarki KHALELULLAH ta musulunta har sukayi aure shekara takwas da suka wuce. Matilda ta girmi MALIKA nesa ba kusa ba don tayi shekara 50, amma zakayi mamaki idan ka ganta baza kace tayi shekara 25 da biyar ba. Kullum yarinya take k'ara zama ga wani irin shirtaccen kyau da take dashi mai firgita maza da sasu zama bayinta. Tunda ta shigo masarautar ABU DHABI ta shiga jikin LK sosai ta zame masa tamkar uwa. Kusan a yanzu yafi amfani da maganan ta akan ta Malika. Sosai sun samu sabani Saboda hakan, amma duk yacce Malika tayi LK baya tab'a daina bin umarnin Matilda. Da yaranta na Uwa wato Portugal tayi masa magana don sosai ta koya masa yaren. "Quem é aquela garota que acabou de sair do seu quarto?" "Wacece naga ta fito daga d'akin ka yanzu?" Kafin ya bata amsa suka tsinkayi muryar Malika data shigo ita da Aafiya basu kula ba. "Matar sace" Da azama suka juya suna kallon Malika dake takowa cikin izza da Mulki Aafiya b'oyenta. A tare suka maimaita. "Mata?" "Wife?" Ran Matilda sosai ya b'aci. Wato Malika saboda taga bata nan taje garin su can Portugal wajen iyayen ta shine tayi masa aure bata sani ba?. Wato Malika bata tsoron abubuwan da suke faruwa duk lokacin da LAMEEN ya yi aure. Ido cikin ido suke kallon juna ita da Malika kafin ta maida idonta kan Aafiya. Wani irin kallo ta watsawa Aafiya da Allah kaɗai yasan abunda ke cikin ranta. Rai a b'ace ta rab'a ta gefensu ta fice daga d'akin. Lameen ji ya yi kaman ya rushe da kuka yana kallon mahaifiyar tashi dake kallonsa babu alamun wasa tattare da ita. "Samu guri ki zauna Aafiya " Babu musu ta zauna kan wata had'addiyar kujera . Hannun sa Malika ta kama ta zaunar dashi kusa da Aafiyan. Baki ya taune ya k'ara matse rigarsa da bai gama cirewa ba. Zama tayi kujerar dake fuskantar su tace "Ga Aafiya matar ka dana aura maka ita yau da safe. Dukkanin wani tunani dake ranka ka ajiye sa gefe don bata amince da auren ba saida tasan kome ke faruwa. Du da haka tace tana son ka a haka zata zauna dakai. InshaAllahu zamu cigaba da Addu'a har Allah ya kawo mana sauki. Yanzu lokaci ya yi daya kamata ace ka ajiye iyali. Girma ka ke Lameen ba yaro ka ke komawa ba. Lokaci ya yi daya kamata ka hau kan kujerar mahaifin ka duk rashin sonta da ka ke" Miƙewa tayi tsaye tana kallonsa ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai tsabar bak'in ciki. Wai sai yaushe Malika zata gane shifa mata ya tsanesu ne in general, saboda wata yarinya data tab'a shiga rayuwar sa wani lokuta da suka shud'e.Numfasawa tayi ta k'ara cewa "InshaAllahu auren ka da Aafiya babu komai sai alkhairi. Zansa yanzu a kawo muku abinci. Ina mai umarta ku, ku fara yin sallah don neman tsari daga dukkanin wani sharri na b'oye dana fili. Naga kaman wanka zakayi Aafiya ki had'a masa ruwa ya yi wanka. Allahumma barikum" Kai Aafiya ta d'aga cikin girmawawa duk irin matuƙar tsoron dake cinta. Kallonsa Malika ta k'arayi ganin har zusa lokacin kansa na k'asa ya kafe kafet da ido. Girgiza kai tayi ta juya ta fice rai a dagule. Shiru ne ya ratsa d'akin bayan ficewar Malika. Aafiya ta cigaba da kallon sa a kaikaice ta k'asan ido tana k'ara kistima matsanancin kyau da yake dashi. Gefe tana shak'ar daddadan kamshi da jikinsa yake na vanilla and flowers. Tsaban yanda kamshin ya game jikinsa ,ya yi wanka ko baiyi ba, yasa turare ko aa. Koda yaushe kamshi yake mai sassanyan dad'i. Sama da minti d'aya suka d'auka haka babu wanda ya yi motsi sai bugun k'irjin ta dake k'ara tsannanta. Can ya miƙe bai kalli inda Aafiya take ba ya nufi wata arniyar glass door. Ko ba'a fad'a mata ba tasan hanyar banɗaki ne. A hanzarce ta miƙe ta bishi cikin banɗakin daya shige. Sarkewa numfashin ta ya yi ganin tamgamemen banɗakin data shiga dake d'auke da wani irin jacuzzi kaman swimming pool. Bata tsaya tunanin Lameen ba daya juyo yana kallonta da b'acin rai ya taune leben sa na k'asa. A hanzarce ta had'a masa ruwan wanka ta fice da sauri don ji take kaifin idonsa na neman shek'ata barzahu. Da ido ya bita harta fice kafin yaja wani dogon tsaki kaman mace ya hau cire ragowar kayan dake jikinsa. B'angaren Aafiya d'akin ta dawo tana binsa da kallo. Tabbas duk kuɗin iyayenta. Duk fice fice da take kasashen duniya buɗe ido, wani abun ma b'ata taba ganinsa ba sai a nan. D'akin Lameen yaci sunan sa Aljanna duniya. K'ofa aka kwankwasa ta matsa da sauri ta buɗe. Wata baiwa ce ta shigo da wasu a bayanta riƙe da kayan abinci. Da girmawawa suka jera kayan suka fice. Guri ta samu ta zauna tana jiran fitowar sa. Sama da minti ashirin ya d'auka cikin banɗakin duk ta kotsa. Finally taji motsin tab'a k'ofar sa. A hanzarce ta daga kai ta kafe k'ofar da ido. Sai gashi ya sanyo kai in all his glory sanye da tawol dake d'aure k'ugunsa. Sai d'an k'arami dake rataye a wuyansa yana goge jik'akk'en gashinsa dashi. Wani irin had'iyar yawu tayi tana binsa da kallo tun daga k'afafuwansa harzuwa k'irjin sa. Tsabar yanda ta shagala da kallonsa bata lura da yanda ya ke mata wani irin kallo ba. Saida ta d'aga idonta zuwa fuskar sa. Lokaci guda ta saki wani irin mummunan ihu da saida gaba d'aya masarautar ta d'auka. Kafin Lameen ya yi wani yunƙuri ta zube k'asa a sume. Numfashi ya fesar mai zafi cikin ransa yace. 'Here we go' A hanzarce ya yi k'ok'arin numfar inda take yashe a k'asa, amma kaman wanda aka kafe ya kasa motsi. Lokaci guda kuma ya kai hannu ya rik'e wuyansa da yake ji kaman an shake shi. Kakari ya fara yana wani irin tari daidai yaji muryar Malika na magana da bada umarni a b'alla k'ofar. Dazun ma daya sa suka shigo saboda yabar muk'ullin a jiki ne. Bayan an kawo abincin Aafiya ta ciresa ta dawo dashi ciki. Luu shima nashi idon suka fara rufewa numfashi ya masa wahalar fita. A take fuskar nan tayi jazur da ita na tsaban wahala . Har zuwa lokacin kokawa yake da koma menene yake tunanin ya shakeshi ta baya. To amma baiji komai a wuyan nasa ba sai hannun sa kawai. Gaba d'aya ya yi k'asa shima daidai Malika ta dannu kai d'akin. Ihu tasa da kiran sunansa tayo kansa a guje kafin ta k'araso tuni ya zube gurin a sume. A tare Malika da Matilda suka k'araso inda ya zube a sume. Da k'araji Matilda ta bada umarni a kira family doctor nasu. Aizak da Aryan suka fad'o d'akin suma a guje don tuni labari ya riske so. Saidai Matilda ta k'anannade shi kan cinyarta ta hana kowa ya tab'a shi sai Dr ya shigo. Tsaban taikaci Malika ta zuba mata ido ta kasa cewa komai. Rai a b'ace tasa aka d'auko Aafiya akayi waje da ita. Sosai gabanta yake mugun fad'uwa duk yanda take k'ok'arin danne wasu zafafan hawaye da suka cika mata ido saida suka zubo. Kan gadonta tasa aka kwantar da Aafiya da bata ko motsi. Duk a tunanin su itama ta mutu kaman sauran matan. Amma na Aafiya yafi ko wanne sauri don su alamu sun suna sai ya fara kusantar su hakan ke faruwa dasu. Yanda taga Aafiya da kayanta batayi tunanin wani abu ya shiga tsakaninsu ba tukun. Tanajin Aryan ya rungume ta ta baya. Hawaye ne kebin fuskarsa shima. Aizak yana can tare da Lameen da Matilda ta kafa ta tsare a kansa. Likitane ya shigo a guje ya yi kan Aafiya. Kallo d'aya ya yi mata ya yaga yanda take numfashi kad'an sai ka zuba ido sosai zaka kula. Numfashi ya sauke a hankali yace da Malika tana da rai. A gaggauce ya bata taimakon gaggawa. Malika ta sauke numfashi mai k'arfi tana kiran sunanyen Allah. Wai wannan wane irin abu ne?. 𝗚𝗨𝗗𝗨 𝗡𝗔 𝒜𝓀ℯ. 𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵♡︎𝓿𝓮 26/30. Saida Lameen ya kwana biyu a sume sannan ya farfaɗo. Matilda ta kafa ta tsare ko nan da can bata matsawa. Malika ta kasa jurewa tayi mata tas ganin yanda k'arfi da yaji take neman rabata da d'an ta. Sosai sukayi fad'a Matilda tayi fushi wunin ranan ko hanyar Lameen batayi ba. A daren ranan ya farfaɗo twins dake d'akin a guje suka rungume shi. Da ido yake binsu yana son tambayar su ko Aafiya ta mutu. Aizak daya fuskanci abunda ke cikin ransa yace. "Ya akhie. Ka kwantar da hankalin ka wannan karon koma menene ke bibiyar rayuwar mu bai samu nasarar kashe matar ka ba" Numfashi ya sauke a hankali ya koma ya kwanta. Aryan dake waya ya mik'o masa da sauri yana cewa 'gashi' da ido yabi wayar kafin ga k'arata a kunne. Wani irin numfashi ya ratso wayar mai k'arfi murya Zain ta ratsa dodon kunnensa cike da damuwa yace "Alhamdulillahi ka farfaɗo?" Lameen bai bashi amsa ba yace "I'm coming " "Dude ina Nigeria. " "I know gani nan zuwa" Baijira Lameen d'in ya k'ara cewa komai ya kashe wayar. Yana buk'atar guri da zaiyi breathing air. Away from all this. Malika ta fad'a d'akin cikin sauri. Kai tsaye ta rungume shi tana masa ya jiki. Rabonda ya kebe da mahaifiyar sa haka shi kanshi ya manta. Don haka ya yi luff a k'irjin ta. Ita ta sahi a gaba yaci abinci ya yi sallah. Da kanta ta had'a masa ruwa ya yi wanka ya fito. Saida ya gama shiryawa a taushe yace mata zai tafi Nigeria don ya samu salama a zuci. Bata musa ba ta amince masa tana son ta kwato d'anta daga hannun Matilda dake nemanyi mata k'ak'anakayi. Aafiya dai har zuwa lokacin bata farfaɗo ba saidai numfashinta ya daidaita. Idan ka ganta kaman wacce ke bacci. To sanda ya diro Nigeria baiyi tunanin Fate zai k'ara had'ashi da macen da yake nema ba ruwa a jallo saboda wani unfinished business dake tsakanin su. Present . Numfashi Zain ya sauke yana cigaba da kallo Lameen da harzuwa lokacin idonsa ke a lumshe. Tabbas Lameen na tare da sirri mai ban aljabi. Ga dai kyau iya kyau Allah ya bashi, amma yana neman tashi a banza. Duk sanda ya yi arba da wata mace sai wani mummunan abu ya faru. A yanzu ma yasan babu tantama Jaleela taga wani abu tattare dashi da ya yi sanadin firgitar ta harta fice haka a guje. Wayarta k'irar iphone x ya juya a hannun sa da tunanin hanyar da zaiyi ya buɗe ta. "Let me help you with that " D'agowa ya yi ya kalli Lameen daya mik'o masa hannu. Kai ya d'an jinjina ya mik'a masa wayar. Wato Lameen ba despite duk wannan abun da yake faruwa dashi, he's a damn genius and hacker. Ya iya hacking na ko wane abu sai dai in baiga dama ba. Wayar ya juya a hannun sa ya yi d'an murmushi. Dan danne danne ya yi saiga wayar ta buɗe. First abunda ya fara cin karo dashi jikin screen d'in wayar shine hoton ta da Anees. Suna sanye da k'ananan kaya kansu babu d'an kwali daga ita har Anees gashin su a sake ya bazo ta ko ina ga iska da take kad'ashi. Hoton da sukayi ne wani amusement Park data kai Anees. Ta d'agata suna dariya akayi hoton. Sunyi bala'in kyau kaman wacce suka zo daga wata duniyar. Ido ya zubawa hoton yana jin wani irin abu na ratsa shi yana kallon Anees. 'She has a daughter?' (Tana da y'a?) Ya furta a fili ya d'ago yana kallon Zain daya zuba masa ido. Cikin rashin fahimta yace "What. Wacece take da y'a?" Fuskar wayar Lameen ya nuna masa yana tunanin . Idan har tana da y'a? Ta tab'a aure kenan? Ko kuma a hanyar prostitution(karuwancin) ta sameta?. Haka nan kawai yaji wani abu ya chake shi a zuciya ya yi saurin kawar dashi yana d'an girgiza kai. Why do i care?. Tunda Allah ya sake had'amu, zanyi making sure life nata is a nightmare har sai ta durkusa ta bani hak'uri. Smirk ya saki daya sa Zain shan jinin jikinsa yace "Me ka ke tunanine?" "Nothing " Bai bari Zain ya k'ara cewa komai ba ya miƙe ya fice daga d'akin rike da wayar a hannun sa. Yana fitowa kuwa guards nashi suka kawaye shi. Duk inda ya wuce ya zama abun kallo. Mata duk sun mutu a kansa maza kuma suna burin ina ma dai sune. Suna kallo ya shige shegun motocin sa dake fake a gurin. K'aramar motar Pecanto dake kusa da tashi ya zubawa tsumammun idanuwan sa. Motar waye wannan har ta iya fakin kusa da motocin sa?. Hmm. "Find who's car is this" (ka nemo motar waye wannan) Yace da right hand Bodyguards nashi. Da girmawawa yace " yes, Boss) Har suka fice daga club d'in

Chapter 3 of 7