zoba, d’inki ma, tabar zuwa
sabida bala’in Gwaggo, wai sai Malam ya saka su duka,
don su Beeba su samu suma mai saya musu kaya.
Malam ko yace”bata isa ba, tayi k’ad’an ta gindaya mishi
sharad’i yabi. Tunda tun farko, Khadi ne tafara cewa tana
so, dan haka ba zaisasu ba. Zaban tayar musu da hankali
yasa Khadi ta samu Malam tace” Baba bana jin dad’i zan
d’an huta da zuwa aiki, kafin wata sati, Tukun ya hak’ura.
Dr Umar ko, bai da tunani da yawuce na Khadijat, so ya
kemata, wanda shi kanshi, bazai iya auna shi, a mizani
ba. Masu karatu zamu so musan, WAYE DR UMAR? Umar
Adam Naira, shine cikaken sunansa, d’a, d’aya tilo girin
Adam Naira. Adam naira haifafen d’an Kano ne, nan yayi
karatunsa, har ya girma, ya Auri maransa Maryama, sun
dade da aure, Allah bai basu haihuwa ba, sai daga baya
Allah ya azurta su da haihuwan Umar, wanda yaci sunan
Baban Mum d’insa, bayan shekaru da yawa, ta haifi
Ilham, wacce itace auta, a yamzu haka. Alhaji Adam
Naira yarike muk’amai, na gwamnati da dama. Wanda
yanzu haka shine gwamnan Kano State mai ci. Ya
kasance mutum ne mai kwatanta gaskiya da adalci,
hakan yasa al’uman garin Kano ta Dabo suke sonsa.
Tunda Umar ya taso, shi bamai son yawan, hayaniya
bane, sannan bai kula yan’mata,sai wata yarinya, Sakina
da ta makalemasa, sam bata cikin tsarinsa, don bata da
kamun kai, yar’gidan, matai makin governor ne, gata da
rashin kunya, shiyasa basa shiri. Yanzuma saukin da
yasamu, ya dawo yasamu sun fita waje, ita da Mum
d’inta. Iyayensa burinsu shine, yayi aure amma baya kula
yan’mata. Tun randa ya had’u da Khadi, tunda yasanar
da Mum d’insa, da murna ta, tasanar da His Excellency.
Yayi farinciki ba kad’an ba. Yace” yana dawowa zasu
samu iyayen yarinyan, ayi magana a sanya rana.wanna
shine labarin Umar a takaice. Dr Umar zaune yau, sai
tunanin Khadijat, da ya damesa. Key mutarsa ya d’auka,
yana fitowa securitys, suka fara gaidasa, da gudu suka
bud’e masa, k’ofar motan yashiga, gida ya nufa yayi
wanka, dun zuwa gun Khadi. Yayi kyau sosai, ya shiga
mota shi kad’ai batare da security’s ba, ya nufi gidan.
Khadi ko tunda ta tashi, tashi tana son yin wanka, kayan
da Dr Umar ya kawo mata. ta d’auko wani less, mai kyau
purple da duwatsu farare a jiki. Tayi kwaliya sosai, ta
kuma yi kyau. Kasancewan yanayi gari, da sanyi, gun sai
yayi, bada yanayi mai kayatarwa. Gwaggo ta shiga
makwabta, sai zuba take musu. Yaro ne yashigo”wai ana
salama, da Khadijat inji Umar. Tace”kace ina zuwa. Yana
fita ta d’auko hijab d’inta fari tasa, bakaramin kyau tayi
ba. Cikin nutsuwa ta fito, tunda Umar ya hangota,
zuciyar sa sai harbawa, ido ya k’ura mata. Gwaggo da
tafito daga, gidan su abula, ganin Umar acikin k’atuwar
mota, nan zuciyarta ya fara tafarfasa. Yau mai zanyi ma
Khadi na huce?. Wata zuciya tace”kawai ki d’auko wuka
ki burma mata. Mtss a’a za’a kamani, can shaidan ya tuna
mata, kawai ki shek’a mata ruwan sanyi, tunda bata so.
Da sauri ta koma gidan Abula, tace”dan Allah samin
ruwan a fridge d’inki. Sam Abula bata kawo komai ba, ta
iba mata, a karami roban plastic. Da sauri tayi gida, ta
k’ara dana randa, kamar wata mahauk’aciya ta fito. Dr
Umar ya shagala, da kalon Khadi, itako tana wasa, da
yan’yatsun hannuta. Sai jin shaaa… sukayi, take idon
Khadi ya kafe, numfashinta ya d’auke, ta tafi luuuuu zata
fad’i kasa. Da sauri Dr Umar ya fito, yana kiran sunanta,
tareta yayi ta fad’i a hannusa yana jijigata, amma sam
bata ko motsi. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻪﻠﻠﺗﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016]
Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-81~85. Malam sun isa
Asibiti, direct office d’in Dr Abdul sukaje, Don
tambayansa, ko nan aka kawo Khadija, don shi har
yanzu, bai san a ina, Dr Umar yake aiki ba. Duk da yasan
dai, shi likita ne, suna zuwa suka tarar da Dr Abdul a
office, cikin yanayi damuwa Malam”ya gaidashi, ya
tambayes ya aiki?. Alhamdulilah!, Malam yace”Dr dan
Allah, ko nan asibitin, aka kawo Khadi?. Dr Abdul ya
amsa masa da eh!. Barin rakaku d’akin da take. Sai da
sukayi tafiya mai d’an nisa kad’an, kafin suka shiga, wani
Ward mai kyau, kana shiga, falo zakagani babba, sai
gurin da likitoci ke zama, gefe kum d’akin hutun likitoci
ne. Sai d’akuna da suke jere, gwanin birgewa, gurin tsab
da shi, kamar ba’a cikin asibiti ba. Kowani d’aki gado
d’ayane a ciki, sai yar loka da ke gefe, Malam suka tura,
qofar d’akin da sallamansu. Dr Umar ne zaune ya zabga
tagumin gaban Khadi, sam bai masan sun shigoba, suka
sake mai-maita sallama, amma shiru, Dr Abdul ne ya isa
gunsa da sauri ya dafasa, yace”my friend, cikin razana ya
d’ago, sai a lokacin yaga Malam, duk kunya ta rufesa.
Mik’ewa yayi da sauri, yana musu, sannu da zuwa. Kalo
d’aya Malam yayi ma Khadi, yaji wani mugun tausayinta,
ya kamasa, tambayan kamsa yayi anya bayi da laifi,
shima acikin cutar da Khadi, da Gwaggo takeyi?. Idonsa
ne ya ciko da kwala, bakin gadon yaje, ya rike hannuta,
cikin muryan damuwa, Yace”Khadijatu kiyafr min, duk
nine silan saki, cikin wannan damuwar. Tabbas Hauwa
watarana sai tayi nadama, mai d’umbin yawa, Allah ya
miki Albarka, ya Allah kajikan Adamu. Duk wanda suke
gurin saida jikinsu yayi sanyi, Beeba kam kuka takeyi
sosai. Malam ya juya ya kali, Dr Umar yace”Umaru na
rasa, da wani irin, kalma zan gode maka. Tabbas ka
taimaki Khadijatu iya taimako, Allah ya bamu, abunda
zamu saka maka dashi.Allah ya maku Albarka Cikin
zuciyan Dr Umar yace”abida zaumin kad’ai kubani
Khadijat, don zuciyata, takamu da azaban sonta. Gwaggo
da ke gida, sai fatan take, “Allah yasa adawo, da gawan
Khadi. Na tsani ganinta, kamar mayya, komai zakamata
bata zuciya. Mtsss ina da daga nan, tashiga uwa duniya,
in huta da fitinaniyan, yarinyannan. Ko da taji Beebah
tabi Malam, sun tafi asibiti, bakaramin haushi tajiba.
Tunanin kalan, rashin mutuncin da zan masu. Kwanan su
Khadi, biyu a Asibiti, Dr Umar shi ke d’awainiya da su.
Kulum yana hanyan Asibiti, yana tashi daga aiki bayan ya
duba Khadi, shagon waya ya zarce, yasaya mata, iPhone
7, wayar ta had’u. Gida yanufa, yana zuwa, yayi wanka,
ya fito dining, Iham ce tazo tazauna a gefensa, tana masa
surutu, can idonta ya kyalo waya maroon, tace”bros
wannan fa?. Tare da kai hannuta ta d’auka, “bros wayan
tayi kyau, bai kaleta ba Yace”na Khadiyat ne, ihu tasa tare
da cewa”wooow wayan tayi kyau. Barin samata number,
nan harda WhatsApp, ta bud’e mata. Sai da yagama
tukun ya amshi wayan yafita. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM,
9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A
K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-86~90. Sai
da yayi musu, sayya mai yawa, ya nufi Asibiti. Ko da ya
shiga, sai da ya biya office dinsa, ya ajiye wasu files, kafin
ya nufi ,d’akin da su, Khadi suke. Da sallama ya shiga,
suka amsa masa. Beebah ne “ta gaida shi, cikin
girmamawa ya amsa, “ya tambayeta ya mai jiki?. “Ba shi
amsa da sauki Alhamdulilah!. Fita tayi ta basu guri, ya
kali Khadi da ke kwance, “ta gaida shi, cikin muryan,
marasa lafiya, “ya amsa mata, tare da tambayan ya
jikinta?. ta bashi amsa da sauki. Ido ya zuba mata, har
saida tasoma jin kunya, ajiyar zuciya ya sauke, ya kara
lumshe idonsa, a hankali ya bud’esu, cikin wani salo, da
karya murya, ya kira sunan Khadeejat!!!. Duk da rashin
lafiyan da take fama dashi, sai da taji, jikinta yamata,
wani iri,”Na’am ta amsa masa cikin siririyan muryanta.
Ya kaleta, yace”Khadeejat!. Na kasa hak’uri akanki,
Khadeejat!. Ki taimaki zuciyata, da take fama da azaban
sonki, My Khady tun randa, na fara d’aura idona a kanki,
nakamu da qaunar ki, ki taimaka in samu gurbi, a cikin
zuciyarki. Duk maganan, da yakeyi Khadi, bata ce komai
ba. Sai lumshe idonta datayi, kamar mai jin bacci, cikin
kasa-kasa da murya, harda d’an sauk’owa daga kujera,
Yace”pls Khadeejat ki taimaki rayuwata. Tabbas nasan
ina aure ki, a matsayin mata, kuma uwar ‘YA’YA NA,
nasan zasuyi alfahari dake, a matsayi uwa ta gari.
Khadeejat!. Ki sani duk wani abunda akeso, mace ta gari
ta had’a, kin had’a. Khadeey na!! I’m deeply in ur love,pla
don’t let me go!! You d joy of my lyf, pls n pls Khadeey!!,
ki samamin matsuguni, a zuciyarki, ko k’ad’an ne. Ganin
shiru batace komai ba, Yace”Khadeetaul~Kubrah, in kin
amince pls ko murmushi, kimin in samu sanyi, a
zuciyata. Ganin shiru yasa yanayinsa ya canza, duk da
idonta na rufe, tana iya ganinsa, amma shi bai lura, da
hakan ba. “Wani lallausan murmushi ta saki, tare da rufe
fuskanta. Ganin haka, ya sauke ajiyar zuciya, yayi godiya
ma Allah. Juya masa baya tayi, duk yanzu kunyansa, ta
soma ji, ya dad’e yana mata hira, ganin tana jin
kunyarsa, ya ajiye mata waya tare da mikewa, Yace”yau
k’anwata kunya na takeji, amma badamuwa, wataran
zanyi maganin kunyan nan. “Ga wannan d’an ajima
zamuyi waya, ya fita abunsa, a waje yayi sallama da
Beebah. Ko da tashi go d’aki, lokacin Khadi ta mike, sai
murmushi take zubawa, Beebah tace”Addah lafiya
naganki cikin wannan fara’a?, cikin zumud’i ta labarta ma
Beebah, itama tayi murna sosai,nan suka bud’e, kayan da
yakawo musu, yasha addu’a kam, suna bud’e na waya,
kalo ya koma kansa, sun yaba da kyan, wayan sosai. Sai
can dare taji wayar na k’ara, ko da tad’aga wayar kasa
d’aukan kiran, duk sun rasa ma ya’akeyi, Beebata tayi
nata basiran ama ina! Har wayan ta yanke, sai can dai
Khadi tace”tsaya inaga wannan, ruwan ganyen ne amsa
kira, do d’azu jan ya katse ne. Tana jan ruwan ganyen, ta
tafara jin magana. Assalamu’alaikum!
Wa’alaikumusalamu! Ta amsa, sai tayi shiru, ” Khadeejat
ya jikin?. “Da sauki Alhamdulilah!. Hira ya rinka janta
dashi, har sai da yaji, kamar bacci na son d’aukanta, ya
kyaleta. Kwanan Khadi 7 aka sallameta, tayi fress kamar
batayi rashin lafiya ba, suna dawo gida, suka samu
Gwaggo bata nan, suka shiga, harda Dr Umar ganin irin
yanayi, d’akin da Khadi take kwana, ransa ba dad’i ya kira
waya, ba’a fi minti talatin ba, sai ga mota da sabuwar
Katifa, irin manyan nan, da filo da bargo, aka gyara
d’akin fess, ya musu sallama ya tafi, ko da Malam ya
dawo yayi godiya, ana haka sai ga Gwaggo. Yau kam ta
cika kamar zatayi hakuka, don ba haka taso ba, taso a
fitar da kayan amma Malam ya hana. Rayuwa sai tafiya
yakeyi, soyayya tsakanin Khadi da Dr Umar sai abunda
ya karu, kulum suna gaisawa da Ilham, harta sata a
group d’in novel ta yi kawaye yanzu. Duk inda kake da
jama’a, baka rasa yan gulma, acikin mukaraban, Dr
Umar ansamu wanda ya sanar da Sakeenat, Dr Umar
yana neman wata yarinya, yanzu haka ana kan shirin
magana Aure, nan take hankalinta ya tashi, bashi ta biyo
jirgi yau ta tazo 9ja. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016]
Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-91~95. Karfe shidan
yamma, jirgin su ya sauka, acikun garin Abuja. Bata bata
lokaci ba, ta sake shiga jirgin Kano, ko da ta iso, anyi
sallah magriba, ana shirin yin isha’i, taso yau taje taga
yar gidan uban waye, Dr Umar ke sonta, kuma da me
tafita da shi, da har zai aureta, tabbas yarinyan sai ta
raina kanta, washe gari da had’a security dinta, wankan
kece raini tayi, ta kira kawarta, Zulaihat tace”Zuly ki
shirya kizo, zaki rakani, wani karamin unguwa, wai shi
Dakata. Cike da tsokana Zuly tace”kawas mai zaki dakata
acan, nan Sakeenat, ta sanar mata da komai, Zuly
tace”ban minti kad’an ina zuwa ko ku biyo ku d’auken.
Haka akayi, suka dauketa, cike da rashin mutunci a
fuskokinsu. Khadi ko wanka tayi, sabi da tasan yau
weekend, Ya Umar d’inta zaizo, tayi kyau kamar wata
amarya. Suna tsakar gida suna tad’i’ ita da Beebah
kasancewan, Gwaggo ta tafi gidan kawarta, shiyasa suka
sami freedom yau. Tun daga nesa suke jin, wi wi wi wi,
kukan jiniya alamar, wani babab yazo unguwan, har sai
da aka zo qofar gidansu, tukun kukan ya tsaya, cikin
mamaki suna jira suji maisu shigowa, Khadi tace”Beeba
kardai police ne suka zo gidannan?. To wayayi laifi?. Tana
wannan tunani ko taga masu bakaken kaya, suna
shigowa cikin gidan, nan take hanjin cikinta ya kad’a. Sai
da suka shigo, sun tsatsaya musu, wasu yan mata ne
biyu, su ka danno kai cikin gidan, kalo d’aya zaka musu
ka gane, sun san bariki, idonsu abud’e yake, ga fiskansu
ta sha man bleaching. Cikin isa da taunar chewing gum,
ta iso gaban su, sai da suka musu kalon, sama da kasa,
kafi ta juya, ta kare ma gidan kalo. A tare suka kwashe da
dariya, Zuly tace”kai yayan talakawa, a cikin ku waye
Khadi ko Khadija, shiru ba wanda ya bada amsa. Cikin
zafin rai suka sake magana, da kyar, Khadi tace” gani nice
Khadi. Sai da suka kaleta sama da kasa, sai da gaban
Sakeenat ya bmfad’i don sai yanzu ta lura da Khadi,
tabbas yarinyan ta had’u, dole Dr Umar ya makance a
sonta. Daurewa tayi, ta fara yi ma Khadi, “concrete
warning, duk randa naji ance kin kula Umar sai na muki
rashin mutunci, sai nasa an d’aureki, tabbas duk halin
naka-naka ne, mai rashin kunya ma wataran yana da
rana. Beebah da Khadi kasa magana sukayi, Rabee’at
dake bacci a d’aki, hayanayi ya fitar da ita, jin yanda,
aketa zaginsu, dana iyayensu ta karaso da gudu, ta kalisu
Sakeenat, ta sama da kasa, ta nuna su da yatsa,
tace”banza mai fiskan biri, kin wani sha bleaching, waye
ke?. Da har zakina zagin iyayena, nan Rabee’at tashiga
sauke musu, kwandon rashin kunya. Dr Umar yayi
wankan sa ya nufo, gidan su Khadi, tun da ya shigo
unguwan ya fara ganin motoci, har ya iso qofar gidansu
Khadi, nan yaga security, gidan gwamnati, da sauri ya
fito daga mota, ya kira wani body guard, tambayesa mai
ya faru, nan yake basa bayani, Sakeenat ne a ciki, da
sauri ya shiga gidan, dai-dai likacin da, Sakeena ta
harzuk’o zata mari Rabee’at da sauri Khadi, ta shiga
tsakanin su, sai jikayi tasss!!, karan saukan mari a fiskan
Khadi, kafin ta motsa, sai nasojin wasu karan tass!!
Tasss!! Tass!! Gar sau uku, Dr Umar ya mari Sakeenat. Ya
juya ya kali security d’in, da sauri suka bar cikin gidan.
Cikin fushi ya kali Sakeenat, Yace” kee waya baki izinin
zuwa gidan nan?. Duk randa na k’ara, ganin k’afarki sai
kinji ajikinki, ki kuma sani Khadeejat ta miki nisa, itace
uwar ‘YA’YA Na, ita nakeso, itace rayuwa, farinciki na, in
part rayuwata bazatayi dai-dai ba in ita, banza sakarya,
ko ana soyayyan dole ne?. Nace bana sonki bana sonki,
ba kuma zan soki ba. Cikin b’acin rai yazo, rik’o hannu
Khadi yace”My wife kiyi hak’uri dan Allah, hannu yasa, ya
share mata hawayenta. Ya rike hannuta, ya Sakeenat da
bakin ciki ya isheta, kaman ta shid’e a gurin. Yace”kee
Sakeenat! Kinga wannan ta fi minke komai, itace
mahad’an rayuwa ta, tafiki kamun kai, da nutsuwa, in
kin…… Da gudu ta bar cikin gidan tana kuka, wi-wi da
hawaye. Tabbas yau taja ma kanta raini agaban,
wayanda take takasu son ranta, yau Umar ya mata
haka?. Tana fita mota tashiga, Zuly ma ta biyota, rake
suka bar unguwan. 9:12] ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ PM, 9/14/2016]
Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-96~100. Tana fita suka
nufi gida, da gudu ta shige d’akinta, kuka ta rinka rusa
sosai, Hajiyarta ne ta shigo, tace”Zuly mai ya sami
k’awarki ne?. Zuly tafara bama labarin komai. Hajiya
tanisa tace”Zulaihat ba ki ba ma kawarki, shawara mai
kyau, tunda Umar baya sonta, sai ta hak’ura, ko ana son
dolene, kusani a ko da yaushe mace, ita ke jan kimarta,
nikam bazan goyi bayan k’arya ba. Kunutsu kusan
mekukeyi kun fa girma fa, ae ko irin shigan da kukeyi,
wazai so ku?. Inayi fad’a Abban su Sakeenah, yace nacika
takura masu, ga irinta nan, nima ina goyon bayan Umar,
matsawan ba canzawa kukayi ba. Kukan Sakeenat ya
karu, sai buga k’afa takeyi, tana cewa”Hajiya ni baki sona,
tunda bakison abunda nake so, “tsawa ta daka mata, ke
bana son aakarcin banza da wofi fa, sai da tamusu ba
dad’i, tukun ta bar d’akin. Dr Umar kuwa lallashin Khadi
yayitayi, Gwaggo ne ta shigo da sallamarta, tun daga
waje an fata rahoto, shiyasa take fara’a, tana ganin
Umar, tace” eehehe duniya yau taimin dad’i, in dai a
kanka ne, da Khadi naso da dukan tsiya suka mata, ka
wani shigo mana gida d’an iska, wato karuwanka ne suka
kasa hak’uri suka biyo ka nan?. Ran Umar in yayi dubu ya
baci, don ba abuda yatsana kaman a danganta shi da
mazinaci. Gwaggo ta zagesu tass shida Khadi, tayi d’aki,
Beebah ko sai basu hak’uri takeyi, Khadi kam kuka takeyi,
kafansa yaja jiki ba kwari ya bar gidan. Malam ya na
dawowa ya samu labari, yajima yana tunani daga
k’arshe, yace anya kuwa bazan dakatar, da Umar da
zuwa gidan nan ba?. Haka ya ta sake- sake, har ya tsayar
da amsa ma kansa. Bayan kwana biyu Umar yazo, tun a
waje suka gaisa da Malam, nan ya fara ba ma Malam
hak’uri, Malam yace”ba komai ya wuce, amma inaga ka
hak’ura da zuwa kawai, tunda daman ba wata alaka bace
a tsakanin ka da Khadeejat, cikin firgici ya d’ago, yanaso
yayi magana ya kasa, Malam yajima yana zargin Umar na
son Khadi, amma bai furta ba, shiyasa yayi hakan don ya
tabbatar. Don zan bada dama ga mai sonta ya turo
magabatan sa, ayi magar Aurenta kawai. Inaga hakan
shine zai zame mata hutu, Umar duk ya rud’e, yakasa
magana jiki ba kwari, yabar unguwan, gudu yakeyi Allah
ne ya kaisa gida lafiya, yana zuwa ya tarar da Mum a falo,
gunta ya nufa, ya kwantar da kansa, a kan cinyanta, sai
ga hawaye. Cikin sanyin murya yace”Mum zan rasata,
Mum ki taimaka min, pls dan Allah!. Cikin rashin fahimta
Mum tace”wacece zaka rasata?. Ajiyar zuciya ya sauke,
Yace”Mun Khadeejat ce, Mum tace”kamar yaya zaka
rasata?. Nan ya kwashe labari, ya fad’a ma Mum komai.
Tab lallae Sakeenat bata kyauta ba, amma ko da Dad
d’inaka bai dawo ba zamuyi waya dole asan abinyi. A yan
kwanakin nan duk Dr Umar ya rame, hakan yasa Mum,
ta sanar da Dad d’insu, ko da sukayi magana dashi,
yace”bazai samu daman dawuwa, a satin ba don haka zai
sa mataimakinsa, yaje da kansa, Mum tace” ni a’a ban
yarda ba, kasan Alhaji Bashir baya da sauki, akan yara ,
kawai inaga zamu nimi wani yaje, kuma kaga yanda
yakeson Sakeenat, komai zai iya yi. Dad yace”shikenan
duk yanda kukayi, Mum ta sanar da Umar komai yayi
murna, sanna yace”shi yanaga a tura Baba Liman, don
yana da halin dattaku. Haka ko akayi, Baba Liman yaje
neman auren Khadi ma Umar, basu wani samu Matsala
Baban Khadi ba ya amince. Nan suka zuba kayan mun
gani anaso, da kud’in gaisuwa dubu 2k, Malam yaki
karba yace sunyi yawa, amma Baba Liman ya dage sai da
ya karba. Da murna yashiga gida, a zuciyar shi, yana mai
cewa tabbas Khadijansa zata huta, don da alama Umar
d’an manyan mutanene, kuma zai riketa da AMANA. da
murna ya shiga gun Gwaggo, cikin zak’uwa takaleshi
“Malam lafiya naga sai farin ciki kakeyi?. Hmm kedai bari
kawai, ina cikin farin ciki, mik’omata su gidan goro da
catoons d’in minti yayi, tare da d’aura mata damin kud’i
akai, ido ta zaro su waje, “Malam wayan nan kud’in fa da
kayan fa?. Cikin murmushi yace”na Khadijat ne, kud’in
aurenta. Jakar uba! Ina bazai yuba, ina na Beeba ko
Rabee’atu?. To ba a gidan nan za’ayi wannan abun ba, sai
dai ko inda Beeba ne. Malam yayi dariya yace”Hauwa
kenan wai meysa ba kya boye hassadanki a fili, ae ni na
d’auka Khadi da Beeba da, Rabee’at, duk d’aya suke a
gunki?. Allah ya sauwake, nawa-nawa ne. Kuma wannan
auren bazai yuwuba, sai dai ko in zaka kawo na Beeba sai
a had’a. Shikam dariya ta basa, don suk tagama fita a
hayyacinta, ya d’ibi kayan ya kai d’akinsa. Khadi najinsu
amma duk ta damu da taji wa Malam zai had’ata aure da
shi?. Malam ne ya shigo d’akinta, ya zauna a kujera, cikin
nutsuwa ya kira sunanta, ta amsa, sai da yamata nasiha,
kamar yanda ya saba, tukun ya saida mata, Umar ya
kawo kayan ,yagani yana so, ina fatan kin amince kina
sosa?. Shiru tayi, daga yanayinta ya gane ta amince,
albarka ya samata ya fita. Washe gari Dr Umar yayi
wanka sa, yayi kyau sosai, sai da yabiya Sahad ya mata
shooping mai yawa, tukun ya nufo gidan, yaro yasamu
ya aika ta fito. Cikin nutsuwa take takawa, tana sanye da
hijab ash yamata kyau, hannu tasa a aljihu yana kare
mata kalo. Da sallama ta karaso bayan sun gaisa,
yace”gimbiya Khadeejatu, murmushi tayi yace kali nan,
tana d’ago fuska ya kashe mata ido d’aya, tare da d’aga
mata gira, duk sai taji kunya ya kamata. Haka sukayi
hiransu a zaure, sai dab zai tafi ya d’ebo mata, kayan
saya mata, godia ta masa har zata tafi yace”tsaya barin yi
surprising d’inki, murmushi tayi. Yace” pls close ur eye,
ba musu ta rufe, ” miko hannuki, bata komai ba ta mika
masa tana murmushi, wani zobe ya ciro sai kyali yakeyi,
ya sanya mata a hannu, nan take hannuta ya d’au kyalu
yana haskawa. Kiss ya kaimta a hannu, sai sukaji, la ha ila
ha illalahu, uhu jama’a da sauri Gwaggo ta damke su
duka. Ta kwalala jama’a ku kawon d’auki na kama yan
iska yau. Ihu take kamar mahaukaciya, Khadi ko duk
jikinta sai bari yakeyi, nan take hawaye ya fara zuba,
Umar ko don takaici kasa motsi yayi. ﻡﺩﺮﻛ ﻟﻠﻪﺍﺪﺒﻋ ﺓﺪﻴﺷﺭ
]9:12 PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA
BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-101~105. Cikin takaici ya fincike rigansa, kalon tsana
yake mata, da sauri Gwaggo ta sha gabansa, yau fa sai na
tona muku asiri. Wani mugun kalon da ya aika mata,
yasa Gwaggo bashi hanya, Khadi da gudu tabar gun.
Gwaggo ta ga kayan da Dr Umar ya kawo da rawar jiki ta
d’iba tayi cikin gida. Beeba na ganin haka tace”Gwaggo
mai yasa keke ma Addah Khadi haka?. Gwaggo cikin
zumud’i tace”kee bari kawai ae ido da ido na kamasu
suna iskanci, cil da cil ganin annabin tsohuwa. Beeba
tace”kai Gwaggo gaskiya Adda Khadi bazatayi haka ba,
zata taba zubar da mutuncinta ba, kuma na yarda da
tarbiyan da Malam ya bamu. Cikin b’acin rai Gwaggo
tace”oh to! to! Wato Malam shi ya kula da tarbiyan ku
bani ba?. Beeba shiru tayi ganin Gwaggo ta d’au da zafi.
Malam na dawowa Gwaggo da munafurci tazo ta fara
labartawa Malam, Malam ya kaleta sama da kasa
yace”tashi ki ban guri bana son gulma, a yanzu a kwai
wani abunda zaki fad’an na yarda, bacin nasan irin
tsanar da kikayi ma Khadija, yarinyan mai hankali, bataji
ba bata gani ba, kna gallaza mata, jiki ba kwari Gwaggo
ta bar d’akin. Dr Umar ko hankalisa kwance ke gudanar
da aiki, yanzu Dad d’insa kad’ai ake jira a kawo sadaki, sai
asaka ranar biki. Sakeenat kuwa sam Mum d’inta, taki
goya mata baya. Hankalinta duk ya tashi, can ta tuno
wata shawara, Zuly ta k’ira a waya. Tace” kqwara kina ina
ne yanzu?. Zuly tace”gani a hanyan zuwa gidan ku. “Ok
sai kin iso. Ta ajiye wayar tana zaman jiran zuwan Zuly.
Ko da Zuly tazo bayan ta gaisa da Hajiyar Sakeenat,
tashiga gun Sakeenat, bayan sun zauna Sakeena
tace”kawa nifa bazan share mari da Umar ya minba
gaskiya. Zuly tace”wani mataki zaki d’auka?. Sakeenat
tace”na bayar a sayo min dorina hud’u masu kyau,
zamuje unguwansu ba tare da securitys ba, in munga
yarinyan ko mu aika tazo sai mu cazata.Zuly tace”good
idea, haka zamuyi. Key motarta ta d’auka suka fita,nan
idi security ya kawo mata sak’onta, ta karba suka ja mota
sai Dakata. Sun dad’e a unguwan Khadi bata fito ba, can
da suka gaji yaro suka tura yaro ya kirata, Khadi ko
kamar bazata fito ba, amma can da yaron yasake
dawowa, ta d’au hijab d’inta tace”Beeba ana kira na a
waje barin duba ga wayata nan. Khadi na fitowa yaron
yace”gasu can a wancan motar. Khadi tana ta raba ido,
don Umar bai tab’a zuwa mata da irin motar ba.
Sakeenat ko suka rike bulala kowa ne bibiyi a hannusu,
sai da Khadi tazo kusa suka bud’e motar atare, suka
nufota da gudu dukanta suke tak’o’ina. Khadi ihu take
amma basu kyaleta ba, Beeba taji kamar muryan Khadi
da gudu ta lek’o ganin ana dukanta, koma gida “Gwaggo
dan Allah kizo, yaran ranan suna dukan Adda Khadi,
Gwaggo tace”ha da gaske Beeba tace”eh!. Duka suka fito
da gudu. Dukanta ko suke Gwaggo ta fara kukara mata,
kunyi min dai-dai. Rab Beeba ya b’aci sosai, ganin ba mai
ceton Khadi, gashi ba maza a gun, yasa ta tuna da Dr
Umar. Da sauri ta duba call history, ta kira number,
bugu biyi yad’aga, “hello hello Ya Umar kazo ga wasu na
ta dukan Adda Khadi, wanda suka zo ranana. Cikin figici
yace”what suwaye?. Kashe yawar yayi ya shiga mota
gudu yake kamar zai tashi sama. Sakeenat ko ganin sun
mata lilis, ga mutane sun soma taruwa da gudu suka
shiga mota, suka bar unguwan. Dai-dai zasufita a layi
motar Dr Umar yadanno kai ganin motar Sakeenat yasa
yasha gabanta, ganin zai tsaresu yasa taja motar da k’arfi
sai da ta buge masa glass d’in mota ta gudu. Da har zai
bita sai ya tuna kowani hali Khadi take kuma?. Sai ya fasa
ya kara gudu. Beeba ko ganin sun tafi dakyar wata
makwabciyar su, ta taimaka mata suka shiga da Khadi
gida. Karkuga fiskan Gwaggo fal farin ciki. Dr Umar na
zuwa yaga mutane, da gudu yayi salama ya shiga gidan,
Beeba ya fara karo da ita cikin damuwa ke tambayrta ina
Khadija?. Hawaye ya k’ara zubowa “tana d’aki a kwance.
Yana shiga yaga halin da take ransa ya b’aci sosai. Ya kira
beeba yace” ki had’a ruwan zafi don tayi wanka, waya ya
kira ba afi minti goma ba sai ga wasu ma’aikatan asibiti
da kaya, da kanta yamata treatment, ya mata allura nan
take bacci ya d’auketa. Yana fitowa yace”sistet Beebah
barinje gida na dawo. Na mata allura ta samu bacci, in ta
tashi ki kaimata ruwa ta watsa zataji dadi. Yana zuwa
gida yasanar da Mum d’insa komai, cikin bacin rai takira
His Excellency yana d’auka, tace” ranka shidad’e! Ya aiki?.
Cikin jin dad’i His Excellency ya amsa. Nan ta sanar masa
da komai, sai