Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
ta ce,"nima na ganshi?" karar bude kofarshi suka ji,ta ce,"leka in shine kice yayi bakuwa.shine kuwa,jin cewa ga bishira ya shigo da zumudi. Umma tace ka kaita ta gaida umman bashir. yace to, ta fito ta tafi kicin ta bar masu dakin,ashe ummi tana uwar daki tana jinsu.ya ce,yanxun fa daga na'ibawa na ke,ina ta xumudi in ganki. tace,na xaci ba xa kaxo ba ne,nace bari inxo ni,dan baxan iya kai dare batare da idanuna sunganka ba.ummi ta toshe bakinta saboda dariyan da yakesan kufce mata,yace sai inga kamar bakya sona.bishira tace haba abba, in kace haka bakamin adalci ba.yace to wadannan kulolinfa me kika kawo min?ta ce bude ka gani.ya bude ya gani yace kai, lalle ashe ni dan gatankine? tace sosai ma.ya marairece murya yace to bani abincin a baki.ummi daga cikin dakin tace, la'ilaha illallahu.abba ya miqe da sauri.kafin ya ankara ummi tayi fitan bindiga tsakar gida tana fadin la'ilaha illallahu,dama yaya abba dan is....umma ta gwabe mata baki,bayan ta fito daga dakin ahj babba.ummi wadda inta s6a magana ko ana hanata sai ta kai aya.ta dafe baki,tace maci gaba da fadin,umma to kinji abinda yake ce mata ne? umma ta jefeta da takalmi tare da cewa,wai baxa kiyi min shuru ba? ummi tace,to fa cemata yayi xai bata abinci a baki,kuma daman xan nuna maki wani kaset da yake kallo. Abba ya riqe kai tare da cewa ummi in na kamaki xaki sani, kaset din wa kikaga ina kallo? tace na yan is....da gudu ya bita ,yayin da umma ta jefa mata murfin kwano,amma duk haka ko da ta fita waje saida tace masa sai na nuna ma ahj kwalin kaset din.take ya tuna da kwalin kaset din daya boye,wanda ya qwace a hannun bashir,kaset din tsiraici ne wanda laanannu sukayi.abba cikin takaici yace,kai ummi! kai ummi!! kinsan allah in kina wasa dani xa karyaki a banxa.ta ce to ba a dakinka na gani ba?yayi qwafa,allah ya sani ya tsani ummi kamar ya shaqeta ta mutu.sai ya samu kanshi da qin komawa gidan,kunya da nauyin umma yake ji,yasan dai ba xata kama xancan ummi ba,amma yasan xuciya da xargi,qila xuciyanta ta xargi wani abu.bashir ya fito daga cikin gidan su abba yace,yauwa bashir shiga gidanmu kace bishira taxo. Bashir rai bace ya shiga,dan yana jin haushi ya amsar me kaset.ya shiga umma na qofar kicin xugun tana tunanin halin ummi.bashir yayi sallama umma ta amsa.yace,abba ne yace in kira bira ne ni yace ne?umma tace gatanan ciki,taxo bakin qofa ta kalli bishira kanta na qasa tana mamakin ummi.yarinyan sam bata ji.umma tace kixo yana kira awaje.cikin kunya ta fita, yace da bashir rakata gun ummanka su gaisa.bashir yayi fara,a antynace ke nan?abba yayi murmushi. bishira ta xauna gaban ummansu bashir suka gaisa. bashir yace,budurwan abba ce. sahura tace,yau kika taba xuwa nan unguwan? kanta na qasa tace, xuwana biyu kenan.ta kalli bashir tace kaji ko? amma shine ko a turo ta nan gidan.nina haifi abba amma an gaje min shi.tace yarinya duba nan.bishira ta dubeta,ta dafe qirjinta ni na haifi abba nine uwansa.matan gidan can mai gidana ya bada shi a gunta,da ubansa da maigidan dan wa da qani ne amma sun gaje shi.bani da ikon sashi ko hanashi amma sun mallakemin shi. da muryan tausayi take maganar. Bashir yace, umma indai ya aurota xamu samu sauqi.bishira tace kada ki damu, insha allah komai xai warware. tace, to yan nan na gode.fati ta shigo ta gaidata cikin nutsuwa, bishira tace wannan qanwansa ce? umma tace eh, ai su ga sakamakon mugunta nan sun haifi yar muguwa mara jin magan. bishira tace, kai yarinyar bata ji. fati ta ce abba ya ce kixo.sahura tace kinji ko? shifa ko nan gidan baya qaunan shigo wa.bishira ta miqe ta balle jaka ta ciro sabbim kudi yan ashirin ko irgawa bata yiba ta bata, tace kinsaya goro.sahura tace harda abin arxiki?to an gode.bashir yace antyna inane gidanku?tace karkasana gidan kwamishinan gona.bashir ya raxo ido, nako san gidan,lalle antyna ina qara gaisuwa.bishiratayi dariya.abba na tsaye suka fito,yace mata to ki tafi xanxo amjima. tace baka kaini dakinka ba.ya girgixa kai, bai dace ba wannan ba mutunci bane,sam bai kamace yar mutunci suna xuwa dakin samari ba. bishira tace danme? yace sharia bata amince ba, damin duk lkcn da mutum biyu suka kebe,musamman mace da namuji. Abba yace na ukun su shedan ne. irin wannan yana haifar da xinace xinace a bayan qasa.tace hakane ta tafi.abba ya rakata har mota, bashir kuma tamkar maroqi, sai fadi yake allah ya tsare antina ki sauka lfy.bayan tafiyanta abba bai iya shiga gidan ba tunaninshi daya kada umma ta xargeshi.dan haka ya nufa gidansu ahmad.ya ba ahmad lbrn abinda ya faru.dariya ahmad yayi tayi.yace kai amma wannan ummin taku yar dirama ce. abba yace cikin takaici yanxu kai har kaga abin dariya?yaja tsaki yace allah na tsana ummi, namata muguwan tsana. dubi wannan yarfin da tai mani. ahmad yace xata bari, wata ranama ko ance tayi watace sam batayi ba.abba yace taf wannan yarinyan dawuya in xata taba yin hankali, duk wanda ya aureta ya auran ma kanshi fitina.ahmad sai dry yakeyi. da magariba ya shiga gidan,cikin saa ya samu ummi tana cin abinci.nan take ya kama hannun ta har saida tayi yar qara, yace muje ki dauko min kwalin kaset din da kika dauka, Umma tace, Abba na soma tunanin yarinyar nan tan da aljanu da gaske. abba yace hakama alhaji qarami yace, amma fa anje babu kowa akanta. ya saki ummi bayan ya ranqwasheta. sannan ya ce, in kika sake yarda ki kaga wani abu a dakina kika dauka sai na balla ki. washegari abba ya tasa ummi ya nufi gurin masu ruqiyya, amma da aka mata babu kowa a kanta kamar yadda ya xata. ya dawo ya sanar da umma,umma tace na gode allah.halinta ne ita kuma irinta kenan? yace irinta kenan umma,baxata canxaba saidai muyi ta mata addua, soyayyan abba da bishira ta bunqara,har dangin abba sun san da batun,sahura duk tabaxa ma dangi.sanadiyyan maganan da tayi ma bushiran na cewa an rabata da daxta. wata rana bishiran tace masa xata xo gaida ummanshi,yace to cikin xumudi sai tace, umman su bashir fa nake nufi, ba ance ita ce mamanka ba? abba ya ce inji wa? inji ummanka. abba yace sam, ummana ba xata fada miki ba sai dai ko ita umman bashir din. tabbas itace ta haifeni, amma ba itace ummana ba.tace dan me? nan take ya hada rai. Abba yace mata ba matsalanki bane, so ban so ki saka kanki ciki. nan take ta yarda da batun umman bashir.ta a mince qwarai umman da abba ke kira umman shine muguwa ce.kuma itace ta raba abba da umman shi.dan haka saita tsiri xuwa gun umman bashir, tare da yi mata kyauta.shiyasa suka saba sosai.duk xuwan da bishira xatayi sahura saita kukkushe umman abba, tare da yi mata sheri. dan kawai bishira ta tsaneta,kuma bata xuwa gunta koda taxo anguwan. abba bai taba sanin haka ba,ita kuma umma bata taba fadan mai ba, dan ummi ta taba fada mata cewan budurwan abba tana xuwa gun umman bashir kuma bata xuwa gunki. umma tace nida umman bashir duk daya ne intaxo gunta tamkan taxo guna ne. sai kuma habaicin da take jiyowa ta katanga sahura nayi.har ya kai umman abba na ganewa in bishira taxo, domin inxata tafi xakaji umman bashir tana cewa,to na gode yar albarka bakya gajiya da abin arxiki,ai ko baki kawo min komai ba yancina da kika fara qwato min kin biya ni. kuma ina tabba tan maki inkinga abba bai aureki ba baya ry/ ZURFIN CIKI book 1 part 4 ZURFIN CIKI book 1 part 4 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:45 Wannan furucin ke sa bishira na qara shige ma sahura, duk wannan sha'anin da sukeyi abba bai sani ba. wanci tashi abba ya samu digree, sannan yaje kamp din shi a damaturu jihar yobe.sati biyu yayi sannan ya dawo. cikin sati biyun nan da baya nan ummi ta baxa iya shegenta son ran ta, umma ta qosa abba ya dawo saboda yanxune ta gane tsoran abba yake sa ummi tayi mata aiki da aike.dan tasan in ya sani baruwan shi da pushin tsohuwa,xai nakadetane, amma ahj da umma duk abinda ummi tayi daxaran xasu hukunta ta xata sa masu kuka tace dan de aci mata xarafine.shi yasa suka sakama ummi sunanta,sannan kuma suke dukanta a gabanta,imba hakaba maisa basuyima mai sunnan malan ba?dan dole suke qyaleta ,duk da ummi ta soma tasawa amma sam bata yi hankali ba. shekarun ummi sha uku tana js2 amma ko yaushe qara tirewa ummi keyi. addua kurun sukasa agaba,kuma sunsan allah xai amsa masu. Ranan da abba xai dawo ummi ta kama yima umma aiki da aike, dan kar a fadama abba. a ranan ne ummi taga wata alama da ta tsoratata cikin fitsarinta. a rudenta da hauka ta nufi gun umma tana cewa, umma na shiga uku na, fitsarin jini nake yi. umma tace, wane irin kuma fitsarin jini? ummi sai tsalle take tana fadin ta bani ta lalace. umma tace ke xonan. ta jawo ta xuwa cikin daki, tace ke yimin bayanin yadda kika ga abin. ummi ta cire xani xata cire siket. umma tace, ke dakata min bance ki nuna min ba, yaya kalanshi yace? ko da tayima umma bayani sai ta fahince girmane ya kama ta. dan haka sai ta kamo ta ta xaunar kusa da ita, tayi mata bayani game da abin data gani, sannan ta nuna mata hadarukan da take ciki a halin yanxu. tace ummi ki natsu kiyi hankali, kisani yanxu kinkai wani matsayi wanda xakiyi taka tsantsa da rayuwanki. hadari na farko shine wasan banxa da maxa, kece mara hankali indai kin sama abokin wasa ba ruwanki da maxane ko mata ke dai kiyi wasa, Umma tace kisani yanxu xaki iya daukan ciki, indai har kika bari wani namiji ya shiga harkanki. ummi tayi xullo tace umma ciki irin na bara'atun baito? umma tace, eh ummi tace wanda har suka yar da yaran aka xo aka kama su yan sanda? umma tace tabbas. ummi cikin fargaba tace to ni umma baxan yi ba. ta soma kuka, to a kaini asibiti a bani magani mana. umma tace duk bayanin dana maki baki fahinta ba? ai wannan kin dunga yinsa kenan har qarshan rayuwanki, ko kuma in kinkai wani mataki na tsufa. ummi tace, to shi kenan, yanxu kuma inna yi wasa da maxa sai in xama irin na bara'atu? umma tace qwarai kuwa. ummi tayi tagumi tana tuna yadda suke tsokanan bara'atu inta fito. suna cewa tayi cikin shege tayi cikin shege! ta dubi umma tace xan daina ma yan maxa magana. umma tace ki dinga maganarki da kowa, kidai kula da kanki, sannan duk sokanan da kikayi da xunubin da ki ka kwasa to fa ki sani an bude maki fayel. Umma tace xunubinki xaki samu,gashi bakya san sallar kan lkc, sannan ga karya axumi.ummi ta sake tsurewa ,tare da fadin, to ba tsohuwa tace min inna mutu baxa ayi min hisabi ba,wai ni yarinya ce wai makarantan annabi ibrahim xa a kaini.umma tace da kenan kafin ki soma kalar wannan fitsarin, yanxun kam in kin mutn xa a tambaye ki a cikin kabari, tambayoyi uku masu sauqi, masu wuya agun mara rabo.sannan xa a maki hisabi inkinyi mai kyau kiga mai kyau. tayi tagumi, umma ta manna mata tsumma a jikin pant. tace tashi kisa in kuma kinje gun haukan guje guje ya fado mutane sun gani shi kenan asirin ki ya tonu, kowa yasan kin girma. ummi dai ranan lafewa tayi kan kujera tanata tunani. tana kwance lkcn da ake hayaniyan dawowan abba kannanshi ne suka shigo mai da kayansa. qasa ya xauna a dakin umma, ya miqe qafa domin duk a gajiye yake. umma tayi ta dire mai abubuwan ci wanda tasan yanaso a gaban shi. sannan ta ba fati kudi ta sayo mai lemun kwalba, dariya yayi ya ce,ni dan gatane, shiyasa ina can ina tunaninki ummana, har nace inama ana tafiya da uwa da na tafi da ke.umma cikin jin dadi tace allah sarki abba, niko ina nan ina maka addua allaih ya baka abin da kaje nema,yace ummana kenan. ummi dai tana jinsu sam baima gantaba, sai can ya lura yace a,a kekuma lfy? umma tace bata dan jin dadine. yace tabdi,lallai kuwa ciwan nan yayi tsanani, ummi da ko a gadan asibiti take bata daina halinta? umma tace ai yanxuma nasan lafawa yayi ko ummi na? ummi dai kallansu take yi. abba yace allah ya yaye. suka ci gaba da firan su yana bata lbrn camp tare da nuna mata hotunan da suka dauka. yace dan ba kusa bane da kunje min kunyi kallo. ummi da xata bayi sai tafiya take wani iri tare da ware qafa. saboda rashin sabo. tsohuwa tace a,a takwara lfy? ummi tace, fitsarin jinin nake yi. umma ta fito da sauri tace ke ummi xo. tsohuwa ta saka salati, tare da cewa yarinnan nan badai faduwa kikayi ba. ummi tace nifa ban fadi ba hakanan ya xo min. umma tayi mata daquwa tace bayin kenan? tsohuwa tace ke suwaiba yarinyan nan faduwa tayi? da yake umma ta fahinci hausanta sai tace um,lkcn tane yaxo. tsohuwa ta saka salati tace, ni habiba yau naga abinda ya isheni? yarinyan yar shekaru nawane kwata kwata. lalle xamani, to sai ayi axaman aurad da ita. umma tace waxai kula ummi da sunan aure ni suwaiba? ki kalla haukan data keyi a gari. abba cikin daki yace umma wa tsohuwa take cema ayima aure? umma tace ummi itama cikin dariya. yace tabdi jam to wannan takwaran taki waxai kwasa, ga muni ga rashin hankali.daga bayi ummi tanata murguda mai baki tana cewa eh din. Tsohuwa kuwa masifa ta hau yi,"gaka nan mara mutunci a gabana kake zagin takwara?kai mai sunan malam ka kiyaye ni" shi dai ya fita ya nufi dakinsa don kintsawa,yana mamakin ummi ta zama babba. Koda umma bata fada mishi ba ya gane haka ne ta yadda tsohuwa tayi maganar. tsohuwa ta dubi umma ta ce,"ki na daure ma mai sunan malam gindi yana ci ma takwara kashi a hannu,alhalin yana zaune a inuwarta.nan fa gidan ubanta ne." umma ta bata rai matuka,ta ce "tsohuwa ni da Abba da ummi duk daya suke a gurina,don Allah kada ki kuma furta haka har Abba yaji. kai ni da za a ce in zaba tsakanin ummi da Abba,na rantse Abba zan dauka."bata jira abinda tsohuwa zata ce ba,tayi ciki abinta. tsohuwa ta gama yan mitocinta ta shiga daki. Kwana biu kamar gaske,ummi an nutsu, amma abinda ya takura mata na daukewa sai umminku ta ci gaba da gashi, sai ma abinda ya karu. Abba ya daga ido sama yana kallon wasu tsuntsaye suna ta shawagi a sama, zuciyar shi tana cikin matukar damuwa sakamakon sheshshekan kukan da bishira keyi, bata san cewa ya fita damuwa da tafiyarshi kaduna ba? in ma da don ta ita ne da sauki tunda gidansu da waya zai iya zuwa (telephone) na bakin titi ya kirata. damuwar shi umman shi. ta katse shi "yanxu Abba haka zan daina ganinka?" ya sake tausasa murya."haba bishira, ina kano ina garin kaduna?" ta ce, "tabdi, nifa dalilin kukana taron matan kaduna nake ji, an ce kwarjini garesu. kawai kaje ka sa samu wata ka manta da batuna." Yayi murmushi "bishira kenan, kada ki dauka son da nake miki mai rauni ne da har zan canza wata dake, ni dai ki min addu'a." ta ce,"sam ban yarda da wannan zancen ba, ni dai bari in kira antina mijinta zai iya taimaka maka a barka kano." kafin ya ce komai tayi ciki da gudu. yayi yar dariya. bishira tunda ya ce kaduna aka tura shi duk ta damu. Anti ta fito daga kicin, bishira ta ce, anti kizo inji Abba. anti ta dubeta, "in zo?" bishira ta kama hannunta "don Allah aunty taimako zaki mana, zo ki ji." 49- suka xauna sannan abba ya gaidaa anti cikin girmamawa.bishira ta dube shi ka fada mata.abba yace me?tace anti kinga fa kaduna aka tura shi,ni kuma wlh ba xan so yaje garin nan ba.anty ta sa dariya.to yanxu so kike yaqi xuwa ko so kike ya tafi dake? tace,ni so nake ki yima abban nasir bayani,nasan ba xai rasa sanin wani da ya sani ba.abba da anty suka sa dariya,yace kamar yaya?tace yayi magana a barshi anan suka sake tuntsira dariya.tayi fushi ta miqe fuuu ta nufi cikin falon gidan.anty tace bishira tana matuqan sanka,dan allah ka kula da ita.ya kalleta ya sunkuyad dakai,yace nima anti ina santa,kuma tuni nasa manya susan xancan,saboda in samu natsuwa,amma tace tana jin tsoron mamanta.anty tace eh to,dole taji tsoro dan ba dole bane hjynmu ta yarda,amma shi babanmu bashi da matsala.abba yace to ni dai xan tura a kowane lkc,dan ahjna yayi min magana tun kafin tafi ta camp. Din nan yake ta min zancan." Aunty ta ce,"to in kun tashi fa ba gurinshi za'a tura ba,gurin kaninshi ne dake jakara.amma kafin hakan sai an nemi izinin Alhajinmu din." Abba ya ce,"to ni ko wa zai shige min gaba gurin neman izinin?"aunty ta ce,"Abban nasir zan sanar dashi,insha Allahu har wannan din ma batun (service)din naka zan mishi bayani." cikin murna abba ya ce,"to na gode,Allah ya saka da alkairi"anty ta ce,"ba komai" ta mike "bari in turo ta don nasan tana can tana cika sai ka bata baki." yayi yar dariya tare da cewa"to". ta zauna tana kumbure-kumbureya ce"haba tawan har yanxu baki huce ba?" ta sake kauda kai gefe,ya ce"to shi kenan,yanzun dai na fasa barin kaduna." ta dube shi da sauri,"ka fasa barin kaduna fa ka ce?" yayi yar dariya"au na manta.kece duk kin ruda ni,cewa zanyi na fasa barin kano." ta share yar kwallarta,"to shikenan" ya ce,"naji dadin kiran anty da ki ka yi.ina ganin nan da yan kwanaki su Alhajinku zasu sanni,Allah yasa ace an bani ke." Wayyo dadi,ta tuntsure da dariya.abbana nawa,bana zaton cewa zaka kai ni murna a ranar."ya mike zan tafi "ta ce tun yanzun? to ka ce ina gaishe dasu umma." Ya ce,"umma bata cin mike,kullum sai ta ci in gaishe ki da kyau.amma ke kin ki zuwa gaida ta." ta ce,"kasan fa ni bana iya sakewa da ita,nafi sakewa gurin umman bashir." ya ce,"kunyarta ki ke ji?" ta dan tabe baki tare da daga kafada kila. ya ce,"ina mamakin yanda kika saba da umman bashir,alhalin ummana tafi saukin kai." ta ce,"ga wannan kanwar taka mara kunya." ya yi yar dariya sabida tuno abind ummi ta musu. ya ce a hankali,"zaki saba da halin ummi."ta dube shi,"tun ranar dana soma ganin ummi din nan fa ban taba jin cewa ina sonta ba." ranshi yadan sosu,har ma ya gimtse fuska,amma baice kala ba.lura tayi da canzawarsa.don haka sai ta ce"ka min afuwa in na bata maka." nan ma bai amsata ba.illa sai da safe. Tamkar Alhaji yasan yadda abba suka yi da antin bishira,da safe Abba yaje gaida shi ya ce,"babana zuwa yanzun ya kamata a ce mun shiga maganarku da yarinyar nan." Abba ya sunkuyar da kai tare da ce wa,"um,dama gidan antinta da naje dazu munyi zancen,yanzun dai su ce sai an nemi izinin shi baban nasu. ta ce,mijinta zai masa magana,in yaso sai kuji ranar da zaku je din." Alhaji ya ce,"to shikenan.Allah ya kai mu.yanzu yaushe zaka tafi kaduna?" kafin abba ya bashi amsa,ya ci gaba da cewa,ban so ba sam da wannan yin nisan da zaka yi damu Abba." Abba ya ce,"ina hasashen cewa za a barni nan kano da yardar Allah,bisa ga taimakon mijin yayar yarinyar da nake zuwa gurinta." Alhaji ya ce,"to Allah ya yarda,sannan in an fada maka lokacin da zamu gana da waliyyan nata sai ka sanar dani." Abba ya ce,"to." Alhaji ya ce,"ina son mu danyi bincike kan yarinyar amma mahaifinta sannanne ne,anata yabonshi." Abba ya ce,"to." Ranar juma'a da misalin karfe biyu da rabi Alhaji ibrahim (wato abban nasir,mijin anty farida),ya samu sirikinsa a gida. bayan sun gaisa ya tambayi yan jikokinshi sai Alhaji ibrahim ya ce,"suna lafiya.dama makasudin zuwan shi ne,akwai wani yaro da ke zuwa gurin bishira,yawancinan gidanmu suke zance. to gaskiya na yaba da hankalin yaron,sannan ya damu yana son ya turo iyayensa.to shi ne nace bari in nemar musu izini tukun." mahaifin bishira ya kalli surukinsa ya ce,"aisha ko bishira?" Abban nasir ya ce,bishira ce." ya gyara zama. "bishira ta gama sakandare ne?" Abban nasir ya ce,"ai Alhaji ba yana nufin ayi auren yanzun bane,a san dashi ne." Alhaji ya ce,"bana haka,ka sani sai dai tayi abu daya,in karatun karatun,in auren to auran. Ibrahim kasan wani abu daya? duk lokacin da kasa yarinya ta soma tsayawa da saurayi bayan tana karatu,musammanirin bishira irin wadda tasan tsarina amma ta danne ta turo min saurayi to gara ayi mata auren. Domin doguwan soyaryannan bata da ma'ana,qarshe sai wata shedana ta biyo baya,balantana bishira tana da rawan kai.ya matsa kusa da wayan tangaraho wadda aka jona ta ke amfani a daukacin gidan,ya dannan nanbobin sannan ya kira hjy.ta amsa daga sashanta,yace bishira na ciki? tace tananan, yace ki turo mani ita,tace to.gaban bishira ya badi,ganin mijin yarta a gidan dan tasan abinda ya kawo shi.ta xauna can gefe tace,gani dady,ta gaisa da abban nasir.mahaifinta yace nasan kinsan dalilin xuwan ibrahim ko? kanta a qasa tace,a'a. yace.yace to saurayin da ce xuwa gunki ne yake san ya turo magabatansa,kuma nasan kinsan da batun?sai dai inasan kisan abu daya bana san doguwan soyayya,da xara nagama buncike akan yaran wanda shari'a tace.inna gamsu,to fa aurad dake xanyi kije can ki qarasa karatun in kina so.ahj ibrahin yace yaran yace shi ba dole sai anyi yanxu ba.nufin shi a amince mashi.shi kuma xai jira har ta gama makarantanta. ahj ya katseshi ta hanyan daga mai hannu,ibrahin kaidai sheda ne bewan bana haka, kuma ba a haka dani ko?yace auran yata fa kakeyi,ka san tsarina.ibrahinyace na sani ahj. yace yauwa,ina nan ban canxa ba.yace yanxu abinda nake san ka dashi kafin na amince da xuwan iyayan shi.ya dubu bishira yace kinasan shi kin amince dashi? tace eh yace tashi ki tafi angama.kai kuma inasan kashiga unguwa uku ka binci komin labarin yaran da usilin shi.ahj ibrahin yace angama.yace naso ace sai ta gana karatu,dan sai anyi sa'a xata qarasa,anma hakan xaifimin akan doguwan soyayya kafin inxo inajin haushi.ibrahin ya miqe to ni xan tafi.ahj shima ya yunqura xai tashi sai waya ta kama ruri dan haka sukayi sallama anan. ummi ta shiga gida daga makaranta take,akuyan umman bashir tagani ta gani a gidansu tana masu barna a kicin da sauri ta koma ta saka sakatan gidan,sannan ta dawo.ta kama akuyan ta kaita bakin fanfo ta tara kanta sai kuka akuyan take tayi. Umman bashir ta jiyo daga gidanta,da sauri ta fita taxo tana buga gidan tana mashifa.yan baqin ciki,mahassada,yanka min akuyan xaku yi?san ummi bata ji ba, dan gidan ba kowa. umma taje sheka can gidansu,hta kuma tsohuwa taje gaisuwa n mutuwa nan kusa dasu.saida taga akuyan ta galabaita sannan ta janyo wata leda ta daura mata a bindi,sannan ta saketa.akuyan ta tashi da gudu tayi hanyan fita,tace shegiya gobe kixo ki bude mana abinci kici.taje ta bude qofar ta jiyo muryan umman bashir,dan haka sai ta cire sakatar sannan ta dan sanmata qofan akuya tayi waje da gudu.saboda ledar da ummi ta qulla mata,sai take ganin kamar binta ake,dan haka ta nausa cikin unguwa da gudu.umman bashir na ganin akuyarta tayi fitan bindiga,sai tabi tana cewa,ku taremin.ummi ta koma ciki tana dariya.ita kuma umman bashir daqar ta samu aka ruqo mata akuyan ta.aka kwance ledan taruqo ta xuwa gida.sai masifa take, tana isowa qofar gidan umma na RFIN CIKI book 1 part 5 ZURFIN CIKI book 1 part 5 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:54 Ita kuma umman bashir daqar ta samu aka ruqo mata akuyan ta.aka kwance ledan taruqo ta xuwa gida.sai masifa take, tana isowa qofar gidan umma na isa. tace yar baqin ciki kun kama min akuya kun jiqata xaku kashe min,ta ta allah ba takuba.umma tace akuya kuma wani iri?ni bana gidan dawowa ta kenan.ta ce kina nan muna fuka.umma sai ta shige gida,amma duk da haka sai da umman bashir ta bita har ciki tace sai ta doke mace akan akuyan ta.umma ta shige daki can qurya tasamu ummi a kwance,tace ke uwar yan daukan magana, ke ce kika jiqa mata akuya? umma tace cinye min abinci tayi.nan abba ya riske ta tana ta tsine tsine.yace meya faru?tace kai ja can ka bani guri,dan baka san darajata ba,banda an raina ni yaya xa'a kama min dabba a jiqa?in nai magana sai a maidani mahaukaciya ko haquri baxa a ban ba.abba yace to kiyi haquri in sha allah baxa a qara ba.tace baxan haqura ba,tunda inta mutu nike da asara.umma tafito tace to yanxu ya kike san ayi?ni dai bananan ummi ce da wannan tsiyan wai ta sameta ta cinye mata abinci. umma tace kinsan halin ummi kuma nima haquri nake da ita.tace to ni baxan iya haqurin ba.umma ta finciko ummi ta hanka da mata.ta gata na ki rama mata.ta juya cikin daki ta kama harko kinta.ba kunya ta kama ummi tana ta jibga.abba takaicin mahaifiyan shi ya cika mai xuciya,amma bashi da daman cewa ta bari.shin baxa tai tunani ba takama yar matan da tariqe mata danta riqon adalci da amana,tana duka haka? sai data gaji dan kan ta sannan ta fito.abba ma fita yayi cikin takaici,ummi kuwa kuwa tayi tayi har tsohuwa ta dawo,ta sameta xaune tana dirxan kuka. Dama taci karo da abba a waje tace mai sunan mlm har ka dawo xaka kuma fita?yace um.tace miskilin banxa saikace mai ciwon hakori,ta riska ummi tana kuka,tace umhum daman tunda naga ya fita yana ta maxurai nasan yaci xalinci.kai na gaji da halin mai sunan mlm.umma tace,ba ruwanshi.ummi taqara satin kuka ba umman bashir bace taxo tayi min duka.meki ka mata?wai din akuyan ta taxo ta cinyemin abinci,shine na jiqata da ruwa,shine taxo tamin duka kuma gashi banci komai ba, ko qala bata ceba,ta juya sai gidan umman bashir.ta sameta tana sinke kayan miya.tace ke sahura saboda bakida mutunci shine xakixo har gaban uwarta ki daka?sahura tace na daketa,kamme xata jiqa min akuya?tace wane shegen ne yace ki saki akuyan ki har taje taci mata abinci?to kashedin ki mara mutunci da baki san

Chapter 3 of 7