da ya jin-jina al’amarin yace”tun da Baba
liman nanan zan sa a tura 1million sai akai sadaki,
2millions kuma a had’a kaya akai. Ina dawowa sai aure
kawai. Mumcikin farin ciki tace”Allah ya ja kwanan mai
girma governor, godiya muke Allah ya tsare mana kai, Ya
amsa da ameen. Malam ko da ya dawo ransa ya baci,
amma yace”duk hakan baza’a fasa auren nan ba sai anyi,
duk mai hassada sai dai yayi ya gama. Dr Umar ko kulum
sai yayi sawu 3 a gidan kula ta musamman ke ba Khadi.
Yau da yazo bayan sun gaisa da malam ya saida masa
“iyayensa zasu zo, za’a kawo sadaki. Malam
yace”Alhamdulilah! Allah ya kawosu lafiya mungode.
Washe gari Baba liman yazo ya kawo sadaki, Malam sai
da ya razana, kin karban kud’in yayi yace”gaskiya Malam
sunyi yawa a rage. Baba liman yace”sam bazan koma da
ko si-si ba, mudai fatan mu Allah ya sanya alkairi. Baban
Khadi ganin Malam ya girmesa, kuma bazai iya masa
musu ba ya sa hannu ya karb’a. Yana shiga gida don ya
ba ma Gwaggo haushi yace”Hauwa kawo min taburma
nan kizo kiga ikon Allah. Da sauri Gwaggo ta fito har tana
tun-tub’e, ta shin fid’a masa tabarma bayan ya zauna sai
taga ya zaro da min kud’i har bunch biyar, ido Gwaggo ta
zaro, “Malam ina kasamu wanna kud’i?. Murmushi yayi
yace”Hauwa wato zakaran da Allah yanufa da cara ko
ana muzuru ana shaho sai yayi. “Kuma d’an hakin da
karaina wataran sai ya baka mamaki. Gwaggo tace”ni dik
ban gane hausanka ba Malam?. Malam yace”hmm
Sadakin Khadi aka kawo har naira na gugan naira million
d’aya. Wayyo nashiga uku sadaki ina Malam d’an yankan
kai ne ba fa zaiyuba. Nima sai ka samo ma Bedba miji,
Gwaggo ta sha kwalan Malam, ihu take tana kuka, tana
fad’in ya cuceta. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016]
Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-106~110. Gwaggo ta sha
kwalan malam sai ihu takeyi, ya sa hannu ya ban-bare
rigansa, yazo zai wuce ta sake shan gabansa, “yaufa
bazaka fita agidan nan ba, yau saika kawo ma Beeba miji.
Ya matsa tabisa yazo zai shiga d’aki ta tare qofar, sai ya
tureta yazo fita ya iso zaure, tazo da gudu ta kama
rigansa saida ta yaga. Ran Malam in yayi dubu ya b’aci
bai san lokacin da ya kikifa mata mari ba, ya hankad’ata
ta fad’i akasa. Yace”Hauwa hassadakin bazaikai ki ko ina
ba, wannan aure matsawan in ima raye ba fashi, sai dai
ki mutu da bakin ciki. Ya juya ya nufi d’aki ya canza kaya,
yazo ya wuceta, har ya fita ya dawo yace”kuma wallahi in
kika kuskura kika tab’a Khadija, a bakin aurenki saki zan
miki ba dawowa, kina dukanta kin san sauran, Yasa kai
ya fita. Gwaggo abun duniya ya isheta, tabbas Malam tun
da ya rantse sai ya aikata, jiki ba kwari ta koma d’aki
tafara kuka, cikin zuciyarta ko cewa take”wanna mari ba
zai sha banza ba tunda yace karna daketa, to ae dole tayi
aikin gida, dan haka ba duka akwai zagi da wahala
yankuma. Khadi tana d’aki kwace, tana group chatt da
kwayenta, wanda suka had’u a WhatsApp ta lura suna da
hankali, shiyasa nasu yazi d’aya. A group d’in Khaleesat
Haiydar suka had’u na Facebook dake Khadi mayar
karatun novel ne. Hiran Novel d’in KAINE SIRRI NA
littafin Aisha Muh’od, Queen Neenah tace” Khadeejat kin
karanta KAINE SIRRI NA? khadi tace”eh ina karantawa
kai, gaskiya novel d’in ya had’u. Farhat B Haske tace”
Queen Neenah n Khadeejat kun karanta MARTABA TA da
MATAR MUTUM na Mrs Umar Soja kuwa?. Sukace “a’a
bamu karanta ba. “Lalle an barku a baya ni harna gama
karantawa, yanzu ina karanta YAR WAYE NE?.na Khairat S
Panisau, da KUDAN ZUMA na Zee Hrt. Suka had’a baki
tare da cewa”Farhat littafin ya had’u ne?. “Eh kai ana
rikici kam, ku tamabi. Hajiya Jamila Aliyu Haiydar tana
dashi sai ta tura muku. Queen tace”Khady bari na
nemomana zan tura miki ina samu. Khady tace”ok
amma fa nagode. Farhat B Haske tace”gaskiya ya kamata
yanda muka saba musan juna, gashi mun shaku sosai, ae
zumuncin bai kamata ya tsaya a chatt ba. Queen Neena
tace” ae fa gaskiya kam, yanzu musa rana sai mu fara
zuwa gidansu Khady. “Ko ya kuka gani yan’uwa?. Duka
suka turo da haka za’ayi. Khadi taji dad’i amma tana
tunanin yanda zasu zo Gwaggo zata iya cin musu
mutunci. Salama sukayi akan ran Friday za’a had’u, a
gidan Hajiya Jamila Aliyu Haiydar sai su taho. Gwaggo
tana gama sake-sakenata tafito ta kwala ma Khady kira,
“fito dan ubanki, mai fiska kaman na biri, kin lashe wa
mijina zuciya kin rabani da yata, gashi kin samu d’an
mutane, kinsa yayi sata sun kawo kud’in aure ko?. “To ni
kam dai ahir d’inki. “Kurwata kur bazaki iya ci ba. “Ko
uwarki ma haka tagaji ta barni don nafi k’arfinku. Nan
take idon Khadi yaciko da kwalla. Gwaggo ta tattaro
wanke-wanke ta tara mata, tashiga d’aki ta d’ebo kaya
harda wankaku, duk ta had’a mata. “Maza-maza kiyi ki
gama su yanzu, ki kuma tabbatar an girkan abicin kar
yayi dare. “Kin san halina basai an fad’a maki ba aha. “Ni
ce Gwaggo Munguwa No1, in kika kuskure min a aiki sai
na miki ba dad’i, tsohuwar mayya kawai. “Mai son raba
aure, amma kuma bazaki iya ba sai dai a fasa naki.
“Kuma ina kan bincike duk randa na gano gidan
saurayinki, sai naje na had’a duk wata manakisa ta, an
fasa auren. Niko Rash”nace Gwaggo rashin sani yafi dare
duhu, da kimsan Umar d’an waye da baki fara masa
rashin mutunci ba, don yafi k’arfin raini. Khadi ta
dunkufa aiki baji ba gani, duk da ta gaji amma bata son
ta nuna bare Gwaggo ta zagi iyayenta, don yafi komai cin
mata rai. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-111~115 Aiki sosai tayi,
Gwaggo tana fita makwabta, Beeba ta fito tafara tayata
aiki, Khadi tace”Beeba da kin bari nayi, yanzu in Gwaggo
tazo ta samemu, ni zata zaga uwa ta uba. Beeba
tace”karki damu Adda yanzu zamu gama aikin, Rabee’a
ta fito sai mika takeyi, alamar daga bacci ta tashi, kitchen
ta wuce ta duna tukunya, taga an kusa gama abinci,
kwano ta d’auko ta d’iba. Beeba tace”Rabee wani irin
iskanci kikeyi ne, kina kalo muna aiki amma kizo ki d’ibi
abinci?. Baki ta murgud’amusu, Khadi tace”kyaketa
Beeba, kinsan Gwaggo na dawowa saita huce a kaina.
Aiki sukayi cikin ikon Allah dake, duna da zafin nama
basu dad’e ba suka gama. Khadi ta raba musu abin ci
suka ci, Gwaggi na dawoa tayi mamakin yanda Khadi ta
gama aiki da wuri, d’aki tashiga kwano ta fito da shi, ta
turo ma Khadi ga wannan masaran kina gama cin abimci
ki surfa min shi, don yau surfen hannu nake so bana inji
ba. Cikin girmamawa tace”to Gwaggo”. A gajiye tayi surfe
ta gama ta wanke ta shanya shi. Yau takama jumma’a
yau ne su Hajiya jamila da Queen Neenah zasu zo, yan
kud’in da ke Hannuta ta had’a ta siyo kaya ita da Beeba
sukayi girki. Ware dubu biyu zata basu kud’in Napep, ta
gyara ko ina sukayi wanka ita da Beebah, sunyi kyau
sosai. Gwaggo na ganin Khadi ta fito tace”mayya inda
kinga fiskanki da bazaki na yawo cikin mutane ba. Rabee
ta mata kalon sama da kasa, sa’a d’aya Gwaggo bata sasu
aiki ba. Sai kusan karfe biyar, su Farhat suka kira waya,
Khadi ta d’auka da “sallamanta kun isone?. Farhat
tace”eh! Gamu a dai-dai gun fire servise”. “Ok gani zuwa”.
Ita da Beeba suka fita, suna zuwa kuwata gansu, da
murna suka tari juna, farhat tace”ikon Allah yau Allah
yayi zamu gana. “Eh wallahi sannu ku da zuwa. Su hajiya
Jamila tace”wanna itace Beeba ko?. Khadi ta amsa da”eh!
Itace, har kin ganeta. Suna hira suka shigo da sallama.
Gwaggo ta musu kalon sama da kasa, Khadi ko sai addu’a
takeyi, d’akin suka kai su. “Gwaggo ta kwala ma Khadi
kira” ta amsa da “na’am gani zuwa”. “Kee dan uwarki ina
kika samu wayan nan?. Ko maitan ki ya dawo har gida
kike lashe mutane?. “Kiyi hak’uri Gwaggo kawaye nane
fa”. “Eyeh har wani daman kawaye kika samu”. “To yau
zaku ci ubanku daga ke har kawaye”. “Dan Allah Gwaggo
kiyi hak’uri ki bari in sun tafi kimin duk abunda kikeso”.
“Kee ko uwarki bazata ban doka nabiba, bare kee yar
karamar kwaro”. “Assalamu’alaikum Malam yayi
sallama”. “Khadi ta amsa” Yana daga qofar d’akinsa
yace”Khadejatu! ” Ta amsa da “na’am Baba”. “Maza kizo
nan” Gwaggo cikin takaici ta ja tsuka. Sam bata so haka
ba, taso saita wulakanta Khadi Malam ya dawo. Da sauri
Khadi ta nufi gun Malam, da sallama tashiga d’akin,
tsugunawa tayi tace”sannu da dawowa Baba” Cikin fara’a
ya amsa da”yauwa d’iyata, naji dad’in ganin ki, a cikin
wannan yanayi” “Ya jinin yau fatan lafiya ko?. “Eh! Lafiya
lau, ga kwayena ma sun zi gaida mu yau”. “Ah madalla
mun gode, in zasu tafi ki fad’amin”. “To baba” Da Murna
tayi d’akin ta nan tayi sannu nasu Hajiya Jamila, Beeba ko
har tayi serving d’insu. “Tace muje ku gaida Baba na”
dukansu suka mike har qofar d’akin Malam sukaje suka
gaida shi, ya sanya musu Albarka. Gwaggo ma tafito daga
d’aki duka k’ara gaidata. A dakile ta amsa, suka koma
d’akin Khadi, hira sosai sikayi, kafin suka mike zasu tafi
don magriba yayi. Ta d’ibi kayan kwaliya, da sabulai,
acikin wanda Dr Umar ya kawo mata, da turaruka
tasamusu a laida. Sun fito Malam ya kirata yace”ga
wanna kibasu su hau adai-daita. Ta karba ta “sukuma
sukayi godiya”. Har bakin titi suka rako su ta mika musu
tare da musu alkawarin zata zo ita da Beeba. Bayan
kwana biyu Khadi na zaman hak’uri, kulum da kalan
horon, da Gwaggo ke mata. Ana haka kwanwar Gwaggo
da yaranta suka zo mata kwana biyu, kulum cikin kunci
da matsi take, itaji sanyi to tana tare da Malam ko Beeba
ko Dr Umar. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-121~125. Gwaggo ta buga
k’irji tace”nashiga uku, anya kuwa ba Khadi mu bane.
Matar tace”nan gidan mana”. Innna Yalwa tace”sannuku
da zuwa ga gurin zama”. Cike da fara’a suka k’ara
shigowa. Nan fa aka shigo da akwatuna, ko da aka shin
fud’a taburma, hmm akwatuna bazai yiwu a bazasu, a
tsakar gidan ba. Inna Yalwa tace”yan’uwa yana da kyau,
kafin mu fara bud’e kaya, muyi addu’a Allah ya sanya
alkairi, ya kad’e fitin-tinun dake ciki, ya kuma kawar da
idon mahassada da makiya, dazasu kawo farmaki ma
auren nan. Gwaggo tace”kee Yalwa wa zaiyi hassda ko
makiyi nasan dani kikeyi, nan Gwaggo ta fara kwala, ko
ta kanta basu bi ba, sukayi addu’a aka fara bud’e kaya.
Yasalam masu karatu karkuso kuga kayan yawanci ready
made ne, ga tsada, ko da ka zo kan takalma duk gulma
na, na kasa k’irga yawansu, jakukuna da poss ba’a
magana. Ko da aka bud’e na d’ankunaye hmm gwala-
gwalai da fashion masu tsada, ga manyan balguls ba a
cewa komai, can idona ya kyalo wani karamar a kwati
acikin kayan, da sauri Inna yalwa ta d’auko, tayi-tayi ta
bud’e amma ta kasa, wannan matar ne tace”kawo ki
gani, tana tab’a qofar akwatin yafara k’ara sauti mai dad’i
gashi da k’arfi. Tana bud’ewa yace Hello My Master, cikin
wata tausasashiyar murya na mata, kai ka d’auka a fili
mutum yayi wannan maganan ba. Wata mata da ke gefe,
tace” a kula da wannan a kwatin, don White Gold ne a
ciki, yana da matukar tsada sosai, kud’insa ya kai miliyan
uku a kud’in 9ja. Inna Yalwa baki har kuni godia suka
fara musu, sai suka d’auko d’an kayan da suka had’a
musu suka mik’a. Inna Yalwa da dubu biyar a jikinta, ta
k’ara musu yadawo 15k. San suki karb’a sai da su Inna
Yalwa sukace”ko kun rainane?. Da fara’a sukace”a’a Allah
ya sanya alkairi, wane mu da raina kyautan da zata fito,
daga gidan surkan Gwamna, matar d’ansa d’aya tilo. Inna
Yalwa cikin rashin fahimta tace” umm Hajiya bam gane
kince Surkar Gwamna ba?. Matar tace” eh ko bakusan
cewa Umar shine d’an Gwamna d’a d’aya tilo na miji.
Inna Yalwa tace”sam bamu sani ba ya ma b’oye mana ko
shi waye”. Take matar ta war-ware musu, aikafin ta rufe
baki. Gwaggo tasaka ihu ta hau tsakiyar kayan tana watsi
da su, tana cewa” wanna fa k’arya ne d’an yankan kai ne,
Hajiya Suwaiba k’anwar Adam Naira cike da mamaki,
tace”lalle tabbas yau naga halinki da’ake fad’a. “Bari kiji
ga kayan Lhadijat nan abu d’aya ya bata sai mun miki
rashin mutunci, kisani duk wanda zakana masa hassada
da bak’in ciki, Allah kan masa sakayya, mugunta da kike
mata ne Allah ta bata. Gwaggo tayi kanta zata cakumeta
wani security ya kaimata naushi ta fad’i a kasa. Hajiya
Siwaiba tace”ae da ka barta da yau na koya mata hankali,
ni ba irin matan da suke d’aukan wargi bane. “Mtsss
bamza sakarya marar imani. “Khadijat takusa hutawa da
muguntanki. Gwaggo na ihu kamar mahaukaciya, tana
cewa”sai kun kawo na Beeba da Rabee’ in ba haka ba
zamana lafiya. Gwaggo hauka tuburan Inna Yalwa ta kali
K’anwar Gwaggo tace”da fa kin kama yar’uwanki kartayi
tsirara, tsabam bak’in ciki. Da kyar aka shigar da Gwaggo
d’aki aka kule ta. Malam da yadawo, ko da yaji labari,
Hamdalah yayi, ya k’ara gode ma Allah, tabbas Khadijat
ta samu miji, don yana jin labarin halin d’an Gwamna.
Kayan yasa ka aka d’eba a gidan aka kai gidan Inna Yalwa
da daddare, ba wanda yasani, motar kuwa ya kai gun
wasu masu ajiye mota aka ajiye masa. Yan’unguwa ko
ina ka leka sai zance akeyi, wasu ko so suke su ga Khadi
matar d’an Gwamna. Gwaggo tana d’aki sai zage-zage
take, Beeba ko murna ba’a magana. ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ
]9:12 PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA
BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-116~120. A gidan su Dr Umar kuwa, sun gama had’a
lefe nagani na fad’a, lefen nun ma sa’a. Cikin kayan harda
key d’in mota, k’irar Honda CRV, Mum d’insa ta saka
masa, Dr Umar shima ya karo wasu kaya aka saka, masu
karatu kar kuso kuga kayan akwatina ma Set hud’u
akasa, zannuwa kuwa ba kananu. Hmmm kayan d’an
Gwamna d’aya tilo aidole ya zama abun kalo, Mum
tace”Umar ka sanar da Khadijat jibi za’a kai kaya. Cikin
murna ya shirya sai da ya je Store ya mata sayya, ya nufi
gidan, bai wani b’ata likaciba ta fito. Sai da sukayi hiransu
yace mata”My Khady!”. Cikin sanyin murya ta amsa da
“na’am”. “Khadijat! Duk wani farin ciki na kene, ina
matuk’ar qaunanki. “Alhamdulilah! Allah ya amsa min
addu’a ta, na bani ke amatsayin mata. “Ki sanar da
mutanen gida, In Allah ya kaimu jibi za’a kawo kayan
lefe. Cikin jin kunya ta saki murmushi, tare da rufe
fuskanta da tafin hannun ta. Hira sukayi mai cike da so
da qauna, sai dab magriba, ya mata sallama ya tafi.
Khady na shiga gida ko da Malam ya dawo, bayan ta
masa sannu da dawowa, ta sanar masa da sak’on Dr
Umar. Cikin farinciki ya yi musu addu’a. Washegari
Malam ya aika ma dangin Mahaifiyar Khady, dangin Uba
ya sanar ma wayanda yakama ta su zo karban kaya.
Malam ya sayo kayan karban bak’i, harda yan kajin sa,
guda biyar ya tura kasuwan kauye, aka sayo masa. Ya
sayo multina da lakacera, kaya iya na talaka, Baba Yalwa
k’anwan Maman Khadi su suka soya kaji, pepper meet
sukayi, yayi kyau ko ina sai kamshi yakeyi. Gwaggo in
banda harare-harare ba abinda takeyi, ko hannu bata
samusu a aiki ba, karfe uku sun gama komai sun gyara
ko ina sai kamshi yakeyi. Malam yaje ya d’an had’a kud’in
da zai had’a na kasan akwati, ganin karamci irin na Umar
ya samo dubu goma yaba ma Inna Yalwa yace a basu.
Khady ko tayi wanka cikin kayan ta masu kyau, suka
zauna a d’aki ita da Beebah don basa son yawo.
Rabee’atu kuwa tana kusa da Gwaggo, sai lashe baki
takeyi, don tunda taga ana soya kaji, yawunta ya kai. Su
Inna Yalwa wanka sukayi, suka saka kayan su, mai kyau,
suna zaman jiran baki. A gidan su Dr Umar kuwa, Mum
kwanta ta kira da matan Baba Liman, sai Kwanwar Baban
su Umar, bata tara mutane ba, sabida tasan yanayin
gidan su Khady, kar suje su musu ba dai-dai ba. Milasalin
karfe hud’u da rabi, suka d’au hanyan. Misalin karge
biyar, cikin unguwansu Khady, ya d’au jiniya, motoci ne
sukayi jerin Gwano ga securitys a motoci sun sanya
sauran motan a tsakiya, suna shigowa take suka fir-fito
dan gani mai zai faru. Motocin qofar gidan su Khady
suka tsaya. Gwaggo dake d’aki taji jiniya mota, tace”ko
lafiya naji karan motar yan sanda?. Rabee tace”ai inaga
wanda suka daki Adda Khady ne suka dawo dukanta
hala. “Don ranan da irin wannan suka zo. Gwaggi
tace”Allah yasa sune, su dakata inga ta inda za’ayi auren.
“Zo mu fita muga ya zasu kare. Suna fitowa dai-dai
lokacin yan sanda suka shigo gidan da bindigansu,
Gwaggo sai zare ido take. ana haka suka ga wasu Mata
cikin shiga ta alfarma sun shigo. Gwaggo tace”lafiya dai
naga kuna shigo mana gida?. Wata mata mai yar kiba
tace”nan ne gidansu Khadijat?. Gwaggo tace”eh! Nan ne.
“Lafiya dai?. “Lafiya klau, kafin tayi wani magana ansoma
shigo da akwatuna. Gwaggi tace”wanna fa?. Matar
tace”kayan Khadijat muka kawi”. Gwaggo ta buga k’irji
tare da zaro ido. Nima Rash sai da wayata ta subuce don
na tsirata da ganin yanayin Gwaggo. ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ
]9:12 PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA
BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-126~130. Hajiya Suwaiba suna komawa, suka sanar
da Mum d’in Umar yanda sukayi, tayi mamaki sosai ashe
da gaske haka halin Gwaggo yake. Nan tace” hmm ni
gwanda His Excellency ma ya dawo ayi bikin, yarinya ta
huta. Hajiya Suwaiba tace”yaushe zai dawo? Mum tace”
nan da 5days zai dawo. Hira sukayi tayi da yanda biki zai
kasance. Gwaggi ko ta hana su Malam bacci sai ihu take,
ko sallah anki bud’eta tayi. Khadi tayi murna tayi godia
ma Allah da zab’in da ya mata, take ta kira su Farhat B
Haske ta fad’a mata, Farhat ma take bata labarin tayi
sabon saurayi, Sunansa Abdul-wasilu Humble, Khadi ta
mata fatan Allah ya dai-daita su. Tana kashe wayar ta kira
Queen Neenah ita ta fad’a mata, daga nan takira Hajiya
Jamila Abubukar ta sanar mata, tayi murna sosai da
sosai, takuma bata shawarwari da yanda zata kula da
Umar kasancewa Hajiya Jamila ta girmesu, tana kwance
dasune don taga suna da hankali shiyasa. Malam ganin
iskanci Gwaggo zai wuce gona da iri, da safe yaje ta
windoq duk ta wargaza d’akinta, yace”Hauwa ki nutsu,
wallahi kinji na rantse, matsawan baki bar haukan da
kike ba to yau zan rubuta miki saki, don ba za’azo biki ina
matsayina na Surkin Gwamna a ga mahaukaciya a
gidana ba, kuma haukanta akan bakincin take ma Surkan
Gwamna. Ni Rash nace”hmmm Malam da biyu yayi
maganan nan, don ya kuna Gwaggo ne. Gwaggo tace” eh
dole kace haka ae dama baka sona don yanzu kaga Khadi
zata auri d’an Gwamna dole kamin haka. Malam yace”
kene bazaki gane ba ina sonki sosai, halinki ne bana so,
ya fita abunsa. Gwaggo jin saki ta nutsu ko da tafito,
jummai k’anwarta tayi mata nasiha tace”Yaya matsawan
baki kwantar da kai ba, ina fad’a miki zaki wahala don
yarinyan nan tayi gaba. Kiyi hak’uri kawao. Gwaggo
tundafa wannan rana ta dawo kamar bata gidan yanzu
bata dai magana da Khadi, amma ta bar hantaranta ko
sabganta tabar shiga. Khadi ko kulum suna mak’ale da
waya ita da Umar, suna waya ne yace”gobe Dad zai dawo
ki shirya, in ya dawo ke da Beebah zakuzo ku gaidashi.
Cike da murna tace”sai mun tambayi Baba in ya barmu.
“Kedai nasan Baba bazai hana kizo ki gaida Surkinki ba.
Haka sukayita hiransu mai cike da ni shad’i. Washe gari
da safe inna ta d’aura ruwa a hita, dai-dai kusa da
d’akinta a kwai soket, ya tafasa ruwan ta kashe, taje
d’auko boket kenan ta sukuya tana d’aurayewa, sai tebur
d’in ya karye yana shirin zubowa akan Gwaggo. Khadi
tafito da ga d’aki karaf idonta ya sauka akan tebur, “kira
ta kwala ma Gwaggo, ganin bata gane mai take nufi ba,
da sauri tayi gun don ceton Gwaggo. Tana zuwa ta ture
Gwaggo ta hantsula gefe kagin ta kauce ruwan ya juye
mata ajiki, wani razanane k’ara tasaki, ta fad’i agun tana
shure-shure. Gwaggo duk ta rikice, Beeba da Rabee sai
Jimmai kanwar Gwaggo suma ihu suka saki, ana haka sai
ga Mal da gudu yayi kan Khadi, wanda azaba yasa ta
suma, d’aukarta yayi waje yafita da gudu yashiga Napep,
Gwaggo ma da gudu duka bisa, Beeba kam sai kuka take,
tana fad’i”wayyo Adda na!. Gwaggo sai hawaye takeyi,
tabbas yau Khadi ta gwada mata yar halak ce ita, gashi
taje ceton rayuwana itakuma zata rasa nata. Tabbas yau
na yarda da kalman nan ta ‘YA’YA DA DUKIYA BA’A
K’ETARSU, bakan wanda zai tai makeka ba. Suna isa
asibiti Dr Abdul suka samu gani halin da take ciki, akayi
Emergency da ita, wayan Dr Umar yakira. Dr Umar suna
Airport shida Mum da Ilham sunje d’auko Dad d’insu,
don har jirginsu ya sauka, Dad ya sauko kenan, sun
rungume juna, wayar Dr Umar tayi k’ara gani Dr Abdul
yasa yad’aga da sauri “hello yace”. Daga d’aya ban garen
Dr Abdul yace”kana ina, kazo ba lafiya Khadijat ta kone
bansam ko garin yaya bane, amma ina zati ko Gwaggo
nane ta konata sabida halinta. “What ina bazai yuba sai
na d’au mataki. Mum tace”Kai da wa?. Cikin muryan kuka
ya fara basu bayani, His Excellency yace” what muwuce
Asubiti yau matan na zata gane ita bakomai bane. Suna
zuwa Asibiti ta ko ina ya amsa da jiniya. Dr Umar da
Gwamna da gudu suka fita duka shiga Emergency, Umar
na ganin halin da Khadi ke ciki, kara ya saki ya fad’i
sume. Mum da Ilham sai kuka suke, Gwamna ya fita
kiran Doctors suka d’au Umar shima. Yana fitowa yaga
su Malam yace”ina Gwaggo da take?. Malam ya nunata
da yatsa, His Excellency da gudu yayi kanta wani damka
ya mata, ya fara kwara mata kyawawan mari,
yace”wallahi in har na rasa d’ana d’aya tilo, da abar
qaunar sa, to kema sai kinyi mutuwar wula kanci. Kisani
‘DA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU. amma ke munguwa nai
bakin hali zaki gane kurenki. Ball yakeyi da ita, yana
fad’an magan ganu, da kyar aka rik’e shi, sijoji yace atafi
da ita CID agana mata azaba. Basu tsaya jiran komai ba
Women police suka d’au Gwaggi sama aka sata a mota,
aka nufi CID da ita. Ni ko Rash tsaban gulma ina leka
motar naga bakin Gwaggo har ya kun bura, fiskan taji
marin manya, tamkar ba Gwaggo mai bala’i ba. ﺓﺪﻴﺷﺭ
9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA
DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-136~140. Umar kuka yake ana haka har suka iso New
Delhi, motane tazo ta d’aukesu har asibitin da za’a mata
aiki, kasancewa a sanar musu, sun sanda suwansu, ana
shiga da ita likitoci, suka hau bata taimak’on gagawa. Sun
d’au awani suna mata surgery, Umar ya kasa zaune ya
kasa tsaye, duka sun dun kufa sai addu’a sukeyi. cikin
ikon Allah likitan ya fito cike da fara’a, hannu ya mika ma
Gwamna, yace’ In Allah ya yarda musa tsamani komai
normal” Hamdalah suka rayi, suna gun akazo aka wuce
da ita zuwa d’akin da zasu ajeyeta. Khadi bata far-fad’o
ba sai kusan 3:00am na dare, doctors aka kira duka
dubata, Umat ko sai addu’a ke mata. Haka suka kasance
cikin jinyan Khadi yau kusan watandu d’aya kuma yau ne
za’a ware mata, bandage, doctor yace”suyi fatan Allah
yasa aikin yayi nan aka shiga da ita, wani room don since
mata, su Umar sai addu’a yakeyi. Awa d’aya ya d’aukesu,
likita ya fito nan ya saida musu komai normal, zasu iya
shiga su ganta, Umar da gudu yayi d’akin yana zuwa ya
ganta kwance, suna had’a ido murmushi ya sakarmata,
zuwa yayi ya rungumeta, ana haka su Malam suka shigo,
sai da Dad yayi gyaran murya, tukun ya san sun shigo,
cikin jin kunya ya koma gefe, sannu suka ringa mata.
Tun daga wanna ranan Umar shike mata dressing d’in
ciwonta, ya bata abinci abaki, ya mata alwala, da
daddare kuwa kafin ta kwanta zai d’auko story book
yana karanta mata, da joke masu dad’i tana dariya, har
tayi baci, inyaga tayi nisa da bacci yazo ya ru gume
matarsa haka rayuwansu, ya kasance gwanin dad’i.
Ganin Khadi ta warke suka fara ahirin dawo 9ja don ayi
biki kowa ma ya huta. Gwaggo kam taci a zaba, in har
kasanta ada kaganta yanzu bazaka ganeta ba, tayi baki
sosai, gashi har hak’urinta sun zube, tsaban duka da
wahala, sai daga baya ne, Beeba ta sanar ma Dr Abdul
gaskiya, shima ya fad’a ma Baban Umar, sai da sukayi
bincike suka tabbatar da gaskiyan al’amarin kafin aka
saketa, randa tashiga unguwansu, matasa suka tashi zasu
mata duka da kyar aka kwaceta, Gwaggo tayi nadama ba
kad’an ba. Kulum cikin saloli take, tana addu’an Allah ya
tashi kafad’un Khadi. Yau jirgin su Khadi ya sauka 9ja,
Umar ko sai wani rawan kai yakeyi, ko kunyasu Dad baiji,
sai yawani rok’o hannuta, sai da Mum ta zo ta rik’e
hannu yarta, Mum tace”Malam za’aban aron yata, zan
tafi da ita kafin biki. Yace”bakomai ae Khadi takune. Suna
isa gida ta kira Hajiya Suwaiba da Ameena tace”ga yata
nan kuje a gyara min ita, banson Umar ma ya ganta sai
biki. 4:55] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 5/25/2016] Rash Kardam :
’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A.
KARDAM. Pg-141~145. Shirye-shirye biki akeyi ba sanya,
su Hajiya Jamila.k’irjin biki, su Farhat da Queen Neena
takanas suka koma gidan Hajiya Suwaiba da zama,
abunda aka shirya za’ayi ran Alhamis kamu, sai Jumma’a
Walima da daddare kuma dinner, washe gari asabar yini.
Komai ya tsaru yanda ake so, yau ne ranar da za’a fara
Kamu, da yamma ko kwaye sun shirya, har an kaisu gun
jiran isowar Amarya ake, ba’a dade ba kuwa ta iso cikin
wata lafiyayiyar mota, tun dana zuba ido ma Khadi kasa
d’aukewa nayi, gaskiya tayi kyau, duk yan guri sai yaba
kyanta suke, taro yayi taro, komai yatafi yanda akeso, sai
kusan shida suka gama kamu, daga gun gidan, Hajiya
Suwaiba aka sake kaita. Washe gari akayi walima shima
tsaru daddare kuwa sukayi shirin dinner. Hajiya Suwaiba
ta bada umurni akai Amarya gidansu daga