Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
ba, balle in kai ga saki a gaba ni in kika bar nima a wautata sai in ce miki ko Umma ba ta fini sonki ba, sai dai nina bambanta son da nake yi miki da irin wanda ita take yi miki, ita taná yi miki so ne irin wanda babu kwaba a cikin shi, ba ta iya bude ido ta kalle laifin ki, balle ta ga kuskurenki, ta yi miki gyara ita komai kika yi a wurinta daidai ne, saboda ba ta son bacin ranki ba ta so ki wahala, farin cikin ki kawai take son gani, saboda tana so ta jiyar da ke dadi ko da kuwa me hakan yake nufi in ba kya son abu to komai alherin shi sai ta taya ki kin shi." Ya dan waiwayo ya dan kalleni a hankali cikin sakin fuska ya ce, "Soyayyar sangartarwa kenan Rabi, idan na taya Umma muka yi miki irin wannan son dukkan mu to ni da ke ne za mu cutu, don ke kan ki ba za ki ji dadin kan ki ba, ni kuma sai a bar ni da wahalar ki. Wannan dalili ne ya sa na bambanta nawa son da nata mafi girmanyan ubancin da na yi miki dai na san bai wucde raba ki da ita da na yi na kai ki makaranta ba, inda za ki je ki yi wa kan ki komai, ki zauna da mutanen da ba 'yan'uwanki ba ne, balle su saurara miki. Ki yi mu'amalla da mutanen da suko son ki da 41 wadanda ba sa son ki, maimakon zaman ki na gida da kowa gudun bacin ranki yake yi, abin da kika ga dama kuma shi za a yi wannan dai na san shi ne babban 'yan ubancin nawa ko akwai wani da ya fi shi?" Ban tanka mishi ba sai ya ce, "To in ba ki sani ba ni bukatata ta biya kan abin da na yi na kai kis makarantar ne don ki je ki yi mu'amalla da jama'a kin yi don ki koyi ki wa kan ki hidima, kinkoya, da kin tsaya kin yi karatu to da kin jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya, ina nufin kin yi mini nawa kin kuma yi wa kan ki karatu da ba ki yi ba kuma wannan ko a jikina don ni fitowar ki da credit biyu bai shafen ba, na dai ji miki takaici ne kawai a a ce kin shekara shida kina karatu kin fito da credit biyu." Raina ya kara baci da yanda Yaya Almu yake cire mini B3 din da na samu sai credit biyun kawai yake ambata. Wani babban shagon kayan kwalliya ya kai ni ya ce, "Shiga ki zabo abin da kike so dan ni yanzu zan kara ka fa-kaffa da ke ne, don kar ki sake cewa ina yi miki 'yan ubanci, duk abin da kika ce yan ubanci ne ya sa na yi, to ba żan sake, shi ba." Wadannan kalaman na Yaya Aimu ba su sa 42 ya cire ni cikin masu girkin gidan mu ba, kamar yanda na yi zato tun da ya ce ya daina duk wan abin da zan ce 'yan ubanci ne. Ranar da girkin ya iso kaina har dakin Umma ya biyo ni da bulalarshi ta dorina a hannun shi ya ce mini; "Rufin asirin ki kawai shi ne ki fito ki yi girkin nan in kuwa ba haka ba to sai na tara yara kanana, sannan in yi miki dukan tsiya a gaban su. Ya juya ya tafi, sanin halin shi da na yi ya sa ban 6ata lokaci ba na fito cikin zuciyata dai sai fadi nake yi, "Ba ka dai yi sa'a ba, tun da ba kai kadai baba ya haifa ba." Na kama aikin girki duk ranar da ya zo kaina sai kawai in kwaba shi yanda na ga dama, ni kaina ba na iya cin abin da nake girkawan, balle kuma sauran jama'ar da ake yi wa. Yara sun rinka zirga- zirga da kofunan gari kenan ko kuma in sun hango Yaya Junaidu su ruga wurin shi suna tambayar ko akwai indome a store a ba su. Wani lokaci yaba su indome, wani lokaci ya raba musu biredi ya ce su je su sha tea, wani lokacin garin rogo. Rannan ina zaunc a dakin Umma da safe ina shan kunun gyada da Umma amarya ta aiko mini 43 da shi, sai ga Yaya Almu ya shigo. Sa hannu ya yi ya karbe kofin da ke hannuna ya dangwarar ya ce mini, "Wuce mo je." Na tashi sum-sum na bishi. Wurin wankc wanke ya kai ni. Duron guda aka shake da abincin da na yi jiya na rana da na dare aka kasa ci ya kama bakin duron din da hannunshi ya rike yana kallona cikin wani irin yanayi da ke kama da na tausayin kai, ya kalleni cikin nutsuwa ya ce mini. "Wannan abincin da Baba ya nemo ne ya kawo mana don mu ci kika yi dalilin da aka juyec shi anan ana neman inda za a kai shi, don a zubar da shi. Abin abin tausayI ne wai ke daya kamata ya yi kifi kowa jin tausayin shi, ke ce kike jagorancin yi mishi ta'adi, a shekarun shi na girma shckarun da ya kamata ya yi su cikin hutu tare da iyalin shi bai zauna ba, saboda kokarin ganin asirin mu ya rufu, amma bai cancanci tausayawa ba a wurin ki, ko in kina yin hakan ne don in gaji da ganin abin da kike yi in fidda ke cikin masu yin girkin ba zan fidda ki ba, kin fi kowa cancantar ki ciyar da mutanen gidan nan, ban ga dalilin da zai sa ba za ki yi hakan ba, sai ki zauna ke ana yi ana ba ki ranar da babu shi da su Umma kina nufin za mu bar mishi iyalin shi ne yunwa ta 44 watsa mishi su?" Ya yi tambayar cikin wani yanayi da ya sa jikina ya dauki rawa, ya zuba mini ido tsananin bacin ran shi ya kara bayyana. Ya ce, "Kina so ne ki nuna mini ba za ki taya ni rike wa Baba iyalin shi ba? Kina so ne ki nuna mini cewar ba ki san kowa ba, sai kan ki? Yaran gida su rinka kwana da yunwa hankalinki a kwance, saboda ke ba za ki kwana da yuwar ba?" Yana ganin na fara kuka ya wuce ya bar ni a tsaye. Na jima a tsaye a wurin ina kuka, saboda kalaman da ya yi mini da kuma ganewar da na yi ban cutar da kowa ba, sai baba. Na biyo bayan shi don in ba shi hakuri ban gan shi ba, sai Yaya Junaidu na gani yana tsaye ana sauke katon-katon din taliya, yana kallo ana shiryawa a store shi ma cikin bacin ran.yake saboda irin kallon da na ga ya yi mini, kafin ya ce mini; "Mustapha zai zabi daya cikin biyu..." Ban bar shi ya gaya mini dayan biyun da Yaya Almu zai zaba ba, don na san bai wuce kan maganar zaman da yara ke yi da yunwa ranar da na yi girki ba, na durkusa na ce mishi, "Ka yi hakuri Yaya Junaidu." Bai amsa ba na mike ina dawowa kacibis muka yi da Anti Aina'u da Anti Basira. 45 "Ke." Sunan da suka kirani da shi kenan. Na matsa kusa da su na ce musu, "Gani." Anti Aina'u ce ta fara bude baki ta ce mini; "Daga yau kika sake kwaba kwaba66en abincin ki kika turo a kawo mana a ce wai ke kar mu jira ki kin koshi, za ki ga abin da zan yi miki." Ita ma anti Basira ta dalla mini harara ta ce, "Sakaryar yarinya kawai, sokuwa." Na wuce na bar su cikin raina ina cewa na dai kusa hutawa in a ka tattaraku aka kai ku gidajen mazan ku. Gaba daya samarin gidan tsuke mini fuska suka yi ko gaishe su na yi ba sa yi mini amsawar da ta wuce guda daya shi kam yaya Zubairu da yake hakuri bai ishe shi ba, kwakkwara mini zagi ya yi, tare da tambayata so nake in nakasa yara da yunwa? Na ce mishi a'a, ya ce to ke kina cin abincin da kike yin? Na yi shiru ina kallon shi. Ni da Umma gaba daya muka shiga cikin damuwa, don ba'ta son ganina a takure. "In ban da Babrngida ba zai yarda ba ai da sai in sa Talatu ta rinka tayaki wannan aikin a yafi karfinki, ina ke ina girkin abincin mutanen gidan nan?" Ranar Asabar da safe ina gama gaida su Umma wurin yin girkin na nufa ko bari in karya ban yi ba na gayawa Baba Maigyada in masu 46 gyaran wurin sun gama ta sa a kira ni. Na je na duba abin da ake da shi a cikin frezeer na fito na nufi wurin Yaya Kabiru na gaya mishi abin da babu a gida, wanda zan yi amfani da shi ya kalleni ya ce, "Ki je ki yi haka ba zan sayo komai ba, yau don mai bayar da kudin ba a kasa yake debo su ba." Yaya Junaidu da Yaya Almu sun riga sun fita don haka wurin Ummana na koma na gaya mata abin da ake ciki ta yi murmushi ta ce, "Ai shi Alhaji sa'a ne da shi tun da yake bai taba rike dan da bai so shi ba, lissafa abin da kike son sai in sa akai Talatu kasuwa ta sayo miki." Na ce mata to. Na zauna nan lissafo mata kasancewar miyar Afang na yi niyyar yi. Ga lissafin da na bukata. Nama. Barkono Ganda. Maggi, gishiri Busasshen kifi. Albasa Cray fish. Sai kayan kamshi Ganyen Afang Manja Umma ta kalli lissafin nawa tayi murmushi ta ce, 'A ce dai ki iya tsarawa ya yi kyau, to je ki ki duba abin da babu a ciki sai ki zo ki gaya mini." Na ce mata to. Kafin tara rannan na shiga kicin sai da na 47 tafasa ganda ta yi laushi, sannan na hada shi da naman na sake dafa su a tukunya guda daya na kuma zuba musu maggi da gishiri na dauko asalin tukunyar da zan yi miyar a ciki wacce take katuwa sosai na dorata kan wnai kunannen karfe din na zuba wadatacciyan manja da isashsshiyar albasa, ban bari ta gama soyuwa ba na dauko tukunyar da naman nan da ganda suke ciki na juye duk da ruwan ciki na kawo gyararren busashshen kifin na jufa, na kawo garin barkono da kayan kamshi gami da maggi da gishiri na zuba na sa murfi na rufe na bar shi yana ta dahuwa. Jimawa can na kawo ganyen water leafda Baba Maigyada ta yanka mini, na bar shi ya yi kamar minti biyar sannan na juye ganyen Afang din na rufe. Nan da nan kamshi ya gauraye ko'ina. Baba Mai gyada sai salati take yi tana cewa, Yanzu nan ke dama yarinyar nan ashe kin iya girki haka, amma kika rinka tabka irin wannan tsiya? Ai kuwa inda na sani da na gayawa su Lamido cewar dukan tsiya ya kamata su yi miki." Ni kam ban ce mata komai ba, kokari kawai nake yi in ga na gama tare kuma da addu'ar komai ya tafi daidai. Tuwon shinkafa na yi wa mutanen gidan duka, su Baba Maigyada da su Baba Talatu suka tuka shi suka tayani, suka yi mini rabon. Su 48 Yaya Almu kuwa na dafa doya na sa aka daka musu sakwara kafin karfe biyu har na baiwa kowa abincin shi na gama na koma kusa da Umma na kwanta ina kallonta tana cin tuwon da na mata, tare da shan miyar da cokali, dadi ya kamata sai faman sanya mini albarka take yi. Ina idar da sallah sai ga Baba Talatu ta shigo tana tambayata. "Uwar dakina ko dabara za mu yi ne mu yi miki girkin daren?" Na ce mata, 'A'a gani nan fitowa zan zo in dora." Ta ce mini, "To." Ta tafi bayan ta ne na sha kunun zaki da Umma ta ba ni, na dan ji sanyi a raina. Na je na samu har su Baba Maigyada sun shirya mini kurfo-kurfo din sun kunna gawayi don haka ina zuwa na dora sanyawar miya. Baba Maigyada ta ce, "Ke yan nan yi musu dafaduka ki huta. " Na ce mata, "Bari kawai Baba Yaya Junaidu baya son cin shinkafa da daddare.". Ta ce, "Uhu! Haka ne Tuwon alkama miyar kuka na yi, suma sun yi matukar jin dadi. Na gama salamar kowa na dawo daki na shiga cikin baf na kwanta cikin ruwan zafi tsawon lokaci ina tunanin wahalar da na yi a yau wajen aikin abincin gidan nan. Wai a gobe ma haka ake so in sake yi. Na dade a 49 kwance ina tunanin kafin na yi wanka na fito na zo na yi sallah na gyara jikina na zo na zauna gaban Umma tana shafa mini gashin kaina, kafin ta taje mini shi ta tubke mini wuri daya. "Yau kam kin wahala bari zan gayawa Babangida ya rage miki girkin nan." Na yi maza na ce mata, "Bar shi kawai Umma, ya ce mini nina fi kowa cancantar in ciyar da mutanen gidan nan, tun da baba ne ya tara su, to zan yi hakan komai wahalar shi." Umma ta zuba mini ido tana kallon cikin tunani, na san tausayina ne ya kama ta, don haka sai na ce mata, "Kar ki damu Umma nima na riga na gane ya zama dole in zama jaruma ba zai yiwu a ce ni da gidan ubana in zauna sai wasu ne za su rinka yin abincin gidan ba." Ta yi maza ta ce, "Haka ne, haka ne Adawiyyah, Allah dai ya yi miki albarka." Tun tara ba ta yi ba barci ya dauke ni a nan wurin saboda gajiya. Washe gari kuwa Fried Rice na yi. Ga abubuwan da na yi amfani da su: Shinkafa. Tumatur Nama Maggi, gishiri Kwai. Albasa Butter Curry 50 Tumaturin gwangwani. Ga yanda na yi hadin sai da shimkafar ta yi ta tafasa na tsawon minti goma sha biyar sannan na sa aka juyeta a kwanduna ta tsantsame aka ba za ta ta sha iska. Na sa aka yi wa albasa yankan kwabo-kwabo aka yanyanka naman suka zamno yan madaidaita, sannan aka soya su cikin butter na sake. hada shinkafar nan tare da butter da yanlkakken kayan lambun nan su karas, kabeji, koren wake, curry da maggi na gauraya su gaba daya, sannan na nrufe na sake maidawa kan wutar. Bayan na rage mata karfi na soya kwan, sannan a zauna na yi mishi yanka na ban sha'awa. Sannan na sauke shimkafar na shiga yin rabo su Baba Talatu, da Baba Maigyada sai murna suke yi, suna fadin wannan yarinya da iya shege kike yanzu a kwanakin bayan nan wa zai ce kin 1ya girki haka? Da daddare kuma saboda Yaya Junaidu sai na sake. yin tuwon semobita da miyar kubewa bushasshiya suma sun yi dadi ba kadan ba. Tun daga rannan ban sake samun matsala da girkina ba, kullum zan yi abinci zan tabbatar na yi shi mai ban sha'awa a ido, mai dandano a baki. Tuni na maida yin girki daga cikin abubuwan da suke san ya ni nishadi, sai na zamo ba ni da 51 matsalar yawan abincin gidan mu, musamman da na gane yaran gidan ma zumudin zuwan girkin nawa suke yi, don kuwa yan matan gidan da ke biye da ni cika wurin girkin suke yi mu yi ta yi tare da su, suna tambayata anti Adawiyya daga ansa wannan sai wanne kuma? In ce musu sai kaza, shi kuma in an zuba shi minti kaza zai yi kafin a sake zuba wancan. A haka sai in yi girkin in gáma ban galabaitaba, suma su Baba Maigyada wurin girkin sa1 ya zamo musu wurin hira ko ban nemi taimakon su ba za su zo su zauna a yi ta hira ana raha suna taya mu dariya, suna fadin kai yaran nan sai a bar ku. Suma masu gidan su Yaya Almu da su Yaya Basira dadi sosai muke yi da su, tun ma ba Yaya Junaidu ba, wanda ko yaushe zai shigo dakin Umma ya same ni yana zolayata. "Ni Adawiyya ki daure ki karbi girkin gidan nan mana gaba daya." In yi murmushi in ce mishi, "To Yaya Junaidu in ka ce a yi hakan ai sai a yi." Ya zauna mu yi ta hirar mu sai ya ga na fara gyangyadi sannan yake tashi ya fita. Tun da yan matan gidan suka kyalla ido suka ga gaba daya jama'ar gidan kara sona suke yi, saboda gwanintar iya girkina, sai aka shiga 52 gasar girke-girke kowacce wai so take a ce ai ita ce gwana, amma ina? Na riga na yi musu fintinkau. Umma kuwa sai cewa take yi, ai shi girki da kike ganin shi har da baiwa a ciki, ni kam dariya na ke yi in na ji ta fadi haka a zuciyata kuma in ce girkin zamani dai har da koyo a ciki. Tun da na riga na saba da girki ko ba ni ce da shi ba sai in ga ina sha'awar yin shi, don haka sai na shiga shiryawa Ummana abin karyawa da safe in ni ce da girkin kuwa sai Baba Talatu ta yi mana. Rannan ina cikin kicin din Umma ina kokarin shirya mata abin karyawa yayin da ita kuma ta shiga wanka, sai ga Yaya Almu ya shigo cikin kicin din. "Me kike yi ne Rabi na ke jin kamshi haka?" Na yi murmushi na ce mishi, 'Abin karyawa nake yi wa Umma." Ya kara matsowa kusa yana kallon yanda nake gauraya tankadadden garin fulawa da citta a cikin narkakken butter, sugar, zuma, da lemon tsami da ke kan wuta. Ya kasa hakuri da abin da yake ganin ya gaji ya ce mini; "Ni Rabi a ina kika koyi girkine haka?" Na yi murmushi na ce, "Yaya Almu kenan ka mance credit biyun da kake cewa na ci a 53 Jarrabawa akwai wata B3 da baka ambatonta wacce na samu a Home Management" Yaya Almu ya rike baki ya ce, "Haka kuwa aka yi, wato har da girki kika koya a zaman makarantar nan da kika yi?" Na ce mishi, "Eh." Ya ce, "To ya tabbata dai na kin ne kawai ba ki tsaya kin yi ba, amma nawan duka sun samu tun da ko ba komai gashi nan yanzu kowwa zumudin zuwan girkin ki yake yi, yara da manya. To me ya fiye miki haka dadi? Na ce mishi, "Babu." Ban san Umma tana jin mu ba, sai da na ji tana cewa, 'Ai wannan 'yan ubanci da ka yi wa Adawiyya ya yi matukar zama mata alheri tun da ya rufa mata asiri." Yaya Almu ya yi dariya ya zauna muka karya tare da shi. Tun da su Yaya Almu suka gane ina yi wa Umma abin karyawa da safe sai suka maida sashinta wurin karyawar su kullum kuma da irin abin da nake shiryawa. Rannan da rana sai ga Yaya Junaidu ya dawo cikin sauri ina ganin shi na ce lafiya? Ya ce, 'Lafiya Adawiyya na dawo ne zan yi shirin tafiya garin Edo gobe da safe." Na rike baki na ce, "Za ka dade ne?" Ya ce, 'A'a na 54 sati guda zan dai yi missing din ki ne na wannan satin, kin san yanda nake son cin abincin ki kuwa?" Ya zuba mini ido yana kallona, cikin nutsuwa na dan yi murmushi na ce mishi, "Na sani Yaya Junaidu to, bari in je in shirya maka abin da za ka rike ka rinka karyawa da shi." Ya yi maza ya.ce mini, "Ai kuwa da kin taimake ni, don ni lokacin karyawa da abincin dare sunan cikin lokutan da nake so a kula mini daa abin da zan ci sosai." Na ce mishi, "Haka ne." Na juya na tafi na je na soma yin shirye- shiryen yi mishi White Bread da Raisin Bread. A White bread din ga abin da na yi amfani da su: Sugar Ruwan dumi Yeast. Margarine Flour Gishiri Shi kuma Raisin Bread sai na yi amfani da wadannan kayayyakin: Seedless raisin cup Flour. Sugar Baking powder. Kwai 55 Soda. Madara Gishiri. Lemon Tsami Oat. Butter Ina gama wadannan na sake yi mishi Meat Ball shi ma ga kayan hadin shi: Nama Madara Albasa. Flour Garin bredi Kwai Butter. Chese Maggi. Mangyada Gyada mai laushi da gishiri. Ba zan iya kwatanta farin cikin Yaya Junaidu ba, a lokacin da na kai mishi kasa ce mini komai ya yi ya zuba mini ido ya ce, 'Adawiyya mijinki zai more." Na yi maza na rage fara'ata na ce mishi, "Sai ka dawo na." Na juya na koma sashin Ummana. Ni kaina ban san mun shaku da Yaya Junaidu sosai ba, sai a wannan tafiyar tashi duk da gidan mu cike yake da jama'a ina kuma da al'amuran yi masu yawa kewar shi sosai na yi don kuwa mutam ne ma'abocin hakuri da juriya ga na kasa da shi, mu'amalla da shi kuwa mai dadi ne sosai, saboda komai na shi akwai 'yanci mai yawa a cikin shi, saboda ya san yancin dan adam. Yaya Junaidu yana cikin mutanen da na sha jin Ummna 56 tana cewa ba za ta mance dawainiyar da suka yi mata da ni ba, ita da kanta tana mutunta shi, haka nan kasancewar shi dan'wan Baba ya sanya shi ya zamo mai karfi sosai a wurin Baban, kuma yardajjen shi mafi yawancm al'amuran da yakan wakilta a yi mishi in dai akan dukiya ne to shi yake dorawa a kai. Mu'amallar shi da Baba mai karfi ce kwarai ban da zamowar shi shi ne mai zuwa ya dauko shi in zai zo gida, babu kan yarda wani ya tuka shi ne kawai in dai yana gari a lokacin da yaya Junaidu baya nan ko yana wurin aiki shi din mutum ne mai cikar halitta yana matukar kama da Yaya Almu, ma'abocin yi ado ne, yana kuma kyau da adon. Mutum ne shi da bai cika son hayaniya ba, 8ai dai yakan yi magana cikin nutsuwa, ga shi da ilimi don ba na mantawa a ranar da baba ya dawo gida na kai mishi sakamakona na gama Secondary ya karba ya gani .ya yi ta yabon kokarina, wanda ba haka Yaya Almu ya so ba, da ya miko mini takardar cewa ya yi; "Maza je ki ki Boye abincki kin yi kokari kar ki yarda ki bari Junaidu ya gane miki ita, don kar ya yi miki ba daidai ba, kin san shi a lokacin da va gama karatun shi na Secondary Excellent bakwai da Credit biyu ya fito da su." 57 Ya juya wurin Junaidu cikin fara'a ya ce mishi, "Baka ga takardar ta ba ko?" Ya ce mishi, "Na gani Baba sai dai ban lura da abin da yake cikinta ba." Yana dariya ya ce, "Yauwa to ka kyauta da ka yi hakan, ka kuma yi dabara kwarai." Ni kaina na san Yaya Junaidu yana cikin yayyena da na ke so, nake girmamawa, nake kuma yawan mu'amalla da su zan iya cewa ma mu'amalla da shi kan yi mini dadi akan da Yaya Almu, saboda shi Yaya Almu akwai tsoro mai yawa a tsakanina da shi, sai kuwa Yaya Junaidu komai na shi mai sauki ne babu fada, babu zare ido balle ga yin barazana ko duka. Sati guda Yaya Junaidu ya yi kafin ya dawo, tun safe ya yi waya ya taso amma. bai iso ba sai gab da za a yi sallar Magriba. Yana isowa sashin Umma ya fara ziwa dama kuma dukkan su al'sdar Su, kenan duk inda suka je suka dawo. to wurin Umma za su fara zuwa, su gaishe ta kafin su je su gaida sauran matan gidan. Ina ganin shi na yi tsalle na karbi jakar da ke hannun shi. Ina ta tsalle kamar wata 'yar karamar yarinya, Umma ta ce, "Kai ke kam Adawiyya Allah ya shirye ki har yanzu ba ki daina yi wa Junaidu irin wannan oyoyon ba?" Yaya Junaidu ya yi murmushi ya zauna a kasa a gabanta suna gaisawa 58 tana tambayar shi labarin hanya yana gaya mata al wurin da nisa. Umma suka dan yi hira da ya tashi za1 fita sai ya ce mini ina fata kin tanadar mini abin da zan ci don tun sauran bread din ki da na ci da safe ban sake cin komai ba. Na ce,"Na yi maka girki, amma ina ganin ba za su hanaka cin abincin gida ba. Anti Basira ce ta yi girkin na kuma ji Umma ta ce ya yi dadi, don ta kawo mata." "Ke ba ki ci ba kenan?" Na ce, "Eh, saboda ban sha ruwa ba tukunna na yi azumi." Ya ce,"To bari in je in gaida su Umma kafin a yi kiran sallah ni in yi sallah in yi wanka, ke kuma kin sha ruwa sa1 ki kawo mini dakin mu." Na ce mishi to. Sai da na gama shan ruwa, sannan na dauki abin da na shirya mishi na je na kai mishi shi da Yaya Almu na samu a.cikin dakin na su suna hirar tafiyar tashi. Na je na duruksa na gaida Yaya Almu kafin na sake yi mishi sannu da zuwa na ajiye mishi kwanukan da na zo mi shi da su a gaban shi na kuma bude mishi ya zuba ido yana kallo cikin murnmushi; "Ke Adawiyya ba zan ci girkin nan na ki ba, sai kin gaya mini sunan shi da yanda kika yi kika 59 yi

Chapter 3 of 8