takaicin Adda Rukayya na samu tazo ina shigowa Dakin Daidai tana ce ma Amma" Ni fa ba wanda ya kirani ballatana ya fad'amin abunda ke faruwa. Sai da Babansu Amna ya dawo ya ke fad'amin a gari yaji ana ta Fadin Labarin da yazo yana tambayanta nace ban sani ba. Amma tsakani ga Allah mganar mutane akan Hasiya ba Canfi ba ne gaskiya ki fa Duba Abunda ya faru da Abubakar ga wannan ma, to ko karayar arzikin Baba da Jinyarsa duk itace sila kema ga naki ciwon matsaloli sun ki su kare mana. Ni fa Matsalanta har neman Shafan zaman aurena ya ke so ya yi Tunda Har Baban su Amna ya ce shi ya fara jin tsoro, Mamanshi har mgana ta tab'amin nace mata kashin Tsiyar Hasiya kad'ai ke da ita ban damu ahto kada dalilinta aurena ya Mutu na shiga Uku"
Ta fad'a kai tsaye babu kuma alamun Tausasawa a muryanta.
Kamewa nayi a kofar dakin Amma na kasa karisawa ciki Amma na zaune kawai tana kallonta, dukkansu ba su san ina Kofar dakin ina Sauraransu ba.
Adda Rukayya ta gyara zama tana Fadin"Shine na kawo shawara Amma.
Me zai hana tunda dai nasan shima auran nan sunan shi Sakakke. Saboda ba iyayen da zasu bari D'ansu ya zauna da Hasiya mganar gaskiya kenan. Ki tarkata ki kaita Dangin ki chan gada wajen Adda ta zauna tunda chan ba wanda yasan abunda ke faruwa yafi nan da labari ya gama Zaga gari. A chan sai tafi samun kwanciyar Hankali ta samu mijinta tayi aure zai fi ye mata kwanciyar Hankali daga ita har mu Amma"
Amma kallonta kawai take yi idanuwanta har sun kawo ruwa.
Takaici da bakinciki sun saka ta kasa mgana.
Ni kuma sai naji kamar takaicin nawa ma ya Dauke gabadaya, hawayen da duka rage a cikin idanuwana na Share sannan na kariso cikin Dakin ina Danne yanayina.
Naso na shareta ne ammh kuma Son nuna mata naji mganganunta yasa na kalleta ina Fadin"Sannu Adda Rukayya?
Sai yau aka zo mana?
Sai ta kasa mgana Daga ita har Amma ni suka kurama ido suna nazarina yanayina sai kawai nayi mirmishin karfin Hali kafin nace'"Amma shawaran Adda Rukayya ta yi. Gwara na koma wajen Adda na zauna tabbas zai min kwanciyar Hankali da ku kanku Gabadaya. Ga Habiba nasan zata kula Dake Amma."
Na fada ina kwaso jarumta zuwa saman Fuskata.
Jin kalamai na yasa Adda Rukayya ta samu kwarin gwiwa gyara zama tana Fadin"Ahto nima haka nagani. Amma kada ki dauki mganar nan da wata Manufa mafita na samo ma Hasiya da mu kanmu"
Sai Amma ta kauda kai kafin tace"In kinga Hasiya ta bar garin nan to ki tabbatar ma kanki Rukayya kafata kafar Hasiya. sannan kafar Habiba.
Nasan Fati zata rika zuwa Dubamu sannan Adda bazata gujeni ba, sannan bazata kyamaci Hasiya ba, har Abada ita din mafaka ce gareni da Ahalina"
Mgana ce ta fad'a ba masu yawa ba ammh masu harshen damo ga mai Hankali.
Adda Rukayya dai sai jikinta ya yi sanyi kafin ta tabe baki tace"Amma ni fa ba bakuwar zafi ba ce. Ki yi hakuri in mgana ta ta b'ata miki rai"
Daga haka ta kakkabe jakarta ta fice daman abunda ya kawota kenan. Duk yadda Amma taso ta fahimci yanayina ban bata Damar haka ba Dakin na kakkabe na share Habiba na makaranta.
Bayan na gama na kwashi wankin Amma na fita da shi na Daureye mata, Ruwa ma almajirai na saka suka Dibomin ruwan tunda Bohol din na kofar gidan mu, Fita na kuma ba zai yuyu ba. saboda ko'ina yi da ni ake yi na zama abar kwantace da nunawa.
Kwana biyar tsakani Adda Fati da Ramatu suka dawo a bakinsu nake jin Salisu da gaske kano za'a kai shi Asibitin Dala ayi mishi Daurin asibiti.
Hankalina duk ya tashi Daman a kwanakinan yana raina kamar naje asibitin na dubashi ammh ina tsoro tare da Fargaban me zuwa na zai iya Haifarwa.
Ammh ban duba abunda zai iya zuwa ya dawo ba nayi ma Ramatu mganar zuwa asibiti na Duba Salisu. Itama ta jima bata ce min komai ba tana nazarin abunda zai faru, ammh bata min gaddama ba ta shawarci Adda Fati itama sai da ta jinjina kafin ta kalli Amma tana fadin"Amma kin ga ya dace Hasiya taje ta duba Salisu?
Amma tace"Sosai ya dace ai mijinta ne. kuma rashin zuwan ma wata mganar ne in zai samu ki shirya har da ke aje a duba shi"
Da wannan shawaran ta Amma yasa har Inna talatu da taji tace zataje itama muka Shirya Tafiyar.
bansan yadda mganar ta fita har matan gidanmu suka ji ba, sai suma suka Daka Tsallen zasu je,nasan dai bai wuce ganin abunda zai faru achan ammh ban magantu ba.
Ramatu ta yo lafiyayyen Ferfesun kifinta daga gida muka tafi da shi. Mota guda muka samu Bus,Tunda matan gidanmu su tara duk da zasu je, Son ganin Salisu da Halin da ya ke ciki ya Boye tsoron dake cikin Raina.
Na shirya cikin Atamfata wata ja riga da Sikat duk cikin kayan aurena da Abubakar ne tunda lokacin akwati shidda ya yi min Shake da kayan alfrma. Sai na saka Jan Hijabi har gwiwana, fuskata fayau daman gata karama sai Zullumi ya kara kankantar da ita.
Bayan La'asar muka tafi, tunda Lokacin Musbahu da Ramatu ta kira yace ana bari shiga. Mun shiga asibitin Chika Hud'u da minti Arba'in muna tafe tiri tiri har Emergency bayan mun yi tambayan shashen yan Hatsari aka nuna mana.
Duk jikina sai ya kara mutuwa sai ya kasance na koma baya ina bin tafiyar Ramatu tamkar nima tsohon cikin gareni.
Bansan wanda ya hangemu cikin yan gidan su Salisu ba ya je ya gayama sauran yan'uwan nasu dake chan wani gefe suna zaune.
Mu dai muna tsaye ne Ramatu na kokarin kiran Musabahu muka ji muryan wani kanin Salisu yana fadin"Wa kuke nema?
Gabana sai da ya amsa ganin su Ritutu, wasu ma ban san su ba. Nasan dai Salisu ba shi da mahaifiya ta rasu ammh suna da yawa a dakinsu. sannan mamanshi na da abokiyar zamanta itama da nata gayyar.
Inna Talatu ne ta sanar da shi munzo Duba Salisu ne, sai naga sun fara kallon kallo kafin su yi mgana sai ga Musbahu yana fadin"Hasiya ne da yan'uwanta daman sun min waya zasu zo duba Salisu da jiki"
Sunana kad'ai da aka ambata ya Rushe sauran Annurin su. Kafin ma mu yi wani motsi wata cikin matan nan mai Kiba ta bake kofar Emergency tana Fadin"A'a kuje kawai mun gode. Ammh bazaku shiga da gayyar tsiyarku ku karisa mana Dan'uwa ba"
Inna talatu da Adda Fati suka kalli juna kafin Inna talatu ta Tausasa murya tana Fadin"Asshaa baiwar Allah meya kawo wannan mganar? Daga Dubiya sai kuma zencen mu karisa shi? Ai bamu muka sakashi cikin wannan Halin ba ballatana kice zamu karisa shi"
Ta fad'a tana mai kwantar da kanta. Ba wacce ta tare kofar ba ce tayi mgana wata mai karamin jiki ne sai dai kallo farko zakayi mata kasan jinin Salisu ne domin suna kama sosai tace"ku ne silar shigar sa wannan Halin mana. Tunda silar auran yarku ce mai kashin Tsiya da bala'i. Ta nakasa mana Dan'uwa ga kuma asaran dukokiyon al'umma duk ta sanadin auranta me zamu ce da wannan auran?
Ta bakin kofar Emergency tace"Sai Allah ya tsine ma auran kawai zamu ce Ikilima"
Sai gabad'aya matan gidanmu suka saka salati na jimami har da masu gulma Ramatu taji jikinta ya yi sanyi ni take kallo ammh sai na samu kaina da jin kunyarta kaina na kasa ina kallon kasan asibitin cikin bushewar ido da na zuciya.
Adda Fati da Inna talatu tare da Musbahu ba yadda ba su yi su barmu mu shiga ba ammh Su ka ki, bayan kuma suna ta bin mu da mugayen mganganu, Har hankulan mutane ya fara dawowa kanmu.
Kallon Ramatu kawai nayi ina Fadin"Ramatu ku taho mu tafi kawai. Allah ya bashi lafiya"
Kasa min mgana ta yi, ta tsaya tana ce min"Hasiya wannan abun da nayo fa?
Sai da na kalli kwandon hannunta sannan nace"Ki ba wa Musbahu in kuma zai zama matsala mu koma da shi"
Ba ta yi musu ba taja Musbahu gefe ta mikamasa kwamdon hannunta bayan sun yi mgana, yana ta bata hakuri tace bakomai, su Adda fati tayi ma mgana yasa muka fito daga wajen da niyar Tafiya. Matan gidanmu suna baya suna ta Gulma daman abunda ya kawosu kenan.
A haraban asibitin muka had'u da Sahura da yan gidansu kallo kallo akayi tsakanimmu an rasa mai mgana, ganin tare take da wata yar Dattajuwan Mata Ramatu ke shaidamin Innar Salisu ce. Ina kallonta suka gaisa da Inna talatu da su Adda Fati cikin sakewa daga yanayinta yasa na Fahimci zatayi saukin kai ba kamar sauran ba.
Cikin Fara'arta tace"kun samu ganin Salisun?
Inna talatu tace"A'a ba'a barmu mun ganshi ba"
Cikin mamaki tace"ah kuma la'asar ai ta gota. Lafiya kuwa.?
Adda Fati Zatayi mgana Inna Talatu ta rike mata hannu tana fadin"Gudun Fitine kawai.
Ayi masa sannu Allah ya bashi lafiya"
Ni dai sai na samu kaina da Jawo hijabina ta sama ina Rufe fuskata.
Nima yanzu kunyar nuna Fuskata nake yi ga Mutane da gaske ni din Annaba ce ko kuma nace gobara Daga kogi mganinta sai Allah.
Inaga ta Fahimci mganar Inna Talatu yasa tayi ajiyan zuciya kafin tace"Rayuwar ne sai hakuri. Abubuwwn duk sun rikice ni na rasa ina zan kama. Ku yi hakuri don Allah gobe ma za'a wuce da Salisu kano ayi masa Daurin asibiti. Ku yi hakuri da duk abunda zai biyo baya don Allah"
Inna talatu tace"Bakomai Allah yasa ayi a sa'a"
Ta amsa da Ameen sannan muka wuce itama ta wuce, Tunda Sahura da gayyarta sun yi gaba suna harare harare da yada mganganu.
Har muka isa gida ban tofa komai ba duk da ana ta maida zence a cikin motar. Amma ma Adda fati ta zayyanemata komai ta sauke numfashi kafin tace"Allah ya kyauta"
Kowa jiki ba Dadi' haka Ramatu ta tafi tana kara bani baki nace mata bakomai Inna Talatu ne sai dare ta tafi gida Adda Fati kuma mijinta yazo Daukanta bayan ya shigo ya gaida Amma.
Har ya bata dubu daya.
Washegari wajen misalin karfe sha daya na Safe sai ga Musbahu abokin Salisu ya yi sallama da ni a kofar gida. Daman tunda naji ance Musabahu na kira na na saka faruwar abubuwa Biyu zuwa gareni.
Ina fita kuwa dayan da na saka ne ya faru Takarda ya mikomin cikin sanyin jiki na saka hannu na karb'a tunkafin na Bude na san me ke ciki ba wannan ne karo na farko, da na taba amsar irin ta ba.
Karfin halina Musbahu ya gani yasa ya ce"Kiyi hakuri Hasiya..Kiyi hakuri iya shi kawai zan iya ce miki.
Ammh ki sani Salisu ba shi da laifi har ga Allah fin karfinsa akayi"
Mirmishi nayi mai ciwo kafin nace"Bakomai Musabahu. Ka gaishe shi Allah ya bashi lafiya"
Ya amsa da Ameen kafin yace"Yanzu zamu dauki hanyar kano."
Na jinjina kai ina musu fatan Sauka lafiya.
Har na shiga Dakin Amma bata Fahimci yanayina ba, ko bud'e takardan ban yi ba. Na turata cikin jakata ta ajiyan karikitai. Na fita tsakar gida na samu Habiba na Hura gawayi zata Damama Amma koko.
Sai na Leka dakin Maman Boy nace ta aramin wayarta.
Ta dauka ta bani chan wajen bayi naje na saka lambar Adda Fati da na riga na Haddace na kirata ta na Dauka nace"Adda fati Hasiya ce!
Ban jira cewarta ba na cigaba da fadin"ki kira Inna talatu kuje ku yi mganar kwaso kayana gidan Salisu.
Saboda ya sake ni d'aazu"
Ina jin ta fara salati na yanke kiran. Lambar Ramatu na saka na kirata sai kudin suka kare ashe ya shiga sai ga shi ta biyo bayan kiran.
Ina Dauka ko cewarta ban jira ba nace"Ramatu shima Salisu ya sake ni"
Cikin Firgici Ramatu tace"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Kina ina ne?
Ina danne kukan da naji ya tasomin nace"Ina gida. Wayar maman boy ce"
Kashe wayar nayi saboda Duhu naji yana mamaye ganina.
Ina juyowa muka had'a ido da Kaltume itama matar gidanmu ce tana kallona da alamu ta gama labemin taji duka mganata.
Cikin son gulma tace"Ba dai shima Salisun sakin ki ya yi ba?
Da kai na amsa mata. Ba na son kwakwazonta yasa na wuce ko kafin na kai Dakin ta fasa kururuwa tana Fadin"Shikenan shima Salisun ya saki Hasiya"
Salisu ya saki Hasiya"
Wancan ta karba wanchan ta karb'a har kunnen Amma.
Ina shiga Dakin tace"Zo nan Hasiya"
Ina kauce ma kallonta na zo na zauna agabanta. Cikin kallona tace"Salisu ya sake ki?
Kai na gyad'a mata ban yi mgana kawai sai ta ce"Saki nawa ne?
Ba musu na mike naje na Dauko Takardan na mikamata Ammi,tayi karatun boko da na addini. Kai tsaye ta warware takardan ta karanta kafin ta ninketa yadda take. Ni ta kallah cikin nazarina kafin tace"Allah yasa haka shi yafi zama alheri gareki damu gabad'aya Hasiya"
Ciki ciki na amsa mata da Ameen kafin nace"Na kira Adda Fati,da Ramatu na fad'a musu"
Kai Amma ta jinjina min kawai ni kuma sai ma mike na fice.
Duk suna Tsakar gida kamar jimamin gaske suke yi na mikama Maman Boy wayarta na juya na koma Daki.
Sai na tsiri gyara jakar kayana ina jin abunda ke sukan raina ya na tab'a har kashin bayana.
Da gaske kenan abunda mutane ke fad'a a kaina ya tabbata?
Tabbas ina da Farar kafa.
Sannan zamana ko rab'ar mutane ba alheri ba ne.
Salisu da Abubakar sun shud'e daga Duniyata gab'adaya, sun zama Tarihi kamar ma ba'a yi su ba.
Sun shud'e saboda ba su ne daman Mahadin kaddaran ki ba HASIYA.!
*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*
*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabooks:JamilaUmarjanafty*
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk
Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.
*03*
Sunana Hasiya Mamman kona, sunan mahaifiyata kuma Aisha-Jari. Bafullatar Garin gadan mallam mamman da ke hanyar Abuja.
Mahaifina Alhaji Mamman Haifaffan garin zariya ne dake jahar kaduna, a cikin kuma tsangayar zariya wato anguwan limancin kona.
Sunan mahaifin shi wato kakanmu kenan wanda shine asalin Tushen mu, Alhaji Mammadi Mamman kona. Shima tun asalin tale talen iyaye iyayen su haifaffun garin zariyan ne ma'ana gaba da baya jinin zazzagawa ne su d'in.
Alhaji Mammadi Mamman kona Manomi ne kuma sannan masaki ne yana dinkin Sakan aikin hannu na manyan mutane har da sarakuna. Sannan yana saka hula shima na hannu kala kala, Dalilin da yasa ya yi suna shine Aikin hannu da kuma Hulan da ya kan saka ma manyan mutane da Sarakun gidan Sarautar zazzau.
shiyasa duk wanda ke garin zariya ya san tarihin tsohon gida na Alhaji Mammadi mamman kona. Tunda a zamaninsa da kudin Sakan sa yaje makka sannan ya mallaki gida kuma ya auri mataye har guda biyu a rana d'aya. Salamatu da Lauratu sune matan na shi suma kuma duka haifaffun garin zariya ne.
Kafin rasuwarsa ya tara ya'ya goma cif,Lauratu ke da Hud'u. Salamatu ita tayi shida, ciki har da mahaifin mu wanda aka maida masa sunan Muhammad, sai a ke kiransa Mamman kamar yadda sunan ya ke. Alhaji Tanko ne Babba sai Mamman, sai Hasiya, akwai muhammad Sani, Hajara sai Halima ita ce karamar su wacce yanzu haka take aure a garin ikko tana zaune tare da iyalanta da mijinta.
D'akin Lauratu kuma akwai Jibril shine Babba yanzu haka kuma yana nan da Ranshi yana aiki da babbar ma'aikata a kaduna sai Saratu, Goggon Kona kenan itama tana da ranta a garin zariya sai Saminu da Muhammad Auwal shi yana saurayi ma ya rasu ko aure bai kai ga yi ba.
Labarin mahaifina na ke baku, ammh zan tabo bangaran dangin babanmu ne saboda kusan ta ko'ina cikin gata na taso kafin tsaka mai wuyar da nake ciki ta jefani ni da iyayena da yan'uwana cikin halin k'ak'ani k'ani.
Babanmu Alhaji Mamman kona, ya yi karatun boko zuwa na arabi tunda Mahaifinsu mutum ne mai yalwata ma iyalansa kafin mutuwarsa. Ya yi kokarin had'e kan iyalansa kafin mutuwarsa kuma Alhamdulillah a lokacin kawunansu a had'e suke kafin mutuwarsa ta yi sanadiyar tarwatsa komai.
Tun bayan rasuwarsa aka raba iya abunda ya bari kowacce taja barayinta ita da ya'yanta daga lokacin sai zumunci ya samu Rauni, kowacce ita tayi fad'i tashin ta ita da ya'yan da aka mutu aka bar mata. Ita lauratu da ya'yanta su suka ci wannan gida na limancin kona,ita kuma salaamatu ta samu na anguwan Madaka itama tare da ya'yanta. Shiyasa sai kowacce ta koma inda ya'yanta da ita kanta suka gada suka zauna. Daga lokacin sai abun ya koma in na samu ya'ya na. In na samu dan'uwa da muka fito ciki D'aya sai had'uwa ta yi wahala abubuwa suka yi ta faruwa batare da Sanin junansu ba.
Alhaji Tanko shi ya gaji Alhaji Mammandi wajen saka huluna da Aikin hannu na riguna Darajar Mammandi kona yasa shima sana'ar ta karbesa sosai. Babanmu kuwa d'an boko ne tunda tun alokacin sai dai ya yi NCE. Sannan ya fara kasuwancin saida taki, tare da Dillanci sai da Filaye da kuma kama Hanyar gona in za'ayi Noma. Da wannan sa'anar ya yi karfi kuma da ita ya yi aure da mahaifiyar mu. A rugar da ke Gadan mallam Mamman ya ganta Farar Doguwar bafullatana da bata jin eh na ko da ilimin boko da arabiya, yana ganinta ya ji kuma ya gani ya na so. Sun je du ba wata gona ne ta wajejen ya ganta tana tallar Nono shikenan ya ga mata.
Amma a gidan auranta ta samu ilimin addini da mu'amala da mutane, Marainiya ce daga ita sai ya yarta Hannatu_Hari Adda. Sai baffan su da ya rike su ya rasu shekarun baya.
Mu dai mun taso mun bud'e ido mun ga rayuwarmu cikin gata da jin dad'i. A anguwan alkali na bude ido na ganmu muna rayuwa cikin gidan mahaifin mu tare da mahaifiyarmu da muke kira Amma da Sauran yan'uwana. Mu hud'u Amma ta Haifa Adda Rukayya ce Babba sai Adda Fati, sai ni Hasiya da Amma ta ce sunan kanwar baba ce da ta fad'a rijiya ta rasu aka maidamin. Sai Habiba da ita ce karamar mu.
Tun tasowar mu bamu san wani wahalan rayuwa ba har mota babbanmu ya mallaka sannan daidai gwargwado za'a sakamu cikin masu rufin asiri.
Na taso naga kowa a dangi na son mu da kaunarmu. Na kuma san babban mu ya rasa wasu daga cikin yan'uwansa ammh na san Alhaji Tanko Baban mu ne,Sai Goggo Halima dake aure a garin Lagos, muna kiranta Baaba. Na kuma san gidan Baba saminu da ke Limancin kona gidan da bayan Rasuwar mahaifiyarsu Lauratu suka gyara shi Baba Saminu ke zaune aciki da iyalansa.
Baba Jibril kuma yana garin kaduna yana aiki chan ya ke zaune tare da iyalansa. Tunda muna zuwa in aka yi haihuwa ko auren. Amma ta fi zuwa anguwa da ni, ni ma kuma tun ina yarinya ina da son yawo duk inda za'a je sai na saka Rigiman sai an je dani. Ko da muka taso kakarmu Salme ta rasu.
Amma tace auran su ba jimawa Allah ya yi mata rasuwa. Lokacin da na taso ba ni da wayau bansan me ake kira da rayuwa ba shiyasa ban taba kawo ma kaina a dangin Babbanmu kowa kansa ya sani ba Daga kafa sai kauri. D'ana nawa ne D'anka kuma na ka ne.
Doguwa ce ni sambal ba ni da kiba kamar a hureni na fad'i ne.
Ammaa na biyo har ta farar fatarta domin jajir take to ni har na fita Fari ma.
Kaf a dakin mu na fi su fari su kuma sun biyo Duhun Fatar babbanmu sai suka Sirka ammh ni Farina har yana Daukan ido, mutane in suka ganni sun sha tambaya ko iyayena Zabiya ne? Suna tunanin kalan Fari na kad'an ne ya rage ban zama zabiya ba.
Ga ni ba kiba sai farin kawai da Doguwar Fuska sannan ina da ga shi, wanda sai daga baya na same shi Amma tace ina yarinya kaina kwaikwai ne duk su Fati sun fi ni sumar gashin kaina ammh daga baya da na Fara girma sai duk nazo na Kire su sumar kai da cika.
Wani abun mamaki kuma komai na jikina karami ne kafafuwana sanda ne sirara, haka hannayena da kaina kamar kwai in ji su Adda Fati.
Na san mun samu ilimin zamani da na addini daidai gwargwado. Ban san wahala ba kuma ko labarinta ban taba ji ba, sai shekarar da na kamallah karamar sakandiri gobara ta tashi a gidanmu da komai sai da ya kone dagamu sai kayan jikin mu muka fita da shi. Daman Amma ta taba bamu labarin Ranar da ta haifeni gobara ta kama Dakin da Babbanmu ke ijiyan Takinsa ba'a fitar da komai ba. Dalilin wannan gobaran ma ya tafka asara mai yawa. Ban taba kawo kaina gobaran da ke faruwa da mu na da alaqa da ni ba, sai da bayan Baba ya kama mana Hanyar wani gida yana ta fad'in tashin neman yadda zai yi tunda asarori ya tafka ba kad'an ba. Wata gobarar ta kara tashi a inda muka koma,shi dai Allah ya takaita Daki d'aya ta ci wato dakin Babbanmu itama ta lashe kudad'e da wasu takardun filaye. To fa daga Lokacin aka fara mganganun a nemi taimako ana tunanin ko Aljananu ne.
Babbanmu duk ya toshe kunnewansa daga mganar mutane ciki har da yan'uwansa. Sai ya kasance Gobara ta zame mana jnin jiki. Ba'a daukan wata uku gobara bata Lashe wani abu na Kudi ko kaddara ba kuma arasa ta ina Gobaran ke tashi. Tun ana Fad'i daga nesa har ya zo kusa ballatana da karayan arziki ta samu babbanmu komai da ya mallaka sai da ya kare ya dawo gida ma yana jinya ciwon kafa haka kurum ta rika Duran ruwa ta kumbura fita ma ya gagaresa.
Ni bansan daga ina mganar ta fara fita ba ammh na san rana tsaka na zama abun gudun mutane da sunan cewa ina da Farar kafa haihuwata ita ce silar Komai sannan duk in da nake gobara bazata daina tashi ba. Sannan baza'a daina saran dukiya ba. Daga karshe ma har da rai sakamakon rasuwar babbanmu sai mganar ta fito fili kowa ya jita. Da rasuwar babanmu da Ciwon Amma duka acikin shekara d'aya komai ya faru. Da kuma tsarwatsewar rayuwarmu daga sama zuwa kasa. Tsangwama da Hantsara ba bu wanda ba mu sha ba a wajen Dangi da Mutanen gari ba duk saboda ni, Naman jikina ma sun ce ba mai kyau ba ne jini na ba jinin alheri ba ne.
Dalilin da yasa zama a ganuwar zariya ya gagaremu muka koma Samaru da zama a gidan haya.
Ba'a dogon gida muka fara zama ba sai da muka zauna a wani gida dake Anguwa y'an Randa, shima watanmu biyu akayi gobara maigidan ya tadamu, sai muka koma layin tsamiya Dogon Gida.
Fad'in irin fad'i tashin da Amma ta yi bazai fad'u ba, tana halin ciwo yau ciwo gobe sauki ta rika sana'o'in hannu domin inganta rayuwarmu. Ta yi saida abinci alale, Alkubus, Danwake da kayyyakin gidajen na mata duka Amma ta yi shi tunda Dangin Babbammu sun gujemu saboda ni kowa ya ce bazai Dauki bala'i ya kai gidan shi ba.
Kafin mu samu gida a samaru gidan Baba Saminu muka zauna Satin mu daya ya koremu saboda Gobara ta tashi a kitchen ranar ya ce Sanadina ne.
Tundaga lokacin Amma ta tsame kanta da mu daga rab'ar zuru'armu. Da taimakon Amma da kuma Jajircewan Adda yayar Amma muka cigaba da rayuwa, bayan Amma ta gama Saida komai na gadonta Adda bata barta haka ba taimako daidai misali tana kawo mana. Komai a ke fad'a a kaina Amma bata yarda ta kan ce"Hasiya ki kwantar da Hankali Canfi karya ne kambun baka Annabi ya sanar da mu. ba bu farar kafa ba bu maita"
Tun kalamanta na tasiri har suka Daina min tasiri na Fahimci da gaske dai ni Hasiya ina da Farar Kafa. Abubuwa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 24