Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
gyara damara don zamushiga inda kabilar dodanni ta hudu take babu mamaki gaba dayanmu mukai labari amma dai jajircewar itace nasarar mu ina maiyi mana fatan nasara da wannan jawabine sammaru ya rufe jawabinsa nan take ya zare takobinsa ya dagata sama yayi ruri suma abokan tafiyar tasa sukayi yadda yayi nan danan ihun nasu ya cika dajin gaba daya al'amarin daya fargar da ragowar dodannin kenan suka fara tsallen murna don sun cewa yau ga abincinsu nan tafe, cikin hanzari jjaruma biyar suka dane bayan aljanun hudu da yake aljani amzil da hurus sun mutu sai yarima sammaru da gimbiya ashwarya sukahau kan aljani guluz tare yarima yauhana, larbuz suka hau kan asgar shikuwa boka karfil shikadai ya haye kan karmash akabar aljani karfil shikadai ba kowa akansa kamar an cilla kibiyoyi haka aljanun suka luluka cikin gajimare suka nausa cikin daji tafiyar da sukayì kadance suka riski kabilar dodanni ta hudu nantake aka garkame da matsiyacin yaki saida aka shafe kwana guda cur ana wannan yakin daya ninka na baya bala'i da tashin hankali a wannan lokacine aljani karfil da yarima larbuz suka mutu yarima sammaru ,gimbiya ashwarya, yauhana da boka karluz kuwa saida suka sume dukda cewa sun gama kashe dodannin gaba daya sai bayan sa'a daya suka farfado, saboda tsananin jigatar da sukayi hakama su aljani guluz bayan hankalinsu ya dawo cikin jikinsu sai bayan sa'a hudu da yake a inda akayi wannan yaki akwai wani kogi sai dukkanninsu suka shiga cikin kogin suka sha ruwa kuma sukayi wanka bayan sun fitone suka zauna suna hutawa tsawon dan lokaci babu wanda yace kala , daga can sai gimbiya ashwarya ta dubi sammaru tace yakai jagoran tafiya kayi sani cewa inada wata shawara agaremu wacce nake ganin zata fisshemu koda jin haka sai sammaru yace fadi shawarar ki muji, yake jaruma mai kaifin basira ashwarya tayi murnushi sannan tace inaganin yana da kyau mu karawa kanmu horon yaki anan wurin domin na fuskanci kowannenmu nada tasa baiwar daban kuma inaganin yakamata mu kirkiri wasu makaman fadan daban wato ina nufin makamai wadanda zasu taimaka mana wajen saurin kashe dodannin nan tunda sun kasance masu yawan gaske koda jin wannan batu sai kowa yayi na'am da shawarar nanfa aka fara tunanin yadda za'a kirkiri sababbin makaman fada sai da aka shafe kusan rabin sa'a ana tunani kowa yayi shiru yana wasa kwakwalwarsa yarima yauhana ne ya fara magana da cewa ni ina ganin mu samo dogayen itatuwa mu ferayesu suyi tsini sannan mu kera manyan baka wadanda za'a dunga harbawa itatuwan ga dodannin suna tsiresu nasan dai mu bazamu iya tabe bakarba, ammasu aljani guluz zasu iyayi koda jin wannan batu sai kowa ya kama tafi nantake akaje aka samo itatuwa masu yawa aka fiffikesu kowanne ice guda bazai daukuba awajen mutum arba'in saboda tsawonsu da nauyinsu amma su aljani guluz da dan yatsa daya suke daukar guda goma bayan an fiffike wadannan itatuwa sai kuma akazo aka kera baka guda uku manya kowacce guda daya tafi yarima sammaru tsawo da nauyi sauran biyun kuwa aka baiwa aljani karmash da asgar nanfa sammaru yayita koya musu yadda ake harba kibiya har suka kware daga nan kuma saisu sammaru suka fara jarraba jarumtaka atsakaninsu ma'ana shida ashwarya suka yaki juna, kowa na nuna tsagwaron karfi, juriya, dabara da jarumtaka haka ma yarima yauhana da boka karluz suma suka ware suka rinka gumurzu awannan karon dai su aljani guluz 'yan kallo suka zama, saida suka cika da tsananin mamakin jarumtaka irin ta gimbiya ashwarya da jarumi sammaru domin kowannensu yayi abubuwan al'ajabi da za'a jinjina masa domin kare jini biri jini sukayi amma abangaren yauhana kafa daya gareshi saida ya wahalar da boka karluz matuka shida kansa ya san cewa ruwa ba sa'an kwando bane domin anfishi karfi, kuruciya da dabarun fada bayan angama baiwa juna horon fada sai kuma aka shirya aka shiga daji na. biyar don asamu nasara akansu cikin kankanin lokaci .kowa yagamsu da shirin, sannan aka zauna aka huta tsawon sa'a hudu wannan karon yarima sammaru baiyi ruriba wato shigar sumame sukayi wa dodannin lokaci guda sukaji ana sakar musu kibiyoyi suna tsiresu kafin dodannin su ankara fiye da rabin su, duk wannan aikine na guluz da aljani karmash da azgar suna cikin wannan barnane kibiyoyin nasu suka kare nanfa ido ya raina fata suka koma bayansu ssammar koda ganin haka sai sammaru, ashwarya, yauhana da boka karluz suka zare takubbansu suka ruga ga dodannin alokaci guda suna ruri suka hausu da sara da suka duk inda suka ratsa sai dai kaga dodannin suna zubewa kasa matattu da yake tun farko an karya lagon wadannan dodannin bisa ganin an kashe fiye da rabinsu basu sami wani karfin gwiwa ba bare su iya karya alkadarin jaruman, nanfa su sammaru suka yita ragargazarsu baji ba gani dukda cewa dodannin sun karaya saida suka kusa hallaka jaruman domin babu wanda bai samu mugun rauni ba ajikinsa akwai wani lokaci da wani dodo ya lumawa sammaru farce agefen cikinsa sammaru yayi ihu ya fadi kasa dodon ya kaiwa sammaru hari da nnufi ya talitseshi cikin zafin nama ashwarya ta janye sammaru daga wajen kafar ta nutse acikin karkashin kasa inda sammaru ya fadi kafin dodon ya cire kafarsa tuni ashwarya tayi alkafira asama ta luma masa takobi a tsakiyar kan dodon dodon ya fadi kasa rikica kamar faduwar giwa haka aka gama wwanna yaki sammaru baya cikin hayyacinsa bisa wannan suka da dodon yayi masa wannan karon kuma babu ruwan maganin da boka hulumul bakahur ya basu tun awancan yakin maganin ya kare dukkanninsu jaruman haka suka kwanta agalabaice babu mai iya tabuka komai gimbiya ashwarya ce kadai mai koshin lafiya shikuwa sammaru yafi kowa galabaita don har wani irin aman jini da kakari yake kamar zai mutu al'amarin daya firgita gimbiya ashwarya kenan bata san sa'adda ta kama kuka ba dakyar boka karluz ya bude baki yace da ita ta bude jakarsa ta dauko wani garin magani ta shashshafA musu aikuwa hannunta na karkarwa ta bude jakarsa da sauri ta dauko magananin saida ta fara shafawa sammaru maganin sannan ta shafawa kowa bayan nan saita koma kusa da sammaru ta zauna ta dora kansa akan cinyarta tana kallon fuskarsa hawaye na diga akansa bazato ba tsammani sai taji sammaru ya kawo gwauron numfashi gami da bude idanunsa nantake farinciki ya lullubeta bata san sa'adda ta rungumeshi ba tana kukan murna sammaru ya mike zaune yana mai kallon fuskarta cikin farinciki yace ''godiya agareki yake ma'abociyar kyawu da kwarjini ina fatan nima nayi miki sakayya irin wacce kika yi min ta ceton raina koda jin wannan batu saì ashwarya tayi murnushi tace sakayya daya nake bukata daga gareka kawai ka bani matsuguni acikin gurbin zuciyar ka ya zamana cewa ni kadaice mai shige da fice da acikinta kodajin haka sai sammaru yaji wani farinciki ya lullube shi harma ya kasa motsi da bude baki dagacan kuma sai yace yake ma'abociyar kyawu da kwarjini kiyi sani cewa tun ranar da idanuna suka fara arba dake naji na kamu da tsananin kaunarki zuciyata da ruhi suka suka aminta dake har ya zamana basa son jin komai akusa dasu face ke tabbas ina matukar begenki da kaunarki kamar yadda da keson iyayensa haarya iya salwantar da rayuwarsa saboda su koda sammaru yazo nan azancensa sai gimbiya ashwarya ta sake rungumeshi suka rukunkume juna kamar ba zasu taba rabuwaba adaidai wannan llokaci su yarima yauhana da boka karluz suka farfado sosai suka mike zaune koda sukaga abinda ke faruwa tsananin gimbiya ashwarya da yarima sammaru sai suka cika da murna aljani guluz da karmash da asgar suka katse shirun dake wajen ta hanyar yin tafi da shewa bisa murnar samun nasarar wannan yaki. MU HADU A PART K DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏**MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART K ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ CIGABAN LITTAFIN.... Cikin hanzari sammaru da ashwarya suka saki juna suna masu jinn kunya. nanfa suka ruga wajen su yauhana da karluz suka rungume su akaci gaba da farin ciki bayan an nutsune sai yarima sammaru yayi gyaran murya ya dubi kowa yace yace yaku yan uwana ku sani cewa yanzu ne fa zamu tunkari kabilar dodanni t karshe wannan kabila tafita sauran bala'i,yawa da karfi don haka ya zama wajibi agaremu muyi shiri irin wanda bamuyi kamarsaba abaya inba hakaba kuma gaba dayan mu babu wanda zaiyi rai kodajin wannan batu sai dukkaninsu hankalinsu ya tashi aka manta da wahalar da aka sha abaya aka shiga fargabar abinda za'a dosa agaba yayinda yarima sammaru ya fuskanci cewa zuciyar kowa ta karaya saiya shiga karfafa musu gwiwa da jinjinawa kowa bisa irin jarumtakar daya nuna abaya lokacin da yaga sun sami kwarin gwiwa sai ya kawo shawarar cewa su sake kera sababbin kwari da baka guda hudu wato shi ya dauki daya ya rabawa su ashwarya,yauhanad ,karluz sauran bayan ya basu yace dasu kada ku harbi ko'ina ajikin dodannin face kansu domin anan ne kawai kibiyar mu zata yi tasiri ajinkinsu amma kibiyar su aljani guluz zatayi tasiri ako'ina ajikin dodannin bayan su sammaru sun tanadi kibiyoyi masu yawan gaske sai kuma suka samo jijiyoyin bishiyoyi danyu murtuka murtuka irin wanda ko mutum yasa kaifin takobi basa yankuwa nan take suka yita saka raga dasu saida suka saka raga mai yawan gaske sannan sammaru ya rabawa kowa aikinsa yayinda aka shiga dajin kabilar dodanni ta karshe yadda ya tsara aikin kowa shine aljani karlaz zai tashi sama ya dinga jeho raga kan dodaninn aljani guluz da asgar zasu tsaya asama ne suna harbo kibiya kan dodannin su kuma su sammaru ta sama zasu ding harbin dodannin da nasu kibiyoyin sai an tabbatar cewa kibiyoyin sun kare sannan za'a far musu da sara aikuwa kamar yadda aka tsara haka al'amari y kasance cikin shammace dodannin nan sukaji an lullubesu kuma ana harbinsu da manyan kibiyoyi da kanana nanfa suka dinga mutuwa kamar annoba kiri kiri dodannin nan suka kasa komai akayita ragargazar su amma da yake yawansu ya wuce kima sai akaga kamar karuwa suke hankalinsu sammaru bai tashiba saida sukaga saura kadan kibiyoyin nasu su kare amma har yanzu basu kashe dodannin ba lokacinda kibiyoyin suka kare say fada ya sauya launi domin ragama ta kare kuma dodannin da raga ta lullube basu mutuba suma suka fire karkatse ragar da kaifin hakoransu suna fita daga ciki,, al'amarin daya firgita yarima yauhana da boka karluz kenan suka juya da baya da nufin guduwa cikin sauri sammaru ya ruko hannunsu yace haba zaratan jarumai ashe kun manta da tsananin wahalar da kuka sha abaya shin mutuwa ce bakuwarku? kokuwa kogin jini ne bakonku? ku tunafa cewa kunga bala'i kunga masifa babu tashin hankalin da baku ganiba karku bani kunya domin maza basa gudu don wuya ko halaka daku mutu ragwaye gwara ku mutu mazaje afilin daga mu hada karfi mu daku da ashwarya tabbas zamu gama da wadannan halittu kamar yadda muka gama da wadancan kodajin wannan batu sai yarima yauhana mai kafa daya da boka karluz mai yankakken kunne sukaji waji sabon karfi ya shigesu kafin sammaru da ashwarya suyi yunkuri tuni sub zare makamansu sun ruga inda dodannin suke cikin hanzari sammaru da ashwarya suka kai musu dauki koda aka hadu da dodannin nan sai wuri ya yamutse, kura ta turnuke sararin sama ihu, ruri da karar karafa ta yawaita nanfa akayita turnuku ruguntsumi, artabu, gwagwarmaya da dauki ba dadi saida aka shafe kwana guda da yini daya ana wannan azababben yaki awannan gumurzune boka karluz ya rasa hannunsa guda na dama domin wani dodone ya gutsureshi yayi loma guda dashi shikuwa yarima yauhana saidaya zamana ko'ina ajikinsa sarane na faratan dodannin jini nata zuba daga jikinsa amma bai fasa ragargazarsuba wani lokacinma saidai kaga ya taso da karfinsa yaci gaba da daukar rai gimbiya ashwarya da yarima sammaru kuwa sun zama tamkar shaidanu atsakiyar dodannin duk inda suka kutsa saidai kaga dodannin na zubewa akasa kamar ana sassabe agona lokacinda gumu yayi gumu sai wani dodo ya shammaci ashwarya ya sureta da hannu daya ya dagata sama da nufin ya rotsata akan wani dutse kamar walkiya haka yarima sammaru ya daka daga can nesa inda yake ya durga agaban dodan kafin ya makata akan dutsen tuni sammaru ya soka masa takobi acikin kwayar idonsa guda bisa dole dodon ya saketa ahankali amma dukda haka saidata fado kasa ta sami rauni agoshinta koda sammaru ya zare takobinsa daga cikin kafar idon dodon sai takobin ta fito tareda kwayar idonsa cake a tsininta nantake dodon ya fadi kasa matacce ashwarya ta mike da nufin ta mike tsaye amma sai wani dodon ya cafi kugunta ya dagata sama kamar ya dauki 'yar tsana kawai saiya bude bakinsa da nufin ya cinyeta nanma sammaru ya sake dako tsalle asama ya saita bakin dodon da tsinin takobinsa tuni takobin ta huda shi ta faso bayan keyarsa ba shiri ya saki ashwarya ta fado tsakiyar dodannin nantake suka kai mata wawa da nufin suyi gutsun gutsun da ita kawai sai ganin sammaru sukayi akansu yana bare musu kawuna da kaifin takobinsa kai atakaice dai saida sammaru ya ceci ashwarya akalla sau goma sha daya awannan yaki amma dukda haka saidata suma sakamakon yawan raunukan dake jikinta bayan sun gama karar da dodannin ne gaba daya su yarima sammaru, yauhana, boka karluz suka yanki jiki suka fadi kasa sumammu aljani karmash kuwa tuni rai yayi halinsa don dodanni sunyi walima da jikkunansu aljani guluz ne kadai atsaye afilin yakin ya tsaya kyam yana shara kuka saboda ganin irin mutuwar wulakancin da yan uwansa sukayi adaidai wannan lokacinne magariba ta doso amma su sammaru basu farfadoba saida sanyin asuba ya busa ,aljani guluz ne ya taimakesu ya bude jakar boka karluz ya debo magani ya shashshaa musu, sannan yaje ya nemo ruwa ya basu suka sha sa'adda ashwarya ta bude idanun taga bata mutuba kuma taga masoyinta araye sai farinciki ya rufeta ta dubi sammaru tace godiya agareka mara adadi yakai masoyina hakika inbadon kaiba da tuni na dade a kushewa sammaru ya yunkura da kyar ya gyara zama ya maida mata damartanin murmushi yace aikema inbadon keba da ban rayuba na kawo iyanzu har na ceci rayuwarki babban farinciki na shine na ganinki araye yana gama fadin hakan ne sukaji boka karluz ya fashe da kuka al'amarin daya dugunzuma hankalinsu kenan gaba daya yarima yauhana yaja kafarsa guda ya matso kusa dashi yace yakai abokina ina dalilin wannan kuka naka karluz yace ka dubi kunnuwana babu su kuma ka dubi hannuna shima babu ka sani cewa har abada halittata ta sauya bazan sake dawowa daidaiba duk wannan abu ya samenine kawai don kwadayin neman sirrikan tsafi akogon muddarul iksina tabbas yamzu na kasance mai nadama bisa barin kasata, dangina da harkata don wannan bukata wacce banida yakinin samun biyanta kodajin haka sai yarima yauhana yayi murmushin yake yace haba abokina aikai kukan dadi kake kadubenifa ka gani kiri kiri na zama gurgu mai kafa daya dole saida sanda zan iya tafiya kuma ka tuna cewa badon bukatar kaina na baro gidaba saidon na ceci rayuwar mahaifin ,ka tuna cewa ni dan sarkine mai takama da mulki amma ga yadda rayuwata ta kasance lallai na fika madama da bakin ciki hakadai akaci gaba da hira awannan waje har yamma tayi dare ya fado atakaice dai saida su sammaru suka kwana biyu awannan wuri suna jinyar jikinsu sannan kowa ya sami kwarin jikinsa yanzudai tafiya ta rage saura su hudu kacal lokacinda sukayi shirin barin wannan wuri ne donshiga daji na biyu wato dajin nan da ake kira zamutul makatul yayinda sammaru ya dubi kowa yace yaku abokan tafiya kuyi sani cewa yanzu zamu shiga cikin jejin zamutul makatul mai dauke da mugayen namun dawa, kuma sihirtattu kamar yadda boka hulumul makahur yayi mana bayani dolene muyi amfani amfani da karfin tsafi da kuma karfin damtse a wannan daji don haka ke ashwarya dake da karluz ne zaku wuce gaba ni kuma ina biye daku in yauhana da guluz su kasance abayana, ina yi muku tuni da cewar wanda duk yasan sirrin daji acikinmu toya dinga nusar damu don musami kubuta da wannan bayanine sammaru ya kammala zancensa ba tareda bata lokaciba ashwarya da boka karluz suka wuce gaba sammaru ya bisu abaya sannan yauhana da guluz saida sukayi tafiyar sa'a guda cif sannan suka iso dajin zamutul makatul dajin zamutul makatul ya kasance yanada dogayen bishiyoyi da manyan tsaunika sannan akwai kwazazzabai da duhuwoyi masu yawa, komai jarumtakar mutum idan ya shigo cikin wannan daji dolene zuciyarsa ta buga don yasan cewa dole asamu muggan dabbobin daji acikinsa da muggan aljanu da shigarsu sammaru cikin wannan daji sai sukaga hanya ta rabu kaso uku hanya ta farko ta nufi inda wadansu manyan tsaunika suke guda uku hanya ta biyu ta nufi inda wadansu dogayen bishiyoyi suke masu yawa ba adadi itakuwa hanya ta uku ta nufi cikin wadansu kwazazzabai ne wasu da ruwa acikinsu, wasu kuma babu da yake gimbiya ashwarya ce akan gaba saita tsaya cak sa'adda aka zo wannan mararraba ta daga hannu alamar atsaya nantake kuwa kowa ya tsaya ashwarya ta waigo ta dubi sammaru tace to ga hanya ta kasu gida uku wacce yakamata mu bi? MU HADU A PART L DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏**MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU✍️✍️ PART L ❤️❤️ Na: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.... Kowa yayi shiru sai aljani guluz yazo ya karewa hanyoyin kallo yana nazarinsu, sannan yace kunga wannan hanya ta farko wacce zata kaimu wajen manyan tsaunikan can tana da mugun hatsari domin ba'a rasa muggan dabbobin daji da aljanu acikin tsaunika domin sukanyi gidajensu aciki itakuwa wannan hanya ta biyu wacce zata kaimu wajen dogayen bishiyoyi anan ne manyan tsuntsaye masu hadari suke buya waccan hanyar kuwa ta uku mai kwazazzabo saidai a samu dabbobin ruwa acikinsu domin mahadace ta teku kodajin wannan batu sai yarima sammaru yace aikuwa indai hakane gwara mubi hanya ta uku domin tafi saukin hatsari nantake gimbiya ashwarya ta wuce gaba suka nufi wannan hanya mai kwazazzabai da yake hanya mai dauke da duwatsu da kuma ruwa saida sukayi tafiyar sa'a guda cif sannan suka iso bakin wata korama wacce sai an wuce ta cikinta sannan za'a hau kan turba koda zuwansu wannan wuri kawai sai aashwary ta daga hannu kowa ya tsaya, nantake tayi 'yan tsubbace tsubbacenta donta gano abinda ke cikin wannan korama amma bataga komai ba face kananan kifaye koda ta gama saita baiwa boka karluz wuri yayi nasa kokarin shima baiga komai ba, kawai sai ashwarya ta fada cikin koramar sannan kowa yabi bayanta kash rashin sani yafi dare duhu inda sunsan masifar da zasu riska acikin wannan korama da basu shigetaba, saida sukazo tsakiyar koramar sannan wata katuwar maciijiya ta taso sama daga karkashin ruwa koda maciijiyar ta mikar da. wuyanta sama sai ya tafi kamar zai tabo rana don tsananin tsawo cciki razani kowa ya zare takobinsa ashe macijiyar nan jeloline da ita barkatai masu tsawo da kaifi tamkar zabira su sammaru suka juya da baya da nufin su fita daga cikin ruwan kawai sai sukaga jelolin macijiyar sun fito sunyi musu kawanya babu inda zasu ratsa su wuce bisa dole suka juya suka tsaya atsakiyar suna kallon wannan dogon wuya nata wanda har yanzu tafiya yakeyi bai tsayaba sa'adda aka shafe sa'a guda sai wuyan nata ya tsaya yakai makura wato iyakar tsawonsa ba zato sai wuyan ya lankwaso kasa wanda shike dauke da katon kan macijiyar bakin ya wangame gaba daya yana aman bakin dafi sannan ga wasu irin hakora gaftara gaftara aciki tamkar an jera hauren giwa guda dari ahankali bakin ya rinka saukowa kasa tamkar yadda wuyan yayi sama dazu ahankali kuma jelolin macijiyar wadanda sukayi wa sammaru kawanya suka rinka kumbura, koda faruwar wannan al'amarin sai hankalinsu sammaru ya dugunzuma kowa ya zare takobinsa yana saran jikin macijiyar saidai kaga tartsatsin wuta yana tashi yayinda takubban nasu ya sari jikin macijiyar tamkar akan dutse suke sarawa nanfa dukkaninsu suka firgice suka saduda cewa ba tsumi ba dabara tabbas hallakarsu tazo sammaru ya nutsu yana nazarin jelolin macijiyar da kuma bakinta wanda ke saukowa kasa ahankali daga can kololuwar sama kawai sai yayi ajiyar zuciya ya dubi ashwarya, yauhana, karluz da guluz yace yaku abokan tafiyata kuyi sani cewa yaufa karyarmu ta kare domin duk abinsa muke takama dashi bazai kwacemuba a wurin macijiyar nan ba ku sani cewa idann ta gama kumbura nantake zata mammatse jikin mu ta kakkarya kasusuwan jikinmu sannan ta lankwamemu da wannan katon bakin nata dake saukowa shin acikin ku babu mai wata dabara wacce zata fishshemu? karluz da ashwarya suka dubi juna kawai sai suka fara jarraba karfin sihirinsu akan macijiyar duk abinda sukayi saiya zamo abanza domin yaki ya fara aiki wannan tasa kowa ya karaya, masu kuka suka fara masu nadama suka ci gaba dayi boka karluz yaci gaba da nazarin kumburin macijiyar dakuma saukowa kanta kasa ya gane cewa adaidai lokacin dakan yazo dafda kawunansu zata kumbura, ta matsesu don haka sai ya cigaba da tunanin mafita azuciyarsa domin shi tun yana yaro baitaba fitarda rai ga samun nasara ba bisa duk abinda yasa agabansa haka dai yaci gaba da tunanin har sa'a guda saida ya rage saura kamu daya tsakanin kawunansu da bakin macijiyar da kuma gangar jikinta danasu boka karluz ya tuno da wata dabara nantake cikin zafin nama boka karluz ya zaro allon tsafinsa ya jefashi cikin bakin macijiyar yin hakan keda wuya sai macijiyar ta kama da wuta ta dinga wani ruri tana faduwa da mikewa acikin ruwan da kyar su sammaru suka samu suka sulale daga jikinta suka haye koramar gaba daya sannan suka yita shara gudu saida sukayi gudu tsawon rabin sa'a sannan suka tsaya suka juya baya daga nan inda suka tsaya din suna iya hango macijiyar har yanzu ruri take tana faduwa da tashi al'amarin daya janyo girgizar dajin gaba daya kenan ahaka dai ta kone kurmus ta daina motsi koda su sammaru suka ga cewa macijiyar ta mutu sai suka zauna dirsan suna haki bayan kowa ya nutsune sai sammaru ya dubi kkarlu yace gaisheka babban boka hakika nayi maka jinjina da godiya mara adadi hakika yau inba don kaiba da tuni mun zama abincin wannan macijiyar shin ya akayi ka tuno da wannan dabarar ta jefa allon tsafinka abakinta? kodajin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa boka karluz alokaci guda kuma ya fashe da kuka al'amarin daya tashi hankalin kowa kenan saida sammaru ya rarrasheshi sannan ya daina kukan boka karluz yayi gyaran murya ya dubi sammaru yace yakai gwarzon jarumi kayi sani cewa bantaba tsammanin cewa idan na jefa allon tsafina abakin macijiyar nan zamu kubuta ba kasan ance komai jarrabawa ake kuma sa'a naga mai rabo lallai rabon kubutar mune yasa na jefa allon tsafina abakin macijiyar kayi sani cewa ba komai ne ya sakani na fashe da kukaba face sanin cewa daga yau na rasa dukkanin sirrikan tsafina har abada kuma bazan sake yin wani abuba wanda yadanganci tsafiba har yayi tasiri har abada saboda na kona allon tsafina da hannuna kaga shikenan na rusa burina na duniya gaba daya duk wahalar nan da nasha abaya ta zama abanza gwarama ace na hallaka tun afarko koda boka karluz yazo nan azancensa saiya sake fashewa da kuka nanfa tausayinsa ya kama su sammaru suka ci gaba da rarrashinsa bayan kamar rabin sa'a sai yarima sammaru ya dubi dukkaninsu yace yaku abokan tafiya kuyi sani cewa mun gama da dajin zamutul makatul yanzu kuma zamu shiga cikin jeji na gaba wanda akekira da halalil masur ina mai tunasar daku cewa shifa wannan daji ne na wata tsafaffiyar wuta maici sama da kasa, gabas da yamma, kudu, da arewa atsakanin sama da kasa ne kawai akayi wata gada wacce saidai mubi ta kanta ne zamu wuce ku sani cewa ita wannan gada anyita ne da zallan itatuwan danyen kara da kuma danyen jijiyar bishiya akoyaushe wuta tana laso jikin gadar kuma wata irin iska mai karfi na jijjigata, kuma duk abin dake kan gadar zai iya hallaka ko kuma ya fado kasa ko kuma iska ta wullashi cikin wuta babu abinda zai kwace mu awannan wuri face karfin damtse hikima da kuma karfin tsafi don haka tun yanzu saimuyi koda sammaru yazo nan azancensa sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zaice uffan aka shiga tunani daga can sai gimbiya ashwarya tace ga tawa shawarar dafarko dai acikin mu nan babu mutum mai karfi da zafin nama kamar sammaru don haka shine ya kamata ya fara hawa kan wannan gada inyaso ni sai na bishi abaya don na taimaka masa da sihirin tsafina yayinda bukatarsa ta taso haka kuma dolene mu daddaure jikkunan mu da danyar jijiyar bishiya ya zamana muna hade da juna yadda karfin iska bazai tarwatsamuba dukda haka dolene mu ruke hannayen juna ya zamana cewa wannan na ruke da wannan aljani guluz ne zai zamo na karshe yarima yauhana kuma ya zamo atsakiya tunda kafa daya gareshi ina ganin hakane zamu cije da karfin tsiya muyi tafiyar kwana guda akan gadar har mu fita daga dajin halalil masur sa'adda ashwarya tazo nan azancenta sai kowa ya gamsu da shawararta kuma aka jinjina mata bisa wannan kaifin basira data nuna tareda tsagwaron hikima da kaifin basira gimbiya ashwarya ta sake duban kowa daya bayan daya tace tofa ku sani wannan dabarar tawa ba lallai bane ta kubutar damuba kawai dai nayi hasashene, zamu iya tsira kuma zamu iya hallaka amma dai mu karfafi zuciyoyin mu akan samun nasara akan wannan bayani ne akarufe bayani kowa ya mike tsaye aka ci gaba da tafiya sai da suka kwana uku suna tafiya sannan suka iso dajin halalil masur koda sukazo daf da farkon dajin sai sukaji radadin zafi na busowa kuma suka hango yadda wuta ke alkafira sama da kasa saiduk suka firgice suka juya da baya yarima sammaru da gimbiya ashwarya ne kadai basu juya da baya ba cikin fushi sammaru ya waiga garesu ya daka musu tsawa yace LIKE DA COMMENT DINKU SUNE SUKE BAMU KWARIN GWUIWAR CIGABA DA ZABO MUKU LABARAI SANNAN MU ZAUNA MUYI TYPING DINSA HAR MUYI MUKU POST. MU HADU A PART M DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏 **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU✍️✍️ PART M ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️ MARUBUCIN LITTAFIN YACI GABA DA CEWA... ************ Ina zaku koma? to kusani cewa bala'in dake bayanku ya ninka na gaba sau dubu domin baku isa ku sake ratsawa ba ta cikin dajin buluzul mahaful da dajin zamutul makatul araye ya zama dole kuzo mushiga cikin wannan daji mu ketareshi don mu isa inda muke hari idan kuwa kuka ki zan yakeku da kaina na hallaka ku gaba daya kodajin wannan batu sai yauhana, karluz da boka guluz suka dawo da baya cikin sanyin jiki da karayar zuci bisa

Chapter 4 of 6