Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
dan akwati a can Kasan kwalin na sa hannu na dauko shi, madaidaitan warwaraye ne masu matukar kyau na gold guda hudu na kalle shi cikin farin ciki kan in yI mishi wata magana sai ya cc mini; "Ban sai miki zobe ba saboda ga al'ada saurayike bada kyautar zobe." Na yi murmushi na ce, "Na gode Yaya Almu." Ya kallc ni cikin nutsuwa ya ce, "To yanzu da ba ki da saurayi ya ya kenan ko kuwa zan yi wa Umma magana ne ta sai miki zobunan da za su dacc da su?" Na cc mishi, "Aa ba ma sai an saya ba, na gode." Hira sosai muka yi da yaya Almu har muka gangaro kan zancen aure na ce mishi, a1 in aka yi bikin ku kuka tafi zan yi kcwar ku. Ya dan kalleni cikin nutsuwa kafin ya ce anya kuwa Rabi? Ai nafi zaton murna za ki yi maimakon kewa musamman ni da na kc takura ki da yawa na ke yawan shiga al'amuran ki wadanda suka dacc in shiga da wadanda ba su dace ba duka. 99 Na dan yi murmushi na ce, 'Ai Umma ta ce mini in daina dauka 'yan uwanci kake yi mini kana yi mini hakan ne don ganin kai ne ka cancanci ka rinka kwabata kan abubuwan da nake aikatawa. Sai da ya dan gyara zama kadan kafin ya ce mini gaskiya ne Rabi ban iya kawar da ido kan kuskuren ki don so nake in ji ana cewa kin fi kowa hankali, kin fi kowa nutsuwa da sanin ya kamata shi ya sa kike ganin ina yi miki abin da nake yi mikin, amma ba don ina kin ki ba. Na ce, 'Ai na yarda." Ya tashi ya je ya yi alwala ya dawo nima na je na yi na dauki riga guda daya a cikin rigunan nan na saka na yane kaina da gyalanta na yi sallah ta. Sai da muka yi sallar Isha'i, sannan muka fito daga wurin maimakon mu shiga gida motar shi ya ce mu shiga na bi umarnin shi yana tashinta yana gaya mini, "Bari mu je mu ci abinci tun da ba mu je gida da wuri ba, balle ki yi mana girki." Na ce mishi to. Muna tafiya cikin tafiyar ya danna mana faifan da ke cikin rediyan motar tashin muryar Maria kelly ce ta soma tashi cikin wakarta mai taken Always be mine baby! Chines Restaurant ya kai mu sai da muka ci muka sha, sannan muka yi wa su Umma take away din abin da muka cin muka kawo musu. 100 Tun daga rannan yaya Almu ya shiga sa mini dogayen riguna masu matukar kyau, kan kaa ce me ye wannan sai suka zamo sune suturar da nake am fani da ita na maida kwalliyar hijab ita ce kwalliya mafi daraja a wurina. A haka muka kasance har ranar zuwan baba ta zo na zamo cike da zumudi fiye da kullum a dalilin ranar ce kuma za ta zamo ranar dawowar Ummana. Tun dare nake ta faman shirye-shiryen abincin saukar da nake shirya mata. Gari na wayewa na gama kintsa komai na tsabtace wurin ta tsab, ko'ina sai kamshi kake ji yana tashi. Na yi wanka na zauna na tsala kwalliya cikin wata doguwar riga mai ruwan kasa, gaban rigar ya sha ado da wasu duwatsu masu daraja na yane kaina da gyalanta, sannan na dauko warawaran Yaya Almu na sanya a hannuna tare da wasu zobuna guda biyu da Yaya Junaidu da ya ba ni kyautar cika shekara na farin gold na yi matukar yin kyau ga kwarjini na fito cikin wani sansanyan kamshi na iso wurin yaya Almu na samu wai lokaci ne zai yi wanka na ce mishi; "To ni gaskiya zan bi Yaya Junaidu sai ka zo." Ya kalleni cikin murmushi ya ce, "Haba Rabi dan jiran da za ki yi mini na mintina da ba su fi 101 talatin ba. Na yi maza na ce mishi, 'A'a ni kam ba zan iya ba." Ya ce, "To shi kenan sai na zo." Da gudu na fito don gudun kar Yaya Junaidu ya tafi ya bar ni, ina shiga motar na zauna wacce take ledusc Jeep ce. Yaya Junaidu ya kallcni cikin murmushi ya cc kar dai ki cc mini doki ba zai barki jiran Mustapha ba?" Na ce uh gaskiya ba zan iya ba ya yi dariya ya ce Adawiyya kenan, yau za ki ga Umma ai dole ki yi zumudi. A Airport mun isa babu dadewa sai ga jirgi ya sauka ana bude kofar jirgin sai ga Ummana ta bayyana cikin kwalliyar da ta saba yi in har za ta tafi wani wuri, tarc da baba ko kuma za su dawo tarc wato kwalliyar lafaya. Suna fitowa daga cikin filin suka shigc motar nima na shigc gaba tare da Yaya Junaidu. Tun ba mu gama gaisawa ba baba ya kalleni cikin fara'a da murmushin da ke bayyanar da farın cikin shi ya cc, "Lalle na yarda har da zaman ki kusa da Ummanki yakc kara maida ke yar kankanuwar yarinya, 'uwata kin ga irin giriman da kika yi kuwa a dan tsakanin nan kin kara girma kin kara kyau kin kara hankali, domin gashi yau na ganki cikin suturar da ta kara miki kwarjini. " Na ji dadin kalaman baba cikin ladabi na ce 102 mishi, "Ai na kara shekara baka nan baba shi ya sa ba ka sani ba." Ya ce na sani ban mance ba, ya ya ma za a yi in mance da ranar haihuwar uwata? Sannan ma ai ga Ummanki tare da ni kin kuma sani ita ma ba za ta taba mancewa ba." Na yi maza na ce haka ne Baba. Na tanadar miki kyautar ki tana nan zan baki, na kuma san anan ma ba za ki rasa mai baki ba, tun da ga su Junaidu nan a gidan." Na yi murmushi na ce kowa ya yi mini kyauta Baba. Yaya Junaidu ya yankana mini cake din barthday ya kuma ba ni kyautar wadannan zobunan." NNa daga yan yatsuna na nuna mishi zobunan ya ce, 'A'a lalle Junaidu ya burge ki." Na ce eh Baba shi kuwa Yaya Almu ya bani wadannan warawaran tare da kyautar dogayen riga ya kuma roken in maida su suturar da zan rinka yawaita amfani da Su. Da sauri baba ya ce,"Ya yi daidai uwata, don kuwa nima ba akan son raina nake ganinki da Kananan kayan nan ba, barin ki dai kawai na yi don in gane yaushe ne za ki girma ki daina, don kan ki? To ga shi girman ya zo." Muna ta hirar mu da Baba ita kam Ummana shirnu ta yi, don dama in tana cikin mota da wuya kwarai ka ganta tana magana. 103 Muna isa gida Yaya Almu ya sa hannu ya budewa Umma kofar motar ta fito Cikin girmamawa ya ce mata, Sannu da zuwa Umma. Ta kalle shi cikin nutsuwa a hankali ta bude baki ta tambaye shi, "Lafiya na ganka a gida?" Ya sake shiga wata nutsuwar kafin ya ce mata, "Rabi ce ta ki jirana sai na ji kasalar yin tafiyar babu ita don haka na ce bari in jira isowar ku kawai a gida." A falon Umma tana zaunc ana ta yi mata sannu da zuwa, ni kuwa ina kwance a jikinta ita ma sai shafani take yi, cikin fara'a tana fadin, "Adawiyyata ta girma a bayana." Rannan kusan kwana aka yi ana hira a falon Umma wajen karfe goma ta dawo daga falon baba ta zo ta same mu ni da su yaya Almu da sauran yan matan gidan muna zaman jiranta ta zo a yi hira. Tana shigowa anti Basira ta sake ce mata, 'Sannu da zuwa Umma, gaskiya daga yanzu in za ki yi tafiya sosai-sosai za ki rinka sallamar mu don in bakya nan bushewa yake yi gaba daya aka dauka eh Umma. Umma ta yi murmushi ta ce, To ni ban da ku Basira kwana nawa ma za ku kara ai ina ganin ko 104 zan sake yın wata tafiyar kuma zai zamo sai bayan bikin ku, don abin da babanku ya gaya mini kenan zan tsaya in kula mishi da hidimar shirye-shiryen bakin ku." "Yan mata suna jin haka kunya ta kama su suka rinka mikewa suna sallama da Umma suna tafiya dakin su ni kuwa ina ganin sun gama fita na kara mimmikewa a jikin Umma cikin murna da farin ciki na ce mata, "Umma ba karamin farin ciki zan yi ba in aka sallami kartin yan matan nan suka kama hanya suka tafi gidan mazajen su." Umma ta yi dariya ta ce, "Ke kuwa Adawiyya me suka tsare miki haka?" Na yi murmushi kawai na ce, "Uhum Umma kenan ke dai tun da sun riga sun kusa tafiya to mu bar zancen kawai ba zan kawo miki karar su. ba, don kar su je suna cewa na hada ki da su, amma in ban da haka ai ba dadin su nakeji ba." Yaya Almu ya ja tsaki mai karfi, nuna jin takaicin a fili, ya kalleni ya ce mini, "In an sallami kowa ya tafi an bar ki a gidan nan Rabi na roke ki arziki kar ki ci duniya da tsinke, ki rinka cinta da bakin allura." Yaya Junaidu da Umma suka kyalkyale da dariya, Umma ta ce mishi, "Ba dai fushi ka yi ba Babangida?" 105 Ya ce, "A'a Umma wai dai ta ji dadi ne sosai shi ne nake kara ba ta shawara." Ina kwancc jikin Umma suna ta hirar su har dai barci ya daukeni na farka cikin dare sosai na samu duk kowa ya watse daga Yaya Almu sai Umma su biyun suke ta hirar su, alamar za su tashi na gyara kwanciya na juya ta daya gefen Umma ta kara mikewa sosai wai don in kara jin dadin barcina. Sai wajen karfe hudun Asuba na ji tana yi mini gyara kwanciyar ki da kyau Adawiyya, ko ki tashi ki shiga daki ki kwanta, ni zani in yi alwala. Na ji muryar Yaya Almu yana ccwa, "Ta gyara kwanciya Umma? Ai gwara ta tashi ta yi wa Junaidu girkin da ya ce sammako fa zai yi." Ina in haka na yi maza na watstsake don na riga na san da maganar tafiyar tashi na kuma riga na sabar mishi da yi mishi guzurin abin da zai rinka karyawa da shi a duk lokacin da zai yi tafiya. Baba yana gama kwanakın shi guda biyu ya dauki Umma Karama suka yi tafiyar su, gida ya saura daga Ummana sai Umma Amarya. Sati guda da tafiyar Baba Ummana ta bayar da umarnin yan mata su yi shiri za a kai su su je su yi gaisuwar 106 sallama a cikin dangıi, alama dai kenan lalle biki ya matso. Suna gama shiryawa suka zo suka yi sallama ta kawo kudi masu auki ta ba su ta ce su zuba a jakunkunan su, suka yi mata godiya suka tafi, ni kuwa sai na tashi na na nufi sashin 'yan mata. Ina kara duba fasalin sashin namu da irin gyare-gyaren da zan yi a cikin shi kafin in dawo zaman cikin shi na sosai da sosai, don ina son wurin suna fita nan zan dawo ko yanzu abin da ya sa ba na zama wurin sosai takura mini ne da su ke yi da yawan aiki ko aika komai za a yi in dai ina wurin to Adawiyya za su ce. Adawiyya ban kawo abu kaza, Adawiyya ban abu kaza, Adawiyya dauko mini wannan, Adawiyya sharc nan, goge can, waya ce miki ki yi haka? Aikin su kenan shi ya sa nake gudu in bar musu wurin,, don haka suna fita zan shiga, don babu mai mini wannan takurar kuma na gama nazarın wurin na dawo na zauna ina rubuce-rubuce na tsare-tsaren abubuwan da zan gudanar,Yaya Almu ya shigo ya same ni. "Aiken me yau kike yi haka Rabi? Kin kuwa san ban taba ganin ki kina rike da biro kina aikin makaranta ba?" Na ce, "Ai ba aikin makaranta ba nc ina tsare-tsaren yanda zan gudanar da al'amurana ne in kun tafi." 107 Ya,nemi wuri ya zauna cikin nutsuwa ya mika hannu a hankali ya karbi takardar ya zuba mata ido yana kallonta cikin nutsuwa tsawon lokaci kafin ya dago ido ya kalleni ya ce mini, "Wato ke dai Rabi ina jin kin yin karatu kawa kika yi yanzu ki duba ki ga abin da kika zaunan kika tsara da yake wannan yin kan ki ne da a makaranta ne aka ce ku yi wani abu makamancin wannan dä kin ce ba ki gane ba." Ya miko mini takardar tare da cewar tsarin ya yi kyau. "Saura kawai lokacin aiwatarwar, kuma jiya mun shiga makarantar ta ku ni da Zubairu sun manna sakamakon ku carryover ki biyu." Na yi maza na daure fuska na ce, 'Ai na sani kawayena sun yi waya sun gaya mini." Ya ce, "Okey ai ban sani ba." Umma ta shigo ta zauna tana yi mishi magana alamar ta san da shigowar na shi da suka gama wannan magnar sai ya ce mata, "Ni zan iya yin tafiya ne yanzu Umma ko dole sai na jira yan matan sun dawo?" Ya yi murmushi ta ce mishi, "Me ye gamin tafiyar ká da ta su?" Ya ce, "Babu." Ta co, "To ai sai ka yi ta ka kawai suma suna 108 yin ta sun ko da yake Dan san in da kake son zuwa ba." Ya ce mata, "Katagun." Ina jin haka na yi maza na ce mishi, "Nima za ni." Dan na san wurin dangin Umma za shi. Ya ce, "Me za ki je ki yi wo ki bari sai za a yi miki na ki auren kya je nima yanzu za ni yi musu sallama ne su yi mini ganin karshe ina saurayi daga yanzu kuma za su sake ganina ina matsayin mai iyali." Umma ta yi kamar ba ta jin abin da yake fadi ta hanyar kawar da kanta can gefe ni kuwa sai na shiga marairaice mishi ina cewa; "Haba yaya Almu in na yi maka rakiya ai ba laifi ba ne, tun da dama ka saba zuwa da ni ba sai nima in yi maka rakiyar karshe kana saurayin ba. Daga yanzu kuma ai zan rinka rakaka ne kana matsayin mai iyali." Ya yi maza ya ce, 'A'a yanzu dai shirya yau mu je ki raka nin, amma ana ba ni iyali ai kuma na yi sallama da rakiyar ki kenan, iyakaci na ce za ta rinka raka ni nan da nan." Na ji wani abu ya dan mintsinen a zuciyata, har sai da ya bayyana a fuskata, na kasa boye bacin raina. Shi kuwa yaya Almu tanfar bai gane hakan ba, sai cewa ya yi, "Ai ni in na yi aure Rabi matata zan ba ta matsayi mai karfi a rayuwata, komai zan yi da ita zan 109 rinka yi" Na cc, "Uh hakan yana da kyau." Na tashi na shige daki na yi kwanciyata. Wajen arfc goma sha biyu ya shigo cikin shiri. kwalliyar doguwar rigar tazarce ya yi na yadin farin koil ya yi matukar yin kyau. Ya-7auna ya yi sallama da Umma, sannan ya tambaycta ina Rabin take? Ta mishi ga ta can a cikin dakinta. Ya dan daga murya ya ce, "To fito mu tafi mana Rabi" Na ce mishi. 'Ai na riga na fasa zuwa sai ka dawo ka gaishe su." Da sauri Umma ta ce, "Kar ki fara wannan maganar fito ku tafi sai da kika sashi ya 6ata lokaci yana jiranki shi ne za ki ce kin fasa? in da don tashi kadai nc ai da da wuri ya tafi ya dawwo yau ba, saboda kin cc za kin ba ne ya sa ya ce to bari ku je ku kwana don ki gaisa da mutane sosai." Na cc, "Uh, uh! Ya je kawai." Umma da Yaya Almu suka yi rarrashi har suka gaji na cc babu inda za ni har Umma ta tunzura ta shiga balbaleni da fadi abin da ba ta taba yi ba. Ni kuwa sai na fashe mata da kuka ina cewa, "Ni Umma ni ban san abin da nake yi miki ba, kin fi son Yaya Almu a kaina, komai ya yi shi 110 daidai ne a wurinki da7u kina Jin shi yana ccwa daga ya yi auren shi shi kenan ya daina yin mu'amalla da ni, amma ba ki ce mishi komai ba, ba ki kwabc shi kan maganganun da yakc ta fada ba, sai ni kawai don na ce na daina bin shi daga yau ba sai ya yi aure ya daina ba, shi ne za ki lullubeni da fadi?" Yaya Almu ya ce, "To yi hakuri Rabi ai ban san zancen ba zai yi miki dadi ba, da ban gaya miki ba, sai in bar abin kawai a cikin zuciyata." Na yi maza na ce, "Kin ji shi ko Umma kin ji shi yana nan akan bakan shi na cewar in ya yi aure ya samu mata to ya daina mu'amalla da 'yar uwar shi, kuma kin yi shiru ba za ki kwabe shi ba, ai in ya rabu da ni saboda ita kema zai rabu da kc don haka ba zani ba ya je ta fara yi mishi rakiyar daga, yau." Ya ce, "A'a yau kam ai ba a nuna mini ita b tukunna." Umma ta daure fuska ta ce, "Kai Babangida daina wadannan maganganu naka marasa dadin ji." Ya ce to Umma a yi hakuri. Duk da hakurin da ya yi ta bani bayan fitar Umma daga falon ba mu bar gida ha sai wajen karfe ukun yamma a dalilin tuburcwar da na yi na ce babu inda za ni. 111 Muna tafiya a motar Yaya Almu hirar auren shi da matar shi yake yi mini ni da da kike kallona zan so matata Rabi, zan so mu'ammala mai dadi tare da ita, zan so a ce muna da cikakkiyar fahimtar juna ni da ita, ba zan yarda wasu can su shiga cikin mu'amallar mu ba. Zuciya ta raya mini wato ni ce wasu can, ya ci gaba da cewar; 'Shi aure da kike ganin shi karfin shi yafi Karfin komai, kusancin shi kuma yafi karfin kowanne irin kusnaci mu'amallar da ke tsakaninka da matarka mu'amalla ce ta kut-da-kut ta rufin asiri ta taimakekeniya da kuma nunawa juna kauna, don haka ai ina ganin bai kamata ka bar wasu su shiga cokin lamarin ka har su zosuna kawo muku matsala ba." Na ce, "Uh haka ne." Na tsuke fuska ta don dani in samu ya yi shiru cikin raina kuwa sai tunani nake yi. ashe dai shi ma yaya Almu irin sullutayen mazan nan zai zama wadanda daga an yi aure sai kuma su mance da iyaye da 'yanuwa sai a koma gindin mata a tare sai kuma yanda ta yi. Ina cikin tunanin nawa ya katse mini shi ta hanyar cewa, "Ni fa na dade ina tunanin hikimomin da kc cikin aure Rabi, ni fa ina ganin duk abin da ka yi wa matarka ba ka fadi ba, to 112 wake maka irin abin da take maka? Wurinta fa kake sauke dukkan lalurornka, to balle kuma a ce ka yi sa'a ta haifar maka da, caf ai ni kam sai in bar komai in zauna in yi ta tarairayarta ina tayata son abin da take so, in tayata kin wanda ba ta so, in ta kalle farin abu ta ce mishi baki ne in yi maza in ce mata kirin kuwa, don dai kar ranta ya baci." Na kalli Yaya Almu na ce mishi, to amma haka aka ce ayi zaman aure ya yi máza ya ce Yaya aka ce a yi? Kin sanni ban sani ba, tun da ban taba yi ba. Ba tare dana gance abin da yake nufi da fadin hakan ba sai na ce mishi ina ce cewa aka yi, ku kare kan ku da iyalanku daga shiga wata irin wuta wacce makamashinta yake mutane ne da duwarwatsu. Ya yi maza ya ce haka ne Rabi na ce to amma a yanda kake cewa za ka yin nan za ká ya yin wannan aikin? A maida fari baki, ka ce mishi bakikkirin? Kenan in aka maida gaskiya karya za ka yarda? Gaskiya ni ba haka na ga 1yayen mu suna auren su ba." Ina fadin haka na soma kuka ina fadin, "Kenan zan rasa ka zan rasaka Yaya Almu, na gane matarka za ta kwace mini kai, dama kuma ba ni da kowa sai kai. Kai ne dan'uwana da uban mu ya haife mu tare muka kuma taso a daki daya. Kai 113 ne nafi shakuwa da kai, kai na fi so kai ne nake damuwa da duk wani al'amarinka tun inan ganin abubuwan da kake yi mini 'yan ubanci ne da takura a dalilin ba ka son ganina a cikin gida har sai na fahimci cewar kana yi mini abubuwan da kake yin ne don kana nufin gyara a kaina, to amma yanzu wadannan kalaman naka me suke nufi?" Ya yi maza ya kauce hanya ya nemi wuri yaa yi parking a cikin jeji ya fita ya je ya bude but idin motar ya dauko jakaar ruwa ya zo ya bude wurin zamana ya miko mini jarkar. "Bar kuka Rabi ki wanke fuskar ki kar mu isa su ga hawaye a idon ki, ai tun da na gane kin damu da ni haka ba zan bari ta raba mu gaba daya ba, zan rinka yi miki waya a kai a kai duk sati biyu zan yi kokarin in kiraki." Na sa hannu na karbi jarkar ina wanke fuskata cikin zuciyata kuwa fadi nake yi, lalle wannan ya gama tafiya ba zan sake kuka a kan shi ko.damuwa da shi ba, in kuma ya kira n1 a waya bayan sati biyu da kiran farko to ba zan taba dauka ba, gara mu yanke kawai gaba daya. A Katagun a gidansu Umma karba sosai aka yi mana dama yaya Almu ba bako ba ne a gidan yama fini sanin 'yan'uwan Umma da mu'amalla da 114 su, don haka ban sake komawa ta kan shi ba, kowa harkar gaban shi yake yi, ko wani wuri za ni ba na neman shi sai kawai in kira yaran gidan su rakani, shi ne ma in zai je wani wuri yake aikowa in zo mu tafi tare, sai in ce mishi ya je kawai ni na riga na je. Wani abin takaicin dai kawai da ya kara kular da ni a tafiyar shi ne yanda duk inda na je sai a rinka nuna ni a matsayin wai ni ma a amaryar ce, har suna tambayata to in ban da sakarci irin na ki me ya hanan ki biyo sauran yanmatan ku yi tahowarku tare gwanin sha'awa sai ki wani coge sai Lamido ya kawo ki don ba ki da kuny? Na yi ta kokarin yi musu bayani ni fa rako Yaya Almu na yi ya zo ne ya yi muku sallama armma ni ai ba yanzu zai a yi mini aure ba Umma ta ce bikina ni kadai za a yi ba za a hadani da wadannan kartin ba, wajen shekara hurhud fa suka ba ni sai a ce mini ke tafi can ko shekara nawa-nawa suka baki ai kin kamo su har ma kin dara su tun da duk cikin su waccce ba ki kercta a tsayi ba? Na ce to shi kenan ku tambayi Yaya Almu kan wannan dalilin nema har na nemi Yaya Almu don ya bayar da shida kan cewar babu ni cikin wadanda za a aurar din ya ce musu ch a1 ita yanzu ita ce za a bar wa rikon gidan, in an hada 115 har da ita ai zai zama babu wata mai kula da sashin 'yan matan kuma ba ta karasa karatun ta ba, ga shi tun da tana faduwa jarrabawa to ba bana nema za ta fita ba, sai badi za ta gama diploma, sannan ta yi H.N.D. kamar na su Aina'u kenan don haka ina ganin auren Rabi kam da saura tukunna. Gaba daya suka shagala kan cewar kai amma kuwa da abin bai yi dadi a irin wannan girma da ta yia ce kuma sai an kara wasu shekaru nan gaba? Ya yi murmushi ya ce yarinya ce fa kwanakin baya ne ai ta cika shekara goma sha tara, suka ce au to in ban da nan wurin ku ina ake yin haka ka bar 'ya tana ta yi maka wanki a gida? Ai mu nan shekaru sha biyu, sha uku in ta yi tsauri sha hudu sai a gabatar da yarinya. Kwana biyu muka yi muka kamo hanyar dawowa a wannan lokacin ba wani dasawa muke yi da Yaya Almu ba, don sau uku yana subutar baki yana kirana da sunan Aina'u sai ya kiranin sai ya ce mini wai sorry please na riga na sanya ta ne a raina a dalilin ke ma ita kika zaban mini sai na ke ganin to watakila dai ita din za a ba ni bari in koyi sonta tun kafin a ba ni itan, doon komai ya tafi mana daidai, ko kuwa? Kin san ni ba zan taba yin musu da baba bkan wacce zai ba ni ba, to balle kuma in yi sa'a a ce ita din na samu ga ta mai kyau, ga ta 116 gwanar iya kwalliya, ga 1ya taku. Na yi maza na ce a'a nan kuma daya. Ya ce au to ashe kwalliya kawai ta iya ban da takun tafiya? Uh to amma ai na samu mace gwanar kwalliya ai dadi ne da ita za ta fidda ka kunya duk inda kuka shiga ni ko ba ta iya girki ba babu komai zan nemo mai yi mata girkin, ta yi kwalliya kawai ta yi zamanta in na dawo gida ta yi ta tarairayata tana ina taka saka da ni, tana mini tausa tana mini abin nan. Ai ni kuma shi kenan ta tafi da komai nawa ta. gama da ni ta tafi da ruhin rayuwata. Na tsuke fuska cikin jin takaici na ce, "Kai Yaya Almu dai wani abu ya same shi tir!" Na ja tsaki. Ya dan waiwayo ya kallen ya ce, "Ba dai ni kike wa tsaki ba ko?" Na yi shiru ban ce mishi komai ba. 'Rashin kunyar taki har ta kai ga yi mini tsaki?" Shiru na yi ban kula shi ba, da na ji zai yi magana sai na katse.shi na ce mishi, to wai ni yaya Almu me ya sa duk inda muka tsugunna muna magana sai ka gaya musu faduwa jarrabawa nake yi? Ya ce ban san ba kya so a sani ba ba zan sake gayawa kowa ba, tun da ma ai kin san in na yi aure zan dauki matata in yi tafiya ta da ita, ba zama ki rinka ganina a kai a kai ba, balle in

Chapter 6 of 8