Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EWbg67q1lN37avGTWa58je *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabooks:JamilaUmarjanafty* *ZAN SADAUKAR DA WANNAN LABARIN NA TSAKA MAI WUYA ZUWA GA KARAMTATTUN MUTANE GUDA BIYU, MASU MUTUMCI DA DATTAKO* *HAJIYA HABIBA ABUBAKAR IMAM IKIRA(YAYATA) TARE DA* *AUNTYSIS(MYANTY)* *YADDA KUKA KARRAMANI A NAN DUNIYA DA KARAMCIN KU, INA MUKU FATAN KUMA ALLAH YA BAKU ALJANNAH SABODA KARAMCIN KU, ALLAH KUMA YA SHIRYA MUKU ZURU'ARKU TARE DA DAIDAITAN DUKA LAMURAN KU NAGODE MUKU SOSAI* *GARGAD'I* *LABARIN TSAKA MAI WUYA HAKKIN MALLAKA NA JAMILA UMAR JANAFTY NE,  A GUJI SARRAFASHI TA HANYAR TAB'A SHI KO SAUYA SHI ZUWA WANI MANUFAR DA BANI DA MASANIYA, YIN HAKAN KAMAR SAB'A MA DOKAR HAKKIN MALLAKATA NE. A KIYAYE* *MANUNIYA* *LABARIN TSAKA MAI WUYA KIRRARREN LABARINA NE, DUK ABUNDA AKA CI KARO DA SHI YAYI KAMANCECENIYA NA SUNA, HALLAYA, GARI KO DABI'A TO A YI HAKURI AN SANE DOMIN ARASHIN LABARIN, BA DOMIN NUNIYA KO TOZARCI GA WANI KO WATA BA* *NA GODE* *GODIYA GA* *KAWATA SURAYYA DEE* *NA GODE MIKI, UBANGIJI YA YARDA DA KE, SANYIN IDANIYA NA KE MIKI FATA TARE ZAMAN LAFIYA MAI DOREWA A RAYUWARKI TA HAR ABADA.* *TUKWAICIN LABARIN TSAKA MAI WUYA ZUWA GA* *AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINA)* *KHADIJA SALISU YUSUF(UMMINA)* *HAFSAT MUSTAPHA(SAHIBATUNA)* *ZAINAB MUHAMMAD CHUBADO(CHUBA)* *MARYAM JUMARE* *HALIMA YUSUF GWARZO(BESTY)* *FIRDAUSI FEEDHOM(MY MENTOR)* *NUSAIBA IBRAHIM USMAN(ALHERI RADIO ZARIA)* *FATAN ALHERI GA MARUBUTA* *ANTY SUMAYYA ABDULKADIR TAKORI* *SANAZ DEEYAN* *MARYAM AMINU(KITTY)* *NANA HALEEMA(MASOYIYATA)* *AISHA ADAM(AYUSHERCOOL)* *AYSHER DANSABO LEMU* *HALIMA HZ(RIVAL)* *HASINA AUTAR MANYA* *NAZIFA SABO NASHE* *NI'IMA SULAIMAN(NIMCY)* *RAMLAT ABDULRAHAMAN MANGA(MAI DAMBU)* *FARIDA ABDULLAHI(FEDDYNBASH)* *SISTER LUBNA SUFYAN* *FATAN ALHERI MADALLAH DA KU NA GODE* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* *01* *SHIMFID'A* *KADUNA_Zaria* _Samaru_ Dogon gida. Tun wayewar garin ranar Asabar nake cikin Fargaba da tsoro, Wani irin sanyin jiki da faduwar gaba. gabad'aya gabbaina sunyi sanyi, gabana kuma bai daina tsananta fadi ba. Duk lokacin da na tuna halin tsaka mai wuyar da nake ciki. Fargaba na da tsoro sun karu ne tunda naga sha biyu na rana ta gota, sai na kasa zama duk yadda naso natsuwa ya samu muhalli a jikina da zuciyata na kasa. Sai faman Safa da marwa nake yi a tsakiyar Dakin Maman Boy, tunda a dakinta na shirya cikin Riga da zani na Atamfata English mai kalan Duhuwa. Sabuwa ce domin duka duka bai fi sau uku na taba sakata ba, kuma sau d'aya na tab'a wanketa. Tana daga cikin kayan aure na da Abubukar, ban yi kwalliya ba saboda ba na cikin wannan sukunin, Daga ni sai kanwata Habiba ne a Dakin da Safe itama d'azu shigowar Ramatu ta jata sun fita tare. Dakin mu nake son na leka ammh kuma Kafafuwana sun yi sanyin da sun kasa daukata zuwa Tsakar gidan namu. Tsorona  na raguwa ne in na tuna da yau Amma ta tashi jikinta da Sauki har tayi wanka ta saka kayanta masu kyau, tunda yan gidan su marigayi Alhaji Mammandi limancin kona sun zo, gidan da aka haifi mahaifin Babanmu kenan. Duk da ina da tabbacin suma din ba domin taya Amma murna suka zo ba, sun zo ganin yadda za'a kare ne kamar yadda Hasashen su ya saba gaya musu a kaina. Ina jin Hayaniyar su Adda Fati a tsakar gida duk da ba wani taro zasu yi ba, ammh dai suna Dafa abinci saboda makota da yan'uwan da za su zo ko ba da yawa ba. Kamar ma sun gama ne saboda naji ana mganan matan gidan duk su kawo kwanukan su, Hassana ta zo ta Dauki kwanon Maman boy. Sanda ta shigo sai da ta ce min"Sannu Adda HASIYA.." Sai da ta fice ne na dawo hayyacina domin nayi zurfin acikin Tunanin da nake yi, kowani Dakika na Bugawar agogon dake kafe a dakin Maman Boy tare ya ke da Bugawar zuciyata. Gif gif! Gabadaya a tsorace nake na kasa kuma addu'a a fili nake fad'in"Ya Allah! Ya Allah!." Daganan sai bakina ya yi nauyin da nake gaza fad'in komai. To me zan ce? Ko me zan roka? In dai rayuwar da nake ciki ita ake Kira TSAKA MAI WUYA to zan iya cewa ni Hasiya tun haihuwata nake cikin Rayuwar Tsaka mai wuya. A kan idanuwana Karfe d'aya ta Buga, daidai da wani irin fad'uwa da gabana ya yi Ras!. Kafafuwana suka fara rawa, Tsoro nake ji ina ji ajikina kamar abubuwan dake faruwa a kaina ba Canfi ba ne, sannan ba Kuskure ba ne. Da gaske ni ina da Kashin da Rab'ata kada'i kan iya Sanadin Ruguza rayuwaka da Dama. Hannanuna guda d'aya na saka na Dafe kirjina da nake jin yana tasowa kamar zuciyata zata fito. Wlh ina jin Tsoro, tsoro nake ji tsoron da ya bayyana har a cikin jikina zuwa saman Fuskata. Ramatu ce ta fad'o dakin da gudunta ko Nauyin cikin jikinta da ya tsufa bata ji, Gud'a ta daidaici kunnina na Dama ta Rangad'amin da ya yi sanadiyar da naji ni kamar na suma ne, wani irin Shuuu! Naji na wucewa na cikin kunnuwana, ban dawo cikin Hayyacina ba naji muryanta cikin Zak'i daman Ramatu akwai zak'in murya tana Fadin"Ta zama..ta zama matar Salisu" Kin zama..kin zama Amaryan Salisu. An daura auran ki yanzu Hasiya, Salihi ya shigo da gudu yana fad'a'" Kalamanta sun yi daidai da lokacin da sanyayyin kafafuwana su ka gazamin sai na bi umarninsu wajen zubewa a kasan ledan Dakin Maman Boy da karfi, ina haki kamar wacce tayi Gudun Tsere. Hawaye na ji sun cika kwarmin idanuwana, na dago ina kallon Ramatu da ke kallona ina jin hayaniyar fad'in an daura aure daga matan dake tsakar gidanmu, Ramatu nake kallo kamar ban ji daidai ba nace"An daura? Da gaske Ramatu an Daura aure na da Salisu? Na fad'a cikin Sigar kokwanto da Tambaya. Mirmishi ta sakarmin mai cike da kaunar da take yi min tun ranar da ta fara ganina. Gefena ta zauna itama ko Cikin jikinta bai damunta, cikin son kwantar min da Hankali ta Dafa Kafad'ata tana fad'in"Da gaske an Daura auran ki da Salisu. Kuma in sha Allahu wannan auren mutuwa ce zata rabashi Hasiya" Sai ta d'an dakata tana lura da kuma nazarina ganin na Runtse idanuwana hawaye suka zubomin sharr! Kamar an Bud'e famfo. Da irin baiwar da Allah ya bata na Tattausan lafazi ta kira sunana cikin Zakin muryanta "Hasiya..Hasiya D'ako ki kalleni don Allah" A raunane na D'ago ina kallonta kuka na son kwacemin. Da sauri ta saka hannunta guda d'aya tana sharemin Hawaye da suka bata Farar Fuskata. Cikin irin kalaman ta Tausasawa ta cigaba da Fad'in"To kuma me meye na kuka? In sha Allahu wannan auren sai ya shafe mganganun mutane a kanki Hasiya sai yasa sun yi nadaman kiran ki da mabambamta sunaye" Kalamanta suka sake Raunana ni. Cikin karfin Hali na Bud'e bakina nace"Ramatu anya gaskiya kike fad'amin? Ta ina bak'in bakin Fentin da tun haihuwata yake bibiyata sannan kuma kice zai gogu a lokaci d'aya? Na fara girgiza kaina Lokaci d'aya Hawaye suna zubomin nace"Ki na dai Fad'amin hakane saboda naji Dad'i kuma saboda kada na damu" Na karishe fad'a cikin gunjin kukan dake fitowa daga kasan raina. Gabadaya na fad'a jikin Ramatu na saki kuka na, sai naji cikin jikinta ya Tokare ni,Sai kuma naji sanyi ya mamayeni na Dora hannuna saman cikin ina Fad'in"Ko ban yi aure ba..ko ban haihu ba. Na tabbata yar da zaki haifa ko d'a zai kira ni Mama watarana Ramatu" Duk dauriyan Ramatu sai da naji Muryanta na rawa tana fad'in"In sha Allahu ki Dauka duka ya'yan da zan Haifa naki ne Hasiya" Ta fad'a tana rumgumeni gabadaya sai kuma muka had'e kai muna ta kuka, kukan tuna rayuwar mu tunda Fari Lokacin da Ubangiji ya hallicemu. Kai bawa ba'a bakin komai ya ke ba, kuma shi mutum tun daga Haihuwarshi a mutuwarsa yana cikin Kalubalen Rayuwa ne da Jarabawa. Sai da muka yi kukan mu muka gaji sannan muka yi shuru shima Maman Boy ne ta d'ago labule ta ganmu muna ta Rafzan kuka. Baki ta rike kafin tace"To kuma miye na kuka? Aure dai ai an Daura shi sai dai Fatan Allah ya fidda auren ku a bakin yan bani na iya" Tana gama fad'in haka ta saki Labulan D'akin ta juya, kalamanta yasa muka saki juna tana sharemin hawaye nima ina share mata Fad'i take yi"ki kwantar da Hankalin ki in sha Allahu babu abunda zai faru" Kaina na Dagamata ba domin na yarda da ba abunda zai faru d'in ba. Ko sauran Lokutan baya da abubuwan ke faruwa ba sani nake yi ba kawai zuwa suke yi ba zato ba Tsammani. Hira Ramatu ta cigaba da yi min saboda na warware, sai na bi yunkurinta ban gwale mata, ina biye mata cikin Hirar nata. Habiba ce ta kawomana Jalop din shinkafar da suka Dafa, da ruwa tace in ji Adda Fati har zata fice na daga ido ina kallonta cikin Dashewar murya nace"Habiba Amma fa? Ta juyo tana fad'in"Amma na lafiya,wani abu za'a karb'o miki a abu a wajenta ne? Sai na kasa mgana to me zan ce? Ganinta kawai nake son yi ,ban samu damar mgana ba Ramatu tace"Kin ji Habiba jeki abun ki" Sai ta kad'a kai tayi ficewarta. Duk yadda na so na nuna komai ba komai ba ne na kasa. A saman fuskata zaka hango tsoro da wani irin Fargaba. Har sanda Adda Fati ta leko ta kira Ramatu kafin fitarta sai da takara jadaddamin kada na damu babu abunda zai faru. Kai kawai na Daga mata, sanin da nayi komai zan fad'a zata ga kamar na raina kokarinta a kaina ne. Kasa zaman Dakin nayi, hankalina na wajen Amma yasa na mike dakyar kafafuwana sun yi tsami sosai. Abincin ma da aka kawomana idon Ramatu yasa na ci kad'an ammh a kirji na ya tsaya tunda ga shi nan ina jinsa, Kirjina suya yake yi min. Daman tun a kwanaki nan nake fama da ciwon kirji da baya, nasan Ulcer d'ina ce ta tashi ammh halin da nake ciki yasa ban tsaya bi ta kanta ba. Jan kafa take yi saboda ta yi min Tsami ga wani sanyi da jikina ya yi a haka na fito daga Dakin Maman Boy. Gidanmu irin Dogon gida ne ba shi da Fili ko kad'an a tsuke yake ga kuma Jerin gwanon Dakuna reras fin goma shiyasa in dai ka shigo anguwan Samaru kace a kawo ka DOGON GIDA ko yaro ko Babba zai kawo ka har Kofar Gidanmu. Ko sha'ani ake yi a kofar gida ake yi girki saboda ba fili ko a shiga makota ayi, Matan ne aure reras Goma sha uku ne a gidan Amma ce ta sha Hud'u da bata da miji. Kuma kowacce na da Tarin ya'ya kamar tsaki shiyasa kowani babban gidan albarka bayan yaran gidan ma har da na makota. Gida kuma gidan Haya ne, shiyasa bakomai ba ne zaka ganshi cikin Tsari a ire iren gidajen da rayuwa ta kan jeho ire iren mu. Koda na fito duk matan gidan suna waje ana ta cin shinkafa ana Hira, Yaran kuma suna ta guje gujen su, suna ta Hayaniya ni fa ba domin su Addaa fati ba, ba taro na so ayi ba, Tunda nasan da yawansu taron su ci abinci ne su koma suna Dariya da Kaddarata. Ko Amma sai da tace bata son Taron nan Adda Fati ta roketa tace adai yi ko yaya ne yafi ace ba'ayi gayya ba. Har ga Allah ban so ma wata ta ganni ba naso ne na sulale na shige Dakin Amma ammh ina sai da Maman Salihu ta ganni ta ko Rangad'a gud'a tana Fad'in" Amarsu ta ango" Sai kallo ya koma kaina, nan fa suka taru a kaina suna ta min Shegentan ka da suka saba,ni dai ina kauce musu saboda hayaniyar tayi min yawa tana  kuma kara tafiya da Fad'uwar gabana. Dakyar na yakice su na Fad'a Dakin Amma tana zaune gefen katifar da waje wajen zamanta shekaru masu yawa, bayanta an kara mata Filo guda Biyu saboda ta zauna Dakyau. Gefenta kuma Wasu abokan wasa suke wajen Babanmu. ni sauran ma ban tsaya kallon su ba kafafuwana ke Hard'ewa kamar zan fadi ganin ina shigowa kallo ya Dawo kaina. Suma din kamar matan gidan namu Gud'a suka saki suna kirana da Amarya sunan da in sun kirani da shi nake jin wani rauni ya lullubeni a shekaru biyun da suka gabata an kirani da suna Amarya, ammh bai Dore ba na tashi daga Amarya na koma Bazawara da wasu jerin sunayen da bazan iya fad'an su ba. Ni dai ban tsaya biye musu ba, samun kaina nayi da karisawa in da Amma take zaune tunda na shigo ta Dago tana kallona da Mirmishin da ya kasa bace mata a saman fuskarta. Bansan na zube a gabanta ba sai da naji kafafuna sun gamu da siminti har yar kara sai da suka ba da Kas!, Cikin Fara'ar da ta boye tsoron dake kan Fuskata nace'"AMMA.." Kai tsaye tace"HASIYAA."! ta kirani cikin muryan ciwo ammh cike da karsashi da Fata. Da Rarrafe na karisa gabanta ina mai riko hannunta guda d'aya, ganin haka yasa ta dora dayan hannunta nata Gabadaya ta jimke hannayena cikin nata. Kwallah suka cikamin kwarmin ido ammh ina kokarin maida su cikin yanayin muryanta tace"Allah ya albarkaci wannan auran naki Hasiya. Fitinar Duniya ya kare ki da shi, Allah yasa gidan zamanki ne Yasa mutuwa ce zata rabaku" Su na d'akin ne ke amsawa da Ameen koda bai kai zucci ba, ni kuma duk yadda naso kada hawaye su kawomin sai da suka zubo kar kan hannayen Amma, itama kamar zatayi kukan tace"Ba kin ce Allah ba? Ai shikenan Hasiya kin gama mgana share hawayen ki kin ji" Sai na zare hannayena cikin nata ina Share hawayen da suka faramin Tsere a saman fuskata. Kamar Daga sama naji wata mata na Fad'in"To an dai Daura auren Allah yasa zuwa anjuma kada mu ji wani bala'in ya afkama angon" Da rinanun idanuwana na kalleta Gambo ce a matsayin y'a take wajen Babanmu. Na kasa mgana to me zan ce? Gaskiya ta fad'a nima Fargaban dake damuna kenan tare da Tsoro. Kafin ma mganarta ta sha iska Inna Talatu Mahafiyar Ramatu tace"Da ikon Allah ba abunda zamu ji sai alheri" Sai kuma Dakin ya Dauka da Insha Allahu cikin yakinin da su kansu ba su Tabbas din hakan zai kasance ko abunda ya faru a baya ne zai maimaita kansa. Had'a ido mukayi da Amma sai ta gyada min kai cikin yakinin da nagani a kwayar idanuwanta, sai na jinjina mata kai Lokaci d'aya ina goge fuskata. Na mike a kasalance ina jan Kafa zan fice Inna talatu ta taidani da Fadi'n"Kada ki ga baki ga Ramatu ba Fati ta kirata suka tafi gidan Dilalliya Jummai, mganar sauran kayanki dake Hannunta" Da kai na amsa mata ina Ficewa, acikin jikina nake jin wannan karon kayan ba zasu dad'e kamar baya ba zasu sake komawa Dilalliya Jummai kamar baya dai. Wannan karon ba Dakin Maman Boy na koma ba,na maman Salihi na shige tunda shi ke kusa da Dakin mu. Kan kujerata na samu na Kwanta ina Numfarfashi. Rufe idanuwana nayi kamar mai barci nan ko ba barci nake yi ba,Tunani ne suka Daibaye Duniyata Gabadaya. In tunanin in na samu zama gidan Salisu Matarsa fa? Wacce tayi ikirarin duk abunda ya samu mijinta sai ta Kasheni. Na tuna labarin da Habiba ta bani da sukaje min jere ita da yan'uwanta haka suka taru suna zagin su da Tijara iri iri, Tunda gida D'aya zai Had'amu da Matarsa uwar ya'yansa. Tunanina ya tsaya cak da tuna in kuma Abunda ya faru da Abubakar ya Faru da Salisu fa? Jikina sai da ya Dauki Dumi da Tuna da Abubakar da abubuwan da suka Faru a baya, har kwanan gobe duk inda wani Dangin Abubukar ya ganni ko ya ga d'aya daga cikin yayyina ba'a rabuwar arziki ba irin sunan da ba su k kirani da shi ba, mugun bala'i kuma sun jima suna rokarmin shi, sun yi kuma ikararin yadda na nakasa Rayuwar Dan'uwansu nima sai sun nakasa ni. Tuna hakan da nayi bansan Dumin da naji a saman fuskata dumin hawaye ba ne, sai da naji digarsu har dogon wuyana da ko Sarka Babu. Yanzu in wani abu ya Faru da Salisu fa? Me zan ce ma mutane da suke kallona da Tabon kashin Tsiya?Da masu cewa Naman jikina ba shi da kyau kuma Rab'ata ma kawai in mutum ya yi da sunan neman aure na shi da arziki har Abada sai dai yaga anayi, ni da akayi min canfi dalilin Haihuwata ne karyar Arzikin marigayi mahaifinmu Alhaji Mamman Mammadi Kona. Ba kuma a bakin bare ba ne wannan mganar abakin Dangin Mahaifin mu ne. Har ciwon Amma da aka kasa gane kanshi an ce duk Sanadina ne, duk in da na zauna na Rayu wajen bazai kara zama mamaro mai amfani ba. A cewar su ni wutsiyar Rakumi ne gani na ba alheri ba ne. Bansan ina kuka ba sai da naji Shesshekan na fita sannan nasan kuka nake yi, ba zan iya hana kaina kuka ba shiyasa sai da nayi ya isheni sannan na hakura na share hawayena. Ba na sallah ina fashi shiyasa na kara gyara kwanciya Barci na neman saceni naji Muryan Ramatu na kiran sunana, daga cikin Dakin na kwala mata kira sai ta jiyo ta shigo. Tashi nayi zaune na matsa mata ta zauna a gefena labari take ba ni yanzu Daga gidan Salisu suke sun je sun kaimin sauran kayan da suka amso wajen Jummai Dilalliya. Kamar da mgana a bakinta yasa na kalleta ina fad'in"Me ya faru? Da sauri Ramatu tace"Babu abunda ya faru kinga Dakin ki? Yayi kyau sosai. Da ya ke kinsan kayanki ba su yi komai ba sai suka kara haska wajen gashi Salisu kamar ya sani ya yi mana Fenti kalan kayanmu" Ta karishe Fad'a cikin Dariya, kallonta kawai nake yi ban yi mgana ba ta cigaba da fadin"A kofar gida muka had'u da Salisu da abokan sa kin ga bakin Mutumin naki kuwa?kamar gonar Auduga" Sai a lokacin nayi mirmishi Da ya fito daga kasan zuciyata. Da gaske ina son Salisu domin kamar Abubakar sun  so ni da dukkan zuciyan su, sannan sun toshe kunnuwansu da duk wata mgana mara kyau ko Dad'i a kaina. Lura tayi da Labarin Salisu na Farantamin rai yasa ta cigaba da bani Labarin shi tana fadin"Yana ganin mu ya fara washe mana baki. Ganin Adda Fati yasa bai kwafsa ba, sai da tayi gaba ya bini yana fad'in ki kularmin da Matata. Kin ji yadda yaja kalmar Matata kuwa? Tafad'a tana Dariya nima sai da na Dara, ba ni da waya a hannuna kwanaki ita na Saida da Jikin Amma ya tashi, Salisu ya so ya siyamin na Hanashi ganin Hidimar biki na kanshi, da niyar sai bayan biki zai kara siyamin wata. Daga mganar Salisu muka koma hirar Haihuwarta da zatayi watan gobe, Tana Fad'amin duk ta gama siyan kayan Haihuwa. Cikin karfin jiki da na Zuciya nace"Ai Nura ba daga baya ba. Akwai son kyautatama iyalansa Namiji ne samun kamar sa a wannan zamanin sai an tona" Tayi wani kayattacen Mirmishi kafin tace"Na ma manta ya kirani Dazu muna Hanya. Yace na yi miki Fatan alheri" A d'okance na amsa da Nagode. Domin kaf cikin layin masoyana bayan Iyayena da yan'uwana Ramatu ta Biyo baya wlh Nura na sahun su Salisu da Abubakar su din shakikan Masoya na ne da har addu'ata ina sakasu da Fatan Allah ya had'amu da su a aljannah Firdausi. Mun cigaba da Hira da yasa na saki jikina, muna tare da ita har yammah lokacin mun yi mgana da Salisu da wayar Ramatu yace ba da jimawa ba abokan sa zasu zo Daukana, da yake ba nisa gaban anguwan mu ne da Kad'an. Ramatu ta sanar da su Adda Fati suka fara shirin mika ni gidan mijina a karo na biyu. Da farko tsoro ya hanani sakewa ammh da naga har yammah tayi ban ji wani abu ya taso ba sai na saki jikina, ammh in na tuna na Abubakar shi har an kai ni gidansa. Ya shigo Dakina kenan da ledojin kajin sa na amarci aka kirasa a waya,wayar da ta tarwatsa duka farincikinmu har ma da auran Gabadaya. Wanka Ramatu ta matsamin na sake yi na sauya kaya zuwa wata Shadda milk, ita ta dinkama ni da ita da sunan in ta haihu mu saka ammh da auran nan ya taso sai tace mu yi amfani da shi. Ban yi kwalliya ba na dai shafa Hoda na saka man baki. zuwa Lokacin hayaniyar gidan ta ragu, Kayana na sawa Ramatu ta had'amin su a wata karamar akwatina tun na aurena da Abubakar ne. Dakin Amma a ka kaini bata tawaita nasihan ta ba, Albarka ta sakamin kamar yadda ta saba. kuka nake yi kukan da har ya fito ana jin Sautin shi Ina ji Gambo na sake fadin"Kuka kuma Hasiya? Ke da ba auran Farko ba? Ina cikin Babban mayafin da Ramatu ta sakani sawa, na ke kallonta tunda Shara shara ne ana ganin na waje,ban sa waye ya bata amsa ba tunda akwai muryoyi da yawa a dakin Har da Gabadaya matan gidanmu suna Dakin. Daga karshe naji Muryan Ramatu na Fadin"Ko ba auran Farko ba ne ai aure dai sunan shi Aure" Ni dai ina hawaye muka baro Dakin Amma zuwa Dakin Maman Boy, Adda Fati ta shigo tana fad'in"Ramatu ina ga dai sai bayan mangriba angayen zasu zo ko? Domin naji ana ta kiran sallah" Ramatu tace"To kila dai sai an yi sallar"  Adda Fati ta fice tana fad'in"Gaskiya dai mu ma bari mu yi sallar kafin su iso" Tafad'a tana ficewa Daga Dakin sai alokacin Tunanin ina Adda  Rukayya ya Fad'omin tun safe da na ganta sau d'aya ban kara ganinta ba. Ko ya'yanta ban ga ko D'aya ba, sai yaron Adda Fati nagani kuma shima zuwa ya yi ya gaisheni. Sai na kalli Ramatu da ke faman latsa wayarta ina fad'in"Ramatu wai ni ina Adda Rukayya ne? Ko ta koma gida ne? Tsam naga tayi kamar tana nazari ni ko na kafeta da ido ina nazarinta, taasan na santa sarai bata isa tamin alaye ba. Sai kawai nayi mirmishin takaici

Chapter 1 of 24