Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Ajininsa yake 2-01 Posted by ANaM Dorayi on 11:39 PM, 11-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . .Gaba daya tsarguwa ta kama shi, dole ya sake kallonta, ya kirkiro murmushin karfin hali yace " an dawo lafiya? tace "lafiya lau" shiru ya sake yi yana tunanin me kuma zai sake cewa? ji yayi tace " Ya wasan Polo? ya dan dube ta ya amsa, " muna dan tabawa." Abba ya ce yayi sabon Jah- Jah, shine ya-ce har Yakubu ya tsufa ne? yayi dan Murmushi yace ai komai lokaci ne, mu ma wata rana daina yayin mu za'a yi." ta ce "Gaskiya ne. To ya antin tawa? Ya amsa "Tana gaishe ki." "Ina amssawa." Tayi shiru kamar yadda shima bai kara cewa komai ba. Wayar sa ta hau ruri, ya jawo ta ya duba. Nan da nan ya dauka, "Hurul aini." Da sauri ta daga ido ta dube shi yayin da ya ci gaba da fadi" An dawo school din ne? Ta ce na dawo, to yaya? Ya-ce "Muna tare da ita." "Ban yarda ba". Ya ce kin san ba zan miki karya ba. Shi yasa ma tun jiyan na kira ki na gaya miki." Ta ce in da gaske ne, ban ita mu gaisa.' Kai tsaye ya dubi Nusaiba, ko dama shi take kallo, kuma sai taji kamar kishi zai kamata. Mika mata wayan yayi ya ce "ga Zarah." Tana yar fara'a ta amsa,............ Tayi mata sallama, haka kawai ita ma taji kishin ya dirar mata, Ta daure ta amsa sallamar, Nusaiba tace 'Ya school? Ta amsa, "Lafiya lau, Kin ga Maigidan namu ko? Tayi dan Murmushi, Ta ce "Na gan shi" Ta ce Zaki sha surutu har sai kin gaji, ta dan saci kallonsa, don ita bata ji surutun ba, Hankalinshi bashi kanta, shi dayar wayar ma yake faman latsawa, tana kallonsa ta ce "Yarima kam bakunta na damunsa." Shi yasa ya dubeta ya tabbatar da shi su ke, Ta janye idonta a hankali, tana mai bayyanar da murmushi. Shi kuwa takaici ne ya tokare wuyansa. " Wane shisshigi kuma Zarah ke yi? ya tambayi kansa, wani asirtaccen tsaki yayi, ya dauke kai, Nusaiba da Zarah kam hira ce ke neman gocewa, basu ma san lokacin da zukatansu suka saba da juna ba, kawai ji suke sun amince da juna har suna dokin ganin junan su.Domin a halin yanzu Nusaiba ke fadin,"To yaushe za ki zo? Kodayake ni ce k'arama, ni ya kamata in fara zuwa." Zarah ta ce,"Yanzu na ji magana, to yaushe za ki zo? Ta ce,"Ki saurare ni zuwa karshen satin nan, ki turo min lambarki, ni ma zan turo tawa." Ta amsa, "O.K, zan turo miki. Bari in bar ki da ogan, kar in yi laifi." Tana dariya, ta ce,"Tsaya in mika masa ku yi sallama." Haushi Zarah ta ba shi, don haka tana mika masa wayar, ya kashe, ya zira ta gaban aljihu. Kashewa tayi?" Ta tambaya. Ya ce,"Uhm......... Ta ce,"Anti na kenan. Da ji za ta yi kirki." Ya ce ,"Sosai take da kirki kuma tana da halaye masu yawa wadanda kullum suke kara min son ta. Iyayen ta talakawa ne iri na. Sai dai Allah yayi mata baiwar da bai yi wa kowane mahaluki ba. ZARAH, sunanta kadai ya kan sanya ni nishadi, ballantana ita kan ta. Kar fa ki ji wani abu a rai, ba wai ina fad'i bane, saboda wata manufa. No, ina son ki sani ne, ba kowace mace zata yi abin da Zarah tayi ba. Tun muna yara mu ke tare, sai da biki ya zo gaf, sannan aka ce ga wata a hada 2, ina nufin kishiya, ko ke ce yaya za ki ji? Gaba daya jikin ta yayi la'asar, ba don komai ba, sai don tausayin Zarah d maganganun Naseer suka sanya ta. A take nan ta ji kaunar Zarah na shiga jikin ta. Tabbas Zarah tayi bajinta, kuma abar tafa mata ce. Ta sauke numfashi. "Gaskiya ne, ko ni ta burge ni, sannan bayanin ka a yanzu ya sanya min kaunar ta cikin raina. Hakuri babban Jari ne, kuma ita rayuwar duniya mai karewa ce, shi yasa ni ma ban ga dalilin daukan ta da zafi ba. Tsakanin mai kudi da talaka kuwa, wata hikima ce irin ta Ubangiji. Ya kuma halicce mu ne saboda mu taimakawa junan mu. Da ya so, da gaba daya masu kudi zai hallice mu. Haka ku ma daya ga dama, da sai ya aje mu dukkanmu a talakawa. Mai hankali idan ya natsu, zai gane dimbin dalilan da su ka sa Ubangiji ya bambance ababen halitarsa. Saboda haka kar ka yi tunanin komai akan zama na tare da Zaraha, wai don ni na fito gidan wadata. Insha-Allahu za ka same ni da irin halayen da ka ke so." Yayi dan shiru, tunanin sa Nusaiba na da kalamai, sai dai ba su wani girgiza shi ba, saboda ya saba jin kyawawan lafuza a wajen Zarar sa A takaice ma dai ji yayi kamar tana son tayi gasa da Zarah, don ya ce ta ji yana yabon ta. Ya girgiza kai, ya ce,"Shi kenan." Ya duba agogon hannunsa, ya ci gaba,"Bari mu yi sallah ko? Karfe daya ta gota." Yana rufe baki, ana kwala kiran sallah. Ta mike ta ce,"Za ku shiga masallaci ne? Ya ce,"Sosai kuwa." Ta fice ta bar shi yana zancan zuci, "Ka ji 'ya da a dakin ki za mu yi sallar? Ya dan ja tsaki, sannan shi ma ya fita ta kofar da suka shigo. Ita kuwa wajen Sageer ta nufa, ta kira shi ya fito, ya iske Naseer a waje, suka tafi masallaci. Nusaiba na sallamewa sallar. Wayar ta ke ruri? Ta dauko ta, ta duba Kausar ce, ta dauka tasa wa kunnen ta,"Ban son wulakanci, ba za ki zo din bane? Ta ce,"Gaskiya zai yi wuya. Wallahi lakcas sun yi yawa yau. Ko wacce kuma na da muhinmanci da sai in tsero. Sorryy kwata, ki ce da Jah-Jah gaisuwa na ke.:" Ta dan ta6e baki, ta ce,"Ban fad'i." "Ai na ce sorry. Ke ma kin san sbd karatu ne kawai.." Ta ce,"Shi kenan, ni zan zo gobe, idan kin dawo ki kira ni." "O.K Matar Jah-Jah. Tana murmushi ta ce,"Kya ji da shi." Suka yi sallama. Kowa ya aje waya. Madubi ta nufa ta sake gyara fuskarta da daurin dan kwalinta, ta suri waya ta bar dakin. Mariya ta kira, ta tambaye ta maganar abinci, ta ce duk ta shirya su a can falon. Kai tsaye can ta wuce. Takalman su Naseer na kofar falon, don haka ta shiga da sallama. Duk suka amsa. Kai tsaye wajen abinci ta wuce ta bubbude kulolin, ta ce kowa ya bi abinda yake so. Sageer ta za6i Frie rice, shi kuwa dan gogon da kyar ya cusa lafiyyan (Coleslaw). Sun dan ta6a hira zuwa karfe 3, Naseer ya ce tafiya za su yi. Sageer ya ba su wuri su yi sallama. Tsawon minti 2, bai ce da ita komai ba, sai ta mike ta ce bari ta kawo masa sakon Zarah. Shi ma ya tashi ya ce ta same shi a mota. Suna tsaye jikin mota, ta fito da manyan jakunkunan leda guda 2, cike suke da kayan shafe-shafen mata. Ta mika wa Sageer ta ce,"Leda 1 Zarah, 1 ta amaryar ka, don ni ban yarda ba da ka ce babu ita. Dariya yake yana fadin me zan 6oye miki? Kin san Allah babu ita a halin yanzu sai an kammala karatu. Kin san taura 2 basa taunuwa a lokaci guda." Ta ce,"Gaskiya ne, to mun gode, amma ki rike wannan, tunda dai yanzu babu ita." Ta ce,"To lodawa Antina duka." Ya ce,"Lallai Zarah ta gode. Allah ya saka da alkhairi." Naseer ya dube ta tsakar ido, ya ce,"Kayan nan sun yi yawa da kin rage." Ta dan kada kai, ta ce,"Ba su yi ba, kuma ai Antina na ce akai ma wa ko? Ya ce,"Shi kenan ta gode. Sai wani lokaci." Ta ce,"Ni ma na gode, a gaida kowa da kowa. Za su ji." Ya fadi yana shiga mota. Tuni Sageer ke mazaunin direba. Ya tada mota. Mai gadi ya bude get, suka fice, sannan ta wuce gida." A falon sama ta iske Umminta. Gefen ta, ta zauna ta ce "Wash! Na gaji." Aikin me ki ka yi? Ta ce,"Haka kawai na ke jin kasala." Sun tafi ne? "Eh, sun tafi yanzu." Ta dan yi shiru, kafin ta ce," O.k." Ta dan dafa kan ta." Ko dai yunwa ki ke ji? Fuska yamutse ta amsa. "Wallahi kuwa. Don ko dan ruwa ban kurba ba." Ta ce,"To maza tashi ki je ki sami abinda za ki ci." Ta mike ta wuce, tana jan takalma, da gani ta gajin da gaske. Umminta tayi kasake, tana tunanin ya dace ace Naseer ya shigo ya gaishe ta. Da ta rasa dalili, sai ta watsar da zancan, ta kama abinda ke gaban ta. Sageer ya ja na dogon salati. Da sauri ya dube shi, "Menene? Ya ce," Zuwan duk bai da amfani." Da aka yi me? Ya ce,"Ka san tamkar a kan kaya na ke zaune cikin gidan nan, maimakon ka ce min mu je mu gaida Hajiya....... Shi ma salatin ya dauka ya dire,"Girman Allah na mance, abinka da ba sabun ba. Gaskiya ba'a kyauta ba. Kuma anyi abin kunya. Yanzu ka kira wayar Nusaiba, ka ce ta ba Hajiya hakuri, mantawa mu ka yi. Ai kowa yasan ajizani na Dan-Adam." Naseer ya ja tsaki,"Zancan banza. Ni ina da lambar ta ne? Ba ka amsa ba? Ya tambaya a firgice. Wani tsakin ya sake yi. Sageer ya hau fada.Ka na ta tsaki, wannan ai wulakanci ne, ka ma nuna zahiri ba ka damu da ita ba, ai ko da ba'a sai ka ce ta ba ka lambarta, tunda dama can zuwan ba don Allah ka yi shi ba! Amma wannan rashin mutuncin da me yayi kama? Ya balla masa harara, ya ce,"Don Allah ya ishe ka Malam. Ka fi ni jin zafin abin ne? Saboda me zan ki gaishe da Hajiya? Bayan kodayaushe na je gun Alhj, zan shiga wajen ta mu gaisa. Kawai mantawa na yi." Ya ce,"Ai saboda rashin daukan wannan zuwan da muhanimanci, duk shi ya kawo hakan." Eh, kai haka din ne, sai me? Kai da ka dauka da muhinmanci me yasa ba ka ce aje a gaishe ta ba? Yayi shiru ya ci gaba da kallon gaban sa. "Mts.......... Naseer yayi tsaki. Ka fein ya ce "Wallahi da gangan ka ke ba ni laifi. Ya dan dube shi, ya sassauta murya,"Yanzu saboda Allah Naseer ina abin kushewa a wajen yarinyar nan? Ya gyara zama sosai, ya ce,"Ni ka ji na kushe ta ne? Nusaiba tayi. Wallahi babu gatse a cikin magana ta, duk inda ake son mace, yarinyar nan ta kai wajen kuma har ga Allah ta wuce da aji na da ace haka kawai na gan ta a titi, babu yadda za'ayi in tunkare ta da maganar soyayya, saboda ba aji na bace. Saboda haka na ke son ka gane. Allah bai sa min son ta ba ne. To wa ya isa ya sanya min? Shi fa so gamuwar jini ne, kuma mu2m ya kan ji shi ne kawai cikin ran sa. Ka san Allah, har mu ka bar wajen nan, babu komai cikin raina, sai k'unci, to ina son yake anan? Sageer ya numfasa, tausayinsa ne ya kama shi, wannan murdaddan al'amari da me yayi kama? Ya kara kwantar da murya ya ce,"Sarai na fahimce ka Naseer, amma shawarar da zan ba ka, ita ce ka rinka yaki da zuciyar ka. Kullum ka rinka nuna mata rayuwa na iya sauyawa a kodayaushe. Domin ba ka san abinda Allah ya 6oye a cikin wannan aure ba. Please! Ni rikon ka na ke? Ya mirgina kai gefe, ya ce, "Na ji." Aiki da shi ba dole ba kenan? Ya dube shi ido warwaje,"Yau na ga ikon Allah! Abinda fa ke hada ni da kai kenan. Kai komai ayi shi dole. Na ce na ji, sai ka bar shi a anan jin. Shine za ka bude min ido? Ya juya yana guntun murmushi, "Kai kai, Sageer Tela kenan.!."Allah yasa su Baba su samo maka mata a kauye." To menene? Ya ce, "Ba komai. Har na hango mu ne mun je tadi, ta ci uban jan baki da gaxar ga uwar dammara." Yayi 'yar dariya, ya ce,"Duk babu komai, a hankali zan canza ta. Kai ba ma za ka ta6a gane ta ba, idan ta waye." Ya jingina da kujera ido rufe, yana fad'in ,"Ya Allah ka amsa. Allahumma amin." Sageer ya ce,"Please stop that nonsense, ba shine a gaban mu ba. Ka yi kokari ka kar6i lambar Nusaiba, ka wanke kan ka." Ya bude ido yana duban sa a karkace, bai ce komai ba, haka shi ma Sageer bai k'ara cewa uffan ba. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Ba k'aramin farin ciki Umma tayi ba, lkcn da su Naseer suka dawo. Shi da kansa yake gaya mata irin kayayyakin da Nusaiban ta bayar a kawo wa Zarah." Ba ta ma rude ba, sai da Sageer ke gaya mata kyautar gida da sabuwar mota inji Alhj." Ta tallafe ha6a ta ce,"Dole mu je Kaduna godiya, bari Malam ya dawo. Oh ni 'ya su. Allah ka k'ara had'a mu da masoyan mu." Ganin Umma na ta murna tana k'ara masa takaici, shi yasa ya ce zai k'arasa gidan su Zarah ya kai ma ta sakon ta. Sageer ya sallame ta, suka fito tana ta sa albarka. Gida ya fara aje shi, sannan ya juya akalar motar sa zuwa gidan su Zarah!.Yana tafe zuciya na masa saka iri-iri, tana aibanta masa auran Nusaiba. Tana nuna masa Zarah fa kallon sa kawai take yi. Allah kadai ya san abinda ke cikin ran sa. Watakila ma yana so gulma ce kawai. Nan da nan ran sa ya shiga kuna da kiyayyar Nusaiba ta tokare masa zuciya. Dole ya taka birki ya kashe mota, ya jingina da kujera ya runtse ido ya na kiran, "Inna-lillahi"Wa-Inna- ilaihir-raji'un! A zahiri ya nuna masifa ce babba ta same shi, domin anyi masa dabaibayi ta k'oina, an daure shi da jijjiyoyin jikin sa. Tasbihin da yake wa Allah, shi ya taimake shi zuciyarsa ta sassauto ta daina bugawa. Ya bude ido jajur! Ya numfasa, sannan yayi hucin zafi. Ya kada kai, yayin da yake tayar da mota. A haka dai ya lalla6o kofar gidan su Zarah. Nan ma ya jima zaune kafin ya dauko sakon ta ya fito, ya kulle mota ya shige gidan. (DUHUN KAI, GABA DA KISHIYA).Shine sunan littafin da Zarah ke karantawa a tsakar gida, wanda Ustaz Abubuakar Abbas Rjiyar Lemu ya rubuta. Sallamar Naseer yasa ta cira kai, ta dube shi tana amsawa tare da wani kayataccan murmushi. "'Yan Kaduna. Har ka yi me? Take zuciyar sa ta wadata da farin ciki. Amma fuskar sa, ba walwala sosai, ya zube ledoji gabanta ya ce,"Na dawo. Ina Inna?"Ta ce,"Bata dan jin dadi ne, shine ta kwanta, ina jin ma barci ne ya kwasheta." "Ya ce, "Assha-assha, ta sha magani? Ta sha. To ya hanya, ya aka baro amarya? Ya kara kirne fuska ya ce, "Tana gaishe ki. Wannan kayan ma sakon ki ne, wai a kawo miki." Ya wuce dauko kujera, ya bar ta nan tana bubbude ledojin. Ta wangame baki cike da mamaki, ta dube shi yayin da yake zaune bisa kujerar yana fuskantar ta, ta ce,"Wadannan kaya, yayana ai sun yi yawa." Ya ce." Ah to, ai dole a baki kaya da yawa, tunda an cuce ki. Abin ba siyasa ba ce." Ta dan daure fuska, ta ce "An cuce ni fa ka ce? Haba yayana bai kamata ka fadi haka ba, ina laifin mai son ka? Ya ce,"Babu ai ke ba za ki gane wayon ba. Wai ni ma ina zuwa Alhjn ke gaya min zai ban gida a Hanwa da sabuwar mota. Duk kallon su na ke, me ya sa da can bai ba ni ba? Kin ga ya nuna min ginin da na daddage na yi, ya raina shi kenan. Saboda haka ki karbi duk abinda su ka ba ki, ki ci banza, ni Naseer na ki ne har abada, ruwa da iska, babu mai raba mu, balle karfin dukiya. Tayi zuru tallafe da ha6a, tana kallon sa ya kai aya. Idanuwan ta suka dan jirkita, na rashin jin dadin maganan. Ta dan kada kai, ta ce,"N kuwa yayana ban ta6a zaton ka na da irin wannan tunanin ba akan mutane. Zato? Zunubi ne ko ya tabbata gaskiya inji Manzon Allah (S.W.A). Saboda haka na ke shawarta ka, da ka daina wannan zargin a ran ka. Komai za ka yi, ka yi shi don Allah, hakan shine cikar mummuni. Na san ka na kaunata............Yayana ni ma kuma ina tare da kai." Ya sauke numfashi ya ce,"Ba kaunar ki kawai na ke yi ba, son ki na ke mai tsanani, irin wanda ban jin sa ga ko wace 'ya mace. Na je Kaduna na ga Nusaiba kuma ina mai tabbatar miki bata da makusa, amma ko alama ban jin son ta cikin raina ba. Na san ba dole bane ki yarda da abinda na ke fada, sai dai ya zama dole in gaya miki, anyi min fin karfi. Anyi min tilas, ancusa ra'ayin da har abada ba shi cikin tsari na. Gaba daya an rusa ginin da na tsara zuciya ta, wanda bai wuce son da na ke miki ba, in zauna da ke cikin gidan da wasu ke rainawa. Saboda haka kar ki ga laifi na akan duk abinda na fadi, bacin rai ne." Ta ce,"Duk na ji, kuma na tabbata idan za mu kwana anan, ba zan ta6a kada kai ba, don ka fi ni baki. Amma ina son in roke ka arziki, saboda girman Allah, ka yi min alkawari za ka rike ni da Nusaiba a matsayin 'yan uwa daya a muslunci? Shiru yayi, yana kallon ta sama da kasa. Ta sake fadin,"Yayana........."Kar ki hada ni da addini. Ki tauye ni Malama! Yayi saurin taran numfashin ta, don haka ta bi shi da kallo." Gaskiya na fada, kin san na fi ki sanin 'yar uwa ta ce a muslunci. Ubangiji kuma duk ya fi mu sani, shi yake sanya kauna da soyayya, to bai sa min ta, sai yaya? Ta dan yi jim! Tana masa kallon mmk kafin ta k'ara kwantar da murya ta ce,"Ni kuwa yayana ganin na ke duk zance ka ke yi, a hankali za ka so ta." To fa! Ta tsokano tsuliyar dodo. Mintoci barkatai ya kwashe yana kallonta kawai, da gani, ta san ta ta6o shi, don haka ta sunkuyar da kai ta sake fadin,"Allah ya huci zuciya yayana." Ji tayi kawai ya shura takalman sa, ya wuce. Ta bi shi da kallo har ya fice. Ta kama baki tana sallami,"Yayana kamar kuturu? Nan da nan zuciya iya wuya. Dama ya lafiyar kura? Da anyi magana, ya tashi yayi waje, ai za mu sha fama, gara in sami mai taya ni." Ta shiga fiddo kaya daga leda, kaya ne 'yan waje. In banda setin kayan Nivea da Naseer ke siyo mata, babu wanda ta ta6a gani cikin su. Turare kam sai ta gaji da fesawa. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Nusaiba kwance bisa gadon ta shiru, ta rasa abin da take tunani. Ta dubi agogo karfe 5 daidai, nan da nan tayi tunanin yakamata ta tambayi su Naseer, ya suka isa gida? A lokacin guda wani sakon ya sake zuwa kwalkwarta, Ashe, ba mu yi musayar lamba ba. Tayi wuf, ta tashi zaune,"Yaya aka yi haka? Ta tambayi kan ta. Abin ya bata mamaki kwarai, saboda shi ya bata lambar Zarah, tayi amfani da ita ta aika mata da ta ta lambar. Ta kada kai tana dan murmushi, kafin ta ce,"Ban ma san wanda ya fi shirme ba tsakanin ni da shi." Wayar ta dauka gefen filo ta nemo Zarah. Wayar na jikin ta a lokacin da take ta ba ido abinci, ta shafa wancan mai, ta goge (Lotion) ta fesa turare. Kukan Wayar ta ji a jikinta, ta daga da sauri ta dauka, ta dubi lamba. Nan da nan ta dauka, " Hello! Hello Antina." Ta ce,"Wallahi ban so ki ka kira wayar nan ba yanzu, domin na baza sakon ki ne ina ta gani, jira na ke in gama, sannan in kira, in yi godiya." Tayi dan murmushi ta ce,"Antina kenan ashe har sun iso? Ai kuwa sun dawo tun dazu, yanzun nan ogan ya bar nan. Ta ce,"Ba ki san wani abu ba. Ashe ba mu amshi lambar juna ba, ni ban tuna ba, sai yanzu da na ke son inji yaya suka je gida? Shi yasa ma na kira ki, ki ba ni lambar in masa gori." Mamaki ya kashe ta, ta ce,"Ta6d'i, ai kuwa abinda ya fi gori ma ki yi masa, ni ma zan taya ki." Ta ce,"Na ko gode miki." Ta ce,"Na ga sako, gaskiya amarya kayan sun yi yawa, har yanzu kallon su na ke yi." A'a Wallahi bakomai. To na gode. Allah ya saka da alkhairi." Ta amsa,"Amin, sai kin sake ji na. A gaida mutan gidan." Za su ji, na gode." Kowa ya kashe wayar. Take nan Zarah ta tura mata lambar Naseer. Tayi shiru tana mamakinsa, domin tuni ta gano manufar sa. Ta numfasa ta ce,"Abinda yayana ke yi sam-sam ba shi da amfani." Ta hade kaya cikin ledojin su ta kwashe ta shige da su daki. Inna na ta barci, ta aje gefe kafin ta tashi. Riginginen da Naseer yayi bisa gadon dake dakin barcin sa, babu abinda yake tunani, illa kalmar da Zarah ta gaya masa. Ba karamin kona masa rai tayi ba, haka kuma yake mata fassara kala- kala. Ko shakka babu, abinda yake zato, ya tabbata gaskiya. Zarah kallonsa kawai take yi. Rashin sanin yadda zai yi, ya wanke kan sa shi yasa shi cikin damuwa tare da k'ara tsanar auran sa da Nusaiba. Wayarsa da ke ta faman ruri, bai sami daga ta ba har ta katse, ta sake dauka. Sannan ya ja dogon tsaki, yasa hannu ya lalubo ta a aljihun gefen rigar sa. Kawai O.K ya dannan, ya kanga wa kunnansa, "Hello! Ya fadi murya dakushe. Ta ce, "Hello, Nusaiba ce." "Wuf ya tashi zaune, shiru yayi, yana tambayar kan sa, ina ta samo lambar sa? "Hello! Ya sake fadi ya ce. "Hello, ya ki ke? Ta amsa, "Kalau. Kawai na kira ne inji ya ku ka iso? Ya ce,"Lafiya, na gode." Koda yake lambar ma sai da na roka. Ban cancanci samun ta ba ko? Ya kara 6ata rai, kamar ya amsa da eh. Abban sa kadai yake dubuwa,"Ya dan lumshe ido, ya bud'e ya ce,"Ba haka bane, amma ba za ki gane ba. So ki bar shi a mantuwa kawai.". Ta ce,"Na yarda, ai kowa na mantuwa, sai dai wani lkcn akwai rashin kulawa." Jin za ta gano shi, yasa yayi mata dabara ya ce ,"Ke ma ai ba ki ba ni ta ki ba, ba ki damu da in sami lambar ba kenan? Tayi dan murmushi, ta nuna masa ta fi shi, duk abinda yake tak'ama da shi." Tsakanin na da kai wa ya kamata ya tambaya? Tambayar ta, ta kure shi, kuma tuni hirar ta ginshe shi, don haka ya gunutle ta da fadin "Na ce mantawa na yi, ina ganin ya wuce, tunda kin samu, wannan ce ta ki? Ta ce,"Kwarai, ya wuce, in dai Antuna na nan ban da matsala. Lamaba ta kenan. Sai na ji ka." "Shi kenan nan gode." Ya kashe wayar yana dan tsaki." Washe gari tun safe ya wuce Kano, don gudanar da wasan su da (Kano Riders). Ko alama Naseer bai da kuzari, domin tun ranar da Alh. Basheer yayi masa albishir da auran Nusaiba, ya rasa duk wata natsuwa ta sa. Gaba daya ya dora wa kansa damuwa. Ya dawo tamakar maras lafiya. Tambayoyin da Yakubu ya rinka yi masa kenan a dakin (Hotel) din da

Chapter 1 of 6