aranar ta had'a kayanta Adda Fati da tazo suka tafi Tare sai Murna ta ke yi. Ammh da niyar gobe in zamu tafi za su zo mu yi sallama da Safe.
Matan gidanmu da makota sai jajanta Tafiyar Amma suke yi. Sabo shi a ke yi ma kuka daman duk sai suka ji ba Dad'i muma haka.
Mun kwana da shirinmu sai ga shi Allah mai sauya lokaci Da safen Isuhu ya kira Adda a waya yace matarsa na kan gwiwa zata haihu tun daran jiya ya kawota asibiti shuru har lokacin bata Haihuwa ba. Kuma ba kowa a wajenta ba yar garin ba ce yar kwanar farakwai ne da ke nan kaduna.
Jin haka yasa sai Hankalin Adda ya tashi ta yi shirin tafiya mu kuma tace zata je ta gani in an sauka Lafiya Isuhu zai dawo ya tafi damu.
Har acikin raina ban dauka wani Shafin kaddara rayuwa zata kara Bud'emin ba.
Sai ga shi ko da yan Sallama su ka zo Adda ta kusa isa gida ma.
Mu kuma muna nan bamu tafi ba sai dai kawai su ka sha yinin su tare damu Ramatu na ta murna harda addu'an Allah yasa Adda ta fasa tafiya ta hakura ta barmu anan.
Amma kuma acikin ranta addu'a ta ke yi Allah ya sa wannan tsaikon da aka samu Mafitan da ta roki Allah ne ya fara sama mata ta yi ta addu'an Mafita a wajen Ubangiji ga Hasiya ba ta son ta tafi da ita ammh in har Hasiya ta samu inda zata zauna na Har Abada zata koma gaban Adda ta zauna cikin salama har mai kasancewa ta kasance tare da ita. Ba zata rika kwana cikin Fargaba da Damuwa ba.
Habiba dai tunda Adda Fati ta riga ta tafi da ita bata dawo ba sai ya rage daga ni sai Amma. Tunda nasaka tafiyar a raina sai na cire sana'ar Danwake a raina tun ballatana da Assadiq ba ya nan sai sana'ar ta fita raina. Sai dai ana ta zuwa neman Danwaken sai nace ma Maman boy ko zata fara yin Danwaken ne kada ma su siya su gudu.
Nan da nan ko tace zata had'a jari ta fara, ni na zauna na nuna mata Tsarin komai sannan na bata shawaran ba sai ta tara jarin ba. Ta fara da kad'an a sannu sannu dai zata ga jarin nata ya taru.
A rana sau d'aya na ke girki tunda dagani sai Ammah wani lokacin ma ba na yin girkin sai da Daddare da Safe ko Tea ko kuni mu ke sha sai Dare mu ke kara neman abinci. Tun tafiyar Adda ba mu yi waya ba tunda ba ni da waya sai da Adda Fati ta kira wayar maman boy mu ka yi mgana tace Adda ta ce a fad'a mana matar Jauro ta sauka mu duba Isuhu cikin Satin zai zo mu tafi tare.
Tunda naji haka sai muka zama cikin shiri daman kuma ba mu wargaze duka shirin kayammu ba tunda ba fasawa muka yi ba.
A daran muna zaune da Amma ina yanke mata farcenta tace"Hasiya ni ko kwana nawa Abubakar yace zai yi achan garin su?
Kai Tsaye nace"Ban sani ba Amma. Nasan dai yace zai kwana biyu kafin ya dawo."
Muka yi shuru dukkanmu ina ajiyar Zuciyar Amma sai kuma chan tace"Na so a ce yaron nan ya dawo ko godiyar irim Dawainiyar da ya yi damu na samu na yi masa. bazai ji dadi ba duk ranar da ya zo ya iske ba ma nan"
Shuru na yi ban yi mgana ba saboda abunda ke raina ne Amma ta fad'a.
Da safe mai gidanmu yazo Daman Amma ta aika a fad'a masa zamu tashi akwai ragowan kudin mu tunda bamu cike Shekara ba.
Da ya nemi ya bamu ragowan kudin sai Amma tace ya barshi kawai mutumcin sa a gareta ya fiye mata komai alokacin duk in da muka je neman haya a hanamu a ke yi saboda Hasiya ammh shi ya ba su wajen zama tagode sosai Allah ya jikan magabata.
Suka rabu cikin amimci ta na masa addu'a shima ya na yi mata Fatan alheri.
Na riga na Sadakar tafiya ba fashi sai na saki raina kawai Acikin raina na ke jin shima Assadiq ya na daga cikin Mutumen da na ke had'uwa da su a rayuwata ammh kuma na d'an Lokaci ne zasu fita daga Rayuwata batare na so ba sai dai nayi addu'an a duk inda ya ke Allah ya biyasa sannan ina Fatan Allah ya had'amu a Darussalam.
Ina da tabbacin a wajen Adda bazamu sha wahala ba tunda ta baro Rugga da jimawa domin isuhu ya gina gida acikin gari ya Daukota suka dawo.
Sannan daman ya'yanta duk maza ne tafi Amma yawan haihu. Matan nata guda Biyu ne Halima(Tumba) sai Fatima( Baddo') da itace Auta yanzu a gabanta. Shiyasa na cire damuwa Assadiq a cikin raina ammh na kasa daina jinsa a chan kasan zuciyata.
******
GUSAU.
Da gaske Sadiq ya ke yi da yace Hutu zai je gida ya yi. Saboda tunda ya zo ko kofar gida bai fita ba iyakarsa cikin Shashensa ko Shashen Innani ko Bakin get wajen Mallam Taju in za su yi karatu ko yan'uwansa da suka Damu da ya kai musu ziyara bai je gidan kowa ba.
Ko bangaren Umma daman bai cika zama ba saboda su Sultana in ya na son mgana da ita ne ya kan shiga. Shashen Mama kuwa sai dai in ya shiga su gaisa.
Daman bangaren Innani ne wajen zamansa kowa ya sani ba shi da in da yafi nan. Har acikin ransa ya na kaunar Tsohuwar nan duk ko da Tarin Rikice Rikcenta.
Sai ko Shashen Abba in wani lissafin kud'i ya had'a su. Ko wata mgana da ya shafi Dukiyar Abba tunda komai Sadiq na da masaniya a kan su.
Duka kaddarorin Abba da Filayensa tsabar kudad'ensa., Akwai ma wasu kaddarorin da Alhaji Sulaiman da Sunan Sadiq ya siye shi daga shi sai Sadiq sai Lauyansa Barrister Tafida suka sani.
Ko Pin dinsa na akwatunan bankinsa duka Shekarar da aka haifi Sadiq ne mabud'in su. Yau ma tun safe Barrister Tafidan ya zo suna Shashen Abba suna lissafin kudade da zakkar da za'a cire wannan Shekarar.
Abba na gefe komai da Sadiq a ke yi Tunda shine Dan boko.
Wani Alfahari ke mukurkusan Abba in yaga yadda Sadiq ke sauya yare ya na Turance Barristet sannan ga Lissafi a kansa da kuma iya Sarrafa Na'ura.
Haba duk wanda ke gidan SS SHINKAFI bai iya sarrafa Na'ura ba ai yaji kunya tunda kowa tasowa ya yi ya gansu agidan tunda kasuwancin Abba ne na tun Tale tale ne.
Lissfin ya Dauke su har Yamma tunda Sadiq yasa Abba ya ware wasu kudad'e saboda yan'uwansa da ke kauye tare da yan'uwan Umma da Mama.
Bangaran abincin gida daman na Shekara suke ajiye sai wata Shekaran kuma ta zagayo.
Sai bangaran sauya motocin gida Umma da Mama suna da Motocin su sannan yara ma na da shi ta zuwa makaranta Abba kuma baya sauya Mota sai Sadiq yace ya kamata a sauya su. Sadiq kuma har yanzu ba shi da ko keke yace ba yanzu ya ke Ra'ayin Mota ba tunda shi ba mazauni ba ne.
In fita zai yi ya fi bin Abba wajen harkokinsa ko ya Tukasa ko kuma Direba ya tukasa. In kuma zai shiga gari ne sai ya hau ta Umma wani lokacin d'ayar ta Abba ya ke hawa Benz dinsa baka da bai cika Fita da shi ba.
Sannan yasa an ware ma ma'aikata na su albashin sai Hidiman makaranta su Siyama. Daganan sai aka cire Riban Shekaran sai kuma zakkar da suka fita Daman Abba yasan wad'anda ake ba ma Zakkar mabukata ne da takalawa yan'uwansa daman Sadiaq na so kason Dabam ya ke cire musu Abba bai isa ya ce Uffan ba.
In magajin gida yace haka za'ayi Abba jiki na rawa zai ce ayi haka d'in magajin gida.
Sai ana gabda mangariba suka gama Barrister Tafida ya tafi shi kuma yace bari ya koma Shashensa ya yi wanka saboda zuwa masallaci.
Abba ma yace wankan shima zai yi yinin ranar duk anan suka yi shi abinci ma sai dai aka shigo musu da shi.
Sadiq shashensa ya koma ya yi wanka ya saka Jallabiya bata kai masa kasa ba sosai sai ya saka wando baki. Tare da Abba suka tafi masallaci ba su dawo ba sai da aka yi isha'i.
A masallacin ma ana ta neman taimako gyaran speeker masallaci Sadiq ya ce ma Abba za su ba da na su Taimakon.
Abba yace ya ba da nawa yaga ya kamata yace Dubu ashirin za su ba da, Sadiq yasa Abba ya yi mgana da Liman suka ba da acct lamba za'a Tura musu sai godiya su ke yi daman in dai Sadiq na gari yaji ana neman tainmkon masallaci sai in da karfinsa ya kare.
Suna dawowa kai Tsaye Shashen Innani suka nufa suka isketa ta na sallah sai da ta idar suka gaisa.
Ta kalli Sadiq ta na fad'in"Magajin gida duk yau ban gan ka ba tun Safiyar Allah da ka shigo mun gaisa in jin dai lafiya ko?
Kai Tsaye yace"Lafiya ta kalau aiki muka yi da Abba."
Sai ta washe baki ta na fad'in"Au ho to Allah ya yi albarka."
Abba ne ya zauna yana karanta ma Innani abunda suka cire na kudade.
Ta na jin ance an cire ma Mama da yan'uwanta ta tabe baki kafin tace"Daman kwadayyayu ne ba domin Allah Suwaiba ta auri Sulaimanu ba."
Sadiq ya yi dariya kafin yace"Ke da ki ka ce d'an ki ba mai kudi ba ne Rufin asirin Allah ne,.Kuma wata mgana ki ke yi haka Innani.?
Kai Tsaye tace"Uhm to karya nayi? Ya na da kudin ne ba domin Rufun Asirin Allah ba, kaima kasan komai akan Suwaiba da Danginta yi shurun ka Magajin gida."
Sadiq ya gyara zama ya na fad"in"Koma menene wannan ya wuce innani. Mama matar Abba ce sannan sun tara zuru'a atsakani ya kamata ki iya bakin ki, Suma jikokin ki ne kamar yadda mu ke jikokin ki. Ba kyau ki na nuna wariya Hakan ba Daidai ba ne."
Innani sai ta yi shuru taki mgana. Ya na kallonta yace"Baki ce min kin bari ba yar kakata mai kyau?
Innani ta washe baki kafin tace"Na bari magajin gida mganar ka ai itace akan gaba."
Mirmishi ya yi bai ce komai ba karamar wayarsa ya ke dubawa d'azu Tahir ya kirasa bai dauka ba ya bari sai ya natsu sai ya kirasa.
Shigowar Umma da Mama ya katse Mganar da Abba ke fad'ama Innani.
Kasa suka zauna suna gaishe da Innani ta amsa kai tsaye.
Sadiq ya juya ya gaida iyayen nasa su kuma suka yi ma Abba sannu da gida.
Batare da damuwa ba Sadiq yace"Umma yaushe zaki je Gummi?
An ware mu su na su zakkar. Ke ma Mama har da na wajen naki."
Mama ce ta fara fad'in"Angode Allah ya kara girma."
Umma kuma cewa ta yi"Tunda kana nan sai kaje ka kai musu daman Mallam sai mganar ya ke yi nace baka dawo ba."
Innani najin haka ta yi Zaraf tace"Ni ma zani na jima ban je mun gaisa da Mallam Zakari ba."
Sadiq ya kalli Innani cikin mamaki kafin yace"Ba inda zan je da ke. Kalle ki fa tafiya ma dakyar kike yi ammh da kin ji zencen yawo jikin ki na rawa."
Innani na jin haka kawai sai ta fara Sharan kwallah ta na fad'in"Ai Shikenan sai na hakura. daman na so na sada zumunci ne."
Abba na jin haka ya kalli Sadiq ya na Fad'in"Magajin gida ka tafi tare da ita tunda ta na son zuwa."
Sadiq ya kasa mgana shi fa ba zuwa da Innani ba Fad'i ba'a tambayeta ba.
Innani na jin Abba yace a tafi da ita ta washe baki ta na Fad'in"Bari na kira Sulsana ta had'amin kayana a jakata kwana nawa zamu yi ne magajin gida?
Baki ya Bude kafin yace"Ba kwana zan yi ba. Sai dai ke in zaki Tsaya ki kwana."
Ya fad'a kai Tsaye Innani tace"Kaji min Sharrin yaran zamani. Ina laifin mun kwana dangin duk su zo su ganka ayi zumumci."
Sadiq ya mike ya na fad'in"Innani ba zamu kwana ba shikenan."
Innani rai ba dadi tace"Shikenan..salamatu Allah na gani na so na sada zumumci Magajin gida yace a'a."
Ta fad'a ta na wani gyara zama gilashinta kamar ta Allah.
Abba ne ya ke tambayanta wayarta ya daina ganinta kwana biyu.
Innani ta karkace baki tace"Allah dai ya Tsine ma barawo da uwar barawo an sace ta. Tun kwanaki na daina ganinta ballatana ihun nan da ta ke yi in ana kirana."
Sadiq da ya so ya fita sai ya fasa ya Juyo ya na kallon Innani ya na fad"in"Wai ke tsohuwar nan bakya jin mgana ko? Ba na hanaki Tsine ma mutane ba? Ki tsine ma ya'yan wasu da jikokin wasu mu ma wasu su tsine mana."
Da Sauri Innani tace"Arr. Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu. Jikokina y'an albarka ne haihuwan Sulaimanu haihuwan kwarai."
Kai kawai ya girgiza ya fice ya na fadin"Umma ina bangaren ki."
Da toh ta amsa shi.
Shi dai na ya bar su da Innani ta na musu wani Toshon Tarihi tun Abba na yaro irin labaran Innani kenan in ba labarin Abba ba, Labarin kowa a wajenta bamai kyau ba ne ta kan ba da shi ba wani ma yasan harda karin maginta.
Sanda ya shiga Falon Umma ba kowa sai tashin kamshin Turare.
Kan d'aya daga cikin kujerun falon ya zauna ya Dauko wayarsa ya kira Tahir
Sun jima suna mgana har ya ba shi Hajja suka gaisa ta na tambayan Innani yace yanzu ya baro bangaranta.
Shi fa ya kiyaye had'a Innani waya da Mutane in ta shiga Surutun da ba'a saka ta ba sai ta kunyata Mutane.
Kafin su yi sallama sai da Tahir yace yaushe zasu koma zariya.
Sadiq ya yi shuru kafin yace zai fad'a masa in ya saka rana.
Bayan ya gama wayar ya koma ya kishigid'a saman kujeran Umma hankalinsa ya koma kan Tv a tashar Mbc3 Cartoon.
Ya na mamakin waye ya ke kallon Cartoon Umma da ba ta da yara sai kamar an yi masa wahayi ya ce"Sultana."
Kamar ta na jinsa sai ga ta ta fito daga Daki dauke da karamin Kofin Tangara a hannunta kamar kitchen zata je. yadda ta fito kanta Tsaye yasa yasan bata san ya shigo Falon ba.
Duk da tasani shima ya san alaqarsu ta wuce ta yaya da kanwa ammh ba wani sakewa Tsakaninsu.
Illah girmamawa da Sanin Darajan juna bai taba wani Hira da Sultana ba bayan gaisuwa ko Hiran makaranta.
Har ta kawo Tsakiyar falon bata gan shi ba shi kuma sai ya yi lamo ya na kare mata kallo.
Doguwar rigar jikinta ta Roba ce ta Lafe ajikinta abunda ba dabi'arsa bace yau ya yi kallon Sultana Tundaga samanta har kasanta.
Ido ya waro ya na kallon manyan kaya wajen karamar yarinya.
Sultana ta na da cikar kirji duk da siririya ce daga kasanta ta na da Fad'i
Fuskarta ya kallah ta na da cikar Fuskar sannan kafafunta da hannayenta suna da kauri ba kamar na HASIYA BA.
ashe abun ba Shekaru ba ne tunda Sai yanzu yasan Hasiya zata girmema Sultana ammh ita ba ta da komai.
Bai taba ganinta ba Hijabi ba ammh acikin Hijabin ya ke ganin komai nata ba babba ba ne karami ne.
Yaji matsanancin kunya Lokacin da Sultana ta kamasa dumu dumu ya kura mata ido.
Sai da yaji muryanta ta na Fad'in"Ina yi ni ya Sadiq"
Sannan ya dawo cikin hayyacinsa.
Basarwa ya yi da sauri ya na amsa mata. Ya na gani ta wuce kitchen a kunyace duk yadda ya so kada ya bita da kallo sai zuciyarsa ta rinjayesa ya bi bayanta da kallo har ta shige Kitchen.
Sannan ya sauke ajiyar rai har da Sarke hannuwansa a saman kirjinsa ya na sakin mirmishin da ya ke fitowa daga kasan ran shi.
Ta jima kafin ta fito kila ta na Tunanin ko zai tafi ne sai dai ta fito ta tarar da shi kunya take ji ya ganta ba Hijabi.
Ko da mganar aure a tsakanin su Umma bata barinta ta na zama kusa da shi ba Hijabi.
Ta na kame jikinta ta fito kanta a kasa ta na wasa da yatsun hannayenta.
Daki ta ke shirin komawa ya sa ya gyara zama cikin muryan kasala ya kira sunanta.
"SULTANA."
Tsayawa ya yi kafin ta juyo ta na kallonsa da kai ya yi mata mgana kafin yace"Zo nan."
Kamar tace Bari ta Dauko Hijabi sai kuma ta fasa shi ko aransa mamakin yarinyar ya ke duk da ba shi da Dabiar yawan kallo ai bazata ce bai santa ba yarinyar da ya sani Tun tana jaririya.
Kujeran gefensa ta zauna ta kasa kallonsa daga gani a matukar takure ta ke. Sai da ya sha iska sannan ya kalleta yace"Kun gaji da zaman gida ko?
Da kai ta amsa masa bai damu ba ya cigaba da fad'in"da an koma Hutu zaku fara zuwa makaranta in sha Allahu ke da Siyama."
Cikin murnan da ya bayyana akan Fuskarta tace"Allah ya kai mu."
Ya na kallonta kai Tsaye yace"Sai ku dage da karatu ban da wasa. In naga kun maida Hankali wata Shekarar sai a siya muku wayoyi ko?
Da Sauri ta Dago kanta ta na washe baki tace"Da gaske?
Kai ya gyad'a mata kafin yace"In sha Allahu."
Hakoranta sai da suka bayyana awaje daga gani taji dadi.
Cikin mamaki yace"Kina son waya ashe? Wa zaki rika kira?
Cikin jin dadi tace"Baba da su Ma'u"
Bude ido ya yi ya na fad"in"Ku kad'ai Sultana? Sai ta gyad'a kai alamun eh.
Cikin marairacewa yace"Ban da ni ko? Shikenan.".
Sai taji kunya ta Rufe Fuskarta da Tafukan hannayenta ta na yar dariya Lokaci daya tace"Kai ma zan rika kiran ka."
Tabe baki ya yi kafin yace"A'a ai mganar Farko sarki ke fara kamawa. Na gane kin fi son Baba da Ma'u a kaina shikenan na zama maraya Sultana bata so na."
Ba zato ya ji tace"Kai ma ina SONKA wlh."
Sai da ya kalleta ta san abunda tace ai da Gudu ta tashi ta shige daki.
Bai san Lokacin da ya kyalkyace da Dariya ba.
Yarinta akwai dadi cikin lokaci ya yi mata wayau ta fad'i abunda ke ranta.
A fili ya Furta"Sultana ta fi Hasiya Auki."
Sai kuma da ya fad'i sunan Hasiya ya yi tsam me yasa ko lissafin zai yi sai ya kawo sunan Hasiya? ya na kuma da Tabbacin ba ta inda Sultana zata iya Had'uwa da Hasiya.
Ko da Allah zai had'a su ta sanadin ka?
Saboda jiran Umma yasa bai koma bangaransa ba. ita kuma Sultana Tunda ta gudu bata dawo ba.
Sai chan da jimawa Umma ta shigo ba su jima suna mgana ba gajiya ta sauko masa yace zai je ya kwanta.
Ammh sun bari akan gobe za su tafi Gummi shi da Innani tunda yace ya kusa tafiya.
Baisan bayan Innani har da Sultana za'a tafi ba sai da safe bayan sun shirya ana zuba kayan abinci acikin Booth din mota.
Innani ta sha lullubinta da kayanta ma su kyau da wani faskeken gilashinta.
Har da uban kaya domin ta rantse ita sai ta yi kwanaki.
Sai da yaga Sultana ta shirya itama Dauke da Jakar kayan Innani tun wacce taje Saudiya ne.
Yadda Innani ta ke ji da jakar nan ana tabata sai Tsine tsine ya fara tashi.
Ciki Sultana ta saka kayanta kala Biyu.
Umma ke fad'amai Sultana tace itama Zataje shiyasa tace ta shirya.
Ko mgana bai yi ba yana ji ta na gaisheshi ya amsa a tamke kamar ba shi ba ne jiya ya sake da ita ba.
Kafin su tafi sai da suka kara samun wata abokiyar tafiyar Siyama tace zata je Innani tace ta shirya
Salima dai ita da Mama za su tafi Gidan su acikin gari.
Sadiq na gidan gaba Innani da jikokinta na baya gabadaya ta cika Motar da Surutunta kuma komai tagani a hanya sai tace an Tsaya an siya ko gajiya da ciye ciye ba ta yi.
Takaici yasa Sadiq bai yi mgana ba har suka isa Gummi.
Gidan su Umma babban gidan ne mahaifinta malamai ne a garin.
Mahaifiyarta ta rasu ammh Babanta Mallam zakari na nan da ransa da Inna Meri matarsa.
Da ya ke an san da zuwan su sun samu Tarba shi dai Sadiq ya na dakin Mallam zakari suna Hirar jika da kaka su Innani na cikin gida.
Sai da suka natsa sannan ta shigo su gaisa.
Sai ga Innani ta zauna ta na rattaba bayanin ta so ayi auran su bad'i nan ammh Sadiq yace sai ya samu masta dinsa sannan za'ayi auran.
Mallam zakari yace"Me wani masta kuma Dije? Aure ai sunnar ma'aiki ne tunda yara sun hada kansu me ake jira? Kai Saddiqu ko baka so ne na shiga cikin Layin nameman daman fin karfi ka yi min"
Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba.
Innani ta saka ana la'asar suka kamo Hanya shi da Direba.
Duk wanda ya shigo sai ta nuna sa shi da Sultana ta kuma ba da labarin komai Tun daga Tushe.
Da zai tafi yace yaushe za'a zo a Dauketa ya na so su je shinkafi kafin ya koma.
Innani tace sai yadda tafiya ta yi da su, Tunda yanzu sha'anin Tafiya na Allah ne. Yana jin haka ya kama kanshi shi da Direba suka Dauki Hanya
Shima Mallam zakarin irin Innanin ne biye mata ya ke yi su ta yi basa gajiya.
Shi dai tunda ya ba su sakon Abba ya sauke nauyi suka kamo hanya sai mangariba suka iso Gusai.
*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*
*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk
Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.
*19*
Koda su ka dawo babu Innani ba wanda ya damu sanin halinta. daman tunda aka ganta da wannan uwar jakar an san sai ta hantse zata dawo.
Kuma daman ta na son garin su Umma tunda Mallam zakari da iyalansa suna biye mata shiyasa ta ke matukar son zuwa garin Gummi fiye da zuwa Shinkafi.
Sadiq ya na so ya koma cikin Satin nan mai shiga daga kamfanin da ya ke Hidimar kasa sun kirashi.
Shiyasa ya shirya tafiya shinkafi ya jima sosai bai je ba tun wani rashin Lafiya da mahaifin Sultana ya yi ya matsa ma Abba suka je tare kuma za'ayi shekaru biyu da faruwar abun.
Wannan karon ma yace Abba ya shirya su tafi ba shi ta cewa illah Toh.
Yaje Gummi da kwana uku su ka tafi Shinkafi shi da Abba.
Tafiyar ta su da Sassafe ne saboda a ranar zasu dawo ba za su kwana ba.
Gidan Baba Sammani suka fara sauka aka rika ina za'a saka da su. Da kansa ya aika ma su Hussau sai ga su kowacce ta zo gaishe da Abba.
In kunga yadda su ke girmama Sadiq ko Abba albarka.
Ga shi matashi ne ammh yadda su ke kallonsa ya wuce tunanin shi.
Dalilin Sadiq yasa Abba ya yi ziyara sosai a garin Shinkafi. Sannan ya kuma Fitar da kudade.
Tunda aka ji yazo garin mutane sai zuwa su ke da bukatun su.
Su Baba Sammani kuwa an ba su na su zakkar har da karin kudad'en da Sadiq ya ware musu.
Kowa ya zo sai yace yaushe ne bikin Magajin gida da Sultana?
Abba ke rattafa bayanin sai lokacin da Sadiq ya gama karatunsa ya baro Zariya gabad'aya.
Gabadaya labaran daga bakin Innani suka fita Sadiq acikin ransa sai fad'i ya ke yi Tsohuwar nan bazata daina karya ba, ta tsufa ammh ba ta san Darajan Tsufan ta ba.
Su ne har gidan su Sultana kowa ya san Sadiq Surukin gidan ne shiyasa karramawan da aka yi musu suma din dai duk mganar Innanin ne na bikin Sadiq da Sultana.
Nan ma Abba ne ya yi musu bayanin ba yanzu ba in Lokaci ya yi zasu sanar da su.
Sun jima nan suka yi Sallar la'asar su ka kuma ci abinci sannan suka yi shirin Tafiya. Sun kamo Hanya Booth dinsa cike da abubuwa irin ta mutanen kauye. irin su gyad'a aya da su kuka da kubewa,goriba da sauran su, suka baro Mutanen Shinkafi suna ta zamabad'a musu godiya tare da addu'an Fatan alheri ga Alhaji Sulaiman da Magajin gida.
Ranar da suka dawo har washegari
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 24