Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels DOCUMENT COMPILED BY SHURAIHU USMAN TYPING HABIBULLAH MUHAMMAD KABARA POSTED BY NAJIBULLAH MUHAMMAD **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU✍️✍️ PART A ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: Habibullah Muhd Kabara ✍️✍️ Tom mun dawo bakin aiki... Ina mana barka da JUMA'A fatan Allah ya maimaita mana❤️✍️🙏 Marubucin littafin ya ci gaba da cewa.... Lokacinda su jafar suka tsinci kansu a cikin wata sabuwar duniya a samaniya sai suka kidime suka cika da tsananin mamaki domin kuwa komai akan iska yake yawo hatta gidaje d dabbobin garin kuwa ba atsaye suke ba awaje guda su kuwa mutanen garin sun kasance masu wata irin halitta tamkar dodanni kuma jikinsu kwari gareshi kamar dutse kaurin jikinsu da tsayinsu duk iri dayane babu wanda yafi wani gaba daya jikinsu lullube yak da gashi kowannensu na da kaho guda biyu akansa sunada manyan kunnuwa kamar n jaki kuma idanuwansu da bakunansu irin na mutane ne sosai amma hannunsu 'yan kanana ne kamar dosana su akayi suna tafiya ne acikin iska kamar ana cilla kibiya duk da cewa basu da fukafukai su kuwa su jafar idan suka daga kafafunsu da nufin suyi tafiya sai suga ana juyasu acikin iska kamar katantanwa bisa dole suka tsaya waje guda suka cure su biyar din gaba daya mutanen garin babu wanda ya kalle su bare yace ci kanku, kuma duk wanda sukayi kokarin yiwa magana baya sauraronsu haka dai sukaci gaba da tsayuwa awaje daya her tsawon wani lokaci kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga gungun mayaka sanye da kayan karafa kimanin su dari sun taho garesu cikin matsiyacin gudu acikin iska wadannan mayaka suma irin mutanen garin ne kowannensu na dauke da wani irin lafcecen makami irin wanda su jafar basu taba ganiba da zuwan mayakan sai suka yiwa su jafar kawanya ya zamana babu 'yar kafa wadda zasu iyabi su wuce daya daga cikin mayakan ya fiddo wani abu acikin rigar karfensu mai kama da madubin karfe ya shafe shi saiga hoton fuskar sarkinsu ta bayyana akai sarkin ya kasance mai rafkeken kai wanda yafi na kowa girma agarin kuma shi kaho dayane akansa hakama idon sa da kunnensa duk dai dai ne wanda ke rike da madubin ya dubi sarki yace ya shugabana gamu nan tare da bakin me kakeso ayi musu? kodajin wannan tambayar say sarkin ya kyalkyale da dariya cikin wata Irin murya mai kama da karar karafa yace yauwa kuyi maza ku kawosu fadata hakika burin mu na daf da cika domin abin da muka dade muna nemane bamu samuba to yau sune sukazo suka kawo kansu yana gama fadin hakan ne dakarun suka cafke su jafar sukayi sama dasu suka cilla aguje cikin iska nanfa sukayi ta gifta garuruwa da birane da kauyuka iri iri har suka iso wata babbar alkarya wadda tun akofar birnin sukaga an rubuta BARKA DA ZUWA BIRNIN HARJULUL MULK birnin harjulul mulk ya banbanta da sauran biranen dake wannan duniya, domin gidajensa da komai nasa akan turba suke waje guda, ma'ana babu wani abu dake yawo asama cikin iska, koda aka shigar dasu cikin birnin sai suka ga an sauko kasa ancigaba da tafiya akasa bisa turba, abindaya basu mamaki shine gaba daya biranen birnin anyi sune da zallan karfen zinare kuma an kawatasu da kayan alatu fiye da tunanin kwakwalwa haka kuma mutanen garin da mutane masu irin halittar su jafar wato b dodanni bane dukkansu al'amarin daya jefa su jafar cikin matukar mamaki kenan koda ganin su jafar ahannun dakarun tsaro sai jama'ar suka kura musu idanu suna mamakin ganin su babu wanda yace dasu kala har akayi tafiyar kusan rabin sa'a sannan aka iso wani babban gida mai tsananin fadi da tsawo wanda idan mutum ya daga kansa bai isa ya hango rufinsa ba har yanzu dakarun suna rukunkume dasu jafar ko kyakkyawaan motsi basa iyayi da kofar gidan sarki sai wata kofà mai siffar kwai ta bude kanta ,kai tsaye dakarun suka shige dasu jafar ciki sannan kofar ta rufe kanta da shigarsu sai suka ga wasu ma'aikata azazzaune kan kujeru da tebura akan kowanne tebur wani farin allon tsafine gaba dayan ma'aikatan kowa na rike da wata siririyar sandar tsafi ajikin kowanne allon tsafi ana ganin abinda yake faruwa awata duniyar daban akalla za'a iya samun allon tsafi guda miliyan dubu daya awannan tamgamemiyar fada hakama adadin mutanen dake sarrafa madubin yake daga can karshen fadar kuwa bisa wani gini mai tudu sukayi arba da wani katon allon tsafi wanda yafi gaba daya sauran girma, zaune agaban allon sarki arbir ne zaune yakurawa su jafar idanu yana murmushi abindayà daurewa su jafar kai kenan cikin tsananin mamaki jafar ya dubesu alokacinda dakarun nan suka watsar dasu agabansa tamkar an watsar da tsummokara jafar yace yakai sarki azbir ya akai kazo nan alhalin mun rabu dakai tun acan duniyarka abakin rijiyar nan data zukemu sarki azbir ya mike tsaye yazo gabansu jafar wadanda ke zaune dirshan akasa ya tattashesu tsaye sannan ya rike hannun jafar yace ka kwantar da hankalinka yaka jafar ku sani cewa yau kun fado hannun sarki azmul gallar mai mulkin birnin harjulul mulk birnin da shine mafi girma da daukaka acikin wannan nahiya ta duniyoyin sama inason ka sani cewa sarki azmul gallar ya tsani sauran duniyoyin dake can kasa wato kamar irin duniyarku kuma bashi da wani buri wanda yafi ya shafesu gaba daya daga doron kasa yayi binik ya gano cewa idan yana son ya hallakar da duniyoyin dake doron kasa dolene ya kera wani sundukin tsafi mai tsananin haske ya aikashi izuwa can duniyoyin kasa hasken wannan sundukine zai narkar da wannan duniyoyin gaba daya yanzu haka angama kera wannan sunduki amma an kasa aikashi saboda so ake asamu mutane irinku acikin wannan sundukin guda uku ko sama da haka sannan sundukin zai iya tafiya haka kuma sundukin babu wanda zai iya sarrafa sundukin face ni kadài shiyasa sarki azmul gallar ya kamoni ya kawoni nan kuyi duba izuwa can kuga abin mamaki cikin sauri jafar, jelisa, gulzum, da mazalish suka juya suka dubi inda sarki azbir yayi musu nuni kawai sai. sukayi arba da ita ba kowa bace face katuwar macijiyar nan mai kawuna barkatai wadda ta had! yesu cikin tsananin tsoro suka ja da baya gaba dayansu adaidai wannan lokacin ne macijiyar ta sauko da kanta guda daya kasa ta wangame shi kamar zata hadiye komai dake wajen bisa mamaki sai suka ga sarki azmul gallar ya fito ta cikin bakin macijiyar yana kyalkyla dariyar mugunta yana fita daga bakin macijiyar ya dafa kanta yace jeki abinki uwar macizai na sallame ki kamar walkiya macijiyar ta bace bat sarki azmul gallar ya dubi su jafar daya bayan daya ya jinjina kai sannan ya sake bushewa da dariya wacce tayi dai dai da irin ta mutane ba dodanni ba kamarsa azmul gallar ya dubi su jafar yace gaisheka takadirin yaro kaine wanda ya zamewa boka shamharu alakakai kuma kaine mai shirin zama alakakai agareni amma bazan baka damar yin hakanba ka sani cewa ahalin yanzu ka bankado sirrin boka shamharu domin kaine sanadin bude KUNDUN TSATSUBA tabbas gaba daya sirrikan tsafin boka shamharu na nan cikin littafin KUNDUN TSATSUBA na farko nikuma nawa suna nan acikin sabon KUNDUN TSATSUBA na biyu wanda yanzu haka mahaifinka ruziyal yana kam aikin ruvutashi acan duniyarku tareda aljni rafkamagu da boka hajarul makarus wadanda ke taimaka masa wajen ziyaràr sarakunan duniya suna basu labaran abubuwan al'ajabi ya zama dole agareni na tsaida wannan aiki nasu ta hanyar ta hanyar kulle sabon KUNDUN TSATSUBA da kubar MUFTAHUL ZARBIL yanzu haka kubar MIFTAHUL ZARBIL na nan ajikin kundun na farko wanda kuka fara karantawa kubar ba zata zaruba daga jikinsaba ta kowanne hali harsai kun gama karanta littafin gama karanta littafin kuwa zaikai tsawon shekara goma sha tara da "yan watanni kuma lokacin zaizo daidai da lokacinda za'a gama karanta sabon KUNDUN TSATSUBA zai zo dai da lokacin da za'a hattama rubuta kundi na b!yu idan na bari aka kai wannan lokacin za'a san sirrina ya zama wajibi agareni na kera sabuwar kubar MIFTAHUL ZARBIL wannan kubar kuwa bazata keruba face na narkar da duniyarku gaba daya da narkakkiyar kasar duniyar kune zan iya kera kubar MIFTAHUL ZARBIL yanzu sai ku shirya don zan sauya muku halitta ne yadda zan iya c!ka burina koda sarki azmul gallar yazo nan azancensa sai hankalinsu jafar ya dugunzuma yeli$a,mashrila, da sarki azbir suka kama kuka saboda sunji ance za"a sauya musu halitta kuma koba komai sunsan ba karamar wahala zasu sha ba akan wannan aiki wata kilama su iya rasa rayuwarsu jafar, mazalish, da gulzum kuwa kokadan basu razanaba dajin wannan batu na sarki azmul gallar cikin rashin tsoro da gadara jafar ya dubi sarki azmul gallar yace yakai wannan sarki inason ka wayar mini dakai akan matsayin boka shamharu awajenka domin na fuskanci cewar kusan burinku daya shin yanason ya mallaki komai da kowane dake duniyar kasa, kai kuma kanaso ka hallaka komai da kowane dake duniyar kasa, kodajin haka sai azmul gallar ya bushe da dariya yace yaro baka fahimta sosaiba ai tsakanina da shamharu babu komai face matsananciyar gaba kamar yadda na fada muku cewar bazan iya kera kubar MIFTAHUL ZARBIL ba saina narkar da duniyarku haka shima shamharu bazai iya tsaidaku daga karatun KUNDUN TSATSUBA na farko ba harsai ya narkar da wannan duniyar tamu kusan kuwa abune da bazai taba yiwuwaba agareshi. Mu hadu a part B don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️ **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU ✍️✍️ PART B ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️ TYPING: Habibullah Muhd Kabara ✍️✍️ MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.. Kafin wani daga cikin su jafar ya kara cewa komai sai sarki azmul gallar ya dubi dakarun nan da suka zo dasu jafar take suka kama su suka hada da sarki azbir suka nufi wni bangare daban dasu sai da akayi wata 'yar doguwar tafiya dasu sannan aka shigo wani katon daki babu komai acikin dakin face tarin wasu manya manyan tukwane na gilashi acikin tukwanen ruwan zafine launi launi yanata zabal bala wani ruwan sai kaga ja ne, wani kuma shudi, wani kore kai atakaice dai babu irin kalar d babu ba tareda bata wani lokaciba dakarun nan suka daure su jafar d wata sarkar tsafi wadda da zarar su jafar sunyi yunkurin kubuta zasuji kamar ana tsotsar jinin jikinsu bisa dole suka rungumi kaddara ,wani abin mamaki shine aljani gulzum yafi wadannan dakarun girma da kwarjini amma sarrafa shi suke kamar dan mitsitsin yaro da babba koda su jafar suka ga anyi musu mummunan dauri haka sai hankalinsu ya dugunzuma suka rasa abinda yake musu dadi tsoro ya baibaye zuciyar su ta fara bugawa da sauri nantake dakarun nan suka kama sarki azbir da karfin tsiya suka nufi wata kwalba mai dauke da shudin ruwan zafi nan take sarki azbir ya kama ihu da koke koke yana rokon su kyaleshi al'amarin daya kara dugunzuma hankalinsu jafar kenan don basu san dalilin dayasa sarki azbir ya firgice haka ba her yake kukaba adaidai wannan lokaci ne sarki azmul gallar ya shigo cikin dakin yana kyalkyla dariyar farinciki kawai sai ya dakawa dakarun nasa tsawa yace me kuke jirane dashi? maza ku jefasho cikin kwalbar mana kafin azmul gallar ya gama rufe bakinsa tuni daya daga cikin dakarun yasa hannu biyu ya bude murfin kwalbar mai kma da katon faranti aikuwa yana budewa aka jefa sarki azbir a ciki aka rufe ,tamkar an sanya alli acikin ruwa haka jikin sarki azbir ya dinga zagwanyewa tun yana ihu ana jin muryarsa har muryar ta dishe ahankali gaba daya jikin nasa ya narke ya cakude da ruwan cikin tukunyar ya dinga hautsinewa yana bori kamar kwalbar zata fashe jim kadan kuma sai aka g ainihin siffar sarki azbir ta dawo kuma ya dinga rikida ya zama abubuwa iri iri kamar kyanwa, maciji, kunama, da sauransu saidaya zama abu dari da daya acikin darin ne ya zama wani irin mummunan gwaggon biri ya zana zama hakan sai kwalbar ta fashe da kanta gwaggon biri ya tako da kafafunsa yaje gaban sarki azmul gallar yana mai sujjada alamun yin biyayya, cikin tsananin farinciki azmul gallar ya bishe da dariyar mugunta duk wannan abu dake faruwa au jafar n gani kuma tuni sun fara kuka da bakin ciki jafar ya dubi gulzum yace amma dai kaji kunya tunda karfinka da girmanka ya zama na banza bazaka iya ceton mu ba gulzum yayi tsaki yace amma dai kai banzane waya gaya maka cewa karfi da girma zaiyi tasiri anan? ina tabbatar maka da cewa ko boka shamharu ne ya kuskura y fado nan ya zama nama sai yadda akayi dashi bare ni daban zama komai a ilimin tsafiba ita kuwa yeli$a saita dubi mazalish tace yake ma'abociyar hikima, ina rokonki daki hanzarta tunanin kubutar damu inba haka b yanzun nan za'a mai damu irin ahinda aka maida sarki azbir kodajin wannan batu sai hawaye ya zubowa mazalish tace yake kawata kiyi sani cewa. hikima ko karfi ko sihiri ba zasuyi aiki anan ba domin sunzo gidan kakanninsu inda kunsan ma abindana sani da kun gwammace mutuwa gaba daya yanzu take ina bakin cikin sanar daku cewa idan har sarki azmul gallar ya mai damu burarrika to har abada babu wanda zai iya dawo damu ainihin siffar mu face shi kadai ku sani cewa idan aka samu acikin sundukin haske aka tura mu duniyar mu to mun tafi kenan ba zamu sake dawowaba bare ya dawo damu ainihin siffofin mu ku sani cewa alokacinda sundukin hasken zai narkar da duniyarmu to tareda mu zata narke kunga shikenan tamu ta kare mazalish na gama fadin hakan kenan sarki azmul gallar ya tsaya da dariyarsa sannan ya dubi su jafar yace to idan akwai wanda yakeda wasiyya ga danginsa ko 'yan uwansa saiya fada kafin n jefaku acikin kwalbar tsafi tabbas zan taimaka nakai wasiyyar mazalish ta share hawayenta tace inada wasiyya amma ga masoyina JARUMI HUBAIRU abokin gaba LU'UMANU inason ka bashi labarina ka fada masa cewa na baro kasata saboda shi, na kashe mahaifina saboda shi kuma na rabu da mahaiyata sabodashi don kawai y zama abokin rayuwata wannan shinè kadai burina lallai banaso na. mutu ba tareda hubairu yasanni ba a duniya kodajin wannan batu sai sarki azmul gallar yayi yace ai wannan mai saukine nayi alkawarin zan idar da wannan wasiyya, waye kuma zai sake bayarda wata wasiyyar daga cikinku? azmul gallar ya tamb@ya jafar ya dubeshi yatsine cikin raini yanzu kai nan nufinka shine zakayi amfani damu wajen biyan bukatrka mu kuma mu hallaka? to kasani cewa buktarka bazata biyqba kuma zamu dawo nan mu yakeka mu tarwatsa dukkanin irinka kodajin wannan batu sai sarki azmul gallar ya tuntsure da dariya ya karewa jafar kallo sama da kasa sannan yace yakai jafar kai kuwa mene takamarka? ka sani cewa nafiku karfi, sihiri da komai tayaya zaku iya yakata harku sami nasara akaina? jafar yace bana takama da komai face sa'a ka sani cewa babu wanda yayi tsammani cewa zamu iya dauko kundun tsatsuba bare har mu iya samo kubar miftahul zarbil mu budeshi gashi yanzu harmunyi nisa acikin karatunsa muna kan shafi na ashirin da daya bana mamakin cewa zamu iya kubuta daga hannunka harmuje wata duniyar inda zamu hadu da wani takadirin wanda yafika shaidanci azmul gallar yayi murmushi yace ai yaro kayi kuskure babu wani mahaluki kmata tsakanin duniyarku ta kasa da sauran duniyoyin dake nan sama da wannan kalami nake muku sallamar karshe ina maiyi muku fatan riskar ajalinku @saukake cikin "yan dakiku kadan yana gama fadin hakan ne dakarun nan suka kama jafar, yeli$a, gulzum, da mazalish suka tsomasu acikin kwalaben nan masu ruwan zafi nan take jikinsu y fara narkewa tun sunayin ihu har suka kasa ahaka dai har siffofin su suka juye izuwa na burarrrika kamar yadda aka maida sarki azbir koda aka fito dasu daga cikin kwalaben wato bayan kwalaben sun farfashe da kansu sai suka jeru su hudun suka zube gaban sarki azmul gallar suna masuyi sujjada agareshi cikin tsananin farinciki azmul gallar ya kece da dariya sannan ya dubi dakarunsa yace ku tafi dasu izuwa dakin sundukin 'aske cikìn biyayya dakarun suka iza keyar burarrikan shida sukai gaba saida sukayi tafiyar rabin sa'a cif sannan suka iso wani tangamemen daki babu komai acikin dakin face wani mulmulallen karfe mara nauyi asamansa ankifa wani zagayayyen gilashi mai siffar kwai wanda ta cikinsa na iya hango wasu kujeru guda shida dake cikin sa kujera ta farko nadaga gaba sauran kujerun kuwa guda biyar suna bayanta ajere reras agaban kujera ta farko kuwa wadansu yan kananan ramukane guda huda ja, fari da ruwan dorawa kowanne rami arufe yake da gilashi amma akwai siririn tsinken tsafi ajikinsa da shigowa cikin wannan daki saisu jafar sukayì arba da wannan gabjejen sunduki na farin karfen gurar ruwa nanfa suka wangame baki suna kallon surar dukda sun kasance acikin siffar burrai kasan cewa mamaki sukeyi batareda bata lokaciba sarki azmulgallar ya nuna su jafar da danyatsa kawai sai suka bace bat basu bayyanaba sai acikin sundukin karfen sarki azbir ne agaba, jafar yelisa ,gulzum, mazalisha na daga kujerun baya koda suka tsinci kansu cikin wannan sunduki sai suka mimmike tsaye sunata dukan gilashin daya rufesu don su sami damar fita amma abanza kamar suna dukan dutse koda sarki azmul gallar ya ga haka sai ya sake nunasu da hannunsa na hagu t@ke suka koma suka zauna, zamansu keda wuya sai sarki azbir ya taba daya daga cikin tsinkayen tsafin dake gabansa yin hakan keda wuya sai wani irin haske mai tsanani ya baibaye sundukin tareda wata irin iska cikin gaggawa azmul gallar da dakarunsa suka ruga waje suka rufe kofar dake dakin bayan kamar dakika goma sai dakin ya kama girgiza nantake sundukin ya tunbuke kansa daga jikin wasu turakan karfe da aka daurèshi ajiki yayi fitar burgu tacikin wata tangamemiyar fada koda sundukin ya baiyana asararin samaniya saiya juya ya kalli kasa ya fara azabbabben gudu dauke da burarrrika shida acikinsa sai dai wannan gudu da sundukin yake yafi gaban kwatance domin zai iyq cin zango miliyan dubu acikin dakika biyar WANNAN SHINE ABIN DAYA FARU GASU JAFAR BAYAN SUN FADA CIKIN SHAFI NA ASHIRIN DA DAYA ACIKIN KUNDUN TSATSUBA Al'amarin gimbiya sima kuwa lokacin data ruke mashì ta nufi jarumi hubairu gadan gadan da niyar sokeshi kawai sai akaga sararin samaniya ta cika da wsu fararen abubuwa masu kama da balbelu cikin sauri sarki lu'umanu ya daga kansa sama ya fara nazarin abubuwan don yaga ko menene itama gimbiya sima saita tsaya kyam tana kallon sama. MU HADU A PART C DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏 **MATSATSUBI**💥💥 LITTAFI NA UKU✍️✍️ PART C ❤️❤️ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️ TYPING: Habibullah Muhd Kabara ✍️✍️ #LEGENDs. Marubucin littafin ya ci gaba da cewa.... KODA abubuwan sukayo kasa kasa sai akaga ashe sarki hudes ne mahaifin aljani abtarul hudes tareda sauran dakarun musulmi dukkansu sunyi shigar fararen tufafi rike da makaman yaki kuma suna ta firfita tutar musulunci mai dauke da kalmar shahada koda ganin haka sai gaba daya dakarun sarki lu'umanu suka firgice saboda kwarjinin dakarun muslunci cikin dacin rai sarki lu'umanu ya zare takobinsa ya yi tsalle sama ya dira kan daddumarsa ta tsafi sannan ya dubi dakarunsa ya daka musu tsawa yace me kuke jirane ga makiyan mu maza ku taresu kafin su sauko kasa da ike akwai sauran dakarun nan na shamharu tareda lu'umanu sai suka bude fukafukansu sukayi sama wato suka tari sarki hudes aka fara rubdugu asararin samaniya shikuwa sarkin lu'umanu sai yayi amfani da wannan dama ya nufi inda jarumi hubairu ke daure da niyyar sare masa kai koda ya iso kansa ya daga takobinsa ya kai masa sara awuya da nufin ya tsinkeasa kai kawai sai yaga an kare saran da wata zabgegiyar takobi mai ban al'ajabi da matukar girma wadda ta haddasa tartsatsin wuta da kara mai firgitarwa koda ya dubi wanda ya rike takobin saiyaga ashe sarki hudes da kansa ya kawowa hubairu dauki duk d jarumtaka da sadaukantaka irin ta lu'umanu sai daya firgita ya dan ja da baya ya tsaya yana shawarar ya gudu ko ya tsaya sarki hudes ya dakawa lu'umanu tsawa yace yakai tsohon makiyin allah ai na gane cewa ba kaine ainihin lu'umanu ba tabbas aljani zarmukune ya shiga jikin gangar jikin lu'umanu ina umartarka daka hanzarta fita daya jikinsa yanzu yanzu nan ko kuma n gama dakai yanzùn nan kuma daga yau idan na kara haduwa dakai ako ina saina kasheka in baka tuba ba a daina taimakon mushrikai koda fadin haka sai lu'umanu ya kece da wata irin mahaukaciyar dariya wacce ta kasance bata ainihin muryarsa bace lokaci guda kuma aljani zarmuku ya fita daga jikin lu'umanu take gangar jikin t fado kasa bisa daddumar tsafi sannan aljani zarmuku ya dubi sarki hudes ya dubi sarki hudes ya nunashi da yatsa yace yakai tsohon abokin gaba kayi sani cewa tsakanina dakai tsohuwar gabace akalla nayi yaki dakai akalla sau dari uku d arba'in da hudu idan muka sake gwabzawa yanzu shine cikon na dari hudu da arba'in da biyar tsakanina dakai ba gudu ba ja da baya kuma bakin rai bakin fama kayi sani cewa irina guda dubu ne masu shiga sarki lu'umanu ayanzu haka jarumi hubairu ya kashe daya daga cikin mu saura dari tara da casa'in da tara, don haka koda ka kasheni kayj abanza akwai sauran yan uwana suna nan cikin fushi sarki hudes ya sake dakawa aljani zarmuku tsawa a karo na biyu yace kai la'anannen allah kayi sani cewa koda kunkai miliyan dubu bazan gaji da yin fada dakuba har saina karar daku dani daku mu zuba mu gani dan halak ka fa$a kafin zarmuku ya kara cewa wani abu tuni sarki hudes ya zare takobi ya kai masa wawan sara akafada cikin zafin nama aljani zarmuku ya goce sannan ya rikida ya zama haske ya shiga jikin sarki lu'umanu kamar an tabe baka haka lu'umanu ya mike tsaye zumbur ya zare takobinsa suka fara artabu, dama tundazu an dade ana gwagwarmaya acan sararin samaniya koda aka fara wannan gumurzu tsakanin hudes da zarmuku sai waje ya sake rikicewa gab daya ya zamana band@ ihun maz@je da karafkiyar karafa babu abinda kunne keji aljani zarmuku cikakken kafirine wanda ya tsani musulunci da musulmi ya dade akan wannan akida tasa, kuma ya jima yan@ hada rundunar bakaken aljanu don su murkushe musulman aljanu na duniya baki daya amma burinsa bai cikaba ya sha haduwa da sarki hudes amma idan gamo yayi gamo yaga zai hallaka saiya tsere wannan guduwar da yake yi zuciyar sarki hudes ba karamin sosuwa takeyiba don haka wannan karon shima yaci alwashin wannan karon bazai sake sakewaba yabarshi ya gudu lokacinda aka sami sa'a bakwai ana wannan dauki ba dadi sannan dakarun sarki hudes suka samì nasarar gamawa da dakarun lu'umanu ya zamana sun kashesu gaba daya don haka ya rage saura sarki hudes da zarmuku kawai ats@kiyar sararin samaniya suna gumurzu tuni awannan lokaci gimbiya sima ta fadi kasa sumammiya sakamakon bala'in gumurzun da akeyi da tartsatsin wuta ihun mazaje da karar makamai suma mutanen garin gaba daya sun fashe wasu sun sume wasu $un haukacebisa ganin aljanu kiriri anacikin fafayawar ne sarki hudes ya sami nasarar yiwa zarmuku wani mummunan sara ahannun sa n dama take hannun ya gutsire ya fadi kasa zarmuku ya kwalla ihu cikin tsananin jin zugi nantake ya rikide ya zama wuta, wutar tayi feshi ga hudes ga hudes da niyyar ta konashi cikin ikon allah sarki hudes ya yi kabbara koda wutar ta sauka ajikinsa saita zama ruwan sanyi nanfa zurmuku yaci gaba dayin tsafi yana zama mugayen abubuwa don ya lahanta sarki hudes amma saiabu ya gagara koda sarki hudes yaga zarmuku zai bat masa lokaci saiya shiga karanta wadansu manyan addu'o'i masu dauke da ismul a'azam aikuwa sai nanda nan sihirin tsafin zarmuku ya karye ya kasa yin komai babu yadda baiyiba don ya bace amma ya kasa cikin zafin nama sarki hudes ya sakè daga rantsatstsen takobinsa ya kaiwa zarmuku sara da nufin ya tsargeshi gida biyu kawai saiyaga anyi sama da zarmuku kamar an janyeshi da kugiya cikin sauri sarki hudes ya daga kansa sama don yaga wanene sai sukaga bakan gizone ya bayyana kuma shine ya dauke zurmuku cikin abinda bai wuce dakika dayaba bakan gizon ya sake sure gangar jikin lu'umanu wacce ke sharbe akan dardumar tsafi, ya sake kaiwa jikin sima sura da nufin ya dauketa sai sarki hudes ya lullube ta da fukafukansa yana mai cigaba da karanta addu'o'insa kawai sai yaji wani irin ihu da karaji dga bakan gizon lokaci guda bakan gizon ya bace tareda zarmuku da gangar jikin lu'umanu koda ganin faruwar hakan sai dakarun sarki hudes suka kama kabbara cikin farincikin samun nasarar wannan yaki waziri kuddaru kuwa saboda farinciki saida kwalla ta zubo masa adaidai wannan lokacin gimbiya sima da jarumi hubairu suka farfado koda gimbiya sima ta kyalla ido taga mashinta saita ruga ta dauka ta nufi inda jarumi hubairu yake da niyyar ta tsireshi cikin zafin nama sarki hudes ya sha gabanta ya kama mashìn ya ruburbusheshi tamkar nukakken kashi sannan ya shafeta da gefen dan yatsansa take ta sake faduwa kasa sumammiya wannan abu daya faru ba karamin mamaki ya baiwa jarumi hubairu ba yana mai cewa aransa yanzu sima ce ke kokarin hallakani? adaidai

Chapter 1 of 6