Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 12
mai isarta dakuma samawakanta mafita ,kaitsaye Fatima dakin takoma da sallama aa ganin uncle adakin tagaidashi sannan tace uncle naganka annan kasan mara lafiyanne eh mana Fatima aishine maibabban suna wandayataimakamin ok nagane Allah yasakamai da kalkairi shikuwa Muhmd duk abinda sukeyi yanajinsu sbd yanason yakebekansa shikadai sbd yayi tonani yayi alkawarin bazai fitoba harsai wannan yarinyar tatafi sbd bayasan godiya shiyanzumma bayasan kallan fuskar mace indaiba wannan yarinyar ba shiru dakin yatauka babu wandayace wani Abu sbd kowa daabinda yakesakawa akansa ,Fatima tagane yanzundai tafahimta wandaya taimakawa uncle dinta dakuma wandatagani agado anashiga dashi dakuma wanda tayimai tufi duk abudayane tabbas duk mutum dayane amma kuma wane abokina doctor mai irin kanshin turarensa? dakuma sunansa to amma wane abokina Abdallah wato " farisinta " hartsayin mintina ,doctor neyadago yakalli Fatima gimbiya dama baba tsohu uncle dinkine eh uncle dinane, tsohuwa ashe hajjiya duk abin nagidane eh wllh to munadai godiya Allah yasaka da alkairi ameen mungode mumasosai hira akeyi sosai amma Fatima hankalinta gabadaya bayakan hirartasu tunaninta shine tabbas tanason yakara fituwa dan takalleshi amma hakan yagagara dan itakanta tafara tunanin sbd itayakifitowa amma aibaisan itaceba to kumayazatayi da kunyarsa tabbas zataje takira Aisha dansuzo tare ,bari inje indawo to doctor bari inrakaki aa nagode aikuwa sainaje duk kansu murmusawa sukayi amma tsohuwa sai taji badadi sotayi Muhmd nedawannan yarinyar maihankali da nutsuwa shikuwa jiyayi zuciyarsa namasa zafi dan jin Kalmar da doctor yafada, amma yazaiyi to mashi inaruwansa yaji dayanbangare nazuciyarsa yana fadamai sukuwa tsohuwa da tsohu nanfa wata sabuwar hirata kalle . Tafiyasukeyi amma shikadai yake maganarsa ita kawai kallanshi take dansotakeyi yagama sannan tafara jiramai tanbayoyi amma dataji yaki denawa saita tsaya tace doctor dawata irin murya a kasalance yace naam gimbiya inason zantanbayeka karkayimin mummunar fahimta wannan abokina naka nakesan sani murmushi doctor yayi sannan yace to anawa murmushi tayi wanda yatsaya iya lebenta sannan tace inajinka kafadi abinda kakeso kallanta yayi sukahada ido sannan yace abinda nakeso shine zuciyarki dakuma number dinki pls dan Allah kibani wannan damar kosaudayane ok kawaitacemai sannan tace doctor yazaayi naganshi saikin bani number dinki wllh zanhadaki dashi amma mezakimai to karfa kamanta addini yace kada kashiga abinda baburuwanka to naji amma bani number din aa saikafara kiranshi aa aiyana asibitinnan kaikiwurinshi kawaizanyi to tabude Jakarta tadauko card tabashi ,sannan sukakarasa bakin dakin sukashiga atare sannan tagaida mama yau Aisha batazuba ,mama tace Fatima munaganin kaya Allah yasaka da alkairi ameen mama Aisha fa batazuba eh ,tajuyo takalli doctor yaushe zaasallami mama eh nan da gobezaa iyasallamarta to gaskiya asallameta tagajidazaman hospital ,angama gimbiyata ,yauwa Fatima dama nagaji da zaman hospital dinnan wllh to mama yanzun mekedamonki babukomi yata to doctor dubata kasallameta to gimbiya angama takeyadaga waya yakira nurse takara dubata take yarubuta sallama, Fatima take takira direbata yazuyadaukesu tafadamusu uncle dinta yananan sannan tayimusu sallama tatafi doctor yace to yanzun nakaiki wajen abokin nawa eh muje ,kaitsayi dakin mai babban suna suka nufa tajuyo takalleshi tace yanaga haka eh aishine abokinnawa kasamagana tayi yakalleta yadai bakomai suka karasa dakin yabude suka shiga dauke da salama a bakinsu Muhmd yana zaune kusa ga uncle dinta yandayagansu a tare sun jiru ba karamin hargetsa zuciyarsa yayiba yarasa meyasa yake jin wani Abu akan yarinyar nan tsohuwa ce tace hajiya kin dawo eh na dawo kaka ya mai jikin da sauki alhmdllh toh allah kara sauki sannan ta juyo ta kalleshi da wata irin murya mai sa kasala tace ya jikin naka said yaji jikinshi yayi wani mugun sanyi ko kallon inda takebaiyiba sannan yace jikin alhmdllh masha Allah dan shiru ne yadauka na wani lokaci sannan ta mike tace Allah yakara sauki ajima zan rako dad yaduba jikin naka, toh shikenan cewar tsohuwa munagodiya Anatare ai kallan uncle dinta tayi tace uncle akwai sabo adakinka zantafi sai anjima Allah yakara afuwa dannasan bayanzun zakatafiba aikuwa dai ina zani mebabban suna ba lafiya aikuwa dai garakakula dashi sosai to shikenan kigaidamin da Ahmed da kuma, kiranda akayimatane yasata fitadasauri taduba bilal ne yakira karawa tayi akunnata yayimata sallama ta amsa madam dama bakene kikayi ok tuganinan amma dad yasanda zuwansu aa gaskiya amma barinakirashi natanbayeshi aa kabarshi barinakirashi to madam kaitsaye wajetayi tajiance gimbiya angama ne zakitafi, eh amma zuwa darezan dawo insha Allah to harbakin kofar mota yarakata sannan taja tatafi agajiye tashiga gida su Abdallah nekefalo yana danduba littatafansa shialallai soyake saiya wuce Antysa yanakuwa hakan saiga Fatima tashigo yataso yarungumeta, sannan yace to dazun nakejiranki shiru amma inakikashogane naje hospital na duba jikin mama da uncle dakuma maibabban suna, amma Abdallah inaso mujewajen Yaya bari inshirya saimutafi to Anty kice Anty kinfarasan abokina aidamanagayamaki shidinfa nadabanne acikin maza amma Anty idan munje karkice komi nine nan zansaka shiyayimaki magana amma kekuma duk yadda kikaga abokina karki wulakantaminshi sbd shibaabin awulakanta bane ,duk danasan wannan bahalinki bane kuma inaso kitaimakamai dan Allah Anty sbd inaganin wani Abu atattaredashi to Abdallah insha Allah zanyi yaddakakeso yauwa matar Yaya ,murmushi tayi tace angama alkalin masoya dariya yayi sannan yace to yanzun dai kitashi kishiga kihuta sannan kici abinci inbahakaba bazankaiki wajenahiba Allah Abdallah banajin yinwa ,Allah saikinci nikuma zanrakaki karfa kimanta ninemagajin dad wllh karkibar raina yabaci danyanzun zankira dad nagayamai ,dariya sosai tayi tace Abdallah nakenan kanasani farinciki aa kirani da dad,kai ko eh mana maza oya maza banasan western time to kawaitace tashige dakinta tanamurmushi tabbas adduarsa tafarakarbuwa yanzu Allah nagode maka ,sannan yacigaba da karatunsa itakuwa bayantayi wanka sannan tayibitar litattafanta sakamakon yau tana hutu harkarfe biyar tayi basutafiba sakamakon dad dayakirata yacetajirashi sutafi tare basuji dadiba amma hakasuka hakura tare dashiryawa yau Fatima itace zatayi driven yadda zasuringa zagawa sosai aikuwa bayansun dad yadawo sukashirya sukatafi dad dakyar yayarda zatayi toki itada Abdallah ne agaba shikuma dad da Ahmed sunabaya saikuma jaridarsa dayake faman karantawa talarabawa sunata tafiya subitawannan hanyasubulla tawaccan dad becemusu kalaba harsuka isa bakin super maket tajuwo takalli dad barimushiga dad mudanyo siyayya to amma tamarasa lafiyace ko dan sosa kaitayi sannan tace da Abdallah neyakeso amma barisuma ayomasu yauwa kinsan idan mutum bashida lafiya saiyaji bakinshi badadi eh hakane dad amma bari inyo dasudin Ahmed tasomana aa nibazaniba to shikenan sukawuce sukashiga ita da Abdallah aciki suketattaunawa gashi baaganishiba to yazaayi ahakura saigobe to shikenan sosai sukayo shopping kowanasa daban sannan akasamusu mota sukatafi hanyasuka dauka har hospital dad neyakalleta yace mamana bakuga wandakuke neman bane eh bamuganshiba cewar Abdallah to shikenan itakuwa Fatima kunyace taisheta duk datafahimci baiganeba, harkuwa hospital dinsuka iso sukashiga dakin uncle amma bayanan suka ajemai kayannasa sannan suka wuce dakin Muhmd itakuwa Fatima gabadaya jikinta wani iritakeji gawani sanyi datakejiyanashigarta dad nanne dakin mara lafiya wanda yataimakawa uncle ok tomuje aha dayagata tsaya yasakai yashiga da sallama yashiga dukkasuka amsamai sannuda zuwa gaguri yauwa yazauna sannan sukagaisa sukuwa Fatima da Abdallah kasa shigowa yayi Anty kawaiki shiga kibasar kinji to Abdallah amma kaizaka fara shiga aa kekifara shiga itamutumce marasan jayayya hakatasa kaitashiga dauke dasallama aikuwa karafsuka had a ido sannan Abdallah yayi tasa sallama yashigo Muhmd dayayi kasa dakansa ,kuma tundazun yakekallan Ahmed Allah sarki Abdallah na muryar Abdallah ce tasashi saurin dagowa Abdallah sunahada ido dayaya dayakwasa aguje yafada jikinshi yarungumeahi kicin farinciki Yaya na naam Abdallah na sundade ahaka kafinsu saki juna Abdallah na inakashiga nayi missing naka sosai nima haka yayana . Itakuwa Fatima gabadaya jikinta wani mugun sanyi yayi tadaskare awajen sbd tsabar mamaki ashedai duk abudayane cab akaimatsala tunanuka takeyi kalakala tsohuwa ce tace hajjiya gagurinzama zauna itakuwa tazauna nanfa akabayyana komi dakomi,shidai Muhmd sai zubamai godiya akeyi amma yayi shiru baice kalaba itamakuma batace komiba dad yaji dadin haduwarsa da Muhmd din sbd yarone mai hankali wanda kowanne mutum zaiyi alfaharin kasancewarsa ataredashi ,dad yace nagode sosai abokina ai anatare dad yanzun yaushezaasallameka dad wllh bansaniba ok barinatanbayi doctor din danzaman hospital babudadi uncle dinyarafa yaushe shizaa sallameshi dad shiharyanzun baigama warwarewaba dan Allah nima a sallameni wllh nagaji nima gashi haryanzu su mama harira basuzo dubiyaba garakullum adinga zuwa gida anamin diresing to shikenan barinakira doctor din aa abari mugama tattaunawa to shikenan shirasukayi sosai shikuwa duk abinda akeyi Abdallah najikin Muhmd sai gayamai maganganu yakeyi akunne shikuma saidan murmushi yakeyi da alama zancen Abdallah yanashigarsa itakuwa Fatima gabadaya tashagala da kallansa bakaramin kyau murmushi yake maiba amma kuma wane sashinazuciyarta yanafada mata Abdallah gayamaisa tanasanshi yakeyi inna lillahi wainna ilaihirraju'un shikenan Abdallah yagama dani . Dad neyace abokina Abdallah kenan wannan soyayyar taku hadin Allah ne murmushi Muhmd yayi Abdallah ne yace aidadi bazakasan hadin Allah bama sairanda yayi hada ido dasukayi da Fatima ne yasashi yinshiru doctor neyashigo harkasa yagaida dad sannan yace gani idan bawani abu yakamata a sallamesu to shikenan tabangaren Muhmd bamatsala amma uncle dinta shine kullum sai andingayimai diresin to shikenan badamuwa saizuwa gobe idan Allah yakaimu zaasallameshi to shikenan tashi kaka mutafi nakaiku gida saimuwuce to shikenan hardaki sukaraka uncle sannan sukayimai sallama sukatafi, itada Muhmd da Abdallah dakekan cinyar Muhmd itakuma taketoki cikin nutsuwa nuni kawaiyakemata da hannu nahanya ahakahar Allah yakawosu inda gidan yake yakalleta yace yaisa haka sukasauka dukkansu kaka tabude gidan suka shiga sannan akashigada kayan daakasiyomasu hardakin kaka sukaje sukazauna sannan sukayimusu sallama sukatafi kowanensu da abinda yakesakawa aranshi dad Abdallah dakuma Fatima gabadaya kowanne da abindayake tunani tabbas ageramasu gidannan gaskiya wannan mutumne kalli yadda gidansu yake amma yaiya dunkulekudi yabayar akayiwa uncle dinsu aiki kuma anyi anyidashi akan yakarbekudinsa yaki yaceshi dan Allah yayi ,harsuka karasa gida sannan kowa yashige dakinsa yayi wanka sannan sukafito yin dina bayan sun gamane dad yakalli Fatima yace mamana kinga yadda gidansu takwarana yakeko eh dad nagani to yanzun mekike tunanin zaayine dad kawai ageramasushi kokuma acanzamasu wani to mamana kome yanahannunki kiyi abinda yadace insha Allah dad amma inaso insan gidan nasune kokuma nahaya eh hakan nadakyau amma dad gakaine zaka kirashi katanvayeshi sannan dakuma inda zasuzauna kafin agama ginin to shikenan bari zankirashi saimuyi magana insha Allah dad dama jiya munyi magana da manajan company turkiya zasudinga kawomin kaya masu kyau nima kuma zandinga aikamasu da wasu kayan irinnamu to amma yace zaizuwajenka kuyi magana sbd niban aminceba cewanayi sai abinda kace to bakomi Allah yasanya alkairi acikinsa ameen kinga Allah yasamaki nasibi gashi daga one company harkinada three company Allah yatayaki riko mamana ameen dad kominazama duk jinjinar takace murmushi yayi sannan suhaukaratun littattafai harsuka kammala sannan yace akwai wata makaranta da zabude amma ancemin saikin amince zakizama daya daga cikin shegabannin cikinta ,dad kaga wanna mata haddar haka akayi gaskiba bayan iyaba abubuwa sunmin yawa aa mamana kikarba kinga sai kigayamasu ko saubiyune a sati kiringazuwa to dad kace naamince yauwa mamana Allah yayi maki albarka yabaki Yaya masuyimiki biyayya dakuma miji nagari duk dama baba Abdallah yayimaki miji dariya tayi sannan tace ai dad lamarin Abdallah saishi to maga aje akwanta ,Allah yatashemu lafiya ameen dad tawuce dakinta ta kwanta . shikuwa dad wllh bakaramin so yakeyiwa hadin da Abdallah yayiba dan wllh lokaci daya yaji yanasan Muhmd sosai harransa yanafatan aceyazama sirikinsa tabbas zansasu a addua Allah yasa suso junansu kuma suzama alkairi gajunansu amma tabbas yarannan namijine Wanda bakada wane haufi akanshi zakabashi danka wllh indai Fatima tanasan wannan yaron wllh zanbatashi batareda duba wani abunasaba amma indai Fatima batasanshi bazanmata doleba saina hakura dahakadai dad yagama saka da warwararsa sannan yatashi yashiga dakinshi dan kwanciya . Itakuwa zulaihat tayi bincike sosai akan Fatima angayamata yar gidan minister ilimi ce ta jaha tabbas asiri bazai citaba kumagashi itama malamar kantace tabbas saidai tacanza shiri dole zatazama kawar Fatima duk dadai basaartabace,zama kawar Fatima shine mafita shine zatasamu damar da yin abinda takeso indan tasgiga jikinta saitayimata takaruwai takwaceshi sannan daga bayata shiga rayuwarsa koda boka koda malam tabbas hakazaayi kawarta Hauwau kawarta tafada tana dariya. Bangaren Fatima kuwa dad yakira Muhmd yatanbayeshi sannan kuma yayimai maganar zasudawo kusa da gidansu wani karamin gida suzauna kafin agera masunasu Muhmd yakafe akanshi baiyardaba saida dad yanuna bacin ranshi sannan yahakura gobeni zasukomu kusa da gidansu Fatima babu Wanda yakai Abdallah jindadi Fatima tasa drive ya kwaso masu kayansu sannan tace itakuma da yamma zatazutadaukesu baiji dadin cewar Fatima ce zatazu tadaukesuba amma maganar dad ce babu yadda yaiya sbd shikansa yanasan dad kamar yadda yakesan Abdallah aikuwa bakaramin shiri Fatima tayiba dan gidan dazasu zauna tasa angerashi sosai barema dakin dazaizama na Muhmd ga kayan abinci data zubamasu babu abinda babu, dayamma ita da Abdallah sukadau hanya zuwa gidansu Muhmd suka isa kaitsaye suka shiga dauke da sallama abakinsu kaka taamsa masu taredabasu wajen zama,danfa sukayita hira sosai dan lokacin datazu Muhmd bayanan Abdallah ne yasa tsohuwa agaba yanata tsokanarta dan shibaisan dadin kaka ba ,kaka barira bakaramin masifa takemasuba ko gidan basazuwa sosai dama Fatima batazuwa gidan sbd yadda kaka barira ta tsaneta hirasukeyi sosai kafin Muhmd yashigo Abdallah yafada jikinsa yadaukeshi, yauma yakara fadamai Abu akunne suka kwashe da dariya yaune karan farko da tafarajin dariyarsa sosai takekallansa shima kuma itan yake kallo sosai hankalinsa nakanta ,Muhmd ne yace Abdallah kasanme aa yaya saikafada kainefa babba sbd kafi hankali kagakai hargaidani kayi tsohuwace tayi dariya to itama samun itazakuyi agaba kuyita tsokanarta shiru sukaimata Fatima duk abinda sukeyi batasaniba sbd hankalinta baakansu yakeba Muhmd ne yajawo Abdallah yafadamai wata maganar sai sukakuma sa dariya Muhmd ya sauke Abdallah yace maza mutafi mota kafin wani yarigaka ya matseminkai sukakuma dariya Muhmd yakashewa Abdallah ido daya ,nidai nayi gaba kufito mutafi cewar tsohuwa tafita tabarsu abinta har lokacin Fatima bata mutsaba sai da Muhmd yadaidaice idonta yahura mata iska sannan yace kallan yaisa haka kitashi mutafi tareda kashimata ido daya ,itakuwa toni tayikasa dakanta tashimana tayimai banza yajuya zaifita sannan yace aiga kenkesonan a kanhijabinki aikuwa dasauri tamike tayo indayake aguje beankaraba tafado kansa cikin gigita da fitar hayyaci sosai tarikeshi dayakasa kwakwaran mutsi yanata kokarin cireta jikinsa amma yakasa sai kawai yarabuda ita sbd yafahimci sosai taji tsoru saida hankalinta yadawo jikinta sannan tasakeshi takumayi kasa da kanta ,to aitunda burinnaki yacika kinrungumeni aisaiki wuce mutafi ,arazane tadago kanta idanta tab da hawaye ya kashemata ido itakuwa tuni wani kuka yaballemata sosai tayikuka mai isarta sannan tawuce zuwa mota ,tabbas shima kansa baijin dadin abindaya mataba kumajiyayi yanajin kukannata har zuciyarsa itada shine a gaba saikuma Abdallah da tsohuwa abaya harzasu wuce tawani katan shop Abdallah yace Anty dan Allah kitsaya zanyi siyayya ranta abace yake danko annuri babukan fuskarta tadago yace Abdallah nidai bazan iyashigaba amma idan kaizakaiyashiga saikaje kayisauri tasani tabbas sai Muhmd yarakashi shiyasa tayihakan ,Muhmd ne yace Abdallah nidai bari inrakaka Fatima tajuyo takalli kaka mezaasiyomaki bakomi dan Allah kifada zanfada amma saikintashi kunje tare ,yauwa kaka gayamatadai karfahimanta acikin wani hadisi dakikaimin ( manzan Allah s.a.w. yace lesal shadidu bissuraati garinkayi bashine sadaukiba immashshadidu hakika shisadauki lamyamliku nafsahu indal gadabi sadauki shine Wanda yake mallakar kansa yayin fushi )haderaitayi naji kumanasan dahaka ,amma dan Allah Muhmd yafadashima to Abdallah amma dasharadi daya indai zanfito mutafi saiya bude fuskarsa sbd bazantafi da mutum hakaba kamar munafiki murmushi yaya yawarware sannan yace to kifito mutafi, fitowa tayi raibace sukanufi cikin shop din harsunfara tafita kowa da indayake kalla Abdallah yatsayakam tare da danyi kara duk kansusuka juyo afirgice suna kallanshi ataresuka karasa tare da rikishi atare suka hadabaki sukace Abdallah lpy kuwa kukayafarayi dan Allah Abdallah kagayamana mekedamunka ,saida yatabbatar ya Fatima tajuya sannan yakashewa Muhmd ido daya, bakuneba memakon kutafi ajere saikudinga tafiya a haka yadda zaagane kowa basanzuwayakeba ,Fatima ceta dagakai tace wannan shine maganar eh ,to indai wannan ne bamatsala mutafi cewar Muhmd ,aikuwa tare sukajera har shop din aikuwa bakaramin kallo mutane sukemasuba harsuka karasa ciki tafiya sukeyi atare Abdallah shine agaba yanata zabar kaya gurin turaruka suka karasa dayake wajen babbane sosai tafiya sukeyi atare harsuka karasa daidai kanwani turare atare sukadaura hannunsu kanturaren sai duk Kansu suka tsaya sunakallanjuna Muhmd ne yakalleta tayi kasa da kanta shikuwa yakara zuwa daf daita daidai kunnanta yazu wato dazun kinramako cikin shakwaba tace badole naramaba to nikike turuwa baki aa kaina nakeduruwa , baibata amsaba yaji ance barkadai Masoyi nandanan ya maida fuskarsa yadda take yacigaba da tafiya mamaki abunyabata aikuwa tace wai yaya badakai akeba banza yayimata yamaja Abdallah sukabar wajen itamatatakemai baya binsu tacigaba dayi tanacewa masoyi dan Allah katsaya gabadayaran Muhmd yagama baci kayan dabasusiyaba kenan sukafita sunafita harsunkusa karsawa mota tadaga baki tace masoyi cikin tsokana tare da sadariya . Kubiyuni dai nagodeiyuni dai nagodedan•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *SANADIN YAR ALARAMMA* *Written by* *FATiMA ALARAMMA(F. M. Y)* *Bismillahir rahamanurrahim* *littafin abin dariya kuma abin tausayi hadida mamaki dakuma soyayya* *Sadaukarwa ga mahaifina da mahifiyata dakuma Anty tagari kuma abin alfaharina Allah ya sakamunsu cikin aljanna* *Tukwaicine ga sadiq Abubakar* *pg* 13 & 14* Shigewa motar yayi yabarta awajen itakuma budurwar takame tana kallan ikon Allah maida tayi dariyarta mai isarta sannan tamike takoma tayo siyaryarta sananan tafito kaitsaye motar tanufa,shikuwa Muhmd tsohuwa ce taketanbayarshi lapiya amma yayi mata banza to ina kuka barmin hajjiyan nanma suka karayimata shiru jinhakannema yasa itamatayi shiru saiga Fatima tafito tasa kayan abaya sanan tashiga tamikawa kaka tata ledar tace kaka wllh inacikin farinciki sosai gaskiya gara danaje dashikenan anyibani,hajjiya mene yasaki farinciki ,kaka mekikace hajjiya kuma nifa sunana Fatima Zara ba hajjiyaba dan Allah kidena fada aisaikibani kunya dan Allah kikirani da Fatima ko Zara to aisunan mamanane to shikenan saikice mamana yadda dad kefada ,kaka kinsanmene kunyifa sirika wani banzan kallo Muhmd yawatsa mata,kaka dama shinenaga muhmdu yana wanicin magani shimakuma dan uwannasa natayashi ya wllh nabatama address dimu,mamana ita yarinyarce zatazo eh kaka cab gaskiya bayar mutumci bace bamasonta kai kaka,Muhmd yauwa tsohuwa shiyasa nakejidake sosai gaskiya kam cewar Abdallah kinafa jidani tsohuwa Muhmd yafada cikin dariya kaka to aiyakisaurarantane shiyasa itakuma tacezatazo keda zakisabaki zakuma kice aa mamana nifa nayiwa Muhmdu mata,kaka aikuwa zaiwatsamaki kasaa ido, Muhmd gayamata kaka kuma nima inasanta sosai ai gaskiya kaka kin iyazabe dan nur haskece agareni danmadai rigimarta tayiyawa,wani kallo Muhmd yawatsawa Fatima dan yaga yazatayi,itakuwa tundataji haka tamaida hankalinta kantukinta sannan kuma tahaderai kamar baitacetake dariya dazunba dan yakara tabbatar da hakan yace kaka sbd sandanakeyiwa nur zansai waya sbd ita yafada yanakallan fuskarta ,itakuwa karanto addua takeyi danjin zuciyarta takeyi kamar zatafito ahaka dai harsuka karasa gida tayi farking sukafitu sukashiga gidan a falo tazauna yayinda akashigo da kayan. dan mintina tayi sannan tace kaka zaasamumaki mai aiki wadda zata dingataimakamaki aa mamana nifa abarzancannan baniso amma bari inje intanbayi Muhmdu injimaizaice to shikenan tashitayi danzuwa tanbayarshi yanazaune kangado shida Abdallah hirasukeyi sosai, kaka tayi sallama suka amsa yauwa Muhmdu dama mamanace tace wai zatadauko mai aiki wadda zatadinga tayani aiki nikuma nace mata aa tabarshi dan banason abinda bakaso ,lallai abarzancannan dannibanaso to shikenan zankara gayamata . Abdallah Yaya kasan Anty itama bawanisan yan aiki takeyiba dan wataran babu abinda sukeyi saidai suyi barci saikuma makaranta to amma meyasa akabarsu agidan sbd tanaso suyi ilimi idan akamaidasu gida aure zaamasu shine kawai gaskiya Abdallah Anty akwai taimako umm ammafa,saikuma yayishiru ammafa me bakomi Yaya kasan dai bamahaka dakai dan Allah kagayan gaskiya kasan mene bataso arayuwarta aa batasan mutum mekarya ko cin amana indaitasamu mutum da wannan to dagaranar sunrabu,sannan batasan raine ,Abdallah wannan daidaine hakan yayi banga laifintaba Yaya wai inawayarka umm Abdallah ainibanida waya hakanake rayuwata to amma yaushe zakasiya zansiyane ,daga dayan bangaren sukaji anakiran Abdallah Yaya bye bye zamutafi aa kabari sai anjima sai inrakaka koka kwana,anan to amma bari ingayamata inajiranka . Muhmd ne yatashi yakasara gaban mirundake gabansa yace inasanki nur ina kaunarki sannan yayi murmushi ,Abdallah Anty gani Abdallah gida zamutafi ,Anty kibari Yaya zairakoni kinji to karatunnakafa yayannezaima Yaya zaimin katabbata eh to shikenan tamikamai wata jaka guda biyu tace wannan takace dayankuma ta abokinka gakuma takaka ninatafi to shikenan bye karkadai dare to Anty kaka nabarku lapiya Allah dai yasaka makida alkairi mamana ameen kaka,Allah yabamu alkairi. Shikuwa Abdallah dakin yayan yashiga yamikamai ledar yace gashi inji,Anty ,karbayayi yafarabudewa cak yatsaya yana kallanshi Abdallah yaakayi tasan inasan wadannan abubuwan, kagani Yaya naga komidanakeso shine acikinnan,to mugakayan yakallesu harda turarenda yadaga yanaso saigashi,aciki saikuma chocolate saikuma lemuka marasa gas, sosai yajidadin kayan Allah sarki "nur" I love u yafurta tareda mirmushi Abdallah kallanshi yakeyi,amma wace nur? Abdallah nur itace rayuwata kuma farincikina inasanta sosai ita alkairice a gareni,tunda yafara maganar Abdallah yahade rai sosai, saida yaya yagama sannan Abdallah yace Yaya kakaini gida banajin dadi yanzun,sannu Abdallah na kabari sai gobe aa Yaya kawai karakani gida to shikenan Allah yabaka lapiya, sukafita atare kayimata godiya sosai to kawai yajuyo hargida yarakashi sannan yashiga, shikuma yajuyo gida jikiba kwari sbd yafahimci Abdallah baijidadiba tabbas gobe zaigayamai gaskiya sbd bayasan alakarsa da Abdallah talalace wannan shine daidai haka yashiga gida jikiba kwari. Abdallah yashiga gida jikiba a sanyaye dad da Fatima nekawai a falon sunakaratu,bayan yagaidasu yazauna,Anty suna godiya,tafahimci yadda yanayin kaninnata yake shiyasa Abdallah yaakayine naganka'ahaka kobakada lapiyane,aa Anty banajin dadine abarima inje inkwanta dan nagaji sosai to Abdallah Allah yabaka lapiya ameen kawai yace yashige dakisa Ahmed ne yace yau gaskiya akwai abindayake damun Abdallah duk sanshi da karatu yaubazayiba to Allah yayayemai abindakedamunshi saida suka kammala komi sannan kowayatashi yayinashi dakin . Fatima kai tsaye dakinta tayi ,kayan barcitasa sannan takwanta taredayin addu,oi, abin da yafarun dazunne yashiga dawomata zuciya da gaske " farisi" nada wadda yakeso? anyakuwa hakane amma aidabahaka bane dakaka batace ba kai innalillahi,wainnailaihirrajunun Allah gani gareka kokadan takasa barci zuciyarta namata zafi amma tainazari taganetanasan shirts amma tabbas tanasan "farisi" tayadda dahakan,dahakadai barci yadauketa. Abangarensa shima dai abinda yafarun kenan amma shibabban tashin hankalisa shine yadda Abdallah yacanzamai lokaci daya Abdallah shine mutum nabiyu wanda bayasan wani abuyashiga tsakaninshi dashi,yanasan Abdallah kamar yadda yakesan nur,tabbas zanyiwani abu akanhaka gashi yanzun banazuwa kasuwa,gashi dad yakirashi da maganar zaibashi aiki yabashi zabi akan company Fatima yakeso kona dad yacena dad yakeso . Yau zalaihat ce dakawarta Hauwa sunshirya zasuje gidansu Muhmd dakayan alheri,damatasan komi takuma San,inda sukakoma,tacikwalliya sosai tayikyau sukadau hanya zuwa gidan tafiya tayisiyayya sosai Dan takashekudi wai yadda zatasiyashi bakuwa tasan tamakaruba, harbakin kofar gidan tayi farking sannan tasaka yara suka shigadakayan . Tsohuwa tana zaunetanakallan ikon Allah wai mamana batada hankaline duk uban kayan dake gidannan amma tadingakaruwasu saikace bakudi takesawa tasiyaba baritazu zanmatafada tanazaune taji anyi sallama taamsa sannunkudazuwa yauwa kushigo amma ina Maman tawa ,aa kaka mukadaine mukazu ok to mushiga,sukashiga takawomasu ruwa da juice maisanyi bayan suntaba tace amma banganekuma ko kawayen mamanane aa kaka amma tuwane yaaiko wannankayan gaskiya inagakunyi badaidaiba bananne gidanba, aa kaka ceyar hauwa kaka wannan dakikegani itace budurwar Muhmd wadda yakeso !!! Eyee,eh kaka wannan kayan itace taaikomaku dashi,aikaka sundade da Muhmd,kaddai itace wadda yakecewa nur amma dayagama batamata rai,itadatakesa,ace ya auri mamana gaskiya yasakebatu Dan wannan lamarin baiyimataba yar kirkice za,ace tazugidansaurayi gaskiya dasake, shiru dakin yayi babuwanda yakecewakowakomi kuma kowada abinda yakesakawa ,kaka kuwababu walwala akan fuskarta,kaka tace amma yasan dazuwanku aa wllh dama sonakeyi inyimai surprise ne tonda bansamuzuwa dubashi a hospital ba,to shikenan aisaiku zaunakujirashi tatashi tabarsu awajen,saida tafita sannan hauwa tacewa zulaihat wannan itace zatabamu matsala dagagani akwai wani Abu azuciyarta,zulaihat tace eh wannan hakayake amma mubatawani Abu muganiko zatakarba aikuwadatadawo tazauna hauwa tace kaka gawannan aa wllh kibarshi dan bazankarbaba nagode iyayin hauwa amma kaka taki karba kudin,hakasuka hakura. Muhmd da Abdallah taresukafita kasuwar waya sukayiyo taredayin Sim sannan sukatahu,haryanzun Abdallah baisakijikinsa da Muhmd ba,Abdallah na,am Yaya inason zamuyi magana kafahimceni to Yaya Abdallah na,am inason " nur" baninadorawa kaina Santaba Allah neyadauramin Abdallah karkaga laifina tabbas " nur" haskecigareni Abdallah duk sandanakewa " nur" batasaniba kuma batasona,kuma bazantaba yimata doleba,to Yaya Abdallah yafada amma Yaya niwallh banasan maganar " nur" dinnan wllh gabadaya batayiminba arayuwata ko sunanma sainajinatsaneshi, Abdallah nasan bakasan wace " nur" ba dabazaka fadihakaba,Abdallah nakasance inasan mace karamar yarinya wadda bazata wuce 17 ko 18 ba kuma burina nabiyu na auri maidaddini na uku maitsabta nahudu maisan jamaa nabiyar inasan maisuna Fatima kumaduk Allah yahadawa " nur" Abdallah

Chapter 6 of 12