Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ο»ΏPart one free πŸ’žπŸ’žπŸ’žWAZAN AURAπŸ’žπŸ’žπŸ’ž (THE BEGINNING) fictional😩 traditional 🏚 politicians πŸ‡³πŸ‡¬ loveπŸ’– story WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU. DEDICATED BY RALEEYAT YA'U (UOM KHADY) ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com MARUBUCIYAR :GIDAN GADO AND NOW WAZAN AURA INA TAWASSALI DA SUNAYENKA KYAWAWA YA ALLAH KA BANI IKON RUBUTA ABUNDA ZAI AMFANI AL'UMAR MUSULMI BAKI DAYA KA HANENI DA RUBUTA BA DAI DAI BA, IN DA NA FARA WANNAN NOVEL LAFIYA YA BANI IKON GAMAWA LAFIYA, Aunty na kanmu Allah ya Kara lpy da Nisan kwana ya Albarkaci Zuri'a (Aunty Hauwa) Na sadaukar da wannan page ga duk wani ko wata mai fama da laluran SICKLE CELL ANEMIA (sikila😭😭😭) Allah ya yayemuku wanga lalura, Kira ga yan mata da Samari please Taya Allah kiwo yafi Allah na nan ki tabbatar kunyi gwajin genotype before kuyi Aure, Allah ya bamu Zuri'a nagari Ameen πŸ‘πŸ‘ Wannan lbr kirkirarrene Kuma basirata ne duk wanda yayi dai dai da rayuwanshi to akasi ne, Inna gyarane sai ya gyara, kuma ban yarda wani ko wata ya juyamun lbr ba, πŸ’˜πŸ’˜PAGE 1 TO 2πŸ’˜πŸ’˜ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. "Wayyo Allah na Ummu ki daukota muje Asibiti karta mutu, "Uhmmn yanzu Sumayya ina muka ga kudin da zamu kaita asibiti kin san in munje ba kudi ba wanda zai kallemu, "wai Mutanen duniya yanzu Ummu basa taimako ne, wlh nima in na zama wani Abu nan gaba bazan taimaki kowa ba"Kull kar in Kara jin kin fadi haka Sumayya, wani Kakari da ihu da Wanda ke kwance tayi, duk sukayo kanta kakkafewa idonta yayi, Da gudu tayi Hanyar Kofar gidan ta fitowa taci karo da wani makocin su yana dan gungoro mashin dinshi dayayi faci, da gudu ta karasa gareshi "don Allah Mudi ka taimakemu Yar uwata ce bata da lpy ka taimaka mu kaita asibiti, "subhanallahi badai Sikilan nata bane ya tashi, "eh shine wlh suna karasawa suka ga Ummu tana rungume da ita tana kuka da sunbatu, "don Allah Maryama ki tashi karki tafi ki barmu a duniyar nan, "Kamata Ummu Sumayya mu kaita asibiti, "Mudi bamu da kudi fa, "kamata haka mu tafi Allah zai rufa Asiri, Sumayya yi Maza kitaro abun hawa kan hanya, da gudu Sumayya ta fita, su kuma suka kamo Maryama suka fito da ita tamkar da matacciya, sai a lokacin na karema ta kallo kyakyawa ce na ajin karshe sai dai daka kalleta zaka gane bata cika koshin lpya budurwa ce yar kimanin shekara Ashirin Amma sbda lalurar dake tare da ita zaki dauka yar sha hudu ce, Suna fitowa suka tarar har Sumayya tazo da me Nafef din, haka suka samu suka sata ciki yaja su, Sai Asibitin Aminu kano teaching hospital, Suna isa aka shige da ita, Sukuma suka tsaya a waiting room, Me napep ne ya biyosu "Hajiya baku bani kudina ba, "Nawa Zamu baka, "kudinku Dari biyar"Haba Mallam ga dai dari biyu nan, kayi hkr"gskya Hajiya Anmun son rai, wlh kuje ku da Allah, "Haba bawan Allah mare lpy fa muka dauko ba taimakone a duniya don Allah kayi hkr wlh shikenan mun badon haka ba dana cika ma, karkace ka barni da Allah, "Oho nima fa mai nake sawa a Napep din nan ba ruwa ba, ehe, wata matane dake zaune take jin duk abunda yake faruwa, ta ciro dari uku a jakanta kudin ma duk Yaji jiki Daga gani itama bashi gareta ba, ta mika mai bako kunya ba tausayi ya karba yayi gaba yana maganganu, "Baiwar Allah mun gode Allah ya saka da alheri, "ba komai Allah ya rufa mana Asiri, Sumayya ce keta kaiwa da dawowa, "Ummu ina Mudin? Ai ya tafi tun dazu, nasha zai tsayane ya taimaka mana da wani abun, "yadai ce bari yaje ya dawo, "Suwaye yan uwan wacce aka shiga da ita Emergency yanzu? "Gamunan Ummu ne da Sumayyah suka hada baki gurin fadin haka, "likita na nemanku, "to muje, binta sukayi a baya suka shiga Office din hade da Sallama, wani Farin kyakyawa matashi ne zaune a Office din yasa kayan likitoci da, alama shine likitan ita kuma Maryama tana kwance kan gadon dake Office din, Amsa musu Sallaman su yayi ba tare daya dago ya kallesu ba, zama sukayi suna jiran jin me zai cemusu, sai da ya kai gurin minti goma suna zaune baice musu komai ba, har Sumayya ta fara tsaki sbda ita fa a ka idanta bata jure wulakanci, "oh Sorry kune yan uwan Maryama Nuraddeen wurno, "eh mune Doctor, "kun san tana da sikila koh? "Eh mun sani Doctor, "Ok to gskya ciwonta ne ya tashi kun san shi wannan ciwon ba wuyan ya shanye ma Mutum jini, in so samune ma a ce duk ending Month a dunga kwashe jininta Ana samata wani, yanzu dai kafin abata duk wani taimako tana bukatar Jini Leda uku, "wayyo Allah a debi nawa doctor a samata, ko Leda goma ne, "how old are you dazakice a debi jininki, ko ba haka bama ba,a diban jinin mace Sai ya zama dole, yanzu in zaku kawo wanda, za,a dibane zaku biya Dubu bakwai na diba da test din da za,a yimata, in kuma siya zakuyi zaku biya dubu sittin Leda uku, "don Allah doctor ka taimaka mana wlh bamu Da wannan kudin, bamu da Wanda zai taimakemu bamu da kowa, mu yan gudun Hijirane Daga garin Sokoto duk an kashe mana Ahali gaba daya dukiyoyin mu sun salwanta, "dakata baiwar Allah bashi na tanbayeki ba, zaku iya fita kuje can ku nemo, haka kuke ai kudunga karya kuna batama Hausawa suna, tashi yayi ya tafi har ya kusa fita ya juyo in har baku kawo kudi ba, nan da Awa uku zaku iya rasata yana gama fadin haka yayi ficewanshi, dukewa Ummu tayi ta saka ihu, "shikenan nasan mun rasaki Maryama ina zamu samu wannan kudin, dagota taji anyi Sumayya ce ta dago Mahaifiyan nata ta fara magana cikin Dakiya, "Ummu bazamu taba rasata ba zanje duk inda zani sai na nemo kudi a yau dinnan Nayi miki alkawari, da sauri ta juya tayi hanyar fita Office din, da sauri Ummu ta biyota tana kwala mata kira, ina ai ko waiwayota batayi ba tai gaba,,,,,,,,,!!!! Kudai cigaba da bin alkalamin yar mutan zazzau yanxu aka fara wasa farin girki, shin Sumayya ina zata samo kudi har dubu sittin don yima yar uwanta aiki, to nima dai ban sani ba kubi ni sannu a hankali✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ Share Vote Comment Follow me on whatpad ZainabSalihu933 More Comment more typing ✍️✍️✍️✍️ ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com πŸ’žπŸ’žπŸ’žWAZAN AURAπŸ’žπŸ’žπŸ’ž (POOR GIRL) Fictional 😩 Traditional 🏚 Politicians πŸ‡³πŸ‡¬ Love πŸ’– Story WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU. DEDICATED BY RALEEYAT YA'U (UOM KHADY) MARUBUCIYAR: GIDAN GADO AND NOW WAZAN AURA Na sadaukar da page dinnan ga duk wani wanda Basu da gata Basu da Mai taimaka musu, Ubangiji bai manta daku ba, ku kyauta ta Ibadunku ku kadaitashi gurin Bauta, kuyi hakuri ku rungumi rashinku, Shi da kanshi ya fadamana yana tare da masu hakuri, Allah ka rufamana Asiri duniya da lahira Ameen ya Allah. πŸ’˜πŸ’˜PAGE 3TO 4πŸ’˜πŸ’˜ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. ************************* Fitowan Ummu bakin Asibitin yayi dai dai da tafiyar Sumayya a Napep, "Ya Allah ka karemun diyata duk in da zata shiga a fadin duniya, Karka ba ma Mutum ko aljan damar cutar mu da diya, 😭 tana fadin haka tana kuka, juyawa cikin Asibitin tayi ta zauna jikin wani bishiya, ta zabga tagumi, ************************* Itako Sumayyah tana tare me Napep tace mai kasan gidan Govnor yace mata "eh nasani Amma keko yarinya me zakije yi gidan gwamnati? " "Nidai kawai tunda kasani muje Kawai, Direct Sumayya gidan gwamnati suka nufa don ita a dan karamin tunaninta Da haukanta na kuruciya ai su shugabanni ne kuma Malaminsu yasha fada musu cewa hakkin Al'uma yana wuyar shuwagabanni, bata san cewa su shuwagabannin namu ba haka suke ba Basu tausayawa talakawansu tsakanin su da talaka sai lokacin zabe in ya zo, shine suke sanin talaka nada Anfani a gurinsu, itakuma ta kudurta ma kanta saita ga govnor tace ya taimaka ma Rabin ranta karta Mutu, ta na isa Ungwar mai Napep ya sauketa a farkon layin yayi mata nuni da gidan daga nesa ya tafi abunshi, sauka tayi ta fara tafiya, sai ta fara ganin jami'an tsaro kota ko ina tundaga farkon unguwar gabadaya kallon ta sukeyi sbda wasu yamutsatstsun kayane a jikin ta duk sun kode ta kasan doguwar rigan ma ya yage dinkewa tayi da tsare da allura, haka hijabin da ke jikinta duk ya yage har ta wuyan hijab din rike wuyan hijabin nata takeyi sbda karya fadi, duk da haka tsaf tsaf take bata da datti ga kwantaccen gashinta da ya kwanta gaban goshinta, kyakyawa ce Sumayya Yarinya ce yar shekara goma sha uku a duniya gata tana da irin saurin girman nan, Amma yarinya ce mai basira da iya sarrafa magana, gata da kafiya da juriya da rashin tsoro don ita tun tana karama bata da tsoro kuma in tamaka wani abu zaka dauka yar shekara Ashirin ne, akasin Yayarta data kasance Matsoraciya, duk wanda ya taba mata Yaya to bashi ba zaman lpy don sai ta hada mai jini, gata akwai zuciya, "Ke ina zaki iyeh? wani security ne ya taso yazo ya tareta daga shiga gidan gwamnatin don sunga tabbas nan ta nufa kuma in aka barta shiga zatayi, lpy Malama muna tanbayarki kin mana shiru, sai data gama kare musu kallo tsaf tace musu"nazo gurin Govnor ne, gaba dayansu kwashe mata da dariya sukayi, wani a cikin su ne yace mata"Haba yan mata anfada miki ganin Govnor ganin mai talle goro ne, kowani karabiti ne zai ganshi, sai kinada Appointment dashi kuma yasan da zuwanki, "to kusamun Appontamant din mana don ni wlh bazan bar nan ba sai naga Gwamno, juyawa security yayi suka kashe ido da yan uwanshi, sukayi wani murmushi mai ma'anoni da yawa, dayan ya fara shafa kai "yan mata kwantar da hankalinki zaki ga Govnor badai Govnor ba tace "Eh shi, "to kin ganshi kin gama, kin ganninan nine na hannun daman Govnor, biyoni muje, haka ta bishi a baya har suka shiga cikin government House, wani guri yabi da ita tana ankare da hanyar da suke bi, har suka isa wani guri da ba hayaniya ba Jama'a a gurin kaman ba cikin gidan ba, kuma tana lura da duk in da suka wuce sai ance mai Oga anyo kamu kenan wannan yar shila haka akwai kwasan gara yau kenan, da Fatan za,a rage mana, "karku damu, wani guri suka je wucewa taga wani hadadden gaye ya fito rike da jaka a hannun shi can kuma taga ya kira wani security, sai taga ya daddan na wasu abu a jakar sai ta bude kudine cike da jakan, tsayawa tayi tana kallon shi ji take kamar ta bigeshi ta kwace kudin don da ganin wannan baida da wani karfi, cire wasu kudin yayi ya ba security "kayi kokari ka shigo mun da ita fa Karka bari kowa ya ganka lokacin dazaku shigo, "angama ranka ya dade, yana jujjuya kudin "kudi masu gidan rana in kana dashi ka wuce gori, juyawa yayi ya tafi shikuma gaye ya bude Motan ya ajiye jakan kudin bai rufe ba ya juya zai tafi karaf suka hada ido da Sumayya data tsaya tanata raba ido, gabanshi ne Yaji ya fadi, da sauri tayi gaba tabi wannan security, waige waige ya farayi, bai ga inda tayi ba, "kai dama Ana ganin Aljanu da rana ne, don dai wannan yarinyar tafi Kama da aljana, niko nace yallabai Mutum ce, juyawa yayi ya shige ciki, "Dallah Malama ina kika tsaya naga alamar baki son ganin Govnor din, "wlh bawan Allah ina so, ka taimaka mun, "to Naji duk abunda na ce kiyi karki min musu Kinji? "To insha Allah indai ni zan ga gwamna ai da sauki, "sosai zaki ganshi, wani daki taga ya bude yace mata ta shigo, "a nan ne zan ga gwamna? "Eh mana shiga tayi, kallon dakin tayi dakin ya hadu falone madai daici Yaji royal furniture's farare kal kal ga wani madaidaicin TV jikin bango dasu home teather kananu masu kyau gefensu ankawatasu da wasu golden flowers, tana can tana kalle kalle, har yaje ya kulle dakin ya dawo kusa da ita ya zauna matsawa tayi tace"mallam ina gwamna meye kakeyi haka, dora yatsan shi yayi akan bakin shi, yace mata "shiiiiishh kibani hadin kai kin san rayuwar duniya taimakeni in taimakeka ne, in kin taimakeni kin bani Zuma nima in taimaka miki kiga Govnor, in kuma kin ki in danne ki in miki ta karfi, kuma bazaki ga Govnor ba, ga mamakin shi dariya yaga ta kamayi, ta tashi tana mai kallon baka da hankali, "ni tun farko inda ka fada mun haka da baka wahalar da kanka ba, a zuciyan ta kuwa ji take kaman zai fado saboda tsananin tsorata da jin abunda yace, "muje to ko a falo zamuyi harkan washe baki yayi yace kice ke yar hannune ashe? "Sosai ma Amma don Allah kanada igiya? "Mezakiyi da igiya kuma? "Oh ashe ma kai baka kware a harkan ba kenan, ai wani style ne Sai anyi Anfani da igiya, "ok yana fada yana washe baki aikuwa kaman ina da wani bari in duba kicin dina, "tom binshi da kallo tayi shege ramammen banza ita data daure wanda suka fishi ma ta bugi banzaye, balle shi da daga gani sigari ya tsotse shi, jeka kawo igiyar daureka dan iska kawai, Agogon dake dakin ta kallah taga har anci Awa daya da barin ta Asibiti, "yauwa Baby gashi ko, to cire hijab dinta tayi ta ajiye gefen gadon dakin, karban igiyan tayi, tsayawa tayi kuma ta rasa ta ina zata fara, can wani dabaran ya zo mata, yauwa ka kwanta mana, shiko banzan kamar wani sakarai haka ya kwanta yana wani washe baki, "ke zaki ciremun kayan koh Baby, "Eh Karka damu cire mishi riga ta farayi tanayi tana istigfar har ta cire mai, daga igiyar tayi taga ashe ma uku ne a hade, "ka rufe idonka Karka bude Sai nace maka ka bude, kaji "to baby ba matsala, igiyar ta jawo ta cire guda daya, hannuwar shi ta Kama ta fara daurewa, ta tabbatar ya dauru don Sai da yayi karan Azaba, "Haba baby ban son raki fa, "na bari sorry, a zuciyarta tace kai ka san Wani Sorry, kafanshi ta Kama ta fara daurewa aiko ya bude idon shi da Sauri "wai ke lafiyan ki haka akeyi zaki dunga daureni, banza dashi tayi ta cigaba da abunda takeyi, tun yana daukan abun wasa har ya fara, mata bala'in ta kwance shi baison style din wannan ai iskanci ne da mugunta, Hhhhh dariya Sumayya tayi "to sannu dan bunsuru,!!! yau ba, abunda zai hana in dan dakeka daga kaina bazaka kara marmarin yi ma wata yarinya fade ba, igiyar da batayi Amfani dashi bane ta daukeshi ta fara zanan shi dashi ihu ya farayi, ta samu kyalle ta daure mai baki saboda karya cika mata kunne Sai da ta mai jini da majina, ta dauki Key din ta bude dakin ta fito, sai Sauri takeyi kokarinta ta isa inda taga saurayin nan na dazu, Fatan ta bai tafi da kudin nan ba ta rokeshi ko shi zai taimaka mata, tana isa taga ba kowa gurin Sai Motar da taga saurayin ya saka jakan kudin nan dazu da Sauri ta isa gurin Motar tana zuwa, ta leka Motar ta hango jakan a ajiye akan seat din jawo murfin tayi Sai taji ya bude, wani ajiyar zuciya tayi, waige waige ta farayi ko zataga wani na kallonta, aiko dataga bataga kowa ba jawo jakan kudin tayi Sai taga ya bude, hannunta na rawa tasa hannu zata dauki kudin kara wani abu taji ta bayanta firgigit tayi, ✍️✍️✍️✍️✍️✍️ Share Comment Vote Please πŸ™πŸ™πŸ™ Follow me on whatpad ZainabSalihu933 Yar mutan zazzau ce 😍😍😍😍 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *πŸ’¦{Arewa ginshiΖ™in al'ummah}πŸ’¦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.comPart one free πŸ’žπŸ’žπŸ’žWAZAN AURAπŸ’žπŸ’žπŸ’ž (CLEVER GIRL) fictional 😩 Traditional 🏚 Politicians πŸ‡³πŸ‡¬ LoveπŸ’– Story WRITTEN BY ZEEYTERH YAR MAMA YAR MUTAN ZAZZAU. DEDICATED BY RALEEYAT YA'U (OUM KHADY) MARUBUCIYAR : GIDAN GADO AND NOW WAZAN AURA Na sadaukar da Page dinnan gaba daya ga Dillalai Family Allah ya Kara mana dankon zumunci ya hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinki daya, Ameen ya Allah. πŸ’˜πŸ’˜PAGE 5TO 6πŸ’˜πŸ’˜ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. ************************* Da Sauri ta waiga Sai taga ashe wata kyanwace ta sagale a wani karfe shine datayi tsalle Sai karfen ya fado, shine yayi wannan karaπŸ˜‚ nasan reader har kun tsorata koh, da Sauri ta dauki rafa daya a cikin kudin ta cusa cikin riganta ta maida Motar ta rufe juyawa tayi tana tafiya a hankali ba wani alamun tsoro ko fargaba a tare da ita duk security da ya ganta bai cemata komai sbda anganta da Oga dazu, tana isa gate aka bude mata, ta fita, haka ta cigaba da tafiya harta kai karshen layin, nan ta fara falfala gudu, wata Babban motane tasha gabanta kasan cewar layin ba kowa, ungwar shirune, wasu manyan mutane ne suka fito daga Motan fuskan nan ba Rahma Kwata Kwata "GB ku riketa fa kalan wanda Oga ke sone fa, kasan kusan sati daya kenan muna yawan bamu samu ba gashi yau abu har gida karku sake ta gudu, haka sukayo kanta kaman mahaukatan zaki juyawa tayi ta diba a na kare su kuma suka ce dawa Allah ya hadasu, Gudu takeyi kaman ranta zai fita don ta tabbatar in wa innan mutane suka kamata shikenan bata ba kara ganin Ummun ta da yar uwanta, in bata kuma ya rayuwarsu zata kasance, tuna haka yasa ta kara wani masifan gudu kudin data dauko ne, taji faduwar rafa daya dayan ma na shirin faduwa, haka ta kara damke daya, ta cigaba da gudun ta ga Ungwar da uban nisa kafin a fito hanya, ga karfinta ya kusa karewa, gashi su kuma Basu da niyar dena binta kokarin su su kure mata gudu, ta gaji don kanta, Zuwa tayi ta tsallaka wani dutse tayi tuntube ji kake Tim ta fadi kanta ya bugu da dutsen, Amma karfin hali irin nata kokarin mikewa takeyi, jirine ya dibeta, ga wani tsafi dataji a kafarta, kara ta kwallara, sbda Azaba, dai dai lokacin da suka kariso gurinta matsawa baya ta farayi, a tsaunen datake, "don Allah kuji tausayina karku cutar dani ni kadai na ragema Mahaifiyata, Sun kashemun Uba sun kashe mana yayyina da yan uwana sun tarwatsa garin mu da Ahalin mu, don Allah kumin rai, "hhhh Oga kajita fa waya fadamiki yan mata mun san Allah, to mu Umarnin Ubangidan mu Kawai muke bi, gunda ki tsayama mu cire abunda zamu cire a jikin ki ta sauki, ko kuma mu miki ta Azaba, idon ki kawai zamu cire da halshenki, da Nonon ki guda daya kacal, fashewa da wani irin kuka tayi tana tuno da Addu'a da kullum Ummu take koya musu, Addu'a na neman tsari Addu'a ce mai karfi, a lokacin da kke neman taimakon ubangiji: Bismillahil lazeey la ya dhurru ma'ah ismihi shai'un fill Aradhi walah fis sama'i wahuwas sami'un Aleem, Addu'an da ta dunga mai maitawa kenan, a cikin ranta, "GB!!! "Na, am oga, "bani wukar nan, da askan nan, "angama Oga miko mishi yayi, "ku bankaremun ita, to nufanta sukayi gadan gadan. Wani mahaukacin iska sukaji yayi sama dasu kafin su isa gareta, dukan su saida suka tsorata har itama Sumayya Sai data tsorata wani kyakyawan saurayine ya bayyana, yace "duk wanda ya fasa tabata a cikin ku, ko in ce duk wanda ya shirya mutuwa ya taba yarinyar nan, "kai a waye dubeka kanajinka kaman tsinke, "ai abun ba, a nan yake ba, "GB gamamun dashi, "angama oga Nufo mutumin yayi gadan gadan, yana isowa ya kawoma saurayin nan duka, yaga ko motsawa baiyi ba, aikuwa kafin ya maida hannunshi Sai ganinshi yayi a sama Ana hajijiya dashi, Saurayin nan da Hannu daya ya dagashi, hadashi da gini yayi tuni ya sume, yace akwai wanda yake bukatan ya bishi, tsagayawa daya yayi, yaje ya kamo Sumayya yasa mata wuka a wuya, "Karka sake ka motsa in ba haka ba zan kasheta, bai gama rufe vaki ba Yaji sauka dutse a kanshi, da Sauri ya yarda wukan, Sumayya tayi Sauri ta dauke wukar wani ne ya nufota gadan gadan, "Sumayya da Sauri ta waigo ganin wani ya nufota da gudu da wuka a hanunshi aiko wani tsalle saurayin nan yayi Sai gashi gaban mutumin nan wukar hannun mutumin ya kwace ya hankadashi daga daga yayi ya fada kan Sumayya dake tsaye tayi ready da wukarta a hannu, fadowar dazai yi Sai a kan wukar hannunta, jikake lubus a cikin shi, ihu tayi hadi da tureshi, jinine ya tsartu mata gaba daya hannunta ya baci da jini da riganta don tuni hijab dinta ya fadi, na shiga Aljanna nayi kisa, ganin haka yasa sauran suka ranta a na kare,"shegu mushirikai kawai tashi Kinji, "wai dazu Sai Naji kaman Sunana ka fada bawan Allah, "au wai dama sunanki Kenan kawai ni zuwamun yayi raina naga kuma kin dace da Sunan shiyasa na fada fa, "wai ya akayi kake jin Hausane don Nidai Banga alamun kayi Kama da Hausawa ba, kafi Kama da larabawa, ko indiyawa, dariya yayi mata"kema ai hakane, inda kika iya nima haka na iya, kema ai bakiyi Kama da bahaushiya ba, "nidin ai kai kafini kyau, kamar wadda ta tuna wani abu da Sauri ta mike, ihu tayi

Chapter 1 of 7