Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
aka sauke su, amma ya ce babu komai, kawai jikin sa ne bai masa dadi. Sannan yana jin kamar baya sha'awar yin wasan. Yakubu yayi ta kwantar masa da hankali, yana kara koda shi tare da nuna masa nan fa garin bayinsu suka zo. ***hhh wai bayinku,hada rai,dan karamin tsaki,,mttssswww.. Maji magani**** Ya zama dole ya zage damtse ya ba mara da kunya, su nuna masu sun zo garin su, sun fi su rawa.Ya ji ya amince da shawarwarin Yakubu, amma ba su cire masa damuwar sa ba. Karfe 2 saura 'yan mintoci, gasa ta kankama. Naseer dai ya hau doki ne. Alh. Basheer na ta yi masa addu'ar samun Nasara. Yakubu ya bubbugi kafadar sa ya ce,"Ja mu je, dan gidan Alhj, ba wani bayan kai! Ya zaburi doki, ya fada sahu. Duk dawakai sun jeru izini. Kawai suke jira su tashi jimawa kadan aka ba su izinin tafiya. In ba ka yi, ba ni wuri. Naseer fa ya cilla, sai dai tafe yake yana tunanin zuci. Babu abinda ya fi masa yawo a rai, sai zancan Zarah muryar ta yake ji tana fad'in **"Ni kuwa yayana gani na ke duk zance ka ke yi. A hankali za ka so ta!** Yana tafe, yana girgiza kai da karfi, don bai son jin muryar. Kamar ma karuwa ta rika yi. Shine akan gaba,"Jama'a na ta hargowa, muryoyin su suka yamute masa tare da ta Zarah. Kiris ya rage ya iso karshe, bai san lkcn daya saki linzami ba, ya kame kan sa, yana layi tare da kiran "Inna- lillahi"Wa-Inna-ilahir-raji'un! Duk su Alhj suka kame kaf, suna hangen sarautar Allah. Ko kafin su gama mamakin meke shirin faruwa? Naseer suka hango yana mulmulowa kasa. Alh. Basheer ya keto fili a guje, dukkan yaran sa suka rufo masa baya, yayin da tuni 'yan taimakon gaggawa suka kai wa Naseer dauki. Ya ji ciwo sosai, in ban da jini, babu abinda ke fita ta hanci ta baki. Kowa ya rude musamman Alh. Basheer da Yakubu. Nan take motar asibitin ta dauke shi zuwa asibitin Murtala, inda ya sami taimakon Likita. Bayan an gama bincikarsa babu karaya, inda ya ji raunuka, an daure su da magani, sai Alhj ya dauko shi zuwa gida. Ba su tsaya Zariya ba, kai tsaye Kaduna ya wuce da shi asibitin Likitansa, yasa aka ware masa daki na musamman shi kadai. Daga bisani ne suka sanarwa duk wad'anda suka dace su sani, musamman su Abba. Kan ka ce kwa6o? Asibitin ya cika da iyaye da masoyan Naseer, duk da dare ya fara yi. Anan Zaran da Nusaiba suka fara haduwa ko da ganin junan su, babu gabatarwa, take nan suka shaida junan su. Nusaiba ta rike hannunta, ta nuna ta ga su Alhaji. Ta gaida su cikin ladabi da girmamawa, su ma suka amsa cikin fara'a, tare da nuna kauna gare ta. Shi kuwa Naseer barci kawai yake yu, bai ma san wad'anda suka zo ba. A daran nan suka sake biyo hanya, suka dawo Zariya, aka bar Abba tare da shi. Zarah da Nusaiba kan ba su runtsa ba, saboda tunanin yanayin da suka baro Naseer. Duk da cewa Likita ya ce da saukin jikin amma abin akwai tausayi. Abu kamar hadarin mota, ko ina ciwo. Haka hankalin Alh.Basheer ke tashe, domin bai bar asibitin ba, sai 12 dare, suna tare da Malam Balarabe. A lokacin ne suke shawarar dole a rink'a yiwa Naseer addu'a, saboda yanayin bakin mutane. Don Yakubu ya gaya wa Alhjn labarin da Naseer din yake fadi, kafina fara wasar. Washegari haka su Umma suka dawo mota guda (Bus). Naseer na kwance baya ko iya tashi, saboda tsamin jiki. Komai da ake bukata, sun iske direba ya kawo daga gidan Alhj. Bayan kamar awa daya, motar ta juya da su Inna. Aka bar Umma da Zarah tare da Sageer. Su Biyun ma kadai ke tare da shi lkcn da Direba ya sake dawowa da Nusaiba da Umminta. Ummi na gama gaishe shi, suka sake fita tare suka bar Nusaiba tare da su. Kowacce na zaune, sun tasa shi gaba. Sageer ya dube su, yayi dan murmushi ya kada kai. Naseer ya dago ido, ya ce,"Lafiya? Ya ce,"Lau. Me aka yi? Ya amsa,"Gatan yayi maka yawa. Kamata yayi ka mike kawai, ka ce ka warke. Ko me ku ka ce tagwayen Jah-Jah? Lumshe ido yayi, ya kauda kai, yayin da Zarah ke fadin,"Gaskiya ne, amma don ragwanci ko motsi bai iya yi." Nusaiba ta ce,"Ina fatan ma dai ya ci abinci? Don na lura, baya son cin abinci." Ya bude ido, ya kwada mata harara, in ban da salo, yaushe ta san ban son cin abinci? Ya maida idon ya runtse, yana wani gajeran tsaki. Zarah ta cafe,"Babu 'yar tsaki anan yayana, ina jin Abba na gaya wa Umma ko dan Tea kadan ka sha. Ba tare daya bude idanuwan sa ba, yake fadin,"Ai sai ku yi min dure."Ta ce,"Yanzu kuwa, amarya hado min Tin ya gani, idan gatse yake yi." Ta kuwa mike ta hado shi. Yana kallon su. Sageer na ta dariya. Sageer dago mana shi." Inji Zarah. Ya dubi Sageer din, ya kara daure fuska,"Ta6a ni, ka ga yadda zan fasa ma baki." Ya ce,"A hakan? A hakan kuwa." Nusaiba ta ce,"A janye 'yar wasa, yakamata ka sha Tin nan. Daurewa za ka yu." Ya rufe ido,"Na koshi." Da anyi magana kuwa, sai ka rufe ido, zama da yunwa ai wani ciwon zai sa maka." In ji Zarah. Wani irin kallo yai mata, bai ce komai ba, ya maida idon ya sake rufe shi. Shiru bai kara tankawa kowa ba, har suka gaji da rarrashin sa ya sha Tea. Alhaji na shigowa Nusaiba ta labarta masa. Bakin gadon ya zauna ya ce Sageer ya kama shi ya tashi zaune. Da kyar ya iya zama, saboda ciwo ga takaici. Alh. Basheer yasa aka miko masa kofin Tin. Ya debo a cokali ya ce,"Ungo ka sha Naseer ciwo da yunwa mazaunin su daya, gaba daya suke mukurkushe mu2m." Malam Balarabe da Umma suna ta murmushi. 'Yar kunya ta kama shi, ya sunkuyar da kai." Kar6i mana, menene abin kunya, ni ba Abbanka bane? Ya miko hannu ya kar6i kofin." Zan sha Alhaji, kawo." Ya mika masa yana 'yar dariya. Kur6a yake a hankali. Alhj na rarrashin sa har ya shanye, a je kofin. ~~~~~~~~~~~~~~~ Sati 2 yayi a asibitin, shi kan sa idan zai fadi tsakani da Allah, ya san shi dan gata ne, kuma Alh.Basheer ba karamin so yake masa ba.Hatta Hajiyar su Yakubu, miyar kajin turawa tayo masa dakwale cikin kwano, ta kawo masa. A 'yan tsakanin nan shakuwa tsakanin Zarah da Nusiba tayi karfi sosai, sun fahimci juna kwarai da gaske. Kausar kanta, ta yaba da Zarah kuma tana mata kallon wacce za'a zauna lafiya da ita. Shi kuwa uban gayyar tamkar ya dauke kan sa ya maida gida yake ji, saboda ginsa da yayi da zaman Kaduna. Abu mafi ban haushi a gun sa, wanda yake k'ara sanya shi damuwa, shine gaba daya aka hade masa kai. A ganinsa kenan babu wanda zai kai wa kukansa, illah mutum daya, watau Naseer B. Shi yasa daya zo asibitin, ba shi da abokin hira, sai shi. Yayi ta yi ma sa famfo, yana k'ara cusa masa kiyayyar Nusaiba a rai. Koda aka sallame shi, haka a kodayaushe Alhj ke tafe masa da abubuwan alkhairi., sai da ya tabbatar da Naseer ga gyagije sosai. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Watannin 4 suka shude a cikin wannan hali, babu abinda ya sauya a zuciyar Naseer a game da auran Nusaiba. Yana zuwa wajen ta, don bin umurin kawai, haka ya kan kira waya, ya ce mata ya take? Sai dai idan ta turo masa (Text) da ingatattun kalamai, shi sai ya tura na shi babu komai ciki (Blank) Ga musun tsiya, idan za ta shekara gardama, ba zai ta6a sakar mata, dole ne ta yarda, ya turo sako, wayar ta ce mai matsala. Saboda haka ne ta daina ba ma kanta wahalar aika sako. Sai dai abin yana bata mamaki yana kuma sanya ta a tunani. Me yasa sauran sakwannin ke shigowa dai-dai, amma ban da na shi?Musamman sakwanin gaisuwar Ibrahim da take yawan samu. Kodayaushe baya gajiya wajen aiko mata da (Text) din gaisuwa da addu'o'i, wani lokacin har da kalaman so da kauna masu neman dagula lissafin ta. Haka nan take dauke kai, ta fuskanci zabin Abban ta, koda sau daya, za ta ga murmushi sa a sati. Wannan ta aje shi a kila haka halittar sa take, miskilanci. Kuma haka kawai, ta ji miskilancin yayi mata dai-dai, domin ita kanta bata cika son namiji mai yawan dariyar tsiya ba. Karshen watan nan su Zarah suka kammala jarrabawrsu ta karshe. Ko dama ita kadai ake jira. Nan da nan shirye-shiryen biki ya kankama musamman a Kaduna gidan Alh. Basheer. Ba k'aramin gagarumin biki aka shirya ba. Gidan daya ba su, tuni aka gama gyare-gyaran cikinsa, aka fent shi ciki da waje. Sannan yasa aka zuba tsaddadun abubuwan bukata na gani na fada har sashin Zarah. Duk da haka Naseer ya kashe wa Zarah makudan kudade wajen siya mata kayan daki, musamman kayan kicin, kuma kullum gaya mata yake yi ta rage shishshigewa Nusaiba, don kar ta raina mata ajinta. Ko alama Zarah bata son irun wadannan kalamai na sa, a kodayaushe, tana nuna masa ita da zuciya daya take kaunar Nusaiba. Biki saura kwana 7, Alh. Basheer ya kira Naseer, abinda ya gani ya daure masa kai, wasu kaya setin akwatuna ne guda 2, gaba daya shakare da kaya. Ummi ta bubbude masa daya bayan daya,kafin Alhj ya ce. Wad'annan akwatuna seti daya Zarah ne, daya kuma na Nusaiba ne. Kamar yadda yake a al'ada, kowace amarya ana kai mata. Wannan tsakani na da kai ne ko Umminku na gargade ta, ban ce ta gaya wa kowa ni ne na yi su ba, kai ne ka kawo wa Nusaiba. Wancan setin kuma ka kai wa Zarah. Shiru Naseer yayi, ya rasa ta cewa, domin zuciyarsa cunkushe take fa mmkn Alhj. Watau ya dai dage sai ya siye shi da karfin Naira. Kudi shegu ne. Ya karkada kai,"To ni me zance yanzu? Idanuwansa suka cika fal da hawaye. Irin wannan hidima ko kallon banza na yi wa Nusaiba, idan Abba ya sani, ai na kade, sai ganye na." Bai san kwalla ya zubo masa ba, sai da ya ji Alhaji ya dafa shi, yana fadin. "Haba Naseer, menene haka? Kai ba Da na bane? Kullum ina gaya maka hakan, amma kamar har yanzu ba ka yarda da ni ba. Look! Ka na ji na? Nusaiba kawai gare ni, sai Allah ya k'ara min da kai, na kuma gode masa. To kai ma ka gode masa domin kyautar daga gare shi take. Share hawayen nan don Allah."Ya kai hannu ya goge kuncin sa, yayin da Ummi ke fadin,"Namiji ai jarumi aka san shi, kar ka ba matan ka kunya mana." Ya kara sunkuyar da kai Alhj na dariya., Mai-gadi ya loda masa akwatunan a bout, shi kuwa yana zaune, yana zuba godiyar karfin hal. Nusaiba bata nan? Sun shiga gari da Kausar shirye-shiryen biki." Saboda haka ba 6ata lokaci, ya damko hanya, ya dawo cike da aljabi tare da wasi-wasi wai kauna ce ta sa Alhj ke masa hidima? Shi kam bai yarda ba, saboda 'yar sa da yake son lik'a masa ne kawai. ****Kai jama'a nifa Naseer dinnan yafara bani haushi**** Ga Abba tare da Umma, sun baje akwatuna ba sa aikin komai, face sa albarka. Umma har kwallanta sharaf-sharaf. Bayan sun natsa. Naseer ya ce dole a kaiwa Zarah gaba daya kayan, watau da nasa setin akwatunan da yai ma ta., Abba ya ce hakan bai zama adalci ba, zai fi kyau ya aje su, bayan sun tare gidansa, ya raba masu kowacce ta kwashe kason ta. Umma ma ta goya wa Abba baya. Akan dole Naseer ya karbi wannan shawarar. A yammacin ranar. "Yan-uwa da abokan arziki suka kai kaya gidan su Zarah. Hakika iyaye da 'yan uwan Zarah sun ga abin mamaki, domin sun ga kaya iya ganin su. Su kuwa Abba da Umma a kodayaushe a cikin dogiya da shi wa Alh. Basheer albarka suke har zuwa ranar daurin aure, yayin da hidimomi da dama na shagalin biki akai tayi a Kaduna da Zariya. Nusaiba tana zuwa na Zarah. Ita ma Zarar ta halarci walima da (Mother's day) a Kaduna. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Ranar asabar da safe karfe 11, aka daura auran Naseer da Zarah. Karfe 2 dai-dai ita ma Nusaiba ta tabbata mata Naseer, tun daga lokacin duk wani farin ciki da ke zuciyar ango ya rufe kofar sa. Wani irin yanayi daya rinka yi a wajen, shi ya tabbatar wa Sageer lallai abokin sa na cikin wani yanayi na daban, don haka ya ja shi gefe, ya kare masa kallo, gaba daya idanuwansa jajur! Suke. Ya sanyaya murya ya ce,"Ka ga yadda ka dawo kuwa Naseer? Bai kamata ka rikide haka ba a wajen nan, don ba haka aka san ango ba." Ya sauke numfashi, a yamute ya ce,"Ban son yarinyar nan Sageer, ka na zaton wasa na ke yi? Mts! Yayi dan gajeran tsaki, ya kauda kai, "Rayuwa ta vata damu kowa ba, sai shahalinku ku ke yi, ni kadai na san abinda ke damu na. Ka je ku ci gaba da hidimomin ku. Ka kyale ni kawai." Jikin Sageer yayi sanyi, tausayi ya kama shi, ya kamo hannu Naseer ya ce, "A hankali za ka so ta mutumi na. Please ka jure, ka zama namiji, kar ka mance kuma har da Zarah yau ta ka ce, halas-malak. Yakamata ka gode Allah, domin yayi maka kyautar da ba kowa ke samu ba. Mata 2 a lokaci guda ko a zamanin da, sai dan gata. Illar kawai da ba ka son Nusaiba. Amma ina gaya ma za ka so ta, saboda yarinyar bata da wata mishkila." Ya dauke numfashi." Sageer ba zai gane ba, menene amfanin maimaita magana 1? Ya fada a ran sa. Ya daga ido zai ce wani abu. Kausar ya hango tana dube-dube, da gani, su take nema, don haka ya ce,"Ha sarkin kaudin can zuwa, da alama mu take nema." Sageer ya juya, ko kafin su fito fili ma, ta hango su. Wajen ta nufo,"Haba ango kuma sai ka 6oye, ina ta billayin nema? Ya ce,"Magana muke." Ta ce,"Ummi ce ta ce in tambayi motoci nawa ku ka zo da su? Sageer ya bata amsa." Akwai kanana 10, ga kuma wata Bus can, sun isa ko a karo? Ta ce,"Bari na tambayo. Ta sake duban Naseer." Ango! Ango!! Ya dan murmusa, ya kauda kai, ta ce, "Har yau din ma murmushi kawai zan samu? Bakin ango ai baya rufuwa, balle kai mai Double. Zan so in ga Competition din. Ni zan ba ka abinci a baki, ni zan kai ka ka sha madara! Dole ta sanya shi dariya. Sageer kam har da kyalkyawa. Ta wuce da sauri, tana fadin " Ku jira ni, na tambayo, Naseer ya gintse dariyar, ya ce,"Wannan 'ya da tsanannan surutu take." Ya ce,"Ba ga shi ta sa ka dariya ba? Mts! Ni yanzu ma zan sa6e." Ka je ina? Ya ce, "Zariya zan koma." Wajen Zarah ko? Me za ta yi min? Ban da ta k'ara 6ata min rai? Ai duk bakin ku daya. Makullin Naseer B zan kar6a, in je dakin sa, in huta awa 2, kafin ku iso."Sageer yayi dariya, ya ce,"ANGO kenan, kai wane hutu ka ke nema a wannan yamutsin? To Allah ya kiyaye hanya, amma ka san duk taron nan, saboda kai aka yi shi ko? Hakkin ka ne ka ba kowa kulawar da ta dace." Ya ce,"Menene amfanin ka? "Ba wasa na ke yi ba, tafiya zan yi idan na ci gaba da zama wajen nan, jini na zai hau. In wannan kwakwazon ta dawo, ka san yadda za ka yi da ita. Sai kun taho. Kamar wasa, haka Sageer ya saki baki yana kallon Naseer ya amshi makullan Naseer B, ya wuce ya fada mota. Jama'a da maroka na bin sa, yana fadin yanzu zan dawo. Yana nan tsaye. Mamaki ya kusan kashe shi. Kausar ta dawo ta shaida masa moticin sun isa, idan ma da k'ari. Ummi ta ce ba matsala. Abba ya ware wasu masamman, don dibar jama'a. Naseer bai san lokacin da barcin takaici ya sa ce shi ba, bisa katifar Naseer B. Can a mafarki yake jin wayarsa na bugawa. Ya bude ido da kyau, duk jikin sa yayi tubus! Saboda tsabar gajiya, da gaske wayar ta sa ce ke bugawa. Ya lalubo ta, ya duba Sageer ne akan layi. Cikin muryar barci ya ce,"Ya aka yi? Ya ce,"Me kuwa aka yi? Dan rainin wayau. To mun iso muna fly-over yanzu. Idan ka ga dama, mu hadu a can ,"Yanzu da gaske kun dauko yarinyan nan." Haushi ya kama Sageer, ya rasa me zai ce? Sai yayi tsaki ya kashe wayar sa, ya ci gaba da tuki. Naseer ya dubi agogo karfe shida da kusan kwata. Ya mike da kyar, yayi mika, kansa kawai ya ji ya dauki ciwo, ba kadan ba. A haka ya fito ya kulle dakin ya shiga mota, ya nufi (Hanwa Low-cost). A hanya ya kira wayar Umma, ya shaida mata bakin sun iso. Nan da nan aka shirya kayayyakin abinci kala-kala. Bus guda tare da 'yan tar6ar baki suka tafi. Naseer na isowa. Jeep din Antin Jordan na fakin. Ta fito da yaranta, wajen ta ya nufa, ya dan rankwafa, yana mata sannu da zuwa. Bakinta har kunne, ta bubuga kafadar sa. "Angon Nusaiba. Angon Zarah. Ina ka shige, na yi neman duniya, ban gan ka ba? Ya shafi k'eya, ya ce,"Kira na aka yi nan Zariya, dole na dawo." Anti ta ce,"Haka wannan abokin na ka ya ce, "Dama an daura aure, ban ga ango ba, ko sau daya, shi yasa na tambaya. To Allah yasa albarka." Ya ce, "Amin." Ta wuce ciki, shi kuwa ya wuce wajen su Sageer. Yana wa Allah godiya da karyar sa ta zo dai-dai da wacce Sageer yayi. Karfe 9 saura kwata aka kawo Zarah, a lokacin bakin Kaduna duk sun juya, wadanda suka rage, ba su fi mu2m 10 ba. Antin Jordan da kan ta, ta jagorance su zuwa sashin Zarah. Bayan yan kawo amarya sun gama ba ido su abinci, motoci suka koma da su gida. Aka bar mu2m 3, suka taya ta kwana. Haka ma Zarah ba karamin mamaki ta sha ba da ganin dakin auranta. Ko a mafarki bata ta6a tunanin irn sa ba, saboda haka ta kwana yi wa Allah godiya tare da rokon sa zaman lafiya dauwamanme. Washegari safiyar lahadi, karfe 9 za'a gudanar da hawan Yakubu. Sukuwa ta musamman wacce Yakubu ya shirya. Filin sukuwa ya ci ka fal da Zaratan 'yan wasan tseren Polo daga ko'ina 'yan kallo kuwa babu masaka tsinke maza da mata. Alh.Basheer da tawagar sa ma suna wajen. Tsofaffin 'yan wasa irin su Yakubu da shi kan sa Yakibu su suka fara sharar fage, inda dokin Yakubu yayi wa saura fintinkau. Daga nan sukuwa ta ci gaba. Kowa na nuna bajintr sa, abin gwanin sha'awa, sai wanda ya gani. Karfe 11 dai-dai, rana ta soma zafi, wasa ya zo karshe, kamar yadda Yakubun ya shirya. Ango shine zai rufe fili, don nuna farin cikin sa ga dimbin masoyan sa da suka taru. Saboda haka Yakubu ya mike ya dau lasifika yayi wa ango kirari, ya kwarzanta shi, sannan yayi kiran sa, "NASEER, ta so ka ja mu je! Yana mike wa, duk wuri ya yamutse da hargowa da tafi, shi kuwa kansa ne ya ji yana sara ma sa. Domin duk lokacin da aka kira shi angon Nusaiba, ya kan ji jinin sa ya k'ara hauhawa. Ya tsaya gaban dokin da ya saba hawa, ya cire kuben da ke kan sa. Yakubu ya dora masa ta kwano. Ya taka ya haye doki. Ji ka ke tafi, ta ko'ina. Yayi karfin hali, ya daga hannayen sa sama, yayi gaisuwa ga kowa, sannan ya tsala wa doki bulala, yayi haniniya ya zura a guje. Naseer fa bai san abinda yake yi ba, gudun kawai yake yi kura na tashi., Rayuwar sa gaba daya cikin kunci take har ya kan kai ga lokuta da dama yana mancewa da tunaninsa. Abinda ya faru da shi kenan a halin yanzun. Ya sakarwa dokin sa linzami, ba san irin gudun da yaje yi ba. Ai kuwa ba a jima ba, kafafuwan dokin suka sarke, yayi haniniya, yayi sama, me jama'a za su gani? Ango ya watso k'asa warwars! Wuri yayi tsit!Na 'Yan dakikai, sannan gaba daya jama'a suka dauki salati, yayin da tuni jama'a da ke kusa da wajen, suka yanyame shi. A sume suka wace da shi asibiti. Ba 6ata lokaci aka kai shi (Emengency). Kowa ka duba, hankalinsa tashe yake, musamman da Likita ya ce yana da karaya 2, a hannun sa na dama. Alh.Basheer zufa kawai ke keto masa, fadi ya ce, "Inna-lillahi"Wa-Inna-ilaihir-raji'un! Ana cikin halin haka, su Malam Balarabe suka iso, ba'a jima ba Jeep din Antin Jordan ta aje su tare da amare. Kowacce ido warwaje, ta sha kuka. Ba su ma yi kuka ba, sai da suka ga angon su magashiyyan a kwance, bai san halin da yake ciki ba. Antin Jordan kuwa tunda ta iso ta tsinke da fada, kamar ta ari baki, wai me yasa za'a bar ango yayi sukuwa? Duk laifin na su Alhaji ne, haka take ta fad'a. Sam ta mance haka Allah ya kaddaro. Bai farfado ba, sai la'asar, ya sha mamakin ganin sa a gadon asibitin. Wani sabon bakin ciki ya sake turnike shi. Wannan wace irin masifa ce? Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 2-02 Posted by ANaM Dorayi on 11:41 PM, 11-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . .Gaba daya an gur6ata masa rayuwarsa? Take nan ya kara tsanar Nusaiba, ba wai a zuci ba ya kadai ba, har cikin jinin jikinsa yake jin bai sha'awar zama tare da ita...Lallai iska na wahalar da mai kayan kara, domin Alhj ba karamin hidima ya sha ba a asibitin nan da kudin mai dorin gargajiya. Angwanci dai ya dawo asibiti. Anan abokansa da suka zo daga nesa suka yi bankwana, suka koma zukatan su cike da tausayin Naseer. Baya magana da kowa, illah iyaka eh, ko a'a, ko kuma ayi masa sannu ya amsa. Hatta ita kan ta Zarah kallon ta kawai yake da ido, domin haka ya fiye masa kwanciyar hankali, kar a gane da ita kadai yake magana. Kwanansa 3 a Shika. Likita ya gama tabbatar wa Alh.Basheer babu wani rauni a jikin sa, sannan aka sallame shi. Aka dawo da shi gida. Haka suka wuni kar6ar baki, a cikin su harda su Lubabatu, Hauwa'u da Maryam, watau mutanen Zarah na makaranta. A daren wannan rana Zarah ta feso wanka, ta sa wani dan karamin dinkin atamfa riga da siket, ta fito ta leka sashin Nusaiba, ita ma wankan ta shiga, saboda haka ta wuce sashin Naseer. Bisa kafet ta same shi zaune, ya jingina da bango, idanuwansa rufe suke, sallamar da ta yi. Shi yasa ya bude idon, yana kallon ta har ta zo kusa da shi, ta zauna. "Yayana tashi ka yi? Ya ce,"Na gaji da kwanciya, jiki na duk yayi tsami."Ta dan dube shi, ta ce,"Sannu yanzu me za ka ci? Ya dan kada kai,"Ban jin yunwa." Suka yi dan shiru 'yan dakikai, ta dago ido ta dube shi. Ita shi ma yake kallo, don haka tayi dan murmushi, ta sauke na ta idon. Hannun sa ta ji ya riko na ta, jikin ta yai sanyi, ta kasa motsi." "Zarah!" Ya kira ta a wata siga mai taushi. Kunya kawai ta ji ya lullube ta, ta kasa duban sa. Ya kara kwantar da muryar ya ce,"Ki dube ni, na ce, ni ba angon ki bane? Ko don kin ganni a karye? Hannun ta daya, ta dan kare baki, tana murmushi. Ya kara runtse yatsunta ya ce,"Kin ga irin ta, ba don kun jawo min ba, ai da tuni na kauda wannan kunyar." Ya kara bata kunya, kamar ta tsere. Ya jawo ta, ta matso shi sosai, ya rungumo kafadarta ya ce, "Zarah kullm ina yiwa Allah godiya daya ba ni ke, saboda ke kadai na ke so a rayuwata. Sai dai yanayin da na ke ciki, ya zame min wani jarabci, wanda na ke ganin sai kin taya ni addu'a. Allah ya kawo min iyakar sa. Allah yana gani, kuma ya ga abinda ke zuciya ta, tamkar kan k'aya na ke cikin gidan nan. Saboda haka na ke neman hadin kan ki, ki taimaka min kullum ki kasance tare da ni, domin ke kadai ke yaye min bakin cikin da ke rai na."Ta sauke numfashi, cike da tausayi, ta dan dube shi ta ce,"Kullum ina tare da kai yayana, na sha gaya maka, ka daina damuwa. Ka kuma daina daukan wannan aure a wani matsayi na daban, face hadin Allah. Ba ka san abinda Ubangiji ya 6oye a cikin sa ba. Ba wai ba na kishin ka ba ne, ko alama ba haka bane. Ban ki in kasance ni da kai a gidanka ba, amma na yi imani da cewa, duk wanda zai yi jayayya da shinrin Ubangiji. Tabbas yana tare da wahala, ga kuma tarin zunubi. Domin daga nan ne mutum yake fadawa muguwar hanya, saboda bakin kishi. Na san ka na so na yayana, amma ka sa ni. Nusaiba ma amanar ka ce." Shi fa ba ya ma ko son ya ji an ambaci wannan sunan, sai ya ji kamar ya kurma ihu. Yayi ta maza saboda Zarah da ke kusa da shi. Ha6arta ya dago ta dube shi, yayi murmushi sosai, ya ce,"Na ji maganar ki, kuma zan yi iya kokari na. Abinda ba na so kawai a rink'a saurin kama ni da laifi.." Ta ce,"Kamar yaya? Ya kada kai, ya ce,"Wannan sirri na ne, ba zan fada ba, na samu ana kallo na, kunya ta sa a daina. Kinga na yi wa kai na." Ta sa hannu ta dan buge hannun sa da ke ha6ar ta, ta kauda fuska, tana 'yar dariya. Shi ma dariyar yake yi, ya sake juyo fuskar ta, ya jingina gashin sa jikin na ta, ya ce,"Kin min alkawari kullum ki na tare da ni, me yasa za ki kauda min fuska? Ta kwantar da ido k'asa, bata tanka ba." Kin sa tayi 'yan sumbatar kuncinta,"Da ke na ke magana." Ta ce,"Bari in kira amarya mu shirya yadda za mu rink'a girki." Ta yunk'ura za ta mik'e, ba tare da ta ji ta bakin sa ba. Hannun ta gam!Ya rike shi. Ta juyo dauke da murmushi ta ce, "Don Allaj bari in kira ta." Ya lumshe ido, yana girgiza kai,"Ban ce ba." Ta dade tana kokarin kwacewa, amma ta kasa. Motsin bude kofa suka ji. Tare da sallama, ta dage da karfi ta fizge hannun a lokaci guda, shi ma ya sake ta yayin da Nusaiba ta kawo kai. "Bata fahimci komai ba, domin Zarah a tsaye take. Shi kuwa dan gogan tuni ya dauke kai cike da haushin Nusaiba, ta katse masa hanzari." Ke za ni kira amarya, na lek'o dazu ki na wanka." "Ta

Chapter 2 of 6