Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
girman nagaba ba.bashir ya fito yace a'a tsohuwa kidaina xagan mana uwa har cikin gidanmu.tace iye!kaxone ka nuna min rashin tarbinyan ka?nan har wata uwa gareka?nanfa sa in sa ya tsarke a tsakaninsu.ummata juyo su tarasa yadda xatayi,sai ga abba ya shigo.yauwa abba shiga gidan can ka lallaso min tsohuwa taje kasgedi ataba yar gwal dinta.ta dubi ummi tace duk aka yar marajin can ni naji dadin dukan da tayi mata,dan dukan algaki tayi.banda xalunci ya xata kama dabba ta jiqa? abba ya fita ba tare da yace qala ba. abba na shiga gidan bashir yana tsigale tsohuwa tankar xai kai mata duka,abba ya daga hannu ya wanka ma bashir mari,sannan yace tsohuwa saankace da xaka dunga mata wannan fadan.ya dubi umman bashir dan allah kiyi haquri.sannan yaja hannu tsohuwa,shi kuma bashir yana ta xagin abba yana cewa allah ya isa. umman bashir ta ce abba tir da hauhuwan ka tir!tir! kuma gab nake da in dagama ka nono.cak! abba ya tsaya kalaman mahaifiyan shi sun shi jeshi,a hankali ya saki hannun tsohuwa batare da tasan ya tsaya ba.dan sababin da takeyi yaja hankalinta.ya juyo har gabanta yace dan allah ki yafemin ki ya femin.ba tareda ya jira amsan ta ba ya fita. baiji muryan taba amma koda bata ya fe maiba jikinta yayi sanyi.da yamma bayan su ahj babba sun dawo kasuwa sai suka shiga dan gaida tsohuwa.nan ta saka masu kuka suka rude tare da fadin me aka mata?cikin kuka tace ni sahura xatai ma rashin mutun ci tare da danta bashir nan ta koro masu bayanin komai. Ahaji dai sukai ta bata haquri,ahj qarami yace shi kam dole ya cimata mutunci daga ita har bashir din.da suka fito ahji babba ya ce kada gaje ka mata da tsin hankali,nashihaxaka yi mata shi kuma bashir ya girmama yayansa.abba kuwa yana fita sai ya bar layin dan bacinrai,dakin ahmad yaje ya kwanta duk da cewan ahmad din bayanan.tunani yake tayi akan mahaifiyanshi,yadda ta runtse ido da alkairin da umma da ahj suke mata.ahj qarami cikin damuwa da takaici ya shiga gidansa,da bashir ya soma yin karo,nan take ya rufeshi da fada.sahura na ji ta taso cikin mashifa kada ya xagan mata da,dan ya nemi tare mata mutunci.ahj yace har wani mutunci ne dake wanda xai kare maki?to da kinada mutuncin kin tunkari mahaifiyata ki mata cin xarafi?tace har gidannan ta shigo saboda na daki yar gwal dinta,takan wannan wara mutuncin yarinyan xata xo ta xage ni?umma tace ma ahj babba ka fito gashi can fa ahj qarami rigima ta kaure tsakaninshi da umman bashir.da qyar ahj babba ya kashe wutan,abba da ya dawo yaji hayani ma mahaifanshi sai ya qara barin layin sai can sha daya na dare ya dawo ya kwanta,ranan ko abinci bai ci ba.da safe yana gaban umman shi yana fada mata kalaman da umman bashir ta masa jiya,una ta ce ashsha,kai banji dadin wannan kalaman na sahusa gare ka ba.saidai na gode daka nemi yafiyanta,sannan ka kiyaye duk abinda xaisa tayi maka munmunan furuci.dan bakinta dafine a gareka.kada kaga cewan baka yimata komai ba,to intayi ma mugun furuci sai kamaka.yace xan kula,tace yauwa abba.saka makon binci ke da mahaifin bishira yasa amishi iri daya da wanda sirikinshi ibrahim yayi mishi,ma'ana halayan kirki da mutuncin iyayanshi da shi kanshi yaran.duk dadai ance masa ba wasu masu hali bane?sai rufin asiri da suke da shi.wannan bai dameshi ba tunda dai ance mashi yaran yana neman na kanshi,sannan yana karatu. to tunda tana sanshi ba ruwan shi. ya kira wayan cikin gida ya kira hjy sai yaji sallamanta ta turo qofa.yace yauwa dama ke xan kira.ta dire tire mai dauke da kayan shayi akai,sannan ta xauna tana gaishe shi. Ya amsa sannan yace ina jin gobe masu neman auran bishira zasu je wajen yaya a jakara. Hajiya zainu ta gyara zama,"ka ce, bishira ko Aisha? ya ce bishira dai tayi yar dariya yaushe bishira tayi saurayin da har zai turo? ya ce,"a'a ba ki sani ba? ta ce,"na dai ji yanzun" ya ce to na basu izinin turawa tun jiya tunda tana sonshi babu ruwana da doguwar soyayyar nan kin sani Hajiya zainu ta hade rai,"amma kana sane da cewa ss2 zata je ko? ina laifin ta gama sakandare? Tace ,"gaskiya ranka ya dade ka bar batun auran bishira." ya dubeta,"kada ki damu kanki fa.don kin san ba zan canza ba" ta bata rai,to dan wanene? shima ya daure fuska dan babanshine.ta mike a fusace ta fita sai dakin su bishira. Lokacin suka farka daga baccin da suka koma bayan sallar asubahi.ta ce,"ke bishira,ke ce kika turo saurayinki gurin dadynku? wai yaushe ma kika yi saurayin? Aisha tayi zaraf tace, momy kin ma san wanene? hajiya zainu ta ce,"wanene?" Aisha ta ce telanmu Abba din nan." Hajiya zainu ta saka salati Abba tela? tela fa? Aisha ta ce,"tela kuwa" hajiya zainu ta isa gurin bishira ta rike mata kunne. "kece kika zabi auran tela? me ya ci shi kansa bare ya baki? zai iya da karatunki? wallahi tun wuri kije ki fada ma dadynku bakya sonshi." Bishira ta ce,"nifa shi nake so momy."hajiya zainu ta rufeta da duka. washe gari su Alhaji babba da abokinsa Alhaji sani,sai makocinsu malam ma'aru suka je nemawa Abba auran bishira a jakara gidan Alhaji musa wan mahaifin bishira. an amshesu hannu biyu,sunyi magana ta fahimta an basu,kuma sun karba.an yanka sadaki da dukiyar aure,sannan sunce suna so za'a hada da yarta. Su Alhaji suna ta godiya nan dai gemu da gemu suka rabu cikin mutumta juna. Hajiya zainu ta dauki karan tsana ta dora ma bishira,tunda tayi-tayi cewa ta janye batun auran Abba taki,ta ce to bazan miki komai ba.sannan in babu ta sameki kada ki ce kin sanni,in ki ka zo nan gidan da sunan neman taimako saina wulakanta ki. Duk bishira dai ta yarda,nan aka sa rana kusan wata shida. Abba ya iso kofar shagonsu da sauri don hangen da yayi gurin ya cika da jama'a,yana zuwa sai yaga ashe ummi ce tazo wucewa ta taba wani shagon fale-fale ta taba sai yayi mata shocking. shikenan ta tsaya tana jiran wa zai zo tasa shima ya taba,can sai ga wani yaro,tace kai ka iya karatu? yaron ya ce,"eh" ta ce karya kake in da gaske ne nuna mun acan.da gudu yaro yaje ya dangwala dan yatsa a kan A sai ko shocking ya debe shi ya jefa kwata. Ashe yayan yaron na kallonta sai ko ya biyota shine ta fallo da gudu ta fada shagon,shi kuma y ce sai ya duketa. Abba ya kalleta kallon tsana ya ce,"fito shegiya ya hankado ma yaron ita ya ce ka mata dukan tsiya yaron ya ce na hakura ta ci darajarka Abba ya ce don Allah ka duketa,don wannan bata da wani amfani daya wuce duka. yaron ya ce,ku dai ku ja mata kunne don kar taje tasa dan wani a matsala,ko ma ya rasa ransa,domin shocking zai yi kisa nan da nan. Abba ya ce dama zai kasheta ai da munyi murna.ummi ta kalleshi a ranta ta ce sai kazo ka kashe ni. Bayan kowa ya watse na nan yasata tsalle kwado. Ahmad abokin shi ya shigo shagon ya ganta tana ta tsallen kwado ya ce a'a Abba meye naka nasa mace irin wannan horon? Abba ya ce kasan Allah da ace yarinyar nan namiji ce da tuni na zuga an kaita gidan horon yara,kaini da in kayi kisan kai babu laifi da sai na ba yarinyar nan gamalan 20 tasha ta mutu. Ummi cikin kasa-kasa da murya ta ce nima da zaka mutu a dadina. Ahmad ya ce haba Abba ya kake irin wannan maganar? ya dubi ummi tashi ki tafi abinki.ummi taki tashi don tasan in don Abba ne sai ta tashi ya ce ta sake sabon lale don haka sai ta ci gaba da tsallan kwadonta. kuma bata nuna kasalarta domin ya ce sai taji jiki tukunna zai barta. wannan ya shigo ya ce Allah sarki ai mata hakuri wannan ya shigo ya ce don Allah a kyaleta.sai kurum ta saka kuka. da kyar Ahmad ya shawo kansa har ya ce ta tashi ta tafi.ya ce kuma inta yarda yazo gida ya samu tayi wani laifim shi da ita ne.daf da magrib yana sauri za shi masallaci sai ya ganta da dan tasi tana kasa shi kuma yana tuko motar a hankali yana ce mata an kusa gidan tana cewa eh. bata lura da Abba ba saida ya ce ke ina zaki? da sauri ta fice da gudu dan tasi yace ke yarinya zo nan. Abba ya matsa gurin shi ya ce malam lafiya? dan tasi ya ce yarinyar can ce ta taro ni tun daga bakin titi.wai an aikota ta kira dan tasi za'a dauki kaya zuwa wambai. nan na dibo fasinjan cikin gari ne ma sauke su tare da basu hakuri,to da mukazo hanya sai tace mun jaki ne za'a dauka nace jakin lafiya? ya ya za'a iya saka jaki a tasi? ta ce mun ita dai tashi aka ce mata ta taro,kuma nayi-nayi ta shigo motar taki. Abba ya ce,kayi hakuri karya takeyi,kanwata ce.wallahi bata ji. dan tasi cikin takaici gashi ya sauke fasinjanshi yajuya ya tafI. Abba ya nufi masallaci yana kyalkyata dariya.don shi lamarin ummi tsoro ma ya soma bashi jaki a tasi.kai shima dan tasin mashiririce ne.banda haka tunda ta furta jaki ai sai ya kama gabansa. yau bai ma bi ta kanta ba.don yana sauri yaje gurin masoyiyar sa bishira. Ummi ta shiga ajinsu na makaranta.kai tsaye ta nufi kujerarta wadda babu wata yarinyar data isa ta zauna duk ajin don suna matukar tsoron ummi. Tun daga lokacin data bigi kirji ta ce kujerarta ce,kowa ya sallama mata.malamai ma da suka gaji da rabon fada cewa suka yi a bar mata kujerar. duk makarantar babu wanda bai san ummi ba,malamai da dalibai saboda yawan fadanta da tsokana,har malamai bata bari ba a tsokana. sun fita fitsari ita da kawarta Amina,kafin su dawo malamin (social studies)ya shigo. Amina ta ce ummi dubi har malamin(social studies)din ya shigo. ummi ta ce,"ina ruwana,ko wanene ma ni shiga zanyi abuna."Amina ta ce,"in dai tica hassan ne gara mun juya don sai ya zane mu." ummi ta ce,"tab ai gara dukanshi da in tafi gida yanxun wannan mugun yaya Abban ya ci zalina." sam ummi bata kalli malamin ba,sanda take takai kujerarta,yayinda Amina ta labe ta kasa shigowa,kamar cikin mafarki taji muryarshi y ce,"ke daga ina ki ke?" ta dubi gurin da sauri,"yaya Abba ne ya hade rai,fuskar nan tashi babu annuri sai kace mai bada mugun labari. ta tsorata matuka,ya ce" zo nan kiyi 'kneel down'." jiki na bari ummi taje ta zube gaban allon.nan take yayi mata bulala guda goma masu kyau. take yan ajin suka shiga taitayinsu,don sunga ummi tsiga tana kuka irin wanda bata taba yinsa ba.don ko an duketa daurewa takeyi ta kuma shanye dukan. sannan sabon malami dan bautar kasa kamar yadda ya gabatar musu da Kansa daga zuwa yayi wannan duka.lalle dole su tsorata. ya ce,wuce ki zauna dakikiya mai idon jaki.wannan kalma ta daga hankalin ummi,domin taga yan ajin sun guntse dariya. ummi ta koma kamar ruwa ya cinyeta a cikin ajin duk tsokanarta ta tsiya,tsunguli wancan,shuri wancan,duk an samu saukinta. taimako daya Allah yayi mata,duk da halinta ta da kan daukar karatu.a zaton Abba bata iya komai ba,tun da basa shiri. don haka baya ko duba takardunta,islamiya ne yafi tsarata don tashi hikimar fannin addininta ne dole a matsa mata ta sani,boko kuma in bata yi ba ta yiwa kanta. duk rubutun da Abba yayi ummi yake ta dawowa ya ce ta karanta shi in ko ta mike sai ta karanta shi tsaf.in da ta dan samu saukin shi kenan. tun daga wannan ranar ummi alkadarinta ya soma karyewa gurin yan ajin,domin in suna fada shh da yazo ba bin ba'asi ita yake horawa. sannan in ta duki wani kafin ya shigo.daya shigo za'a fada mishi,don shine ya basu damar cewa duk wanda ta taba in yazo a fada mishi. duk da sun gano kanwar shi ce,gashi kuma wani lokaci tsokanarta suke tunda ya ce mata ummi mai idon jaki. sam bataji dadin zuwan Abba ba amma tasha alwashin itama sai ta mishi abinda zaiji bakin ciki kwatankwacin yadda taji. wata rana Abba ya siyo wayar sadarwa, lokacin tana farkon fitowa,yazo da ita gidan yana nuna ma su umma. nan akayi ta mishi murna umma ta ce,"kai Abba,kai da zancen aurenka ke karatowa ina kai ina siyan wannan abar har kusan dubu ashirin ka ce?" Yace umma amfani kai,kema xan sai miki ai tunda nan gaba kadan xata sakko.ahj babba dai yace xaya bani kudi in sayo musu shida ahj qarami.ummi na wanke wanke tana kallan su,wayar ta birgeta,irin wanda suke gani a cikin fina finan indiya, ta xata yan sanda ne kawai suke riqe irin wannan wayoyin.kai ko na bakin titin nan da take ganin mutane na bugawa birgeta yake yi,har ta tuna ranan da sukayi doguwan tafiya sukaje phone book.suna xuwa suka tarad ana layi,haka suka koma gyefe saida kowa ya gama sannan suka shiga sunata latsa latsan nanbobi suna karawa a kunne.saida wani mutun yaxo ya kore su,bayan ya dundungure masu kai. tayi murmushi, sannantace a ranta, allah yasa ya sai ma umman su,ita ko ta samu abin latsawa. daya nunama tsohuwa wayan tace shirman banxa,inba qarya ba da wannan xaka kira wani daga nesa?yace kn da a saudiyya kike xan kira ki.ta ja tsaki tayi daki shiko ya fice nana dariya.cikin satin ahj babba ya ba abba ya hada masu waya da layi,ahj babba yafi kowa murna da wayan, saboda shi mata fiyine. Wata safiya abba ya shiga wanka, umma na kicin tana soya masu dankalin hausa. zirif ta shige dakin abba tanata danna danne,da taji motsin bayi sai ta aje ta yi waje da gudu.saida ta tabbata ya shiga daki sai tayi xirif da shige gida.lkc da taxo kawo mai abin kari tasame shi yanata danna wayan,ya dubeta kinxo kin tabamin waya ko?da sauri tace a,a.yace munafuka,kece gashi kinyi min delete din duk numbers din dake cikin wayan, muguwa. tace to ni na shigone?ya harare ta yace fita, da ace ban rubuta lambobin na aje ba da yanxun kin min asara, muguwa kawai. ummi ta fita tana dariyan mugunta,domin in da abin da tafi so bai wuce taga bacin ran abba ba,kamar yadda tayi imani shima burinsa kenan. umma ta lakato man xafi tana shafama ahj a qafa tana murxawa.yace yauwa suwaiba kamar kinsan tun daxu yakemin kwankwatsa.daxidariya tace in dan tamu ne kariqa ware ranaku biyu a sati kana hutawa.yayi yar dariya,ina wani hutu da xanyi a gidan nan,matsalar ummina kadai ta ishe ni.umma tayi dariya,sannan tace ai ummi sai addu;a Ta canya xancan da cewa,af na manta niko yanxu auran abba yayi wata hudu nangaba?ya ce hudu ne da yan kwanaki.tace tofa!gashi ni uwarsa banida ko kobo,bari naxo na kama sana'a. ya tuntsure da dariya,sannan yace sai yanxu kika san da sana'a?itama dariyan tayi tace, in ba haka ba ahj ranar biki ko an kirani bana amsa ba.yace gashi kuma ke xaki mishi lefe.tace,to na shiga aljihunka,in yaso in an soma sana'a sai in biya ka.yasa hannu ya dago fuskanta yace sannu sarkin wayau.suka sa dariya.yace in san muje yaga gidajen nan na layin gabanmu,sai ya xaba guda daya a baiwa masu hayar notice sai a gyara shi.tace ya xabi na farkon layin dan yafi kxau.yace amma bashida girma.tace ya ishe shi daga shi sai matarsa fa?wanda ke cikin gidan ba mata bixu ne dashi ba?yace to xamuje dai ya xaba.sannan akoma kan lefe,tace allah ya saka da alkairi,allah ya kaimu.yace amin.wayanshi dake caji ta soma ruri,yace dauko min wayar can.ta miqe tana cewa har naji tsoro,na kasa sabawa da wayan nan.yace kuma gashi na kusa bar maki ita. tayi dariyan jin dadi,tana kallanshi.to ni wama xai dinga kirana?yace ni mana,bana iya yi miki wata magana in na kira abba na ce ya kawo maki,sai inga kamar yana tsaye,inko taki ce dana kira sai ki kebe daga jama'a muyi hiranmu. tayi dariya, daidai lkcn da kiran ya sake shigowa,ya daga. ahj buhari ne wanda ke sarin kaya gun shi daga kaduna.suka gaisa yace ahj ka kira kan in dauka ta katse.ahj buhari yace,dama ina san ince maka ne dan allah gobe xan shigo,kasa ahada min kayan nan da wuri.yace ba komai xa a hada.bayan sunyi sallama umma tace ni abin da yake bani al'ajabi da wayan nan, har kullum yanda xaka kira wani daga nisan duniya,kuma kuyi xance radau.ahj yace ci gaba kenan,wata rana ma sai kinga fasahan data ninka wannan.tace haka ne.abba yana xaune gaban ahj da safe bayan sun gaisai,sai ahj yace abba ina ganin da yamma ko xuwa dare kaje ka duba gidajen nan ka xabi guda,saboda a ba su notice dan a gyara didan.yace ahj ba sai naje ba duk wanda aka bani yayi.ahj yace ummanka tace ka xabi na farkon layin. cikin murmushi abba yace,ta shi kenan,nima shina xaba domin duk abinda umma ta xaba min shine xabina. tuni sahura ta fito da anko,xaqewanta da nuna isarta akan bikin sai kace ba dan fari ba. duk dangi sai surutunta ake yi,har danginta.umma kan cewa tayi anko ba shine damuwanta ba,dan haka sam bata bi ta kansu ba.abba a cikin ajin da yake koyarwa,ummi tana 2n gefe in da yayi mata maxauni a qasa,can in da ba knwa sakamakon ganowa da yayi in tana ajin ba a xaman lafiya,sannan babu me ikon xama a kujeranta.yace,in ma ya sake ganinta ko a wace kujera ce bas,xai ballata.rubutunda yayi take yi ranta bace.ya kalli gun datake yace ke!ta dago ta dube shi,yace xo nan.taje yace,amso min bulala acan ajin.kafin ta dawo sai da ta duke wata yarinya ta rugo.nan kuwa yarinyan ta biyo ta har aji,abba kam daya amshi bulalar saida ya xaneta tas.sam abba ya sama uni ido ko ta ina,ba makaranta ba, ba gida ba.dan haka ta matsu yayi aure ya bar gidan sannan ya gama service dan shi ya qara gaba. tabbas lkcn auran sa xata yi party.RFIN CIKI book 1 part 6 ZURFIN CIKI book 1 part 6 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:56 Tabbas lkcn auran sa xata yi party. Ummi party xatayi na murnan barin gidan shi.ahj ya ba umma wayarshi kamar yadda ya fada mata,ya ba abba ya suya mata layin mtn kamar yadda ya fada mata.ummi tafi kowa murna da wannan wayan,domin in umma ta aje takan dauka tayi ta latse latse,har dai ta iya abubuwa a wayan saboda ta iya karatu.kwanci tashi bikin abba ya rage saura yan kwanaki.duk gida biyun sai shirya shirye suke,mu samman gidan amare saboda yan mata biyu xasu auran.gidansu abba tuni ahj yasa an masu fantin gidan biyun,gidan ango kuwa ya sha gyara da fenti.ahj ya sabunta mishi qofofi da wundunan gidan, batun lefe kam dama tuni ya ke sayen xannuwanshi da kadan da kadan yana kawo ma umma tana adanawa.dan haka ahj karami yana kawo akwatuna umma ta fito da kayan dan tasan me xa a qaro.sannan ya yaba da hankalin abba.wannan ya nuna mishi cewa abba xai iya riqe gidanshi.lalle sana'an hannu tana da amfanh ga yayanmu a wannan xamanin namu.umma tai mashi lissafin sauran abubuwan da xannuwa da leshi xuwa shadda,tace ahj dan allah adubo mana masu tsada, Ahj yace suwaiba xan yi daidai qarfina,ba xan yi qarya ba dan sun san cewa dana talaka ne,kuma suka ba shi.umma tace,sai batun abin da xa a ci.yace suwaiba kenan,saunawa xakimin lissafin kayan abincin?na xata ma xakice kayan sawanku?umma tace suma a kawo mana da wuri dan mu dhnka da wuri,ba abba xan ba c saboda harkokin sun masa yawa.saura sati uku biki aka kai lefe.hjy xainu dai unguwa ma ta tafi a ranar,danginta na maigidan su ne suka amsa.sai yatsina suke tare da raina kayan da suka duba ma sai um da um suke cewa,wata tace to an gode fa,tunda taji ta gani mu menene namu?suka ba da tukuici, nan dai yan kai lefe suka dawo jiki babu qarfi.koda suka dawo suka sanar da umma sai tace ku qyale su.mu dai mun yi daidai qarfinmu.umman bashir kuwa da qannanta suka kai mata labari cewa,tayi ina ko xa suyi maraba da kaya?suwaiba ta karbe mishi kudi bada xuba kayan kirki ba,banga laifinsu ba.ummi kam sai dibar ma umma kayan abinci take a boye tana kaiwa gidan maman iman maqotansu ne,matan suna shiri da ummi, don ita rayuwar ummi dariya take bata,ta gwado shinkafa ta kawo,taliya,ta tsiyayo mai,ta ce sauran kayan miya da magi,har nama debowa zanyi. maman imam ta ce lallai kawayenki zasu sha party. ummi ta ce tab ai dole inyi party zan rabu da alakakai sarkin mugancin duniya. maman imam ta saka dariya,ummi ta kuma fita da gudu tana fadina na tuna inda gishiri da maggi suke. daga gidan amare anzo anga gidan amarya,nan ma sun tafi suna mita,fadi suke "bishira batayi sa'ar miji ba,wata ta ce ya aureta ne don kudin ubanta. koda suka je suka fada ma hajiya zainu fasalin gidan,daki uku ne duka falle dai dai sai kicin da bayi a tsakar gida. kanwar zainu ta ce,"kai gaskiya bishira bata yi dabara ba.hashimu dan gidan Alhaji mansur ya jima da sanar dani ya kamun bishira." hajiya zainu ta ce,"shi kadai?ko yayan abokan babansu nawa ke sonta?tunda taki tsayawa tayi karatu ta zabi ta auri tela,ba shi kenan ba?dubi gidan ubanta amma ta zabi zama a wani gida dakuna jere sai ka ce ajin primary."lol. suka ce,"kwarai kuwa kamar ajin makarantar gwamnati."ta ce,"shi kenan ai kaya dai asai mata daidai tsarin gidanta ba iri daya za a sai musu da Aisha ba." sun siyo sunje sun jera komai ras,yanzun kam sai daura aure ya rage,Abba da abokanansa walima kadai ya shirya. can gidan ne suke ta bukukuwansu irin ma masu hali.shi kam dai yasan yan'uwanta ba sonshi suke ba. sam be je gurin shagalinsu ba. ranar lahadi aka daura aure,misalin karfe goma na safe,unguwar kam ta cika da mutane da motoci. Abba da zugar abokananshi salisu yayan amare yayi musu jagora cikin gidan. sun gaisa da mutane sannan suka fito kowa fadi yake."kai amma angon bishira zankadede dashi tubarkalla."gashi Abba da iya daukar wanka,tsafta ce dashi ga son kamshi. KAI MATA IYAYEN GULMA. Can gidan ango ma anata shagalin cin abinci, jama'a dangi da makota sa gudunmawa suke ba umma tana a'a amma sai ace ta rike sabida ita mutum ce mai kyauta. umman bashir kam sai takaici take ji,kowa ya shigo sai dai ya ce mata."Allah ya sanya alkairi"kawai musamman ta shigo gidan don taga ko ana ba umman Abba ne. Nan fa na fita ta koma gida babu ko kunya tana ta masifa, fadi take "lallai suwaiba,gudunmawar auran dana duk ita ce ke karbewa? gaskiya naga sai dai amin Allah sanya alheri a wuce,to da sake,ni na haifi abuna ta bari sai ta tashi auran wannan figaggyar yar tata sannan ta amshi bikin." ta gama fadanta ta matsa,danginta suka soma yi da ita,suka ce wa zai baki wani abu ke da ko dan uwanki baki san ki bashi gudunmawa ba bare kyauta.tsinanni yar rowarki ce taja miki." kanwarta ta ce,"sahura sai dai ta ci na wani ba dai aci nata ba,dama irinsu sun cika son banza." ummi kam anci kwalliya an gayyato kawaye anata party a gidan maman iman,an kunna rediyo sai rawa suke yi,kafin a gama partyn an bige da fada da dambe,da kyar aka rabasu,nan taro ya watse. da misalin karfe takwas na dare,ango da abokanshi sun taso sallar isha'i Ahmad ya ce don Allah ango muje mu rakaka. ya ce,"Allah sai nayi wanka."mukhtara ya ce,"gidan cunkus da jama'a zakayi wanka?" Aminu ya ce,"don Allah malam kazo mu tafi,in ma kifi zaka zama a gidanka." Abba ya ce,"bari dai ku gani." a zaure suka ci karo da ummi,ya ce,"ke jeki ki wanke bayi ki kai mun ruwan wanka." ta sobare baki ta koma ciki tana fadin. na dai kusan hutawa, masifaff. ta wanke bayin sannan takai ruwan,yana shiga gidan dangi sukayo kanshi,ga ango! ga ango!! abokan wasa suka za na can zamfara suna tayi masa tsiya. dan gidan ummanshi yau dai za a kwana wani gidan ba na umman tashi ba.ya dai samu ya shige wanka. bayan ya fito ya bude dakinshi,ya shirya cikin wata shadda mirror,lokacin su ake yayi.ruwan kasa mai duhu. yasha hula mu hadu a banki ita ma kalar shaddar,ya feshe jikinshi da kalolin turaruka.ya shigo cikin gidan yaje kofar dakin umma. ya ce umman tana nan.aka ce mishi tana dakin Alhaji,yayi sallama a kofar falon Alhajin basu ji ba,suna ta hira tsit ya yi lokacin da yaji umman tana cewa Allah dai ya basu zaman lafiya da zuri'a tagari. Amma har ga Allah naso Abba ya auri..... ringing din wayar shi ce ta hana jin kowa ummanshi ta ce,sai dai muryar Alhajin ya ce wallahi suwaiba nima tsarina kenan. ahj yace ta allah ya riga ya shirya ba ita ce matarshi ba.ya daga wayar,ahmad ina xuwa mana. ba tare da yaji abinda ahmad din xai fada ba ya katse kiran,dan yaji haushi.yaso jin wacece iyayansa suka so ya aura?ya sake doka sallama,suka amsa.ya shiga ya xauna ya gaishesu,sannanya dubi umma.dama naxo miki sai da safe ne.ahj da umma suka yi yar dariya,umma tace to abba,yanxu dai ka girma,dan allah kyawawan halayenka dinnan kaci gaba da su.yace na gode.ahj ma yayi masa nasiha,daga nan ya fita jikinshi a sanyaye.da muwarsa me yasa umma bata sanar da shi yarinyar da taso mishi ba tuntuni?haka dai suka rankaya da abokanansa dan xuwa dakin amarya. gidan kam tun daga tsakar gida qamshi ke tashi.sun taradda qawayenta biyu,ita kam tana lullube kan gado.nan dai suka sayi baki akayi yan shaqiyanci tare da barkwanci,sannan qawaye suka yi mata sallama suka tafi,shima ya raka abokansa. ya dawo ya xauna bakin gadan yana dubanta, itama kallonshi take cike da so. sukayi ma juna murmushi,ya janyo ledan kaxan da suka shigo da ita. Ya warware takardar,y yago cinya ya mika mata a baki,"ci,nasan yau kin wuni da yunwa ko?" ta ce,"na koshi bana jin yunwa ma,ni kam duk yau banji yunwa ba." ya ce,"ni ma haka,dama yau bai da ce muci abinci ba."ta dube shi da alamar tambaya a kwayar idanunta.ya ware idanunshi. "taron da muka tara ko ina cike da jama'a." yayi yar dariya sannnan ta bude baki ya saka mata kazar.ta dan figa.haka yayi ta bata tare da zuba mata juice a kofi shima yana bata. ta ce,"to kaima ka ci." ya ce,nima ke zaki bani."ta sunkuyar da kai don kunya sannan ta dauka ita ma ta soma bashi. sai da suka yi dam.sannan ya ce mata kije kiyi alwala kizo muyi sallah. ta ce ai tun dazun nayi sallah.ya ce wannan ta ma'aurata ce,zamu gode wa Allah taare da rokonshi zuri'a tagari,da kuma fatan ya tsare mu daga sharrin shaidan dama duk abin ki. Ta fita ta dauro alwala,shi kuma ya kuskure baki.shine yaja su sallar,raka'a biu sannan sukayi ta addu'a,shi ne ma yake addu'ar ita kuma tana cewa amin. bayan sun idar da sallah idar da sallar,ya yi mata tambayoyi game da addini ta sanar da shi,yayi mata yan gyare-gyare sannan suka kwanta. sam Abba be daga kafa ba,a ranar ya angwance abin shi.don haka yayi kwanan farin ciki. da asubahi ya dawo masallaci,har lokacin amarya tana ta shirga bacci ya zauna bakin gadon yana kallonta.yasa hannunshi a gefen kumatunta. "sleeping beauty" tayi mika sannan ta bude ido,ya ce"a tashi ayi sallah

Chapter 4 of 7