Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
wannan lokacine sarki hudes ya sa aka kwance igiyar data daure jarumi hubairu da waziri kuddaru kafin wani daga cikinsu yace uffan tuni sarki hudes ya bada umarnin subar garin nanfa aka dauke jarumi hubairu, waziri kuddaru da gimbiya sima sukayi sama cikin 'yan dakiku kadan aka kule acikin gajimare al'amarin daya jefa mutanen birnin tehran cikin rudani da rikitar kwakwalwa domin wannan shine karo na biyu da mutuwar sarkinsu lu'umanu mutuwar da basu da tabbacinta awannan karo na farko sunga ya mutu kuma y dawo to shin wannan karon ma zai sake dawowane wannan tambayar babu wanda yasan amsarta aduk fadin garin shin zasu sake nada sabon sarkine ko kuwa zasu jirane zuwa wani lokacin kamar yadda akayi a wancan karon? WANNAN SHINE ABIN DAYA FARU ABIRNIN TEHRAN BAYAN ANYI GAGARUMIN YAKI TSAKANIN SARKI HUDES DA ALJANI ZARMUKU ALJANIN DAYA ZAMA DAYA DAGA CIKIN ALJANUN DA SUKE SHIGA JIKIN GANGAR JIKIN SARKI LU'UMANU SUNA BARNA ADORON KASA Bayan bakar gizon ya bace bat da zarmuku da gangar jikin lu'umanu bai sake baiyana ba say a tsakiyar fadar nan wacce akewa lakabi da. BAHAR ZUZ DA BAYYANARSU SAI BAKAN GIZON NAN ya rikide ya zama BOKA SHAMHARU cikin fushi yayi wurgi da aljani zarmuku kamar yayi wulli da jikakken tsumma ahankali ya ajiye gangar jikin lu'umanu akan tebur adaidai wannan lokacine gaba daya hadimansa sukayi sujjada agareshi cikin girmamawa shikuwa zarmuku sai ya kama kuka saboda takaici musamman idan ya dubi dungulmin hannunsa mai zubar jini shamharu ya nuna wata kofar lu'u lu'u da hannun sa sai kofar ta bude sarki lu'umanu ya fito daga cikin ta ya taho garesu cikin kunar rai da fushi sannan ya dubi shamharu yace ya shugabana yana dakyau ka barni na shiga jikin gangar jikin nan nawa dakaina naci gaba da yakar makiayan mu na karar dasu gaba daya don na fuskanci cewa su zarmuku bazasu iyayin komai ba. Mu hadu a part D don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️ **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU✍️✍️ PART D ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️ MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Cikin alamun damuwa shamharu ya dafa kafadar lu'umanu yace yakai babban wakilina adoron kasa kayi sani cewa banida kamarka aduk cikin bil'adama kuma na sani cewa aikin da zaka iya yi mini babu wani aljani dazai iya yinsa amma ka sani cewa ma'abota addinin musuluncin nan hatsabibaine matuka musamman sarki hudes dinnan ina shakkarsa domin sihirinsa nada matukar karfin da zai iya nasara akanka,shiyasa bazan bari kayi fito na fitoba dashi gwara day muci gaba da amfani da gangar jikinka amma ruhinka yaci gaba da zama anan harsai ragowar aljanun guda dari tara da casa'in da takwas sun kare yanzu aljanin dazai shiga gangar jikinka shine makabu makabus yafi aljani zarmuku karfi, juriya da jarumta sau arba'n,tabbas ina ganin zai iya kawar dasu sarki hudes nida kai zamuci gaba da aikina na cika MATSATSUBI ina mai bakin cikin sanar dakai wani bakin labari bisa wata babbar masifa datakeson afko mana tabbas idan her masifar nan ta samemu tamu ta kare kuma dukkan shirin my ya wargatse cikin tsananin damuwa lu'umanu ya sake rissinawa yace ya shugabana wace irin masiface ke ahirin afko mana? maimakon shamharu ya ce wani abu sai yayi nuni da hannunsa izuwa wani babban allon tsafi take hoton sundukin haske ya bayyana sai gashi dauke da birirrika guda ahida acikinsa yana mai tsala gudu shamharu ya ce kaga wadannnan birarrika na cikin sundukin nan to ba birarrika bane,sarki azbir ne tareda su jafar yelisa, mashrila, mazlish da kuma aljani gulzum tun tuni nayi maka bayanin ko suwaye su jafar da irin bala'in da suka janyo mana wannan sundukin da kake gani daga can wata duniyar aka aikoshi don ya narkar da duniyar su jafar idan har duniyar su ta narke tamkar ankone sirrikan tsafinane gaba daya dani da kai da dukkan hadimaina mutuwa zamuyi gaba daya kodajin wannan batu sai hankalin lu'umanu ya dugunzuma yace ya shugabana yanzu menene abinyi? shamharu yayi ajiyar zuciya yace abinyi guda daya ne tak Yanzu zan nuna maka shi ka gani nantake shamharu ya shafi allon tsafinsa say sunduki sarki azmul gallar ya bace wani sabon sundukin ya baiyana wanda ya kasance ankerashine da zallan lu'u lu'u kuma yana dauke da wasu dakarun boka shamharu guda goma sha biyu acikinsa sundukin nata tsala gudu acikin sararin samaniya tamkar gudun tauraruwa mai wutsiya shamharu ya ce kaga wannan sundukin nawane kuma na turashine don yaje yayi karo da sundukin azmul gallar su tarwatse gaba daya asama shin tabbas idan sukayi karon zasu tarwatse? lu'umanu ya tambaya shamharu ya ce haka dai nake kyautata zato amma banida tabbas, lu'umanu ya ja dogon numfashi yace ya shugabana kayi hakuri d yawan tambayoyina kasan na kasance cikin damuwa shamharu ya kyalkyale da dariya yace karka damu ina son bil'adama mai yawan tambaya domin ni kaina ina kara samun ilimi daga cikin tambaya fadi kome kake son fadi zan bka amsa iyakar sanina lu'umanu yayi gyaran murya yace yanzu idan sundukin nan guda biyu suka hadu suka tarwatse halittun dake cikin sa suma sun hallaka kenan? kodajin wannan tambaya sai shamharu ya bushe da dariya yace kwarai kuwa ai indai sukayi karon nan say su jafar sun hallaka hakama dakarun dake cikin nawa sundukin yanzu haka shingin sa'a uku kacal sundukin ya riski sundukin azmul gallar don haka say muci gaba da kallon allon tsafin nan don muga abinda zai faru idan sundukin biyu suka hadu yayin da shamharu yazo nan azancensa sai sarki lu'umanu ya sake kidima yayi shiru yana mai kallon allon tsafi kawai daga nan kuma sai ya dubi shamharu yace ya shugabana dazu kace wancan sundukin dazai hallaka duniyarmu daga wata duniyar aka aikoshi kuma yanzu naji kace sundukin sarki azmul gallar kuma awacce duniyar yake shamharu yayi murmushi yace hakika kayi tambaya mai amfani kuma mai mahimmanci, yakai lu'umanu kayi sani cewa sarki azmul gallar shine ke mulkin wata duniya dake sama wacce akewa lakabi da duniyar iska yana zaune acikin babban birnin kasar wanda ake kira da harjulul mulk aduk dunuyoyin dake sama babu mai girma da fadi kamar duniyar iska kuma halittun cikintama sunfi nako ina karfin sihiri da hikima sarki azmul gallar yayi bincike y gano cewa duk cikin duniyoyin dale sama da kasa babu waji sarki mai karfin sihiri kamarsa face ni don haka na zama babban makiyinsa babu yadda za'ayi yasan sirrikan tsafina face ya narkar da duniyar ku ni kuma babu yadda za'ayi nasan sirrikan tsafinsa face an kammala rubutun KUNDUN TSATSUBA na biyu wanda a halin yanzu su ruziyal suke kan aikinsa bayan ya sami nasarar narkarda duniyar kune zai debi kasarta ya maida ita kankanuwa sannan ya kera kubar MIFTAHUL ZARBIL da ita idan yayi wannan kuba zaiyi amfanida ita wajen kulle nasa KUNDUN TSATSUBAN wanda yanzu haka yana nan a kulle acikin fadadsa wacce ake kira da saukatul askur yakai lu'umanu kayi sani cewa halwar tsafin dana shiga kwanakin baya na gano hanyarda zambi na zamo matsatsubi da wur wuri basai nabi waccan hanyarda nakeson biba da farko hanyar kuwa itace ta shiga fadar saukatul askur don sato kundun tsatsuban sarki azmul gallar shiga wannan fada ba karamin bala'i bane da tashin hankali agareni. kayi sani cewa zuwana duniyar iska abune mai sauki kamar cire silin gashi daga cikin tandun mai ammafa bazan iya shiga fadar sa ba face na kera wata kubar wacce zata bude kofar shiga fadar ita kuwa wannan kuba daidaì take da MIFTAHUL ZARBIL irin wacce za'a kulle KUNDUN TSATSUBAN da ita idan ina so na kera wannan kuba cikin kankanin lokaci saina samo abu uku abu na farko shine narkakken ruwan dutsen da yafi kowanne dutse girma aduniya abu na biyu shine dutsen wuta wanda ke cikin duniyar karshe ta duniyoyin kasa abu na uku shine rabin ruwan tekun dun8ya kaf wadannnan abubuwa uku su za'a cakuda adafa su sannan a sana'anta kubar MIFTAHUL ZARBIL wacce zan iya bude kofar fadar saukatul askur da ita don na dauko kundun tsatsuban sarki azmul gallar idan har na karanta wannan littafi saina sirrikan tsafi gud@ dubu sau dubu wato ninkin na cikin nawa kundun tsatsuban koda shamharu yazo nan azancensa sai lu'umanu yayi ajiyar zuciya yace ya shugabana ai wahalar wannan aiki tafi ta mujira agama rubutun kundun tsatsuba na biyu nikam banga ta yadda zaka iya samo wadannnan abubuwa uku ba harka kera kubar da zaka bude fadar saukatul askur da itaba idan kuwa kayi hakuri nanda ahekaru ashirin za'a iya gama rubutun sabon kundi cikin tsawa da fushi boka shamharu yace kai lu'umanu ashe baka da hankali bak@ da wayo ai idan na bari akakai wannan lokaci su jafar zasu iy gama karance kundun tsatsuba sa'ata kawai itace ace a yanzu su hallaka acikin sundukin haske na sarki azmul galllar yanzu dai ka saurara kaga abinda zai farù garesu bayan nan zanyi maka bayanin yadda zamu samo wadannnan abubuwa uku acikin kwanaki arba'in kuma zan sanar dakai yadda zamuyi sihiri mu tafi duniyar iska don mu yaki sarki azmul gallar mu hallakashi tareda jama'arsa sannan mu shiga fadarsa mu dauko kundun tsatsuban sa koda shamharu yazo nan azancemsa say yayi shiru baikara cewa komaiba har lu'umanu ya bude baki zaice wani abu sai yayi masa nuni da yayi shiru su duka biyun suka kurawa allon tsafin idanu suna kallon yadda sundukin shamharu ke keta giza gizai asararin samaniya aikuwa sa'a uku na cika saiga sundukin azmul gallar ya doso kan sundukin shamharu cikin abinda bai wuce dakika daya ba sundukan biyu suk@yi karoda juna take sundukin shamharu ya tarwatse ya dagargaje asama babu abinda ya rage ajikinsa face ruburbushin wuta da toka lokacinda wannan abu ya faru saida fadar shamharu tayi girgiza zata rushe faruw@r 'akan keda wuya sai sukaga wata iska mai karfi ta fasa sundukin hasken azmul gallar ta debe birarrikan nan guda shidata bace dasu take shima wannan sundukin ya bashe ya dagargaje koda ganin haka sai shamharu ya shafi allon tsafinsa hoton ya bace cikin tsananin bakin ciki shamharu ya takarkare ya kwarara uban ihu sannan ya fashe da kuka, al'amarin daya janyo girgizar kasa afadar tasa kenan saida rabin sa'a ta shude sannan fadar ta samu ta tsaya waje guda. Mu hadu a part E don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏 Najibullahi Muhammad ☝️ #LEGENDs. **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU✍️✍️ PART E ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ marubucin littafin ya ci gaba da cewa... Cikin fargaba d tsoro sarki lu'umanu ya matso kusa DA shamharu yace yashugabana menene ma'anar wannabe Abu daya faru? shamharu ya dagakai ya dubi Lu'umanu idanunsa back DA wuta din tsananin takaici yace shikenan anyi biyu babu bukata batata biyaba haka ma ta sarki azmul gallar yakai lu'umnu kayi Sam I cewa wannan iska daka Gabi wacce ta fasa sundukin sarki azmul gallar ta zuke su jafaru dake ciki bakomai bace face iskar kundun tsatsuba kuma y karanta kansa sannan yabi su jafar inda suke ya zukosu suka fada cikinsa dama ka'idarsa kenan yanzu babu abinda zamuyi face ka biyoni izuwa cikin dakin halwata domin muyi wani aiki na tsawon sa'a guda cif amma kafin hakan zansa aljani makabus ya shiga jikinka y tafi izuwa birnin tehran domin yaci vaba da mulki domin yanzu haka mutanenka sun shiga tararrabi irin wanda suka shiga awancan karon saukinta ma mun taho d gangar jikinka bamu barta acan ba shamharu ya dubi makabus yace na umarceka daka shiga cikin jikin nan kuma idan kaje birnin tehran kayi mulki irin wanda sarki lu'umanu yakeyi bayan kwana biyu kayi shiri ka tafi neman gimbiya sima wacce ke tareda su sarki hudes duk bala'in da za'ayi ka tabbat ka rabasu da gimbiya sima inyaso saika gudo da ita izuwa nan nidakaina zan daura aurenta da lu'umanu koda gama fadin haka say aljani makabus yace angma ya shugana nantake aljani makabus ya rikide yazama haske ya shiga jikin gangar jikin lu'umanu wacce ke kwance akan tebur kamar gawa shigar hasken keda wuya sai gangar jikin ta mike zumbur kawai saita rikide ta koma aljani makabus take ya mike tsaye tsaye ya bude fuka fukansa yayi sama ya ratsa ta cikin gini kamar yadda danshin ruwa ke ratsa gini yayi fitar burgu bayan faruwar hakan say sarki shamharu ya dubi aljani zarmuku ya daka masa tsawa yace banza rago tashi kaje ka cigaba da aikinda kakeyi afadar nan tunda ka zama nakasasshe bazaka iyayin aiki awajeba cikin biyayya da kakkarwar jiki zarmuku yace angma ya shugabana nan da nan zarmuku ya shiga wata kofa shi kuwa shamharu saiya kama hannun lu'umanu ya shiga dashi cikin dakin halwarsa ta tsafi WANNAN SHINE ABINDA YA FARU TSAKANIN BOKA SHAMHARU DA RUHIN LU'UMANU ACAN FADARSA DAKE TSUBURIN BAHAR ZUS Acan fadar sarki dujalu kuwa hankalin kowa adugunzume yake shidai sarki dujalu ya tsorata ainun d tsoho rafkanagu domin ko alanari baitaba jin ance ga wani mutum daya jefa mage abakinsa ba da ranta ya taune ya hadiyeta ba amma yau gashi y gani da idonsa tabbas zuciyarsa ta fara saka masa cewa duk yadda akayi rafkanagu ba mutum bane aljanine abangaren tsoho rafkanagu, ruziyal, da boka hajarul makarus kuwa hankalin su ya tashi sakamakon tsoron kada sarki dujalu ya ki karasa musu wannan labarin na bokanya tazubul luhucul lokacin da ayyuka suka rikice afadar sai sarki dujalu yace afitar da tsoho rafakanagu daga cikin fadar har antusa keyarsa za'a fita dasu say boka hajarul makarus ya dubi sarki dujalu yace yakai wannan sarki mai adalci da cikar mulki shin kayi imani da tsafi kuwa? sarki y daga hannu alamar adawo dasu take aka maido dasu hajarul makarus yace saboda na fuskanci cewa baka da kariyar tsafi ajikinka ka tuna cewa awancan karon an turo damisa gidanka donta hallaka ka, yanzu kuma an turo mage gidanka don ta hallakaka amma duk ka kasa fahimtar cewa makiyanka ne ke son ganin bayanka yanzu take zan nuna maka hujja don ka gamsu da zancena ina mai sanar da kai cewa nida abokan tafiyata matsafane ahiyasa muka gano haka kafin sarki dujalu yace wani abu tuni hajarul makarus yayi nuni da hannunsa izuwa g bango saiga hoton wadansu mutum biyu ya bayyana sunayin maganar sirri acikin wani daki daya daga cikinsu sunansa amad wandaya kasance kanine ga sarki dujalu uwa daya uba daya dayan kuwa sunansa madarus yakasance sarkin yakin birnin armad ya dubi madarus yace kai ammafa shegen sarkin nan namu ya cika taurin rai ka dubafa ka gani mun tsafance damisar gidansa donta kasheshi amma ya tsallake munsake tsafance kyanwar gidansa ya tsallake kaga inda ya mutu da tuni na zama sarki kai kuma ka zama wazirina yanzu menene abinyi? madarus yace abinyi kawai shine ka tashi mu koma wajen bokana don ya bamu wata sa'ar ai ance mai nema yana tareda samu armad yace kwarai kuwa nantake suka fice daga cikin dakin gaba daya asannan ne hajarul makarus ya sake nuna bangon da hannunsa hoton ya bace dujalu yayi ajiyar numfashi ya kama yiwa tsoho rafkanagu godiya bisa taimakonsa da yayi nan take sarki dujalu ya a tura aka kamo dan uwansa armad da sarkin yaki makarus aka bankaresu ya tsiresu da mashi da hannunsa sannan aka kwashe gawarwakinsu akai waje dasu bayi sukayisauri suka goge jinin daya zuba agurin sarki dujalu ya koma kan karagarsa ya zauna sannan aka kawo sihirtaccen shayi aka baiwa kowa yasha harda shì kansa sannan yayi gyaran murya yace to saiku shirya zanci gaba daga inda na tsaya acikin labarin hikayar bokanya tazubul luhucul dujalu ya sakeyin gyaran murya Bayansu yarima sammaru sun gama begen gimbiya fauwaz acikin zuciyoyinsu sakamakon ganinta da sukayì acikin madubin tsafi sai boka hulumul bakahur ya dubesu daya bayan daya yace yanzu wacce shawara kuka yanke? shin zakuyi wannan tafiyane akan dawakai ko kuwa akan aljanu zaku tafi? gaba dayansu sukayi shiru suna dùban juna aka rasa wanda zaice uffan daga can sai gimbiya ashwarya tace haba ya za'ayi mu zabi wahala alhalìn ga sauki aikawai ka hadamu da hadimankasu kaimu nikam na sallama rayuwata don ceton mahaifina, dadaina koma gida babu maganin cutar nan gwara na mùtum awajen nemansa koda ta gama fadin haka saita dubi yarima lubaiku, yarima larbuz, yarima sammaru, yarima lauhana, da boka karluz tace shin acikinku akwai mai shawara daban wadda batayi daidai da tawaba? gaba day@nsù suka sakeyin shiru daga bisani suka ce muma mundauki zabinki na t@fiýa akan hadimam hulumul bakahur koda jin haka sai boka hulumul bakahur ya kyalkyale da dariý@ yace yanzun nan kuwa zaku tafi izuwa kogon muddarul ikisina batareda bata lokaciba boka hulumul bakahur ya kira sunayen wadansu aljanu guda shid@ guluz, amzil, hurus, karmash, karfil da azgar suka bayyana agabansa, gaba dayan wadannan aljanu sun kasance manya manya masu siffofin jakin dawa saidai sunada fuka fukai guda hudu, kuma sunada hannaye hur hudu irin na bil'adama masu dauke da yatsu biyar da cako cakon farata, komai nasu iri dayane babu wanda yafi wani girma kuma jikinsu gaba d@ya alullube yake da farin gashi tamkar fatar rago kuma ga laushi boka hulumul bakahur ya dubi aljanun shida yace yaku manyan hadimaina kuyi sani cewa ban kiraku nanba saidon ku debi jaruman nan guda biyar tare da boka karluz ku tafi dasu izuwa tsakiyar duniyar nan tamu inda bishiyar gwandar nan take mai tsawon zira'I dari uku kodajin wannan batu saì guluz, amzil, hurus, karmash, karfil da azgar suka fashe da kuka gaba d@yanSù, cikin matukar damuwa guluz ya dago kai ya dùbi boka hulumul bakahur yace ya shugabana kayi sani cewa babu wani aiki da z@ka umarcemu dayì muki yinsa ina mai rokonka daka sauya mana wannan aiki d wani domin tabbas mumsan bamu isa mu iya kètarè dazuzzukan nan guda uku b@ masu mugun hatsari face mun zama gawa kayi sani cewa iyayenmu da kakannin mu sun hallakane acìkin wadannan dazuzzukan lokacinda suke bauta ga mahainka, mai zai hana kayi mana adalci muci gaba da rayuwa. Mu hadu a part F din Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️ **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART F ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Wannan kalami na aljani guluz ba karamin firgita jaruman shida yayiba domin sun fara tunani aransu cewa lallai abinda yasa aljanun firgita b karami bane yarima sammaru da gimbiya ashwarya ne kadai basu firgitaba domin sun sallama rayuwarsu bisa wannan tafiya basa tunanin dawowa araye saidai da yake dan adam baya fitar da rai ga samun rabo suna masu fatan samun dacewa boka hulumul bakahur ya dubi aljani guluz ya daka masa tsawa yace dolene kuyi wannan tafiya walau zaku dawo ko ba zaku dawoba idan kuwa kuka bijere mini dayanku bazai sake shakar numfashiba cikin rawar jiki su duka sukayì sujjada ga hulumul bakahur suna masu cewa tuba muke ya shugaban mu ba tareda bata lokaciba hulumul bakahur ya sa aka kawowa matafiyan guziri mai yawa aka dora akan aljanun guda shida sannan hulumul bakahur ya dauko wani mulmulallen siririn ice wanda akan tsininsa akwai kyallin haske ya mikawa yarima sammaru yace kaine shugaban wannan tafiya ungo wannan ka rike idan kukaje gindin wannan doguwar bishiyar gwandar kayi nuni da wannan ice izuwa karkashinta take kasa zata bude ku shige cikinta harku isa tsakanin duniyar bakwai da duniya ta takwas inda kogon muddarul ikisina yake ku sani cewa tun kafin ku shiga cikin karkashin kasa zakuyi sallama da wadannan hadiman nawa wato guluz don su dawo gareni idan har sun tsira da rayuwarsu kafin ku isa hulumul bakahur ya bude tafin hannunsa sai g wani kuttu yace ungo wannan ka rike shi da kyau bakomai bane face maganin rauni duk wanda yaji ciwo acikinku ku zuba masa wannan maganin akan ciwonsa take jinin zai tsaya kuma ciwon zai warke sumul komai girmansa da muninsa wannan ce kadai gudun mawar da zan iya baku ta karshe ina mai muku sallama tareda fatan samun nasara tabbas nasararku nasarata ce ina mai yi muku tuni da cewar koda kun samu nasara ba lallai bane ku dawo gabadayanku ba cikin koshin lafiya koda boka hulumul bakahur yazo nan azancensa saiya juya ya shige cikin wata kofa ya kulle jaruman suka tsaya suna kallon junansu sukuwa aljanun sai sukayì zugum kamar an aiko musu da sakon mutuwa boka karluz yace to me muke jira ne aisai kuzo mu tafi kafin dayansu yace wani abu tuni boka karluz y haye bayan aljani guluz cikin sauri yarima sammaru ya daka tsalle ya dirga akan aljani amzil yauhana ya hau kan hurus, yarima lubaiku ya hau kan karmash yarima larbuz ya hau kan karfil, itakuwa gimbiya ashwarya ta daka tsalle ta haye kan aljani azgar nan take aljanun suka bude fukafukansu suka tashi dasu sama suka fice daga fadar ta cikin wata wangamemiyar taga sannan suka luluka sama sukaci gaba da tsala gudu duk wanda yaga wadannan aljanu guda shida asararin sama awannan lokaci dolene su birgeshi su bashi sha'awa amma inda yasan inda zasu nufa da saiya zubar musu da hawaye su baka tausayi WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU YARIMA SAMMARU BAYAN SUN HADU SU SHIDA AFADAR BOKA HULUMUL BAKAHUR al'amarin bokanya tazubul luhucul kuwa lokacinda ta isa birnin hindu tareda hadimanta bata samu wata matsala domin cikin 'yan dakiku kadan ta sami nasarar sakawa sarki bahacal cutar mutuwar barin jiki tareda duk makusantansa batareda bata lokaciba ta wuce birnin farisa acanne ta gamuda muguwar matsala wadda tasa taji kamar ta fashe da kuka bakomai bane ya janyo hakanba face ta tararda cewa sarki katimul barhul da yan majalisarsa sun kasance tare waje daya sunata bautar gunki acikin wani daki na gidan sarautar daya bayan daya ta rinka tura hadimanta don cika aiki duk saida suka mutu guda daya ce tayi saura, saida rabin jikinta ya kone wannan hadiman na kiranta da suna izlis yayinda izilu taga rabin jikinta ya kone saita fashe da kuka ta dubi lazibul luhucul tace ya shugabata kinga dai abindaya faru ga yan uwana duk sun mutu saura ni kadai, nima din kuma gashi rabin jikina ya kone, kiyi sani cewa babu irin dabarun da bamuyiba, don ganin mun sami sa'a amma abu ya faskara , na rantse da darajar tsafinki idan kika sake turani mutuwa zanyi ina mai rokonki dakije da kanki ki aiwatar da wannan aiki domin yafi karfina kodajin haka sai jikin tazubul luhucul yayi sanyi ta kasa cewa komai daga can sai idanunta suka ciko da kwalla bakomai bane ya haddasa hakanba face takaici da bakinciki wai ace kamar ita yau ga wani aiki ya gagareta cikin tsananin fushi tazubul luhucul ta bace ta bayyana akofar dakin da sarki katimul barhul da yan majalisarsa suke ciki suna bautar gunki kai tsaye tasa hannunta n hagu ta bude kofar ahankali faruwar hakan keda wuya sai wani irin haske ya fito daga cikin dakin ya bugi hannunta take hannunta ya soye ya motse kamar an tsoma auduga acikin ruwan zafi tazubul luhucul ta kwarara ihu mai ban tsoro ta bace bat daga wajen saitaga ta sake bayyana agaban azlis koda azlis taga shugabarta da motattsen hannu saita sunkuyar da kanta don biyayya a sannan ne ta tsuguna kasa ta fashe da kukan bakin ciki domin tunda ta fara harkokin tsafi bata taba samun bacin ranaba say yau ba zato sai taji an dafa kafadarta ta baya cikin razani ta waigo sukayì arba ba wata bace tsaye akanta ba face kawarta kuma uwargidanta aljana saubatul azwas itama hannunta na dama ya zama dungulmi kuma hawaye na zuba a idanunta tazubul luhucul ta fasheda kuka sannan suka rungume juna itada saubatul azwas her tazubul luhucul ta bude baki zatace wani abu sai saubatul azwas tayi mata nuni da tayi shiru kawai saita dafata suka bace tare suka bar izlis atsaye awajen ba tareda sanin abinda zatayiba saubatul azwas da tazubul luhucul suka bayyan agaban gidan sarautar sarki katimul barhul nesa kadan kawai sai saubatul azwas taga wani katon mulmulallen dan buda ya taho daga sama ya fado kan rufin dakin dasu sarki katimul barhul ke ciki al'amarin daya haddasa girgizar gidan kenan gaba dayansa tareda wata irin kara mai iya kashe dodon kunne nan take sarki katimul barhul da yan majalisarsa suka firgice kuma suka watse kowa ya cika wandonssa da iska sai gashi suna kokawar fita daga dakin bautar aikuwa duk wanda ya fito sai ya fadi rabin jikinsa ya shanye dayansu bai kubuta daga masifarba koda ganin haka sai farin ciki ya lullube tazubul luhucul da saubatul azwas suka rungume juna suna masu kyalkyala dariyar mugunta her suka bace agaban izlis suka sake bayyana suna kyalkyala dariyar bayan sun nutsune tazubul luhucul ta dubi saubatul azwas tace yake kawata yaya akayi kika rasa hannu guda daya? koda jin wannan tambaya sai fuskar saubatul azwas ta yi bakin kirin tace yake kawata kiyi sani cewa inbadon da sauran kwananaba aduniya da tuni na hallaka abirnin misra, lokacinda naje garin n iske sarki usman da duk mutanensa nayin ibadarsu awannan lokaci ko kusa da gurin ibadarsu ban isa najeba koda naga saura dakika dari uku lokaci y kuremini sai nayi kundun bala n fada gidan sarki usman ai kuwa ina taba kofar gidan sai hannuna ya kone kurmus bisa dole na bace daga wajen na koma bayan gari awannan lokaci saura dakika dari lokaci y cika nanfa na zauna ina takaici da bakin cikin abu biyu wato rashin sa'a da kuma nakasa kwatsam saiga wani aljani waishi kalmus kalmus yakasance ma'abocin addinin muslunci ne amma kuma yana muna furtar musulman duniya ya kasance mai himma wajen bautar ubangijinsu na musulunci dayin addu'o'i ka'in da na'in dare da rana amma fa bisa samun biyan bukatun duniya idan her kalmus yaji zai sami kyautar dukiya mai yawa babu irin aikin da bazai iyayiba koda kalmus ya bayyna agabana saiya rissina ya kwashi gaisuwa yace yake saubatul azwas inda zaki biyani wani abu daga gareki dabaje na aiwatar da burinki akan sarki usman da 'yan majalisarsa koda jin haka sai farin ciki ya kamani nace fadi abinda kakeso indai I na dashi zan baka kalmus yace inason ki bani makullin taskar dukiyarki naje na debi iyakar iyawata koda jin haka sai nayi shiru Ina tunani bakomai ne y sani wannan tunani ba face sanin cewa shekarata dubu bakwai d dari bakwai ina tara wannan dukiya acikin wani kogon dutse mai tsananin tsawo da fadi babu komai acikinsa face akwatunan lu'u lu'u,zinare, jauhar, murjani, yakutu da zubar daji wadanda ni kaina bansan adadinsuba, kullum saina kai akwatu dubu cikin wannan kogo banida burin tsaywa da kai akwatunan sai nan da shekaru guda dubu bakwai da dari bakwai sannan ne nake ganin babu wani mahaluki daya kaini tarin dukiya kisani cewa na tsafance wannan taska ta dukiyata yadda babu wani mahaluki daya isa ya shiga face ya mallaki wata kuba mai lakabi da miftahul dinar ko yaushe wannan kuba tana makale a kuguna kuma adaure kamar guru bayan nayi dan tunani na tuno da mahimmancin aikin dake gabana saikawai na fiddo kubar miftahul dinar na baiwa aljani kalmus ai kuwa yana karba saiya fizgi sihitacciyar hodar nan yaje ya watsawa su sarki usman da yan majalisarsa duk suka kamuda ciwon barin jiki. https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share Mu hadu a part G don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️ **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART G ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ #LEGends. https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share Marubucin littafin ya ci gaba da cewa... Daga nan sai kalmus ya kama hanya y tafi izuwa taskar dukiya ta wacce ke can karshen bangon duniya ta arewa saida kalmus yaje tsakiyar teku yayi kicibus da sarkin barayin aljanu

Chapter 2 of 6