Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 8
kuwa da Asuba ina cikin kwanciyata ina lullu6e cikin bargona mai laushi sai kawai na ji an fige bargon na shiga rarume- rarumen-abin rufawa, ina fadin, "Umma me ye haka? Umma me ye haka? Umma ba na son irin wanna. Kan in karasa fadin abin da zan fada din sai 21 kawai na ji saukar bulala a jikina tsal! Tsal!! Saboda gigicewa sai na saki fitsari akan gadon, kafin na iya kurma ihu da gudu Baba Talatu ta shigo tana fadin, "Me Uwar dakina ta yi wa Lamido? Ka yi hakuri, ka yi hakuri, ka huce ka hadiye wannan fushi da ka yi." Da sauri ya juya ya fita ya bar dakin, ni kuwa na samu damar kurma ihu ina birgima a cikin fitsarin da na yi, ifa kuwa sai rarrashina take yi tana kakkana ni da kyar ta shawo kaina na yarda na je na yi wanka na yi alwala na zo na yi sallah. Tun daga ranar tashi daya Umma take yi mini ta ce mini tashi ki yi alwala ki tafi masallaci an kira sallah, in kuma kin ki kin san sarai Babangida zai shigo bar nan ya zo ya same ki. Ina ii ta fadi hakan zan tashi in je in yi alwala in nufi masallaci, tun ina tashin ina tsaki har na saba ya zame mii dabi'a. A wannan zaman da na yi ne Yaya Almu ya tiasta mini cin abinci, tare da yaran gidan mu. A farko ya hada ni da wadanda na girma da na ce mishi ba su iya tauna ba, kuma in muna cin abinci suna ci mini gabana. Sai ya ce to ya raba ni da su ya hada ni da wadanda suka girme ni, ya kuma gaya mmusu cewar tun da ni ce karamna to ni-ce zan rinka zuwa ina dauko abincin 1n an gama kuma in 22 fita da kwanukan su kuma abin nema ya samu don su dukkansu da wuya in akwai wacce ba ta jin haushina saboda rashin kunyar da na rinka yi musu a baya, don haka gaba dayansu tasa ni a gaba suka yi in na yi magana su kai karata wurin shi, suka hada suka takura mini babu halin in ce na koshi sai su daka mini tsawa su ce kamon wa za ki barwa sudi? Na gaji da matsin su na ce mishi ya maida ni cikin yaran kawai ya ce a'a anan yake son ganina. A haka na zauna a gida har lokacin komawa makaranta ya yi a wannan karon ni da kaima na gayawa Yaya Aimu wasu daga cikin sayayyar da ya yi mini sai dai hakan ba vwai yana nufin na Soma son karatun ba ne, a'a sani dai kawai na yi ya zama dole zan koma don baka a yanzu Allah- Allah nake yi in gama makarantar in dawo gida in ga kuma inda za a sake turani da sunan karatu. A makaranta a yanzu na wastsake na fita daga cikin mafi yawancin wahalhaluna da na yi gamuwa da su a karatuna na junior a yau na zama cikin yan mata masu fada a da yawan yara tsorona suke yi, wasu don tsiwata wasu-kuwa don Kullum cikin ba su abin masarufi nake. A haka har muka zo ajin karshe wato S.S. 3 muka yi jarrabwa muka dawo gida sakamako ya 23 fito na samu C guda biyu da B daya, ba zan iya kwatanta bacin ran Yaya Almu ba, ranar da ya duba sakamakon nawa ya zo ya tasani a gaba ya ce, "Credit a Hausa da Islamic Studies Rabi?"Na bata rai na ce, 'Allah bai wa masu F9 hakuri." Ya kalleni cikin takaici ya ce, "To amin." Alhaji Bello Mustapha sannanan mutum ne da sunan shi. ya riga ya shahara saboda dalilai masu yawa. Farko dai kasancewar shi babban dan kasuwa, yana rike da sarautar gargajiya a garin mu, ban da haka mai taimakon jama'a ne. Gidan mu babban gida ne kwarai, ba zai yiwu in tsaya ina kwatanta girman shi ba, abin da zan iya fadi kawai shine da katangar gidanmu data pen House din mu sune sukamamaye sashin bangaren da mukegaba daya girman gidanmu ya wucea tsaya ana kwatantashi akwai sashin baba dana wurin saukar bakin shi da wurin ajiye motoci da dakunan taro da sashan matanshi guda uku wadanda aka yi musu ne ba da juna akwai sashan yara maza wanda shima kashi biyu yake bangaren samari dana yara kanana haka nan sashin yan mata shima yake ga bangaren masu aiki da wurin yin girki haka nan can karshen bangon gidanmu ta baya wani babban fili ne da aka yi shuke-shuken bisbiyoyi a wurinne kuma 24 baba yake kiwon raguna amma basa iya shigowa cikin gida saboda akillace suke. lyali ne masu yawan gaske a gidanmu a lokacin dana ta so ina kara mata mu kusan arba'in ne yara a gidan maza da mta manya da kuma kanana amma daga cikinmu duka mu biyu ne kadai muke amfani da sunan baba dagani sai yaya Almu duk sauran 'ya'yan dangine dana tsofafftin abokan da aka taso tare don ko akan idona ma an kawo yara da yawa daga kauyenmu wadanda suka isa sawa a makaranta don ma dawowa yaya Almu ya ajiye ka'ida na kawo yaro daya ko biyu daga gida guda in za'a kawo biyun kuma to sharadi ne akawo mace da namiji ba maza kawai ba, shine abin ya danyi sauki amma in da donta babane shi babu ruanshi. kO guda nawa za'a kawo ba zai ce komai ba. Baba mutume mai daukan nauyi da dawainiyar jama'a bai taba gajiya da hidimar mutane ba rikon ya'yna yan uwa da yakeyi ya dauki hidimar komai na al'amarin rayuwarsu bai hanawa kuma iyayensu su taho neman wasu bukatun nasa a wurinshi tun ma ba lokacin damuna ba kullum zaka sameshi yana aiken kudin takin zamani wai wanda zasu yi amfani da shi a gonakinsu wata ran ina tare dashi yana ta fadin 25 abinda za'a baiwa kowanne nace mishi haba baba kudin takin ma kaine maibasu in sunyi nomanfa basa kawo mana komai gidan nan sai ya kalleni yayi murmushi ya ce ai sun taimakeni uwata da suke yarda in sun karbi kudin takin su tsaya su noma gonakin nasu su samu abinda za su ci basu rinka jiran sai ni na kawo musu ba, shi dan uwanka makusanci da ki ke ganishi. yana da hakkin mai girma cikin abinda ka mallaka shi yasa ma baya cikin lissafin mutanen da aka ce ka baiwa zakka kin gane? Na ce mishi eh baba. Baba mutumne mai saukin hali ga sanyin rai ga hakuri ga kanrama mutanen da basu sanshi ba sukan yi mamakin ganinshi in ance musu wannan shine Bello Mustapha' da kuke jin sunanshi saboda sau kin al'amarinshi kullum zaka same shi ne cikin yadi dan shara shura da aka yiwa dinkin kwado da linzami. Dawowar yaya Almu ne ya tsara zaman gidan ya zamo samarin gidan suna da karfi sosai akan al'amuran gida sune ma suke tafiyar da mafi yawancin al'amuran gidan maimakon da da matan gida ne suke sa ido akan komai tunda baba ba mazauni bane. Tsarin da yaya Almu ya yi ne yasa gaba daya 26 yaran gidan suna karkashin kulawar yaya Zubairu ne in an kawo sabbin yara shine zai basu wurin zama da sutura shi zai yi maganar sanya su a makaranta wurishin ake kawo kara babu wani mai hukunta yara a gidanin ba shi ba sabanin da da kowa aka yiwa laifi sai yayi duka to an hana yin hakan babu mai yanci hukunta kowa sai dai a kawo kara wurin yaya Zubairu hakan sai ya tabbatar da bin doka da oda arami ya girmama na gaba da shi shi kuma babba ya yi wa na kasa ashi adalci. Yaya Junaidu kuwa shine yake kula da sito din gida shike fitar da duk wani abin bukata tun daga kayan abinci har zuwa na masarufi duk wani abin amfani a wurinshi akr karba hakan ya taimaka kwarai wajen rage yawan ta'adin da ake yiwa baba a gida haka nan in baba zai zo gida shike zuwa dauko shia airport. Sai yaya Kabiru shine yake. kula da cefanen gidan a hannunshi komai na cefane yake saboda dama matan baba basa cikin wadanda ake yin girkin da su. Shi kuwa yaya Almu shike kula da tsabtar gidan dabbobin gidan da ma'aikata da kuma lafiyar mutanen gidan gaba daya duk wani wanda bai da lafiya wurinshi yake zuwa. 27 Wannan tsari da yaya Almu ya yi ya kawo canji mai yawa da kwanciyar hankali urin mutanen da ke gidan sabanin da da ake gwada karfin tsakanin matan baba in wannan ta bayar da umani sai wannan ta ce a'a ba abinda, za'ayi ba kenan. Kamar yanda ake da manyan samari haka Dan akr da manyan yan mata a wannan lokacin ni bana cikin manyám yan matan gidan don akwai biyar a gabana wadanda a lokacin da nake final year dina a secondary su sun fara karatunsu na HIND' sune su Aina'u, Basira, Rahma, Kubra da Rashida su din su yaya Almu ya baiwa kula da abinda ya shafi yara mata, ganin yanda suke tafiyar da al'amuran shugabancin da aka basu ya sani 2akuwa da ganin anyi musu aure don in zamo ni ce babba a gida tunda sauran 'yan matan da zasu biyo bayana duk na girme su kullum inna kadaice tunanin na baya wuce in aka kawar da su ni yanda zan tafiyar da nawa shugabancin gashi kuma zanyi hakan ne a lokacin da shima yaya Almu ya bar gidan shine kuma dama mai takura min a duk lokacin da nayi wannan tunani to bana sanin lokacin da anke kyalkyalewa da dariya don dadi. Baba yana da wata dabi'a ko al'ada da yake 28 burge mutanen da suka sanshi da ita take kuma kara baiyanar da darajar shi wurin yaran da yake rikewa ita ce ta hada aure a tsakaninsu. A duk lokcin daya reni samari da 'yan mata suka kawo munzalin yin aure mazan suna gama samun aiki zai tarasu ya gaya musu cewar ga 'yan matan da zai basu wane zan hada shi da wance wane ma da wance tun da yake yin hakan kuma bai taba samun tangarda ba. Umma na ita ce matar baba ta farko auren saurayi da budurwa ita ce kuma marikiyar yaya Almu don shi yaya Almu amaryar gidan Umma amarya ita ce ta haifeshi Umma karama itace matar baba ta biyu ita ce kuma ya auro daga cikin dangishi haka nan ita da Ummana sune suke fafata matsanancin kishi a cikin gidan don kuwa har a shekárun nan nasu na girma babu sassauci a cikin lamari don ma dawowan yaya Almu ya dauki matakan kawo gyara a tsakaninsu an kuma samu dan sassauci saboda kasancewar shi wanda Ummana take sauraro yaya Almu ne ya kawo Rarshen zaman wariyar da Ummana da Umma amarya suke yi wa Umma karama. Zuwan shi ne ya ki yarda da wareta da suke yi a cikin dukkan al'amura ya ce lalle ne a rinka sanya ta a ciki tun da dai ita ma matar Baba ce. 29 Ummana tana barin abubuwa da yawa, saboda Yaya Almu misalı, kowa ya san ita da Umma Karama ba sa jituwa, ni da kaina na san ranar da suka yi 'yar tankiya tsakaninsu a falon Baba, don sun hadu dukkansu a can, saboda shi din yana gari Yaya Almu ne ya biyo bayanta har falo ran shi a bace ya zo ya durkusa a gabanta ya ce, 'Umma ashe har yanzu ana yin wannan abin aa gidan nan? Har yanzu ba a kai lokacin da za ki daina sauraron irin wadannan abubuwan ba ki kawar da kan ki akan komai?" Cikin yanayin jin kunya ta ce mishi, Yi hakuri Babangida ni ban san kana wurin ba da ban tanka mata ba." Ya ce mata, "Bana nan a wurin Junaidu ne ya yi waya ya kirani, amma ina so in roke ki daga yau kar ki sake daga ido ki kalleta balle ki gane wani abin da ta yi, don ranki ya baci in kin yi hakan ba tsoronta kike ji ba ni da Rabi kika rufuwa asiri." Ta yi maza ta ce mish1, "Ba za a sake ba na yau din nan shi ne zai zamo na karshe." Ya yi mata godiya ya tashi ya tafi. Ni da kaina ba karamin tsayuwa Yaya Almu ya yi ba katin na rinka zuwa gaida Umma Karama kullunm safiya, saboda a bayyane yake ba ta sona komai 30 kankantar abin da na y1 sai ta ce mini wai ai 1n ban yi haka ba sai a yi mamaki, ko a yi shakkun asalina, in kuma rabon abu take yi sai ta gama rabarwa ni ba ta ba ni ba sai da wata rana ya je ya same ta ya ce mnata don Allah in abin da take da shi bai isa ta bai wa kowa ya samu ba to ta rinka ajiyewa kawai ko kuma ta aika da shi can a waje a bayar sadaka, amma ba a cikin gida a bai wa wasu a hana wasu ba. Ta ce mishi to. Akwai kyakkyawar alaka ta soyayya da biyayya tare da ganin darajar juna tsakanin Yaya Almu da Umma, duk wani abin da ya shafi Umma yana da girma a vwurin shi, ko bakinta ya gani a gidarn karbar da yake yi musu daban ne, ita ce abokiyar shawarar shi kan lkomai in kuwa ya ganta cikin wan: yanayi na daban ya rinka gaya mata maganganu masu dadin j1 kenan da kwantar da hankali, har sai ya ga ta samu nutsuwa. Da yawan mutane dauka suke yi Ummana ita ce mahaifiyar shi, saboda yanda suke ganin mu'amalarsu, ba sau daya ba, ba sau biyu ba ya sha zuba kudin shi ya gyarawa Umma wurinta, saboda kasancewar mafiyawancin bakin da ke Zuwa gidan wurinta suke sauka sai ya zamo a duk lokacin da Baba ya yi musu gyara na ta wurin kan riga na saura bukatar a sake duba shi, a duk 31 lokacin da Yaya Almu ya lura da hakan sai kawai ya sa a fitar da kayan wurinta ya zuba mata sababbi. Shi Yaya Almu da daya ne tamkar da goma kasancewar shi da namiji guda daya da Baba ya haifa bai sa shi ya maida kan shi daban da sauran mutanen da ke gidan ba, yana matukar girmama Yaya Junaidu da Yaya Zubairu, saboda dan girman da suka yi mishi, wanda bai wuce shekara ko shekara da yan watanni ba, komai a ka zo nema a wurin shi sai ya ce a jira sai sun dawo ya yi shawara da su, in kuwa bakin Baba ne suka zo suka same. shi to ya kan saurare su ne kawai idan ya san ba sa nan a gidan, in kuwa suna nan to cewa zai yi bari ya kira musu Yayan shi, ga shi da kokarin gami da tausayin iyaye, tun dawowar shi daga karatu daya nutsu ya soma tafiyar da al'amuran shi a matsayin shi na Lauya, ya shiga taimakon baba da hidimomin gidan ba komai sai an nemi Baba ya yi aiken kudi ba. A lokacin da na ke karama ta babu abin da na ki irin in ga baki sun cika wurin Umma su yi ta furzar mata da goro a ko'ina su ajiye kunshe- kunshen bahunansu masu boye da daddawa da kukar da suke kawo tsaraba. A duk lokacin da na gan su daure fuska nake yi, wani lokacin ma 32 shigewa daki nake yi in yi kwanciyata ko gaishe Su ban fitowa in yi sai in Umma ta kwala mini kira, "Ke Adawiyyah ba ki ji zuwan baki ba ne?" Sannan ne nake fitowa in gaishe su ina gama gaisawar kuma zan fara jidar kayan su ina kaiwa dakin baki, in na gama in ce musu ga kayan ku na kai muku can su ce mini to su bi bayan kayan na Su, babu yanda Umma ba ta yi da ni ba in daina yin hakan na ki kowanne lokaci ta yi mini magana sai na ce mata to tun da yan 'uwansu Baba ne su rinka zuwa gun Baba Karama mana, ita ma ba 'yar uwarsu ba ce sai su zo nan su rinka gurbata miki yanayin wuri da warin daddawa? Kowanne lokaci na fadi hakan ita Umma cewa take yi Allah dai ya shirye ki Adawiyya. Rannan sai muka yi haka da Umma a gaban Yaya Almu bai ce mana komai ba sai da ya tashi zai fita sai ya ce mini, To zo. mu je mana Rabi." Na ce mishi to. Na yi maza na bi bayan shi zuwa dakin shi. Muna shiga ya juyo ya cafke mini kunnena ya rike da karfin shi, sannan ya soma tambayata. "Sau nawa na ji Umma tana yi miki kashedi akan bakinta?" Ihu nake kurmawa, saboda tsananin zafi shi 33 kuwa sai kara matse kunnen yake yi yana fadin, "Sai kin gaya mini abin da ya sa kika maida Umma abokiyar wasan ki, saboda kin ga ba ta iya yi miki komai sai rokon miki shiriya?" Yaya Jnaidu ya turo kofar ya shigo dama kuma su biyu ne da dakin. "Sakar mata kunne Mustapha ko ba ka rike shi ba za ta ji abin da kake son gaya mata." Yaya Almu ya kallé shi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ya ce mishi, "So nake in cire mata wannan guda dayan in barta da daya." Yaya Junaidu ya yi murmushi ya ce, "Kai da Baba kenan in ka cirewa Adawiyyar shi kunne. Ya sa hannu ya rike hannun na shi da ke rike da kunnen nawa ya ce, 'Sake ta." Ya saki kunnen ba tare da ya sake ce mishi komai ba sai dai ya kallen ya ce mini ina so in sake ganin an yi baki kina kwashe musu kayan su ba tare da kin jira an baki umarnin yin hakan ba. Washe gari da safe ya shigo ya same ni a falon Umma ina ganin shi na mike tsaye na fara tafiya ina gaishe shi, bai amsa ba ya ce mini, "Zo mana." Na dawo na ce mishi gani. Ya nuna mini kujera ya ce mini, 'Zauna mu yi hira." Na koma na zauna don tsoro da bin umarni ya zuba mini ido cikin nutsuwa ya ce, "Labari nake so ki ba ni 34 yanzu misali a ce ke din kin je gidan mijinki kin zama uwar gida a wurin mij1 mai yawan jama'a wane irin shugabanci za ki yi?" Na daga ido ina kokarin in kalle shi na kasa saboda yanda ya tsura mini na shi idanun yana kallona. Ya ce, "Gaya mini mana za ki sa hannu biyu ne ki rike shi tare da jama'ar shi ko kuwa za ki watsa mishi su ne?" Na kawar da kaina don kaucewa idanun na shi, sai da na yamutsa fuskata sannan na ce mishi, "To ni zan zama uwar gida ne?" Na tauna bakina kafin na ce mishi ba na so ni in mutum ya ce zai karo wata bayan ni tafiyata zan yi in ba shi wu. Na sake hada rai na ce kai ni in mutum zai auren ma sai na yi mishi kashedi, don ya san da sanin shi yin auren shi bayan nawa auren yana nufin ne kowa ya kama gaban shi tsakanin ni da shi. Zuba mini ido Yaya Almu. ya yi cikin al'ajabin jin kalamaina. Can dai ya daure ya bude baki ya ce mini, "To ita Umma anan gidan baba ya yi sa'a halinta ba irin na ki ba ne, ita ta amince ita din uwargida ce tana kuma iyakacin kokarinta akan hakan....." Tun kan ya karasa na kasa-kasa da muryata na ce mishi, "Madallah. Ya yunkura yana tambayanta, "Me kika ce? 35 Na yi maza na soma yi mishi kuka ina cewa; To ni me na ce?" Ya mike ya kama hanyar fita tare da fadin, Kwanan nan zan yi maganin ki tun da har nima kunkuni za ki fara yi mini." Sati biyu bayan wannan lokacin Yaya Almu ya dawo daga wurin aikin shi ya aiko a kira ni na yi maza na bi dan aiken zuwa wurin shi, don a kwanakin nan duk ni da shi dasawa mukė sai da na bi ta wajen Baba maigyada mai dafa abincin gidan mu nan karbi na Yaya Almu sannan na wuce na je na kai mishih tare da yi mishi sannu da zuwa, sannan na nemi wuri na zauna. Yaya Junaidu ya fito daga bar dakin da ke dakin ya kalli Yaya Almu da ke tashe da kwanon abinci ya ce ni fa gaskiya na gundura da.cin abincin Baba Mai gyadan nan. Yaya Almu ya yi dariya ya ce, "Ka ce dai kawai ka kosa baba ya yi sallama a koma cin na iyali." Yaya Junaidu ya yi murmushi ya ce, "Ba ka ji Zubairu ba rannan yana fadin wai har yanzu Baba bai gane mun girma ba ne." Ya wuce ya fita ya nufi masallaci ya bar Yaya Almu yana dariya, sannan ya kuma soma cin abincin shi Ko loma biyu bai gama hadiyewa bai sai ya kalleni ya ce mini gaskiya Rabi irin 36 tunanin maida girkin gidan ya koma hannun yan matan gidan baba maigyadan nan ta gaji, ni kuma ba zan sake dauko wata mai girkin ba, alhalin ga kartin 'yan mata a gidan. Na yi maza na ce masa, "Eh Yaya Almu ka sa su girkin kawai don in ba haka ba zuwa za su yi suna kwaba muku shirme a gida don ba su iya komai ba in ban da su wanke goma su tsoma biyar in kana so. ka ga kokarin su to wurin iya kwalliya ne kawai, na kuma ji Umma ma rannan da Baba ya yi mata waya tana gaya mishi cewar ya fa tsare ku da yawa gara ya sallame ku haka ya ba ku matanku kowa ya koma inda zai zauna da iyalin shi, tun da duk kun dade kuna aikin ku kai da Yaya Almu ina jin anti Aina'u za a ba ka, don duk cikin su ta fi su iya hadin kwalliya." Dago idon da na yi na kalle shi ne na gane tuni ya dade da hada fuska, nima sai na yi maza na kawar da murmushin ta hanyar tsukewa. Tsaki mai karfi ya ja kafin ya ce mini, "Ki daina na gane ki kunya ta anini ba ki da ita, ni kike yi wa maganar aure? Me kike cewa a yi a sallame mu? " Na yi tsuru-tsuru da ido saboda irin wannan maganar ba ta taba hada ni da shi ba. Washe gari kuwa da safe sai na ji shigowar Yaya Almu wurin Umma. Bayan sun gaisa sai ya 37 ce mata, "Umma da za ki amince da sai yan matan gidan nan su karbi aikin abincin daga hannun Baba Maigyada ita ta zama tana sa musu ido nne kawai, amma ba ta rinka yi ba." Umma ta dan jinjina lamarin kafin ta ce mishi, "Abincin baya dadi ne?" Ya ce, 'A'a Umma mun dai gaji da cin natan Tie kawai ita ma ta dan huta ai ta girma tun muna yara fa muke cin abincinta." Umma ta yi murmushi ta ce, "Za ku gaji da komai ma yanzu ai Alhajin ya rike ku da yawaa a gidan nan bai taba rike samari haka ba ko Kabiru da ya gama karatu baya bayan ku yafi shekara da kama aikin shi rannan ma sai da na ce mishi ni me yake jira da ku ne haka?" Ganin da ta yi Yaya Almu bai amsa maganar tata ba ya sa ta gane kunya yake ji, ta ce mishi, "In kun ga bakan zai gamsar da ku sai ka yi." Ya yi mata godiya kafin ya ce mata,"To Umma tun da su Kubura dukkansu suna zuwa karatu ita Rabi ce har yanzu ba a samar mata wata makarantar ba, saboda matsalar jarrabwarta, ina ganin sai su rinka yi daga Monday zuwa Juma'a na dare kawai ban da na rana, ita sai ta rinka yin na Asabar da Lahadi na rana da na dare." 38 Ina zaunc ina sauraron jin abin da Umma za ta fadi akan wannan mummunan hukunci na Yaya Almu. Sai kawai na ji ta ta ce mishi, "To." Haba ai ban san lokacin da na kurma musu ihu ba, na shiga birgima ina cewa, Gaskiya na gaji na gaji da 'yan ubancin da Yaya Almu yake nuna mini, na gaji da takurar da yake yi mini. Na.gaji da tsanata da ya yi ta sani a gaba ya hana ni sakat, ni da gidan ubana ni ina cikin 'yan matan gidan nan ne da zai yi kason girki har da ni? Gaskiya ni Umma ni ki karban mini. Ban karasa maganar ba na ga ta zabura ta sunkuto wani murfin tangaran da ke gefenta wai shi za ta rotsa mini. Yaya Almu ya yi maza ya tare ta yana fadin; "Ki yi hakuri Umma in na bar ki kika rotsa mata wannan a gabana ai sai yan ubancin na mu ya kara bayyana." Bayan fitar Yaya Almu Umma ko kallona ba ta sake yi ba sai dai na ji ta tana ta rokon min shiriya alamar dai ranta ya kai matuka wajen baci kenan da abin da na yi. Ni kuwa ko a jikina, saboda na samu na dan gayawa Yaya Almu abin da ya dade yana cina a rai, shi ne yan ubanci ke sawa yana takurawa rayuwa ta, yana bakin cikin 39 ganina cikin walwala. Fuskarta a daure ta kalleni ta nuna mini bokitin da ta shake da damammiyar fura ta ce mini, "Dauki ki kai wa su Babangida." Hada fuskar da ta yi ne ya sani daukan bokitin, amma in ban da haka da na ce mata gaskiya Umma aiki wani ya kai musu. Daga nesa na hange shi a kan bayan motar shi yana zaune a gindin bishiya baba maigadi ne á gefen shi a tsaye suna yin hira, na matsa wurin na ce mishi; "Ga damammniyar fura mai sanyi Umma ta ce in kawo muku." Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, "Kai wa su Zubairu suna dakin su sai ki zo." Na je na kai musu na dawo na samu ya sauka daga kan motar yana cikinta har ya tayar da ita shi ma baba maigadi ya tafi ina ce mishi gani ya ce mini shigo mu je in kai ki wani wuri ladan rashin kunyer da kika yi mini. Ban yi musu ba don kuwa ni in har akwai abin da ba ni musun shi to fita yawo nea zaga gari. "Me kike so yau a sai miki?" Na yi maza na ce mishi, "Oho." Ya ce, "Uh kin san ni yanzu lallabaki zan rinka yi tun da kin gane 'yan ubanci ne ya sa na ke yi miki abin da na ke yi miki na takura, na tsane ki na takura miki, 40 na tasaki a gaba abin da kika fada kenan ni kuma a wurina ban taba tsanar ki ba, ban taba takura miki

Chapter 2 of 8