da guri ya
lafa,Dr Abdul yace”Baba ka same ni, a office d’ina. Biyosa
yayi, suka nufi office d’insa. Sai da Dr ya zauna,
yace”Baba ka zauna, magana zamuyi da kai. Malam ya
zauna, ya na fiskantan Dr, gurin shiru kusan, na minti
biyu, kafin Dr ya nisa yace”Baba ina son in tan bayeka ne
game da Khadija.miye alakarta da wannan matar? Kusan
yawanci lokuta, in kun kawo Khadija ba ta da lafiya,
matan nan sai ta mata abun da zai kunta ta. anya kuwa
mahaifiyarta ce?. Malam ya nisa yace”gaskiya ba
mahaifiyarta bane, Khadija yar riko ne a hannu mu, nan
Malam ya kwashe tarihin Khadi, ya basa a takai ce, ba Dr
Abdul ba, ni kaina Rash na tausaya mata.wayar sane tayi
haske alamar kira ya yanke, d’agawa yayi, ya ga duration
wajan awa d’aya da rabi, sai alokacin ya manta, bai kashe
wayar ba. Dr Umar da ke jin, duk abun da ya faru da
Khadi, tare da tarihin rayuwan ta, take yaji yana son tai
maka mata. Ta bashi tausayi, da ace yana 9ja da ya san
abunyi, kwanciya yayi, a lafiyayen gadon sa, fiskansa
yana kalon silin, cike da tunani kala-kala, har bacci ya
d’aukesa. Dr Abdul ya nisa yace”gsky Baba ya kamata ka
d’au mataki, don yarinyan nan, tana yawan aiki da ruwa,
ga wahala ya mata yawa. Malam yace”nagode in Allah ya
yarda, zan d’au mataki, sallama ya masa ya koma, gunsu
Khadi da har a lokacin, kuka takeyi sosai, ko da ya iso, ya
kalleta cike da tausayawa, yace”Khadeejatu~Kubrah!, ki
kara hak’uri akan na da, nasan ki mai biyyace, duk da
Gwaggo tana cutar da ke, kuma kina hak’uri, ki ‘kara
akan na da, kinji ‘yar albarka, kai ta d’aga masa alamar
eh!. Sanna tace”Baba ka maida Beeba gida, tunda Gwaggi
bata son zamanta anan. Murmushi yayi, yace”Beeba ba
inda zata koma, har sai an sallame ki, Beeba ‘yatace nafi,
Gwaggon ku iko akanta. Nan ya ta gaya mata kalamai
masu dad’i, har ta mance da muwarta, dariya suke yi, ita
da Beeban ta. Gwaggo ko da ta koma gida, taringa masifa
da zage-zage, har Malam ya dawo bata daina ba, har tana
cewa”kasake ni mana, tunda yarinyan ta lashe kurwanka,
d’aki ya shiga, ya kyaleta ta gama sababinta. Kwanan su
Khadi biyar, a cikin Asibiti aka sallame su, tun a hanya
take far gaban, dawowa gida, don bata san dame,
Gwaggo zata tareta ba. Dr Umar kuwa tunda yaji
labarin,Khadi yaji yana son tai maka mata, yarinyan ta
bashi tausayi. Wayarsa ya d’auka ya kira Dr Abdul bayan
sun gaisa yace”ya aikin dai? Daga ban garen Abdul
yace”Alhamdulilah! Aiki ba dad’i. hira sukayi sosai, Dr
Abdul yake tambayar Dr Umar yaushe zaka kare course
d’in nan?. Ajiyar zuciya yayi, kafin yace”saura wata shida
mu gama, nima na damu in dawo 9ja, nayi missing
abubuwa da yawa. Cikin zolaya Dr Abdul yace” harda
Baby Sakina ko?. Mtss yayi d’an tsaki yace” ana ta kai,
waya ke ta kaya. wannan mayyar yarinya, maras kamun
kan, ina zan kaita?. Ae saninta ya fi nawa. Yauwa ranan
wacece naji ana hayaniya akanta?. Rannan muna waya
da kai, kamar a Ward d’in mata ne, sai da Dr Abdul ya
d’anyi tunani kafin yace”ok! Khadijat ne, nan ya kwashe,
labarinta ya basa. Dr Umar ba karamin tausaya mata
yayi ba. Ya kuma kudiri aniyar, duk randa ya ganta cikin
damuwa sai ya tai maka mata, duk da bai san ya kamani
ta yake ba. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-46~50 Suna isowa gida,
Beeba ta ba wa mai Napep kud’insa, ta d’auko su bargo,
da pillow, suka nufi k’ofar shiga gidan. Khadi ta tsaya,
Beebah ta juyo ta kali Khadi, Tace”lafiya naga kin tsaya?.
Nan take idon Khadi ya kawo ruwan hawaye, tafara
magana, cikin muryan kuka,”Beebah ina tsoron shiga
cikin gida, don Gwaggo zata iya dukana, kinga Baba baya
nan, Beeba ta kalleta cike da tausayawa, Tace”Addah
muyi addu’a in Allah ya yarda bazata yi mana komai ba.
Kalamai masu dad’i, da ‘kwantar da hankali, tayita fad’a
ma Khadi, kafin ta yarda sukayi addu’a, tare da shiga
gidan. Assalamu’alaikum! Gwaggo dake d’aki, tanata
sababi, taji kamar muryan Beeba da sauri ta fito, har
tana tuntube, tana fitowa taga su Khadi, wani uwar ashar
ta narka mata, da kalon yau zaki sani. ‘Daki ta koma, ta
d’auko wata zu’ke’kiyar bulalan ta, Gwaggo tace” yau sai
na rama, marin da kikasa Malam yamin, kuma wahala
yanzu kika fara, Mayya kawai, sam tsabar bala’i, bata lura
da qofar window, dake bud’e ba, jikake Garamm
Gwaggo ta gwaru da window, sai da ta fadi a kasa. Nan
take, ta saki ‘kara, oh ni Rash nace”su Gwaggo ko d’an
dauriya babu. Ihu take kamar qaramar yarinya, Khadi da
gudu, ta iso gunta fiskanta, d’auke da hawaye, sannu take
ma Gwaggo, cikin tausayawa. Gwaggo da ‘kyar, ta iya yin
shiru, tana d’agowa kuwa, bakin ya kumbura sundum,
ko danaga bakin, bansan likacin da nasaki dariya ba.
Gwaggo d’aki tayi, ko magana bata iyayi, sabida bakinta,
paracetamol ta sha, don ta ji sanyi ajikinta. Khadi kam
d’aki ta shiga, ta takure gu d’aya. Tana cike da tunani, mai
tasa Gwaggo ta tsane ta haka?. To mai iyayenta sukayi
ma Gwaggo ta ke tsanar su haka, har ya shafeta?. Duk
wayannan tambayan bata da amsansu, haka ta hak’ura,
dan bata da amsan tambayanta. Gwaggo tunda baki ya
d’anyi sau’ki, ta soma gana ma Khadi azaba, na yau
daban, na gobe daban, wani saran da ta samu, in Malam
nanan, bata cika gallaza mata ba, amma in Malam ya fita,
Khadi sai ta gwammace kid’a da karatu. Khadi ta yanke
shawaran samun Malam, Tace”Baba ina son, in fara zuwa
gurin, koyan d’inki, yafi zaman da nakeyi. Malam ba
k’aramin dad’i yaji ba, kuma hakan zai ragemata, yawan
damuwa, sati guda ya nima mata, tafara zuwa, amma sai
dai yana nesa da unguwansu. Gwaggo tayi bala’i ba
‘kadan ba, gani bata da mafita yasa ta hak’ura, tafara
tunanin, sabon hanyan da zata, gallaza ma Khadi.
Kwanaki sun tafi,Yau saura sati d’aya, Dr Umar ya
kammala course d’insa, suna yawan waya da Dr Abdul.
Khadi tana zuwa gurin k’oyan d’inkinta, gata da hazaka
da basira, yanzu har ta fara had’a kayan yara, zata yanka
da kanta ta had’a. Ganin haka yasa Malam ya sayo mata,
keken d’inkin hanu, dontana, yan facin da sanda na
mutane, tana samun biyar goma. Masu karatu karkuso
kuga Gwaggo ranan, kamar zatayi hauka, dan bak’in ciki
da takaici, Khadi kam kule kanta, tayi a d’aki, don
Gwaggo tace yau ko ita ko Khadi. Fanz kumin hak’uri, na
rashin jina, k’wana biyu, bama samun wuta ne. ﺓﺪﻴﺷﺭ
9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA
DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-51~55. Gwaggo tun da taga Khadi, tana d’an samu a
d’inki, hankalinta ya tashi, Gwaggo ta kudiri aniyar sai ta
b’ata keken d’inkin. Beeba ko murna ganin Addah ta,
tasoma iya d’inki yanzu zata bar kai d’inki, ana wulakanta
ta, Gwaggo ko kulum sai ta zagi Beeba, akan yanda take,
nuna zakewar ta ga Khadi. Haka rayuwa tayi ta tafiya,
Khadi na cikin kunci da matsin Gwaggo, hak’uri takeyi da
ita, kulum sai taci kuka, yanda Gwaggo ke zagin
iyayenta.Yanzu har ta kai, yan’unguwa sunsan, Khadi yar
riko ne a hannusu. In Gwaggo taga Malam baya gida ta
hana Khadi zuwa gun d’inki, in makwabta sun kawo faci,
Gwaggo ta korasu, ta hana su shiga cikin gidan. Khadi
kusan sati bataje, gun koyar d’inki ba. Malam baya
samun zaman gida, sabga sun masa yawa, gashi yau
tafiya ta kamasa zuwa Jigawa, tunda asuba yatafi. Zaije
ya sayar da Gona’nsa dake garin, don fara sayyan auren
Khadi. Da wuri ta tashi tayi wanke- wanke’nta gama, ko
karyawa batayiba ta d’au hijab da nikaf d’inta, ta fito
cikin sand’a, takalmanta a hannu ta rike dan Gwaggi
kartajita, cikin sand’ a ta fita, a qofar gida ta sanya hijab
dinta. Sauri- sauri ta fara tafiya sai da tayi nisa ta duba
jakanta, taga naira d’ari ya rage mata, Gwaggo duk ta
amshe sauran kud’in. Mai Napep ta tsara, ta masa
k’watancen gurin, Yace”tabada naira d’ari, nan tafara
“rok’ansa ragi, da kyar ya yarda zai kaita a naira Saba’in.
Ta shiga suka d’au hanya, ko da taje sai da mai
koyamusu d’inki, ta mata fad’an rashin zuwanta, hak’uri
ta bata.nan suka fara aiki har sai da karfe hudu suka
tashi, din yau sun samu K’wangilan dinka uniform d’in
wani school. Dr Umar ne ke waya, yana sanar da Mum
d’insa zai da wo 9ja, girki na musamman Ummin sa ta
masa, ko da jirginsu ta iso, driver ne da kanwarsa Iham
sukaje d’auko sa. A hanya suke hira da ilham, yana
tambayar ta, yan’uwa da abokan arziki, har suka iso gida,
tun daga nesa nake hango securitys a qofar gidan,
tabbas ko ba’a fad’amin ba, Umar d’an wani babban
attajiri ne, ko mai mulki, don masu karatu, bazan iya
tsara muku kyan gidan ba. Tundaga gate masu aiki, ke
masa sannu da dawowa, har ya isa cikin wani falo, niko
Rash ganin irin kyan gidan nace”bazan bari a bani labarin
cikin gidan ba, da hanzari na sanya kaina cikin falo,
yasalam masu karatu hmm wai in bakayi bamu guri,
karkuso kuga cikin falon, sannu a hankali, nafara bin
falon da kalo, komai na golden da brown ne, ko dana
d’aga kaina wasu koyaye ne tamkar zinari, sai haskawa
sukeyi a cikin falo. Gefe na samu na rab’e don yanda
sanyin A.C ke bugani, ga wani sassayan kamshin da ke
tashi, wata yar datijuwa ce, ta fito d’auke da fara’a,
afuskan ta ta iso cikin falon, tana cewa”ur welcome my
son. Cikin girmamawa yaje yayi hugging d’inta, yana
fad’i” i miss u too my lovely mum. Kanshi ta shafa, tare
da rike hannusa, my Son “muje ka watsa ruwa sai kazo
ka ci abinci ka huta. Mikewa yayi ya nufi side d’insa,
komai a canza masa na d’akin, wanka ya shiga, bayan ya
fito ne ya nufi falo, nan ya cika cikinsa da abinci kala-
kala, yana kammalawa kenan ya nufo falo, wani daga
cikin security d’in yazo, yace”Oga kana tare da bako Dr
Abdul, ya kalesa cikin girmamawa, Yace” barshi ya shigo
ae ba bako bane shi d’an gida ne. Dr Abdul ne ya shigo,
sai da ya gaida Ummin su Dr Umar, tukuna suka nufi
side d’in sa, hira sukayi sosai kafin ya masa sallama, akan
zasu had’u, sai da ya rakosa, har jikin motarsa yashiga sai
da, Dr Abdul ya bar gidan, kafin ya koma cikin gida.
Amin afuwa, har yanzu wuta bai tsaya ba, shiyasa kuke
jina shiru. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-56~60. Yau kwanan Dr
Umar 8 da dawowa, har ya koma bakin aikinsa, tun safe
yake jin son yawo zai zaga gari, kuma bai son security ko
d’aya yabisa, don shi daman bai cika fita da security’s ba,
don Dad ke matsa masa baya son yana yawo haka, ko
driver yana bari yana jansa, yana tashi a office karfe
3:30pm, gida ya nufa yayi wanka, yau sai ya tsinci kansa
da son sanya jamfa, nan ya ciro wata shadda dark blue
amata aiki, da surkin farin zare da blue, hularsa ma blue
ce da surkin fari, ya d’auko ta kalminsa ya tare da agogo,
tsayawa yayi a madubi, yana kare ma kansa kalo, gaskiya
ya hadu ko ni Rash dana kalesa, sai da kirjina ya bada
dumm, Umar mutum ne mai kyau ga kamala ga
k’warjini, fari ne tass, yana da dogon hacci tare da
karamin baki, kai in ka kallesa sai karasa da wani yare
zaka danganta shi, India ne ko balarabe, ko Fulani. Tunda
ya sauk’o falo falo, umma ta ga d’anta, sai murmushi
take zubawa, tace”Baba na sai ina haka?. “Wananan
wankan fa?. “Ko nayi surkace?. Don raboka da saka
manyan kaya ka dade. Cike da murmushi ya kalli Umma,
Yace” Ummana duk wannan tambayar ni kad’ai, bata
surka Umma da saura tukun, zan dai zaga cikin gari ne.
Cike da kulawa tace”Allah yasa futanka a samomin surka
mai hankali da tarbiya, yar mutunci, cikin jin dad’i ya
amsa da Ameen. Tace”Son Allah tsare a dawo lafiya, ka
kuma tafi a hankali, to ya amsa ya fita, tun a harabar
gidan ma’aikata ke masa sannu kud’i ya ciro a aljuhunsa
wanda bai san nawa bane ya basu, ya shiga motarsa ya
ja. Khadi tafe take, tana tunani yau ta kad’e, in cikin
zuciyar ta tace” yau gashi malam baya nan, nikam na
banu, bansan wani irin duka zata min ba. Hala yau
kamma, k’wananane ya kare, nan tafara “Ya Allah ka yafe
min, kasa na cika da imani, wasu hawaye ke bin fuskarta.
Tafiya take sam bata san inda take nufa ba. Tsaban zance
zuci, har ta hau kan titi, jama’ a dake hanyar sai kalonta
suke, wasu na tausaya mata, gashi fuskanta da nikaf,
jama’a na ta mata magana sam bata sani ba, bata ma san
sunanyi ba,”wai kunu a wani gida”. Dr Umar na tafe a
cikin motarsa, ya kuna qira’ar Ahmad Sulaiman, yana
tafe cikin nutsuwa, ya wuce ran about baban gwari
kenan ya d’auki hanya. Sam bai hangi yarinya ba, sai da
yazo kusa ya ganta. Sai tafiya take a tsakiyar titi ga
mutane sai kalota suke horn yayeyi da k’arfi, amma sam
bata ji, gashi ya d’au gudu sosai, wani wawan burki da
yata kane yasa dawo cikin hayyacinta, damar motan, ta
gabanta ya tazo, suman tsaye tayi, dan tsaban razana ita
bata fadi ba ita bata motsaba. Da sauri ya fito cikin
motar, yana zuwa kusa da ita, yaga bata motsa ba ga
idonta sun kafe, cikin dakiyar zuciya yave” ke lafiyarki
klau kuwa kika hau kan titi?. Me kike tunani haka? Luuu
yaga ta tafi zata fad’i cikin zafin nama ya tareta, ta sauka
a jikinsa. Jijigata yayi yaga bata motsi, cikin sauri ya
fincike nikaf dinta, sam bai ga fuskanta ba, juyaa yayi, ya
kali wanda suka taru a gun, wasu na masa kalon
mamaki, wani d’an tsoho yagani yace”Baba pls kazo ka
taimaka min dan Allah. kamata sukayi, suka dawo da ita
gefen titi, da sauri Dr Umar yaje da gudu ya bud’e
motarsa, ya d’auko goran ruwa, yazo ya yayya fa mata,
sai a lokacin ya kali fuskan, kasa d’auke idonsa yayi, yana
furta”Sarki ya tabbbata ga ubangijin sammai da kassai,
lalle ubangiji yayi hallita a gurin. a hankali tasoma bud’e
idonta, tarass ta sauke su akan, Dr Umar da ya zuba
mata na mujiya, ya kasa d’auke kansa ga fiskanta. ﺓﺪﻴﺷﺭ
9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA
DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-66~70. Gwaggo cikin hayaniya da masifa, Tace”mai
yasa baka tura, Beebah ko Rabee’atu, sai Khadi, to sai dai
na k’ona kayan. Malam kasa magana yayi, tsaban takaicin
dake damunsa, wannan wace irin fitinaniyar macece?.
Gwaggo ta d’ibi kayan, tayi hanyan kitchen dasu, Malam
na ganin haka ya bita, kafin ya isa, har ta fara sawa a
wuta, kwacewa yayi tare da zaro na wutan, wani gyalens
mai kyau, da sauri ya taka, da takalmin sa, wutar ta
mutu. Wani gumun kalo ya mata, duk iskancinta sai da
ta shiga taitayinta, ta fito a kitchen, koda tazo dai-dai gun
Khadi shureta tayi da kafa, sai da Khadi ta fad’i, ta Beeba
ne ta d’aga ta, rana mata sannu, Malam yace”Hauwa mai
yasa baki da tausayi ne?. Kina tuna kema zaki mutu
kuwa?. Ki sani fa duk inda, iyayen Khadeeja sukaje, kema
zakije, kuma Allah baya kyaleki bane, kuma nima ba wai
fa tsoronki nake ji ba, ina d’aga miki k’afa ne. Hauwa
kisani ‘YA’YA DA DABBA, DA DUKIYA, BA’A K’ETAR SU,
bakisan wacce irin baiwa Allah yayi ma Khadija ba,
bakisana wani irin taimako, zata miki a rayuwan ki nan
gaba. Gwaggo ta kali Malam cikin kalon da ban d’au
maganar ka da muhimmanci ba, tace” ehehehe Khadi ne
zata taimaken, ahir ahir, Allah ya tsare gatari da saran
k’ota, ni da Khadi badai muzauna inwa d’aya ba. Malam
ya kaleta yace”Hauwa da badun Allah bayason saki ba, to
da yau tabbas sai kin bar gidana, kuma kinci albarkacin
Khadi da ‘YA’AYAN da kika haifa. Koda Malam ya ambaci
saki, sai da k’irjin Gwaggo bada sautin damm! damm!..
Amma cikin k’arfin hali, dake shaid’an ya mata
kururuwa, tace”sai me in ka sakeni?.daman wani abu
nake samu a gidanka, in banda gayyan tsiya. Malam ya
d’aga hannu yace”Ya Allah kana jina, kana ganin abunda
ke faruwa, Ya Allah ka azurta Khadi da abunda zata
taimaki Hauwa’u. Yana dasa aya, Gwaggo tace” ba amin
ba har abada, sai dai ku da wannan mayyan, talashe
zuciyarku. Fuuuu Gwaggo takama hannu Rabee, tajuya
ta kali Beebah, kee da ta lashe maki zuciya, saikiyi ta
makale mata, suka shiga d’aki. Malam ya kama hannu
Khadi, da Beeba ya kaisu d’akunsa, albarka ya samusu, ya
musu nasiha, tare da k’ara bama Khadi hak’uri. Tace”
Baba ba komai, ae Gwaggo uwatace, ita na bud’i ido na
gani, ita na santa, kuma ina mata fatan Allah yasa ta gane
Ameen ya amsa. Dr Umar kuwa, yana komawa gida, ya
tarar da Mum d’insa, suna hira da Ilham, shima zama
yayi, tare dacewa washh, Mum tace” daga ina haka Son?.
Gyara zama yayi, ya kali Mum yace”daga gidansu
Khadeejat nake. Kafin Mum tayi magana Ilham tace”bros
nikam ina son gani Aunty Khadejat d’inana. Kulum sai
labarinta mukeji, fuskansa cike da murmushi, yace”zaki
ganta har sai kin gaji da ganinta ma. Mum tace”
Alhamdulilah! Allah ya nunan ranan da Babana ya samu
wacce yake so, sai fatan Allah ya kaumu lokacin biki, cike
da zumu d’i ya amsa da Ameen. Dr Umar yace” Mum
baki ga yarinyan bane, gata da hankali, kuma inkinji
rayuwanta abun tausayi, nan ya basu labarin
had’uwansu, da irin wahalan, su Mum da ilham sun
tausaya mata. Ilham tayi karaf tace” bros to ina wacce
katab’a ban lbr ta, itama wacce Khaji a agun Dr Abdul?.
Ummm itakam har yanzu ba labarinta. Mikewa zai haura
sama, yakali Mum yace”yau she Dad zai dawo daga
Dubai d’in?. Umma tace” umm sai next week. Ok! Allah
ya kaimu. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-61~65. Sai da ta dad’e
kafin, ta d’an tashi, sannu suke mata, bata iya amsawa
ba, sai da ta huta sosai, Dr Umar ya kaleta, cike da
tausaya, Yace”yan’mata mai yake damunki haka?. Da har
kike irin wannan tunanin?. Kasacewa komai tayi, sai da
yamata fad’a sosai, Yace” ki tashi mukauki gida, sai a
lokacin ta zaro ido, kai ta girgiza musu alamar a’a,
bayanda basuyi ba, amma fir taki, daga k’arshe Dr Umar
ya tsara mata Napep, nan ta bada kwatance gidansu, sai
da tashiga Napep sun d’au hanyan, Dr Umar ma motarsa
yashiga, har yayi hanyan gida, komai tuna ya juya kan
motarsa zuwa Dakata, gudu yakeyi sosai, cikin sa’a ya
hango Napep d’insu, a baya ya rinka binsu har suka kai
k’ofar gida. Mai Napep ya tafi, ta tsaya a k’ofar gida, tana
tunani shiga, gashi yamma tayi sosai, ga yunwan da
takeji, da kyar ta iya shiga gidan. Ganin ta nufi cikin
gidan ya fito daga motarsa yazo dai-dai zauren.
Assalamu’alaikum ta fad’a cike da tsoro, kara shiga ciki
tayi ganin Gwaggo bata kusa, da sauri Gwaggo ta
fito,”kee karuwa yar’iska ina kika fito?. Cikin fargaba da
zaro ido, Khadi tace” wallahi Gwaggo gun d’inki naje.
“Karya kike dan ubakiki, dukanta Gwaggo tayitayi kamar
ta samu jaka. Dr Umar tun daga, nesa ke jin murtan ta
tana ihu, sai leke yaykeyi, zuciyarsa na tafarfasa, ganin
Gwaggo ta d’auko muciya, Beeba da ke gefe sai kuka
takeyi, tana bama Gwaggo hak’uri, Dr Umar dake cikin
zaure, ganin Gwaggo, ta d’aga muciya zata kwada mata,
bai san lokacin da ya shiga gidan ba, rike muciyar.
Gwaggo cikin fushi, d’ago tana masa kalon raini, daga kai
waye ne?. K’ok’arin fincike muciyar takeyi, Malam da ya
dawo daga tafiya, yaji da sauri ya k’araso cikin gidan,
ganin abunda ke faruwa yace”Hauwa mai kikeyi haka?.
Nan fa tafara ba Malam labarin karya da gaskiya, ta
d’aura dacewa”Khadi karuwa ce yar’iska, da sauri Malam
ya dafe kansa, don harcikin zuciyan sa, yaji kalman ta
dake shi. Cikin kunan rai, Dr Umar yace”wannan sharri
ne wlh, nan ya kwashe abunda ya faru ya fad’a musu.
Gwaggo nan ta tire, “sam ni banyarda ba, shine ya
d’auketa suke iskanci tare, Malam ya mata kwalon uku
saura kwata, hak’uri ya fara ba Dr Umar, tare da masa
godia. Dr Umar yayi musu salma ya nufi gida, cike da
jimamin rayuwan Khadi. Tun daga wannan ranan, Dr
Umar yasamu gurin zuwa, gidan gun Malam susha hira
sosai, wani lokaci Malam ya turo Khadi su gaisa, sam
bainuna musu ko shi waye ba, kuma bai taba sayan wani
abu ya basu ba. A hankali shak’uwa ta shiga tsakaninta da
Dr Umar. Kamar kulum Dr Umar, yayi wanka cikin
manyan kaya, yayi kyau sosai, sai da ya biya ta, Sahad
store yayi sayya, kaya ya had’a ma Khadi, less da atamfa
da shadda d’inkaku, da su takalma da jaka. A hankali
yake tafiya, har ya shigo unguwan, cikin sa’a ya samu
Malam na gida, sai da suka gaisa, ya bud’e boot din
motarsa, buhun shinkafa biyu, na tuwo dana dafawa, sai
taliya carton biyar da makaroni, harda su maggi star.
Malam dake gefe, ya tsaya yana kalon ikon Allah. Sai da
aka gama shigarwa, Yace”Umar mai yasa kayi irin
wannan d’awainiyar, kai ya sunkuyar, Malam ae ba
komai, kai mahaifi ne ae. Godiya yayi masa sosai, dai-dai
lokacin, Khadi tafito Gwaggo ta aike ta, tazo wuce musu,
ta gaida Dr Umar ya amsa cikin kulawa zata wuce,
Yace”tsaya ki amshi sak’onki, don ina sauri yau, wasu
manyan ledoji ya miko mata, Malam Yace” Umar
d’awainiyan yayi yawa, bakomai Baba sauri nake, sai na
dawo, godiya yayi masa Dr Umar yaja motarsa ya bar
gidan, Khadi ne tafara shiga cikin gidan da laida, Malam
na biye da ita. Gwaggo tana ganin laida a hannu Khadi,
da sauri taso zata amsa, ganin Malam tace”yau samuwa
mukayi haka?. Malam yace”eh! Wallahi wanda ya
taimaka ma Khadi ne yayi mana alkairi, Gwaggo ta dafe
k’irji lokacin ta zazzage kayan ciki, nan fa ta tsorata, “ae
wallahi abunda bazai yuwuba kenan, wannan k’arya ne.
Malam daman funa furci ka kula shine ka tsiri kai Khadi
koyar d’inki, don kana son ta had’u, da wanda ya kawo
kayan, mai yasa baka tura Beebah ko Raee’atu ba?. Sai
Khadi, nan tafara tonan silili ma Khadi, cikin takaici
Malam ke kalonta. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016]
Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-76~80. Da sauri ya tareta,
ta fad’a hannusa, sunanta yakira, Khadijat! Khadijat
Khadijat… Pls ki tashi, kar ki tafi ki barni lokacin dana ke
bukatarki, kene farin cikina. Pls Khadijat, yana jijigata,
amma sam ko motsi batayi, Dr Umar ya fita a
hayyacinsa, sai sam batu yakeyi, Gwaggo ko wani ruwan
sanyi, tasake d’ebowa bata tsaya, wata-wata ba, ta k’wara
ma Dr Umar. Duk da na da lafiya sai da ya razana, ajiyar
zuciya ya sauke, nan take ya dawo cikin hayyacinsa,
hannu sa ya kala, da sauri ya d’auketa, cikin mota ya
sanya ta. Da gudu yabar unguwan. Asibitin Murtala ya
wuce, yana zuwa ya d’auketa a hannu, Emergency yayi
da ita. Kasancewar shi duty safe ke dashi, Dr Abdul ke
duty kwana. Da sauri ya d’aga waya ya kirashi, “Dr Abdul
dan Allah kazo Emergency, Khadija tace bata da lafiya,
kazo ka taimka min, muryansa kaman zaiyi kuka, duk ya
rud’a Dr Abdul, don bai kuma taba jin, Dr Umar cikin
wannan, yanayin ba. Dr Abdul yace”Friend wacece
Khadija?.cikin fushi yace”Malam in zakazo to in bazaka
zo nakira, DR James, kashe wayan yayi, yafara kiran Dr
Jame kenan, Dr Abdul ya turo qofar ya shigo. Da sauri
yayi kanta, yana ganin Khadi ce, mamaki ya cikasa,
tambayoyi yafara yi makansa,” daman Umar yasan Khadi
ne?. “To mai yasa yarinka min tambayoyi akanta?. “Ta
ya’akayi tazama Khadijansa?. Maganan Dr Umar ne ya
dawo da shi, daga dogon tunanin daya shiga. Dr Umar
Yace”kai Malam, lafiya kake mata, irin wan kalon?. Da
sauri yazo ya kareta, cikin kishi da jin haushi, yake
maganan. Dr Abdul bai cemasa uffan ba, cikin hanzari
yasoma dubata, daman yariga yasan matsalanta, cikin
ikon Allah, ansamu numfashin ta, ya dawo dai-dai. Sai
dai bata farka ba, sun mata aluran baci, don ta samu
hutu. Special room aka kaita, don hutawa ita kad’aine a
d’akin. Dr Umar ya zauna, a bakin gadon ya zuba mata
ido, ko kyaftawa ba yayi. Ji yake kaman ya k’arba mata
ciwon, Dr Abdul ne ya shigo, yace”Ya mai jiki?. Da sauki
ya bashi amsa. “Allah ya k’ara sauki. “In ka gama
kasameni a office d’ina. Ok! Dr Abdul ya fita, office d’insa
ya koma, ya zauna cike da tambayoyi, a fuskansa. Dr
Umar sai daya kai, kusan kamar 1hrs, kafin ya kira nurse,
yace”ta kulamasa, da patient d’insa. Da sallama ya shiga
office d’in Dr Abdul, bayan ya zauna ne, Dr Abdul
Yace”friend ina kasamu Khadi?. Ko dama ka santa tun-
tuni, Dr Umar yace” kai ka santa ne?. Dr Abdul ya d’aga
masa kai alamar eh!. Ajiyan zuciya Dr Umar yayi, nan ya
kwashe labari, tunga randa ya fara ganinta, har yanzu,
dayake fama da azaban sonta. Sai da Dr Abdul ya jijina
kai, yace”Allah mai iko, to ae itace Khadijan, da ranan
kaji ana case akanta. Cikin mamaki Dr Umar yace” mai
kace ne ban fahimta ba. Nan Dr Abdul yabashi labarinta,
iya yanda ya sani. Umar ya tausaya mata ba kad’an ba,
wani Sonta da Qaunarta, suka k’ara shigansa. Cikin
tsokana Dr Abdul yace” friend amma gaskiya, ka cika
kishi, kawai don ina mata kalon sani, amma kawani tare,
dariya Dr Umar yamasa, tare da kai masa dukan wasa.
Malam dawowansa, daga kasuwa kenan, aka basa
labarin, abunda ya faru bai iya shiga gidan ba, ya juya zai
tafi kenan, yaga Beeba ta fito, duk ta rud’e hijab ma bai-
bai tasa. Da sauri ta bisa, Napep ya tsara musu, suka nufi
Asibitin Murtala. Zuciyan Malam sai tafasa yakeyi, yana
tunanin wani kalan hukunci, zai yanke ma Gwaggo. Don
abuntan yayi yawa,”to wai mai Khadi ta tsare mata a
rayuwanta ne?. Da takeson ganin bayanta, tabbas zai
Aura da Khadi, don ta huta da bala’in Gwaggo. ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ
9:12] ﻡﺩﺮﻛ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA
DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-71~75. Khadi kulum tana cikin k’unci, Gwaggo ta sata
a gaba, baran in taga, Malam ya fita kasuwa. Gashi Dr
Umar ya kwana biyu bai