Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 8
shi" Na kalle shi na yi murmushi na ce, "Ai kuwa don na matsu da ka ci ne kawai zai sani yin hakan ka ga wannan salad ne, amma kaza wato cikin salad, wannan kuwa." Na kara karkata mishi kwanon don ya gani da kyau na ce mishi, "Salmon pie sunan shi, bari in lissafa maka abubuwan da na yi amfani da suu kafin in gaya maka yanda na' yi." Shi kam Yaya Aimu bai jira bayanin da zan yin ba ya mika hannu ya dauki Salmon pie din guda daya sai da na gyara zama sosai na fara lissafawa Yaya Junaidu kayayyakin amfanin na ce, Bari mu fara da Salmon pie, na yi amfani da kwababbiyar fulawa da na cakudata da butter, gishiri, pakin powder, sai shinkafa, albasa, cream, kafin gwangwani, dafaffen kwai, butter da na dafa shinkafa na tsameta na tsantsame sai na yanyanka albasa na soya shi cikin butter, sannan na zuba shinkafar da kifin tare da cream na gauraya su da kyau na rinka yanko kwababbiyar fulawar nan ina amfani da board wajen murzata tana yin fadi. Sai na rinka debo hadin shinkafa da kifin nan ina zubawa a tsakiya ina rufewa da rabin 6arin fulawar bayan na zuba yankakken kwai a kan shinkafar in ya ruhu da kyau sai in sa wuka in 60 yanke sama da kasa, don ya zamo a bude kamar haka." Na daukoo guda daya ina nuna mishi, don ya gane sosai. "Don ya rinka fitar da tururi daga nan sai na salka a oven ya gasu na kusan mintoci ashirin, shi kuwa chiken salad ga abubuwan da aka yi amfani da su: Dafaffiyar kaza, kwai dafaffe Mai, cokali biyu. Atile Mayonniase. Tafarnuwa Dakakken 6awon lemon tsami, yaji. Ina shirin fara gayawa Yaya Junaidu yanda na yi na shirya mishi chicken salad din sai kawai wayata ta yi kara in dauka sai na ji muryar Julde yana tambayata. "Ina kika shiga ne? Gani nan a falon Umma ina jiranki." ne? Na kashe wayar na kalli Yaya Junaidu cikin murmushi na ce mishi, "Kawai Yaya Junaidu tun da ka ce sai na yi maka bayanin yanda na yi na yi za ka ci, to ka ci salmon pie din kawai, tun da shi na yi maka bayanin komai barwa Yaya Almu kawai ya cinye chicken salad din. Ni na yi bako Julde ya zo wurina zan je mu sha hira." Ina fadin haka na fice dakin da gudu na nufi sashin Umma, 61 don ganin Julde Julde dan aminin Baba ne da suka taso tare suka kuma matukar son juna, har suka zama kamar yan'uwa saboda dadewar abotar su baba Wulle. Ina shiga falon Umma na same shi a zaune ya sha kwalliyar Rananan kaya dama kuma ma'aboCin sanya su ne sai kamshi yake yi, yana ganina ya saki wani lallausan murmushi ya ce, Ban gajiya na zo miki." Na yi maza na yi wura-wura da ido don ganin ko Umma tana kusa ta ji abin da ya fada, da na ga an yi dace ba ta nan sai na fada mishi a hankali. "Kai Umma fa ba ta san na je ba." Gaba daya ya bude baki da idanuwa nuna alamar mamaki. To ya ya aka yi haka?" Na dan yi murmushi na ce mishi, "Kai dai ka shown kawai." Ya yi murmushi ya ce, "To na yi." Na je na kawo mishi abin sha na kuma zauna muna hira, har sai wajen goman dare, sannan ya tafi saboda ya san 1yakacin hirar da bako ke yi a gidan mu kenan in dai ba kwana zai yi ba, don goma tana yi ake rufe get din gidan mu, in an rufe 62 kuma ba a budewa. Wannan umarmin Baba ne. Sati guda da faruwar haka mun fita unguwa ni da Yaya Almu cikin sabuwar motar shi Kwalliya sosai na yi na kuma yi matukar yin kyau, sai ma da Umma ta yi ta rokona sannan na yarda na yane kaina da dan siririn gyale, don kuwa kwalliyar kananan kaya na yi muna tafiya cikin motar ina sauraron wakar da Yaya Almu ya sanya a cikin motar mai matukar dadi ta Whitney Auston ce mai taken 'lam sabing all my love for you. Yaya Almu ya dan waiwayo ya kallen ya ja tsaki mai karfi tare da galla mini harara ya ce, "In wani ya ga yanda kike kada wannan sai ya yi zaton wani rawar arziki kika iya, nan kuwa ba ki iya komai ba." Cikin sauri tanfar na mance da wanda nake magana na ce mishi, "Allah ya sauwaka ai ni cuwa na rantse ba daga nan ba, lalle ma baka sani ba Yaya Almu ai ni duk wanda ya sanni ya san ni gwansce wajen iya rawa in ba ka sani ba ma ni lokacin da nake S.S.3 har Queen kawayena suke kirana. " Na seke kallon shi na ce, "Tafdijan ashe dai ba ia sanni ba, ai lko kwana biyar da suka wuce na faki idon Umma tana barci na fita na je gidansu 63 Asabe Aliyu tana partin cika shekarunta a can muka gamu da Julde har muka yi rawa tare da shi, shi ne ma ya biyo ni'wai ya yi mamakina har yana yi mini rantsuwar ai duk 'yan matan da ke wurin babu wacce ta kai ni iya rawa." Shirun da na ji Yaya Almu ya yi ne mai tsawo ya barni ina ta zuba yasa na juyo don in ga abin da ya ke yi. Yanayin da na gani a tare da shi kuma sai ya kara fahimtar da ni cewar ba karamin sabutar baki na yi ba naa bashi wannan labarin. Tsoro ya yi matukar kama ni, har na rinka tunanin lalle ni kam ina jin ungozman da ta yi bikina ba ta gasa mini baki ba da kyau. Jimawa kadan sai na ji ya ce, 'Ai ni ma na yarda ban sanki ba Rabi, amma yanzu zan soma neman sanin naki, wato har party kike zuwa da daddare, Umma ba ta sani ba? Shi Baba maigadi fa yana ina?" Jikina ya dauki rawa na ce mishi, 'Ai sau daya ne kafin nan ban taba zuwa ba." Ya ce, 'Wannan shi ne karya." Ya juya kan motar ya fasa inda ya ce za mu je ya juyo damu gida kai tsaye dakin shi ya wuce da ni. "Ta ina kika fita kika bar gidan nan ko kuwa Baba Maigadi ne ya bude miki?" Na yi maza na ce mishi, 'A'a." Cikin rawar 64 Jiki da rawar murya na ce mishi, Ta can baya ne wurin raguna akwai wata wayar da ta balle tanan na bi" Yaya Almu ya kara zuba mini ido fuskar shi dauke da alamar mamaki ya sake cewa, "Na kara yarda dai ban sanki ba, to da kika dawo sai kika cewa Umma me?. Jikina ya dauki rawa sosai na shiga yi mishi kuka ina ba shi hakuri, ya ce, "Ai sai kin gaya mini in kuma kika yi mini karya zan yi bincike in na gano za ki gane kuskurenki." Muryata tana rawa na ce mishi, "Cewa Umma na yi dakai muka tafi don in ba haka ba za ta yi wa duk wanda nan kira mata sunan shi magana." Ya yi shiru ya buga uban tagumi ya zuba mini ido yana kallona, ban da kukan da nake yi kirjina sai dakan uku-uku yake, saboda tsananin tsorata da na yi da irin kallon da yake yi mini gani nake tanfar in ya mike kaina zai nufo. "Ka yi bhakuri Yaya Almu. Ka yi hakuri ka rufa mini asiri kar ka gayawa Baba da Umma za su yi fushi da ni gara ka yi mini koma me za ka yi mini na roke ka kar ka bari su ji su yi fushi da ni, tun da ka ce mini fushin iyaye bala'i ne akan da." Ajiyar zuciya mai tsananin karfi ya yi, kafin 65 ya sauke tagumin shi ya ce, 'Ai ke ba kya tsoro, ba kya gudun bacin rai wa zai taba tsammanin za ki 1ya yin wannan abin da kika yi? " A hankali ya bude baki ya ce, "Ko a mafarki an taba zaton za ki iya yin hakan ba, amma je ki zan yi tunanin abin da ya dace in yi a kan ki." Har kusan kwana bakwa ina sauraron hukuncin da Yaya Almu zai yi mini. A duk lokacin da na gan shi da Umma sun kebe kuwa gabana ya rinka faduwa kenan, sai in rinka ganin kamar abin da ya zo ya gaya mata kenan. Gaba daya hankalina baya tare da ni, kowanne lokaci cikin zullumi da tunani nake na me zai yi mini? Ko me zai faru? Rannan dai da safe sai aka wayi gari ana kara tsawon katangar gidan mu, ashe dama tun washe garin wannan maganar ya sa aka soma aikin ginne can bayan dáma kuma shi ne bangaren da aka yi amfani da waya wajen tsare shi aka kara gini, sannan aka zagaye saman katangar da murdaddiyar wayar nan ta tsaro mai dauke da wutar lantarki. Ban samu dan kwanciyar hankali a jikina ba har sai da na ga Baba ya zo gida ya yi kwana biyu ya tafi ban ji an ce mini komai ba, haka nan Umma sai na gane dai Yaya Almu ya ji rokon da 56 na yi mishi na kar ya hada ni da su. Julde kuwa tun daga wannan lokacin ban san dalili ba, ko waya na yi mishi baya dauka in kuwa a wani wuri muka hadu to yana ganina zai yi maza ya bar wurin. Ana cikin haka ne yaya Almu ya samar mini Federal Poly garin mu na soma zuwa har ga shi na shekara guda har da wasu 'yan watanni a cikin ta tun da ga shi an turo ni nan hukumar zabe ina zaman koyon sanin makamar aiki. Tun da na fara zuwa dai Yaya Almu ne mai dawainiyar kai ni da dauko ni, saboda ku san kullum a makare nake zuwa su Yaya Junaidu ba sa iya jirana, saboda su dukkansu ma'aikatan gwamnati ne, shi kuwa Yaya Almu Lawyer ne mai zaman kan shi, in ba yana da zama a kotu ba uzurin gaban shi kawai yake yi, tun da harkokin kasuwancin shi ma yake yi, tsakanin Nijeriya, da kasar China. Ina zaune kan kujerata da ke Daura da ta yallabai a offishin hukumar zabe 'yan takardun da aka nuna mini yanda zan rinka cikewa nake ta faman kokarin yin hakan cikin tsaiko don na san yallaba1 yana ganin na gama cike su zai sake miko mini wadansu. Ran Hajiya Rabi'atu ya dade gabana ya 67 yanke ya fadi jin iin kiran da yallabai ya yi min1, don dai na san kwanan zancen a duk lokacin da ya yi mini irin wannan kiran na dan zuba mishi ido cikin suararo da nuna girmamawa ya dan sha mur kadan a dalilin ya fara gajiya da murmushin da yake yi mini, a duk lokacin da zai mini irin wannan maganar. "Ina fata dai yau ba za ki sake kawo mini wani uzuri akan 'yar rakiyar da nake cewa ki yi mini ba?" Na zuba mishi ido cikin nutsuwa na ce mishi, To bari tun da ka matsa a kan hakan in Yayana ya zo sai in nemi izini wurin shi." Da sauri yallabai ya fara cewa, Kai ashha! Ashsha!!" Sannan na ja wani irin mummunan tsaki kafin ya fara cewa, 'Ke kam ina jin ke ce 'yar farin gidan ku? Gaba daya saboda wautarki ta yi gaban kwatance." Na ce.mishi, 'A'a ba ni ce 'yar farin Babanmu ba." Ya ce, "Eh ai na yarda da abin da kika gaya mini na cewar shi wannan miskilin mutumin mai muzuran tsiya wanki don sai da na je na yi bincike kan hakan aka tabbatar mini, saboda ko kadan dabi'unshi ba na watarin na kusa ba ne, yafi kama da saurayi mai matukar kishi akan budurwarshi, 68 shi ne za ki je kna gaya mishi wannan maganar ta shirri da za ta kasance tsakanin ni da ke kawai ko kin san tun da yake zuwa wurin nan bai taba amsa gaisuwar da nake yi mishi ba? Ni kuwa ina yi mishi gaisuwar ne kawar darajar an tabbatar mini ubaku daya, amma inda don ta bayanin da kika yi mini ne ba yarda zan yi ba, sai in dauka kawai irin wayon ku na yan mata za ki yi mini." Turo kofar kawai ya yi ya shigo ba tare da ya nemi izinin yin hakan ba, abin da na yi ta rokon ya daina yin hakan, saboda yanda kullum sai yallabai ya gaya mini cewar shi bai taba ganin mai yi mishi irin wannan cin kashin ba a ofis din shi, sai shi. Kullum na yi mishi maganar sai ya ce mini wai shi bai san hakan yake yi ba, amma bari gobe in ya zo zai kula ya gyara, amma kuma hakan ba zai hana shi goben in zo zai kula ya gyara, amma kuma hakan ba zaj hana shi goben in ya zo ya sake ba. Na daga ido na kalle shi fuskar shi kadaran-kadahan yana tsaye cikin shigar suit farare sol, ya zuba hannayen shi duka biyu cikin aljihun wandon shi, ko kallon inda yallabai yake bai yi ba, balle ya sa ran zai gaishe shi. Ya ya kin gåma ne ko da saura?" Cikin nutsuwa na-ce mishi, "Da dan saura kadan." 69 Ya dago ido ya kalli agogon da ke ofice din alamar lokaci yake son sani a bankali ya bude baki ya ce mini, "Bari in jira ki." Ya juya ya fita. Yana barin office din yalla6ai ya dube ni cikin takaici ya ce, 'Shi kuma don fitinar tsiya ba ma zai rinka bari sai an tashi ba, ya rinka zuwa daukar na ki? To duk tsiyar shi ma dai ai dolen shi ya bai wa wai auren ki ko kuma a bayar yana kallo tun da bai taba ganin inda wa ya auri kanwarshi a, balle ya ce shi haka zai yi." Ya rufe zancen na shi da jan wani mummunan tsaki. "Tashi di bishi ku tafi ke ashe ma ba wani niss ya yi ba, gashi nan na hapgo shi koma ya ji maganata ne ya sa ya yi motsin? Oho," Na yi maza na karasa cike takardun na mika mishi na dauki jakata na fito. Na samu ya dan fara tafiya na biyo bayan shi. A hanya muna tafiya na shiga rokon Yaya Almu akan ya rinka gaida yallabai. Ya ce mini, "Ke kar fa ki kawo mini sakarci nine zan rinka bin samarin ki ina gaishe su? Ina ce a ka'ida ni ya kamata su rinka gayarwa tun da nine in ta dauro zan ba su." Na yi maza na ce, "Yallabai yana gaishe ka Yaya Almu ko yau din nan na ji shi ya 70 gaishe ka sau biyu, sannan ma shi ba saurayina ba ne. " Ya ce, "To ban ji gaisuwar ba, gobe in na zo daukan ki zan kasa kunne in ji, don in amsa." A gida da daddare ina hira a dakin su Yaya Almu shi da Junaidu ne a ciki suna cin danbun shinkafar da na yi wa Umma na debo musu suna ci muna hira sai kawai na ji bakina ya sako wani zancen na daban. Na ce, "Kai ana teba a duniyar nan. Tebar yallabai din office din mu fa ta kai girman wancan filon sau biyu." Yaya Almu kam ko motsawa daga inda yake bai yi ba, bai bar cin abincin shi ba, hakan nan bai daga ido ya kalli fillon da nake magana akai din ba, balle ya nuna wata alama ta ya ji maganar da na yi. Sai Yaya Junaidu ne ya ce mini, To ai burgewa kenan ita teba da kike ganinta ai ado ne wurin namiji da.yawan mata kuma ita suka fi so da sha'awa a jikin mutums, kuma ga dukkan alamu ke ma kinan cikin su, don na lura son yallabai din kike yi, saboda kullum sai kin yi mana hirar shi, ai in kin ji mace tana yawan maganar namiji ko da kushe shi take yi, to son shi take yi, ita irin nata salon soyayyar kenan." Na ce, "Kai Yaya Junaidu." Ya yi maza ya ce, "Eh mana ai in kin ga kare 71 yana sunsunar kashi to daukan shi zai yi." Na juya ta wurin Yaya Almu don in ji shi kuma abin da zai fada. Yanayin da na gani a tare da shi ya sa na yi maza na mike na yiwo waje da gudu bayan na ce musu sai da safe. A daki kuwa ina kwance ina tunanin ya kamata a ce ni da kaina na dauki matakin gasawa kaina baki. Ranar Asabar din karshen wata ya zo ranar da yake zamowa ranar tsabtar muhalli ne a kasa gaba daya, ban da haka kuma mu a gida mu ranar zuwan Baba ne, don haka ana fitowa daga imasallaci muke kama aikace-aikacen tsabtar gida, wanda su Yaya Almu suke jagoranta, daga gidan mu bar zuwa fence house babu inda ba a gyarawa tsab. A irin. wannan ranar suma su Umma ba a zaune suke ba, rana ce ta haduwar matan gidan a babban kicin din taraiya na kusa da sashin baba, don shirye-shiryen abincin da za a tanada don Baba da bakin da za su cika gidan don zuwan shi. Kasancewar Umma Karama ce a can ita ce za ta dawo yau tare da shi, sai Umma amarya ta tafi ita da Umma Amaryar ne a gida sune za su jagoranci aikin da za a yin komai na su a tsare yake, tuni sun riga sun shirya duk wani abin da za su yi saboda akwai hadin kai da fahimtar juna 72 cilkin lamarin su. A duk lokacin da Umma za ta yi wani abu tare da Umma Amarya abin kan zo mata da sauki kwarai, saboda irin biyayyar da Umma Amarya ke yi mata, ita kuma tana matukar kokarinta wajen kame ginmanta ba ta yarda ta yi amfani da ra'ayinta kawai wajen zartar da hukunci sai ta saurari na Umma Amarya ko da kuwa ba ta gida to za ta yi waya ta tambayeta hakan nan duk wani abin da za ta saiwa kanta, to takan tabbatar ta sai biyu ne. Wajen karfe goma. sha biyu na shiga kicin din don in kira baba Maigyada ta tayani nawa aikin, saboda nima yau ban shiga aikin tsabtar gida ba, a dalilin ni ce mai yin abincin gida, kuma mafi yawancin yaran yan matan da kan tayani aikin su na wasu aikace-aikacen da aka sanya su tun a lokacin na samu har an gama sinasir, masa, funkaso, da miyoyin su, masu dandano daban- daban an kuma shiga yin wani abin daban. Shia biyu da rabi na yi na bar wa su Baba Maigyada sauran aikin na je na yi wanka, na yi sallah, na yi kwaliya mai ban sha'awa cikin wata atamfar Holland fara sol, zani da riga da dankwalinta. Na sanya sarka da yankunne, awarwaro da zobuna sannan nan yi amfani da jaka da takalmi tare da gyalen da suka dace da kayan. 73 Wani kamshi mai nutsar da zuciya nake yi lokacin da na iso inda Yaya Almu yake zaman jirana a Cikin motar shi ya kuma yi jiran ne don ya san tuni tun ba yau ba tun ina 'yar kankanuwata baba ya sanya dokar tafiya da ni wurin taro shi bai yarda a bar ni a gida in jira isowar shi ba. Ina shiga na zauna na ce mishi; Kar dai har su Yaya Junaidu sun tafi?" Daidai yana kan titi ya ce mini, "Ai sun isa Aiport yanzu muma dai ina ganin daga kafa za mu yi, don kar ya iso ba ma nan." Ba mu fi minti goma da isa airport din ba jiriginsu Baba ya sauka.Yan mutanen da suka fito kadan ne sai ga Unmma Karama ta bayyana Baba yana biye da ita. Cikin zuciyata na ce kai Baba ya more kyawawan mata, to wace ce ba wacce ba a cikin su? Umma Karama doguwar macece ta samanta ba ta da girma sosai, kamar ta kuturinta, sannan fara ce sol tafi duk sauran matan farar fata. Ita kuwa Umma Amarya madaidaicin tsawo ne da ita, wankan tarwada ce, tana da cikakkiyar fuska mai dauke da manyan idanuwa. Sai Ummana wacce take doguwa a tsaye ingarmar mace mai surar jiki mai kyau da bayyanar da yawan shekarunta, kalar jikinta yana tsakanin na Umma Karama ne da 74 Umma Amarya tati wanan ba ta kai wancan ba. Gata da gashin kai mai yawan gaske, har a yanzu da furfura ta soma ratsa shi, tsawon shi da cikar shi yana nan a hakan kuma na san jin Yaya Almu yana gaya mini ke kam in da kin yi sa'a kin dauko gaba daya gashin Umma da ban san abin da kika yi ba. Ni da kaina na san ni din kama da Ummana ake yi a komai in ban da wuri biyu na darata manyan idanuwa sai kuma hasken fata da ban karasata ba, ta dan wadannan abubuwan guda biyu tanan ne nake ganin na dauko Baba, don shi mam Yaya Almu da Yaya Junaidu duk kalarmu kusan daya ne, dan hasken da na fishi bai wuce na ni din, don ina mace ba ne. Motar da, aka dauko Baba na shiga dama kuma haka yake yi in shigo gaba ni da Yaya Junaidu shi da matar da ya dawo da ita kuma suna baya. "Ya ya dai uwata?" Ya yi mini tambayar bayan na gama gaishe su shi da Umma Karama. "Tsakanin Junaidu da Zubairu da Kabiu da Lamido wanene mai takura miki? " Na yi murmushi nace, "Baba ai su Yaya Kabiru su ba sa fada su sai dai kawai a yi ta mutunci da su, babu ruwan su Baba ya yi dariva ya ce. "Sun dai fi Junaidu 75 da Lamido kirki kenan?" Na yi murmushi na ce, 'A'a Baba ba haka nake nufi ba, ba su dai kawai mu'amallar mai dadi ce ba ruwansu da ka ga sun sawa mutum ido in dai ba gani suka yi za a fita can waje ba, shi ne za su ce ina zuwa?" Baba ya yi murmushi ya ce, 'A'a lalle lamarin su.mai dadin ne, to bari tun da ba kya son sa ido zan yi magana da su Junaidun su kawar da idanuwansu daga gare ki kar wanda ya takurawa uwata," Na yi murmushi kawai don na san raha kawai Baba ke mini a dalilin na sha kai karar Yaya Almu wurin shi kan takurawar da yake yi mini sai kawai ya ce mini in je wurn mu ta yi wannan shari'ar amma shi ba zai shiga tsakanin mu ba. don mun fi kusa, Umma kuwa ko akan idonta Yaya Aimu ya yi mini ba ta magana don haka babu amfanin in kai mata karar shi. Muna isa gida sashin Ummana baba ya zarce duk da ya samu mutane da yawa da suka san da zuwan shi, sun zo Suna jiran sh1 al'adar baba ne a duk lokacin da ya iso gida sashin matan shi yake Wucewa sai ya gama gaisuwa da sù, sannan ya taho wurin jama'ar da ya samu mati yawancin lokaci ya kan ci abincin shine tare da su, sannan 76 ya gana da wadanda zai gana da daddare kuma ya kan yi zama tarc da su Yaya Junaidu gaba daya manyan samarin gidan su bata lokaci suna tattauna al'amura hakan nan bai tafiya sai ya samu lokaci ya zaga dakunan kwanan yara ya kuma gan su gaba daya, mun cika falon Baba mu yaran gidan bayan fitowa daga sallar Asuba kananan yara amsa gaisuwar su ya yi suka tafi. Ni da su Anti Rashida da su Yaya Almu kuwa dukkan mu muna ciki har da Umma na ma don ita ce ta kasance tare da shi a zuwan nashi saboda in ya tashi tafiyar zai tafi ne da Umma amarya. Anti Aina'u ta sake gaisheshi ya amsa sannan ta soma zata yi mishi magana akan bukatarsu kan karatun su bai bari ta karasa ba ya katseta ta hanyar ce mata bana zaton hakan zai yiwu kuna nan gidan Aina'u in kun lura sa ku ga ban taba tsare samari da yan mata sun kai matsayin dadewarku ba akwai wani kwadayi da buri da nake dashi ne yasa nayi haka na jira lokaci to yanzu kuwa ina ganin lokacin yayi don haka nan bada dadewa ba zan sallameku ku je dakunan mazajenku ku huta maganar karatunku zai zammo tsakaninku da su ne duk da dukanku abin iko na ne hakan ba zai sa in shiga cikin hakkin aurenku ba saboda haka in kunje gidajenku sai ku yi 77 kokarin sasantawa da su. Ina jin haka na saki wani lallanlausan murmushi da ya kara baiyanar da tsananın farın ciki na na dan mike na duckusa kan kafafuwa na don ya ganni da kyau na ce. "Uhum, Baba." Ya juyo da natsuwarshi zuwa gare ni ya ce. "Menene Uwata?" Na sake sakin wani murmushin kafin nace mishi "Zan zama kenan nice babba a cikin gidan nan idan su anti Kubra suka tafi gidajensu da su yaya Almu dukansu." Baba yayi murmushi ya ce "Ai yan zuma ke ce babba a cikin gidan nan uwata ko da wani wanda ki ke ganin ya girmeki ne? Kece fa uwata ina wani girma daya wuce miki wannan? in kuwva Su Lamido da Junaidu nc suke saki ki ke shakkar hakan bari iny miki maganinsu ina Lamido?" Ya ya Almu ya ce mishi "Gani baba." Baba ya kalleshi ya ce "Kai kafi kowa ta kurawa uwata na hana ku daga yau shekara daya da rabi daya wuce ta kawo min kararka kan kasata girkin da bazata iya ba to daga yau na sauke mata wannan giurkin da ka dora mata karta sake shiga kicin sai don ra'ayinta hakan nan sauran yan matan dukansu a nemt sabbin masu aiki in kuna 78 ganin wadan nan sun girma." Yaya Almu ya amsa ckin ladabi ya ce "To Baba." Baba ya sake kallona ya ce "Yaya da akwai wata mas'alar uwata?" Na yi murmushi na ce "Babu." Ya ce "To dena tunanin wani girma da ya wucc naki na yanzu kece uwar mutanen gidan nan gaba daya don haka kina da girma mai yawa kin ji ko?" Na ce mishi "To baba." Na koma na zauna cikin zuciyata kuwa ina tunanin baba bai gane irin girman da nake nufi ba. Gaba dayanmu baba ya sallemmu bayan ya yi mana addu'a ya sanya mana albarka kowa ya tashi ya fita ni kuwa nayi nufin ci gaba da zamana a wunin sai da yaya Almu ya sake lekowa ya kira ni na tashi naje inda yake tsaye sai kawai ya kalleni ya ce "Mun ke kam zan ga ranar da zakiyi hankali baki ji kalmar da yayi amfani da ita bane wajen sallamar mu?

Chapter 4 of 8