Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
idon kowa, ta fiyo a hankali ta bar asibitin. Aca6a, ta haye ya aje ta gida. Bata yi sallama ba, har ta shigo cikin gida. Umma na can ciki tana sallah. Abba kuwa bai dawo daga masallaci ba. Don haka ta wuce da sauri sasan su, ta tura falon ta shiga. Shirin na ta gwanain sa'a, domin Nusaiba na can bayainta tana wanka. Saboda haka ta wuce dakin ta. A rufe yake, amma ba da makulli ba, tayi hamdala ta shige, ta mayar a hankali ta rufe. Ta aje jaka ta koma gado ya kwanta don hutawa, don bin dokar likita. Naseer bai shigo Zaria ba, sai tara saura kwata, kai tsaye asibiti ya wuce don ganin Zarah tare da neman sanin dalilin rashin daukar wayar sa.Kowa na bisa gado, amma gadon Zarah babu kowa. Ya tambaya. Suka ce su ma ba su ganta ba, babu ma wanda ya san lokaci da ta bar asibitin. Hankalin Naseer in yayi dubu, ya tashi, ya bude wa Nosis wuta masifa yake kamar ransa zai fita. Da kyar suka samu ya sassauto ya saurare su. A inda suka shawarce shi da ya je gida ya duba, tunda ga shi babu kayanta ko daya sai 'yar karamar kular abinci kan dirowa. A fusace ya fice asibitin baya ko ganin titi sosai, saboda tsabar fushi. Lokacin daya shigo gida karfe goma saura 'yan mintoci ne, su Umma har sun rufe sasan su, wucewa kawai yayi ya fado falon. Nusaiba ma ta jima da rufe dakin ta. Sai dai ba barci take yi ba tunanin duniya ya ishe ta, tare da juyayin irin yanayin da ta tsinci kanta, wanda a kodayaushe take aje shi a matsayin kaddara daga Allah. Kofar dakin Zarah ya wangame, cikin zafi da fushi. Kwance ya ganta ba kuma barci take yi ba, domin idanunwanta ya fara arba da su. Bai rufe kofar ba, ya wuce da sauri yana fadin." Zarah kin kuwa san abinda ki ke yi? Don me za ki baro asibiti, ba tare da izinin kowa ba? Ta dauke kan ta, tayi banza da shi har zai ga zama bakin gadon." Ba za ki yo magana ba?" Shi yasa na ke ta kiran wayar ki, ki ka ki dauka? To kar ki ji da wai, yanzun nan za ki koma asibitin, tashi- tashi! Kar ki 6ata min lokaci." Ta dube shi, ido fal da hawaye ta ce,"Ba zan koma ba yayana." Ta yunkura ta tashi zaune, yayin da ya saki baki yana al'ajabinta, "Ba za ki koma ba? Ta ce,"Kwarai ba zan koma ba Ai ban san rashin adalcin ka har ya kai haka ba yayana. Don me? Saboda me? Ka na cutar da 'yar mutane ka na so ka ci wutar Allah ne? Hawaye suka soma zuba. Ya ce,"Nusaiba ba matar ka ba ce? Don me za ka aje ta shekara daya da rabi, ka na cutar da ita? Kuma tana kallo na, tana sane da abinda ke Faruwa. Wannan zalunci ne. Allah ba zai bar ka ba yayana, gara ka san halin da ka ke ciki, ka gaggauta yin gyara........... Ya daka mata tsawa wacce ta kara jawo hankalin Nusaiba da tuntuni take jin 'yan surutan da bata gane daha inda suka fitowa ba, don haka ta taso a hankali ta fito. "Ya isa Zarah! Ya isa! Dama saboda wannan maganan ki ka baro asibitin ba izini? To ina son ki sani, babu ruwanki a ciki wannan maganar, ban kuma ce ki sa kanki a ciki ba, zamanta daban, zaman ki daban, kar ki sake yimin wannan maganar." Tayi zuciya sosai, idanuwan ta suka kara yo waje, ta ce,"Kwarai akwai ruwa na a ciki domin ni ban dauki Nusaiba a matsayin kishiya ba, 'yar uwa ta ce, kuma ina kaunar ta tsakani da Allah. In don akan wannan cikin yasa ka ke kumfar bakin, don me na baro asibti, bari ka ga yadda za'ayi da shi, tunda shi kadai ka ke so, ba ka tsoron Allah." Tana fada ya ga ta mike bisa gado ta hau buga tsalle sama tana direwa da karfin tsiya, hawaye na zuba bakinta na fadin,"Ban son shi, sai ya zube wallahi! Nusaiba ta kara mannewa da bango, ta fasa kuka sosai, ciwon zuciyar ta ya karu, har sai da ta sulale kasa. Da kyar ta rarrafa ta koma dakinta. Nan bisa kafet ta kife, tana rusar kuka, wanda ita kanta ba za ta iya tantance dalilin yin sa ba,Illa iyaka ta san ita abar tausayi ce, sai dai kuma ai bata ratayawa ranta son Naseer ba, tana dai zaune ne kawai, don farin cikin Abbanta kamar yadda ta fahimta shi ma Naseer ya amshi auranta ne saboda girman Abban na ta a idonsa. Amma da ciwo, ka na zaman mu2m bai damu da shirgin ka ba. Sai da yayi ta maza sosai, sannan ya cukuikuyo Zarah yayi iya kokarinsa kafin ya samu ya manna ta ajikin sa,"Kin yi hauka ne Zarah?? Za ki kashe kan ki ne? Ta rushe da kuka sosai, bai ta6a ganin tashin hankalin Zarah irin na yau ba. Gaba daya jikin sa yayi sanyi,"Ki yi shiru Zarah, na ce na ji, na yi laifi, zan gyara." Ta sulale a hankali ta zauna, saboda yadda take jin jikin ta ko'ina ya daddure. Ya biyo ta da sauri, ya dago fuskarta,"Za ki takaita ni ne Zarah? Don me za ki min haka? Murya na rawa ta ce,"Dole in yi maka yayana. Domin rayuwar ka na cikin hatsari, kai har da ni ma, tunda ta gaya min na sani, hakki na ne in gaya ma ka gaskiya. Zalunci babu kyau yayana, kar shaidan ya kai ka ya baro, shi gaba daya mece ce rayuwar? Ya tallafi kuncinta, ya goge hawayenta." Duk na ji, na ce zan gyara. Amma ita ma bai dace ta gaya miki ba, wannan rashin kunya ne." Ta ce,"Tayi rashin kunyar. Ai ba kanta tsaye ta gaya min ba. Magana mu ke akan zamana asibitin, na ce ya ishe ni, zan dawo gida, tunda tana nan za ta dauke min komai. Ka ji abinda ya kawo maganar. A hakikanin gaskiya ka cutar da........ Ya toshe bakinta,"Yi shiru, ya isa haka. Na dauki kuskure na, shi kenan? Saura gyara." "Ai zan gyara. Yanzu da ki ka baro asibiti me su Umma suka ce? Ta ce,"Ni ba wanda ya san na shigo gidan nan, har ita amarya." Ya ce,"To ki taso bakin ki alaikum in maida ki." "Muryar Umma ya jiyo tana kwala ,"Naseer! Naseer!! Ya runtse ido, "Shi ke nan ga Umma can ta fito." Ya mike yana amsawa ya fito. Tana tsaye kofar falo. "Hayaniya na ke ji, wai me ke faruwa? Ya rasa me zai ce, sai kawi ya ce,"Umma Zarah ce ta gudo daga asibiti." Zarah? Ta fada cikin al'ajabi. "Ina take? Ga ta nan cikin daki, na yi na yi ta zo mu koma ta ki."Jin muryar Ummar yasa Nusaiba ta buda kofa ta fito. Tare suka cusa kai dakin, tana zaune tana faman share kwalla. Nusaiba ta ruga ta rungume ta,"Antina, me yasa? Ganin Zarah na kuka, ita ma na ta ya dawo. Umma ta ce,"Amma dai Zarah ba ki da hankali, ki na wasa da lafiyar ki ko? Maza mike ku koma, kafin in kira Abbanku, ba na son jin wata magana." Nusaiba ta sake ta, ta kamo hannayenta,"Tashi Antina mu je a maida ke." Ta mike Umma na fadin"Nemo mata hijabi." Kafin Nusaiba ta dauko hijabin, jini ya malalo har bisa diddigen ta. A hankali ta yaye zane ta duba, ido waje ta kalli Umma. Wasu hawayen suka tsirgo. "Umma duba ki gani." Ta hau salati da tafa hannu. Naseer ya rude,"Kin ga irin ta ko? Kafin su yi haka ya sunkuce ta yayi waje. Nusaiba ta biyo su da gudu hijabi a hannu. Umma ta kwala wa Abba kira ya fito a rude. A rudan take gaya masa, ta fice da gudu. Kafin ya fito waje. Naseer ya ja mota sun wuce, nan ya tsaya yana ta sababi shi kadai. Da ka gan su ka san a rikice suke gaba dayan su, babu mai takalmi balle mayafi. Zarah ta sha fada wajen Likita da Nosis. Suka yi mata allura maimakon jini ya tsaya, sai ciwon mara kamar za ta wuce barzahu.Dole a kwance mahaifa. Haka Likita ya gaya wa su Naseer. Zufa ta keto masa, babu abinda zai iya yi, tunda hakan shi ne samun lafiyar ta. In anyi sa'a a sami dan.Komai na Allah ne, haka nan suka fauwala wa Allah. Ana kwala kiran sallah ta haiho dan ta namiji. Sai dai yayi k'ank'anta. sosai. Naseer yayi kamar zai rasu, don murna, haka Nusaiba ke sauke numfashi tana kokarin dai-daita shi. Ba su ga Yaron ba, saboda an hanzarta sa shi a kwalba. Bayan an kintsa Zarah, an fito da ita dakin hutu, can suka kutsa kai suna rige-rigen gaishe ta. Minti 15 bayan fiddo ta. Naseer ya koma da Umma gida, don kwaso kaya da dukkan abinda ya dace. Nan suka bar su tare da Nusaiba, duk doki ya ishe ta, ta kosa ta ga Baby. Tare suka dawo da Inna. Daga bisani ne su Abba da Malam Umar suka zo asibitin, suka duba Zarah! Zarah kam ta sha fada wajen iyayenta akan baro asibiti da tayi. Ta amsa laifin ta, ta kuma bada hak'uri saboda bata son kowa yasan dalilin barinta assibiti. Babu wanda ya ga Baby, domin likita ya hana, ya ce sai karfe 6 yamma za'a fito da shi, idan ya sha nono a maida shi.Ai kuwa Umma sai da ta jira lokacin yayi. Wata Nos ta fito da shi don koridon dakin aje jarirai wanda shi ma a rufe yake ruf. Kai! Wannan Yaro Allah ya zuba halitta mai kyau a wurin nan. Tamkar Naseer yayi kaki, kamanin su daya, amma ya zarce Naseer kyau, nesa ba kusa ba. Tun da yayi arba da Baben nan, jikinsa ya dauki rawa, ya ji gaba daya duniya, babu abinda yake so fiye da Bebin. Da haka Nusaiba ta tsinci kaunar Bebin nan cikin ranta, kamar ta gudu da shi. Amma ina. , Minti 30 aka ba su, su gan shi, lokacin na cika, da kyar Nos ta kar6e shi hannun Naseer, ta koma da shi. A ranar Abba ya rada wa Yari sunan sa watau Iliyas!. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Satinsu 3 a asibiti sai dai Zara ta zo gida tayi wanka ta koma. Babu wanda bai zo ganin su a asibitin ba, hatta Fa'iza. Sageer ya kawo ta, ta gaida Zarah. Haka Kausar bata yi kasa a guiwa ba ta zo, ta kuma ce za ta dawowa ranar da aka tsaida shagalin suna. Cikin wayoyin Naseer hotunan Iliyar (Ameer) ne birjik iri-iri. Babu yadda za'ayi ya wuce awa, bai bude ya gan shi ba, kwarai ya kwallafa Yaron nan cikin ran sa, kamar shi kadai ya fara yin Da.Sun shafe sati 3n nan cif! Sannan aka sallami Bebi. Nusaiba na son ta rike shi a mota, amma ubansa yayi kane- kane. Sageer na tuki, yana masa tsiya, ganin yadda yake ta kara rurrufe shi da shawaul, don Likita ya ce kullum ya kasance a lullu6e. Ranar da ta zagayo, aka shirya gagarumin shahalin suna. Nusaiba ta kashe kudi, abubuwa kala-kala tayi na ci da na rabo, balle uban gayya. Ko lokacin bikinsa bai saki jiki da aljihu irin na wannan yaron ba. Mai-jego kuwa ta kwashi kaya akwatuna 2 manya. Nusaina ta shirya kayan Bebi da zannuwan Mai-jego. Banda wasu tarkace cikin (Ghana most go). Bayan kowa ya watse. Nusaiba da Naseer na zaune suna kallon yadda Umma ke wanke Bebi da ruwan zafi, yayin da Zarah ke bayinta tana na ta wankan. Nusaiba ta dube ta, ta ce,"Ni kuwa Umma in ki na wankan nan, sai in ta mamaki." Mamakin me? Ta ce,"Ni gani na ke kamar zai sumbule, ke kuwa ki na tayi masa, ba kya jin komai." "Dariya Umma tayi. "Nusabai oho! Ka ji Naseer, ashe in ta haifi na ta, ba za ta iya wanke shi ba." Tare suka kalli juna da Naseer, yayi yaken dole, ita kuwa kunya ce ta rufe ta, ta mike za ta wuce, ya ce,"Ina za ki kuma? Ba ke ki ka dauko zancan ba?Tsoma bakin sa yasa ta k'ara azama ta bar dakin. Umma na dariya. Naseer na murmushi, yana fad'a a ran sa, "Yarinya sai salon tsiya."Umma ta nade Yaro a tawul mai laushin gaske, tana fadin,"Ita ma Allah ya kawo masu albarka." Ya shafa k'eya ya ce,"Umma hanzarta ki sa masa kaya akwai iska. Ta zubo masa ido ta ce,"Na k'i, ka fi ni son shi ne? Ya kada kai yana murmushi,"Tuba na ke UmmaTa." Yana rufe baki. Abba yayi kiran sa, ya tashi ya fice. Abban na falon sa a zaune bisa kafet, shi yasa yana zuwa ya tamkwashe kafa gaban sa, ya ce,"Ga ni Abba.." Ya dube shi da kyau ya ce,"Na yi maka zuru in ga irin hankalin ka, sai na lura lallai ba ka da hankalin." Gabansa ya fad'i, ya k'ara matsowa ya ce, "Me na yi Abba? Ya ce,"Maganar komawa Hanwa, na ji ko tada zancan ba ka yi, me ka ke nufi? Ya dan sunkuar da kai, ya sauke numfashi,"Yaya mu2m zai ba ka gida, amma ka ki zama? Saboda 6arayi sun shiga ma sau 1? Anji ba ka da lafiya wancan karon, har yanzu ba ka warken bane? Yayi dan shiru kafin ya ce,"Abba ba haka ba ne. Ni kai na ina son komawa can, amma da zarar na tuna da irin dukan da na sha wajen 6arayin nan, ni kan ji tsoro ya kama ni. Kar ka damu Abba za mu koma."Ya ce,"To ka hanzarta sa ranar, ku koma. Na san Alhj na da kawaici, ba zai ce komai ba. Amma babu dadi mu2m yayi ma ka kyauta, ya ga ka na yi wa abin rikon sakainar kashi, ko kai ne ranka ba zai maka dadi ba." Ya ce,"Haka ne, insha-Allahu zan san yadda za'a yi." Yauwa sai ka yi wa Allah godiya kawai kan matanka a hade yake, asirinka ya rufu dari bisa dari, domin zaman lafiyar iyali a cikin gida, shine kwanciyar hankalin Mai-gida." Ga su dai yara k'anana, amma Allah yayi masu kaifin hankali, shi yasa a kodayaushe na ke k'ara jawo hankalinka a kan kamanta adalci tsakaninsu. Ba cuta ba cutarwa,Naseer wannan shine tsoron Allah, ka sani zai tsaida ku ranar da ni da Umman ka ba za mu iya cetonka ba. Ina fatan ka ji ni da kyau? Ya numfasa sosai, ya ce,"Na ji Abba, na gode." Ya ce,"Ita kenan maganar, je ka wajen iyalinka." Ya mike jiki babu kwari, ya fito kai tsaye dakin sa ya wuce, bisa gado ya kwanta rigingine. Tunani ya addabe shi, ya rasa ta inda zai 6ullowa al'amarin. Sati 4 kenan da suka yi sa'insa da Zarah akan Nusaiba, sam ya rasa ta yadda zai fuskance ta, domin shi mu2m ne mai tsananin son ra'ayin sa. A JININSA YAKE!." Idan ya so abu, ya so shi har abada, inda ya kyama ce shi baya waiwayar sa balle ya daga masa hankalli Sai dai a yau Abbansa yayi maganar da za ta sa dole ya waiwayi abinda ba shi cikin tsarin sa, wanda a da yake ganin sai dai rai yai halin sa ko in ta gaji, ta nema wa kan ta mafita. Ya tashi zaune yayi wawan ajiyar zuciya, ya dubi agogon hannun sa karfe 9 na dare. Ya diro daha gado, ya fice ya dauki mota iya bar gidan. Kwana 2 tsakani. Ya kama ranar juma'a. Wannan rana za ta iya zama daya daga cikin ranakun tarihin rayuwar Nusaiba. Shigowar ta daki kenan, sun gama shan hirar su da Antinta, misalin karfe 10:30 na dare. Ta yi shirin barci ta haye gado, ta jawo littafin turanci (Novel), ta fara karantawa, don kauda tunani, kafin zuwan barci. Bata wani jima ba, ta ji an dan kwankwasa kofar ta, ta aje littafin ta taso ta sa makulli ta bude. Sai da gaban ta ya fadi, saboda wanda ta gani tsaye a kofar dakin ta. Ido waje take kallon sa, shi kuwa bai saurari komai ba, ya wuce ciki, hannun sa dauke da lemun gwangwanin. (Coke). Tsakar daki ta iske shi, ta nemi gefen gado ta zauna tana mai tsananin mamaki. Lemun hannun sa ya miko mata. Ya ce,"Ki sha yanzu." Ta kar6a ta duba, bakin gwangwanin a bude yake, ta sake kallon sa, bata iya cewa komai ba. Ya zura hannaye aljihu ya ce,"Ko ba za ki sha ba? Ta gyada kai, ta ce,"Zan sha mana." Ya ce,"To ki shanye, kin ji? Ta amsa da kai. Ya juya yayi waje. Ta bi shi da kallo, sannan ta juya bisa lemu, ta tsura masa ido,"Menene dalilin bani lemu in sha da tsohon dare? Kashe ni kuma yau zai yi? Gara ya kashe ni ma kowa ya huta, shi kenan an raba gardama." Kwalla suka tsatso mata, ta goge su. Kan ta tsaye ta kafa gwangwanin lemu ta yi sha, har ya kare. Tayi zuru gefen gado tana jiran abinda zai biyo baya. "Yan mintoci kadan ta fara hamma, idanuwanya su ka yi nauyi. Kafin ayi haka, ta rasa duniyar da take, nan ta wuce lauuuuu........bisa shimfida warwas! Minto 10 tsakani ya dawo dakin, ya zura mata ido. Sai kuma ya ji tausayinta ya kama shi. "Tabbas kwayoyin nan sun fi karfin jininta ga shi yayi mata (Over dose)." Ya gyara mata kwanciya, ya dafa goshin ta yayi addu'a. K'arfe shida na safiya, ya shigo dakin Zarah rike da carbin sa, yana ja. Ko gaisawa ba su yi ba, ta ce,"Ban ga amarya ba, bari in duba ta." Ya ce,"Barci take yi, tunda ta tashi tayi sallah, ta zube kamar matacciya." Wayyo, gajiya ce, bari in kyale ta, ta huta baiwar Allah. Tun da ka yi haihuwar nan bata yi sukuni ba? Ya zauna kusa da ita ya ce,"Ke ba kya gajiya da wasa amarya."Ta watso masa harara ta ce,"Me ye na ka a ciki? Ya langwabe kan sa a kafadar ta ya ce,"Babu komai Antin amarya. Ni matsala ta na yi missing din ki da yawa, yaya bayanin yake ne? Ta janye kafadar ta, ta ce,"Koma dakin ka yanzun Umma za ta kwaso ruwan wanka." Turo mata fuskar sa yake yi kamar zai cinye ta, kawai muryar Umma suka ji daf da kofar daki tana fadin,"Jama'a, wai yau ina Nusaiba ne? Yayi zumbur ya suro Ameer yana girgiza shi," Kai sarkin kuka ne ko? Ka hana mutane barci da sassafe kuma ka tashi. Dariya ta kullewa Zarah ciki, da kyar ta kirne ta ba Umma amsa,"Barci take yi Umma." Ta ce,"Allah sarki, gajiya ce, komai sa ta ce ita ce za ta yi." Ta dire bahon wanka Zarah ta miko mata kujera da kayan sabulu. Naseer ya miko Bebi, sannan ya tsugunna ya gaishe ta, ya samu ya sulale ya koma dakin sa. Agogo ya fara duba wa kafe 7 sau kwata. Yayi kasake yana tunani,"Kai 'yar mutane fa shiru? Ya tambayi kan sa. Ya zubara ya fito. Kofar ya murda a hankalu ya bude. Kwance ya hango ta yadda ya bar ta, tun kiran sallar farko. Ya shigo ya maida murfin a natse ya rufe. Ya matso ya shiga bubbuga ta, "Ke! Tashi! Ba ki san gari ya waye bane? shiru ka ke ji. Malam ya ci shirwa.Tsoro ya fara kama shi, bai san lokcin daya haye gadon ya tarairayi ta ba, ya dan bubbuga kuncin ta,"Ke Nusaiba! Ke! Can cikin sambatu take ta surutan da bai san abinda ta ke cewa ba. Tayi lauuu.....ta fada bisa filo. Idon Naseer fa ya raina fata. Bayi ya shige ya debo ruwa ya tarairayo ta, yana shafe fuskarta, yana kira tare da bubbuga kuncinta. Da kyar ya samu ta dan budr ido jajur! Ta dube shi,"Ki tashi aka ce, gari ya waye, kowa sai tambayarki yake yi." Ahaf, ashe duk surutun banza yake yi, zurun da tayi ma sa a cikin barci ne. A hankali ya ga idon ya karasa rufewa. Ya dafe goshi, ya runtse ido, ya ce,"Na shiga uku.!" Da ya rasa na yi, sai ya gyara mata kwanciya, ya rufe ta ya bar dakin. Mota ya dauka ya nufi gidan Yakubu ya dauki doki ya bazama filin sukuwa yayi ta zagaye, ba ji, ba gani, saboda damuwa. Ba shi yasan halin da yake ciki ba, sai da ya ji shi cikin ciyayi yana birgima. Yayi lamo kamar ya mutu. Wasu mutane 2 suka dago shi suna tambaya,"Ba ka ji ciwo ba? Ya mike ya na fadin,"Ban ji, ba na gode." Ya kar6i akalar dokinsa a hannun su, ya taka ya haye, nufi Tudun Jukun. Karfe 10 saura kwata, yake fakin, ya shigo gidan yana fargabar me zai shiga ya ji? Yana yin sallama kuwa. Umma ta kwala masa kira. Ya nufi gunta ajikinsa a sanyaye,"Ga ni Umma."Ta ce,"Nusaiba barci har tara da rabi, da kyar muka tashe ta ni da Zarah. Wane irin barci ne haka, yarinya bata ko iya tsayuwa? Ya zaro ido, ya ce,"Ina take yanzu? Ta ce,"Tana daki, ta ce kanta ma ciwo yake yi, shine na ce ko asibiti za ka kai ta? Ya wuce da sauri, yana shiga falo yayi karo da Zarah ta fito kicin,"Yayanmu, barcin amarya yau ya ba mu tsoro, kamar wacce ta sha wani abu? Tana nan kai na faman ciwo." Tana daki ne? Tana nan akwance." Ya wuce dakin, ya bude ya shiga. Tana kwance Idanuwan ta rufe, ya tsaya kan ta yayi kira,"Ke! Ki tashi aka ce a kai ki asibiti." Ta bude ido jazur, ta dube shi, wani sabon takaici ya lullube ta, hawaye suka cika idanuwanta fal, ta ce,"Na sha magani, ya daina." Umma ta ce,"A kai ki asibiti, ta so mu tafi mana." Tayi shiru tunani ya rufe ta, bata ta6a zaton Naseeer yana kin ta haka ba, sai yanzu ta tabbatar da bata da makiyi kamar sa. Shi yasa tunda ta wartsake, ta tantace halin da take ciki, ita ma ta fara tsanar sa, irin wanda bata ta6a ji ba. Tayi kuka cikin bayi, ta kuma roki Allah yayi mata sakayya, idan har akwai cutarwa a cikin abinda Naseer ya yai mata. Yayi sauri ya kauda kai, jikinsa ya k'ara la'asar. Ya kama hanya da sauri zai bar dakin. Zarah ta kawo kai." Asibitin za ku? Ya ce," Ta ce bata zuwa." Saboda me? Ta wuce gun ta, "Amarya! Me yasa? Ta goge kwalla ta ce,"Na sha Panadol Antina." Ta ce,"Ai yanayin barcin da ki ka yi ba'a gane masa ba, shi yasa Umma ta ce ki zo a kai ki."Tayi shiru bata da niyyar tashi. Can ta jiyo muryar Umma,"Ina Nusaibar? Nan da nan ta sakko daga gado, ko kafin Umma ta karaso cikin dakin, ta dauko hijabi. Ya ce,"Kin ce ba za ki ba?" Za ni Umma, hijabi zan sa." To ki je yana jiran ki a mota." Suka fito Zara ta rako ta bakin kofar gida. Ta shiga mota. Suka tafi, babu mai yi wa wani magana. Sun iso cikin asibitin. Nusaiba fa ta kafe ta ki fitowa daga mota. Yadda bai ce mata fito ba, haka ita ma bata motsa ba daga inda ta ke zaune ba. Haushi ya kume shi, yana ganin kamar tana son ya rarrashe ta ne." "Lallai yarinyar nan ta raina ni." Hannu yasa ya zaro wayarsa, ya danna (Ear piece) yana jin gindan Rediyon (Queen FM). Ga hotunan Ameer yana kallo hankalin sa kwance. Kusan minti 30 suna zaune, ita ji take kamar ta fice daga motar tayi tsuntsuwa ta ganta gidan iyayen ta. Da ya ga abin na ta da gaske ne, sai ta buga tsaki. Shi take 6ata wa lokac, sai ya buga tsaki yayi wa mota key, ya figeta a guje. Yana yin fakin kofar gida, ta bude ta fito ta shige cikin gida. Ya bi ta da kallo, kafin ya ce aran sa,"Duk su Zarah su ja siyo min raini." Yayi tsaki ya fito ya shiga ciki. Suna tare da su Umma suna tambayar ta yadda aka yi? Yana isowa, tana fadin,"Babu komai Umma, dama maganin barci na sha, don un sami barci, ashe ya fi k'arfin jini na, amma Likita ya ce ba komai zai sake ni." Umma ta ce,"Ai shi ke nan, sai ku kiyaye shan maganunguna haka kawai. Don Allah kar ki sake, kin ji? Ta ce,"To Umma." Yinin nan guda, bata iya cin abincin kirki ba. Saboda tsabar tunanin kaddarar da Allah ya sauko mata. Washegari ta tambaye shi zuwa Kaduna.." A dawo lafiya." Ya ce da ita. Da kan ta ta tuka motar ta tafi.."Can ta wuni tare da Umman ta, suna hira ta ji dan sanyi a ranta. Kamar kar ta dawo ta rink'a ji, shi yasa ta rink'a nuk'u-nuk'u. Yamma tayi sosai. Abban ta kuwa ya ce ba za ta kwanan ba. Direba yasa, ya ja mata motar ya dawo da ita. Shi ya koma a ta haya. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Sannu a hankali Zarah tayi arba in. Kodayaushe Ameer na wajen Nusaiba, ita ke masa komai, ta shaku da shi sosai, kuma tana son Yaron, duk da irin cin kashin da Baban sa yake mata. Wanda har yanzu abinda yai mata, yana cikin ranta. Ta sa ido ta ga ko zai sake kwantawa, amma baiyi gigin k'arawa ba, saboda shima al'amarin ya dan sanya shi nadama, bata dai isa ya nuna mata ba, balle ya bada hakuri. Saboda haka suka ci gaba da zaman da suka saba tuntuni. Kwanan Ameer 50 dai-dai, yayi wayo ya kumua shiga ran kowa. Da asuba Zarah ta farka tana mamakin irin barcin da tayi. Lallai Ameer ya sha kuka, bata ji ba. Domin tayi tunanin tun lokacin da ta bashi nono take barci. Tausayin shi ya kamata, ta tashi ta dauki shi. Kara bude ido tayi sosai, don sai taga kamar. Gaba daya jikin sa ya sandare Tsoro ya kamata, jikinta ya dauki rawa ta dan girgiza shi, ina rai ya riga yayi halinsa, da sauri ta diro daga gado tare da shi ta nufi kofar dakin Naseer ta bubbuga, ya fito ya bude mata. "Duba Yaron nan ka gani ko motsi ba yayi. "Inna-lillahi"wa-Inna-ilaihir-raji'un! Haka yake ta faman fadi yana girgiza shi. Tuni Nusaiba ta ji, sai ga ta a gigice. Naseer yayi waje da shi, suka biyo bayan sa, suka dunguma sasan su Umma. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 2-04 Posted by ANaM Dorayi on 08:19 PM, 20-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ Abba ya kar6e shi, ya rungume a jikin sa ya ce,"Ku yi hakuri. Allah ya kar6i abin sa." Nusaiba ta sulale nan hawaye suka tsinke mata. Zarah kuwa dakin ta ta koma ta zauna bakin gado tana sallallami. Shi kuwa Naseer kafewa yayi kai da fata aje asibiti a duba masa Yaro, k'ila suma yayi. Ya dube shi ya ce,"Hakuri fa za ku yi Naseer, wannan yaron ya riga ya rasu, babu abinda za'a iya yi masa. Kujera ya zauna dabbas! Idanuwansa suka bushe kamas! Kirjinsa na bugawa. Abba ne ya iya gayawa duk wanda ya kamata ya sani. Nan da nan jama'a suka taru. Umma tayi masa wanka, aka shirya shi,

Chapter 5 of 6