Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
gunki tamkar almajiri agaban malaminsa shamharu na cikin bincikensa saiyaji motsi acikin aljihun rigarsa al'amarin daya bashi mamaki kenan domin asaninsa bai ajiye komaiba acikin aljihun nasa kawai saiyha zura hannunsa a cikin aljihun mai zurfin rijiya gaba dubu ya kwaso abinda ke aljihun nasa ya watsa bisa bisa tebur din dake gabansa bisa mamaki saiyaga ashe boka jinsan,boka sulbaini,markahus sabus ,aljni durfus,da bokanya samaratune sai asannan shamharu ya tuno da cewa shida kansa ya watsasu acikin aljihun nasa. shamharu ya dubesu daya bayan daya dukda sun kasance mitsi mitsi agabansa sannan ya bushe da dariya.yace yanzu ku nan atunaninku zaku iya ja dani? shiyasa kuke tunanin yadda saku aiko aljani balbus yazo har nan ya sato muku addar tsafi hakika kun tafka babban kuskure wanda zai zamo muku abin nadama lu'umanu ya karewa markahus sabus kallo sannan ya dubi sarki shamharu yace ya shugaba na ai wannan markahus sabus ne wanda y nemi matata fatisa nasa aka sashi acikin akwatin karfe aka kulle acan kurkuna dake karkashin kasa shamharu yace kwarai kuwa shine abinda baka saniba ai su jafar je suka fito dashi suka turashi yaje ya samo musu kubar miftahul zarbil har suka sami narar bude kundun tsatsuba kai makahus sabus k cika tsinanne,matsiyaci domin .duk bala'in nan dana shiga kaine sanadi inda bakaje ka dauko kubar mitahul zarbil ba da yanzu hankali na akwance yake lallai kaine k bankada sirrina ga duniya idan kuwa kanason ka tsira da rayuwarka dolene ka sake rufe wannan sirrin kodajin haka sai markahus sabus ya rissina agaban shamharu yace ya shugaba na idan kwai yadda zanyi na rufe wannan sirri nka zanyi ko menene koda kuwa zan rasa rayuwata shamharu ya tuntsure da dariya sannan yace hakika akwai yadda zaka rufe wannan sirri nawa zan turaku ku tafi izuw aiwatar da wani aiki ku hudu banda mahaifiyarka samaratu damin zan tsareta anan harsai kun sami nasara kun dawo gareni sannan n sake ku gaba daya ku koma duniyarku idan kuwa bakuyi nasara ba zan kashe mahifiyarka sannan kuma na hallakku gabA daya kodajin haka saihankalin markahs sabus ya tashi ya rasa abin dake masa dadi aduniya lu'umanu ya dubshi yace haba jarumi uban jarumai ka tunaa cewa kaine ka kara da dodo kiryanu harka debo tsumin tsafinsa kaine aljanin da baisam tsoro ba kuma kaine sarkin sa'a da nasara wanda bai san bacin ranaba markashu sabus yayi yake yace haba lu'umanu ai indai jaruntaka nake takama da ita da tsagwaron karfi ban kaika ba meyasa kai baka tafi aiwatar da wannan aiki ba wanda za'atura mu yi? lu'umanu yayi shiru ɓaice komaiba don baisan amsaar da zai bayarba shikuwa shamharu saiya busheda dariya yace wannan matsalar kuce ku biyu kai darfus nasan cewa kafi jinshan,sulbaini da markahussabus karfin sihiri ayanzu don haka dolene ka zamo jagoran wannan tafiya.da za'ayi don samo abubuwa guda uku wadanda dasune zan kera kubar muftahul zarbil wacce bude fadar saukatul askur ta sarki azmul gallar don na dauko kundun tsatsubansa kaikuma markahus sabus nasan kafisu hikima,rashin tsoro da juriya domin gado kayi wajen mahaifinka larkatul bin sabus lallai kaine jarumin wannan tafiya da za'ayi kafin n gaya muku abubuwan da zaku samo mini kuma na sallameku inda akwai mai tambaya yayi tambayar sa naji gaba dayansu sukayi shiru sai markahus sabus yace ya shugabana tambaya ta guda biyu ce kacal inaso kayi mana bayani akan wanene azmul gallar tambaya ta biyu itace dama akwai wani kundun tsatsuban daban banda naka wanda su jafar suka bude? kodajin wadannan tambayoyi sai shamharu yayi murmushi yace gaisheka dan masu hikima hakika kayi tambayoyi masu amfani saidai basu da mahimmanci acikin wannan tafiya da zakuyi ku sni cewa sarki azmul gallar wani basarake ne dake mulkin wata babbar duniya daga cikin duniyoyin sama shikuwa kundun tsatsuba guda uku ne akwai kundi nafarko wato nawa wanda su jafar suke karantawa sannan akwai kundi na biyu wanda ahalin yanzu su ruziyal suke karanta wa shikuwa kundi na uku yana nan an kammala kuma an ajiyeshi acikin fadar azmul gallar acan duniyar sama.wannan kundin ne wanda nakeso naje na dauko amma dole saina mallaki kubar miftahul zarbil wacce da taimakon kune zan kerata abu na farko da zaku tafi nema shine narkakken dutsen da yafi kowanne dutse girma aduniya shidai wannan yanzu haka yana can wani tsubiri da ake kira narul mahut acan kusa da karshen duniya bangon kudu kuyi sani cewa babu komai awannan tsauni face duwatsu kala kala wadanda akarkashinsu wutace takeci fiye da shekara dubu arɓa'in duk shekara sai daya daga cikin duwatsun yayi bindiga ya tarwatse saidai kaga tafasasshen dutse ya cika dajin gaba daya ya zama kamar teku idan kukayi rashin sa'a kukaje wannan tsubiri alokacin da daya daga cikin duwatsun ua fashe kuma narkewa zakuyi saboda tsananin zafin dajin dolene kuje inda wannan babban dutse yake wanda yafi sauran girma kuyi haka akansa zira'i dubu arba'in sannan ku debo narkakken dutsen da kuka tarar ku kawo mini abu na biyu da zaku kawo mini shine dutsen wutar dake duniyar ku zuwa wannan duniya tafiyace ta shekara dubu arba'in amma zan sanyaku acikin sundukin tsafi wanda zai kaiku acikin kwanaki hudu a inda zaku debo wannan dutsen wuta akwai wasu halittu masu kama d birrai hikimar kuce kawai zata kwace ku ahannunsu har ku iya debo dutsen wutar ku baro duniyar su abu na uku da zaku debo shine rabin ruwan tekun duniya nasan zakuyi mamaki kuce tayaya zaku iya debo wannan ruwa to ku sani cewa zan baku wani siririn bututun tsafi wanda dashine zaku tafi tsakiyar bahar zulmus ku sani cewa ita bahar zulmus itace cibiyar dukkanin tekunan duniya anan ne zaku tsoma bututun tsafin dazan baku kuna tsomashi zakuga ruwa yayi tsiri yana tafiya sama ,asaman ne ruwan yana rikida yana zama hayaki sai ruwan yayi kwana arba'in yana tsiri asaman shikuwa wannan hayakin gaba dayansa zai koma cikin bututun dana baku ya rufekansa kuma shine rabin ruwan tekun duniya indai kuka sami naaarar kawo mini shi sai anyi wahalar ruwan sha aduniyarku domin tekuna da koguna da koramai zasu kafe d yawansu koda shamharu yazo nan azancensa saiya dauko abubuwa guda uku ya ajiye agabansu markahus sabus,abu na farko shine gatari wanda aka kerashi da lu'u lu'u abu na biyu sundukin tsafine abu na uku kuwa shine bututun tsafi shamharu yace ga kayan aikin nan na baku yanzu zan hadaku da bokin tafiya wanda dashi zakuje wadannan gurare gaba da ya kafin wani daga Cikin su markahus sabus yace wani abu tuni shamharu ya kira wani aljani waishi darmazulu take aljani darmazulu ya bayyana. MATSATSUBI B PART 7 Author:-ABDL'AZIZ SANI MADAKIN GINI TYPING:-HABIBULLAH KBR Posting:-Ahmad Munir Muhammad Durmazulu yakasance gabjejen gaske domin ya ninka shikansa shamharu agirma sau goma yana da fuka fukai guda miliyan daya guda dubu dari biyar akwibinsa na hagu dari biyar akwibinsa na dama durmazulu n iya zuwa duniyar kasa daga fadar boka shamharu ta baharzus adakika arb'in duk duniya babu wani aljani mai karfin gudunsa awannan lokaci shamharu ya dubi durmazulu yace na umarceka daka dauki su markahus sabus da kayan aikinsu ku tafi izuwa wuraren nan uku don samo mini mahadin kera kubar miftahul zarbil kodajin haka sai durmazulu yace angama ya shugabana kaine MATSATSUBI uban KUNDUN TSATSUBA ita kanta TSATSUBAR IDAN TA GANKA FIRGICEWA TAKE shamharu yayi dariya saboda jin dadin wannan kirari da aljanin yayi masa sannan yace kaidai bari kawai ai har yanzu da saurana domin sai kun kawo min wadannan abubuwa uku sannan zan zan cika MATSATSUBI uban TSATSUBA kafin shamharu ya gama rufe bakinsa tuni aljani durmazulu ya suri su markahus sabus ya dora abayansa harma ya hada da samaratu saida shamharu ya fisgota ya ajiyeta kasa yana mai cewa banda wannan durmazulu y sake debo kayan aikinsu markahus sabus guda uku ya azasu abayansa sannan ya bude fukafukansa gaba daya guda miliyan daya ya tashi sama ya ratsa ta cikin saman ginin fadar baharzus kamar haske sannan ya cilla da gudu ya iso duniya su jafar inda za'a samo wadannan abubuwa guda uku WANNAN SHINE ABINDA YA FARU TSAKANIN SU MARKAHUS SABUS DA BOKA SHAMHARU SHAHARARRE ACAN FADARSA TA BAHAR ZUS WACCE KE SARARIN SAMANIYA Al'amarin su sarki hudes kuwa bayan sun dauke jarumi hubairu daga birnin tehran sa'adda aka fafata kazamin yaki tsakanin sarki lu'umanu mai rai dubu sai suka tafi dasu izuwa birnin sarki hudes har aka sauka agidan sarautar gimbiya sima bata farfadoba saukarsu keda wuya saiga abtarul hudes tsaye abakin kofar fada kamar dama yasan da zuwansu koda jarumi hubairu ya hango abtarul hudes sai ya rugo gareshi suka rungume juna cikin farin ciki nandai aka dunguma gaba daya aka shiga cikin fadar aka zazzauna abtarul hudes ya kawowa hubairu da kuddaru abinci da abin sha irin nasu na bil'adama suka kimtsa cikinsu awannan rana dai babu wanda yafi waziri kuddaru farin ciki saboda ganin ya kubuta daga hannun sarki lu'umanu saidai har yanzu hankalinsa nakan gimbiya sima wacce aka shimfide ta bisa wata kujera akwance cikin halin barci koda aljani abtarul hudes ya ga cewa waziri kuddaru na cikin damuwa bisa halin da sima ke ciki sai ya dubeshi yayi murmushi yace yakai kuddaru ka kwantar da hankalinka ka sani cewa babu abinda zai taba lafiyar sarauniyarka gimbiya sima lallai tana bukatar addu'a sosai domin sarki lu'umanu ya juyar mata da kwakwalwa koda jin wannan batu sai jarumi hubairu ya yi ajiyar numfashi yace haba nifa mamakin yadda sima taso ta hallakani da hannunta alhalin ta kasance mai matukar kaunata jini da tsoka hakika sarki lu'umanu ya kasance hatsabibin gaske hubairu na gama fadin haka kenan sukaga sarki hudes tareda manyan malaman garin sunyiwa sima kawanya suna karanta addu'o'i suna tofa mata bayan kamar dakika arba'in da kammala addu'o'in sai 'yan yatsun hannun gimbiya sima suka fara motsi daga can kuma sai tayi attishawa sau uku ta mike zumbur tana mai fadin innalillahi wa inna ilaihirra ji'un gaba daya musulman aljanun suka dauka da alhamdulillah cikin farin ciki abtarul hudes ya rungume hubairu yana. cewa barkanmu masoyiyarka ta sami lafiya koda gimbiya sima ta kyallara ido taga kuddaru da jarumi hubairu saita cika da tsananin mamaki cikin murmushi ta dubi kuddaru tace yakai kuddaru yaushene zamu koma gidane? kuma nan inane? waziri kuddaru ya rugo gareta ya rissina yana mai kwasar gaisuwa yace ya shugabata kiyi sani cewa abubuwa da dama sun faru abaya tsawon kwanaki masu yawa bakisan da faruwarsuba don bakya cikin hayyacinki labarine mai tsawo wanda ya isa a rubuta littafi babba akansa yanzu dai saimu godewa allah tunda mun samu kanmu sai kuma batun komawa birnin luharim kici gaba da mulkinki sima ta sauko saga kan kujerar. da take zaune ta ruga ga jarumi hubairu suka rungume juna cikin farin ciki her suna zubarda hawaye asannan ne sarki hudes ya taho garesu koda ganinsa sai hubairu ya rissina yayi godiya bisa taimakon gaggawan da ya basu ya ceci rayuwarsu daga hannun sarki lu'umanu sarki hudes yayi murmushi yace yakai wannan jarumi kayi sani cewa bani zakayiwa godiyaba allah zaka godewa ka sani cewa ya zama wajibi agareni na yaki mushrikai adoron kasa, kuma bazan gusheba ina wannan aiki harsai ajalina. ya riskeni, yanzu babu abinda zakuyi face ku tafi izuwa birnin laharim don a daura aurenku acan amma wannan tafiya bazata yiwuba face na baku kyakykyawan tsaro kuma dolene ku rike wadansu addu'o'i wadanda zakuyita yinsu harku isa can birnin luharim akwai wadansu 'yan kyaututtuka da nake son na baku na wadansu littattafan addini dana tarihi da kuma wadansu sitturu da kayan ado amatsayin tawa gudunmawar ta aurenku wadannan kayayyaki na can ajiye agidan ajiye kayan tarihin kasarnan don haka saiku saurara na aika aje a debo muku kayan nanda rabin sa'a domin wajen nada dan nisa wani garine da ake kira madinatul auzal kodajin wannan batu sai gimbiya sima ta cika d farinciki tace yakai wannan sarki kayi sani cewa nakasance mai matukar sha'awar tafiya bisa doron kasa don na morewa idanuna kallon abubuwan al'ajabi dana tarihi don haka zanso ace ka shirya mana wannan tafiyar bisa dawakai muje birnin madinatul auzal naga wannan gida na kayan tarihin ku da idanuna sarki hudes yayi murmushi yace ai wannan mai saukine saidai kawai maimakon aje madinatul auzal acikin rabin sa'a sai anyi sa'a uku sarki hudes ya dubi dansa abtarul hudes yace yakai dana ka sani cewa kai zan baiwa jagoran wannan tafiya kuma zan hadaka da dakaru dubu goma don ku tsare lafiyarsu gimbiy sima don haka tabbas nasan sai makiya sun biyo bayanku nantake sarki hudes ya kira sarkin kira aljani ikmal yace yaje ya kera sabon keken doki mai karko sosai da zallan karfe wanda ingarman dawakai shida zasu ja ikmal ya rissina yace angamayq shugabana, kamar walkiya ikmal ya bace shikuma sarki hudes saiya shiga cikin turakarsa ya dauko rantsatstsiyar takobinsa ta yaki ya baiwa abtarul hudes yace ga wannan ka tafi da ita zatayi maka amfani matuka abtarul hudes ya karbi takobin cikin murna ya ratayata akafadarsa dama ya dade yanason abashi aron takobin amma anki itadai wannan takobi ta sarki hudes na dauke da rubutun wasu addu'o'i guda dari ba daya addu'o'in gaba daya na neman tsarine bisa shaidanu da kuma samun nasara akansu tun sa'adda sarki hudes ya mallaki wannan takobi bai taba jagorantar yaki anyi galaba akansa ba saidai a gudu abarshi bayan kamar dakika dari hudu da sittin da tafiyar sarkin kira aljani ikmal sai gashi ya dawo dauke da sabon keken doki na karfe zalla mai kyan gaske harda kosassun dawakai guda shida daure ajiki bisa tafin hannunsa ikmal ya ajiye hannunsa akas ahankali dawakan nan suka ja keken dokin suka sauka daga kan tafin hannunsa suka tsaya kyam awaje guda koda gimbiya sima da jarumi hubairu sukaga keken dokin saiya yi matukar basu sha'awa suka hau dudduba keken dokin ba tareda bata lokaciba sarki hudes yayi bankwana dasu hubairu kuma yayi musu addu'ar tsari domin daga can birnin madinatul auzal zasu wucene birnin luharim inda za'a daura aurensu hubairu da gimbiya sima suka shiga cikin keken dokin shikuwa kuddaru saiya hau kan daya daga cikin dawakan keken dokin ya zauna take aka ware dakarun musulunci guda dubu goma wadanda zasuyi musu rakiya har izuwa can birnin luharim sarki hudes ya raba dakarun kaso uku kashi na farko suka tsaya a sama gaban keken dokin su hubairu kaso na biyu agefe da gefen keken dokin kaso na uku kuma bayan keken dokin ba tareda bata lokaciba aka kama hanya akayita tafiya sauri sauri gudu gudu don a isa birnin madinatul aulaz inda kayan tarihi suke da wuri saida akayi rabin tafiya cikin kwanciyar hankali ya zamana jarumi hubairu da gimbiya sima sun shagala suna ta yin hirarsu ta ma'abota soyayya a wannan lokaci aljani abtarul hudes na saman keken dokin yana kada fuka fukansa hannunsa na dama na dafe da rantsatstsiyar takobinsa kuma yana kalle kalle da waige waige don tabbatar da tsaro koda akazo tsakiyar wata gada wacce kasanta ramine mai zurfi sai dawakan nan guda shida sukayi turjiya suka daga kafafuwansu sama cikin alamun razana suna masu son juyawa da baya, al'amarin daya baiwa su abtarul hudes mamaki kenan don basu san dalili ba hubairu da gimbiya sima kuwa wadanda suka shagala da hirar soyayya sai sukaji keken dokin yayi girgiza kuma an tsaya cak cikin fargaba suka leko waje ta cikin tagar keken dokin don suga abinda ke faruwa ashe gungun dakarun bakaken aljanu ne suka tsorata dawakan wadanda suka baiyana agabansu kamar walkiya. A DAI-DAI NAN LITTAFI NA UKU YA KARE, DON HAKA SAI KU SAURAREMU RANAR LARABA DOMIN JIN CIGABA☝️☝️✍️✍️✍️🙏🙏 FATAN ALHERI. DOCUMENT COMPILED BY SHURAIHU USMAN TYPING HABIBULLAH MUHAMMAD KABARA POSTED BY NAJIBULLAH MUHAMMAD An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6