Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
cikin likafanin sa, suka sallace shi, aka wuce da shi makabarta. Naseer bai iya zuwa ba, saboda ba zai iya jurewa ba, yana kallo a cusa masa Ameer cikin rami. Yana zaune kai cikin guiwa a falon Abba, ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Ji yayi an dafa kansa, ya dago a natse, yadda ya bi wanda ya dafa shi. Alh.Basheer ne a gabansa, yayi mamakin da bai ji sallamar su ba. Ya mike yana masa sannu da zuwa, ya amsa, ya ci gaba da fadin." "Zauna ka ji?" Suka zauna tare, ya gaishe shi. Bayan yayi masa gaisuwa, ya ce, "Umman ku ta ce an je kai shi ko? Ya ce,"Sun tafi tun dazu." Ya ce,"Allah ya kara mana hakurin rashin sa. Tare muke da Ummin Nusaiba, tana can sasan wajen Umma." Ya ce,"Bari in je mu gaisa." Ya mike ya fice. Alhj na masa kallon tausayi. "Yan mintoci kadan ya dawo, ya sake zama. Bai iya cewa k'ala ba, har zuwa wani lokaci, kafin Alhj ya katse shirun,"Naseer! Ya dan dube shi ya amsa. Ya ce,"Don Allah ka daina yawan tunani, komai ya sami bawa da izinin Allah. Ba kai kadai ba ne, Ubangiji na jarabtar bayin sa da masifu iri daban-daban. Amma idan bawa yai hakuri, ya jure komai wucewa yake yi, tamkar bai ta6a faruwa ba. Abinda na ke son ka da shi shine. Ka k'ara yawaita sadaka da addu'a, domin ita sadaka tana yaye masifa da damuwa. Sai kuma hamdala ga Allah. Ko wane yanayi ka tsinci kan ka, to ka gode wa Allah. Ubangiji na wadata mai yawan yi masa godiya. Ba wadatar kudi kawai na ke nufi ba, har da wadatar zucci. Ka sani idan zuciya ta wadatu da imani, duk abinda zai zi wa bawa, zai kasance mai mika wuya ga Allah. Kar ka damu, ka ji? Ya sauke numfashi ya gyada kai, ya ce,"Na gode." Sun jima. Alhj Basheer na yi masa nasihohi kafin su Malam Balarabe da sauran jama'a suka dawo daga makabarta. Nan ya bar su ya fita,Suka yi sallama da jama'a, yayi masu godiya kowa ya kama gaban sa. Aka bar su su 2 da Sageer. A hakikanin gaskiya Alh.Basheer na son Naseer, shi yasa duk ya damu da irin halin damuwar da ya shiga, tunda yayi aure. Yau wannan, gobe wancan. Shi kuma Naseer na masa kallon duk matsatsin daya shiga. Alhj ne sila, don haka babu wani dadin bakin da zai masa. Ya fadi, kunni yaji, amma aiki da shi ba zai ta6a zama dole ba. Naseer kenan. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Wata 2 da rashin Ameer. Bikin Sageer da Fa'iza ya rage saura sati 2, ka na Kausar tsakanin su sati 1. Watau na sati 3 ya rage. Angwaye da amare na ta fafutikar shirye-shiryen biki, ita kuwa Nusaiba wani abu ke daure mata kai, mai kama da al'amara. Al'adar ta d'if, ta dauke wata 2 kenan. Ana neman a shiga na uku. Ga wani ciwon kan safe da take fama da shi, yawan kasala da taruwar miyau a bakin ta. Bata gane kan gadon ta ba, ko alama sai dai bata fidda shakkun ciki take dauke da shi. Ta runtse idonta tamau? Ta dauki salatin Manzo ta yi wa Allah tasbihi mai yin yadda ya so." Watau rabon Da, ya kawo ni cikin gidan nan kenan? Ta dan yi murmushi, domin take nan ta tsinci soyayar abinda ke cikin ta.Tana so ta nuna wa Antin ta alamomin da za ta gane, amma tana jin tsorin kar Naseer ya sani. Watakila ba zai so haihuwa da ita ba, tunda baya sonta. Kar ya munafunce ta da wani abin, ya zubar da cikin. Saboda haka ta ci gaba da 6oye yanayin ta, babu wanda ya fahimce ta, illa tsiyar k'iba da Antin na ta kullum take yi mata. A haka suka sha bikin Sageer. Amarya ta tare kusa da gidan su Sageer din, ya kama hayar gida karami dakuna 2, kicin da bayi. Sageer ya kama angwanci, babu kama hannun Yaro. Sati da ya zagayo tun ranar alhamis Nusaiba na Kaduna, ko dama duk ta kosa ta sami 'yar damar da za ta gida, ta dan kwana 2. Tana like jikin Umminta, dadi ya ishe ta, ga madarar Holandia mai sanyi take ta faman sha, tun isowar ta. Haka Ummi ke cikin farin ciki ganin yadda Nusaiba tayi k'iba, ta k'ara haske sosai. Tana ta kallon ta, tare da lura da yanayin ta, ita kuwa Nusaiba ta k'i yarda wani abu yanke a bakin ta, kar miyau ya taru, kamar dai yadda take yi a gida Zariya. Bikin Kausar yayi armashi kwarai da gaske, angonta Injiniya Abdul-Malik yayi bajinta. Haifaffen Unguwar Sarki, amma yana aiki da hukumar gida da ke Lagos.Ta tare a makeken gidan sa da ke (Abuja Road) kafin lokacin da za su d'aga Lagos. Ranar asabar Zarah ta zo, kuma ta so kwana. Kiri-kiri Naseer ya hana, ya kasa, ya tsaye da yamma dole ta biyo shi, ya dawo da ita. Nusaiba kuwa sai da ta kai litinin. Alh.Basheer yayi ta ciwon baki, yana wa Ummi fada yana ganin kamar da hadin bakin ta Nusaiba ta kai Mondy. Karfe 4 kayanta an gama kintsa su a mota. Direba zai maida ta. Tayi tsaye tsakar falo tana kallon iyayen ta, kamar kar ta tafi. Hawaye ya gangaro kafadarta,"Kuka za ki yi shagwa6a66iya? Ta tsura masa ido, hawayen suka zubo shar-shar! Yasa hannu ya goge su, ya sake cewa,"Menene abin kuka? Kin ga kama hanya ku tafi. Allah ya kiyaye hanya. Ki kula da kanki da kyau. Kin ji? Ga katon 4 nan na Holandia, na ce a sa miki a but." Umminki ta ce,"Yanzu shan ta ki ke yi sosai ko? Ta dan sadda kai kasa. Yayi murmushi, ya dago ha6arta,"Haka Umminki ga gaya min, ga ta dai a tsaye, ko ba ke ki ka gaya min ba? Ta wuce shi da gudu ta koma gun Ummi, rungume ta. Ya ce,"Ummita, sai mun yi waya." Kafin ta ce wani abu, ta bar wajen da gudu, ta fita. Me za su yi, ba dariya ba, kamar almara ta ga Naseer na fakin a harabar aje motici. Ta ja tsaya, tana kallon sa. Mamaki ya ishe ta. Daga bayan ta, ta ji muryar Abbanta na fadin , "Ah , ga ma mijinta nan ya zo." Ya zo ya wuce ta, ya nufi wajen Naseer da ke fitowa daga mota. Da sauri ya tsugunna. Alhj ya mika masa hannu tare da sallama. Ya mika na sa yana amsawa. Sannan suka gaisa, kafin Alhj ya ce,"Ashe za ka sami zuwa? Ai tun jiya na tambaye ta, ta ce min ka na da.(Exams), ba za ka zo ba." Kan sa tsaye ya ce,"Mun fito da wuri, shi ne na ce bari in zo kawai in dauke ta." "Yayi kyau. Dama fitowar na ta kenan zu su tafi. Bari direba ya kwashe kayan, ya mayar but din ka." Ya bude but din. Direba na juye kaya, shi kuma ya shige cikin gidan, don gaisawa da Ummi. Ko dama Nusaiba tuni ta koma ciki, kan ta daure, tana tambayar kan ta." Wai ashe maza ma sun iya kisisina? Kurame sak! Suka zama cikin mota, yadda ya like kunnensa da Ear piece haka ta manne na ta da sauraren tafisr din Marigayi Sheik Jafar Mahmud Adam Kano. (Allah yajikan Mallam Ja'afar na Gadon kaya me Ahlussuna, tare da iyayenmu baki daya Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6