Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
baro Hanwa, ba zan koma ba, Idan kuma ba kya son rayuwa ta, shi kenan, zan kai kaina a kashe." Nusaiba tayi wuf ta ce,"Umma, ku kyale mu mu zauna anan din. Ni na san Abba, ba zai ce komai ba. Kuma kula da kaya, ai ya fi ban cigiya. Tunda yana ganin nan zai fi mana sirri, sai mu zauna, ko Antina? Ta ce,"Gaskiya ne,Umma ku kyale shi kawai."Umma ta nisa kafin ta ce,"Ka ji Malam, yanzu wa zai kira Alhjn yayi masa bayani?" Ya ce ,"Shi mana. Ba shi ke da uzirin ba? Je ki dauko masa makullin sasan su, su gyara."Umma ta mike, ta wuce dakin barci. Malam Balarabe ya ci gaba da fadin,"Ka dauki waya yanzu-yanzu ka kira shi, ka gaya masa." Ya dauko wayar sa ya mika mai,"Ungo yi anmfa da tawa." Yasa hannun hagu ya amsa yana neman layin. Umma ta kawo makullan, ta mika wa Zarah. Ta kar6a suka fito tare da Umma. Tsarin ginin yayi matukar burge su, musamman Nusaiba. Ita kan ta, ta tabbata babu laifi Naseer ya kashe wa gidan kudi. Umma ta kawo tsintsiya da abin goge-goge, ruwa cikin bokiti da Omo. Nan da nan suka gyara wuri ko wacce ta za6i dakinta. Alh. Basheer kuwa abin dariya ma ya ba shi. Nan take ya yanke hukuncin ya ce duk su zauna har zuwa lokacin da hankalin su zai kwanta. Babbar mota yasa Sageer ya samo, su Zarah suka je suka kwaso iya kayayyakin da zasu iya debowa. Suna ta aikin gyaran Waje. Umma na taya su. Shi kuwa dan gogan yana kwance karkashin inuwa inda aka zuba masa shimfidar karamar (ChaniS Carfet) suna hira da Sageer. "Ai ni ban san cewa kai matsoraci bane, sai yau. Ashe gaba da gabanta. Aljani ya taka wuta. A taurin rai irn na ka, ban ta6a zaton akwai abinda zai hana ka sukuni ba." Yayi wata 'yar dariya, shi kadai ya san ma'anar ta, kafin ya ce,"Kowa ma hakan yake fadi, dazun nan Inna ta zo ta gama min tsiya. Amma ka san wani abu? Ina sane da abinda na ke yi. Kawai yarinyar nan na ke so na kure, a zato na za ta ce ba za ta biyo ni ba, ko iyayen ta. Ka ga na sami wata kafar taso da rigima. Sai kuma ta ba ni kunya mayyar." Wani zabgegen tagumi Sageer yayi, yana kallonsa, wani haushi ya kama shi, ya jima kafin ya ce,"Ni kai na da ni na aikata ba na ji kunyar. Yanzu kuma sai yaya? Ya ce,"Haushi ka ji? Idan ba na yi, ina nuna ni ma na isa ai raina ni za'a dama ta samu kuwa, dole in yi amfani da ita tun kafin yarinyar nan ta yi min gori waya rana. Ka san mata. Ni ban damu da shirgin ta ba, ta nemi ta raina min wayau." Sageer ya kada kai, ya ce,"Duk rashin soyayyan ta ya kawo wannan matsalar. Saboda haka magana ma 6ata baki, sai dai a kullum ba zan daina gaya ma ka, ka bi a hankali ba. Ni zan koma. Allah ya k'ara lafiya, ya kuma tsare na gaba." Ya ce,"Amin." Je ka, kai dama ai ba abokin kuka bane." Na ji, a nemi abokin kuka a gaya masa, ranar da ta dariya ta zo, kar ace an san mu." Ya mike ya wuce, yayi sallama da Umma da su Zarah. Suka yi masa godiya, ya fice, ya bar gidan, ba tare da sun sake cewa juna affan ba, shi da Naseer. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ BAYAN WATA BIYAR a hankali Nusaiba ta fara fahimtar irin zaman da su ke yi da Naseer, tamkar zaman doya da manja ne. Haka ya bata daman gane banbancin karara yake nunuwa tsakanin ta da Zarah. Al'amarin ya soma damunta, saboda ta ka sa gano dalilin da yasa hakan ke faruwa? Su kuwa iyayenta a kodayaushe kokarinsu ta zauna gidan mijinta tana mai ladabi da biyayya. Watannin 5r kenan da barin su Hanwa, kuma tuni hannun Naseer ya warke, amma Alh. Basheer ko Umminta babu wanda ya sake ta da zancan su koma can. A tunanin su babu komai, tunda suna jin dadin zaman su anan Tudun Wada, kusan duk abubuwan da aka sace masu, sun maida masu sabbi. A yanzu ba abinda Alh.Basheer ya fi maida hankali a kai, shine ya g a Naseer ya koma makaranta sosai,hankalinsa ya karkata ga karatun sa, akan ya dawo wasa gadan-gadan. Shi kuwa Naseer kallon hadarin kaji yake wa kowa. Komai aka ce yayi, sai ya nishadantu sannan yayi shi. Shi a dole da kan sa yake so ya ja akalar sa. Safiyar wata juma'a Zarah ta tashi da wani azababben zazza6i mai dafa jiki. Hankalin Nusaiba ya tashi lokacin da ta shigo dakin, don ganin yaya Antinta ta kwana? Nusaiba ke da girki, kuma wannan al'adarsu ce kullum safiyar su binciki yadda dayansu ya kwana. Wannan halastacciyar dabi'a mai kyau ce, kuma hakan shi ya wajabta ga kowanne musulmi a hakkin zaman tare. Da gudu ta koma dakin Naseer, barci mai dadi ne ya dauke shi. Bata san lokacin da ta dasa hannunya a jikin sa ba, ta hau bubbuga shi, "Yayanmu! Yana ji, ya kyale, haushi da takaici duk suka yi masa bargo. Idanuwanta suka kawo kwalla, muryar ta, ta soma rawa,"Yayanmu, don Allah ka tashi,"Antina ba lafiya......... Bata gama fada ba, ta ga yayi wufe ya mike, ita da ke duke gefen gado har ya riga ta ficewa. Ta biyo bayansa, cikin sauri ta iske shi a dakin. Bisa gadon ya haye, ya yaye bargon yana kira. "Zarah! Menene? Jikinta yayi zafi sosai, tana rawar sanyi, ta kasa magana. Ya rumgumo ta jikinsa." Zarah! Bude ido ki dube ni, ina ke miki ciwo? Da kyar ta iya fada,"Zazza6i.""Tun yaushe? Ta ce"Da shi na kwana. Ku kai ni asibiti." Idanuwan sa suka kada nan da nan. "Haba Zarah, ya za ki kwana da ciwo ba ki yi Magana ba? Ai haka babu kyau. Zarah menene amafani na a gidan nan? Hawaye suka tsunke wa Nusaiba, ta juya da gudu, tayi waje ta nufi sasan su Umma. Shi kuwa Naseer tuni ya kule, iya wuya. Duk yadda yake ji da matarsa, ace ta kwanta cikin wani hali babu taimakon kowa, alhali yana cikin gidan nan da ransa. Me ya jawo wannan, in banda zaman Nusaiba cikin gidan nan. Ba don haka ba, me zai nisanta shi da abar son sa na tsawon awa daya balle a kai ga kwana? Har ta kwana yashe ita kadai cikin mawuyacin hali, abin tausayi. Ya runtse ido, tamau, kamar ya kwarma ihu. Tabbas an rusa masa shirin tsarin rayuwar da ya ci burin yi da Zararsa. Ya kuwa zama dole ya tsani duk wanda ya zama sila ko shi waye. Muryar su Umma ya ji suna fad'in, "Ka zauna ka rike ta a daki? Asibiti ya kamata ayi maza-maza a kai ta." Umma ta amso ta daga hannun sa, suka shirya ta tare da Nusaiba. Suna tafe a mota, yana k'ara wa kan sa zafi da tunanin abinda ba shine ba, a iska yake sawa ransa kunci, har ya soma sambatu cikin zuciya. "Gaskiya ina son na sake da mata ta. Wannan ai cutarwa ce." Ya daki sitari tare da ajiyar zuciya. Umma ta ce,"Je ka a hankali Naseer, za ta sami sauki da yardar Allah." Sun ga Likita, ta sha bincike da gwajegwaje, sakamako ya fito k'arara Zarah na dauke da ciki wata 2 cif. Ba karamin girgiza Nusaiba tayi ba, kuma take nan ta warware wa zuciyarta sark'ak'in da ta shiga na me yasa Naseer yake nuna bambanci a tsakanin su? Amsar kawai baya son ta ne. To me ya sa ya aure ta? Tambayar da bata gano amsar ta ke nan ba, har suka dawo gida. (Tofa me Nusaiba take nufi Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 2-03 Posted by ANaM Dorayi on 11:45 PM, 11-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______. . . Cikin Zarah wata 3 kenan har yanzu ba wata lafiyar kirki ta cika ba. Duk ta rame ta dushe. Gaba daya ayyukan gidan Nusaiba ta dauke mata, ga shi kuma tana kula ita sosai, a lokutan da Naseer baya gida. Sai dai tsakanin ta da shi ido ne kawai. Ba wai abubuwan da yake yi ba sa damun ta ba ne. A'a kokari take yi tana hadiye wa, saboda farin cikin Abbanta. Shi kuma Naseer matsalarsa ke nan, rashin nuna damuwar ta, so yake ya cusa mata, ta ji haushi ta nuna 6acin ranta a fili. Amma ko alama ta ki. Yau yana Kaduna don amsa kiran Alh. Basheer. A offi ce ya same shi. Yayi gaisuwa kamar yadda ya saba. Alhj ke fad'in,"Saura kwana hudu mu tafi Katsina, ban ga ka na zuwa atisaye ba, kamar yadda ka saba? Ya shafa keya, ya sunkuyar da kai,"Kodayake ku manya ne, ba ha bukatar atisaye." Ya kada kai,"Ba haka bane Alhj. Ka san jibi za'a fara rubuta (External WAEC), ina zuwa wasu 'yan (Lesson) ne shi yasa, "O.K." na ji. Yana da kyau haka. Za ka sami zuwa Katsina kuwa? Ya ce,"Watakila in sami zuwa, sai dai na duba (Time table) tukuna." To Allah ya bada sa'a." Amin." Ya amsa. Yayi shiru, kamar wanda ruwa ya ci. Da ka kalle shi, ka san a susuce yake. Alhj kan sa ya gane hakan, shi yasa yake ta kallo sa. Jim kadan ya dago, ya dube shi, suka hada ido, ya ce,"Zan karasa wajen su Yakubu.Ya ce,"To shi kenan. Daga can za ka wuce gida ne? Ya mike yana fad'in, "Eh!" A gashe su don Allah." "Za su ji." Ya wuce. Alhj ya raka shi da kallo. Kai bai yarda ba, akwai abinda ke damun Naseer, don haka har ya kai kofa, ya kira shi, ya dawo ya ce da shi,"Zauna Naseer." Ya ja kujera ya zauna. Alhj Basheer ya dube shi da kyau ya ce,"Naseer ni na gaba daya ka sauya min. Ba ka da kuzari kamar yadda na san ka. Me ke damun ka? Gaya min." Yayi dan yake ya ce,"Babu komai Alhj." Ya ce,"A'a ban yarda ba. Look Naseer, ni Babanka ne na dauke ta tamkar dan na haifa a ciki na. Kar ka 6oye min komai, idan akwai abinda ke damun ka, ka gaya min, muddin bai fi karfi na ba, zan maka maganin sa." Ya sake girgiza kai ya ce,"Allah, Alhj babu komai." Yayi jim, yana kallon sa kafin ya numfasa ya ce,"Shi kenan, ina sauraron ka, idan dai ka ga da matsala tafiyar nan, mu na iya dage wasan har zuwa lokacin da za ku gama (Exams) din, ko me ka ce? Ya ce,"To zan duba in gani." Ya mike,"Zan tafi." Ka gaida Abban ka da kyau." Ya wuce yana amsawa, Alh. Basheee yayi shiru, yana tunanin, amma sam ya kasa gane kan al'amari, ga shi a zahiri ya san Naseer ya canza, ba haka yake ba, musamman idan suna da wasa, ya fi kowa kosawa a tafi. To ko har sha'awar wasan ma aka cire masa a rai? Ya tambayi kan sa. Wani sabon tausayi ya lullube shi, ya ce,"Allah ka shiga tsakanin mu da makiyan mu." Shi kuwa dan gogan tafe yake, yana mamakiin yadda aka yi ya koyi shara karya. Shi da ko biyan kudin jarabawar bai yi ba, amma yayi ruwa yayi tsaki akan zai rubuta jarabawa. Yayi dan murmushi, ya ce,"Allah ka shirye ni." Ya jima wajen su Yakubu, suna ta hirarrarkin duniya, sannan ya baro Kaduna, ya dawo Zariya. Kai tsaye shagon dinkinsa ya wuce, ya iske Sageer na zaman jiransa."Dariyar me ka ke ta faman yi ne haka? Ya jawo wata dirowa, ya dauko ambluan ya mika masa,"Ta mece ce? Ya ce,"Kai dai bude. Ka gani." Ya bude, ya duba sannan ya dube shi baki sake." "Teaching ka samu a (Barewa College)." Yaushe Appointment din ya fito? "Dazu aka kira ni, aka ba ni. Ban dade da dawowa ba. Ina samun (Part-time) kuma zan wuce in ci gaba da Digree dina. Yayi murmushi ya ce,"Ka haye Yaro." Allah ya sanya albarka." Amin." To kai ya bayanin karatun? Yayi dan tsaki,"Zan yi mana." Kullum haka ka ke cewa har an gama biyan kudin (External) ka na kallo, ka ki biya. Me yasa saboda Allah? Yakamata ace rashin son karatunka tun na yarinta ya wuce." Ya ce,"Ni na gaya ma ban son karatun ne? Kawai haushi aka ban, na fasa." Ya 6alla masa harara,"To wa kai ma wa? Ya ce,"Kai nai mana." Bata yuwuwa haka Naseer, abinda zai amfane ka, har wani zai ba ka haushi ka fasa?Ya ce,"Zancan ka ke so. Ai ni ma na san abinda na ke yi., Wai don ranin wayau, sai da zai ban 'yar sa yake tambaya ta, ya maganar karatu? Diploma gare ka ko Degree? Ya fadi yana kwaikwayon salon maganar Alhajin. Sageer ya tsura masa, ido,"Ba ka da kunya Wallahi, sirikinka? Ya ce ,"Kyale ni, lokacina na ke ci. Duk lokacin da na nishadantu, na koma makaranatar! Kai me ma sunan ka? Kullum mancewa na ke." Ya tambayi cikin yaran shago. Ya ce,"Abbas." Yawwa Abbas, kwaso min kayan koyon dinkin nan, ka ji? Ya tashi yana fadin,"To." Ya dubi Sageer ya ce,"Yanzu fa sai ka ji haushi na ko? Wai me yasa ba ka goyon baya na ne? Yayi dan tsaki mai dauke da takaici, ya mike ya koma bisa keken aiki, ya ci gaba da yi wa kayan gaban sa aiki." Yayin da Abbas ya kawo wa Naseer kayan koyon dinkin sa. Maida su kawai, maida su." Yaro ya juya da su. Shi kuma ya mike, ya fice daga shagon yayi gida." ********************** Zarah na jingine da gado. Nusaiba na bisa Kujera, suna ta faman hira. Sallamar yayansu suka amsa. Sannan suka hada baki yi masa sannu da zuwa. Wajen Zarah ya nufa, ya zauna bakin gadon ya sumbaci kuncinta, ya ce,"Zarah ta kenan. Maman Bebi ya kike? Ta dan kirne fuska rumgume da hannayenta a kirji, ta zura masa fararen idanuwanta da su ka kara tabbatar yana yin da take ciki. Shi yasa take kara masa kyau. Yayi murmushi sosai, ya sake fadin,"Bebina ya kara miki kyau, ba ki ga yadda ki ka dawo ba. Balarabiya sak! Yana sa aya. Nusaiba ta mike ta bar dakin." Ya bita da kallo har ta fice, sannan ya maido da fuskar sa ga Zarah, ya ja dogon hancin ta, ya ce,"Me ki ke marmari, in je in nemo shi? Ta ce,"Abinda ka ke yi ba shi da kyau, kuma baya min dadi, kullum ina gaya maka zancan nan. Ga shi nan tun bata jin haushi, yau ka kure ta. Ya ja ha6arta, ya ce,"Shine ki ke 6alla min harara? Ba zan yi wasa da mata ta ba? A wane nafsin aka haramta min hakan? Ta ce,"Ba'a haramta maka ba, amma an umurce ka da dalci, kuma an wajabta maka shi. Gaskiya ba na son abinda ka ke yi." Ya dan mari kuncinta, ya ce,"Ni ina so, ba ki ji dadin da na ji ba yau, ba na bata haushi." Ta dan lumshe ido, ta kauda fuska." Nusaiba ta yi sallama. Zarah ta amsa. Ta shigo dauke da tire karami. Ruwan sanyi ne da Jus na kwali da kofuna 2, ta aje gaban sa. Yadda ya zura ido, yana kallon ta, tana zuba masa ruwa. Shi ya ba Zarah dariya. Ta gode Allah da Nusaiba ba haushi ta ji ba, hasali ma ruwan sanyi ta je kawo masa ya sha, ya ji dadin rashin adalci." Ta sa hannu ta, ta mintsile shi, ya dan zubara, ya dube ta. Ta daga gira, tana masa murmushi mugunta. Ya juya kan Nusaiba, ya ce,"Daina zuba ruwan nan, ba sha zan yi ba. Ta aje, ta mike ta ce,"Antina bari in je in dan kwanta, tunda ga yaya na nan ko? Ta ce,"Ayi barci lafiya amarya." Bata saurari komai ba, ta koma dakin ta, ta kwanta tana ta sake-sake har barci ya sace ta. ***************** Yana zaune a shagon dinkinsa, baya aikin komai, alhalin suna da wasa A Kaduna, amma ya ce wa Alhj ana neman su a makarantar da ya ce ya samu. Sageer na ta dinkin wata atamfa. Naseer ya katse shi da tambaya. "Ban gane bane, kodayaushe yarinyar nan ta kawo dinki, sai ka aje na kowa, ka kama na ta. Ta fi sauri biyan kudi ne?" Yayi 'yar dariya, ya ce,"Sa'ido kuma ka koma?" Fa'iza ai kostoma ta ce, dole in yi mata dinki." Ya kalle shi a dage,"Amma kai ba karamin dan rainin hankali bane,"Don tana kostomar ka, sai ka aje dinkunan da suka yi sati 4, ka kama wanda aka kawo jiya? Jiyan ma da yamma." Fada ka ke min, kome? Ya ce,"Ban sani ba. Bari kuma ta zo, sai kun gaya min abinda ke tsakanin ku, kafin a bata dinkin nan. Ina nan ina jiranta." Sageer yayi wata bazawarar dariya,"Ashe za ka kwana anan. Kai idan ma ka ban haushi, sai in kai mata gida, in ce ta bar kudin." Ya nuna su Abbas,"Ka ga 'yan yaran nan? Su za ka yi wa barazana, ba ni ba. Za to zo ta same ni, ka san halina, ban kyalewa." Ya dan kura masa ido, sannan ya baro inda yake, ya zo wajen sa ya kamo shi,"Zo ka ji wata magana." Ya fizge hannun sa,"Babu abinda zan ji Malam." Ya jawo shi da karfi."Taso mana, wani sirri za mu yi.". Ya taso suka fita waje. Me yaran 2 za su yi, ba dariya ba, suna wa juna rad'a,"Yau an k'ure oga Sageer." Suna fita. Naseer ya ce,"Yi sauri ka fadi abinda za ka fada, in koma." Ya ce,"Don Allah kar ka yi min fallasa gun yariyar nan." To menene na aje dinkin wasu ka yi na ta? Ya ce,"Gaskiya sonta na ke yi, ta kuma jima tana kawo min dinkunan ta da na 'yan gidan su, amma ni ban yi karanbanin gaya mata ba." "Saboda me?" Ina tunanin wasu abubuwa ne. Ka ga bai kamata in fara neman yarinya ba. Tunda ba aure na shirya yi ba. Amma yanzu zan taya, in gani idan tana so, shi kenan." Ya kai masa duka a kafada, yana 'yar dariya." Shine za ka dame mu da cuwa-cuwa a shago, ai gara a gaya mata, mu san cewa ta mu ce. Ka ga ko ni, sai in dinka, bari, mu je ka gama dinkin, a sa a leda mu kai mata gida. Ka san gidan na su? 'Yar layin Rimi ce." Ba matsala. Allah yasa kar ka sha kaye." Daina fadi, kar ka sani hawan jini." Suka dawo ciki, suna dariya tare da tafawa. Karfe 6, dai-dai, suna dawowa daga layin Rimi. Cike da farin ciki Sageer yake, domin Fa'izah bata ba shi kunya ba. Da hannun bibiyu ta kar6i tayin sa. Kusan ita ma ta dade da kaunar Telanta Sageer cikin ranta. Kofar shago suka yi fakin, lokacin da wayar Naseer ta dau kuka, ya zaro ta, gaban aljihu ya duba.Tsaki yai, ya mika wa Sageer, ya ce,"Don Allah gaya mata na bar wayar caji ne a shago." Ya amsa, yana dubawa, sai ya ga sunan Nusaiba. Ya dube shi a yamutse ya ce,"Ban gane ba? Ka san abinda ke faruwa a gidan? Kuskure ne wannan. Naseer ka daina." Wayar ta katse. Yana can yana tunani. Gaskiya ne kuma, haka banza Nusaiba bata kiran sa a waya. Shi yasa tana kara daukar ruri, ya figi wayar a hannun Sageer, ya danna O.K. Ya sawa kunnan sa, "Menene? Murya na rawa, ya ji tana fadin,"Jikin Antina ya rikice, ka zo a kai ta asbiti." Ido waje ya aje waya, yayi wa mota key, ya ja ta a guje." Menene? Sageer ya tambaya. "Wai jikin Zarah ya rikice. Ka ji ba...........?" " Yi shiru haka, don Allah." Ba zan yi ba, kai gaskiya ce ba ka so, ba kuma zan daina gaya ma ba." Yayi banza da shi, yana ta surutun sa. Baya ma jin abinda Sageer ke fadi, don ba shine damuwar sa ba. Yana fakin kofar gida, ya fito cikin sassarfa, ya fada gida. Sageer ya biyo bayansa. Suna tare da Umma a dakin Zarar, sai murkususu take, ciwon ciki da mara, nan da nan suka dunguma asibiti, ko kafin su isa, jini ya tsinke mata, shi yasa suna zuwa dakin 'yan 6ari suka wuce da ita. Hankalin kowa ya tashi, ba kamar Naseer da yake jin zuciyar sa na kokarin tsago kirjin sa. Saboda tsabar firgicewa. Haka idanuwan Nusaiba ya raina fata, tana zaune ta cusa kai cikin guiwa. Addu'a kawai take yi, kama-kama har bayan isha'i, sannan cikin dan wata 4 ya fita.Idanuwan Naseer suka yi ja, amma jin Zarah na nan lafiya, sai yayi wa Allah godiya. Anyi mata wankin ciki, ta dan hutu zuwa tara da rabi, na dare, suka dawo gida. Washegari Nusaiba, ta hado kayan karin safe, ta shigo masu da shi dakin Zarah. Tana zaune gefen gado, ta dubeta, ta ce,"Mun yi waya da Kausar dazu, ta ce, in gaishe ki, su Ummi ma ta ce za su zo anjima." Ta ce,"Ina amsawa. Kausar ta ba mu kewa, tunda muka dawo nan, ko ta leko mu." Ta ce,"Kausar ai ba mutunci, da anyi magana, ta ce karatu." Tana da gaskiya." Ba wata gaskiya Antina, ke dai sakko mu karya." Ta jefa filon kujera bisa kafet, suka fara karyawa. Naseer ya shigo ya dau wanka, kananan kaya ya sanya. Ya zauna gefen gado. Zarah ta hada masa Tea ta mika masa. Ya kar6a yana sha, suna 'yan hirarraki tare da Zarah. Wani lokacin Nusaiba kan tsoma baki, musamman idan ta fahimci Naseer ya ya6o mata magana. Bai tashi a dakin ba, sai da Inna ta zo duba jikin Zarah. Kwarai ta ji dadin yadda ta same su. Ba ta jima da zuwa ba,"Direba ya kawo Ummi. Sun dade suna hira a dakin Zarah, kafin Ummi ta koma dakin Nusaiba, suka gana tsakanin da da Mahaifi.. ********************* Shekara guda da rabi kenan da auran su, sau 2 Zarah na samun ciki, yana zubewa duk da dabarar da ake mata a asibiti na daure mahaifarta, saboda sun gano ita ce bata da karfi.Da zarar cikin ta ya kai wata 4, sai a daure, amma kash! Yana kai wa wata 5r, dole a bude ta, don samun lafiyar ta. Zuban jini kamar famfo, har sai cikin ya fita. Wannan shine ciki na 3n, kuma an daure mahaifar har bata hutu a asibitin watau (Bed rest). Wata 2, ta samu, bata aikin kome, illa ta ci, ta sha, tayi wanka ta kwanta. Kusan Naseer a asibitin nan ya tare a 'yan tsakanin nan, musamman da ya ga cikin ya tsaya har ya kai wata 6 da shiga na 7. Zaran kuwa zaman asibitinya ishe ta, ta damu kwarai, tana son su sallame ta, ta koma gida. Yau Naseer na Kaduna. Suna da wasa. Dole ce ta sa shi tafiya wasan, domin yau lahadi ce babu wata karyar da zai wa Alhaji. Ta karatu. Nusaiba ke tare da Zarah a asibiti tun safe. Abincin da soye-soye kala-kala tayo mata, irin wanda take sha'awar ci. Musamman (Cole-slow), tana bala'in son cin sa fiye da komai, ga shi Nusaiba ta iya yin sa, yadda ya kamata. Shi take ci. Bayan sallar azahar, hira tayi hira har suka fada zancan zaman ta asibitin. Ita ta fara fadin,"Asibitin nan ya ishe ni amarya, amma kowa ya ki bada goyon baya, in koma gida ko na dan sakata, in wala." Wata 'yar harara ta sakar mata,"Lallai Antina, da wa ki ka so ya goya miki baya?Ki na ganin an fara samun nasara, muna ta murna, shine za ki ce gida za ki." Ta ce,"Koma ke ki ke zuga yayanmu, kullum yana like da Doctor suna kus-kus? Ta ce,"Allah ko daya. Amma Ubangiji yayi wa mai zuga shi albarka. Me za ki zo ki yi a gidan? Ta nuno ta da cokali." Ki na son in kwashe hakoran ki kenan, kin san na koya wajen yayanmu." Tana 'yar dariya ta ce,"Allah Antina a daina maganar wasa, zaman ki anan yana da muhimmanci, su Doctors din ai sun san abinda suke ji." Tayi dan tsaki,"Don dai ba ke ki ke zaune wajen nan ba, shi yasa. Wai ma to ko a gidan na ke, aikin me zan yi? Taimakon da ki ke min, ai iyakar sa kenan, ko Inna hakan za ta yi min. Ga mai wanke-wanke Ummi ta turo mana. Dama can wanki yi mana ake yi, menene kuma ya rage, saboda Allah. Gaba daya babbar ka'idar ba'a son miji ya matsa min, yayanmu kuwa ba shi da matsala, matansa 2 ne. To ki gaya min menene bambancin zaman nan da gida? Ta sauke numfashi ta ce,"Ni dai ina shawartar ki Antina, ki yi zaman ki anan ba. Ta aje filet ta ce,"Sai ki ban hujja. Idan kuwa babu, kin san Allah ba zan sake kai wani sati anan ba. Sai na na san yadda na yi na tsere." Ta tsura mata ido,babu alamar wasa a zancan ta. Ina sauraron ki." Ta dan yi jim, kafun ta ce,"Hujja ta daya ce, akan babbar k'a'idar nan da ki ka fadi, gara a kiyaye, kin fa san yau da gobe sai Allah. Ta harare ta,"Ban son iskanci, ke zaman me ki ke yi,?" "Aure mana. Amma ina gaya miki ki yi zaman ki anan, shine rufin asirin mu, don Allah ki bar mu mu sami Bebin goyo." "Lallai kin maida abin wasa, za ki sha mamaki na." Ta ce,"To Anti ba sai ana son mutum ake kula shi ba? Ke ba za ki gane ba Anti, amma ina gaya miki, ki yi hakuri, saura 'yan watannin kadan ne." Gaba daya zuciyarta ta girgiza, domin nan take ta gane abinda Nusaiba ke nufi, sai dai a fuska bata nuna mata ba, kara maka mata harara tayi,"Ba ki da hujja amarya, so ku ke kawai ku azabtar da ni da zama waje daya kamar 'yar gidan yari ." Ta kamo hannun ta, tana 'yar dariya,"Antina kenan, Allah ya bar min ke. Ai shikenan, an wuce wurin ko? Ta ce,"Ya zan yi?" Tunda haka ku ka fi so. Ta mike ta dawo gefen gadon, ta dan rungumota,"Da me da me zan kawo miki gobe?" Ta ce,"Za6in ki, za6i na ne amarya. Ki kawo komai, zan ci. Yanzu za ki tafi? Ta duba agogo, sai zuwa 3 da rabi. Ta ce,"To kin ga idan za ki tafi ko ki rage kayan wajen nan sunyi yawa, ki bar min kwandon wanka da na burosh kawai.Wadannan zannuwan duk ki koma da su, gobe a kawo min wasu." Ta ce,"An gama Antina." Suka ci gaba da hira har zuwa 3 da rabi. Nusaiba ta kwashe kaya, kamar yadda Zarah ta ce. Tun da Nusaiba ta tafi. Zarah ke zaune bisa sallaya, 6acin rai cunkushe cikin zuciyar ta, bata san lokacin da hawaye ke satata ba, Sabida tsabar tausayi da takaici. Tana ganin wayar Naseer na ta kururuwa. Amma ta ki dauka, yayi kira ya fi sau 5, sannan ya aiko sako, shi ma bata bude ba, balle ta san me ke ciki. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Karfe 8 bayan sallar isha'i, Zara ta had'a 'yan abubuwan da suka rage, cikin jakar hannun ta, ta faki

Chapter 4 of 6