An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
YAYA DA DUKIYA BA A KETAR SU
Na Rasheedah A kardam
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
YAYA DA DUKIYA BA’A
K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. ﻦﻤﺣ ﺮﻟﺍ ﻟﻠﻪﺍ ﻢﺴﺒﻟﺍ
ﻩﺮﺳﻭ ﻪﺘﻴﻧﻼﻋﻭ ﻩﺮﺧﺁﻭ ﻪﻟﻭﺃﻭ ،ﻪﻠﺟﻭ ﻪﻗﺩ ،ﻪﻠﻛ ﻲﺒﻧﺫ ﻲﻟ ﺮﻔﻏﺍ ﻢﻬﻠﻟﺍ . ﻢﻴﺣ ﺮﻟﺍ.
ﻢﻴﻫﺮﺑﺇ ﻝﺁ ﻰﻠﻋ ﺖﻴﻠﺻ ﺎﻤﻛ ﻪﺘﻳﺭﺫﻭ ﻪﺟﻭﺯﺃ ﻰﻠﻋ ﻭ ﺪﻤﺤﻣ ﻰﻠﻋ ﻞﺻ ﻢﻬﻠﻟﺍ .
ﻚﻧﺇ ،ﻢﻫﺮﺑﺇ ﻝﺁ ﻰﻠﻋ ﺖﻛﺮﺑ ﺎﻤﻛ ﻪﺘﻳﺭﺯﻭ ﻪﺟﺍﻭﺯﺃ ﻰﻠﻋﻭ ﺪﻤﺤﻣ ﻰﻠﻋ ﺖﻛﺭﺎﺑﻭ
ﺪﻴﺠﻣ ﺪﻴﻤﺣ . GATARWA Dukkan yabo ya tabbata ga Allah.
Ina godiya a gare sh’i, ina neman taimakonsa, ina neman
gafaransa, kuma ina neman tsarinsa daga sharrace-
sharracen rayukanmu da mitagyn ayyuka. Wanda Allah
ya sh’irye sh’i babu mai b’atar da sh’i, wanda kuma ya
b’atar ba mai sh’iryar da sh’i. Ina shaidawa babu abin
bautawa da gsky sai Allah, shi kad’ai, babu abokin
tarayya gare sh’i. Ina shaidawa cewa Muhammadu
bawansa ne kuma manzonsa ne. Ya Allah kayi tsira ga
wad’anda suka bish’i da ky’aky’awan kw’aikw’ayo har
zuwa ranar kiyama. Kuma ka musu aminci, aminci mai
yawa Ameen. SADAUKARWA Na sa daukar da wannan
littafi mai sun YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU, ga
Mummy’s d’ina Khadija’s. GODIYA godiya mai d’imbin
yawa gareku, da bazarku nake taka rawa a duniyar
Rubutu, Allah ya barmu tare. Maryam .S. Bello Maryam
Alkali Mamu(Mrs Jabo). Page-1~5. Tari wanki ne a
gabanta, sai faman wanke su takeyi, kalo d’aya zaka mata
ga gane ta gala baita sosai, har k’arfin har bata jin karfin
jikinta. Gwaggo ne ta taho da wasu kayan wankin ta kara
mata, tace “Khadi maza- maza kiyi sauri ki wanke ma
Beeba kaya, zata gidan Innarku. A wahale na d’ago nace
“Inna ga wasu sabbin kayanta can na wanke su, sun
bushe tasa su, kuma suna da ky’au, gash’i nayi wankin da
yawa na gaji. Gwaggo wani uwar ashar ta narko, wanda
ni Rash bansan lokacin da nayi baya da sauri ba. Shako
ta Inna tayi tace”dan jakar ubanki ni zaki fad’a ma kin
wanke wasu, kuma har kina iya cewa kin gaji. Eh!
Lallekam yau zaki gwadan ke yar Zamani ce, ban isa dake
ba ko?. Khadi cikin muryan kuka tasoma cewa”dan Allah!
Gwaggo kiyi hak’uri wlh ba da wara manufa na fad’i
hakan ba. Gwaggo kara shaketa tayi tace”ko uwar ki ma
bazata mayar min da martani ba. Kafin Khadi tayi
magana ji kake tass tass tass ta wanke ta da mari har sau
uku, dukanta tafarayi ta kota ina. Wayyo ni kaina Rash na
tausaya ma Khadi, don ga alama fuskan gwaggo nan bata
da tausayi ko kad’an Taku a kullum mai k’aunar ku ﺪﻴﺷﺍﺭ
9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA
DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-6~10. Gwaggo sai da tayi likis ma Khadi kafin ta
ky’aleta, tace”wlh sai kin gama wankin nan yau ko na
miki dan banza duka, sha-sha kawai, mts tayi tsaki ta nufi
cikin d’akinta. Khadi kam kuka tasha ga wani yunwan da
ke murd’amata ciki. Kama cikin tayi ta tamke da d’an
kwali abunka da Khadija maganin Maza cikin dakiyar
zuciya ta fara wankin , da ikon Allah kafin akira Sallah
la’asar ta gama. Gwaggo ta fito da abinci a d’an k’aramin
kwano wanda ko d’an yaro bazai ish’esh’i ba. Ta turo
mata kwanon ta juya tayi d’akinta ko tausayin Yarinyan
nan bata ji ba. Ga uban aikin da ta mata a cikin gidan
kamar jaka. Malam Ahmadu ne ya sh’igo da Sallamansa,
in donsa ne ya sauk’a kan Khadi dake kwance tamkar
wanda aka d’aura ma dutsin dala da gauron dutsi aka. Da
sauri ya k’arasa gurinta cike da tausaya wa, ya tallabo ta
yace “Mama na ya dai? Mai ya same ki na ganki haka? .
Gwaggo ta fito cike da masifa tace”komai ne ya same ta
ko zaka karb’a mata ne, sai in sani. Cike da b’acin rai
Malam Ahmad ya nufo ta, yace”kee Hauwa wlh ki kiyaye
ni zan sas-saba miki akan Khadija sam ba kya tausayin
yarinyan nan. Gwaggo tace “ina ko zan tausaya mata ba
sanin zafinta nayi ba bare na san miye tausayi. Malam
yace”duk aikin da take yi a gidan baky’a gani ko?. Kuma
ba ky’a sanya yar cikinki. Wannan yarinya Yata ke a gun
mu, duk irin rikon da muka mata Allah zai tambaye mu,
Hauwa kiji tsoron Allah. Gwaggo tace”ehehe wa’azi
zakamin ai tsoron Allah kulum cikinta muke, yar wani ba
yata bace nawa kawai na san, fuuu tayi d’aki in ka gama
sai ka sanar min. Taku a kulum mai k’aunar ku ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺪﻴﺷﺍﺭ
9:12] ﻡﺩﺮﻛ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA
DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-11~15. Cikin ta kaici yazo ya tallabi Khadi ya d’agata
sai a lokacin ya kalli d’an abinci da gwaggo ta bata.
Taburma ya d’auko a d’akinsa ya sh’in fid’a mata, ya
zaunar da ita. Kular abincinsa ya kawo mata tare da juye
ruwa mai zafi ya had’a mata Lipton ya bata da kyar ta iya
sha. Abicinsa ya kara mata, sai da ya tabbatar ta kosh’i
kafin ya ci sh’ima. Khadi ta mik’e jiki ba kwari ta nufi
rijiya ta d’ebo ruwa ta nufi bayi, wanka tayi ta fito, ta sha
fa mai kayanta masu d’an kyau ta saka ta dawo waje gun
Malam don gudun bala’in Gwaggo. Malam yace”Mama
nah bazan fasa miki nasiha ba, inaso ko kasance mai
yawan hak’uri kinga halin Gwaggon ku kullum Addu’a
nake mata Allah yasa ta gane gsky. Khadiya duk halin da
kika samu kanki, ki kasance mai hak’uri zakici riban
rayuwanki. Kai ta d’aga masa alamae Eh!. Heeba ce ta
sh’igo da Sallaman ta, cikin fara’a ta k’araso gun su,
sannu da gida ta musu kafin tace”Addah ina ta sauri inzo
in tayaki aiki, da aka tash’i a makaranta, ban samu abun
hawa ba, Gash’i har kin gama. Khadi tayi murmushi
tace”ba komai k’anwata, ya makaranta?. Alhamdulilah! Ki
d’auko abinciki kici to Adda. Malam yana jin dad’in
yanda yaransa suka had’a kai, baran Beeba da sam bata
gado halin uwarta ba, heeba ya rinya ce mai hankali
kamar Khadi. Sabanin Rabi da ke ji da taken rash’in
kunya, halinta sak na uwarta hatta kama da Gwaggo take
kama. Gwaggo tafito tsawa ta daka ma Beeba kee mai
kikeyi a gunsu, kin dawo ko sanar ni bazakiyi ba, ni bana
son kina taraya da mai fiska kaman na muciya. Oh! Ni
Rash nace”wannan Gwaggon wata irin macece ta fiye
son kanta, anya ma idonta na gani kuwa?. Duk irin kyan
Khadi tana zaginta. Ko beeba ma bazata gwada mata
kyau ba don ta d’aran mata nesa ba kusa ba. Taku a
kullum mai k’aumarku . 9:12] ﻡﺩﺔﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺪﻴﺷﺍﺭ PM,
9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A
K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-16~20. Jiki
ba kwari Beeba ta nufi d’akin, don sam ita bata son irin
yadda mahaifiyarta ke nuna tsana ma Khadi. Gash’i ko
kad’an Khadi bata nuna damuwarta kuma hakan ba sh’i
zai hanata biyayya ba.Allah yasa Gwaggo ta gane. Ya
sh’irya mana ita Ameen. ‘Dakin su tash’iga Gwaggo ta
balbaleta da masifa, Gwaggo tace”Beeba bana son ganin
ki da wancan mai fuskan mujiyan, kema kuma sai niman
kai kike da su. Ni har Malam da ke biye mata ba kyalesh’i
zanyi ba, ko kad’an bana k’aunar in bud’e ido imganta a
gidan nan. Beeba tace”haba Gwaggo ba kyau fad’an haka
fa, kuma ae Addah tana iya k’ok’arinta gurin kyautata
miki. Ita ne kulum cikin aiki bata hutawa ko ni bana miki
aikin da take, nikam ina son Addah na tana da halaye
mai… Bakinta Gwaggo ta make tare da wata harara
tace”kee a kul d’inki kar na kara jin cewa kina had’a kanki
da wannan yarinya, Ko kema ta shanye miki Zuciyan ne?,
kama yanda ta shanye na Malam baya ganin laifita baya
son amata fad’a. Beeba tace”ko d’aya Gwaggo gsky kenan
Khadi tana da halaye mai kyau. Mts Gwaggo ta ja tsaki ga
abinki can maza ki ci don zaki gidan Innan ku, zaki anso
min aika a gunta. Beeba ta d’auko abinci zatafita gunsu
Malam Gwaggo ta dakatar da ita, ba yanda ta iya dole
yasa taci a d’aki badan taso ba, don ta fi jin dad’in
kasancewa da yar’uwanta. Gwaggo tace”Beeba yi sauri ki
sh’irya kije min gidan Inna ku. To ta amsa ta kammala
cin abinci tayi wanka ta d’auko kayanta masu kyau ta
sanya su, ra fes da ita. Gwaggo “nagama sh’irin ke nake
jira kizo fad’an sakon, don inje kar dare ta min a hanya.
Sai da Gwaggo ta d’auko sakon da zata kai ma Inna kafin
ta bata kud’in mash’in tace”kice ta had’a miki duka aikan
harda kayan da na saya d’in, to ta amsa ta fito sai da tayi
sallama wasu Malam kafin ta tafi. Taku a kullum mai
k’aunarku 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺪﻴﺷﺍﺭ PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Notice Masu karatu na zansa
sunan littafina daga KHADEEJATUL-KUBRAH zuwa YA’YA
DA DUKIYA BA’A K’ETARSU, cos Daman YAR’RIKO ne suna
Da na fara sawa, sai aka samu wacce tayi. So yanzu
namar dashi YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU. Yafi
ma’ana kuma sakon littafin akan haka zai tafi. Pg-26~30.
Ana kiran sallah tayi d’akin su ta kwanta, kasanewan
garin da sanyi lokacin hunturu ne. Addu’a tayi ta kwanta
ga yunwar da ke addabarta. Haka har bacci b’arawo yayi
awon gaba da ita. Dukun-kune take a yar ta barmata gefe
kuma katifar Beeba ne yar k’arama wanda mutum d’aya
zai d’auka. Bacci take amma sanyi ya dameta. Kiran
Sallah asuba ya farkar da ita da kyar ta mik’e ta d’ibo
ruwa a randa sai d’ari take yi. Alwala tayi ta koma d’aki
tayi sallah bayan ta idar ta fara azkar d’in safiya wani
bacci ne ya d’auketa kamar daga sama taji an shek’a
mata ruwa mai sanyi nan take ta fara d’ari-d’ari, duk da
haka Gwaggo bata kyaleta ba wani ruwan ta k’ara kwara
mata. Barin da takeyi ya tsananta, Gwaggo tace”ke har
kimsami daman da zaki kwanta bacin safe, uban wa ya
baki dama?. Malam yana karatun Al-qur’ani mai girma
sai yaji kamar ana hayaniya jin maganan yayi yawa ya
fito, yaji d’akin su Khadi ne da sauri ya sa kai cikin d’akin
ganin Khadi ta fi luuuu zata fad’i yaje da sauri yana”Salati
ya tare ta fad’a a hannunsa cikin k’unan rai ya d’ago ya
kalli Gwaggo yace” in kin kasheta ae kin huta, kin san
yarinya tana fama da Pneumonia kuma yayi mata yawa
zaki kwara mata ruwan sanyi, haba hauwa anya kina
tsoron Allah kuwa ae d’a ko ba kai ka haifeshi ba, bai
kamata kina wula kanta ta ba.( Yan uwa mata kira
gareku, kune jigon gida duk lokacin da gida yayi kyau
kune, kusani Ya’ya da Dukiya, da Dabba ba’a mugun tar
su. A rauwa ba kasan wanda zai taimake ba, sai kaga d’an
da ka haifa da cikin ka wani lokacin bai jik’anka ba,
wanda baka san zafin sa ba ya taimake ka kuma Ya’ya
Rahmane dan Allah kuna kyautata ma yara ba sai naka
ba ku d’auka duk d’aya suke a gunku). Gwaggo ko a
jikinta tayi waje tana cewa”ni dai dole ta fito ta min aiki
yau ko ta ji a jikinta. Malam ya kali Khadi ta idanunta
suka kafe a sama da sauri ya d’auketa ya fita waje da ita.
Beba da ta fito daga d’aki ganin halinda Adda ta ke ciki
yasa tayi gun Malam da hanzari suka fita dake garin da
sanyi da kyar suka samu mai Napep yace”Yaro Asibitin
Murtala zaka kai mu, Malam da Beeba suka shigar da ita
ciki suka d’au hanyar Asibitñ, sun d’anyi tafiya kafin suka
iso asibitin, kud’in mai napep ya basa kafin ya d’auki
Khadi suka shiga cikin Asibitin nurse suna hango su, suka
tahoda sauri suka karb’eta. Emergency aka nufa da ita,
Dr Abdul ke bakin aiki, da sauri “nurse suka sanar masa
an kawo patient. Yace “ok! I’m coming now”. Bata dad’e
da isa gun su Malam sai ga Dr Abdul nan ya iso. Dubata
ya soma yi yaga tana wani yanayi numfashinta na shirin
d’aukewa, tai makon gaggawa aka bata cikin ikon Allah
suka samu numfashinta ya dai-daita. Magunguna ya
rubuta ya mika wa Malam yace”Baba gashi kaje
Pharmacy ka sayo, in ka dawo ka bawa nurse sai ka
same ni a office d’ina. Malam ya amsa da rawar jiki ya
nufi pharmacy. Taku a kulum mai k’aunar ku . ﺓﺪﻴﺷﺍﺭ
9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA
DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-21~25. Malam suna hira da Khadi Gwaggo ta fito
wani sak’on kalon da Gwaggo ta aika ma Khadi, yasa ta
mike ba sh’iri ta nufi kitchen ta d’aura girkin dare, sai da
ta magama aiki Gwaggo tazo ta d’auke tukunyan d’akinta
ta sh’iga dash’i duk abun da suke Malam na kalon su bai
ce mata komai ba. A zuciyansa ya na mai jin-jina bak’in
hali irin na Gwaggo, Malam ya mike ya fita waje zuwa
gurin da suke d’aukan karatu. Rabi ce ta sh’igo tayi
d’akinsu ta nufa ta dau naira goman Gwaggo tasa a
wando ta fita waje, alawa ta siya sai da ta shanye kafin ta
dawo gida. Gwaggo tazo d’aukan raina gomanta don a
siyo mata sikari ta saka a surki, taga babu kud’i cike da
masifa tazo ta danki Khadi tace”ke barauniya bani kud’i
na da kika d’aukar min wato satan ma gadonsa kikayi a
gun uwar ki. Khadi tace”Gwaggo ko d’akin ma ban sh’iga
ba ina zaune a nan gurin fa. Gwaggo tace”oh! Sharri zan
miki ko?. Ni a ya’ya na babu b’arawo ba mu gaji sata ba
sai dai ko gun uwarki ne zuri’an barayi. Nan take Khadi ta
soma hawaye jin takaicin yanda ake kiran iyayenta da
suke kasa. Eyeh lalle kin samu gu dan ban dakaki ba
shine kike kuka ko?. Gwaggo ta d’auko dorina tazane
Khadi sai da taji hannu ta ya gaji tace”naira goman da
kika d’auka a madadin abinciki na yau da kuma karin
safiya. Gwaggo ta juya zata tafi sai ta dawo ta rike kunne
Khadi tace”saura in Malam ya baki abunci ki karb’a ki
gani ni dake yau a gidan nan. Ina son ana kiran Sallah ki
sh’iga d’aki ban yarda ki leko waje ba, ina ga munanan
kafarki a guri kin san sauran ta nufi d’aki. Taku a kullum
mai k’aunar ku 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-31~35. Malam ya sayi
maganin dubu buyu da d’ari biyar ya nufo k’ofan
Emergency ya mika ma nurse “Malam ya tambayi office
d’in Dr Abdul nurse ce ta gwada masa, godiya ya mata
nufi office d’in, da Sallaman sa ya tura k’ofar aka bashi
izinin shigowa, Dr ya nuna masa gun zama Malam ya
zauna. Sai da Dr ya gama yan rubuce-rubucen sa tukun
ya d’ago da fuskansa tare da zare yar faran glass d’in da
ke manne a kyakyawan fuskansa. Malam ya msa sannu
da aiki,Cikin girmamawa ya amsa, kali Malam yace”Baba
jikin Khadeeja yayi tsanani sosai, mai yasa kuke barinta
tana aiki da ruwan sanyi?, kuma tana zama a inda ke da
sanyi, mai ya kawo hakan bacin na sha fad’a muku illar
hakan amma kun kasa koyayewa. Malam da jikinsa yayi
sanyi yace”Dr in Allah ya yarda wanan karon zamu
kiyaye fatan mu kawai yanzu ta samu lfy. Dr Abdul ya
kallesa sosai tabbas ya gano damuwa a cikin idonsa ga
alamar magana a bakinsa, amma tunda bai fad’a ba “ni
dai zanyi iya kokarina ganin na taimaka mata, ya Allah
kabata lfy ameen. Ya kalli Malam yace”shikenan zaka iya
tafiya amma akula mata da shan magani. Kai Malam ya
d’aga masa alamar eh!. ‘Dakin da aka kwantar ta ya
yashiga Beeba ya gani a bakin gadon ta zuba mata ido ga
alamar tayi kuka sosai. Da Sallama ya shigo Beeba ta
masa sannu ya amsa tare da zama a d’aya daga cikin
plastic chairs d’in dake d’akin. Yace”Beeba ya jikin Addah
ki?. tace” da sauki amma har yanzu bata tashi ba, bacci
take ya kalli Khadi yace”Allah ya baki lfy, cikin zuciyar shi
kuwa cewa yake” ya zama dole in d’auki mata ki akan
Gwaggo bazai yiwu Khadi taci gaba da wahala haka ba.
Ya mike ya nufi k’ofar Asibiti ya sayo musu abinci ya
dawo ya kawo musu nan Beeba ta karya, shima sama-
sama yaci abincin. Gwaggo ne tafito daga bayi ta na
zuwa d’aki taga ba Beeba ta duba d’akin su Khadi taga
bata nan d’akin Malam ma baya nan, Rabi ta tambaya
tace”kee ina Beebalo?. Rabi ta kalli ina tace” ba sun fita
da Malam ba naga ya riko Adda Khadi, tsaki tayi ta leko
titi basa nan, nan takama bala’i yau zaizo ya sameta akan
me zai fita mata da yarta don wata marar galihu, ita
yarta na galihu, cikin gida ta koma sai surutu take ita
d’aya. WACECE KHADIJA?. khadijatu~Kubrah shine asalin
sunan Khadi ya d’aya tilo ga Malam Adam. Malam Adam
haifafen garin kano cikin unguwan Dakata gurin fire
service. Yayan Malam Ahmad ne Ubansu d’aya ne. Tun
Malam Ahmad na karami Allah yayi rasuwa Mahaifiyar
sa, ya koma hannun Maman Adam wato Kakan Khadi
kenan, ta yi musu rikon tsakani da Allah har suka girma.
Adam shiya fara yin Aure kasan cewan shine babba sun
shekara da yawa da matar sa Balkisu Allah bai basu
haihuwa ba, sai daga baya ta samu ciki ya zo mata da
laulayi haka tayi ta fama har tazo haihuwa, ta kwana biyi
tana na kuda, kafin rannan ukun har ana shirin shiga da
ita operation ta haihu ko juyawa batayi ba Allah ya karbi
abunsa. Malam Adam yayi kukan rashin matarsa mai
hankali da kirki, watan ta shida da rasuwa Baba Ahmad
yayi Aure, ya auri matar sa Hauwa amma auren dangi
sukayi yar kwan war Maman sa ne,(danganta karsu ta
gun uwa kenan da haiwa). Hauwa macece mai masifa
tun tana budurwa ta ki jinin Balkisu Maman Khadi ganin
yanda Ahmad ke zama a d’akinta hakan yana bata haushi
sosai. Cikin ikon Allah Khadi ta samu kulawa in ka ganta
bazaka ce bata sha nono ba madara take sha bul-bul da
ita ga ta da gashi ga kyau sosai, gwanin burgewa. Hauwa
shekaranta 3 da Aure ta haifi yarta Beeba kar kuso kuga
murna gunta, ta d’au son duniya ta d’aura ma Beeba, ta
taso cikin kulawa ga hankali, in ka ganta sak Malam
Ahmad kamar kakinta yayi, yarinya mai hankali da
nutsuwa, jinin su ya had’u da Khadi tun Beeba na
karama Khadi ke mata wasa komai ta samu zata kawo
mata, amma in Gwaggo ta gani ta kwace ta yar ta daki
Khadi, ana cikin haka wata ranan talata Malam Adam ya
tashi da ciwon Ajali kwanasa biyar Allah ya karbi abunsa
tun daga wannan rana Khadi ta dawo hannun Malam
Ahmad da zama, nan Gwaggo ta samu daman galla za
mata, sam bata kaunar ganin Khadi da Beeba sun zauna
gu d’aya. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺍﺭ PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-36~40. Sam Gwaggo bata
‘kaunar ganin Khadik, da Beeba sun zauna gu d’aya. A
kwai wani rana, da Khadi na wasa ma Beeba, Gwaggo na
zuwa ta saka k’afarta ta shure Khadi, ta fad’i akan hannu
ta, sai da ta gurd’e. Ranan ran Malam ba ‘karamin b’aci
yayi ba, har sai da ya mari Gwaggo. Tun daga lokacin ta
‘kara tsanar Khadi, har zuwa girmanta, sam bata tausaya
mata, duk aikin gidan Khadi keyi, Beeba kuwa bata son
ganin Khadi cikin damuwa, in Gwaggo ta bata ma Khadi
aiki, sai ta faki idon Gwaggo ta zo ta tayata su gama. Haka
rayuwansu ya kasance dad’i da ba dad’i, Malam ya sanya
su a Makaranta Khadi da Beeba suna ‘ko’kari, amma
Rabee kam in ban da niman tsokana ba abunda take. A
hakan har Khadi ta kammala Secondary school d’inta, ta
barsu Beeba yanzu ke karatu har islamiya an yaye ta.
Matsalar ta d’aya ne sam bata kula saurayi, ko sunzo
Gwaggo koran kare take musu, wai baa su nimi mayya
ba. Tana lashe zuciyar mutane, har ta lashe na Malam da
yarta Beeba. Hakan sam bai damun Khadi,ita kulum da
Malam addu’a su, Allah ya shiryi Gwaggo yasa ta gane.
Wankin Gwaggo dana Ya’yanta Khadi ke yi, in tafara sai ta
gama, bata isa tace”ta gaji ba Gwaggo zata fara mata
bala’i, wani lokacin, abimci ma hana ta take. Back to lbr.
Khadi bata farka ba, sai kusan k’arfe sha biyu, sai da
Malam ya ga tasamu ta ci abinci, kafin ya musu sallama,
akan zaije shi gd ya dawo, Beeba ta mishi adawo lfy, ya
fita. Yana isa gd, Gwaggo ta taso cikin masifa, tana
tambayar sa ina ya kai mata yarta?. Ko dun bai damu da
ita ba ne, yana son wannan mayyar ta lashe mata kurwa,
kamar yarda uwarta ta lashe zuciyan mutane. Sai da ta
gama sababinta Malam bai bi ta kanta ba, abincin sa ya
d’auka, ya fita tare da tabarma da pillow. Gwaggo na
ganin ya fita, gyale ta d’auko ta fara binsa a baya, har
taga ya nufi Asibitin Murtala, itama tace”ma me Napep
su bi Malam, haka ko akayi, har ya shiga cikin asibitin, ta
bisa a baya, har ‘kofan Ward d’in da aka kwantar da
Khadi. Ta na labe taga ya shiga d’akin bai dad’e ba ya fito,
ya nufi wani guri a cikin asibitin. ta na shiga, gadajen ta
rink’a bi, har ta iso na su Khadi, wani mugun kalo ta
sakar ma Khadi,da ke jin gine da pillow, tace”mayya kin
lashe zuciyar mijina da yata, to bakiyi sa’a ba, tana zuwa
kusa da ita, ta wanke ta da kyakyawan mari, nan take yan
d’akin suka yi mata caaa. Kafin ka ce me, guri ya d’auka
da hayaniya. Dr Abdul ne ya fito daga Ward d’in dake,
kusa da na su Khadi, hannunsa rike da waya, da alamar
waya yakeyi. A hankali ya ke tafiya, tun daga nesa ya ke
jin hayaniya, yace”Dr Umar ina zuwa, naga kamar female
ward na lfy, bai karasa ba ya iso gun hayaniya, yayi yawa,
da kyar ya kutsa zuwa cikin gun, sam ya manta bai kashe
wayar ba. Dr Umar shima bai kashe ba, dai-dai lokacin
Malam ya iso gurin, ganin abunda ke faruwa ya soma jan
Gwaggo da ta rufe Khadi da duka, sai zuba bala’in take.
Dr Abdul ya iso yana “tan bayan lfy?. Gwaggo sai wani fin
cikewa take, Malam ya d’auke ta da mari. Ta d’ago tana
kalon Malam tace”ka mare ni a kan wannan banzan,
mayyan mai kod’ade’en fuska. Ba zan yarda ba, sai na
rama ta sake yin kan Khadi, itakam in banda kuka ita da
Beeba sun rike juna. Dr Umar da ke jin duk abunda ya
faro, duk da baya gurin amma ransa ya baci sosai, cikin
zuciyarsa yace”duk da bansan maike faruwa ba amma
wata irin macece haka?. Malam ya ransa ya baci mari ya
sake wanke Gwaggo da shi, zafin yasa ta nutsu sosai, sai
ta dawo ta fara jan Beeba, ita ko gadon ta rike, security
aka kira suka fita da ita. Sai da guri ya lafa, Dr Abdul
yace”Baba ka sameni a office d’ina ya fita, Malam ya nufi
office d’in sa. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016] Rash
Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-41~45. Sai