Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
dole badon son ransu ba dama tun akan hanyar sun tabaji igiyoyi na danyar jijiyar bishiya nantake aka fito da ita kowa ya daura ajikinsa tamau yadda bazai kwanceba sai da kyar yarima sammaru ne akan gaba, sannan ashwarya, sai yauhana da karluz, aljani guluz ne daga karshe kuma duk suna rike da hannun juna kai tsaye suka nufi cikin dajin halalul masur yayinda suke kara kusantar radadin zafin wuta koda suka zo gaban gadar nan waddaa akayi da itatuwan danyen kara sukaga yadda iska ke majaujawa da ita saiduk suka razana har dashi kansa jarumi ssammar sai da yaki kamar ya koma da baya amma daya tuna wahalar da suka sha abaya saiya dake cikin karfin hali da dakakkiyar zuciya ya kama gadar da hannu guda sannan ya dora kafarsa akai ya fara tafiya domin basu da wani zabi face bi takan gadar. tun da sama da kasa wutace keci ganga ganga gadarce kadai a tsakiya kuma itama wuta na lasota daga sama da kasa babu abinda zai baka mamaki face wutar dake ci a sama domin da zarar mutum ya daga kansa sama saiyaga babu gajimare ako'ina sai wannan kazababbiyar wuta cikin sauri sammaru da abokan tafiyar sa suka haye kan gadar suka fara tafiya ahankali cikin hikima, don kada kafafunsu su zame faruwar hakan keda wuya sai iskar nan mai karfi ta kada al'amarin daya janyo hautsinewar gadar kenan tamkar tamkar an shilla majajjawa saiga su jarumi ssammaru asama suna katantanwa cikin tsananin juriya sammaru ya tattare karfinsa gaba daya yaci gaba da rike gadar yazamana gaba daya karfin abokan tafiyarsa na jikinsa idan harya gaji ya saki igiyar gaba dayansu ne zasu subuto su fado cikin wutar dake kasa kawai sai rigar jikin ashwarya ta kama da wuta haka kuma kafar aljani guluz ta kama ci da wuta cikin dimauta ashwarya ta dinga gwada sirrikan tsafinta da kyar ta samu ta kashe wutar dake cin rigarta sannan ta kashe wadda ta kama kafar aljani guluz amma kafin hakan tuni kafar guluz ta kone kurmus kamar wacce aka tsamo daga cikin tafasahshen ruwa itakuwa rigar ashwarya ta fatattake ta kone amma kokadan fatar jikinta bata taba ba ana cikin wannan haline gajiya ta riski yarima sammaru baisan sa'adda ya saki gadarba gaba dayansu suka rikito zasu fado cikin wuta su duka ba zato ba tsammani sai sukaji an rukosu gaba daya suna reto asaman gadar kuma hannun sammaru aka ruke cikin sauri sammaru ya dago kai yayi arba da wanda ya rike hannunsa ba wani bane face gimbiya fauwaza 'yar sarki usman na birnin misra tana zaune akan gabjejen farin aljani mai kwarjini da haiba cikin jarumta fauwaza ta dagasu sama su duka ta dorasu akan aljanin dake dauke da ita fuskarta cike da murmushi kawai sai aljanin ya cilla dasu aguje cikin 'yan dakiku kadan suka fice daga cikin dajin cikin kankanin lokaci suka bayyana awani daji wanda babu komai acikinsa face wata bishiyar gwanda guda daya kacal wadda tsawonta yakai zira'i dari uku WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA SU YARIMA SAMMARU BAYAN SUN KUSA HALLAKA ACIKIN DAJIN HALALUL MASUR Al'amarin bokanya tazibul luhucul kuwa da kawarta aljana saubatul azuwas lokacinda suka bace bat tareda hadimarta izlis basu sake bayyana ako'ina ba sai sai acikin kogon tsafin saubatul azuwas suna masu kyalkyala dariyar farinciki bisa nasarar d suka samu ta sanyawa sarakunan duniya cutar mutuwar rabin jiki bayyanarsu keda wuya saubatul azuwas taga wani irin jan hayaki acikin wani kaskon tsafinta koda ganin haka sai hankalinta ya tashi ta dubi tazibul luhucul atsorace tace yake kawata kiyi sani cewa lallai akwai wani mugun abu dake shirin faruwa ga shirinmu don haka ya zama wajibi mu gaggauta bincike kafin tazibul luhucul tace wani abu tuni saubatul azuwas tayi nuni da hannunta izuwa jikin wani farin allon tsafi dake jikin wani dutsen kogo saiga hoton su yarima sammaru tareda jaruma fauwaza akan aljani suna sauka akasa atsakiyar tafkeken dajin nan mai bishiyar gwanda guda daya saukarsu keda wuya sai yarima sammaru ya rude ya rikice saboda kyawun fauwaza da kuma kwarjininta kawai sai ya kura mata idanu ya kasa motsi bare yayi magana tamkar gunki itakuwa gimbiya ashwarya sai kishi ya turnuketa ta murtuke fuska ta dubi fauwaza tace yaake wannan 'yar sarki tayaya kikazo inda muke kika ceci rayuwarmu kuma menene dalilin ki na ceton rayuwarmu? kiyi sani cewa mu ma'abota tsafine, ke kuma ma'abociyar addinin musulunci ce lallai babu alaka mai kyau atsakanin mu sa'adda gimbiya fauwaza ta ji wannan tambaya sai tayi murmushi tace kafin na baki amsar tambayarki inaso ki amsa min tawa tambayar tukunna shin kin sannine da har kike kirana da matsayin 'yar sarki? ashwarya ta bushe da dariya tace kwarai kuwa na sanki bake bace gimbiya fauwaza 'yar sarki usman na birnin misra ai tun kafin muzo nan boka hulumul makahur ya nuna mana acikin madubin tsafinsa sa'adda kike yaki abirnin askandariya kodajin wannan batu sai fauwaza tayi ajiyar zuciya tace kwarai kinyi gaskiya kiyi sani cewa bayan naci birnin askandariya da yaki na wuce izuwa birnin hindu wato kasarku nacisu da yaki sannan na wuce izuwa birnin kisra, farisa, rum, da birnin sin na ci su da yaki kuma na kafa tutar musulunci akasashen yanzu haka duk iyayenku da danginku sun zama musulmai kamata na iske iyayenku akwance acikin cutar mutuwar rabin jiki kuma nayi musu alkawari da izinin ubangiji zanzo musu da maganin cutar yanzu haka mahaifinama na can akwance cikin wannan cutar kuma an nuna mini amafarki sewer shima bazai warkeba harsai na shiga cikin kogon muddarul iksina na debo tsumin bokanya tazibul luhucul dake cikin taskar tsafinta na bashi yasha, domin makarin common da tayiwa iyayenmu na cikin wannan tsumin magani yaku wadannan jarumai idan zakuyi imani da ubangiji na zan shiga cikin kogon muddarul iksina na debo muku wannan tsumin magani acikin sauki ba tareda kunsha wahala ba ko kun hallaka idan kuma ba zaku bayarda gaskiyaba zan rabu daku kowa tasa ta fishsheshi sa'adda gimbiya fauwaza tazo nan azancenta saisu sammaru sukayi tsuru tsuru wannan ya dubi wannan, wancan ya dubi wancan daga can sai gimbiya ashwarya tace muna bukatar muyi shawara kawai saita sauko daga kan aljanin suma suka bita izuwa nasa kadan daga inda su fauwaza suke don su tattauna, ashwarya ta dubi sammaru, yauhana karluz da aljani guluz tace kunji abinda fauwaza ta fada, yanzu shikenan kuna ganin ya kamata mu yarda da ita? babu mamaki fa yaudarar mu takeson da tayi yarima sammaru yayi ajiyar numfashi sannan yace yake ashwarya ina son ki sani cewa su ma'abota addinin musulunci sun kasance kaifi daya basa karya, kuma suna rike alkawari hakika na dade inajin labarin su awajen mahaifina kuma na tsinke da lamarinsu ya kamata my tsaya muyi tunani fa masu iya magana sunce biri yayi kama da mutum tabbas har azuciyata na yarda cewa fauwaza taci kasashenmu da yaki kuma tabbas zata iya shiga cikin kogon muddarul iksina ta debo mana wannan tsumin magani idan baku mantaba ai boka hulumul makahur yayi mana bayani akan haka ko a yanzuma zuwan da tayi t ceci rayuwarmu ai ya ishemu abin ishara nikam na yarda da ita kuma ashirye nake dana mika wuya agareta don karbar wannan addini nata mai tsarki kafin ashwarya tace wani abu tuni sammaru yasa takobinsa ya yanke igiyar da suka daure jikinsu da ita ya tafi izuwa ga fauwaza koda ganin haka sai yarima yauhana yabi bayan sammaru boka karluz kuwa saiya tsaya tareda gimbiya ashwarya sammaru yazo gaban gimbiya fauwaza yace yake wannan kyakkyawar 'yar sarki jarumar jarumai kiyi sani cewa na aminta da duk kalamanki don haka na yarda na karbi addininki kodajin wannan batu sai farinciki ya lullube gimbiya fauwaza alokacin ne yarima yauhana ya karaso agaresu ya dungusa kafarsa guda daya shima ya nuna amincewarsa da karbar musulunci LEGEND IS YOURS ALTHOUGT LIKE AND COMMENT THAT IS OURs MU HADU A PART N DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI βœοΈπŸ™**MATSATSUBI**πŸ’₯πŸ’₯ LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART N ❀️❀️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🀴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ BARKANMU DA SAFIYA ABOKAI, MUNA FATAN ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRAN WANNAN RANA YA KUMA KARE MU DAGA DUKKAN SHARRI πŸ™πŸ™πŸ™ MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA..... Gimbiya fauwaza ta biya musu kalmar shahada suka maimaita gamayin hakan keda wuya ashwarya da boka karluz sukazo garesu da zuwa sai ashwarya ta dubi sammaru idanunta na zubda hawaye tace yakai masoyina kayi sani cewa her abada bazan taba karbar addinin musulunci ba domin ma'abotansane sanadiyar mutuwar kakannina tuni nayi alkawari da zuciyata cewa bani basu har abada, hakika yau ne ranar rabuwata dakai amma ka sani cewa har na mutu bazan daina begenkaba acikin zuciyata, yanzu zamu shiga cikin kogon muddarul iksina nida boka karluz inaso ku saurari fitowarmy da sa'a bakwai idan lokacin ya cika kukaga bamu fitoba to tabbas mun hallaka sai ku kuma ku shiga, da wannan kalami nake maka bankwana idan da rabon mu sake saduwa zamu sadu nan gaba koda ashwarya ta zo nan a zancenta sai idanun yarima sammaru suka ciko da kwalla yaji sonta ya dada mamaye zuciyarsa fiye da koyaushe harya miko hannu zai riketa saita goce ta finciko boka karluz cikin sauri ta fizge icen nan daga jikin sammaru tayi nuni dashi izuwa karkashin bishiyar nan ta gwanda take wani wawakeken rami mai tsananin zurfin da babu karshe ya bayyana wata irin iska mai karfi ta fito daga cikinsa ta zuke ashwarya da boka karluz suka fada ciki suka bace bat, sannan ramin ya bace bat tamkar bai taba wanzuwaba adaidai nan ne aljana saubatul azuwas ta shafi allon tsafinta hoton ya bace cikin tsananin bakin ciki ta kurma ihu sannan ta kama kafadun tazibul luhucul ta girgiza tana mai rusa kuka sannan tace yake kawata tabbas shirinmu yana daf da wargajewa gaba daya idan har bamu dauki matakin gaggawaba........ cikin razani tazibul luhucul tace yanzu wane mataki zamu dauka? babu abinda zamu iyayi face gagarumin sihiri mu tafi izuwa kogon muddarul iksina tareda dukkanin dakarun mu na yaki mu yaki wadannan makiya namu mu kawar dasu daga doron kasa kiyi sani cewa idan aka debo tsumin maganin nan daga cikin taskar ki take jikina da naki zai tsatstsage ya ruguje tamkar rushewar sabon gini karshen mu kenan kodajin wwanna batu sai hankalin tazibul luhucul ya dugunzuma ta rude ta kidime nantake ta kira dukkanin hadimanta wadanda sukayi saura ta umarcesu dasuyi shirin yaki itama saubatul azuwas ta kirawo nata dakarun cikin kankanin lokaci suka hado muggan makaman yaki marasa adadi kala kala harda irin wanda ido bai taba ganin irinsaba sukuwa dakarun yakin saida adadinau yakai dukkaninsu aljanu ne zakwakurai masu dakakkiyar zuciya koda tazibul luhucul da saubatul azwas suka dubi dunbun dakarunsu sai sukaji zuciyarsu ta karfafa duk shakkar da sukeyi ta gushe harma sukeji cewa suna da tabbacin samun nasara akan makiyansu domin suna ganin cewa karfin wannan rundunar tasu yakai su yaki dubiyar ma gaba dayanta ba tareda. bata wani lokaciba tazibul luhucul da saubatul azuwas aukayi wadannan dakarun yakin guda miliyan daya jagora izuwa tsuburin muddarul iksina idan mutum yaga wannan tawaga sa'adda suke tafiya saiyayi zaton gaba daya tsuntsayen duniyane suna gasar tseren gudu acan makeken dajin nan kuwa mai bishiyar gwanda guda daya kacal har yanzu gimbiya fauwaza na tareda yarima sammaru da yarima yauhana da kuma farin aljanin nan suna jiran fitowa ashwarya da boka karluz daga cikin kogon muddarul iksina ahalin yanzu sa'a hudu sun shude saura sa'a uku kacal lokacinda suka debarwa kansu ya cika tsawon wannan lokaci hirace ta barke tsakanin gimbiya fauwaza dasu yarima sammaru inda ta basu labarin irin gwagwarmayar datasha afilin daga yayinda ta yaki manyan kasashen duniya guda biyar da kuma yarda ta rinka samun taimakon allah alokacin ne ta basu labarin wannan aljani wanda ke tareda ita wanda ake kiransa da suna hadimul addin wato fassara sunan nasa na nufin mai yiwa addini hidima hadimul addin ya kasance matashin aljani dan kimanin shekara dari shida da arba'in, tun yana yaro ya taso acikin addinin musulunci sa'adda baifi shekara bakwaiba awata kasa ta aljanu da ake kira madinatul azwab kaf acikin wannan gari babu musulmi guda daya sai hadimul addin shikansa ya karfi addinin ne a wajen wani bafatake da yazo zai ratsa ta cikin garin don cin kasuwa a sirrance wannan bafatake ya sanar da hadimul addin musulunci kuma ya koyar dashi yadda ake bautar allah yayinda hasken musulunci ya ratsa zuciyar hadimul addin ya zamana tsoro da kaunar allah sunyi katutu aransa saiya kebe daga cikin aljanu ya shiga cikin wani kogon dutse mai zurfin zira'i dubu ya zauna aciki yana bautar allah kullum dare da rana bashida wata addu'a face allah ya ba bashi karfin dazai iya yakar aljanun kasarsa shi kadai domin ya kafa daular musulunci lokacinda hadimul addin ya shiga wannan kogo ya zauna yana da shekara bakwai ne kacal aduniya bai gusheba yana bautar allah da yin wannan addu'a harsai daya kai shekara dari shida da talatin da uku suka cika awannan rana yaji wani irin karfi mara misali ya shigeshi cikin kankanin lokaci nantake ya fito daga cikin kogon ya wuce kai tsaye izuwa gidan sarki koda shigarsa cikin fada aka ganshi buzu buzu cikin ga shi babu aski sai aka bushe da dariya ana tsammanin mahaukacine hadimul addin yayi tsaye agaban sarki yana kai kallonsa ido da ido yace yakai wannan sarki kayi sani cewa nine wane dan wane yau shekara ta dari shida da talatin acikin dutse ina bautar ubangijin musulunci wanda bai haifaba ba'a haifeshiba, shine wnda bashi da farko bashi da karshe shine sarkin da ba shida kishiya kuma shine ya halicci sammai da kassai da duk abinda ke cikisu yakai wannan sarki ina mai kira agareka daka daina bautar wanin ubangijin musulunci ka dawo izuwa tafarkin gaskiya idan kuma kaki zan yakeka na kafa tutar musulunci awannan kasar tun sa'adda hadimul addin ya fara wannan jawabi nasa fadar gaba daya tayi tsit ana sauraro da mamaki koda ya gama jawabin sai zuciyarsa ta kama tafarfasa ya dubi hadimul addin ya daka masa tsawa yace kai yaro karyarka tasha karya ire irenka sunzo nan da irin wannan furuci kafin kai duk baga bayansu barekai daka zamo dan mu lallai yau zan bar abin misali akanka na rantse da darajar tsafi waninka bazai. sake sha'awar kawo wargiba kamar yadda kayi nan take sarki ya dubi wasu dakarunsa yace ku kama wannan yaron ku daureshi tamau hannu da kafa sannan ku dinga yankar naman jikinsa sala sala harsai kunyi gutsun gutsun dashi kafin sarki ya gama rufe bakinsa tuni dakarun nan sun afkawa hadimul addin nanfa wuri ya yamutse cikin dakika biyar ya karkashesu dukda cewa adadinsu yakai dubu goma kuma baiyi amfani da makamiba ko guda daya da karfin damtse kawai ya rinkayi musu dundu da barin makauniya duk makaminda suka buga ajikinsa baya tasiri tamkar sun sari dutsene, koda ganin haka sai sarki ya ruga cikin gida ya sami guri ya labe, nanfa dakarun garin gaba daya sukayi ta shigowa cikin fadar sukayiwa hadimul addin kawanya sama dasu dubu dari tara da casa'in da bakwai sai da aka kwana dari ba daya ana yaki tsakanin aljani hadimul addin da wadannan dakarun amma shi kadai ya kashesu gaba daya sannan ya shiga gidan sarautar ya kamo sarkinsu ya murde masa wuya daga nan ya tara al'ummar garin gaba daya ya musuluntar dasu koda suka nemi ya zama sarkinsu sai yace bashida bukata, daga wannan rana hadimul addin yaci gaba da yakar kasashen kafiran aljanu kawo iyanzu ya yaki kasashe dubu bakwai da saba'in da bakwai yana kan wannan aikine allah ya sadani dashi na nemi taimakon sa akan ya kawo ni nan don na taimake ku kuma na sami damar shiga kogon muddarul iksina koda gimbiya fauwaza tazo nan a zancenta sai mamaki ya kama yarima sammaru da yarima yauhana suka kara imani da allah suka tabbatar da cewa babu wani abu dazai gagari allah hakadai hira taci gaba da gudana har sa'a bakwai ta cika su gimbiya ashwarya basu fito ba daga karkashin bishiyar yayinda yarima sammaru yaga basu fitoba saiya kaddara aransa cewa tuni ashwarya sun mutu don haka sai idanunsa suka ciko da kwalla ya fara zubar da hawaye koda gimbiya fauwaza taga halin daya shiga saita cire farin kyallen data rufe fuskarta dashi suka dubi juna Ita da sammaru tace yakai sammaru shin idan ka aureni bazan debe maka kewar ashwarya ba? tabbas wannan hawayen dake zuba daga idanunka domintane. MU HADU A PART O DON JIN **MATSATSUBI**πŸ’₯πŸ’₯ LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART O ❀️❀️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🀴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ CIGABAN LITTAFIN ✍️✍️✍️ Koda jin wannan batu sai yarima sammaru ya ji gaba daya bakin cikinsa ya yaye tunanin ashwarya ya gushe daga zuciyarsa baisan sa'adda yayi murmushi ba yana mai cewa yake sarauniyar kyawawan duniya hakika duk wanda ya mallakeki tamkar ya sami maganin takaici da bakin ciki n zan kasance mai matukar farinciki idan kika zamo matata fauwaza tayi murmushi tace idan har muka fito daga cikin kogon muddarul iksina araye nayi maka alkawarin kaina tana gama fadin hakan ne ta umarceshi da hawowa kan aljani hadimul addin ba tareda bata lokaciba ta umarci shima yauhana da ya hawo kan aljanin fauwaza ta daga hannayenta biyu sama tana mai rokon allah da sunayensa kywawa guda dari b daya ya ubangijin komai da kowa na rokeka dan isarka da isar mulkinka ka shigar damu wannan kogon na muddarul iksina inda wadannan makiya namu suka boye tsumin maganin da muke nema ka bamu nasara akansu har mu fito lafiya gama rufe bakinta keda wuya sai kasa ta tsage hanya ta samu take aljani hadimul addin ya shige dasu ciki sukayita tafiya akarkashin kasa kamar na zasu tsaya ba bisa taimakon allah suka iso tsubirin muddarul iksina acikin rabin sa'a alhalin kuwa tafiyar shekara goma sha biyu ce ga sadaukin aljani mai matukar jarumta da karfin gudu koda isowarsu bakin kogon sai suka ga gawar gimbiya ashwarya data boka guluz GASKIYA NI AKAN RA'AYINA BANJI DADIN MUTUWAR GIMBIYA ASHWARYA BA AMMA BANSAN NAKA RA'AYIN BA MAI KARATU Akwance kirajensu afafe alamar aljanu ne suka kwakule cikinsu cikin hanzari su sammaru suka kautarda kansu ga barin kallon gawarwakin cikin yanayin tausayi d tashin zuciya nan dai fauwaza da hadimul addin suka cigaba da karanta addu'o'i take kofar kogon ta bude da kanta suka shiga ciki da shigarsu suka tsinci kansu acikin wata irin tangamemiyar fada mai girma da fadi babu komai acikinta face tarkacen tsafi iri iri fiye sa kala miliyan dubu a tsakiyar fadar kuwa wata irin katuwar tukunya ce atsaye cikin iska itadai wannan tukunya an cikatanr da saiwoyin itatuwa guda miliyan dubu daya kowacce saiwa tana maganin cuta kala daban tukunyar ta cika fam da saiwoyin sai fitar da wani irin tururi takeyi fauwaza taci gaba da karanta addu'o'i har tazo gaban wannan tukunyar da zuwa saita fiddo watta babbar battar fata ta tsoma acikin tukunyar saida battar ta cika fam da ruwan maganin sannan ta tsamota ta kulle bakinta ta ratayata aka fadarta faruwar hakan keda wuya sai su bokanya tazibul luhucul suka bayyana acikin kogon tareda dakarun yakin su guda miliyan dubu daya kafinsu fauwaza suyi wani yunkuri anui musu kawanya babu ta inda zasu ratsa su fita daga cikin kogon tazibul luhucul da saubatul azuwas suka karewa su fauwaza kallo sannan suka bushe da dariya alokaci guda kuma suka murtuke fuska saubatul azwas tayi nuni da dan yatsanta izuwa ga aljani hadimul addin tace kai karamin kwaro maci amanar aljnu kayi sani cewa na dade ina shiri akanka inda shirina ya kammala kafin kazo nan da tuni ka zama mushe amma dukda haka rana bata baci ba yau zan gama dakai domin nasara na garemu ma'abota tsafi cikin fushi hadimul addin ya dakawa saubatul azwas tsawa yace ke tsohuwar munafukar allah, ba tacciyar wadda ta dade tana sabo adoron kasa kiyi sani cewa yaune ranar da dubunki zata cika dake da wannan munafukar ta kusa dake da izinin ubangijin gaskiya sai mun ragargaza ku mun kawar daku daga doron kasa saubatul azwas ta sake bushewa da dariya sannan tace ai sai angwada akan san na kwarai kuma sai miya ta kare ake sanin maci tuwo cikin tsawa saubatul azwas ta dakawa dakarunta tsawa tana mai basu umarnin su afka musu nan take wuri ya hargitse da masifaffen yaki aljani hadimul addin ya tari dakarun aljanun gaba daya shikadai ya zame musu annoba, fauwaza ta tari saubatul azwas suka fara karawa, shikuwa yarima sammaru ya tari tazibul luhucul suka ware gefe daya inda ta fara kyalkyala dariyar mugunta tace kai karamin alhaki yaune ranar da zan nuna maka cewa ba sani ba sabo, kuma alkawarin dana dauka abaya na cewar bazan taba kaba ya kau tabbas sai na yanke kanka na tafi dashi har gaban mahaifinka nanuna masa dan bakin ciki ya kasheshi ya mutu tun kafin lokacinsa ya cika kodajin haka sai shima sammaru ya daka mata tsawa yace ke bakar annamimiya munafukar allah kiyi sani cewa yanzu da da ba daya bace ada ina cciki jahilci amma yanzu hasken ilimi n gaskiya sun baibayeni baki isa ki sami nasara akainaba da izinin ubangijin musulunci saina yi miki kisan gilla domin na huce takaicin wahalar da kika jefamu aciki nida abokan tafiyata da kuma iyayenmu domin jininki ya zama ga rayukan da akayi asara ki sani cewa saduwarmu da gimbiya fauwaza ba karamin rahama bace agaremu domin itace ta cece mu daga hallaka a dajin halalul masur har muka kawo iyanzu. kafin sammaru ya gama ruglfe bakinsa tazibul luhucul ta nuna shi da sandar tsafinta wani irin haske ya bugeshi yayi sama y bugu da ginin dutse ya fado kasa a sume, nanfa tazibul luhucul taci gaba da dariyar mugunta awannan lokaci ne yauhana ya lura da abindake faruwa g sammaru cikin karaji ya daga takobinsa sama yana mai kabbara ya durfafi tazibul luhucul aguje da nufin ya sareta koda taga ya taho gareta gadan gadan saita fara nunashi da sandar ta ta tsafi bisa mamaki saitaga tsafin nata yaki yayi tasiri sakamakon kabbarar da yakeyi, al'amarin daya firgitata kenan tayi sauri ta bace acan bangaren fauwaza da saubatul azwas kuwa addu'a da tsafine suka hadu da zarar saubatul azwas taga fauwaza zatayi mata lahani saita bace bat shikuwa aljani hadimul addin tuni yayi fata fata da dakarun nan guda miliyan dubu daya ya kashe kusan rabinsu duk inda ya kutsa kansa saidai kaga suna yanke jiki suna faduwa kasa matattu yana cikin wannan haline ya waigo yaga halinda gimbiya fauwaza take ciki kawai saiya kwalawa fauwaza kira yana mai yi mata tuni data karanta wata addu'a nanda nan kuwa fauwaza ta fara addu'a afili al'amarin daya janyo karyewar alkadarin saubatul azuwas da tazibul luhucul suka kasa bacewa kenan nanfa fauwaza da yarima yauhana suka kuntata su da sara da suka ya zamana cewa babu abinda yake tasiri face tsagwaron karfin damtse da jarumtaka dukda cewa tazibul luhucul ta tsufa saidata nunawa yauhana tsohon kashi ashe wannan sandar tata ta tsafi takobice take ta zare ta ta dagata ta shiga kai masa sara da suka harta sami nasarar yi masa yanka guda uku daya aka daya akafarsa daya kuma adamtsen hannunsa na dama bashiri ya saki takobinsa ta fadi kasa adaidai wannan lokacinne yarima sammaru ya farfado cikin zafin nama ya mike tsaye yana mai kwalla kabbara kawai sai ya suri takobinsa yayi kan tazibul luhucul ta hauta da sara da sara da suka cikin sauri da bajinta tun tana iya maida martani har ta kasa ya zamana tana kokarin kare kanta kawai take suna cikin hakane sammaru ya shammaceta ya daka tsalle asama ya fille mata kai take kan yayi sama jini yayi tsartuwa ginger jikinta ta fadi kasa riki ca koda ganin abindaya faru sai saubatul azwas ta kwarara uban ihu ta bude fuka fukanta ta nufi kofar fita daga cikin kogon cikin sauri gimbiya fauwaza ta karanta wata addu'a ta tofa mata koda yawun bakin fauwaza ya dira ajikin saubatul azwas sai gaba daya jikin nata ya kama da wuta nanfa ta dinga kurma ihu mai ban tsoro wanda ka iya kashe dodon kunne cikin dakika uku tayi bindiga ta tarwatse ya zamana sassan jikinta yayi gutsun gutsun adaidai wannan lokacinne aljani hadimul addin ya gama da ragowar dakarun dayansu bai tsira da rayuwarsa ba koda su sammaru sukaga sun sami nasara sai farinciki ya lullube su take sukayi wa allah godiya sannan aljani hadimul addin ya debesu ya fitar dasu daga cikin muddarul iksina dama battar maganin nan tana rataye bisa kafadar bisa kafadar gimbiya fauwaza aikuwa suna fitowa daga cikin kogon sai taskar ta kama da wuta gaba daya ta kone kurmus duk abubuwan dake ciki suka kone kurmus suka zama toka aljani hadimul addin bai hutaba saidata kai su sammaru gidajensu kowa ya baiwa mahaifinsa tsumin maganin nan yasha ya warke daga cutar mutuwar rabin jiki hakama sauran sarakunan guda hudu wato mahaifin gimbiya ashwarya da duk 'yan majalisarsu saida suka sha wannan tsumin suka warke lokacinda iyayen ashwarya, lubaika, sukaji cewa 'ya'yayensu sun mutu akokarin nemo wannan mahagani sai suka fashe da kuka sukayi ta bakin ciki mara misaltuwa ita kuwa gimbiya fauwaza saita sake komawa birnin misra tareda yarima sammaru ta gabatar dashi awajen mahaifinta amatsayin wanda zata aura, ba tareda gardaamar komaiba sarki usman ya amince aka daura aurensu, bayan nan ne yarima sammaru ya dauki matarsa gimbiya fauwaza ya koma kasarsu inda ta karbi mulki daga hannun mahaifinsa suka ci gaba da rayuwar ango da amarya cikin jin dadi da kwanciyar hankali. MU HADU A PART P DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI βœοΈπŸ™ **MATSATSUBI**πŸ’₯πŸ’₯ LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART Q ❀️❀️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🀴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️ KT TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ TAKUN KARSHE ✍️✍️✍️✍️✍️🀸🀸🀸 Yaku 'yan uwa da Abokai na wannan gida Mai Albarka, masu bibiyar littafin mu na MATSATSUBI. kuyi sani cewa a yau Allah yasa muka kawo karshen wannan littafi na uku, sannan Kuma zamuci gaba da na gabanshi wato MIFTAHUZZARBIL insha Allah a ranar LARABA✍️✍️☝️ muna fatan Kuna nishadantuwa da irin Labaran da muke Dora maku.. Fatan Alheri a gareku ✍️✍️☝️ Najibullahi Muhammad #LEGENDs of KATSINAπŸ’ͺ βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“ MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Koda sarki dujalu yazo nan alabarinsa sai boka hajarul makarus yayi ajiyar zuciya yace yakai wannan sarki shin yanzu kayi imani da addinin musulunci? hakika wannan labari gaba dayansa yana nuni ne da nasarar mabiya addinin musulunci koda jin wannan tambaya sai sarki dujalu ya bushe da dariya sannan yace yakai wannan boka kayi sani cewa abinda ya hanaka karbar addinin musulunci shine ya hanani karba amma ka sani cewa idan akazo da labari ana fadin hakikanin gaskiyar labari domin idan na boye gaskiyar wata kila nan gaba xata fito da kanta da wannan kalami nake muku bankwana saiku tafi domin na sallameku dama iyakar hikayoyin danayi muku alkawari kenan cikin murna da godiya tsoho rafkanagu, ruziyal da hajarul makarus suka tattara inasu inasu suka fice daga cikin fadar daga nan suka cigaba da tafiya da kafafunsu saida suka isa bayan gari sannan rafkanagu yayi girgiza yace yanzu kuma ina muka dosa? ruziyal yace ai yanzu kuma birnin sin zamuje don mu samo wadansu muhimman labarai awajen sarki mazluch kodajin haka sai boka hajarul makarus yayi tsaki yace kawai kace baya zamu koma ruziyal yace kaga aiba laifina bane abune akan tsari kamar yadda na ziyarci kasashe bi da bi harsaida n rubuta kundub tsatsuba na farko haka ma yanzu zamubi wannn tsari kafin wani dga cikinsu ya kara cewa wani abu tuni aljani.rafkanagu ya suresu su biyun agadon bayansa yayi sama ya nufi birnin sin WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA TSOHO RAFKANAGU BAYAN SUN GAMA JIN HIKAYAR BOKANYA TAZIBUL LUHUCUL AFADAR SARKI DUJALU MAI SIHIRTACCEN SHAYI SHAYINDA IDAN AKASHA SHI BA'AJIN YUNWA DA KISHIRWA KUMA BA'AJIN BARCI DA KASALA Al'amarin boka shamharu kuwa da sarki lu'umanu kuwa lokacinda suka shiga cikin dakin halwar tsafi acan birnin baharzus sai shamharu ya zauna agaban wadansu tarkacen tsafi ya zura musu idanu yana mai nazari da bincike.shikuwa lu'umanu saiya tsaya abayansa ya kame kamar

Chapter 5 of 6