Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Home / ZURFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 1 part 1 ZURFIN CIKI book 1 part 1 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 02:16 UUmmi tana tafe tana yan wakokinta, tareda gudu hade da tsalle. cinikin ummi ne gudu, sam bata tafiya a hankali.daga can gefe ta hango wata yarinya wadda bazata wuce sa'arta ba. tace,"yauwa,ga firdausin data tsokane ni" ta nufi wurinta ,tasha gabanta ta rike kugu. "fiddausi wa kike tsokana? fiddausi tace "ban tsokane ki ba fa".cikin tsoro tayi maganar .ummi ta shako mata wuya. ina jin lokacin da kika ce ummi tsiga.ban ce ba inji fiddausi .ummi ta hankada ta tare da cewa "Allah yaso ki." nikan garin da fiddausin tayi ya tarwatse a kasa tace "kin gani ko? wallahi sai kin biyani"ta soma kuka,ummi ta sheka da gudu,sai gida. tana ajiye man gyadan data siyo ta nufi ba daki don fitsari ya matse ta .umma dake zaune tana fadin. "da mutum!da mutum!!" saida ummi ta bude . Ganin yaya Abba tayi,da gudu ta juyo ta fada dakin umma,jiki na bari bayan tayi bol da dakakken yajin da umma ta daka zata soya mai don cin abincin rana. sai kuma ta tuna cewa bata tsira ba,don Abba tsaf zai binciko ta.ta fito da gudu ta nufi dakin tsohuwa. tsohuwar tana sallar azahar.ummi ta tsallake ta ta kutsa kasan gado.nan ma tayi ciki da furar da tsohuwar keson sha da zarar ta idar da sallah. Alhaji babba tasa ya aiko mata da furar daga kasuwa.don tasha da rana. Abba ya fito wanka ranshi a bace.dakin umma ya nufa yana fadin "ummi ke ummi zonan" Ya samu Umma tana tattara yajin da Ummi ta zubar, tana fada. Ya ce, "Umma ban san irin dukan da zan wa Ummi ba yau. Ta ce,"Abba ka mata dukan mutuwa, na gaji da halin Ummi. Yarinya sai ka ce 'yar fata? Ka dubata ta tafi dakin Tsohuwa, don ta san zata hana a dake ta." Ya ce,"Allah sai dai Tsohuwa ta yi ta fadanta, amma ba zan barta ba. Ya juya zai tafi, suka ji muryar Tsohuwa tana fadin. Ba zan yi fada ba, ka kashe ta ka ji mai sunan Malam, ba na son ka barta da rai. Ta dubi Umma" ke kuma Suwaiba dama kin san ba za ki daraja sunana ba ki ka sa a ka sa miki don kiji dadin ci min fuska?" Umma ta ce," Ba haka ba ne Tsohuwa, Ummi ba ta yo halinki ba. Ita fa rashin hankali ne da ita. Yayanta fa ke wanka ta zo ta leka shi, nan kuma tazo ta zubar min da barkono. Abba ya ce, "Umma don Allah kiyi shiru ki kyale Tsohuwar nan, ai ita ta 6ata Ummin, duk abn da yarinyar nan tayi sai ta hana a yi mata fada. Uhm duk fadanki yau sai na dake ta, ba sunan ki ba in ma kece,"Tsohuwa tasa kuka gami da salati. "Yanzu mai sunan Malam ni ka ke fadawa haka?" ya ce, "An fada miki." Umma ta ce, "kai Abba zan sa6a maka jeka." Ta juyo wurin Tsohuwa, Don Allah kiyi hakuri............... Maman Fiddausi ce tayi sallama tare da Fiddausin suka shigo. Ran Maman Fiddausin a 6ace, ta tsaya rike da gari a hannunta ta dubi Umma. Ta ce, Umman Abba dubi abn da Umminki tayi min don Allah, yarinyar nan tayo nika da kyar," tun safe sai yanzu na samu, amma ta zubar min." Abba ya ce, Kinga halinta ko?" Tsohuwa ta ce, "Wannan ba matar Bala ba ce?" Maman Fiddausi ta ce, "Ni ce." Ta ce," To kije kije ki nemi wanda ya zubar da garinki, Ummi ko fita ba tayi ba. Umma ta ce, " Ta fita Tsohuwa, na aike ta siyan mai." Tsohuwa ta ce," Tsokanarta a ka yi to. Umma ta amshe abin garin ta zuba musu, sannan ta ce, "Don Allah Tine kiyi hkr." Abba ya nufi daki. Sai da ya shirya tsaf, sannan ya dauki belt ya nufi cikin gida, dakin Tsohuwa ya shiga kai-tsaye kasan gado ya nufa. Ya jawo ta, ta soma kurma ihu. Daya ya lafta mata amma ta dane shi tare da cukwikuye belt din tana ihu. Tsohuwa ta iso tana dukanshi a baya, fadi take "Za ka kasheta ne? Jama"a kuyo dauki. Haushin hakan yasa shi damko kanta ya shiga zuba mata kola, ya sirmiyota ya shiga lafta da takalminshi, tunda ta hana belt din. Sai da ya mata tas, sannan ya fita ya bar su, Tsohuwa na kuka Ummi na kuka. , Sai da komai ya natsa ta leka ta jawo furarta don tasha, sai ta ganta a zube. Ta ce, A" a ke ki ka zubar min da fura?" Ummi ta ce, To ba shi ne janyo ni ba Yaa Abban. Tsohuwa ta ce, "Ai ko sai ya siyo min furata. Ta mike ta wuce Umma tana rabon abinci, ta nufi soro in da dakin Abba yake (Zaure) Ya fito yana rufe kofa, ta ce "Au za ka fita ba? To ka sawo min furata da ka zubar. Ko kallonta bai yi ba ya rufe kofarshi ya wuce. Ta ce mishi "Aikin bana, in ba siyo min ba ubanka ai ya dawo ko min dare ya sito min. Abba ya ce, Ku ku ka sani. Ra ce, kaima ka sani, dan jakar uba. Ta dawo ciki tana mitar ya cika bakin rai. Umma ta ce, "Ina Abban? Tsohuwa ta ce, "Ya tafi, in bai sai min furata ba ranshi zai 6aci yau a gidannan. Umma ta ce "Ni bai ma ci abinci ba ya fita, ke Ummi zo ki kira min shi, yunwa fa yake ji. Tsohuwa ta ce, "Ba za ta kira shi ba, ya dake ta sannan ta kira shi? Tunda bai barta taci da dadin rai ba, shi ma ba ya ci ba.,, Umma tayi shiry,sai haushin Ummi da take ji kamar ta shake ta ta mutu. Ummi tayi wanka ta zura kayan Mkrnt, tana saka sandal Umma ta ce, "Ina Ummi? Zo nan." Ummi ta tafi tana cewa a ranta. "ALLAH YASA DAKIN YAYA ABBA ZA TA AIKE NI, SAI NA RAMA DUKAN DA YA YI MIN JIYA, DON YANZUN DUK ME YA MIN SAI NA RAMA.........." Umma ta katse mata tunani da cewa,"dauki shayin Abba ki kai masa kada yayi latti,kai shayin ki dawo ki dauki dankalin,yau shi kadai ma nayiwa dankalin." Tace,"nifa?"umma tace "ke kina cin dumame Abba ko ba ya ci,dan haka dan wanda ya rage shi nayi wa." Ummi ta figi kayan tea din ta nufi dakin Abba tana tura baki.tare da sallama bata jira amsa ba,ta daga labule ta fada. Dabi'ar da yake mata fada akai kullum,ya gama saka singiletinshi kenan yana kokarin saka riga. Yace, "wai ke wace irin majanuniya ce?ban ce miki in kinyi sallama sallama sai na amsa za ki shigo ba? sai kawai ta saki tiren,ruwan zafin ya zube masa a kafa,dankalin ya watse kan rigar da zai saka. tayo waje da gudu,sai dakin tsohuwa.ya fito da sauri yana cewa,"umma ta kona ni! ta kona ni!!" da sauri umma ta fito daga dakin Alhaji babba,shima Alhajin na biye da ita yana fadin "wacece ta kona ka?" Yace "ummi ce! ummi ce!!."nan take Alhaji babba ya rike kafar yana tofa mishi addu'a. Umma ta debo kullun kamu ta zuba mishi,amma duk da haka sai da yan yatsun kafarsa suka kumbura. tsohuwa ta fito daga daki tana fadin,"kai ummi bata ji? wai ni meyasa aka sa mata sunana?" Abba ya kalli tsohuwa cikin takaici yace,"duk ba ke kike daure mata gindi ba?" Umma ta shiga dakin tsohuwa ta janye kayan da tsohuwa ta jera don kada aga ummi,ta janyota tun daga dakin take kwallo da ummi har waje. Alhaji ma yau har dashi aka zane ummi,tsohuwa dai sai yan mitoci take yi,wai yanxu haka ma bata sani bane. Abba dai ranar dai bai je makaranta ba,haka nan da yamma sai da ya saka ummi a dakinshi ya bata gwale-gwale sannan ya zane ta. misalin hudu da rabi na yamma,Ahmad abokin Abba yayi sallama a kofar gidan,Abba ya amsa ya fito. Suna zaune kan dakalin kofar gidan suna hira,sai ga ummi ta yanko da gudu tana waiwayen baya. Ya ce,"zo nan."tazo yace,"kinyo tsokanar fada ko?" tace,"a'a.yace in har tsokana ki kayo zaki sani shegiya mummuna kazama. Ta murguda baki,yasa takalmi ya jefeta,ta shige gida sai ko ga wani yaro jiki duk kwata yayyanshi na biye dashi. ya tambayesu,suka ce "ummi ce ta jefa shi kwata"ya taso yaron har cikin gida ya kamota dakin tsohuwa ya tsareta ta wanke ma yaron jiki,ta kuma wanke kayan. sannan ya zuzzuba mata kola a kai.tsohuwa tana ta yiwa yaran fada,wai ita ma su daina tsokanarta Umma ko lekowa bata yi ba,ya fito ya samu Ahmad yana cewa "kayi hakuri na barka kai kadai." Ahmad yace,"ba komai" sai Abba ya zauna sannan Ahmad ya dube shi. Abba wannan kanwar taka kuwa bata da Aljanu? Abba yace,"ba kowa akanta,sai iskanci." Ahmad yace."a'a,kai dai ku kaita ayi mata rukiyya." Abba yayi dariya,sannan yace kasan Allah ba kowa akan ummi,saboda Alhaji karami ya taba yin wannan tunanin. ya dauke ta yakai ta rukiya bata da komai."Ahmad yace tabdi!,gaskiya in ta isa aure duk wanda ya aureta akwai aiki babba a tare dashi. Abba ya ce,"wane mahaukaci ne ma zaya dibar ma kansa ummi?"Ahmad ya ce,"sai ai muku hadin ggida..." ya kaima Ahmad naushi a gefen ciki,Ahmad ya kauce yana masa dariya. Abba ya ce,"ka cuce ni,ace in auri ummi ai sai na hada kayana na bar garin nan. nan. Ahmad ya s heke da dariya har da rike ciki.sannan ya ce,"don me? Abba ya ce,"to wannan yarinyar ba sai ta hada maka gobara gida ba?gata kazama ga muni." Ahmad ya ce,"kama dai kuke yi." Abba ya bata rai,"Ahmad bana so.in har da gaske ina kamada ummi ba sai na koma ciki an sake haifana ba. Don Allah ni tashi ma ka tafi,don wallahi da don kai bane kake fada min haka da sai munyi rigima,na tsani ummi,bana sonta sam! Zaune suke a kofar gidan Alhaji babba kan katuwar tabarma,sun jere abinci suna ci. kullum Alhaji babba da Alhaji karami nan suke zama tamkar tagwaye,suna matukar kama. mafi yawancin lokuta ma kaya iri daya suke sakawa,domin Alhaji babba duk kayan daya saya tare yake sai musu. haka nan hula ko takalmi,haka nan matansu baya bambantawa.shima Alhaji karami duk da bai kai samun babba ba yana koyi dashi. Alhaji babba ya kalli karami yace,"Aminu ya zancen makarantar bashir?" Alhaji karami ya dubi wansa ya ce,"Alhaji bashi fa ya fadi jarabawa,jiya na tsare shi da maganar sakamakon jarabawarshi yace bai duba ba,saida yaji nace zan hada shi da Abba suje sannan yace min yaje wai duk ya fadi. Alhaji babba yace,"Ash sha! sai ya maimata shekara kenan?"Alhaji karami ya ce,"to in ma ba zai maimaita ba Alhaji shi ya sani,ba sahura ta bata su ba? shi Abba ai ba haka yayi ba,ka dubi fa yadda yaki aikin kanikancin nan,uwarshi ta zuga shi wai yayi karatu kadai yayi aikin gwamnati. kullum haka sahura take kitsa ma yaran."Alhaji babba yayi yar dariyar takaici,sannan yace"in banda abin sahura yadda kasan nan tamu ta zama waye zaici alwashin aikin gwamnati? ina ce masu digree ne ke yawo ba aiki?" "har masu masters." inji Alhaji karami.ya tashi zaune daga kishingidar da yayi,yace dubi misalin dan abokinnan naka Alhaji buhari." Alhaji babba ya ce,"kwarai kuwa,mas'ud ba.yanxu ma fa kasuwa yake zuwa,sai yanxun yake koyon kasuwancin." Alhaji karami ya ce,"to daya dora shi a kasuwar fa tun farko?shi yasa na fada ma sahura ta bar yara su hada da sana'ar hannu. Donni dai yaro kamar bashir yanxun ba zan dauki kudina in ba shi ba."Alhaji babba yace,"shi yasa kulum nake kara son Abba,yaron nan da kanshi yace min in kai shi shagon dinki. Har naki suwaiba ta ce,"Alhaji ka kai shi in ya iya sana'ar hannu ko bai samu aikin gwamnati ba zai rike kanshi da sana'ar nan." Alhaji karami ya ce,"to ai kasan ita suwaiba tasan abinda take yi.amma sahura sai addu'a." Sallamar Abba ce ta katse su,ya zauna can gefe sannan ya gaishe su,duk suka amsa tare da tara hankulasu gurinshi. Ya mika ma Alhaji babba kullin takarda tare da cewa "Alhaji gashi maganin (ulser)ne" Alhaji babba ya amsa ya ce,"Abba sarkin amsa magani, a gurin wa ka samo wannan kuma?" ya ce,"Ahmad abokina na raka ya amso ma babanshi,shine nace bari in amso muku" yace to Allah ya saka da alkairi."Alhajikarami yace"dame ake sha?" Abba ya ce,"da madara peak." suka ce"to" daya mike zai shiga gida Alhaji babba yace ya shige da kwanikan abincin. yau kam Abba bacci yake ji da wuri,don haka ya baro shagon dinkinsu wanda ya kan kai goman dare a ciki ya nufo gida. Ya bude dakinshi ya shiga ya cire riga sai singileti da gajeren wando na jeans.ya nufi ciki don ya kama ruwa ya kuma yi wa ummanshi sallama. tsakar gida ya sameta zaune ta zabga tagumi,inda abinda Abba ya tsana shine,yaga ummanshi cikin damuwa. da sauri ya isa wurinta,"umma lafiya?"ta dube shi "ina fa lafiya,ummi ce tunda tayi sallar isha'i ta fice kusan awa guda zance jiya ka mata dukan fita wasan dare?" Abba yace "to wai me za'a yi wa ummi ne ta zama irin sauran yara?" umma tace,"addu'a ce Abba,kuma muna yi kullum." ya juya cikin bacin rai,layin su Amina kawarta ya nufa,don bata wuce can.duk da cewa Amina bata kaita rashin ji ba. can din kuwa ya sameta,ta tara zugan yayan layi sai tsokanar fada suke yi,ita ce shugaba. wata falwaya Abba ya samu ya jingina yana kallonsu,don yana iya tunkararta su diba da gudu. shi kam ba za ya iya guje-gujen nan ba,duk wanda yazo wucewa sai sun tsokane shi,wani su jefe shi,wani kasa zasu watsa masa su gudu wani kuma rigarsa zasu ja. c can wani shida budurwarsa sun zo wucewa ta fizge ledar hannunsu ta watsar,sannan suka ruga da gudu. tayo gurin da Abba ke tsaye bata zaci da mutum a gurin ba,sai dai taji anyi caraf da ita.sai da Abba ya zabga mata koso a tsakiyar kai har tayi fitsarin wuya,sannan ya tasata har gurin mutumin data yaga ma ledar. suna tsugunne suna tsintar lemunsu da ayaba ya ce,"malam ga wadda ta yaga muku leda." da zafin nama mutumin ya mike,Abba ya ce,"gata"mutumin ya shakota yace yau sai naga ubanki." Abba ya ce,"ko kara ka kai gidansu nine zan hukuntata,don haka gata na kawo maka kanwata ce kuma naga lokacin data tsokaneka." jikin mutumin yayi sanyi ya ce,"na gode bawan Allah,taje taci albarkacinka." Abba yace "daka nade ta." mutumin yace,"ba komai,ke kuma ki canza hali ke mace ce." Abba yace nagode" sannan ya tasa ta zuwa gida. Bokiti ya cika da ruwa ya dora mata,,umma rasa bakin magana tayi daya sanar da ita tsokanar daya tarar da ummi suna yi. Daga karshe ta ce,"Allah ya shiryaki,abind ya sameki kada ya sami sauran dangi. Alhaji kuwa daya sameta dauke da bokitin tana kuka tana fadin "yaya Abba na tuba,bazan sake ba." ya ce,"uwata bakya ji ne fatan Allah yashirye ki."ya nufi dakinshi.tsohuwa takaicin Abba ne ya hanata fitowa tayi magana. nata ganin,ummi bata wuce fita tayi wasa da kawayenta ba,a cewarta ba laifi ba ne. amma an bi an tsangwami yarinya,an hanata walawa.sai da Abba ya gaji dan kanshi sannan ya sauke mata ruwan. Sannan ya mammaka mata takalmi,sannan ta shige dakin tsohuwa.tsohuwana daga kwance ta dubeta. "yaga dama ya kyaleki?kai mai sunan malam akwai mugunta.zo ki kwanta." cikin kuka ummi tace,"kayana sun jike,bokitin ruwa fa ya dora min."tsohuwa tace,"barshi da halinsa,ace mutum ba zai sake ba?" ummi tace,"ai sai na rama,shima din sai yayi kuka."tsohuwa ta ce,"a'a,kada ki soma zancen ramakon nan.kin san ko kin rama ke ce zaki kwan ciki." ummi ta ce,nifa sai na rama."tsohuwa ta ce,"baki gaji da shan wahala ba kema da shegiyar gaddama,ga zanina nan kikin raki ciro ki daura kizo ki kwanta." ummi tayi lamo bayan tsohuwa tana tunanin dame zata rama abinda Abba yayi mata jiya.har bacci yayi gaba da ita waiwaye............. SULAIMAN shine asalin sunan Alhaji babba,Aminu kuma shine Alhaji karami. tsohuwa itace mahaifiyar su,kuma su kadai ne yayan data haifa.Asalinsu yan zamfara ne a kauyen daji a karamar hukumar kauran-namoda. malam Idris mahaifinsu shine ke zuwa yawon fatauci,har Allah ya zaunar dashi a garin kano,da matarshi Habiba. sunzo da yayansu guda biyu,sulaiman da Aminu.sun yi karatun muhammadiyya mai zurfi,amma basuyi karatun boko ba. sannan ya dora sukan harkar kasuwanci,Allahya albarkaci kasuwancin Sulaiman inda harkoki suka bude mishi cikin kankanin lokaci. matsalar shi daya rashin boko,malam idrisu mahaifinsu yana daya daga cikin wadanda basu amshi boko ba lokacin da tazo. Don haka sam bai saka yayansa ba.Sulaiman ya auri Suwaiba wadda suka dauki watanni suna soyayya,ita yar unguwar sheka makaranta ce. Amma asalinsu yan Daura ne jihar Katsina.kafin aurensu sai da yayi gini a unguwa uku gidaje guda biyu iri daya. Ya ce Aminu kaninsa ya zabi gida duk da cewa a lokacin baiyi auren ba,wannan abu yayi wa mahaifisu dadi. yayi ta shiwa Sulaiman albarka,don haka sai aka rufe na Aminu,yayin da sulaiman ya tare a nasa da matarsa Suwaiba. / ZURFIN CIKI book 1 part 2 ZURFIN CIKI book 1 part 2 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:40 Kwanci tashi 5yrs ta miqa suwaiba bata taba ko batan wata ba. awannan yr ne mahaifinsu ya cimma 1yr da rasuwa. saida aka watse makoki danginsu na qauran-namoda suka koma. sannan sulaiman yace da aminu, to ni xan dauki tsohuwa in maida ta gidana,kai kuma aminu ka fito da mata kayi aurenka dan mu xauna kusa da juna. tsohuwa ta saka kuka tace wannan yaran nidai da ka barni na xauna da gidan xai xama kufai. sulaiman yace tsohuwa kiyi haquri, sai a saka haya.aminu yace haka xa ayi. daqar tsohuwa ta yarda dan tace ita wannan gidan mutuwane xata rabata dashi, dan gidane me tsohon tarihi a gurinta. ta ce gidan da mijinta ya rasu gidan da ya kawo ta tun tanada jajayen sawunta. suka dai lallabata. lkcn da aminu ya gabatar da sahura a matsayin matan da xai aura, tsohuwa ta tuma ta ce ba ta laminta ba, don kuwa kowa yasan mahaifiyar sahura gun masifa. sanna sahurace ta gajeta. aminu sai ya watsar da mgnn auran gabaki daya har tsawan lkc. sulaiman yanata roqan tsohuwa ta amince, dan ya lura aminu yayi nisa. Ba yadda tsohuwa ta iya, dole ta amince, aka sha biki ta tare gidan aminu. mai hali dai baya fasawa, dan sahura batasan hulda da suwaiba da surukarta, gashi daga kawota ko 2mth bata yiba ta kama fada da yan unguwa. a cikin 3yrs sahura aka samu ciki. lkcn sulaiman ya samu xiyarta qasa mai tsarki shida tsohuwa dan sauke farali. sunyi addu'a allah ya bashi xuri'a shida aminu.suna durowa gida suka samu lbrn cikin sahura, murna a gun sulaiman tamkar matanshi ne keda cikin.lkcn haihuwa tahaifi da namiji murna gun yan uwa biyu ba'a magana, anyi shagalin suna inda yaro yaci sunnan mahai finsu wato idris shine suke kiranshi abba. Sannan Ahaji Sulaiman ya biyama qaninshi kugeran makka daga nan ne aka samu ahj Babba da ahj qarami tun abba yana jariri ahj babba da matanshi suke dawainiya dashi Sahura ba taso saidai ba yan da xaitai da ita. domin alj qarami na gama shirin fita xai saba shi sai gidan sai yayi kukan nono ake maida shi, saidai tayi ta mitar cewa anriqe mata yaro gidan,sahura dai in an kawoshi bata isa taxoba dan tasan tsohuwa tafita danja.duk da gugar xana da haibaici da sahura take antayo ma suwaiba ta katanga ko inta je gidan, baisa ta daina dawainiya da abba ba. cikin hakane sahura wata ran sahura ta tashi da xaxxabi mai tsanani da amai, shine taje asibiti ganin likita ya tabbatar mata da tana dauke da ciki.ko da ta fadama alj qarami ba qaramin murra yayi ba ita kuma ta batarai, yace tunda abba yana tafiyan shi ko ina ayaye shi. Da yamma bayan yadawo kasuwa ya shiga gaida tsohuwa shine yake gayamata xa'a yaye abba. tace saboda me? ku barshi yayi 2yrs. sai yace ai uwan tanada juna biyune, shi yasa, daman sha waran da nakesan fada maki shine xanba yaya shi kyauta har abada.tsohuwa tace kai amma ka kyauta. Washegari da safe shine ma yayi ma abba wanka tana kwance ya shirya shi, sannan yace mata ta hada kayanshi duka dan xan kaishi gidan ahj babba gaba daya. tace kana nufin kayi kyauta dashi gaba daya? yace ea. tace tabdi!,ba xai yiwu ba. infishari banxane kaxa tayi mana. su wa yace kada su dage su samu nasu dan? nima wahala nasha na haifi dan, ba shago na bude ya fito ba....sam bai kulata ba, ya hada kayan yaran ya fita. ya shiga gidan ahj babba da shi. dakin tsohuwa ya shiga, nan ya samu ahj babba suna gaisawa, yace yauwa, dama gurinka naxo yaya. abba ya sauka daga jikin babansa yaje jikin ahj babba da gudu, ahj ya dauke shi ya rungume. Ahj qarami ya keqa ya kira suwaiba,ta shigo ta xauna sai ahj qarami ya soma jawabi da cewa. tsohuwa ina san ki xama sheda, yaran nan na ba yaya da suwaiba har abada.ahj babba yasake rungume yaran a jikinshi wani saban son shi ya ratsa shi. idanshi suka kawo qwalla, suwaiba ta sa kuka tace mun gode da wanna abu da ka yi mana. Allah ya bamu ikon riqeshi da amana. ahj babba yace bani da bakin da xan maka godiya, saidai ince allah ya qara xumunci. ahj qarami yace haba yaya dana nakane, saidai inasan abba ya xama xaka kai daya. tsohuwa tace allah ya maku albarka daku da yayanku, kaima allah ya baka haihuwa. sukace amin. Sahura kuwa mijinta na fita da yaro, itama ta xari hijabi ta nufi gidan iyayanta, ta shaida ma mamanta cewan aminu yayi kyauta da danta, kuma yaba mutanan da basa qaunan ta. nan da nan uwar tahau masifar cewan ba xai yuyu ba, ai dole ya baki danki. shiko uban cewa yayi ai ikon sane, dan haka baiga laifinsa ba dan yaba dan uwansa dansa. sannan yace ,ta tashi ta koma. uwar tace ba xata koma ba, ya ce ta xauna. bai sake bi ta kansu ba, ya ci gaba da harkokinsa. shiko ahj qarami cewa yayi baxai bita ba, lokacin da ya dawo ya samu batanan, sannan bai fadama dan uwansa ba har aka kwana. sukuma su suwaiba basu fahinci sahura batanan ba dan ba hurda suke ba, saida kukaxo cin abinki ahj qarami bai futo da kwanu ba. sannan wan yace iyalin naka bata nanne? yace yaji tayi, niko baxan bita ba. ahj babba yace akan wani dalili ne? ahj qarami yace ban sani ba, na dawo gida ban ganta ba. da safe ahj babba ya tashi gaba sukaje gidan, sahura ba kunya tace danta takesan ya dawo mata dashi, inhar yana san xama da ita. Ahj babba yace, indai danta ne xai maido shi. ahj qarami yace shi kuma inhar sai an dawo da dan to ya haqura da auranta. kuma na cikin ta ma inta haife shi xaixo ya ansa ya qarama wansa inya so yaga yadda xatayi. duk juyin da akayi yaqi yarda daga qarshe ma tafiyan shi yayi. ubanta yace da ahj babba kaima jeka yadda suka so haka xasu yi. satinta guda taka abincin kirki gagaranta yake yi, ita kuma uwan ta daina samun wani abu daga gun sahurar ke kawo mata. dan haka suka yanke shawaran ta koma, duk da haka saida ya shareta na kwana uku sannan ya sakar mata. haka ta haqura saidai tasha alwashin dun runtsi sai danta ya dawo hannunta. sannan ta kulla sabuwan gaba da ahj babba da suwaiba kuma tace duk tsohuwa ce takitsa abin. abba yana samun kulawa tare da tarbiya mai kyau.sahura ta haihu ta sake samun da namiji aka samasa bashir, daga nan haihuwa akai akai.. Tun abba yana qarami ya koyi wasu halaiya na ahj babba. da farko, sallar asuba,axahar, laasar, magrib da isha. ahj babba kan tasa abba suje masallaci da rana kuma umman sane ke turashi. ranan jumaa ahj na dawowa gida dan ya tafi dashi. dan haka sallah ta xauna ma abba da xaran

Chapter 1 of 7