Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
ko?gashi sai kinyi wanka ko?" ta ce,"eh." ya ce, "to tashi ki gani gari ya soma haske." zani taja ta daura daura ta nufi waje. da kallo tabi tsakar gidan,sannan ta dawo dakin Abba.bazan iya jan ruwa daga cikin rijiya ba. ya fito da sauri yaja mata sannan yakai mata bandakin,ya dawo yayi taja yana cika robobin ruwanta.sai da ya cika mata komai,sannan ya koma dakin. lokacin ta idar da sallah.ya dauko Alqur'ani mai girma ya zauna gabanta,ya ce "madam zamuyi karatu." ta dube shi tareda yatsina fuska,"wallahi bacci nakeji."ya ce,"daure muyi ko aya biyar ce," ta ce cikin shagwaba,"ni biyu." ya ce,"to bismillah,mu fara ta sama ko ta kasa?" ta ce,"ni kam ko ta ina, don haka sai ya soma mata daga bakara yana yi tana maimaitawa,aya biyu kusan minti ashirin ta ce, "zan kwanta." Ya aje kur'ani ya kmama hannunta,zo muje kicin mu gani me zamu nema.dan dole ta bishi zuwa kicin din.suka tsaya suna kallm kayan, tukwane ne zuwa kuloli da sauran tarkace,sai risho.ta dube shi cikin yanayin tsausaya ma kanta. tace, sun qi sai min gas cooker wai gidana ba flate ba ne bai dace da gas cooker ba. ita ko anti aisha an sai mata, kayan girkita ma duk yan chaina. tausayinta ya tsirga ma abba, ya jawo ta jikinshi ya rungume, kada ki damu bishira, duk abin da a ke sai ma yar gata xan sai miki, matsawar Allah ya hore min. ya janyo kwalin risho din ya ciro shi, ya hada yace xan siyo lagwani da kalanxir kenan ko? tace eh. ya miqe bari na dawo. tace to. ta nufi daki ta fada kan gadanta taci gaba da baccinta, shi kam gidansu ya nufa. tun daga nesa ya hango ahj babba xai shiga dakin waje, in da aka sauki baqi maxa, da alama ahjn ya hango shine shi yasa ya tsaya a bakin qofar. abba yana cike da fara'a ya rusuna xai gaida ahj shi kuma ya miqa masa hannu, dan haka sai abban ya kama suka yi musabaha. ahj yace Alhamdulillahi abbana, ka xama mutun, sai ayi ta hakuri da rayuwa. abba ya sunkuyar da kai yana tambayar kanshi ko manya suna ganewa ne in kayi auratayya da matanka? ahj ya katse shi da cewa, ya kwanan iyalin taka? tare suka shiga gun baqin, yana gaida su ya fito xuwa cikin gidan. yana leqawa dakin umma bata ciki, sai baqi. wata uwani dake matsayin abokiyan wasansu tace ango amarya ta koro ka ne? yace, keni karki dame ni, ina umma na? umma daga kicin tace, gani nan dana, xo qyale su uwani. gurinta ya nufa yana cewa,kina kicin ashe? tace, eh ina hada ma baqi abin kari ne. yace kalli yanda duk suka yi mana kaca kaca da gidan,wannan in sun tafi sai kin sha aikin tsaftace gidan.tace to yana iya?dole in gyara in sun tafi,ai arxiki ne ma xuwan nasu.abba yayi dan murmushi,sannanya canxa maganan da cewa,umma galan din kananxir muke so.tace,ga ma kananxir din can da ahj ya siyo jarka babba wai saboda biki.nace yaushe girkin biki xai yiwu da kananxir?shine na aje shi.sai kadau galan ka cika.yayi murmushi. Yace kai ahj akwai qoqari, musamman lkcn bikin nan.umma tayi yar dariya tare da cewa ko abinci fa baya iya tsayawa yaci,in na masa magana sai yace bijin da guda ina yaga ta cin abinci?abba ya girgixa kai,Allah ya rama muku da mafificin alkairin da kuke min,yasa ni ma in goya ku kamar yadda kuka goya ni.tace amin abba ai muma kana yi mana biyayya Allah yasa albarka a cikin auran, ya baka yaya masu binka kaima.yace amin. ya isa gida da kalanxir da lakwani ya samu ta koma bacci,dan haka ya hada ya dora ruwan xafi ya juye cikin plaks yaje ya ce ta shi mu karya. tayi juyi tare da cewa sai an jima,dama tun jiya sun shigo da biredi da kayan tea,shima sai ya sake kwanciya.ya mannata jikinshi suka koma bacci,goma da ishirin wayarsa ta tashe shi da ruri. ya daga ahj ne ke san ganinsa qarfe sha biyu.yace,ya sanme shi can kasuwa,ita ma ta tashi.nan suka karya sannan yayo wanka ya tafi kiran abba.kaya ne ya ba shi da kudin mota, yace ya kawo ma baqi yan xamfara da xasu koma gida yace ka tabbata ka dauki shatar mota har Zamfara abba ya ce to.sai da ya samu motar sannan yaje ya loda su suka daga,suna ta godiya.yau satinsu daya cir umman shi ke kai masu abinci,sannan ita kuma ya shigo da kayan marmari,sai kaji ko tsire da balango.abba ya shirya tsaf cikin qananan kaya xai tafi shago,yace madam yau fa abinci xaki yi mana,kin san abokaina su ahmad xasu xo muci abinci,in yaso daga nan sai mu wuce gaisuwan surukai gidanku a matsayin kina amarya wanda xaki soma girki yau, me xaki dafa mana? ta tashi xaune duk abin da ka ke so.dadi ya rufe shi,kowanne dai ki mana fatana shine ki birge abokaina.tace an gama. yace to bari inje xan turo yaran shago da abinci da cefane tace to, har ya tafi kuma ya dawo yace, xan biya in turo miki ummi,tace saidai in fati.yace,ummi tafi fati hanxarin aiki fa.tace eh nafi son fatin.kamar kullum sai da ya soma shiga gun ummarshi suka gaisa ta tambaye bishira, yace lafiyi lau.yaci gaba da cewa, yau nema xata soma girki,nace na turo mata ummi tace wai fati.umma tayi murmushi, sannantace kai ko yaushe xata so a tura mata ummi umma tace ina xata so a tura mata ummi? ita fa ba natsuwa gareta ba.abba yace, duk da haka tafi fati hanxarin aiki. umma tace,yanxu dai tura mata fatin.ka ko sai kayan abinci?yace ina fa,yanxu dai xan je bin wasu yan kudadena.tace ina xuwa baqar leda ta ciro a cikin adakan suturunta,taxo ta xauna sannan ta umurce shi da ya xauna.ta miqa mashi ledan tace,kwance ka gani.abba ya kwance ledan yana cewa menene a ciki ummana? kudin da yayi arba da su su suka bashi amsa yace,umma kudin nan fa?tace gudunmawa ce da jama'a sukayi ta bani,ka gansu nan.yanxu ka je ka siyi kayan abinci da su.abba yayi dariya, sannan ya kullesu ya miqa mata tare da cewa. Allah ya kyauta in amsan makh kudi, ki boye abinki. tace bana son muyi ta jan magana abba,kawai ka riqe kudin nan.muryan tsohuwa ne ta katse su,inda take cewa yanxu ke suwaiba hakan da ki ka yi adalci ne? yar gudunmuwar da ki ka samu kiba mai sunan malam duka, ummin fa? umma tace,to tsohuwa ummi me xatayi da kudi yanxun?abba yace kai wannan matan sa idan ki ya gota misali. Tace kai tafi can,ni rufemin baki,ke kuma suwaiba da kike cewan haka ba kya siyan mata yan tukwane da kwanonin nan na yayi maigida cika duba ne ku ke ce musu ko ci bari kallo? umma da abba suka sa dariya,tsohuwa ta sake jin haushi ta ce eh dole ku min dariya tunda kema kin xama shi,ai sai kiyi ta bashi naki ne ba nawa ba.umma tace yi haquri tsohuwa, gani nayi nan gaba muna sa ran abba shi ne xai ma ummi kayan dakin ma gaba daya tace,me kika ce?tab mai sunan mlm ne xai yi wa takwara wani abin axo a gani?shi da ya tsaneta.abba yace,in lkcn yaxo ke kya yi ma.ta tafa hannu cikin jin matuqan takaici ta ce,a gayawa mai xuciya ba mai dukiya ba,dan ko xan mata.ta nufi dakinta tana fada.umma tace,tashi abba,dauki kudin nan kaje. yace,wallah umma bari dai in dauka tunda kin matsa,amma ba xan amsa duka ba.ya qirga dubu uku,tace ka qara dan kusan dubu tara ne kudin,yace haka ma ya isa ki adana sauran.tace shi kenan. daga nan kasuwa ya wuce,ya sai kayan abinci.bayan ya amso wadansu kudaden shi ya hada ya kai mata. Sannan ya yi cefanen kayan miyan rigijif da nama ya aika yaran shago.dama kafin ya bar layin ya shiga gun umman bashir ya gaisheta.da tana ta bace bacen rai,sannan da yace umma ina fati? taje xata taya bishira aiki ne.sai ta washe baki,tan bandaki. yace to in ta fito ki tura mata ita.ya fice abinshi.biyu saura ya iyo gidan,tun a tsakar gidan yake jin qamshin shinkafa.ya isa kicin din tuni ta sauke shinkafa sai miya.yace ki xubama yaran shagona.ya dubi fati da ke yanka latas yace,in kin gama jamin ruwan wanka a rijiya.tace to.yana daki yana sa kaya yaji sallamar abokanshi.da sauri ya fito, suna ta yi masa tsiya ango kasha gyara, munxo dibar girki. abba ya bude musu falo,falan yaji jeran samiru abin yayi na xamanin, ga kujeru suka xauna suna yaba dukiyar da aka xuba cikin falon.ya fito yace bishira ta saka hijabi taje su gaisa.ya dauki abinci ya kai musu,sannan yasa fati takai filet da ruwan sha,shi kuma ya koma daki dan qarasa saka kaya.a xatam shi xai samu sunyi nisa da cin abincin amma sai me? dukkansu su shida kowanne filet din gabansa shaqe da abinci da nama,ga cokali a hannunsu,amma kowannansu juya abincin yake,yace a,a kuci mana kai muke jira ka bude da addua.tsaki yayi, yasan halin ahmad gun xolaya,dan haka sai yace muktar kuci abincinku,in kun bi ta ahmad xai ta bata mana lkc.cokali ya dauka shima ya xauna kusa da sunusi ya ce mu ci tare.take ya yatsina fuska tare da dawo da abincin ya xube shi kan ledar yana tande harshansa.dan danan gishirin da ya kama masa harshe ya ragu,cike da kunya ya dubi abokanan nasa suna ta dariyar da suke gimtse.da farko ya dubi sunusi,wai gishiri ka qara ne?sunusi ya ce,qila dai gishirin nan da bakin buhu ta xufa.muktar yace dubi gaban rigata ni da shegen kwandayi na tura nama a baki na tauna ya qwace saboda tsananin qarfi ya dawo ya fado min jiki.abba ya miqe cikin damuwa ya ce bari in maku wata miyar. ahmad yace a,a duk yunwa muka debo, inda yaji da mai a bamu muyi maneji. abba ya fito xuwa kicin.fati ce xaune da nata abincin tana ta juya cokalin. Abba yace ina bishiran?taje daki.ya daga murya ya kirata,ta amsa sannan taxo.ya dubeta fuska a daure ke dama ba ki iya abinci ba shi ne ki ka toxarta ni cikin abokaina?maimakon ki fada min? tace, to ai fati ce nace tayi miyar, danni bansan yadda a ke yi ba. haushi ya kama shi.ya dubi fati, ke dama baki iya komai ba kema?shashasha, gara ki koyi girki, dan duk macen da bata iya girki ba ba mace ba ce.ya daka mata tsawa, tashi kije gidan ummana ki ce ta baki abinci inji ni,ni da abokaina ne.sallamar yaron shagon shi ne ta katse shi,ya gaishe su sannan ya ce,naxo daukan abincin.ya dubi bishira,kina da yaji?tace,eh gashi can cikin kwalba da ummanka ta aiko min.ya ce,xuba ma yaran nan yaji da mai.ta ce ai akwai miyar.yace miyar ai ta xama guba.fati ta dauko abinci cikin kula xata fita,yace wannan fa?ba aikenki nayi ba? tace na ummanmu ne xan tafi mata da shi,ita ce ta ce duk abin da a ka dafa inxo mata da shi, shi ne yaya bishira ta xuba mata.abba baice qala ba, sai al-ajabin halin uwarshi ya ke yi. Bishira ta ce, kawo ita ma a kwashe miyar a xuba mata mai da yaji. ya daka ma fati tsawa,kai mata haka ni ki dauko min abinci gun ummana, minti uku na baki in kin wuce biyar xa ki sani.da gudu ta fita tana shiga gidansu ta aje bata tsaya yin surutu ba, ta fita da gudu.dan wake umma tayi,Allah yasa tayi da yawa,dan haka ta xuba musu ta dora ma fati ba tare da ta tambeyeta dalilin aikowarshi ba. sai dai a ranta tana ta saqe saqe tace,qila sun fasa girkin ne,ko kuma bai kai kayan abincin ba.koda fati ta kai musu dan waken nan suka baje suka kwashi dan wake suna santi.bishira tana jiyo shewarsu.abba na cewa ummana ta iya girki, bari in xo in sa muku waigi.muktar yace, ka kai amaryarka ta koyo girki.garzali yace,saboda irin wannan matsalan kafin in auri yarinya sai na tabbata ta iya girki.ahmad ya ce daya daga cikin illar auran yaqan masu kudin nan kenan, sangartattu ne basu iya komai ba tun da a gidajensu ba sasu a ke yi ba.ado yace wasu ba amma wasu suna saka yaransu. vels / ZURFIN CIKI book 1 part 7 ZURFIN CIKI book 1 part 7 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:59 Ado yace wasu ba, amma wasu suna saka yaransu,dan wani abokin wasanmu a kaduna ya auri yar wani attajiri, ba kaga girki ba kala kala.abba dai yana ta binsu da ido,har aka yi kiran sallar la'asar suka fita xuwa masallaci,daga can xasu wuce gaida surukai.bishirata dinga jin haushi,wai abokan abba sunxo har gidanta sunci mata xarafi.ummi ta fito dan xuwa gidan su amina,domin akwai wata xainab da wai ta musu gulma xasuje su.kirata har gida su dake ta.suna xuwa kuwa suka tsaya a waje suna tunanin yadda xa suyi ta fito,amina ta ce muje mu ce mun xo gunta ne, inta xo rakiyan mu mu duke ta mu gudu.haka kuwa suka yi,har ummarta tana ba su quli quli,ita ga me qawayen yan tana rako su tun daga soron gidan suka soma dukanta.sai da ummanta ta fito sannan suka gudu.ta ce yar tata kin san gidansu?xainab tace,na sani.ummar tata ta taso ta.su kuwa su ummi suna fitowa sai suka canxa hanya.amina tace dan allah muje gidan amaryan abbanku,naji ana ta labarin jeranta an ce kaya ne na uban gari. . Ummi ta ce,"duk da son kirgan samirana ban taba zuwa ba,saboda na kula ita ma yar rainin wayau ce kamar mijinta." Amina ta ce,"ke dai muje inga samirun da aka ce jajaye wai masu shida-shida" ummi ta ce,"mu fara bi ta shagonsa in yana nan to sai muje,in ko bayanan ba zani ba ya dake ni a banza." duk da cewa shagon da gidan tsakaninsu da nisa sai da sukaje suka duba sukaga yana nan,sannan suka je. gidan shiru sunata sallama,ummi ta nufi wata kofa ta tura,ta yafito Amina,"zoki gani nan ne falon."suka kirge samiru tsaf,sannan suka fito. ta window ummi ta leka nan ta hango bishira kan gado tana ta bacci,suka je kicin suka leka suka tura dayan dakin da ba kowa. nan ma sukaga ba komai ciki,an dai shimfida ledar kasa an sa manyan robobin ruwa. suka fito,ummi ta ce,"gaskiya matar nan banza ce,dubi yadda mukaje tana ta bacci." daga can suka sake zuwa gidan wata amaryar don kirga samira,sai kusan magariba sannan ta shiga.umma tana alwala ta ce,"to tunkiya uwar tumbele,tun yaushe ki ka bar gidannan sai yanzun kika waiwayo? sai kararki da jama'a keta kawo min?to na gaji da halinki,bari Alhaji ya dawo,wato tunda yanzu babu Abba a gida shi yasa iskancinki ke son yafi da." tsohuwa ta fito,"suwaiba da a ce ba a gabana kika haifi takwara ba,to da zance ba yarki ba ce,ba dama yarinya ta fita wasa?" umma ta ce,"ban hanata yin wasa ba,amma tayi shi a gida yawo ne bashi da dadi." tsohuwa ta ce,"a'a karki wani fada ma Alhaji,ta daina ko takwara?" ummi ta ce, eh.umma dan haushi ta shige daki ta barsu anan. lokacin da su Abba suka je gidan surukanshi an amshe su ba yabo ba fallasa,har ma da zasu tafi aka basu (uniforms)din bishira na boko wai ranar monday lallai ta tafi makaranta. sun zaga gidajan danginta dake kusa,sannan suka dawo gida.ya sameta tana fushi,shima shareta yayi don yaji haushi barnar abincin da tayi masa. dadin dadawa gidan nan yanda ya bar shi haka ya tadda shi.ita kanta batayi wanka ba ta kwanta tana ta uban bacci.fita yayi daga gidan,sai goman dare sannan ya shigo ya rufe gidan yaja ruwa yaje yayi wanka. sannan ya shiga dakin,tsayawa yayi yana kallon gadon mutsu-mutsu,sannan ga kaya nan duk a kai.ita kuma tana kwance rike da wani littafi tana karantawa. . Ya ce,"bishira wai me yasa bakya son kakkabe gadonki? ta dube shi nifa duk na gajine.tsaki yaja tare da cewa me kikayi da har kika gaji? bani guri ni in gyara shimfidar zan kwanta. shine ya kakkabe shimfidar sannan ya kwanta.duk da ya cike da bukata amma haushi ya hanashi kulata,sai ma baya da ya juya mata. Abba yanada tsafta sosai,haka nan ma'abocin son kamshi ne,duk da gyara gami da tsafta irin na ummanshi wata ran har cin gyaranta yake yi.sam baya so yaga ko ina rakwacan,yafi son komai ya ganshi a muhallinsa. dole kullum shi ke share gidan ya wanke ban daki,sannan da rana in ya dawo ya dora abinci. litinin duk makaranta suka koma daga dogon hutun kirismeti da suka samu.Abba ya koma kan aikinsa na bautar kasa.dan haka kusan tare suka fita da bishira ta wuce makaranta shima ya wuce wurin koyar war shi. . Ya rigata dawowa gidan,dan haka gajeren wando ya samu ya shiga tsabtace gidan.sannan ya dora dafa dukan taliya. uku da minti sha biyar ta shigo ya dubeta ina kika tsaya? ta ce,ba ko ina mufa makarantar mu biyu da rabi ake tashin mu.dan ma na samu direban gidanmu da yazo daukan kannena shine ya kawo ni. Abba y sake had'e rai,motar gidanku? Bn baki kud'in mota ba?Ta ce ka bani, ya ce to bn amnce ki sake shiga motar gidanku ba. Ta ce,"kan me ? ya harare ta ba tare d ya bata amsa ba,y nufi kicin tabi bayanshi d harara,sannan ta shige d'aki. A ganin Abba sam babu wani sauki da ya samu a auranshi,nashi ganin wahala ya d'ebo ma kanshi,kwanciyada ita ne kurum zai ce ya k'aru d shi acikin auren. Ya shiga gidansu d sallama,Umma ta amsa tana zaune kan sallaya bayan ta idar d sallar Isha'i. Ta ce,Abba ba a je an kwanta ba?ya zauna tare d d'an jan tsaki ta ce,A'a ha,jikin ko garin? Ya ce,Umma gaskiya ni abubuwa sun cud'e min,yarinyar nan tunda a kawo ta sam ban huta ba. Umma ta saki dariya "ka ji Abba d wani zance,dama ce maka a ka yi ana bauta d hutu? Aure shi bautane. Ya ce,Tsaya kiji fa ummata,kinga tun Asubahi in nayo Sallah zan hau sharar gidan,in shirya in je gurin d nike koyarwa. In dawo in dafa abnci,sannan in tafi shago kuma don takaici in na zo kwanciya ni zan kakka6e shimfid'a,ita bata iya komai ba ashe daga gidan nasu.Ni fa har ta soma sure min...... "Kai Abba! Umma ta katse shi d sauri, kada in kuma jin wannan furucin, kana hauka ne?yanzu d fada min menene matsalarka?in dai abnci ne ka bari zan diga aiko muku da shi. Ya ce umma ya ya ma za a yi haka?Tab ai ba zai yi wu ba,Ta dai zo ta koya sati d lahadi. Umma ta ce,To shi kenan,tazo din.kayi ta hkr Abba,nasan ka kai ma d zuciya,don Allah kada ka sake in ji wata fitina,ka lalla6a matarka kuyi zamnku lfy. Abba ya ce, To ko da ya sanar d Bishira cewa yana son taje gurin ummansa ta koyo girki,sai ko ta tuma ta ce ita ba zata je ba,dama dai gurin umman Bashir ce, Ya ce,shi kuma gurin ummansa ya turata,koda Asabar din tazo kin zuwa tayi,shi kuma sai ya shareta ta ya daina girkinki. Sai dai yaje gidn ummanshi yaci,hatta ranar litinin d suke d makaranta bai dafa abncin ba da ya dawo a galabaice da yunwa ta iso. Bashir ya ce, Ni har fata nake wata rana 'yar sa' in'sa ta hadu ku umma,wlh in mata shegen duka. Bishira ta ce,Ni dai bata isa ba, in ma ita ce ta turo shi dn in dinga zuwa gidnta to ba zanje ba. Haka suka yi ta zagin umma,daga bisani Bishira ta mike ta tafi dn kada ya dawo bata nan. Rashin iya girki ya kawowa masoyan 2 rashin jutuwa,wanda ko magana Abba bai cika yi mata ba. In ta zauna tayi ta kuka tana mmk,me ta mishi ya juya mata baya dan da nan? Yau kam abn ya yi kamar kaurace mata ya yi daga dakin baccinta, ya dauki filo ya tafi falo ya kwanta. Tayi ta kuka. Kasa jurewa tayi ta mike ta bishi,kwankwasakofar tayi kusan sau 3 ya ce "Waye?" cikin muryar kuka ta ce, Ni ce, Abba don Allah ka bude. Ya kunna wutar falon,sannan ya bude ta shigo ta zauna kusa d shi, ta ce, Abba wai mi na maka ne ka tsane ni? ka duba fa ko wata daya ban rufa ba,kasan dai yadda a ka yi auranmu yanzun in Mahaifana suka ji dariya za su Min. Amma ba komai sai biredi ta samu ta k'asuma,d ya tafi shago sai ta yafa mayafinta ta nufin gidn umman bashir. koda tai sallama umman tana kan turmi zaune suna ta ganzar rake ita d su bishir. umman Abba ce ta aiko musu da shi don rashin Adalci suna sha suna yi da ita. Suka shiga lale d zuwan Bishira, ta kalli bashir 'Ina fushi da kai, shine wato har yanzun ba ka zo ba ko? ya ce, Tab, sau 2 ina zuwa zan shiga gidan sai yaya Abba ya fito ya ce min kina bacci, na gane nufinshi baya son ina shiga masa gida,shi yasa na share.Bishira ta ce Um, wannan Yayan naka halinshi sai shi, yanzun ma fa fushi yake dani. Umma ta ce," A kan Me kuma? wai shi dole sai nazo gurin ummarshi na koyi girki, ai ko nace wlh ba ni zuwa. Umman bishir ta rafka salati. sannan tace 'Naga ta kaina ni Sahura,kai Allah ya isa tsakanina d Suwaiba. yanzun kuma ta gama d ni ke ta sako a gaba, so take ta shiga tsakaninku?' Abba ya kura mata ido, yasan abn d ta fada gaskiya ne ya ce "Me na miki to?" ta kalle shi,"Ba ka ma san abn d kayi min ba?Ta ga daya yanzun fa kaurace min kayi. Ya ce ba kya gyara gadonki,ni kuma na gaji d gyarawa. Ta saka tafin hannunta cikin nashi zo muje in gyara. Tausayinta ya ji,ya tashi ya bita yana kallonta duk kakarin d ta yi dn t gyara ta kasa. Sai dai shi ne ya gyara, Sannan ya janyo ta suka kwanta.Sam bata d gardama ko nuna gajiyawa a gurin ba shi hakkinshi na kwanciya. In zai zo sau nawa ba ya damunta,gurin da ta ke birge shi kenan. Amma ba wannan ba ne kadai namiji ke bukata,Musammanirin Abba dan kwalisa. Wata ranar Jumma'a bayan sun tashi daga mkrntr da ya ke koyarwa,ya ce da Ummi ta jira shi zaya aike ta gida. Kudin cefane ya bata ya ce taje ta sai kayan miya d nama ta kai gidanshi, Sannan ta tsaya tayi masa miyar tare d yi masa sakwara. . Shi kuma zai je ya fada ma umma, dn yana son d dunkunan wata amarya d yake son karasawa ummi ta zun6uri baki bayan ta amshi kudin ta wuce tana yankun-kunai, ya ce "Ke!" ta waigo "Zo nan . ta dawo, Ya kama mata kunne, Kin san kwana 2 bn ta6a lafiyarki ba ko?to kiyi abn d yau zaki gwammace ba ki zo duniya ba. ya rankwashe mata kai, Sannan ta wuce tayi ce fanan ta nufi gidn Matar gidn tana zaune d kayan mkrnt a jikinta,,Ummi ta mata Sannu harara ta zuba ma Ummi, Ummi ko ta rama,sannan ta ce "Mijinki ya ce in zo in yi mashi sakwara d miya. "Bishira ta ce, To sai ki koma gidn ubnki ki dauko tukunya d murhu b dai nawa ba, Ummi ta ce, To ni dai gaskiya d ubana ba. Bishira ta taso tana cewa Sai na wa? Ummi ta ce, Oho,amma ba nawa ba. Za ta kai mata duka ta goce ta ajiye mata kayan miyan ta ce " Gashi sai kiyi, kila ma baki iya girki ba ne. Taje ta fadawa umma, Umma ta ce "Ke ummi karya ki ke daga zuwa zata hauki d zagi sai ka ce Mahaukacciya? To kije ki fada wa Abban in ya so sai kuje tare ya fada mata amma fa kada ki ce masa ta zage ki, ki ce masa dai yazo ya fada mata zaki tayata. Ummi ko kyn mkrnt ba ta cire ba ta nufi gurinshi,yana tsaka dinki taje,Ummi sai ce masa tayi ta ce ba zam mata girki d tukunya ba. Ya ce Muje gidn ganin nan. "a kofar gida ta zauna tana jiranshi, sai d y shiga sannan ta bishi. Tana tsaye tsakar gida tana jin rigimar d suke yi.Bishira ta dage ita fa babu mai yi mata girki d kayan aiki, shi kuma ya ce tunda ba a koya miki girki ba a gidnku dole ne in sa kanwata ta mini. Ta ce ya turo Fati mana,wannan maran kunyar yarinyar mata tarbiyya ba za ta zo mata gida ta zage ta ba. Ran Abba ya 6aci, ya ce Ga ki nan mara tarbiya,ina fada kina fada ina matsayin mijinki.,Ummi tafi ki tarbiyya domin uwar d ta bata tarbiyya ita ta bani har ki ka amince ki ka aure Ni. Ta ce, Ta baka tarbiyya ko ta asirceka? Ta mallake ka har baka ganin Mahaifiyarka d gashi sai ita. Zancen ya soki Abba sosai Har ya daga hannu zai mareta sai kuma ya fasa,ya juya ya fita. Fatanshi Allah ya sa ummi bata ji ba,dn yasan tsaf sai ta fada ma Umma. Tana zaune gefen rijiya ya nufo ta,Ummi ina kayan Miyan? tana nuna masa su tare d cewa 'Gasu ya ce,Dauki ki kai ma ummana. Har ta kai bakin kofa ya sake cewa "Ummi!"ta tsaya ya zo ya kalleta Ummi kin ji me Bishira ta ce? Ummi ta dube shi cikin ido,,sannan ta kalli hanyar fita. Naji duk abnda ku ka ce,Ya lumshe ido "Ummi dn Allah ka da ki fad ma Umma. Ta tsura mashi ido,bata ta6a jin Abba ya yi mata magana cikin tattausar murya ba sai yau tunda ta taso. Ta ce, "To." Ta juya, yasa ke cewa Ummi. a waiwayo Don Allah kin ji? kai kurum ta daga sannan ta fita Tafe take tana Mmkn me yasa Abba baya son Umma taji zagin da Matarshi tayi Mata? Hakika d taso Sanar da Umma amma yanda ya yi 'yar Murya yana rokonta sai t jure,koda taje gida bata sanar d Umma ba. Cewa tayi kawai ya ce a ma barshi sai dai cikin ranta ta tsani Matar Yaya Abba fiye d tsanar d ta yi wa Abba. Shi kuwa Abba duk wata hulda tsakaninnshi d matarshi ya dakatar d ita,saboda yana son nuna mata matsayin umma a gurinshi. In ya fita tn Asubahi bacce ke kawo shi gidan,wanka ma cn gdn Umma yake yi sai ya ce mata Bishira tana mkrnt. A cikin rana t 3 hnklnta y gama tashi,taje t fadawa umman Bashir,ta aiko yaje tayi ta fadan gami d zazzagnshi,ya bata hkr y fita. Amma sam Bishira, bai canza mata ba. Sai ma sabon salon d ya dauko na yn kaura daga falon zuwa dayan dakin d babu kowa,dk kayn sawanshi y tattara y koma can. Abba yana d zcy g taurin kai,Umman Bashir ta ce,"Yanzun in kin samu saukinshi to uwar goyonshi ki ka fada mawa, km gwada ki gani za ki gane ta fini a gurinsa. Sannan ki g aikin asiri. . Shi kuma zai je ya fada ma umma, dn yana son d dunkunan wata amarya d yake son karasawa ummi

Chapter 5 of 7