makale jikin lab coat nata,
Ajiyar zuciya sukayi A tare duka su biyu, har sai da yasa hankalin likitan ya dawo garesu, Murmushi ta musu hadi da nuna musu gurin Zama,
"Sannunku koh, waye Mare lpy a cikin Ummu ta Nuna Maryama datake rike a jikinta tana sharban kuka, Meyake damunta,?
Kasa magana dukansu sukayi sbda kukan da sukeyi, har Doctor din ta tausaya musu matuka, da kyar Sumayya tayi karfin halin cewa fyade akama yar uwata,
Da sauri Doctor ta dago kanta, hadi da cire glass din fuskanta
"Suko wasu marasa Imanin ne suka mata basu tausaya ma situation din datake ciki ba a matsayinta na Sickle cell, tashi muje ki hau gado in dubaki, lallai ma kina da karfin hali, Ummu ne suka kamata suka dorata akan gado, tasowa Doctor din tayi,
"Ya Subhallah Amma ba mutum daya yayi miki fyaden nan ba, gskya kina da bala'in karfin hali da dauriya, yanzu sai anyi miki dinki, sannan bazan kwantar daku ba zaku koma gida, sannan zan rubuta muku Magani,
Godiya suka mata, sosai sbda tayi musu mutunci sosai,
*************************
ZARIA BIRNIN SHEHU
dai dai sunga isowar Motan ta, suka tashi suka ruko Shatu Kwata Kwata bata san inda kanta yake ba, sai jinin dake zuba ta kasanta, da sauri Doctor Nusaibat Habibullah Fulani ta fito Daga motar ta ta iso gareta, "bayin Allah lpy me ya sameta, Duk da Shatu tana cikin Halin ciwo bazata manta da wannan muryan ba, Da sauri ta dago kanta bakinta na rawa gurin furta "HAJJO!!!
Cikin tashin hankali Doctor Nusaibat take kallonta, tana Nunata da yatsa, "Sha,,,tuuu!!
Kece haka???? ✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Like
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu9333
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA'U (OUM KHADY)
PAGE 35 TO 36
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan page din nakane Masoyin Asali true love Never end, Allah ya barmun kai ya tsareka ya kareka a duk inda kake, fatan Alheri (Mubzeey)
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
"Dama kina raye baki mutu ba, da sauri ta kira Nurses suka zo da emergency bed aka dorata akai, nan da nan ta shiga motar ta ta bisu,
Ana shiga da ita Dakin Doctor Nusaibat tana karisowa, dama already Dama an gama hada mata komai da zata bukata tana Zuwa, ta fara dubata ta tabbatar miscarriage tayi kuma tana bukatan jini, nan da nan tayi waya aka kawo mata blood Daga lab tayi mata allurai tayi mata Setting na Blood, fitowa tayi tana tanbayar ina wanda suka kawota aka cemata ba'a gansu ba, komawa Office din tayi ta zauna ta kurama Shatu ido duk ta Rame ta yi baki kamar ba Shatun Baffa ba Fara kaman a taba jini ya fito, gata yar duma duma Amma yanzu ta zama tamkar skeleton,
Allah ya tashi kafadunki Shatu ta fadi haka, hadi da kallan wayanta da ake kira, dauka tayi hadi da karawa a kunne
"Hello Yes I am NUSAIBAT HABIBULLAH FULANI, oh sorry wlh na manta da wanna Meeting din but zanyi kokari inyi Sending my P.A na ta wakilceni dama already yau zata sauka a Abuja Daga Dubai, jirgin karfe biyu, zata sauka,sai kuje ku tareta a Airport, ok tom bye,
*************************
After three weaks later
Su Sumayya suka koma Asibiti domin kara ganin Likita, bayan sun gama komai da ya kamata suka isa ga Doctor, Suna shiga ta tarbesu da fara anta "well Come my patient yau da kanta ta hau gadon ta kwanta, Doctor ta fara dubata, dago kai tayi cikin tashin hankali "ya Allah Maryama what happen, kamar Yoyon fitsari naga kinayi hawaye ne ya zubo ma Maryama, "tace Aunty tun randa muka koma gida bayan na zauna na tashi sai naga na jike gashi Kwata Kwata ban rike fitsari, hankalin mu gaba daya ya tashi,
"Ya Subhallah Innalillahi wa innah ilaihirraji'un, tabbas kin kamu da Yoyon fitsari, kuma sai an miki aiki akalla zai iya kai Dubu dari da Hamsin indai anan za'a miki, cikin tashin hankali gaba daya suke kallonta inda Sumayya ta duke a gurin tana ta kukan da ba sauti,
"Amma taimakon da zan muku dayane shine akwai wata Kawata, Doctor Nusaibat Habibullah Fulani da take zuwa A.B.U teaching hospital Zaria, tana yin wannan aikin kyauta fisabilillahi ga irinku marasu karfi, zan rubuta muku takarda ku tafi Zaria Kuna zuwa ku nemeta ku bata takardan nan kucemata Doctor Raleeyat ta turoku, don dai ni yau zan bar kasan ne, akwai wani Business da Mijina zai fita yi a kasar Ingila, da tare zamu tafi daku Allah ya bata lpy, but Matukar ta ga Doctor to Insha Allah zata mata aiki kuma Za'a samu nasara tunda ita kwararriyar likitan Matane, karku damu kunji, komai yayi tsanani maganin shi Allah,
"Mun gode Doctor Allah ubangiji ya saka da alheri ya daukaka ki, in Ana samun irinku masu tausayi a cikin Al'uma da bamu shiga halin da muke ciki a kasar mu ba, mun gde sosai.
Bayan ta rubuta musu takardan da zasu tafi dashi Zaria ne suka mata salama suka juya zasu tafi, sai Sumayya ta juyo da sauri tace "Aunty don Allah kibamu Number ki,
"Ok ta rubuta mata a paper ta bata, sukayi mata sallama suka tafi,
***********************
BIRNIN MISRA
"Jaddi meyasa zaka hana Zuwa garesu Alhalin yanzu ne suke bukatar taimako? Ya karishe maganar yana bata rai,
"Ya kai Sadaukin Jarumi kasani shi Bawa bai taba tsallake kaddaranshi to kaddaransu ne haka kuma Ubangiji bai bamu daman taimakon su, shiyasa Kaga na hanaka in har Bawa kuma yace zaiyi shishshigi cikin lamarin Ubangiji sai Allah ya karbi Rayuwarka, kawai kayi hkr mu ga ikon Allah, Fasihat ne ta shigo a hargitse ko lura da Mujaheed batayi ba,
"Jaddi ka fadamun ni Wacece, wai Dama ni ba yar gidan nan bane,?
"Yar Albrka waya taboki, duk wanda ya fadamiki haka karya ya fadamiki don ke din nan kinfi kowa iko a gidan nan kuma kina da Babban al'amari a tare da rayuwarki, wanda zan bayyana miki nan bada dadewa ba,
Mujaheed ne yazo ya dagota, hadi da share mata hawaye, "karki damu Seeehat komai yayi farko zai zo karshe Kinji, mubi komai a hankali, har lokacin da Jaddi zai warware mana al'amarin nan,
"Yauwa Jaddi Maryamah kawata tana bukatar taimako,
"Na sani Amna bamu da halin taimakonta,
"Meyasa ya Jaddi zakace haka,?
"Bana san yawan tanbaya zan shiga Daga ciki,
"To a fito lpy, tashi sukayi suka tafi Mujaheed na mata bayanin yanda sukayi da Jaddi, dai dai Zankadaziyyatu ta iso tana huci ta bangaji Fasihat kasan cewar tafi Fasihat karfi da komai yasa tayi baya zata fadi Mujaheed ya riketa, tuni ta bace kaman walkiya, karkada kai kawai Mujaheed yayi, suma suka bace,
***********************
KAUYEN WURNO
"Kunajina koh yau ina son mukai hari zuwa kauyen dake makotaka damu, domin ina bukatar Karin garuruwa, a cikin garuruwan da muka kwace, angama ya shugaba,
***********************
BIRNIN KANO
GIDAN GOVNOR
"My Excellency game da maganar fitan Aslm UK ne zuwa shakatawa yace yana so su tafi Shida Abokanan shine, to Kaga dole za'a hada musu Visa su dukan su, sai kudin kashewan da zasu bukata,
"Eh munyi magana da Mai kula da shige da fice na kasa da kasa cewan ya gama hada musu Visa, kudi kuma yanzu zanyi mai transfer na Ten millions I hope zai isheshi,?
"Eh ya ishesu my Excellency nima dama ina bukatar kudi zan danyi wasu hidiman dasu,
"Hajjaju me zakiyi da kudi ina ce kwanan nan aka muku Salary naku na matan gobnoni, kuma kin san Zamu fita Campaign kwananan tunda kin san Zabe ya matso koh, shi kuma talakar kasar mu tamkar kaji ne da an watsa musu tsaba shikenan sun mance zaluncin da ka musu a baya kinga dole kuwa, mu saki kudi duk da Zanjabiluuu ya bani tabbacin kakkau ya ce mune da nasara Amma in kana da kyau ka kara da wanka,
"Hakane My Excellency nima ina son inje maka gurin Boka dan tsito ne kasan shima sha yanzu magani yanxu ne,
"Pappah!! Pappah tana tafe tana tangadi ta kariso inda suke kamar zata fado ma iyayen nata akai, Nima ina bukatar kudine zanyi Birthday, ta karishe maganar tana zama a kusa da Uban nata,
"Wai Ikram yaushe zaki bar shaye shayen nan ne iyeeh nace miki bana so fa, nawa kike bukata?
"Ai My Excellency bazata daina ba ya zama jinin jikinta,
"Dallah Malama ba ruwanki na kulaki da na shigo ba gara ni Shaye Shaye nakeyi ba, ke da Pappah wayasan me kuke aikatawa,
"Kinga Baby rabu da Mammah nan naku nawa kike bukata,?
"Million Ashirin zaka bani kacal,
"To baki da matsala zan tura miki Kinji yan matana, tashi tayi tana tafe tana tangadi, har ta shige bedroom din dake falon ta haye gado ko cire takalmi batayi ba, sai barci,
Aslm ne ya shigo ya Tara uban gashi a kanshi ga wani sarka da yasa da dan kunne a kunin shi ga ear phone daya makala a kunnen shi, ga gashin ya mai tiri ga wani aski da akayi ba ko tsari,
"Hi Pappah Hi Mammah I hope an gama mun abunda na fada miki Mammah, don ni ban so in kai two a Nijaa,
"Gaye dan gata ba dole ba ai an kammala komai yanzu tafiya ya rage aje a huta kayi komai ba komai gay son in kana da kudi ka wuce wulakancin Duniya, kai harma dana lahira,
Niko nace wa'iyazibillah Aiko Mammah kin tabe, ai lahira ba Duniya bace,
Ranar da Ubangiji ne kadai mai mulki mai iko,
Kamar yadda ubangiji yake fada a ranar alkiyama
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
LIMANIL MULKUL YAUM
sai dukkan halittu suyi shiru ba mai amsawa sai Ubangiji ya Ansa da kanshi yace
LILLAHI WAHIDUL KAHHAR,
to ita dai Mammah ta manta da wannan Nafsin kam
Allah kasa mu gama da Duniya lafiya ya rufamana Asiri Duniya da lahira🙏masu hali irin na Mammah Allah ya shiryesu,✍️✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA'U (OUM KHADY)
PAGE 37 TO 38
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
Wannan page din nakine karamar uwa Abokiyar wasa Baba Zulai ina yinki sosai Allah ya barku tare😍😍💖💖
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Isan su Airport kenan Shida Abokanan shi, suka samu gurin Zama don jiran lokacin da flight nasu zai tashi,
Karfe biyu dai dai aka fara announcement na passenger su matso kusa, Aslam ya fara mikewa, yace ma su KB su taso su tafi in ka kallesu bazakace Yaran musulmai bane, sbda yanayin shigan da sukayi,
Sun isa su ko tantancesu ba'ayi ba suka shige jirgi, dai dai zasu shiga jirgin Sumayya ya hango tana mai wani irin mugun kallo na tsana, murza idon shi yayi, yaga tabbas fa itace to meya kawota Airport, daurewa yayi ya shige jirgi, yana sake sake a ranshi shidai a sanin shi yasan ba abunda zai kawota airport,
Tunanin shi da ganinshi da hankalin shi ne sukayi mai tafiyan wucin gadi sakamakon Sumayya da ya gani a cikin jirgi zaune kusa da sit dinshi, karfin hali yayi ya karisa kusa da ita ya Zauna, duk jikin shi yayi sanyi, Abokanan shi nata magana shidai kawai yayi shiru, yana kallon Sumayya da ko kalan shi batayi ba, tana ta Karatun Azkar dinta a cikin hisrul Muslim, tasha dogon hijab dinta Popul,
Gaba daya ji yake soyayya yarinyar da kyawunta yana ratsa jijiyoyin jikinshi, burin shi kawai baifi ya mallaketa ba, Dis is d first time da Aslam ya fara tunanin Aure a rayuwar shi, gashi yaji yana bala'in shakkar Yarinyar, da tsoronta ga kuma wutar sonta a ranshi, gashi ya zaluncesu yasa bazata taba sonshi ba,
Waigowa yayi suka hada ido da ita, wani matsiyacin kallo ta mai, wanda sai da gabanshi ya fadi, sai yaga ta kara wani masifaffen kyau,
Niko nace aiki ya ganka Aslam muje zuwa dai,
Haka jirginsu ya tashi ya Lula cikin sararin Samaniya sai UK yayi da Aslam gaba daya hankalin shi ya tafi ga Sumayya inda ita kuma ta dukufa gurin Karatun Hisrul Muslim dinta sai ince readers sai mun hadu a UK don dauko muku me zai faru a can, inda sister Oum khady zata cigaba da koro muku bayanin yan Nigeria, nidai nayi UK don dauko muku shaw, Daga nan inga gari😂
*************************
Ummu ne ta fito da shirinta ita da Maryama duk tabi ta rame,
"Wai me kikeyine diyar Albrka kiyi ki fito mu tafi Kinsan ina so mu isa Zaria nan da wuri ne inda zamu samu muga likitan nan da wuri,
"Ummun mu ganinan zuwa yanzun nan ina duba takardan data bamu ne wanda zamu dashi ta fadi haka tana fitowa tare da Daura Nikab din dake hannunta,
Jerowa sukayi suka fita hade da kulle kofan gidan, suka gangara da kafansu kasancewar Asubace ba'a dade da idar da sallah ba gari ko gama wayewa baiyi ba, shiyasa sai da suka gangara bakin titin layinsu da kyar suka samu Taxi din dazai kai su inda zasu hau Mota,
Suna isa tasha suka tarar da motan dama sauran Mutum uku ne a Tashi, suna zuwa suka dauki hanyar Zazzau birnin Shehu,
***********************
ZARIA GARIN ILIMI🙈🙈
"sannu Shatu, I hope yanzu ba'abun da ke miki ciwo, yanxu tsawon wata uku kenan kina jinya, sannan Mahaifarki ta samu Matsala bazaki kara haihuwa ba,
"Shatu har yau kinki bani labarin abunda ya faru dake, in na tanbayeki sai ki kama mun kuka don Allah ki fadamun,
Share hawaye Shatu tayi ta dago rinannun idanuwanta ta zubasu a kan Doctor Nusaibat,
"Hajjo rayuwata ta shiga cikin kunci da garari bayan rabuwar mu dake, yan kidnapping din nan basu kasheni ba kamar yadda mukayi tunani ni dake, sai suka daukeni Daga wannan dajin zuwa dajin Birnin gwari suka mai dani tankar baiwa girki da duk wani abun da suke bukata ni zan musu, sannan na zama abun korewar sha'awar su a rana sai suyi Anfani dani fin sau goma tun ina suma har nazo na daina, kuma duk kansu wanda yaji sha'awarshi a kaina yake saukewa, sun min ciki yafi a kirga yana zubewa, ta karishe maganar cikin kuka, da takaici yayin da Doctor Nusaibat itama take kuka, bayan wasu shekaru da Jami'an tsaro suka taso yan uwansu wanda suke Zamfara da Sokoto sai sukayi gangami suka tafi Sokoto don su taya yan uwansu yaki da Jami'an tsaro, haka suka tasani muka tafi randa muka isa Sokoto komai ya dawo mun, don bazan taba mancewa da garin Wurno ba, inda aka kashe mun dukkan ahali Daga ni sai Baffah na muka tsira Daga baya suma suka kashemun Baffa, bayan tsawon watanni da sukayi Ana fafatawa tsakanin su har suka samu galaba akan Jami'an tsaro kasancewar duk wani shiri da Jami'an tsaro zasuyi suna da Wanda ke fadamusu, sbda suna daurin gindi a gurin wasu manyan yan siyasa da Jami'an tsaro da sarakunan gargajiya, duk da suma anyi musu barna sosai don ankashe su da yawa, ciki harda ogan mu, Daga nan na cigaba da Bauta har ranar da Allah ya kawo ni nan don nidai bazan cemiki ga wanda suka kawoni ba, don ban san halin da nake ciki ba.
Kuka sosai Doctor takeyi,
"A kullum ranar Duniya sai na Samu case din fyade wa Mata da kananan yara, da Case din bata yara Maza, da case din rashin tsaro, kai Duniya ina zaki damu gashi mun kasa kawo sauyi a kasar mu komai Kara tabarbarewa yakeyi, ko kayi yunkurin daukan mataki Daga sama za'a kiraka a dakatar da kai, Allah ka dubemu da idon Rahma ka kawo mana wanda zasu kawo chanji a kasar mu, Ameen ya Allah,
"Yanzu na riga nama Driver na magana zai kaiki gidan mu dake cikin City, ki zauna gurin Kakata Hajiya yayah, sbda ni yanzu ina son zanje Kaduna ne Daga can zan wuce gida sbda Na kwana biyu a nan sbada jinyarki Insha Allah Next time in na dawo sai muyi mgna a tsanake, Kinji ki saki jikin ki tamkar kina gida Kinji, wayar ta ne tayi kara ta Daga "haba Cherry Kaima kasan I miss u too much ina yan biyu na da Aunty su a shafamun kansu, kai ni ba ruwana ai da Hamman sun nan baifa kirani ba don nayi mai fada nace yazo ya duba Mamansu bata da lpy, shine yaki zuwa yaki kuma kirana zan dawo ai sai naci gidan su kam,
To naji na hkr amma yayi abunda na sashi, ok by I love you too my Cherry, ✍️✍️✍️✍️✍️
Share
Comment
Vote
Follow me on whatpad please
ZainabSalihu933
Yar mutan zazzau ce 😍😍😍
Part one free
💞💞💞WAZAN AURA💞💞💞
Fictional 😢
Traditional 🏚
Politicians 🇳🇬
Love💖
Story
WRITTEN BY
ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU.
DEDICATED BY
RALEEYAT YA'U (OUM KHADY)
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
PAGE 39 TO 40
*************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
UNITED STATE OF KINGDOMS
Sun sauka a kasar UK kimanin karfe Hudu na yamma direct gidan Pappah dake cikin kasar suka wuce yayin da ya dunga raba ido yaga ta ina zata bullo gaba daya ya nemeta ya rasa, har suka wuce gida,
Suna isa suka tarar da duk wani kayan maye da suke bukata an tana darmusu ga yan matan turawa nan kala kala, suna isa ba maganar Sallah suka hau Shaye Shayen su, suka kure kida a gidan inda kasan gidan Club yan matan nan sai rawa sukeyi abunsu, gaba daya sun bige, nan da nan kowa ya ja nashi budurwan suka fara badala.
*************************
NIGERIA WURNO
"Ke wai meke damunki ne kwana biyu duk kin canza in mun bukaceki sai mu nemeki mu rasa?
"Kayi hkr Oga banda lpy ne,
"Shine baki magana ba kina ganin Doctor jiya yazo ya dubamun yarana wanda sukayi rauni, mtswww tsaki yayi ya kara gaba, lallabawa tayi kasancewar darene ta fito Daga dan bukkan da take hura musu wani abu tayi wanda suke gadin gurin sunata kaiwa da dawowa, ga haske a gurin kaman rana tana huramusu suka bingire da barci, da sauri ta karishe cikin wani bukka, ta shiga wani mutum ne a kwance shiba matacce ba shi ba rayayye ba,
Wani ruwa ta fito dashi a wani kwarya, ta fara tofa Addu'a a ciki Bayan ta gama ne tayi bissmillah ta fara yayyafa mishi, tana wasu Addu'oi can ya fara motsi a hankali a hankali ya gama bude idon shi, da sauri ya tashi yana salati, ya fara waige waige,
"Zankadaziyyatu me ya faru me mukeyi anan? Ya jero mata tanbayoyi,
"Alhmdulillah da ka farfado lpy lallai kaidin dan baiwa ne ba kowa za'a soka ma wannan takobin ba yayi wannan tsawon shekarun yana kwance kuma, ya farfado hankalin shi bai gushe ba, Abunda nakeso da kai ka cigaba da zama haka, don Matukar suka san ka farfado duk wani aiki namu zai dawo baya, burin su zai cika mu kuma namu bazai cika ba,
"Hakane tabbas kin kawo shawara mai kyau haka za'ayi,
"Ni kuma zan dauki duk wani dawainiyar kawo ma Abinci ko sau dayane a rana, gudun karsu gano mu, ficewa tayi da sauri ta koma makwancinta,
***********************
ZAZZAU BIRNIN ILIMI
Sun isa zaria karfe takwas na safe inda suka isa cikin Asibitin koyarwa na Ahmadu bello teaching hospital karfe Tara da minto ci, bayan Isan su Asibitin ne suka tarar da Security gurin suka mikamai takardan da Doctor Raleeyat ta basu, bayan ya gama duba takardan ne ya dago yana kallansu a wulakance yace musu
"Irinku ne yan san banza bazaku nemi kudi ai muku aiki ba sai dai ku tsaya jiran na bati, to Hajiya ta koma Yola yau ita da dawowa ma sai nanda wata uku in tsaku biya kudi ku biya don ni Banga alamun rashin kudi a tare daku ba, in kuma zaku tsaya san banza to, bai kai ya rufe baki ba Sumayya ta fisge takardan tana huci,
"Har kai ka isa ka ajiyemu ka dunga fadamana magana wlh munfi karfin banza kawai wanda basu san darajan dan Adam ba, ba dole Ubangiji ma ya hadamu da shuwagabanni dai dai da mu ba, ace hatta talaka bazai Tausaya ma dan uwanshi talaka ba, ko yaya ya samu dama sai izgili, Kaima Allah ba yafi sanka bane akan mu Yasa ya baka wannan matsayin ka gane koh,!! Ta karishe maganar cikin fushi hadi da cema su Ummu kuzo mu tafi,
Juyawa sukayi jiki a sanyaye suka fito Daga Asibiti kowa ranshi ba dadi,
"Yanzu Ummu ya zamuyi?
"Tom hakanan zamu koma gida haka Allah ya kaddaro, har nan da wata ukun sai mu dawo,
"Haba Ummun mu yanzu haka zamu zurama rabin rai ido tana fama da wannan laluran har nan da wata uku, gskya bazan iya ba,
Haka suka dunga tattaunawa tsakaninsu har suka fita titi suka hau taxi zuwa hawa motar komawa Kano,
*************************
KANO TUNBIN GIWA
"Mai girma Zanjabiluuu zabe nata karatowa muna fatan mai girma kakkau yasani,?
"Kakkau ya riga ya tabbatar maka da cewa kai keda nasara Karka damu,
"Ngd mai girma Zanjabiluuu babu wani mai girma sai kai, kai ne mai yin yadda kaso,
Wa'iyazibillah niko nace Allah ne kadai mai girma kuma maiyin yadda yaso,
Bayan ya gama surkulenshi ya gama bokan ya bace, ya cire jajayen kayan jikinshi ya maida ainihin kayan shi, ya fito ya maida Kofar ya rufe,
"Excellency akwai fa matsala fa sbda talakawa sun fara bore game da rashin cika musu Alkawari da ba'ayi ba gashi har tenure namu ya kusa karewa,
"Hhhh kar ka damu Wakili muke da Nasara kai dai kawai ka zuba ido ka gani, ina son yanzu a bugo foam kaman Miliyan daya ace ma talakawa za'a basu tallafin Dubu dari dari kowa zai samu, bayan an raba foam din kar ya wuce mutane dari biyu zasu Amfana da tallafin kudin a tabbatar ko wace Local government dake cikin birnin kano An samu kamar mutum biyar biyar ko goma dasuka samu tallafin Kaga da munyi haka mun gama dasu kamar sun zabemu sun gama,
Ya Allah kira ga yan uwana mata da Maza haka fa shuwagabannin mu suka daukemu tankar kaji, duk wani wahalan dasuka sha Daga an watsa musu dawa sai su fara wawa su mance da su wayesu, ku zabi shugaba na gari kar kudi ya rudeku ku manta suwaye ku, ko don inganta rayuwar Yaran mu dazasu taso a gaba, sannan Muma mu gyara halayen mu, sbda duk wani hali da muke ciki mu muke jawo ma kan mu, mun saki Ubangiji mun kama rayuwar Duniya mun mance da cewa zamu mutu, Zinace Zinace yayi yawa Madigo, lud, zubar da jini kuma wai duk saboda Duniya mukeyi, duk wani zunubi da Mutanen da suka gabacemu sukeyi Ubangiji ya halakar dasu, to mu duka mun hada taya Allah bazai jarabcemu da masifu da bala'i kala kala ba,
Ubangiji yana cewa Daga lokacin da bayina su kauce hanya na gari suka fada hanyar bata ni kuma sai in jarabcesu da shuwagabanni wanda zasu dunga Azabtar dasu dai dai da abunda suke aikatawa, Koda sun zabi shugaba na gari ne, sai mu karkatar dashi ya koma Azzalumi wannan shine sakamakon mutane batattu,
Kamar misalin kasar mune da shugaban da muka zaba, mun kyautata mai zato munyi tunanin zai tsamo mu a cikin kangin talauci da wahala, sai muka ga akasin haka, kar muga laifin shi laifin mune da mu bijire ma Ubangijin mu, sai