Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
wato goga balmus, koda ya ganshi sai jikinsa ya kama bari shikuwa goga balmus saiya tuntsure da dariya yace kaga idan kana son ka tsira da rayuwArka kawai ka bani makullin miftahul dinar ka juya da baya ka sani cewa yau shekarata dubu hudu ina labe abayan taskar dukiyar saubatul azwas ina jiran ranar da za'ayi mantuwa abar kubar ajikin kofar kogon amma ba'a taba yin mantuwabarba, sai gashi yau akaron banza ta dauki kubar da hannunta ta baka, duk abinda ya faru tsakanin ka da Ita na gani amadubin tsafina ina horonka daka gaggauta bani kubar nan kafin saubatul azwas tazo nan ta riskemu kodajin wannan batu saì kalmus yayi ajiyar numfashi yace tabdijan ainima shekarata dubu shida ina sauraron dazan sami wannan damar ya za'ayi akaron banza kazo akaron banza ka kwace tabbas idan kaga ka mallaki wannan kuba bana numfashi kafin ya gama rufe baki tuni goga balmus ya zare takobinsa ya kai masa wawan sara, nanfa suka kaure da matsiyacin fada asaman teku sukayi wa junansu jina jina sannan goga balmus ya sami nasarar rike kubar miftahul dinar nanfa suka ci gaba da kokarin fizge kubar kowa yana ja in ja kuma suka cigaba da saran juna adaidai wannan lokacin ne na riskesu saboda tsananin razana da ganina sai suka saki kubar miftahul dinar kowannensu ya cika wandonssa da iska itakuwa kubar miftahul dinar saita nutse acikin teku nan fa na shiga cikin tekun nayita lalube iyakar kokarina amma ban gantaba hakika nayi matukar mamakin batan kubar miftahul dinar acikin tekun kuma nayi iyakar binciikena amadubin tsafi amma bangano inda takeba daga nan ne na dawo wajenki yake kawata tazubul luhucul yanzu zan tafi dake izuwa dakin tsafina don mu zauna mucigaba da jiran lokacinda ajalin sarakunan guda shida nan zaizo don mu ci gaba da hada tsafin mu na gano inda sihirin tsafin yake tazubul luhucul tayi murnushi tace hakan yayi daidai kawata nan take tazubul luhucul da saubatul azwas da izlis suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa ba WANNAN SHINE ABINDAYA FARU TSAKANIN TAZUBUL LLUHUCUL DA KAWARTA SAUBATUL AZWAS 'YAR SARKIN ALJANU NA SIN al'amarin su yarima sammaru kuwa yayinda aljanun nan shida wato hadiman boka hulumul bakahur sukayì sama dasu suna tafiya ,suna tafiya acikin gajimare sai da suka shafe sa'a bakwai cur suna tafiya sannan suka iso dajin farko wanda ake kira baharul mahaful da shigar su cikin dajin sai wata irin iska ta taso ta hana aljanun shida motsi gaba daya bisa dole sukayo kasa da niyyar su sauka bisa turba koda sukayo kasa kasa sai sukayì arba da dubunnan dodannin nan masu cin naman bil'adama har aljanun nan shida sun yunkura da nufin su sakeyin sama sai suka ji an rurruke fuka fukansu ashe dodannin ne da wannan aiki kafin aljanun su ankara dodannin sun fara yage fuka fukansu tamkar ana yagar fallen littafi, nanfa hankalin aljanun danasu yarima sammaru ya dugunzuma cikin zafin nama gimbiya ashwarya ta zare ta takobinta ta kutsa kai cikin dodannin ta hausu da sara da suka koda ganin haka sai su yarima sammaru sukayì yadda tayi nanfa wuri ya hargitse dodannin suka rinka ruri mai ban tsoro suna kokarin cafke jaruman biyar da kuma boka karluz ko kadan basu damu dasu aljani guluz ba domin sun ciccire musu fuka fukai dai dai sun kasa tashi, bare su tafuka komai nanfa aka cigaba da dauki ba dadi shima boka karluz a wannan rana ya nuna cewa shi namijine domin ya manta da batun tsafi sai gididdiba dodannin ya dinga yi da kaifin takobinsa duk inda yasa kai saidai kaga suna zubewa kasa matattu babban abinda yafi tayarwa da su yarima sammaru hankali shine kashe dodannin sukeyi amma kamar dadosu akeyi tabbas idan aka ci gaba da wannan yaki zuwa wani lokaci karfin su sammaru zai kare dodannin su cinyesu aikuwa ana cikin hakane daya daga cikin dodannin ya sami nasarar kama hannun yarima lubaika yasa acikin bakinsa nan take ya gutsure masa hannunsa iya gaba lubaika y kurma ihu, lokacinda sammaru yaji ihun lubaiku ya hanga yaga abindaya faru saiyayi tsalle sama ya dinga taka kan dodannin yana gudu harya iso wajen lubaiku ,cikin hanzari ya zaro kuttun maganin nan da boka hulumul bakahur ya bashi ya kwarara akan raunin dungulmin hannun nantake jini ya tsaya, shima lubaiku yaci gaba da saran dodannin da hannu daya cikin fushi duk wannan gumurzu da akeyi gimbiya ashwarya nata fafatawane tana neman hanyar da zasu kubuta daga can sai dabara ta fado mata ta ruga da gudu tana gudun tana hadawa da saran dodannin koda ganin haka sai su yarima sammaru sukayi kiyi da ita sai gashi kuwa sun same waraka domin wadannan dodannin basa iyayin gudu sosai nan da nan jaruman suka tserewa dodannin suka barsu abaya nesa bisa dole suka diana binsu a sannan ne suka tsaya su shidan sukayì cirko cirko suna haki da kallon junansu kawai ba tareda dayansu yace uffan baa can sai yarima lauhana yace yanzu menene abinyi shin zaku koma da bayane mu karbo ababan hawanmu su guluz ko kuwa muci gaba gaba da tafiya da kafafunmu? kodajin wannan tambaya sai gimbiya ashwarya tace haba wace irin magana kake haka shin ka mantane akwai wasu dodannin acikin dajin nan domin sun kasance kabila kabila kuma dolene fa mayo kwana uku acikin jejin nan kafin mu fita daga cikinsa haka boka hulumul bakahur ya gaya mana ai babu abindaya fi mana kamar mu cigaba da tafiya adaidai wannan lokaci ne yarima lubaiku ya dubi dungulmin hannun sa sai takaici ya turnukenshi take idanunsa suka ciko da kwalla ya fara zubar da hawaye al'amarin daya jefa gaba dayansu cikin tausayinsa kenan ashwarya ta mike tsaye daga inda inda take zaune ta dawo inda lubaiku yake ta durkusa daf dashi sannan ta dafa kafadarsa tace yakai abokina ka kasance mai rungumar kaddara bisa wannan al'amari daya faru domin rai ba abakin komai yakeba indai akwai biyan bukata ka sani cewa muma nan duk bamu tsiraba daga abin daya sameka ba babu mamakima wasun mu su rasa Rayuwarsu gaba daya, abinda nakeso dakai shine ka jajurce kasa aranka cewa lallai sai ka sami nasarar debo wannan magani a taskar tsafi haka dai gimbiya ashwarya ta cigaba da baiwa lubaiku kwarin gwuiwa her yaji baya shakkar komai a ransa kuma yaji ya kagu da aci gaba da tafiya nantake suka mike gaba dayansu da nufin nausawa cikin daji kawai sai suka hango wasu tsuntsaye abayansu sun taho ta sama yayinda tsuntsayen ke kara kusanto su suna kara girma koda sukazo kusa sai sukaga ashe su aljani guluz ne kowannensu na kada fukafuki daya babu daya cikin farin ciki su yarima sammaru suka ruga wajen su guluz suka taryesu, bayan sun sauka sai yarima sammaru ya dubi guluz yyac yaya akayi kuka tsira daga hannun mugayen dodannin nan? sa'adda guluz yaji wannan tambaya sai yayi yake yace kasan ance mai rabon yaga badi sai ya gani ai lokacinda kuka fita da gudu kuka tserewa dodannin suma biyoku sukayì dayansu bai sauraba awajenmu koda naga sun tafi sun barmu kuma dukkan mu ajigace muke sakamakon yagewar fukafukan mu da zubar jinin da muke tabbas babu wanda zai iya kyakkyawan motsi acikin mu a wannan lokaci cikin karfin hali na fiddo irin ruwan maganin nan da shugabana hulumul bakahur ya baka na dinga jan jiki ina zubawa 'yan uwana ajikin raunikansu saida n tabbatar da cewa kowannenmu ya warke sannan na zubawa kaina, nan take muka tashi sama muka kewaye ta bayan hanyarda dodannin sukabi mukazo nan muka riskeku sa'adda guluz yazo nan azancensa sai yarima sammaru yayi murmushi yace amma dai ka iya ganganci yanzu inda ruwan maganin ya kare baka samuba ya zakayi? da shikenan sai yan uwanka su tafi su barka ka mutu abanza tunda duk ka fisu hikima da kokari. https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share Mu hadu a part H don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏 **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART H ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ GORON JUMA'A ❤️🙏 https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA..... Guluz yayi dariya yace aikoda maganin ya kare nasan 'yan uwana bazasu tafi su barni ba kasan muna da matukar hadin kai da dai su tafi su barni gwara su tsaya duk abinda zai sameni ya samesu gaba daya kodajin haka sai gimbiya ashwarya ta tsoma baki acikin zancen tace au kana nufin ku aljanu bakwa tsoron mutuwa nikam ina ganin idan sukaga wani bala'ìn zasu iya guduwa su barka guluz ya sake bushewa da dariya yace aimu aljanu muna da son junanmu fiye da mutane kuma munsan mahimmancin alkawari bama karya shi ku kuwa mutane akan dukiya ma kuna iya karya alkawari ko kuci amana wannan batu ba karamin haushi ya baiwa gimbiya ashwarya ba ta bude baki zata mai d raddi sai yarima sammaru ya tari numfashinta da cewa hirar nan ta isa haka kuzo muci gaba da tafiya cikin hanzari ya haye bayan aljani guluz ya zauna koda ganin haka sai dukkansu suka hau kan sauran aljanun alokaci guda aljanun shida suka tashi sama tafiyar rabin sa'a sukayì kacal suka iso nahiyar wadansu manyan dodanni wadanda suka kasance dogaye zankala zankala saboda tsawon su duk sun kere bishiyoyin dajin da tsaunika koda wadannan dodannin suka hango su yarima sammaru asama 'yan kanana kamaI'm tsuntsaye zasu gifta ta samansu sai suka daga kawunansu sama suka wangame bakunansu suka hura musu wata iska mai tsananin karfi wacce inda acikin garice zata iya rushe gidaje. kuma zata iya daukar mutane ta rinka yawo dasu asama nan da nan gagarumar iskar ta birkita hankalin su yarima sammaru da aljanun shida ya zamana sun kasa gaba sun kasa baya kuma sai gware suke da juna, tabbas idan aka kara 'yan dakiku ahaka zasu iya hallaka, cikin karaji yarima sammaru ya baiwa su guluz umarnin saukowa kasa nantake kuwa suka bi umarnin kafin su iso kan turba tuni jaruman shida sun zare takubbansu suna dira kasa wuri ya hautsine da rurin mazaje dana dodannin wannan karon sai su yarima sammaru suka gane ruwa ba sa'an kwando bane domin saran dodannin suke amma kamar a banza domin dodannin sun kasance masu tsananin juriya karfi da taurin kai nanfa dodannin suka kuntata musu yazamana su yarima sammaru basa iya komai sai kokarin kare kai ana cikin hakane wani dodo ya kama kafar yarima yauhana ya karyata da karfin tsiya yauhana ya kwarara uban ihu cikin dimaucewa kafin yauhana yayi wani yunkuri tuni dodon ya saka kafar gaba daya abakinsa ya gutsireta da bakinsa ya kama ci kamar mutum yana asuwaki da cinyar kaza nantake yauhana ya sulale kasa sumamme koda ganin abindaya faru sai yarima sammaru ya fusata ya daka tsalle sama tun a saman yarima sammaru ya zare wata rantsatstsiyar wuka kawai saiya duro akan dodonnan dake cin kafar yauhan take ya luma masa rantsatstsiyar wukar a tsakiyar kansa kuma ya zareta da karfin tsiya take jini ya kama tsartuwa asama kamar an fasa goran ruwa nanfa dodon ya kama make make da ruri ya fadi nan ya tashi can har rai yayi halinsa wannan ce damar da jaruman shida suka samu suka gano makasar dodannin don haka suka ci gaba da saransu da sukarsu aka kawai sai gani akayi dodannin suna zubewa kasa matattu a wannan lokacin ne yarima sammaru ya samu dama y kwararawa yarima lauhana wannan ruwan maganin a karshen cinyar guntulalliya take wajen ya bushe kamar anfi shekara da gutsure kafar adaidai wannan lokacin ne wasu dodanni suka kawowa yauhana sura don su karasa cinyeshi cikin zafin nama sammaru ya daukeshi ya azashi abayansa sannan ya kaiwa dodannin sara aka alokaci guda cikin sa'a kuwa ya raba musu kawuna Kamar an datsa kabewa gida biyu take suka zube kasa matattu nanfa aka cigaba da ragargazar dodannin nan saida aka shafe sa'a uku ana gumurzu sannan aka karar da dodannin awannan yaki babu wanda bai samu rauni ajikin sa ba sama da guda uku yarima sammaru ne kadai ya sami rauni biyu daya akafarsa wani dodo ya yankeshi da farcen hannu daya kuwa a cinyarsa aka caka masa kahon ka wanda saidaya durkusa kasa yana mai ihu amma cikin tsananin juriya ya sake mikewa tsaye yaci gaba da sara da suka her aka gama yakin yarima lauhana yana sabe akafadar yarima sammaru kuma asume gimbiya ashwarya ce kadai tayi jarumtaka kwatankwacin irin wacce yarima sammaru yayi, amma itama ta sami rauni abayan kafarta saikuma larbuz wanda ya taka mahimmiyar rawa awannan yaki gaba dayan su dai babu wanda baisha wahala da samun raunika da yawaba, don har jirine ya rinka dibarsu saida sammaru ya kai masa daukin magani da gaggawa sannan ya dawo hayyacinsa bayan an gama yakinne kowa ya sharbe akasa harda suma aljanun shida sai yarima sammaru ya bisu daya bayan daya ya saka musu magani aci wukansu saidaya gama da kowa sannan yaje kan gimbiya ashwarya wacce take zaune agefe guda akan wani karamin dutse koda yazo gareta ya kalleta sama da kasa baiga wani rauniba saiya juya da nufin tafiya ya zaka tafi baka samini magani ba? ta tambaya tana murmushi cikin mamaki yarima sammaru ya waigo ya dubeta yace ai banga rauni ko daya ba ajikinki ashwarya tace baka duba sosai bane zagayo bayana ka kwaye rigata ka ga ʀɑuɳi batareda d gardama ba yarima sammaru ya sa hannunsa zai kwaye rigarta sai hannunsa ya kama kakkarwa, bakomai ne ya haddasa hakanba face ganin kyakkyawan surar jikinta da kuma fatarta mai tsananin haske da laushi, duk da cewar raunin dake bayan nata na da dan girma amma bai razana sammaru ba kamar yadda kyakkyawan jikinta ya razanashi, kamar tasan halin daya shiga sai tace me kake jirane ko kuwa kaima zuciyar ragwaye gareka ciwon y firgita ka sammaru yayi murmushi yace ai abin tsoro baya firgita mazajen kwarai saidai abin mamaki hakadai ya daure ya zuba mata maganin hannunsa na karkarwa bayan ya gama da ita saiya juya don ta koma inda yake ba zato ba tsammani saiyaji ankira sunansa cikin mamaki ya waigo suka dubi juna tana mai murmushi agareshi zauna nan abinda tace dashi kenan kawai sammaru ya zauna yana mai mamakin hakan kawai saita karbi kuttun maganin dake hannunsa ta fara zubawa akan rauninsa dake cinya gaba daya. jaruman nan kuwa da aljanun nan shida sai suka zuba musu ido tuni awannan lokaci kishi ya turnuke yarima lubaiku da larbuz idan na barka kasa maganin da kanka banyi maka adalciba domin kai kadai kasawa kowa maganin nan kamata yayi kaima ayi maka kara koda jin wannan batu sai sammaru ya yi murmushi yace nagode ammafa inason zama da mutumin dake da kara kuma inason zama da mace mai zuciyar maza ashwarya ta bushe da dariya sannan tace daina kodani haka karkasa kaina y fashe in banda abinka ina abin yake ai gadai mAce can mai zuciyar maza tana kafsawa dasu cikin mamaki sammaru yace wakenan kike nufi? gimbiya fauwaz mana duk lokacinda na tunoda lokacinda boka hulumul bakahur ya nuna mana ita amadubin tsafinsa sa'adda take ragargazar maza sai naji kishi ya kamani tabbas fauwaza ta fini jarumtaka da kyau nesa ba kusaba ace nice ita da dolene na shahara ko ina acikin duniya awannan zamani, sammaru yayi murmushi yace ai yanzu ma zaki shahara aduniya idan her kika sami nasarar shiga cciki kogon muddarul ikisina kika debo ruwan tsumin tsafin bokanya tazubul luhucul acan taskar tsafinta kodajin haka sai ashwarya tayi ajiyar zuciya tace tana zaton dayanmu zai iya cika wannan buri ka sani cewa naji daga bakin manyan bokayen duniya cewa fiye da shekaru dubu baya babu wani mahaluki daya taba shiga cikinsa ya fito araye don haka ba shigar bace wahalaba fitowarce wahala sammaru ya jinjina kai yace hakika zancenki dutsene, to amma ai ance faduwar gaba asarar namijine dadai mu zauna mu zuba ido muna gani iyayenmu su hallaka gwara muma mu hallaka kan kokarin cetonsu kafin ashwarya tace wani abu saiga boka karluz ya taho garesu da zuwa ya durkusa agabansu sannan ya fiddo madubinsa na tsafi ya ajiye agabansu yace, yakai sammaru jagoran tafiya kayi sani cewa zan iya nuna maka sauran hadarin dake gabanmu acikin dajin nan yanzu anan wurin cikin murna sammaru yace maza ka nuna mini don musan matakin da zamu dauka nantake karluz ya shafi madubin tsafinsa saiga hoton wadansu dodannin acan gaba wadanda sunfi n baya girma daban tsoro madubin ya sake nuna wasu acan gaba suma sunfi na baya harsaida madubin ya nuna kabilar dodanni kala biyar wato idan aka hada dana baya sunzama kabila bakwai cif cif koda gama ganin su sai hankalin sammaru dana ashwarya ya dugunzuma nan take sammaru yakira su lubaiku suma suka gani awannan lokaci ne yarima yauhana ya farka daga dogon suman da yayi koda yaga kafarsa ta hagu a guntule saiya rusa ihu ya fashe da kuka, da kyar sammaru ya rarrasheshi ya daina kukan bayan nan sai sammaru ya dubi jaruman duka daya bayan daya yace. https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share MU HADU A PART i DOMIN JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️**MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART I ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.... Yɑku abokan tafiyata ina mai sanar daku cewa gwagwarmayar da muka sha abaya tamkar sharar fage ce akan wacce zamu tunkara agabanmu ina mai rokonmu damu kara damu kara zage dantse mucire tsoro da fargabar komai domin matsoraci baya zama gwani ko wanene ko dan wa musa aranmu cewa ko mu mutu ko muyi rai sai mun kai gaci, ku tuna cewa akwai sauran aiki agabanmu don haka zamanmu anan tamkar hutun jaki da kaya aka ne ina mai umartarmu damu tashi mu kara gaba ba zamu tsaya ako'ina ba harsai mun karar da dukkannin dodannin dake cikin wannan daji koda sammaru ya zo nan azancensa saiya zare takobinsa ya dagata sama yayi kururuwa irin wacce ke firgita maza afilin daga nantake kururuwar tasa ta cika dajin harda amsa kuwwa izuwa nesa al'amarin daya janyo hankalin sauran kabilun dodannin kenan suka san cewa lallai yau sunada baki don haka sai kwadayi ya kamasu, suka fara tande baki suna dalalar da yawu akasa, lokacinda yarima sammaru suka gama rurinsu don karawa kansu kaimi da kuzari sai suka dane bayansu guluz sukaci gaba da tafiya a sama cikin tsananin gudu aikuwa cikin kankanin lokaci suka riski kabilar dodanni ta uku ana haduwa yaki ya barke akayi dauki ba dadi wohohoho awannan rana rayuka sun salwanta, jini kuwa ya malala don saida ya zamana koramai da fadamomin dajin sun rine sun zama jini maimakon ruwa awannan gumurzun da akayi ne da kabilar dodannin ta uku yarima lubaiku ya rasa rayuwarsa domin saida dodannin sukayì walima da sassan jikinsa ba'a samu komai ba daga barin jikinsa hatta gashin kansa saida suka cinye tabbas awannan lokaci su yarima sammaru sunga tashin hankali irin wanda basu taba ganiba alokcinne aka cirewa boka karluz kunnuwansa aka cinye shikuwa yarima larbuz saida ya rasa 'yan yatsun hannunsa na hugu babu wanda ya bada mamaki kamar yarima lauhana domin duk da kasancewar kafarsa daya zamewa dodannin alakakai yayi musu muguwar barna domin saidaya kashe sama da guda dubu uku shi kadai kuma har aka gama yakin saidaya sami rauni ajikinsa inbanda sammaru da ashwarya babu wanda bai samu mugun rauni ba a wannan yakin bayan an gama yakin ne su duka suka zauna suka fashe da kuka bisa tunawa da irin mutuwar da yarima lubaiku yayi gaba dayansu sai jikinsu yayi sanyi hankalinsu ya dugunzuma kowa zuciyar sa ta fitar da rai ga rayuwa kuma sukayì nadamar baro kasashensu da sukayì don cika wannan buri nasu mai matukar hadari anan ne dare ya riskesu kuma yunwa d kishirwa ta addabesu bisa dole aka kunna wuta aka zagayeta anajin dumi saboda hunturun sanyin dake kadawa sannan aka fara tunanin yadda za'a samu abinci da ruwan sha tunda shi kansa ruwan dake dajin ya zama jini anacikin yin shawarane boka karluz ya dubi aljani guluz yace kune aljanu ina dabara? ko zakuje kudan zagaya ku samo mana abinci da abinsha? guluz yace haba bakaji kunyaba ka fadi haka ka tuna cewa kai bokane zaka iyayin tsafi abinci da abinsha su bayyana nantake karluz ya daka masa harara yace baka da hankali, ai kasanma idan na mayi tsafin wani aljaninne zai kawo kasan kuwa babu wani aljani dazai iya shigowa cikin jejin nan don ya tabbatar da cewa halaka zaiyi ai kawai ku cire tsoron komai kuje ku samo mana abinci abinci dai idan kukayi hakuri mun kusa rabuwa daku tunda saura jeji biyu kacal mu iso takiyar duniyar nan cciki damuwa da tsoro boka guluz yace shikenan munyarda zamuje mu nemo muku abinci amma ka duba mana cikin madubin tsafinka inda zamuje mu nemo muku abinci batareda munsha wahalaba ko mu afka cikin bala'i boka karluz ya bushe da dariya yace oh! waiyau aljani ne da tsoro kamar farar kura nandanan ya fiddo madubin tsafinsa ya ajiye a kasa ya shafeshi saiga hoton wata katuwar barewa kwance acikin wani rami acan gaba kadan daga inda suke zaune yanzu kuma abayan ramin wata korama ruwa na gudu acikinta mai kyau da haske wanda jini bai gurbatashiba agaba daya harabar wajen babu alamar dodanni koda ganin haka sai aljani guluz ya dubi aljani amzil da hurus yace maza kuje ku dauko barewarnan kuma ku debo ruwan koramar nan isasshe ku kawo musu, kafin ya gama rufe bakinsa tuni su amzil sun bace, saida dakika dari uku da sittin ta wuce amma basu dawoba, al'amarin daya tayarda hankalin kowa kenan gimbiya ashwarya tace kai jama'a ruwafa baya tsami banza lallai akwai abindaya faru ga su amzil donya kamata ace sun dawo tun dazu, kodajin haka sai boka karluz yace kwarai kuwa hakane kinyi gaskiya amma bara mu duba muga halinda akeciki cikin sauri ya sake fiddo madubin tsafinsa ya ajiye akasa ya shafe shi saiga hoton aljani amzil shikadai asama daukeda barewa da kumA ruwa acikin babbar batta duk jikinsa jina jina yana tafe yana kayi asaman kamar zai fado kasa koda ganin haka sai Hankalin su ta sake dugunzuma ba'a jimaba saiga aljani amzil ya fado agabansu yana kakarin mutuwa nanfa kowa ya manta da batun yunwa da kishirwa akazo kan amzil aka tsaya aljani guluz ya tallafo kan amzil ya dora akan cinyarsa yana mai kallon fuskarsa yace yakai dan uwana mai ya faru gareku kaida hurus na ganka cikin wannan hali cciki matukar karfin hali amzil yace yakai guluz kayi sani cewa alokacinda muka shiga cikin kogon nan don kama barewarnan bamu fuskanci matsalar komai ba har muka fyadeta ta mutu sai bayan mun fito daga cikin kogon sai kawai mukaga wasu irin dodanni sunyi mana kawanya kafin mu yunkura sunfara kai mana cafka mukuwa saimuka fara kokarin ceton kanmu inaji ina gani suka kama hurus suka dinga yaga jikinsa sunaci saida suka cinyeshi tas, nikuwa dama iyakar karfina nake yakarsu dayake su biyarne kacal saina zame musu alakakai kasancewar nafisu karfi saida suka kusan hallakani dakyar ma samu na tsere musu, koda yake tsiran banza nayi don na tabbatar mutuwa zanyi yakai guluz ina mai rokonka daka kula da matata idan har kana da sauran kwana aduniya kuma ka sami damar komawa gida kasani cewa matata tana da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe idan ta haihu lafiya kuma ta sami da namiji kasa masa sunana idan kuwa macece asamata suna muddarul ikisina don ta zamo abin tunawa da iyakar rayuwata koda amzil yazo nan azancensa sai idanunsa suka kafe, komai na jikinsa ya daina motsi guluz ya rungume gawar amzil ya fashe da kuka al'amarin daya karya zuciyar sauran aljanun kenan wato karmash, karfil, da azgar suma suka kama kuka saida aka dan jima ana alhilin wannan mutuwa ta aljani amzil sannan aka gasa naman barewar nan kowa yaci ya koshi akasha ruwa, daga nan sai yarima sammaru ya tashi ya koma gefe daya ya zauna yana mai tunanin gida koda ya tuno da mahaifinsa sarki alyasil buhus ya tuno halin daya baroshi na kamuwa da cutar mutuwar rabin jiki saiya fashe da kuka, sammaru ya sake tuno lokacinda mahaifiyarsa ta rungumeshi tana kuka sa'adda da suke bankwanan rabuwa kawai saiya rushe da kuka al'amarin daya jefa gimbiya ashwarya cikin tausayi kenan ta taho ga sammaru da zuwa ta zauna dafdashi ba tareda ta kalli fuskarsa ba tace yakai abokina kayi sani cewa aduniya babu abindaya fi dadi sama da zama da masoyi tabbas nasan kana tunanin iyayenka ne 'yan uwanka, danginka da kasarsu shine sanadin wannan kuka naka kayi sani cewa nima na kasance acikin irin wannan tunani naka kuma duk da kasancewata 'ya mace ban bari kukana ya fito filiba amma nayi na zuci harnagaji, inason mu kasance masu hakuri domin ya zama wajibi agaremu koda ashwarya tazo nan azancenta sai yarima sammaru ya dago kai ya dubeta inda yaga kwallah cike a idanunta nan take yaji tausayi da kaunarta sun dabaibaye zuciyarsa baisan sa'adda ya saki murmushiba agareta jim kadan sukayi shiru su biyu dayansu bai ce uffan ba daga can sai sammaru ya katse shirun da cewa yake kawata hakika tun lokacinda na baro gida naji ina cikin kadaici fargaba da rashin kwanciyar hankali amma kuma sanda na farajin kalamanki sai naji duk wadannan abubuwa sunyi kaura daga gareni aduk sa'adda na kalleki ko naji muryarki sainaji kamar ina cikin gidanmu ne tareda iyayena da 'yan uwana tabbas duk wanda ya sami mace kamarki mai dadadan kalamai masu tausasa zuciya ya gama morewa don ko abakin kura yake bazaiyi fargaba da bakin ciki ba koda yarima sammaru yazonan azancensa sai ashwarya taji wani irin farinciki ya baibayeta take itama taji ta kamu da tsananin kaunarsa batasan sa'adda ta kura masa ido ba harsuka shagala da kallon juna duk wannan abu dake faruwa larbuz, yauhana, da karluz nadaga can gefe suna kallo. https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share MU HADU A PART J DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️ Najibullahi Muhammad #LEGENDs. **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU✍️✍️ PART J ❤️🥰 NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ CIGABAN LITTAFIN.... Kuma dukkaninsu sun fahimci cewa lallai soyayya tashiga tsakanin matasan biyu kai hatta su aljani guluz sun fahimci hakan, suma kuma matasan biyun sunsan suna son juna amma nauyin baki ya hana kowannensu yayi ɓɑyɑɳi hakadai sukaci gaba da hira har dare ya raba sosai inda yarima sammaru ya umarci su aljani guluz dasuyi musu gadi su kuma suka kwanta sukayì barci basu farkaba saida gari ya waye her gAri yayi haske rana ta fito sakamakon tsananin gajiyar dake tare dasu bayan sun farka ne kowa ya wanke fuskarsa sannan aka ci ragowar naman barewar jiya akasha ruwa bayan an kimtsa sai yarima sammaru ya dubesu daya bayan daya yace yaku 'yan uwana abokan tafiya inamaiyi muku tuni da cewa adafa mu goma shabiyune muke wannan tafiya amma yanzu mun zamo saura tara don haka ya zama wajibi agaremu mm zage damtse muyi iya yinmu, yanzu sai kowannenmu ya

Chapter 3 of 6