Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
ce,"Ni ma na shiga, ina ta sallama, na ji shiru. Ya jikin na sa? Na gan shi a k'asa ne." Duk suka zauna suka sanya shi tsakiya. Zarah na fadin,"Ni ma na shigo, na gan shi zaune ana. Wai ya gaji da kwanciya." Ai da gajiya, kwanciyar." Koma yau da bango ya jingina, ya rufe ido. Ta ce,"Sannu." Da kai ya amsa. Ta mike ta dauko filo, ta tsugunna gabansa,"Dan daga in sa maka filo, zai fi maka dadi." Yayi shiru kamar ba i ji ba.Yayin da Nusaiba ke fadin,"Shi ke nan gara da ka sa baki. Da su Antina za'ayi min wayau." Ya kalle ta a dage ya ce,"Kyale ta kawai, tashi ki tafi abin ki." Ta kuwa mike za ta wuce, Zarah ta rikota,"Wai sai ki tafin kuwa? Ta ce,"Me zan jira Antina? Ai na yi ma ku hira, yakamata in je in barci." Karfe 9?" "Eh mana. A kwanta da wuri, a tashi da wuri." Fuska yamute ya ce,"Don Allah ki kyale ta, ta wuce mutun na jin barci a hana shi? Tana can tana kallon Naseer, ya 6ata rai ba sauki, Nusaiba ta zame hannunta,"Allah ya ba mu alkhairi. Yayanmu Allah ya karo sauki." Amin." Ya fada a fizge. Ita kuwa Zarah ta kasa ma motsi tayi. Tana kallo Nusaiba ta bar dakin. Dariya ya kamayi, ganin yadda Zarah tayi sukuiti duk jikinta ya mace." Ta nuna shi da yatsa ta ce,"Ka daina sa mana baki idan muna magana." Fuskar ta kunshe da shagwa6a. Dariya ya ci gaba da yi mata. Suka ci gaba da hira. Karfe 11 da kyar ya bar ta ta koma dakin ta, ta yo shirin barci ta kulle dakinta, ta dawo wajen sa. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Bayan kwana 2. Nusaiba ta kar6i girki, a ranar kuwa gidan cike yake da baki da 'yan dubiya har da iyayen su. Tare suka hada suka yi girke-girken abincin su kuma tare suka ji ta kula da bakin su.Kamar yadda suka saba gwanin sha'awa. Zarah ta gaji tu6us! Don haka tana yin ishha'i, tayi wanka ba ta jira komai ba, ta bi lafiyar shimfidadden gadon ta, babu 6ata lokaci, barci ya sace ta. Nusaiba kuwa bayan ta gama shirin ta, sashin Zarah ta soma zuwa, kofar falon na garkame. Ta tsaya kame da ha6a,"Ba dai hat Antina tayi barci ba? Lallai Antina." Ta jinjina kai ta wuce wajen Mai-gidan. Yana kwance, gaba daya dakin yayi masa bakikirin. Babu abinda yake tunani illah Zarah, abinda ke 6ata masa rai kuwa, yai ba ita zai gani a dakin sa ba. Ko sallamar ta bai iya amsawa ba. Ta zauna gefen gadon, tana fadin,"Ka san wani abu? Wai Antina har tayi barci." Ya baki taso ta ba? Ta kulle kofar falon ma Ya ce,"Yayi mata dai- dai. Daga nan bai sake cewa komai ba, nan ya bar ta zaune, a zaton ta ma barci ne ya sace shi. Yana jin ta, ta rufe shi, sannan ya kwanta, sai da tayi barci, ya jawo filon sa, yasa kasa ya dawo nan ya kwanta. Karfe 2 dare, ta farka, don yin sallar dare. Can ta hango shi bisa kafet Mamaki ya kamata. Ta sakko ta tsaya kan sa tana kallo. Kamar ta tashe shi, wata zuciya ta ce ma ta kila ya fi son kwanciyar kasa ne. Don haka ta wuce bayi, ta kama ruwa, ta yi alwala ta fito. Motsin ta ya farkar da shi barci, amma san bai bari ta gane ba. Ta daura zani, ta dora hijabi ta haye sallaya ta fara sallah. Shi kan sa ta burge shi, da zai fadi gaskiya. Ta jima bisa sallaya tana addu."a kafin ta mike, ta nufo gunsa ta tsugunna. Yadda ya kwanta a yaye babu lullubi, sai ta ga kamar sanyi yake ji, don haka ta mika hannu ta janyo bargo ta sake lullube shi. Ta koma gado tayi kwanciyar ta. Naseer yayi shiru ya rasa me yake sakawa a zuciyar sa. Har asuba bai koma barci ba, haka kuma bai daina sake-saken iska ba cikin ransa ba. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Tsawon wata 1, Naseer yana samun kulawa wajen amaransa da wacce yake so da wacce bai damu da kulawar ta ba. A son ra'ayin sa ko sannu baya buk'ata daga gare ta, shi yasa kullum yake jin sa kamar bisa k'aya cikin gidan nan. Kuma bai san dalilin da yasa kodayaushe k'ara tsanar Nusaiba yake yi ba, duk da bajintar da suke nuna masa ita da iyayen ta. Wani lokaci har tsoron zuciyar sa yake ji, ta yadda ko alama ta k'i amsar Nusaiba. Hannun sa yayi sauki sosai, domin har ya kan fita ya je wajen iyayen sa, ya gaishe su. Bai ta6a shiga sabuwar kerarriyar Jeep din sa ba, wace Alhj ya sake masa, sai da Zarah ta goranta masa. Shagon dinkin Sageer ya iso yayi fakin ya fito duk jama'ar wajen idanuwan su akn sa. Idan ka dube shi sai ka rantse da Allah wani hanshakain dan kasuwa ne. Gaisuwa jama'ar wurin ya rinka amsawa, sannan yayi sallama shagon. "Allah ya kiyaye min na Zarah, angon Nusaiba." Ya wuce shi ya zauna a kujera. Sauran yaran shagon suka gaishe shi da jiki, ya amsa. Sageer ya biyo shi, shi ma ya zauna kujerar gefen sa ya ce,"Duk na zura ido in ga wa zai fito daga wannan shimfidediyar mota, ashe Alhaji na ne, ka gan ka kuwa?Ai za'a ce ka ba wata biliyan dari baya mutumina." Ya ce,"Ka bari kawai, ni kai na tsoron gidan nan na ke yi da motar nan. Zarah ce ta matsa min na kinkimota." Yayi dan murmushi ya ce,"Arziki. Kashi Naseer, ka riga ka tako kuma kowa yana da hanyar da Allah ya shiryo masa inda zai sami abincinsa. Allah ya kara hada mu da masoyan mu." Ya dan nisa kafin ya ce,"Yanzu tsakanin ka da Allah ba ka min kallon auran jari na yi? Kyar Sageer ke kallon sa,"Me yasa kai ka cika tsarguwa ne? To idan ma auran jarin ka yi, ina ruwan mutum? Ina cewa shi ma mu2m ya sami damar yin hakan, sannan zai yi? Naseer, ba auran jariba, ko auran damfara ka yi, babu ruwan ka da mutane kowa ta shi ta fishshe shi. Abinda Allah ke duba ita ce zuciya, shi yasa ake so a kodayuashe ta kasance tsarkakkiya." Ya dan yi hucin zafi ya ce,"Na fahimce ka, amma kar ka manta ba kowa ke da irin tunanin ka ba. Ni kuma na tsani zargi, ina fitowa motar nan kowa sai kallo na yake yi, har da gaisuwar gulma, dole in na shiga wannan, ayi magana ta. Ka san ban da hakuru, idan na ji ba za'a kwashe ta dadi ba, komai gemun mu2m." Ya dan bubbuga kafadar sa, yana dan murmushi,"Allah ya ki yaye min angon amare, hakan ma ba za ta kasance ba. Insha-Allahu. Ai yanzu ka wuce da ajin fada, sai dai ka yi rabon na 'ya'ya a cikin gida ko ba haka ba? Wani dan bazawarin murmushi yayi ya ce,"Aje wannan maganar, ka san ina son yara, kar ka tada min kwadayin su." Ko?" Sageer ya tambaya, ido waje. Ya ce, "Ah? To mece ce ribar auran?, Ita Zarah ma ta ki fara laulayi, sai ja min rai take yi." Sageer ya fashe da dariya suka tafa. Sannan ya nuna shi,"Zarah kadai? Har da amarya, lokaci guda za su zazzage ma tagwaye." Take nan ya sauya wani shafin." Ka san wani abu? Na kusan fara zuwa koyon dinki, jira na ke hannu na ya gama warkewa." Baki sake yake kallon sa."Ina son ka ranar yanko zance, babu seti. Mutumin da hidiman karatu ke gaban sa, ga fita wasanni, yaushe za ka sami lokacin zama nan? Lallai za ka sha mamaki, kai ba ka na karatun ba, ka rinka koyon dinkin? Ya ce,"Ai na ma riga na sha mamakin. To wai me yasa ka ke son koyon dinkin yanzu?" "Ra'ayi na ne ya sauya, yanzu kuma dinkin na ke so." 'Yar dariya Sageer yayi,"Allah ya nuna mana lokacin." Ya ce ,"Amin. Ya dan jima nan suna ta hira, sannan ya je ya gaida Umma. Abba ya riga ya fita kasuwa. Daga can gida su Zarah ya nufa, suka sha hira da Innar sa. Haka yayi ta yawon sa a gari, ba shi nan, ba shi can. Saboda yasan Nusaiba ke da girki, bai koma gida ba, sai gab da Sallar magariba. Suna zaune a falo, kowacce ta tsala don mamaki. Yayi sallama ya shigo, suka amsa dauke da fara'a, sannan suka yi masa sannu da zuwa. Idon sa akan Zarah yake amsawa. Kan sa tsaye ya wuce kujerar da take, ya zauna bisa hannun kujerar, yayin da take fadin. "Haba yayanmu, kuma tun safe har magariba ba'a ko waiwayen gida? Haka ake yi? Kawai yadda take motsa bakinya, shi ya tsura wa ido,, yake kallo. Nusaiba ta ce,"Ai ni ban ma san abinda zance ba Antina." Ya dan lumshe ido kadan, ya bude su, kafin ya ce, "Na yi laifi kenan? Ta ce,"Tambaya ma ka ke? Kodayake babu ruwana, tsakanin ka da amaryar ne. Aron bakin ta na yi, na ci mata albasa. Bari na yi haramar sallah." Ta mike za ta wuce, yayi wuf ya cafke hannunta. Adon ta kawai ke kidima shi, tayi masifar kyau,(Material) din ya amshi jikinta sosai." Ta waigo a firgece, ta rasa ma me za ta ce?" Zo in ji warin albasar da ki ka ara ki ka ci." Ta dubi Nusaiba da ke kallon su, tana dariya ta ce,"Au dariya ma ki ke yi, ba za ki kwace ni ba, ki na kallo zai kar ya ni." Ta gintse dariyar ta ce,"Duk zan iya jinyar ku." Ya janyo ta, ta fada da karfi ta dawo inda ta tashi ta sake zama. Ya matso ta sosai, ya ce,"Haba Fati na,, daga shigowa ta kuma sai ki tashi, don me? Ta dan kalle shi a karkace ta ce,"Sallah zanyi,ga ta can ana kira." Ba ta jira komai ba, ta shammace shi, ta wuce." "Zarah! Ya kira ta, ta waigo. Yayi dan jim yana kallon ta, kafin ya ce,"Kin yi kyau." Ta dan kama kugu, ta sauke numfashi ta dubi Nusaiba,"Kin ji abinda ya ce? To kar ki yarda ya kallame ki, sai ya gaya miki inda ya je ya ki dawowa ya ci abincin rana. Ni babu ruwa na." Ta wuce, ta bar Nusaiba na murmushi. Shi kuwa ita ya bi da kallo har ta shige sashin ta. Ya ja gajeran tsaki, wani kullutu ya tsaya masa a wuya. Ga wacce yake so ya sakata ya wala da ita, ance ba haka ba. Mutane na ganin auran gata aka yi masa. Ina gatan? Bayan rayuwar sa na cikin kunci, bai da walwala ko alama. Can cikin tunanin sa, ya ji kamar Nusaiba na kunkuni. Ya daga ido har sun fara ja, saboda damuwa, ya ce,"Mene ne? Ta ce,"Sannu da zuwa na ce." Ya dai amsa ne kawai, amma bai ga dalilin sake yi masa sannu da zuwa ba, bayan sun yi masa tun shigowar sa. Ta ce,"Shiru ka ki dawowa, muna ta tararrabi, duk da dai abincin ba cinsa ka ke sosai ba, ai da dadi ka dan dawo mu gan ka ko saboda yanayin jikin ka."Yayi shiru yana dubanta, sanaben da take yi, shi ya sa shi 'yar dariya. Ya gyada kai,"Yaro man kaza." Ya fada a ran sa. Ta ce,"Dariya ma na sa ka? "Na dai sa kai na, ai kin san ba za ki iya sa ni dariya ba. Ko za ki iya? Ta kada kai,"Wace ni, amma kasan bai kamata ka rinka dogon yawo ba ko? Ya ce, "Na daina Hajiyar. Zan iya zuwa in yi sallah? Tayi dan murmushi, ta ce,"Ruga da gudu, ka yi sallah, ina nan zuwa da kayan abinci." Kya ci abinki." Ya wuce yana fadi a ran sa. Ta bi shi da kallo, yanzu kam ta yarda son Naseer ya fara shiga ranta, sai bata san abinda ke damun sa ba, ba baya sakin jiki da ita sosai ba. Ta sauke numfashi ita ma ta tashi. Ya dade da yin barci tsakar daki bisa lallausar kafet, lokacin daya ji ana kwankwasa kofar dakin ya farka firgigi, ya dubi agogo karfe 4 saura kwata na asuba. Tuni Nusaiba ma ta tashi zaune bisa gado, tana tambaya,"Waye? Bai amsa ta ba, ya wuce kofa yana fadin ,"Zarah! Menene? A lokaci guda yana bude kofar. Me zai gani? Wasu Samudawa ne majiya karfi cikin shigar bakaken kaya, tun daga bisa kan su har kafafuwa, ba ka ganin komai, sai kwayar ido. Sun tado Zarah da bakin bindiga. Ko kafin ya gama shan mamaki, sun hada da Zarah da kofa tare da shu sun bankado su tsakar dakin." Ganin haka yasa Nusaiba ta aza hannu bisa kai, ta kwarara salati mai karfin gaske! Bata karasa ba, wani daga cikin su ya kwashe ta da mari. Ya daka mata tsawa,"Shutu.! Ta rarrafa da gudu ta kwakumi Zarah, suka dunkule waje daya, bakinta na ta tsato jini. Naseer ya bi su da kallo ya ce,"Me ku ke so? Wanda ya fi kowa rashin imani ya dubi hannun Naseer da ke rataye a wuyansa, yasa kwafcecen takalmin da ke kafar sa, ya togar hannun, sannan ya aje kafar bisa hannun ya murza son ran sa.Daga yadda Naseer ya ji yanayin hannun, ya tabatar da babu makawa ya sake karyewa. Amma saboda taurin ran sa, ko kara bai yi ba, ya sake cira kai ya dubi wanda yayi dakali da hannun sa, ya ce,"Menene abin duka bawan Allah? Ina cewa abinda na ke da shi, su zan ba ku? Magana ta gaskiya, kun yi rashin sa'a ban da komai gaba daya cikin kudina cikin gidana na dubu talatin ne, suna cikin jakar can, ku je ku dauka." Ya maka masa kasan bindiga ya ce,"karyaKi na yi segiya, ina kudi? "Abinda na ke da shi na gaya maku." Baba tausayi ya shiga tafka masa takalmi. Nusaiba tayi karfin hali, ta durkusa hawaye na zuba murya na rawa ta ce,"Don Allah ku yi hakuri, ku daina dukan sa, muna da gwalagwalai masu yawa da tsada, akwai wayoyi kuma a waje na. Akwai dubu hamsin, duk zan hada ma ku. Don Allah ku kyale shi, ba shi da lafiya. Zarah kuwa kamar ta mutu, ko numfashin kirki bata iya yi. Take nan ogan ya hada su da yara 2, kowacce aka rakata dakin ta, ta hado duk abinda take da shi. A wajen Zarah ma an sami dubu goma ragowar sadakin ta da Malam Umar ya ce dole sai ta kar6a. Amma gwalagwalan Nusaiba iyaka ne, domin a cikin su akwai na dubu dari biyu da hamsin. Ganin su ne ma yasa ogan 6arayi ya kyale Naseer, ba don haka ba da sai ya kwashi kashin sa a hannu. A ce gida kamar wannan, ya 6ata lokacin sa ya shigo bai sami komai ba? Dole kuwa ya debo rabon sa a jikin Mai-gidan. Amma duk da haka warwas suka bar Naseer. Matansa suka tarairayo shi. Sai a lokacin yaje jin kansa kamar ba a jkin sa yake, shi yasa ma ya kasa tashi tsawon lokaci. In ban da kuka babu abinda su Zarah ke yi, shi kuwa fadi yake,"Hasbinallahu-wani-imal-wakil........ Wasa-wasa fa Naseer ya kasa motsi, abin ya kara firgita matansa. Nusaiba ta bazama falo ta nufi gefen da wayar gida take (Land-line) jikin ta na rawa ido na tsiyaya, ta nemi lambobbin gidan su a Kaduna. Hankali tashe Alhj Basheer ya dauka, don ya tabbatar da babu lafiya, wannan waya karfe 4 da rabi." "Hello." Muryar Nusaiba ya ji cikin kuka yana fadin. "Abba na! B'arayi sun ku san kashe Naseer, ga shi can kwance, ya ka sa motsi! Gabansa ya yanke ya fadi, ya dauki salati, bakin sa na rawa kafin ya ce,"Harbin sa suka yi? Ta ce,"A'a tsabar duka ne Abba na. Don Allah ku taimake mu, sun kwace komai, har wayoyin mu balle in kira wasu anan. Ya ce,"Ku kwantar da hankalin ku, kin ji? Zan kira Abban sa, ni ma ina tafe Insha-Allahu. Ina Zarah take? Ita ma lafiya ko? Ta amsa,"Eh tana can wajen sa." To shi kenan, ki koma ku natsu, kin ji? Ta ce,"To." Ta aje waya tana share hawaye, ta koma dakin ta gaya wa Zarah ta kira Abbanta. Suna nan zaune, sun ta sa yayan na su, sun rasa abinda za su yi masa, kan sa na bisa cinyoyin Zarah. Ya bude ido da kyau, ya ce,"Mai gadi ya shigo kuwa? Suka girgiza kai a tare, suka amsa,"Bai shigo ba." "Ko sun kashe shi ne? Ya kara firgita su. Nusaiba ta mike,,"Bari in dubo shi." Ta mike Zarah ta riko ta,"Yanzu ke sai ki fita? Yana daga kwance ya zura mata ido ya ce,"Lallai ke ba ki da hankali, to fita, su kashe ki ke ma. Ba ta ce komai ba, ta dawo ta zauna. Amma a son ranta da sun kyale ta fita za ta yi, ta dubo lafiyar Mai-gadin su. Tunda ba su ga ya shigo ba, bayan fitar 6arayin, tabbas akwai dalili. Wani sabon tausayin su ya sake rufe ta. Nan da nan hawaye suka tsinke. Nusaiba akwai tausayi, sam-sam bata son ta ga mutum cikin wani yanayi na rashin jin dadi, gaba daya hankalin ta tashi yake yi. Tun daga Kaduna Alh.Basheer ya debo 'Yan sanda mota 1, motar sa na gaba, suna bin sa a baya. Hajiya Zulai tayi shiru tallafe da kuncu bata tunanin komai, illa tausayin sirikin ta. Allah ya sakko masa da jarabci kufi da kufi. .Tayi ajiyar zuciya, ta ce,"Allah ka mayar masa da alkhairi." Alh.Basheer ya ce,"Amin dai, wannan Yaro ai sai an mike masa tsaye da addu'a. Domin ina ji masa tsoron mahassada." Ta ce,"Kai dai bari. Allah abin tsoro,mutum abin tsoro. Ubangiji ya raba mu da kowanne irin sharri." Ya sake fadin Amin. Cikin mintoci 45 suka iso Zariya. Gidan su Abba suka fara wucewa, suka dauko su kamar yadda Alh. ya ce su jira shi, yana tafe da "'Yan sanda. Gari ya fara shaa! Zai waye, suna iso wa (Hanwa Low-coast). Get din gidan na bude, shigewa kawai suka yi. Tun daga nan 'Yan sanda suka fara ganin shaida, domin kuwa Mai- gadi na daddaure, an like bakinsa banda dan banzan dukan da ya sha na fitar hankali. A bakin kofar falo, suka ci karo da su Zarah, wani sabon kuka suka fashe da shi. Gaba dayan su, su Ummi suka rungume suna rarrashi, sannan suka dunguma inda Naseer yake, yana kwance gefen idon sa ya kumbura sumtum! Wajen da aka buga masa kan bindiga. Sallallami kowa ke yi. Su Abba suka tarairayo shi, ya na fadin," "Sun k'ara karya ni Abba. Sai an sake min dori." Babu 6ata lokaci suka sa shi a mota zuwa gidan dori, suka bar 'yan sanda na yi wa matansa tambayoyi. Shi kan sa Mai-gadi tare da shi suka tafi, aka ja masa targade 3 ajikinsa. Daga can suka kai su asibiti, don samun magunguna. Karfe 10 na safiya suka dawo. Gida ya cika. Inna ta dubi Naseer, duk ya muzanta, ya sauya kamanni. Hawaye fal ya cika idanuwan ta, ta ce,"Wannan Yaro ka na ganin tashin hankali. Allah ka yaye mana masifa." Duk saura suka ce Amin. Kowa ya ga Naseer yadda ya galabaita, sai ya tausaya masa. Haka Sageer da Yakubu suka yi shiru, suna masa duban tausayi. Naseer B kuwa fadi yake cikin ransa,"Ba shi fafa ba? Ya wani fito da mota mai nishi, yana kece raini a gari. Ba dole 6arayi su biyo shi ba. Ai ga irin ta nan. Allah sarki, ko alama Naseer B bai yi wa takwaransa halacci ba. Da Naseer zai gane daya tabbar da cewa lallai ba k'aramin sa'a yayi ba a rayuwa, tunda har Allah yayi masa baiwar da wani yake kallo, yana masa hassada." Bayan sallar azahar iyayen su suka koma gidajen su. Alh.Basheer kam ya kara jaddadawa Malam Balarabe maganar nemar wa Naseer taimakon addu'a. Malam Balarabe, ya san yana yi masa cikin sallolin sa , farilla da nafila, amma duk da haka, ya amsa wa Alh. Basheer da lallai za su kara kaimi shi da Umman sa. Shi kuwa Naseer bayan tafiyar kowa, yana zaune bisa Canis kafet. Falo jingine da kujera. Su Zarah na kicin suna wanke-wanke. Ya kwala mata kira ta zo. Ya dube ta fuska daure, ya ce,"Ki je maza daki, duk abinda ki ka san nawa ne, ki zuba min a jaka. Ke ma ki hada da na ki kayan za mu koma Tudun Wada? "Saboda me? "Saboda ra'ayina can ya koma. Ta kada kai, "A'a yayana, 6arayi sun firgita ka, kawai za ka ce. Amma ni ban ga dalilin komawar mu Tudun Wada ba." Haushi ya kama shi ya ce, "Eh haka ne, koma me za ki ce. Za ki je ki hada min kayan, ko in tashi da kai na? Ta kwala wa Nusaiba kira, ya 6allo mata harara ya ce,"Ke na ce ki hado kaya, ina ruwan ki da ita? Bata tanka masa ba har Nusaiba ta iso,"Menene Antina? Ta ce,"Ki zo ta mu ta same mu. Yayanmu ya ce mu hada kayan mu Tudun Wada za mu koma." Saboda me? Kafin ta ba amsa. Naseer ya yi kukan kura ya tashi ya bar falon. Suka bi juna da kallo, kafin Nusaiba ta matso kusa da Zarah, ta ce,"Me ya faru Antina? Fuska yamutse ta amsa, "Ooho, amma zai wuce maganar 6arayin nan ne? Ni ma shi na gani, zo dai mu je mu same shi."Cikin daki Naseer ke ta hada kayansa da hannun daya, cikin jaka. Gaban sa suka tsaya Zarah ta fara cewa,"Yanzu yayanmu da gaske ka ke yi? Ai da ka san haka ne, sai ka tada maganar a gaban su Abba ka ji me za su ce? Ya ce,"Kuma shi kenan ba ni da wani ra'ayi nawa, komai sai an takura ni? Ba zai yuwu ba, kin gane ko? Ke ba ki da wata hujjar ma da za ki ce ba za ki koma Tudun Wada ba. Gara wannan ita nan gidan Babanta ne, ko bata biyo mu ba, tana da hujja. Idan kuma duk anan za ku zauna, ba matsala, na gama magana, kar wace ta sake yi min wata." Ya suri jaka yayi waje. Su kuwa sansarai suka tsaya suna kallon ikon Allah, duk jikin su yayi sanyi, ba ma kamar Nusaiba, domin kalaman Naseer ba su yi mata dadi ba. Hawaye suka cika idon ta, ta dubi Zarah ta ce,"Antuna, me yasa yayan mu ke fadar wannan maganar ko gidan Baba na ne, zaman wa na ke yi a cikinsa? Hasalima Abba na bai ce ni ya ba gida ba." Zara ta kamo ta cike da tausayi, ta ce,"Kar kiyi kuma amarya. Ba wani dalili yasa yayan mu wannan abin ba, illa firgici 6acin rai." Ta ce,"Amma ai mu yakamata ace mun shiga wannan halin ba shi ba." Koma dai menene, ki manta kawai amarya, yanzu menene abin yi? Ta ce,"Abin yi bai wuce mu bi shi ba, duk abinda Abbansa ya ce, shi za'ayi ko? Shi kenan, je ki hado 'yan kayan bukata, mu tafi."Kowacce ta nufi dakin ta. Nusaiba kam jikinta a salibe yake akan maganganun Naseer, musamman da ta tuna da hudubar Abbanta kafin a kawo ta gidan miji: "Nusaiba, babu abinda za ki yi a rayuwar ki gaba daya a halin yanzu, wanda ya fi biyayya ga mijin ki. Ki sani da Ummanki da ni Alh.Basheer, ba mu da ikon komai a kanki, saboda girman darajar aure. Sai abinda mijinki ya hukunta akanki. Saboda haka Nusaiba kar ki dauki aure da wasa, ki yi amfani da ilimin ki, domin a yanzu ne yake da amfani a gare ki. Magana ta gaba wacce na ke son gaya miki, ita ce, koda wasa ban lamunce miki yin wata magana akan abubuwan da na mallaka wa Zarah da mijinku ba. Ina nufin gori, da babbar murya na ke miki wannan maganar. Duk ranar da ki ka gorantawa daya daga cikinsu, ban yafe miki ba, domin kin watsar da mutuncin ki, kuma kin rusa tarbiyar da muka baki. Ba kuma sai na gaya miki ba, kin san matsayin matar da ta yi wa mijinta gor.......... Ta share hawaye, ta zage zif din jaka, tana fadi a ranta,"Har abada ba zan baka kunya ba,"Abbana." Muryar Zarah ta jiyo tana fadin,"Amarya kin gama? Ta amsa, Eh. Suka kwaso kayan bukata, suka kulle ko'ina, suka fito. A zaton su Naseer na waje, yana jiran su, tunda ba su ji tashin mota ba. Ashe shi tunda ya fito, ya tako ya tsare aca6a, ya haye yayi tafiyar sa. Mai-gadi ke gaya ma su tuni ya fice. Kallun juna suke yi baki sake. Dole Nusaiba ta koma ta dauko makullan motar ta, ta ja suka bi shi. Ita Zarah ta san rigimar Naseer, shi yasa, ma abin bai dame ta ba. Nusaiba kuwa abin 2 ya hade mata, damuwar da Naseer ya shiga, ga kuma maganganunsa, ba su yi mata dadi ba. Sannu a hankaki Zarah ke ta warware mata kullin zuciyar ta, ta hanyar dibar ta da labaran wasu abubuwan da Naseer din yayi na jarunta. Al'amarin kuma ya koma daure mata kai. Ta saki waccan maganar, ta koma tana tambayar kan ta, me yasa yau ya tashi hankalinsa haka akan 6arayi? Zarah ma oho ta ce, shi yasa har suka iso kan ta na daure. Suka yi sallama cikin gidan dauke da jakunkunan su. Umma ta fito ta tar6e su,"Ku shiga yana nan falo. Ko kunya bai ji, wai ya taho ya baro ku can. Naseer ai baya gajiya da abin fad'i. Yana zaune gaban Abba suka zube suka yi gaisuwa. Malam Balarabe ya dube shi, ya nuna su "Yanzu ba ka ji kunya ba? Koma menene, ai sai ka hado matan ka ku tahu tare, kai dai kullum bahagon mu2m ka ke. ba ka sauyawa. Wai ma in tambaye ka, me ka ke nufi da kun baro can? Rai 6ace ya ce,"Ni fa gaskiya Abba ba zan zauna gidan nan ba. B'arayi na ganin bangajejen gidan suna shigowa ba sa mun komai, wata rana kashe ni za su yi, kar fa ka mance Abba ni fa ba mai kudi bane, rufin asiri ne kawai. Saboda haka nan zamu zauna, idan ina son asirina ya kara rufawa.Malam Balarabe yayi dan shiru, saboda Naseer yana da dalilai masu karfi. Can ya dan nisa ya ce,"To ka gaya wa Alhj ko? Ya kada kai,"Ban gaya masa ba." Umma ta amsa,"Ka ji matsalar ka, tunda ya zo yakamata ka yi maganar nan a gabansa, amma ka ki, me zai ce? Malama, ni ban goyi bayan zaman su anan ba. Su koma. Ya kira Alhjn a waya, ya gaya masa tukuna." Ran Naseer ya k'ara 6aci, ya zuba wa Ummansa ido, tunanin sa kuwa, shi kenan kuma yanzu ba shi da wani ra'ayi, sai abinda Alhj ya ce, ya runtse ido, ya cije le6e,"Na shiga uku. Alhj ya mallake min iyaye. Ya fada cikin ran sa. Ya bude ido, ya dubi Umma,"Gaskiya Umma, sai dai ki yafe min, na riga na

Chapter 3 of 6