Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
yace mu dan bashi wun ya ga matarshi kafin jama'a su zo." Na bata rai na ce "A'a, to ba Ummana banc a ciki kuma ma ai wasa yake. yi daya fadi hakan ba shima dariya ya yi ba?" Ya ce "Wasa? To daga yau na sake ganin shi 79 da Umma suna ciki kin shigar musu ba tare da kin Jira sun kra ki ba, sai na 6ata miki." Da karfi na ce mishi "Ha'a ba ance muku ku sakar min mara ba?" Ya ce "Ai yanzu ki kace duk maganar da akyi ana dariya ko murmushi wasa ake yi." Ya dan saki fuska ya ce" Wuce muje can falon Umma ki shirya mana abin karyawa kafin ta fito." Na ce "A'a yau baba kadai zan yiwa abin karyawa." Ya ce"To muje ki yi mishin in taya ki." Na waiwaya na kalleshi nayi murmushi na ce "Ka taya ni fa ka ce?" Ya ce"To menene don na taya ki kinyi wa Umma da baba abinda za su ci? Muna cikin din Umma ina aiki na shi kuma yana zaune kan kujera mai tsayi yana gaya min ya kamata ki rinka ganc kingirma rabi ki rinka barin Umma tana morcwa rayuwarta amma ba kowane lokaci kina manne da ita ba tana daki kina daki manne da ita ba tana daki kina daki tana waje kina waje wai babuma inya zo sai kin je kin zauna musu ba zaki barta ita kadai tare da shi ba kamar yanda kowacce a cikinsu take yi. Na 6ata fuska na ce "To meye? " Ya ce "Ba komai bane tunda ta kyaleki kina 80 yi mata shima Baba ya sa muku ido amma ni da wanda ya sa ya shiga tsakani na da mata ta ne? Ranar farko." Da naji yaya Almu ya yi min maganar da ta sahfi matarshi nayi murmushi na ce mishi "Ka ce in na zo gidanku kai da anti Aina'u in bi a hankali." Ya kalleni yayi murmushi ya .ce Wai me yasa ki ke zaban min Aina'u ne a cikin duka 'yan matan?" Na ce mishi "Nafi ganin kyau kwalliyartya in ka lura kwalliyarta daban take da ta sauran ba kowacce irin sutura take sanyawa ba bata kumna dauri ta wani karka toshi, amma kuma kana kallonta ka san yar gaye ce." Na ce "Kuma ta kasa 6oye son da take yi maka." Yayi maza ya tsuke fuska ya ce "Kar ki yi mata sharri to gaya min wacece mai hankalin cikinsu?" Da sauri na ce mishi "Anti Rahma ai ta fisu natsuwa ma ko sallah akan lokaci ta fisu ni nama fison ta saboda mun fi shiri da ita, ita ba ruwanta ma da tadin samari." Ya ce"To me yasa baki yi tunanin ki za 6anmin ita ba tunda gashi ma kuna shiri ko da yake ban tabbatar ba don kuwa kakan yi shin ne 81 da mutumin halaiyar ta dan zo zaya ke kuwa baki da irin halayen nan nata da ki ka lissafa natsuwa, hankali da sallah akan lokaci." Na ce "Uhm, aikina shi kuwa hran yake so mu yi don haka sai ya sake shigo da wani zancen amma ai ina ganin rabi in aka kwashe 'yan matan gidan nan aka yi aurensu aka barki daga ke sai yan yara aiki zai miki yawa. Da sauri na kalleshi na kyalkyale da dariya na ce "Ai ni a dadina babu wani aikin da zai dameni wa za rinka sani? dama kai da yaya Juanidu ne wadannan samarin da za'a barni da su kuwa kwanta-kwata shekara biyu zuwa uku suka bani ba wani takura min da zasu yi don bazan yarda ba shi ya sama tun bara na dena sake musu fuska ko gaishesu zany sai na bata rai don karsu ga alamar wasa suce zasu kawo min raini." Sai da na kawo nan naji gaba na ya fadi nayi maza na waiwaya na kalli fuskarshi don in gani ko yau ma nay subutar bakin nawa dana saba banga alamar hakan ba don haka naci pgaba da yi msih baya ni "Kuna bari gidan nan ko kwana bakwai bazaku yi ba zan fara hawa mota." Ya ce "A'a haba Hajiya zumuzi ai kya bari ki koya." Na yi maza na ce "Ni na dade da iya tuki 82 wurin jul... Nayi maza nayi gum ban karasa ambaton sunan ba, shima sai ya nuna bai gane wanda nayi -niyyar ambaton ba. "Abin karyawan na mutum nawa zaki yi ne?" Na ce "Da Baba da Umma da Umma amarya dani." Ya ce "To ki hada da Umma karama ko kuma ki kai mata na.wajenki ki zo mu karya ana gida." Ya tashi ya fita ya barni ina fadin hu'un. Kwanaki biyun baba sun cka ya kuma dauki amaryarshi sun tafi sun barmu da kewa shi kam yaya Almu ko a jikinshi har mamakinshi nake yi bai taba nuna ya damu da Umma amarya ba balle ka ga alamar wata shakuwa a tsakanin su. Ranar monday na isa wurin 1.T. na a makare saboda a safiyar na muka yi sallama da Baba shima yaya Almu sauke. ni ya yi ckin sauri ya wuce don yana da case a kot yau, cikin ladabi na gaida yallaba ya amsa tare da bina da kallo in ce ko yau daga wurin party ku ke ne ke da yayan naki? Nayi maza na dago ido na kalleshi ya ce "Eh, ai wannan yayan naki yayan zamani ne babu abinda da bazai ya ba ai na ganku shekaran jiya can ranar juma'a da yamma ke da shi saboda haka ban sake karbar wani uzuri ni da shi duk so muke 83 yi don haka babu wani mai haramtawa wani" Nayi shiru ina sauraronshi sai da naji ya yi shiru sai na ce mishi "To ba shi bane shekaran jiya ba muje ko'ina ba ni da shi da yaya Junaidu muka fita." Ya ce "Afto ke ki ce mun duk gidan naku samarin kine to koma dai menene banga laifinsu ba kina da kyau don haka na guji .da zamun zurawa juna ido da muke yi in baki sani ba ni a takure nake yau wa muyi mu'amallar hadin kai kawai ki amfane ni ni ma in amfancki in bak sani ba ita mu'amulla mai dadi in anyi ta babu wanda bata amfani in bazan miki karyar kudi da gold ba tunda ki na dasu ai kuma takardunki zasu biyo ta hannuna knga kenan ina da wani abin yi akanki." Shiru kawai nayi ina sauraronshi dana ji yayi shiru sai kawai na sunkuyar kàn ai kina sha biyu tuna ciki ya mike ya ce "To lokacin break ne yanzu tashi muje mu dawo da sauri. kan ya zo daukan naki, na daga ido na kallesh jikina sai daman rawa yake yi saboda ganin da nayi mishi a tsaye a kaina, ai sai kin tashi min tafi yau na gaji da cintar da ki ke yi min ya miko hannu zai taba min jikina nayi maza na shige karkashin teburin na mukure ina ta faman bashi hakuri. "Ai sai kin fito abin da bai wuce in ture 84 teburin ba." Sai kawai ga yaya Almu a office din ya yi rin shigowar shi da ya saba ta rashin ne izini. Yallabai yana ganinshi ya saki hannuna da ya riga ya kamo yana kokarin jawoni in fito daga karkashin teburin yana fadin fito kawai ba komai a hankali ma za'a gani na fito daga karkashin teburin jiki na sai faman bari ya ke yi kam in gama fitowa tuni yaya Almu ya yi waje na mike ina kuka na biyo bayanshi zan fita shi kuma yallabai yana tambayata wai kukan na menene ko so nake in kulla mai irin janhurun da yan masa suka saba kullawa mutane shi da nan da nake ganinshi babu abin da zai firgita shi don babu Irin mutumin da bai gani ba ban tanka mishi ba, na share hawaye nakwai na fita na taho wurin yaya Almu ina tunania irin tuhumar da zai minkan abin da tarar yana faruwa tsakanina da yallabai. Ina zama a cikin motar ya tasheta cikin sauri ya fada kan hanya bai ce min komai ba ni ma bance mishi ba har muka iso shatatalen unguwar mu yana gama shi yayaya tsaya bai kallen ba, ya ce min sauka ki shiga gida sauri nake yti na dankalleni cikin damuwa na ce mishi dagan da zuwa cikin gida da.. kan in karasa ya daka min tsawa sauka ki bani wuri nace da sauri na fita na 85 bar mishi motarshi na kama hanya ina tafiyaa hankali cikin zuciyata ina tunanin to ni da ba tashi muka yi ba me ya dawo dani gida wannan tafiyar da nake yi ma ai kafin in gama ta an koma break din. Ina shiga falin Umma nayi sa'a na sameta a ciki ita da baba talatu kwanciya nayi a jikinta ina kuka ina gaya mat "Umma bana son 1.T ya isheni a takure nake zama a wurin ki taimake ni ki yiwa yaya Almu magana ni a barin haka bana son karatun bokon wahla yake bani yanzu ma kafafuwana ciwo suke yi min." Baba Talatu tayi maza ta shiga matsaminsu tana fadin "Sannu da kokari uwar dakina." Ina na wurin akwance jikin Umma har yaya Almu ya shigo "Tashi mu je in mai da ke." Na daure fuska na ce. "Ni abarni kawai in huta a gida." Ya ce "Yi hakuri rabin Umma." Umma ta yi dariya ta ce "Haba babangida Adawiyya ai takace tashi ku je tashi tashi maza kina ji yayank yana baki hakuri kina wani minmike." Na mike na tashi naje na samu motar a sashin Umma don haka ban yi tafiya mai yawa ba na bude ta na shiga sai dai zuciyata cike take da 86 tsoro saboda ban san me zai faru ba, tsakanin a da yallabai ni zu manar ba don nasan halin yaya Almu cewa zai yi sharri zan yi mishi nice nake sonshi, haka dai na daure na koma office bayan ya auke ni gabana yana faduwa na shiga office din yallabai yana zaune kankujerarshi kirjina yana bugawa na ce mishi "Barka da aiki yallabai." bai daga ido ya kallen ba, ya masa kanshi a sunkuye. "Yauwa, baiwar Allah." na wuce sum-sum na je na zauna ina aikina ina kuma sauraron abin da zai ce min har aka tashi bai kalli inda nake ba balle.ya yi min wata magana nayi mishi sallama yan labini sai gobe ba, tare da ya kallo ni ya ce min yauwa mu kwana latiya na fito ina mamaki tare da tunanin abin da ya hana yaya Amu zuwa daukana sai da na fito kofar ma'aikatarmu na ganshi a zaune a bayan motarmu yana kallon masu wuce wa na shiga na zauna muka dawo gida tun daga ran nan yaya Almu bai sake leka office dinmu ba in ya zo a waje yake jira na in fito in same shi da na tambaye shi dalili sai ya ce wai ya lura ne bana son shigan nashi danhaka ya dena, shima yallbai bai sake kallona ba balle a ci ga anbaton suna ko har a samuyin wata magana na yi 1.T. na na gama cikin kwanciyar hankali muka yi sallamar arziki sabanin yanda ya yi ta rantsuwar 87 zai rike min takardu na. Kullum na dauko zancen daon in yiwa yaya Almu hirar yallabai da mamakin canzawar shi, sai ya tsuke fuska ya ce wai bawanini daikawai naga na dawo gida bai biyo ni ba nikuma gashi ina mutuwar son shi, a dole na dena kawo mishi hirar yallabai. Ina gama hutun gama I.T. da nayi na sati guda na koma zuwa makaranta karatun da ba wani dadin shi nake ji ba dama dai inyi za'a in maye gurbin carry over da nake da shi a jarrabawa ta ta second semester gashi na ce wa yaya Almu ya je ya ga malamin tun kafin su kai makon ya fito aboda ni ma nasan ban kulla wani abin kirki ba a cikinshi ya ce wai abinda ba zai taba zuwa ya yi ba kenan ya bada wani abu don aba ni cin jarrabawa in bazan yi ba, to inje inyi ta cin carry over ni ta saba shima yaya Junaidu da nayi mishi maganar sai ya ce mun haba Adawiyyah kamar. kikuma sai anje ana neman wani malami don ya baki ci to me zaki yi da wannansakamakon tunda kin san ba na guminki ba ne? Ai kije ki yi jarrabawarki kawai tas zaki cinye sai dai in baki tsaya kin duba note din ki ba. Haka dole na hakura na yi jarrabawar tunda babu halin in gaya musu cewar ba sosai nake 88 hallatar lectures ba. Ana cikin wannan lokacin ne tafiyar Umma ta zo, saboda dawowar Umma Amarya dan kiris ya rage mini in roki Ummana ta bar tafiyar in ya so ita Umma Karama ta je sai na tunan maganar Yaya Almu ta cewar in daina shiga lamarin jin dadin ta da mijinta, don haka na ja bakina na yi shiru muka yi musu rakiya muka dawo na shiga falon ta na zauna cikin kewa da tunanin kwanakin da za ta yi kafin ta dawo. Duk da hirar da su Yaya Zubairu suka zo suka yi mini bai hana ni kewar Umma ba, da sassafe na kama goge hotunta da ke ajiye a falonta da ke ajiye a falonta, duk wanda na goge kuwa sai na zuba mishi ido ina kallonta a jiki tanfar dai na shekara rabona da ita. Sai da na gama wannan aikin na tsabtace ko'ina, sannan na shiga kicin don shirya abin karyawa. Yaya Almu ya shigo ya same ni. "Wa kike yi wa abin karyawa haka bayan Ummana ba ta nan?" Na kalle shi na dan yi murmushi, don na san cewar da ya yi Umman shi ya yi amfani da yanda nake kiranta ne na ce, 'Umma anmarya? Ni fa na ce kai ma za ka iya samu, don na mutum hudi: zuwa biyar na nke shiryawa." Ya ce, "To bari in je in 89 dawo." Sai da na gama komai sannan na dauki abin karyawar na je na kai mata, daga nan na zauna mata muka dan yi hira kafin na dawo saboda na san Yaya Almu zai zo nemana. Na shigo kenan ina shan kunun gyadar da na taho da shi daga wurinta sai ga shi shi ma ya dawo na je na kawo mishi yana karyawa ina gaya mishi. "Umma amarya ta ce in rufe ko'ina in koma can wurin ta." Yaya Almu ya yi maza ya ce, 'A'a Rabi sai dai in so kike duk ki takura mana yanzu nan muu biyu ba za mu iya rike dakin uwar mu ba? Sai kuma kawai don ba ta nan mu rufe wurinta gaba daya mu koma wani wuri? Kenan har yanzu mu din yara ne kanana? Ai kawai mu yi zaman mu anan su Junaidu ne za su rinka zuwa mana hira, kin ga kamar tana nan kenan ko kuwa?" Na ce, "To bari in anjima in na je kai mata abincin rana sai in gaya mata inta yarda shi kenan." Ya cc, "To rokonta za ki yi sai ki gaya mata cewar za ki iya zaman ba cewa za ki yi wan zai taya ki ba." Na ce mishi, "To." Zaman da Yaya Almu ya sani na yi a sashin 90 Umma ya sa baki ba su yanke ba a wurin kowa ya zo nan din dai yake sauka tanfar. dai tana nan. Hakan sai ya sani a cikin kidima da ayuka masu yawan gaske, don sai na zamo ni ce mai karbar su, sai na sauke su anan sannan na ke kai su wajen su wato masaukın su ni ke tsayawa in ga an kai musu wadataccen abincin da zai ishe su, kumna akan lokaci in kuwa gari ya waye ina idar da sallah zan je in ga na ba su ruwan wankan su su da 'ya'yan su, in je in kawo musu abin karyawa, in sun gama in je in sakc kawo wani in ajiye musu, saboda ya'yan su kar su ji yunwa kafin a gama abincin rana. Nan da nan na wastsake na shiga hidimar da da ba na kulawa da ita, sai dai in ga Umma tana ta faman zirga-zirga tana dawainiyar jama'a ban san wahalar abin ba, sai da na samu kai na a cikin shi lokacin ne na gane ashe ba karamar hidima Umma take wuni a cikinta ba, gashi ko na je na samu Umma Amarya na ce mata Umma ga bakin nan sun ce za su tafi sai ta ce ai ba sai kin zo kin gaya mini ba, kina ganin yanda Hajiya Babba take yi ba in na ce ch sai ta ce to je ki ki yi hakan don haka komai zan yi a kan su Yaya Almu nake kira in gaya mishi kamar yanda na ga Umman tana yi. Rannan na sallami wasu baki na yi musu 91 rakiya suka yi wa Umma Karama da Umma Amarya sallama sai da suka tafi na dawo na sanu Yaya Almu a falon shi kadai yana zaune na zo na wuce da doguwar riga a jikina na shiga kicin na dauko filas din kunun gyada na zo na zauna zan sha ya kalleni ya ce, "Kar dai tuntuni ba ki sha kunun nan ba?" Na. ce, "Na jira ne in sallame su su tafi takunna." Ya dago idanuwan shi ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini, "Amma ba ki ga kamar za ki iya gadon Ummana a kan komai ba? Ai na ga kamar za ki iya uwargidanci ki iya sa hannu biyu ki rungumi mijinki, shi da jama'ar shi." Na yi maza na tsuke fuska na ce, "Ni fa ba na Son irin wannan maganar,. na ce ba na son maganar uwargidancin, ni ba na so, ba na so na kara." Na kara fuska ya ce, "To yi hakuri Rabi ba maganar bacin rai ba ne, ni dai ina yi miki sha'awar girman ne tun da kema na ga kina yi wa kan ki." Na yi maza na ce, 'A'a ni ba na yi wa kaina wani sha'awa in dai irin wannan ne." Sati biyu bayan nan na wayi gari cikin murnar cikana shekaru goma sha tara, sai dai abin takaicin shi ne Ummana ba ta nan duk da haka 92 Umma Amarya ta sa an yi ta tuyan masa da funkaso tun cikin dare ana idar da sallar Asuba tasa aka yi ta fita da shi a mota ana kaiwa makarantun allo na cikin gari a gida ma an yi saukar Alkur'ani mai girma abin da na sani kuma shi ne ko Umma da baba suna nan iyakacin abin da za su yi kenan. Na fito daga sashin Umma amarya bayan na yi kwalliyar kara wata shekarar, na je gaisheta. Addu'o'i da nasihohi masu yawa ta yi mini, na shiga falon zuciyata cike da jimamin al'amuran da Umma ta yi mini nasiha a kan su. Ina shiga ko gama zama ban yi sai ga yaya Junaidu ya shigo yana rungume da wani kwali yana ganina ya saki wani irin lallausan murmushi ya ce; "Kai mun ji dadi yau Adawiyya ta kara wata shekarar. Na tayaki murma bebina." Na taya shi murmushin na ce mishi, "Na gode maka Yaya Junaidu." Ya durkusa a gabana ya ce, Dan lumshe mini idanuwan na ki sai na kirya goma kafin ki sake bude su." Na sake yin wani murmushin, sannan na yi mishi yanda ya ce din, na kuma shiga taya shi kirgen cikin nutsuwa, sai na ji ya kai karshe ya ce in bude idona. Na sake yin wani murmushin don 93 dadi wani kayataccen cake ne da aka kayata shi da kalmomi na fatan alheri ya sa yar kankanuwar wukar da ke soke jikin cake din ya yanke dan kankanin loma ya ce, "Bude dan bakin na ki in jefa miki shi a ciki." Ban yi mishi musu ba don haka sai na lumshe idona na bude mishi bakin nawa kamar yanda ya nema sai da na ji gardin shi ya sauka kan harshena sannan ne na maida bakin nawa na rufe na kuma bude idanuwana ina tauna cikin murmushi na ce, "Wace ce ta yi cake din gwana ce kwarai." Ya ce, Uhm Adawiyyah ba ta kai ki iyawa ba, ke dai na sa ta ta yi ne kawai don ina son burge ki." Na sake yin wani murmushin cikin lumshewar idanuwa, saboda tsananin. dadin da nake ciki na ce mishi, "Na gode Yaya Junaidu." Ya mike tsaye alamar fita zai yi ya ce mini, "Bari in je in dawo Adawiyya zan zo in yi miki hira." Na ce to sai ka dawo. Yana fita na kira Hauwa na ba ta cake.din na ce ta je ta yanyanka ta raba musu. Ta ce to, ta dauka ta tafi. Wajen karfe biyu da rabi na barwa Baba Talatu 1ura da sashin Umma na tafi ferce house don amsa kiran da Yaya Almu ya yi mini. A bakin 94 get din shiga wurin na same shi yana sanye da farar kufta ya yi matukar yin kyau yana harde da hannayen shi akan kirjin shi, hanyar da zan fito yake kallo yana ganina ya dan saki ranshi kadan ya dan yi mini kallon sama da kasa, kafin ya ce mini. "Wasa-wasa dai kin iya wani abu." Ya dan mintsina zuciyata na ce, "Ni ma fa ka ce kenan da wacce ta fini?" Na yamutsa fuka na ce, "To ai ko budurwar da za ka aura sai dai ta koya a wurina." Ya zuba mini ido yana kallona a hankali ya ce mini, "To hadiye fushin naki ki maida wukar, in ma abin da na gaya mikin bai yi miki dadi ba ki ranki na yi don in faranta miki rai in taya ki murna Rabo ba don in 6ata miki ba, yanzu ina kike so in kai ki?" Na dan yi shiru kadan cikin tunanin dadin da nake ji ba mai yawa ba ne, a dalilin rashin Umma kusa da ni na ce mishi, "Mu shiga nan kawai." Bai yi musu ba ya wuce gaba na bi bayan shi yana fadin, "Duk yanda kika ce ai hakan za a yi." Mun keta cikin fence house din dawakin suna ganin Yaya Almu suka shiga haniniya, suna zarya, wai su ma nan sun ga wanda suka sani. Na ce, "Oh ka ji mini dawakin nan wai suma sun gane ka." Ya dan kalle su ya ce, "Eh yau da gobe 95 ai ta ki karfin wasa, suma kuma suna irin tasu fahimtar." Na ce haka ne. Cikin gidan katakon yaya Almu ya bude mana komai na ciki a tsare yake gwanin sha'awa ga kamshi ga iskar da ke kadawa ta ko'ina, tana kara nutsar da zukatan dan adam. Ina zama yaya Almu ya miko mini kofin ruwan sanyi na ce, "A'a." Ya ce dan karbi ki sha ko kadan ne ai ruwa rayuwa ne. Ban yi mishi musu ba na karba na sha, shi kuma ya nemi wuri ya zauna yana fadin, "Shekaru goma sha tara ne yau tun da Rabi ta shigo cikin duniyar nan mai cike da al'amura masu ban mamaki da al'ajabi a wancan shekarar kamar yau na gaya miki muhimmancin shekaru goma shatakwas na kira miki su shekarun girmna da hankali da nutsuwa, haka ne ko ba haka ba ne?" A hankali cikin nutsuwa sosai na ba shi amsa da cewar, "Haka ne." Ya sake kallona ya ce, "TTo tun da kin shekara kina da hankali ya kamata a ce mafi yawancin abubuwa na rashin hankali kin rage su, in ma ba ki daina gaba daya ba. Sai na ce to bari yau in yi amfani da muhimmancin ranar wajen baki shawara ina fata ba zan takura miki ba, ko ki dauka ina yawan shiga cikin harkokin ki, tun da baba ya ce bai yarda a yanzu a yi miki 96 hakan ba." Na dan yi murmushi na ce, "A'a babu takura" Ya ce, "To me zai hana ki canza yanayin shigar da kike yi? Ina nufin ta yawan mu'amala da kananan kaya, ba ina nufin ba sa karbarki ba ne, amma ado ne da na ke ganin ya dace ki yi a gidan mijin ki, yanzu ba da ba ne kin riga kin girma, in kowa bai lura da hakan ba, ya kamata ke ki lura da kan ki misali dubi siket din da ke jikin ki, ko gwiwar ki bai rufe ba, sharabarki tana waje ji 'yar rigar da ke jikin ki kin yi kyau har kyau tun da kina da shi, amma bai dace kowa ya rinka ganinki a haka ba. Rabi ai kina da daraja ya kamata a ce kinan rowar kyan jikinki ga mutane da bai dace su rinka gani ba." Na kalleshi cikin sakin fuska na ce mishi, "To. zan gyara. "Kin yarda za ki gyara da gaske?" Na ce. mishi,, "Eh ai in nka ba ni shawara ina amfani da ita." Ya yi maza ya ce, "Haka ne aike mai ganin girman na gaba da ke ne. Rabi to tun da kin yarda za ki gyara bari mu fara gyaran daga yau sai ya zama tun ranar da kika tun daga ranar da kika cika shekaru goma sha tara ba ki sake sanya suturar rashin hankali ba, ko ya ya kika gani? 97 Na dan yi shiru cikin nazari da tunanin abin da hakan ke nufi, kenan ba zan sake sanya kananan kaya ba? Na tuna irin kyan da nake yi a cikin su da nishadin da suke sanyani kan in ce mishi komai sai ya dan matso kusa da ni ya rada mini. "Mafi darajar tuban da ake so bawa ya yi shi ne na barin abu a lokacin da yin abin yake matukar yi mishi dadi, sannan in ba ki sani ba daina sanya su ba yana nufin daina yin kwalliyar ba ne, a'a sai dai fita daga yin wacce ba ta dace ba, zuwa komawa wacce dace da ke." Na gyada kai nuna alamar yarda tare da cewar hakan ne. Yana jin na fadi hakan ya yi maza ya mike ya dakin hutawar baba ya fito rungume da wani dan madaidaicin kwali da aka kawata shi ya sha ado tanfar dai kar a kwance shi a bar shi haka in ya so ma a yafe abin da ke cikin shi, Zuwa ya yi ya ajiye shi a gabana yana kallon cikin sakin fuska. "Zan bude miki kwalin ne ko za ki yi da kan ki?" Na yi murt ushi na ce, "Bari in yi da kaina." Na matso na durkusa a gaban kwalin ina ta faman ailkin daye adon nan da aka kawata shi da shi, har na kai ga jikin kwalin, wani kyakkyawan 98 kati na 1ara gani a jikin shi an yi rubutu kamar haka: Happy Birthday to my lovely sister. " Sannan wasu kalmomi suka biyo baya. Na bude kwalin sosai gaba daya cikin shi dogayen rigunane, hijab, after dress da wani

Chapter 5 of 8