Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 6
bakin Aliyu Rashid. Acan kuma waje gurin da masu jinyar marasa lafiya ke zazzaune Imran da mahaifiyar Aliyu Rashid, gami da mahaifiyar Rabi'atu tare da yan uwanta su goma sha daya. Domi lokacin da Imran ya je musu da labarin mahaifin Rabi'atu bayanan, kafin wasu lokuta, tuni rade-radin labarin ya watsu a kusan duk rabin asibitin kamar wutar daji. Tunda mahaifiyar Rabi'atu tazo gurin take kuka, su kuma sauran matan suna ta bata hakuri, gami da dada jaddada mata cewa komai fa me wucewa ne in Allah yaso. "Sai dai munji daga bakinta insfecta Ja'afar yace da Aliyu Rashid. "Domin ba zamu iya yadda da abin da kace ba, sai in munji daga bakinta." A daidai lokacin ne to, malamar asibitin ta kwankwasa kofar sannan ta shigo tana rausaya. "Yallabai kuna iya ganinta yanzu." Aliyu Rashid ya mike jikinsa na rawa yace: "Yaya jikinnata." "Da sauki, daman cikinne ya sami yar tangarda, to amma yanzu ya koma yadda yake, da dai ace kun dauki tsawon lokaci baku zo asibiti ba, to da juna biyun zubewa zai yi me yiyuwa ma itama ta mace a hannunku." Aliyu Rashid yayi ajiyar zuciya sannan ya juya yabi bayan Insfecta Ja'afar da sajen Danlami wadanda tuni su sun kai kofar dakin. Sauran yan uwa da abokan arziki dake zazzaune a dakin jinyar suka dubi yansandan biyu tare da Aliyu Rashid ayayin da suka nufi dakin da Rabi'atu take, koda suka karasa kofar dakin sai Insfecta Ja'afar ya juya ya dubi Aliyu Rashid gami da tattausan murmushin dake cewa kada ka damu, yace. "Ina ganin da zaka dan jiramu a waje da yafi, domin mu kadai muke son ganawa da ita." Kafin Aliyu Rashid yace wani abu tuni yansandan biyu sun wuce cikin dakin, suka rufe kofar dum! A fuskar Aliyu Rashid. Mahaifiyar Rabi'atu ta taso tana kuka ta tari Aliyu Rashid tace. Me ake cikine bawan Allah?". "Kada ki damu in Allah yaso babu abin da zasu yi mata" Aliyu Rashid Yace. Mahaifiyar Rabi'atu ta sake fashewa da kuka. Acan gefe guda Sagir da Imran na zaune basa ko wani kwakkwaran motsi kowa na karatun wasikar jaki. ****** Karfe hudu dai-dai suka fito daga dakin. Mutane gaba daya suka bisu da kallo. Aliyu Rashid ne ya fara bin yansandan a baya." "Yaya ake ciki yallabai" "Kada ka damu" Insefecta Ja'afar yace dashi." "Labarinta akwai alamar gaskiya, amma babu wani abu indai hukuma ta tabbatar da cewa labarinta gaskiya ne, to tana iya tsira tunda tsaron kanta tazoyi, kuma ba niyyar ta bace ta kashe Bose, musamman ma idan akayi la'akari da juna biyun dake jikinta. Yanzu dai zamu bar yansandannan uku anan, mu kuma zamu je mukai maganar gaba, domin Ojo Uban gidan Bose ya shigar da kara, amma kada ku damu, ku dai kawai ku dauki lauya, ammam ina tabbatar maka babu inda Ojo zashi, domin (Club) dinma nasa dayake tara yayan iska irin su Bosen an rufeshi tunda Allah ya kawo mana rahamarsa, ansamu canjin shugaba mai Adalci." "To insfecta na gode." Aliyu Rashid yace, gami da ajiyar zuciya. "Ba komai." Insfecta Ja'afar yace, sannan ya miko musu hannu suka gaisa, shima sajen Danlami ya miko hannu suka gaisa sannan yace. "Acikin yansamarin can wanene Sagir, idan yana gurin kuce dashi wai Rabi'atu tana son ganinsa." Yansandan biyu suka yi gaba abinsu, sannan yan uwan Rabi'atu suka zo suka zagaye Aliyu Rashid, wanda ya fara yi musu bayani akan su kwantar da hankalinsu babu abinda zai faru. Adai dai lokacin ne to ya dubi Sagir yace. "Kaje tana son ganinka, amma kayi sauri ka fito domin yanuwanta da kuma mu kanmu muna son muje mu duddubata. To amma yanzu dai sai kaje babu mamaki wani abun ne take son fada tunda tace kai kadai take son gani." Sagir ya juya ya nufi dakin da Rabi'atu take, sauran mutanen kuma suka bishi da kallo Imran yayi mamakin me Rabi'atu ke son fadawa Sagir ne take son ganinsa shi kadai. Allah ya tserar da abar kaunarsa Rabi'atu, yace cikin zuciyarsa, domin ko yanzu shi mai iya aurenta ne. Sagir ya tura kofar dakin a hankali ya shiga, sannan ya dubi Rabi'atu, Rabi'atu na kwance tana kallonsa. Fuskarta ta kara fari, haka nanma idanunta. "Sannu Rabi'atu" Sagir yace a sanyaye. "Sagir! Sako zan baka ka kaiwa Abdul "Rabi'atu tace a hankali kusan a cikin rada, Sagir ya dubeta kawai, amma bai amsa ba. Rabi'atu taci gaba da cewa. "Idan kaje kace dashi, bana kaunarsa, na tsaneshi, bana kuma sake kaunar ganin mummunar fuskarsa mai munin hali, kace dashi, Allah ya dawomin da masoyina Imran, shi zan aura indai Allah ya tserar dani daga kangin dana shiga.....". Tayi shiru tana shesshekar kuka sannan tace gaba da cewa. "Sagir, kace dashi nayi bakin ciki da banyi barin dansa ba, kace dashi naso juna biyun dake jikina ya zube domin na tsane shi saboda shi" "Sagir ya dubta, sannan hawaye suka fara zuba daga idanunsa. "Ki yafe shi Rabi'atu, don Allah ki yafe masa, domin indai don Abdul ne to kisa ranki a inuwa, domin kuwa Allah ya dauke abinsa, Abdul ya mutu ya barki, ya kuma barni a duniya ba Uwa ba Uba, ba kuma wani dan uwana na jini sai wannan dan dake jikinki, dan da kike cewa kin tsana, idan kin haife shi Rabi'atu, ni inaso ki kawomin shi, domin kuwa bani da wani dan uwa a duniya sai shi." Kafin ta farga Sagir ya fice daga dakin da gudu yana kuka. Rabi'atu ta fashe da kuka. Ba mutuwar Abdul take yiwa kuka ba, sai dan da zata Haifa maraya, ba Uba shi take yiwa kuka. . ƘARSHE An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6