sun yi san yi da Had'uwar Amma da Inna talatu a Dogon gida ni kuma muka kulle da Diyarta Ramatu sannan tun dawowarmu sai gobara bata kara bin mu ba, Na samu na cigaba da makarantar gwammati Adda Fati ce gwammati ta biya ma Neco. Adda Rukayya daman ta gama ita. Amma bata kwanta ba tana sana'ar sai da Danwake da wake da shinkafa da wake da mai da yaji kuma tana samu tunda ga Adda fati na tayata,nima kuma ba ni da kiyuwa ina da son aiki.
Da farko rayuwar ta juya mana baya ammh daga baya sai ta waiwayo mu. Adda rukayya ta samu miji mai hali ma'aikacin gwammati. Sai da mganar aurenta ne Amma ta nemi dangin su Babanmu suka shiga mganar, muna tunanin In Adda Rukkya tayi aure zata ji kanmu ashe ba haka ba ne.
Shanun Adda aka saida akayi mata yan kayan Daki tare kuma da sana'ar Amma na ba dare ba rana.
Adda Rukayya ta na da wani Hali bata da son yan'uwa kuma bata da Kulafacin uwa ballatana damuwa da Halin da muke ciki,bkomai daga bangaranta ba ma samu tun Amma na Damuwa har ta daina ni daman ban wani shaku da ita ba, tunda ta sha Hantarata da mai Farar kafa har tab'a ce min tayi"Wannan Farin fatar naki ba na banza ba ne. Yanzu haka na tsiya ne da Talauci."
Sai da Adda Fati ta yi aure ne sannan muka san taimakon daga bangaran gidan surukai, Habibu mijinta Bakanike ne, kuma yana da Rufin asiri yana sonta,shiyasa mu ma ya ke rikemu da Daraja alherai kala kala yana yi mana sai godiya.
Adda Rukayya kuwa ba ta ma Dauke mu da Daraja ba ballatana shima mijinta da Danginsa su darajamu. Mijinta ma kwata kwata zuwansa gaida Amma bai kai sau biyar ba. Kamar ma kyama muke ba shi. Ni ko daman Adda Rukayya ta sha fad'in ni ce na saka Baba ya rasa komai na shi muka talauce kuma kafin mutanen gari su fad'a masa ita ta gayamasa. Shiyasa bai taba amsa gaisuwata ba acewarsa irin mu ko mgana da Fatar baki ce sai ya bi mutum ya Lalace.
Bazan ce ban da mu da karatun boko ba,ga yanayin da mu ke ciki yasa ban zurafafa ma kaina sai na yi karatun boko ba, Na san na iya karatun Hausa da Rubutu sannan na iya karanta Turanci iya inda zan iya, Karatun addini kuma ban zurfafa ba,na yi islamiya a anguwan Alkali bayan dawowarmu Samaru na shiga makarantar Dare ta mallam Habu tare da Ramatu na san addinina daidai gwargwardo.
Sallah da yadda zan gyara ibada ta gabadaya da sanin hukunce hukunce tsarki da sallah,sanin abu mara kyau da mai kyau, sannan ina iya karanta bakin karatu a duk in da na ganshi.
Tun tasowata bazan ce ina da Farinjini ba, ballatana ga yanayina ba kowa ne in ya ganni yake jin ina Burgesa ba ko kawa ban taba yi ba sai akan Ramatu shiyasa har gaban Abada na ke jinta a raina. Sannan na ke sakata cikin farkon Farkon jerin masoyana. Ko a cikin dangin mu ana Hantara na ballatana ga jama'ar gari shiyasa kasancewa ta, mai farin jini bai dameni ba. Ban san me ake kira Saurayi ba sai dai in ga ana zuwa wajen Ramatu ni kuwa bai dameni ba na fi damuwa da lafiyar Amma tare da sana'o'in da muke yi domin rike kanmu.
Amma ciwon ta ba shi da suna ko sanadi, ta fara shi daga zazzabi mai zafi sai kuma karkawa da ciwon kai mai tsanani da abun ya yi girma sai ya ke had'a mata har da Ciwon duka gabbanta,kafa, Hannaye, baya da sauran su in ta farashi kamar bazata ta shi ba, sai an kai ta asibiti an mata allurai da ruwa sannan ta ke dawowa hayyacinta. An yi gwaje gwaje har an gaji an rasa gane sanadi ko ciwon, mgana D'aya ce Typoid da Maleria ne, ammh kowa ya ga yadda Amma ke jin jiki sai ya ce ciwonta ya fi karfin maleria. Ta rame ta Lalace ga ciwo ga wahalar rayuwa.
Ni da Habiba mu ne karfin sana'ar Danwake da shinkafa da wake,sau biyu muke yi a rana da Safe da yammah, ni na ke yin na safe da yammah kuma Habiba in ba makarantar yammah sai ta kama mun, Amma kuma ba ta iya zama sai dai in ciwon ta ne ya yi tsanani. Mace ce mai kazar kazar da son kai da kawo ta na da karfi na Fulani acikin jikinta kamar yadda Adda ta ke, itama mace ce kamar maza a tsaye take kan kafafunta ta fi Amma Lafiya tunda ita har yau har gobe bata da wani ciwukan wannan zamanin.
Ba mu da kowa sai kawunan mu sai Allah, sai Adda fati da ta ke taimako mu, sai Inna talatu tunda Yayan Ramatu tela ne na mata kuma yana samu sosai, tabbas zaman su a gidan nan sun taimaka mana matuka.
Adda Rukayya kuma ba ta cikin Lissafi ita wannan da ita da ba bu duk D'aya ne sai ta jima ba ta zo ba, in ma tazo ba ta zuwa da komai, matar da ko haihuwa zata yi sai dai ta kira kawayenta ko Dangin miji sai daga baya ma muke samun Labari. Adda fati ke zuwa ni tun sunan Yarta ta Biyu Madina. Da muka je dangin mijinta suka rika nuna ni suna mganganu. Har suna fad'in daga ganin fari na daman na cuta ne ba na lafiya ba, Allah ya sa ma ba maita na ke da shi ba, a gabanta kuma bata tsawarta ba Da Adda Fati ta yi mgana sai ta fara Fad'an in mun zo mu watse mata taro nata ne, mu kara gaba ta gode. Tundaga ranar ban kara kafafuwana ba su kara taka gidanta ba sai jikin Amma da ya tashi na je na gayamata ta fito ta ce min kada na kara zuwa saboda Mijinta ya ce ba ya son ina zuwa masa gida. Ba ni da Fad'a ina da mgana ni d'in ba Shuru Shuru ba ce sai dai na san a inda na ke yin sa, Ina da wani Hali na zuciya da Taurin kai ko dan'uwana ne ya nemi ya wulakanta ni ina janye jikina Daga garesa wulakanci ne babban abunda zaka yi min kaga bacin rai na. Ko ka taba Amma to a nan ne zaka ga ainihin wacece Hasiya Mamman kona.
Bazan iya fad'in wani lokaci ne Abubakar ya shigo rayuwata ba. Ni dai nasan watarana na je kasuwa siyo ma Amma dawa da rogo na garin Danwake, muka had'u da shi a bakin Hanyar cikin motar abokinsa,ya yi min mgana ya nemi lambar wayata na ce masa ba ni da waya sai ya nemi na kwatanta masa gidanmu. Na kwatatan masa, a daran ya zo ya ganni mganarsa ta farko da bazan taba mantawa ba ita ce"Hasiya ni fa son ki na ke yi da gaskiya. Kuma in sha Allahu Auran ki zan yi"
Tabbas mganganun sa sun yi tasiri a raina yadda ya ke d'an gayu dan boko dan gidan manyan mutane. Gidan su gidan arziki ne,tunda Mahaifinsa dan kasuwa ne shima Abubakar din Shaguna garesa na kayan yara a kasuwar sabon garin Zariya.
Fari ne tas Bakano ne tunda Mahafinsa bakano ne mahaifiyarsa yar Danja ce da ke jahar katsina. Ni da bakina na fad'amai komai da ya danganci Rayuwata saboda naga kamar yanayinsa ya yi nisa da tawa rayuwar ammh ya ce yaji ya gani. Har ga Allah kyakyawan dabi'unsa mu'amalansa ya sa na fara son shi ban sani ba. Abubakar ya yi min komai a rayuwa in nace komai ina Nufin komai!.
Ya so ni,ya kaunace ni a yadda na ke ya kuma toshe kunnuwansa da duk wasu suka ko yarfe a kaina shi dai ya ce yaji ya gani. Abun da ya yi min da har gobe na ke jin sa a raina ya Daraja abunda ya ke a kusa da ni. A lokacin ko ni ban kaisa kula da Lafiyar Amma ba. Ba ni da fargaba ciwon ta ya tashi Ina da Abubakar. Cikin Lokaci ya maidani mace mai aji da alfarma ya siyamin waya da kayan kwalliya da Suturu ban san iyaka ba.
harta Kanwata Habiba yana yi mata Hidima Amma ko har yau ta na Daura d'aya daga cikin irin kayan da Abubakar kan siyo ya bata. Adda Fati har gobe ta kan ce bazata daina min bakincikin Rabuwa da Abubakar ba Masoyi ne da ya amsa sunan masoyi a gareni. Har gidanta mun sha zuwa tare, Har gadan mallam Mamman mun je na kai ma Adda shi sun gaisa ta na ta saka albarka bakinta ya ki rufuwa. Ban tab'a tunanin watarana soyayyata da Abubakar zai iya kasancewa a tsaka mai wuya ba. Na riga na gama sakin jiki da shi ban sani ba ashe sanda ya kai mgana ta gidansu a kayi bincike komai nawa sai da aka warware har da Kagen abunda ma bai faru ba.
Mahaifiyarsa ta yi tsalle tace Allah ya tsareta Abubakar ya auro mai Farar kafa Rigima ta yi tsami domin Abubakar ya ce sai ni Hasiya. Gaddama ta farko da ya taba yi ma iyayen shi a kaina, ni bansan Halin da ake ciki ba tunda baya Fad'amin. Sai da Mahaifinshi ya tsawarta da mganar yace abunda Abubakar ya ke so shi za'ayi mishi. Shi ya jagoranci neman auran wajen Dangin Babbanmu Alhaji Tanko shi ya karbi mganar Tunda shi ne waliyin mu.
Kuma ba kunya ba tsoron Allah. Ya ke karb'an mgana ba tare da sanin ya muke rayuwa ba. Ammh yana karb'an mganar ne sisin shi in bai ga Dama ba, bazai ba da ba. In sha'anin ya tashi matansa su zo in kuma bai ga dama ba, ba wanda muke gani. Ballatana ya'yan sa da suke ganin kansu suma wasu ne.
An saka mana Rana da Abubakar wattani bakwai. Dalilin da ya kawo Kannen Abubakar gidan mu. Har tsakar gidanmu suka ci mana mutumci, sai ga sirrin mu A bakinsu suna mana maimaici. Sai alokacin nasan Dangin Abubakar ba su sona. Da nayi masa mgana sai yace kada na Damu shi dai yaji ya gani. Na tab'a masa tambayar "Haka zai aureni Ahalin ina da farar kafa? Kada wani abu ya same shi fa?
Dariya ya yi kafin yace'"Farar kafa ba shi cikin addini ban yarda ba Hasiya ki bar ma wannan Tunanin Allah ne ya isa ya yi komai ba Mutum ba'" wannan yakinin na shi yasa na kara sakin jikina a kan Abubakar ballatana da Mahaifin shi ya zo har gida ya ba ma Amma Hakuri sannan ya Tursasama kannen Abubakar suka Dawo har gida suka ba ni Hakuri ni da Amma. Sai mgana ta wuce zukata suka samu natsuwa da kwanciyar Hankali.
Komai da akayi min na aurena Amma ce da Adda Hari, sai Adda Fati da ni kaina Tunda ina samun kyatuttuka wajen Abubakar na kudi da Suturu, sannan ga Ramatu a gefe lokacin itama ta Had'u da Nura shima ba laifi yana sonta sannan Hidima Daidai misali ya na yi mata. Ga Inna talatu ita ce kamar Aminiya wajen Amman mu, an yi min kaya Daidai misali na yar talaka. Gidan da Abubakar ya na a Hanwa ne 2bedroom da falo sai kitchen an samu dai an yi min gado d'aya. Shi ne wajibi wadanda sukeje jere sun dawo suna Santin Muhallina. Akwatuna Bakwai Abubakar ya yi min shake da kayan alfarma kayan da aka jima ana zencen su a gidanmu da anguwan gabad'aya har ta da dangin baban mu da ban san ta ina labari ya je musu ba, sannan sunzo ganin ma idon su. Ko acikin Dakin ku akwai wada'anda basa son Cigaban ka. Irin Adda Rukayya ce kiri kiri ta kalleni tace" ina fatan kin fad'a masa gaskiyan yanayin ki?
Sai na kasa bata amsa Adda Fati ce ta mata mgana sai ta tabe baki tace"Ahto gwara dai a fad'amai tunda wuri kada wani abu ya biyo baya. "
Ni fa na jima da cire Adda Rukayya a matsayin yar'uwata na riga na gama Fahimtar ta, bakinciki ta nuna da Hassada ga nin ko ita albarka. Ta rika Fatan wani Sanadi ya yanke wannan jin Dadin da zan shiga Tunda tun asali bata kaunata. Shiyasa ba zata so Cigaba naba.
Tunda ta na Dauka komai ya faru damu ni ce sila. Tun Amma na Dauke mata kai, har sai da ta dawo tana mata Fad'a in ta yi wani abun gaban mutane.
A chan gidan Marigayi Mammadi Mamman kona aka daura aurena da Abubakar. Auran da ya zo cikin Tarin kalubale da ban tab'a tsammanin Farincikina zai koma bakinciki da kuka ba.
Lafiya lau muka yi taron biki na tara yan makarantar mu ta Dare sai makota ma su zuwa ganin kwakwaf. Sai Adda da iyalanta sai matan gidanmu sai Matan Baba Saminu da iyalansu sai Goggon Kona Baaba ta Lagos sako ta turo ma Adda Fati dubu ashirin tace a ba ma Amma ba yawa. Alhji Tanko da Baba Jibiril ba sako ba aike ba kuma iyalansu. Amma daman bata jira su ba. Har gwara Baba Saminu bayan Daurin aure ya zo har gida ya yi ma Amma Murna shi daman ko matansa na kukan Son abun Hannunsa ba ya kwantuwa.
Na dauka sanda aka kaini gaban Amma ta min nasiha na yi kuka na har abada kenan. Ashe ban ma yi kukan ba, An kai ni gidana a d'aya daga cikin Tsala Tsalan Motocin da abokan Abubakar suka kawo mana. An je da yawa kuma duka motocin sun Dauke mutane da Kafar Dama na shiga gida tare da Rikon Inna Adda da Goggon kona.
Na samu salama da farinciki Lokacin da na ji ni saman gadon aurena. Daga lokacin hayaniya da Mganganun mata ya rika tashi an kawo mana abinci da nama da Ruwan gora sai lemuka an ci an sha har mutane sun yi guzarin sa. Zuwa Tara na dare suka maida mutane gida Ramatu kad'ai a ka bar min sai da Angaye suka shigo. Bayan yan Nasihu da barkwanci suka mike suka tafi. Ina kuka Ramatu na kuka muka Rabu. Na san Abubakar ya raka su ya kuma dawo bayan ya Rufe gida, ya zauna a gefe na yana kiran Sunana da Hasiya Amarya.
Na ga sanda ya cire Babban Rigansa ya fita sai ga shi ya dawo da Filet da Kofuna ya baje kazan da ya shigo da shi. Shi ya rika ba ni a baki har na koshe daganan duk wata Hidima shi ya yi a wannan daran ya jagoranci sallar Nafilan albarkan aure. Daganan ya bi da ni cikin Salama har ya maidani Cikakkiyar mace mun yi kwanan Farinciki da Annushuwa. Daga wannan Daran har rabuwata da Abubakar bamu kara kwanan Farinciki ba. Da asuba wayar sa ta tashemu da mummunan Labari da ya yi silar Rugujewar aurena.
Labarin Shagunan Abubakar sun kama da wuta cikin Dare ko Tsinke ba'a fitar ba. Abubakar ya fita cikin tashin Hankali ya baarni cikin Zullumi. Zullumin da har na yi wata uku gidan Abubakar ina cikin shi. Da D'aya da D'aya komai na Abubakar ya ke karewa Wuta ba'a san ta ina ta ke fitowa ba ita ke lashe komai. Bayan konewar shagunansa Mahaifinsa ya Farfado masa da Shago daya shima ko wata bai yi ba wuta ta lashe komai. Kuma duk inda wutar ta tashi tsinke ba'a Fitar da shi. Dangin sa suka taso min caa akan ni ce sillar duk abunda ke Faruwa. Tun Abubakar na Boye min Damuwarsa har ta kasa boyuwa ta bayyana. Abubakar ya yi shaguna sama da Biyar Gobara na lashe su na karshen ya tafi kano siyayya a hanya bata gari suka masa dukan kawo wuka suka karbe kudin suka watsar da shi a bakin Hanya.
Sanadin da Abubakar ya rasa komai na shi. sannan shima Mahaifinsa ba shi da shi, tunda shi ya rika tallafama Abubakar jari. Shigowar Abubakar duniyata yasa na aminta da Mganar Ammi na ba mai yi sai Allah. Ammh daga Lokacin da abubuwan suka yi ta faru dani na aminta da cewa ni Hasiyar Bakar tsiya ce. Tabbas na zama Sanadin Lalacewar arzikin Abubakar na yi kuka kamar raina zai Fita auran mu na da wata uku Mahaifiyarsa ta zo har gida ta saka shi Gaba sai da ya Rubutamin Saki biyu. Yana kuka ina kuka.
Har kuma gobe ban kullaci Abubakar ba na san shi din mai sona ne duk mganganun da gari ya dauka a kaina bai taba aminta ba in nace ni ce sanadin komai sai yace ba ni ba ce daga Allah ne shi ke da Jarabawa da Kaddara.
Rabuwar aure na da Abubakar da abubuwan da suka biyo baya. Sai Tambarin sunana ya amsa kuwwa a gari, Hasiya na da Farar kafa Hasiya Bakar tsiya ce, Hasiya ba Alheri ba ce. Ban isa na hana Mutane fadin abunda suka gani a kaina ba. Na san har na gama Idda ina kukan Rabuwa da Abubakar. Mun rabu rabuwar da har yau ban kara ganinsa ba.
Na dai ji labarin ya bar zariya ya koma kano wajen yayan babansa ya na tayashi kasuwanci.
Gama iddata ba Dadewa aka yi auran Ramatu, sun koma sabon gidansu da Sati d'aya aka yi bikinta da Nura sai Kadaici ya yi min yawa. tunani da mganganun mutane duk ya isheni ba'a waje ba acikin gidanmu ma ana yadamin mgana. daga kuma Lokacin sai jikin Amma ya rika rikicewa ba'a wata bata ziyarci asibiti ba sai karfin Sana'ar da duk wata Dawainiya ya koma kaina.
Kayan aurena kuma Wata Dilalliya da ke kusa damu aka baiwa ajiya tunda ba mu da wajen Ajiya. Har ga Allah na cire rai da kara wani auran na Dauka kowa yasan me ke faruwa da ni in wani namiji ya Rabe'ni ma manta Allah ke yin komai a lokacin da yaso. Ba zato ba tsammani sai ga Salisu ya shigo Rayuwata. Da ya yi sanadiyar wanke duk wani bakin Fentin da Auran Abubakar ya shafamin. Salisu shima ya kaunace ni. Ya so ni da dukkan Zuciyarsa.
A auran Salisu ban saki jiki ba. Nasan abubuwa da dama za su iya Faruwa ammh ban tsammace su yadda suka faru d'in ba.
Aure na da Salisu ya zama kamar ba'ayi ba. Cikin lokaci Allah ya raba wannan auran da shi da kanshi ya Kulla shi. Ina tunanin tunda Rayuwata ta na cikin Tsaka mai wuya mafi al'ala na cire mganar aure a raina na tsaya na kula da Amma tare da Habiba.
Ammh tabbas na Fara Tunanin na Lallashi Amma mu koma Wajen Adda Hari in da ba kowa yasan ni Hasiya Bakar tsiya ba ce.
Na cigaba da Bautar Ubangiji da kula da Amma, har ta Allah ta kasance dani.
Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari.
Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah.
Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus
*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari.
Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah.
Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus
*04*
*Bayan Sati D'aya*
Bayan Sati d'aya da sakin da Salisu ya aiko min da shi, Kamar ba'ayi ba. labarina tsakanina da Salisu ya Shud'e kamar bamu taba Had'uwa ba, Kayana da aka riga aka jera tun kwana biyu da sakin su Adda fati suka je suka kwaso min kayana. Maganganu da mugayen bala'i ba irin wanda Sahura da danginta ba su jefani da shi ba.
Wannan karon ma Dilalliya aka bawa ajiyan kayan sauran kuma Adda Fati ta tafi da su gidanta. Sauran kayan kitchen kuma gidan Ramatu na kai mata ajiya,tunda ita kad'ai ne a gidan kuma 2bedroom gareta, guda daya ne ke da gado d'ayan tarkace ne aciki.
Ko sau d'aya ban bari damuwar da na ke ciki ta bayyana saman Fuskata ba.
Saboda Amma nasan irin ciwonta nasan irin tashin hankalin da na ke shiga in Amma na ciwonta, shiyasa na ne kafa kafa da lafiyarta.
Ni kaina nasan na yi dauriya sosai ban zauna nayi kuka ba, ko hakurin Adda Fati da Ramatu suka rika ba ni, ko a fuskata ba su ga alamun na damu ba.
Duk da mgana ta zaga gari har gida ake zuwa da sunan yi ma Amma jaje, saboda kawai a ganni a fita ana nuna ni, a dangin Babanmu Baaba ce kad'ai ta lagos ta kira Adda fati suka yi mgana. Tace Goggon Kona ta fad'a mata aurena ya sake mutuwa, Kuma ta saka bayan Adda Fatin ta zo gida ta mata Flashing ta kira suka yi mgana da Amma.
Nima an bani tayi ta ba ni baki, Sai Baba Saminu da ya zo da safe Ana sati da abun ya share kafa yana ce ma Amma abun nan fa ya yi yawa,ya kamata a nema min mganin Farar kafa har da na maita ma.
Amma kamar ta yi kuka cikin Dauriya tace"Hasiya ba ta da Farar kafa, sannan ba ta da maita. Ba ta gaje ta ba, ni ba mayya ba ce sannan uban ta ma da Maye ne da kun sani"
Kalaman Amma yasa ya fara kame kamen mganganu kafin ya yi mata sallama ya shura takalmansa ya fice. Ranar Amma ta sha kuka, ni kaina mganar tasa ta dakeni Maita fa? Zargin maita ai abu ne mai wahalan sha'ani.
Saboda damuwar da na ga Amma ta shiga yasa na ce mata mu koma ga sana'armu tunda dai komai ya wuce, Da ya ke jarin duk ya lalace saboda sha'anin bikin nan, sai muka fara da Danwake ,shinkafa da waken sai zuwa gaba in jarin ya tarfu sauran siyayyan rogo da dawan ma Habiba taje kasuwa ta siyo komai ni ba ni da Damar Fita, Tunda in dai na fita sai na zama abun Nuniya.
Ni na ke jefa Danwaken Amma na taikamin da zubawa, kuma ana ciniki sosai, Saboda matan gidanmu suna siyan ma ya'yan su har da mazajen su.
Da kuma makota tunda a irin gidajen da muke zaune ba kasafai akan Dora abinci ba yawanci an fi siyan irin su Danwake da Shinkafa da wake
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 24