Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
kofar dakin da sauri ko da ta je kofar dakin sa ta juya domin kawai ta yiwa dakin kallon karshe, sannan ta dubi gawar Bose da ke kan gadon kwance tana barci, barcin da ba za ta farka ba, sai ranar da aka busa kaho, Rabi'at ta juya a hankali ta nufi kofar gidanm tana sharar hawaye, cikin takaicin auren Abdul, wanda ya janyo mata sanadiyyar kisan kai, ta san cewa da zarar an kamata kashe ta ita ma za a yi. Za ta shiga duniya, ta ce da kanta. Sai ta haife za ta dawo ta kawo kanta ga hukuma. Abin da ba ta sani ba, shi ne, koda laifin kisan kan ya tabbata a kanta, ba za a zartar da hukunci ba har sai ta haihu, to amma kuruciyar Rabi'atu ba ta bari tasan hakan ba ita a shi ne tunaninta da an kama ta haka za a kashe ta. Rabi'atu ta jingina kanta a jikin kujerar motar hayar, sannan ta shafi dan matashin juna biyun da ke jikinta tace cikin zuciyarta. Allah ya sa na miji ne, Allah ya sa kuma bai yi halin ubansa ba, sannan ta ce a hankali kamar mai tsammanin dan da ke cikin nata zai ji abin da take cewa Allah ya raya min kai ka ji IMRAN wannan shi ne sunan da ta kudurce a ranta za ta sawa dan. Sunan tsohon saurayinta abin begenta Ko da Rabi'at ta dubi yadda gine-gine da bisoshin garin su ke ta giftawa ta jikin gilashin motar sai ta yi mamakin in har za ta sake ganinsu nan gaba. Me yiyuwa ita da su har abada . Mutuwar mahaifin su Abdul ta girgizashi da farko sai dai kuma daga karshe sai ya ji kamar an daure masa nannauyan kaya daga bayansa Domin sau da yawa tsoron mahaifin su ne ya sa Abdul ke rage wasu abubuwan Bayan da aka dawo daga jana'izar mahaifin nasu. Sagir da Abdul suka zuna a kofar gidan suna ta karbra gaisuwa kamar dai yadda ake yi a al'ada "Mene ne sanadiyyar mutuwar tasa ne Abdul ya tambayi Sagir lokacin da mutane suka dan tsagaita da zuwa Sagir ya kalle shi sannan ya ce "Abin da ya saba damun sane hahhawar jini kasan tun kafin na tafi Amurka yake ta fama da cutar ashe Allah dai ya kaddara ita zata kai shi kushewa yau da asuba." "Allah ya jikansa." Abdul ya ce, gami da namijin kokarin ganin ya sanya alamun damuwa a fuskarsa. "Ameen." Sagir ya amsa yana duban Abdul cikin mamaki, bai taba tsammanin zai yi wa mahaifin nasu addu'a ba. Kamar Abdul shi ma Sagir mutuwar bata dameshi ba, domin mutuwar mahaifin nasu tamkar wani sabon lasisi ne a ka bashi na sheke ayarsa yadda yake so domin babu wani sauran me yi masa fada. Har zuwa magariba, mutane ba su daina zuwa ba, Abdul da Sagir suna ta karbar ta'aziyya. Da yake Insifecta Rabi'u watau mahaifinsu mutum ne mai adalci da mutunci a zamanin kuruciyarsa, mutane da yawa sun girgiza da mutuwar da ya yi haka ta karo daya babu wata doguwar rashin lafiya. Abdul bai tashi tunawa da Bose ba sai bayan karfe shida da Rabi. Shi kansa bai san abin da ya mantar da shi ba, to amma a tunaninsa yawan mutanen da ke zuwa gaisuwar ne ya mantar da shi wanda da yawa daga cikinsu suna zubar da hawaye sharaf- sharaf suke zuwa. Abdul ya mike tsaye sannan ya ce da Sagir. "Zan je gida na dawo, ka san ko matata ban fadawa ba, tun da kai da kaje kin fada min ka yi." Sagir ya dube shi, sannan ya ce. "Ka ga kada ka rana min hankali, ka ce kawai za ka je gurin Bose, na ga fa shigarta gidan, na kuma ga lokacin da matar taka ta fita tana sharar hawaye, duk a kan idanuna." Abdul ya dubi Sagir cikin kaduwa. "To...to kai kana ina lokacin." "Kaga Abdul yi tafiyar ka ni ban rike ka ba ban kuma hana ka ba abin kawai da nake son na gargade ka akai shi ne, idan ka san wulakanta yarinyar nan zaka yi to ka sake ta sai ka ci gaba da neman matan ka, ban hana ka ba, amma ina tabbatar maka da cewa muddin ka ci gaba da haka to wata rana za ka ga ba daidai ba, ka yi a hankali ba ka san mata ba ne, suna iya jure komai amma banda kishi, irin wannan ne wata mace ta harbe mijinta a Amurka, kwanaki biyu ya rage na dawo gida." Sagir ya dan yi shiru yana duban Abdul wanda ke tsaye cikin kaduwa yana dubansa. "Ai gara ka tafi kada ka bari Rabi'atun ta dawo gidan su hadu, domin suna iya yin rigima, kuma ka z ka kwana ciki, tun da matarka na da ciki, idan karuwarka ta lahanta ta kai ta janyowa, ba ka san mata ba ne har yanzu." Sannan ya dada da cewa. "Ai muna tare da makwabcinka Alhaji Ibrahim ina sanar da shi rasuwar baba na ga fitowar Rabi'atun daga gidan, ba a dade ba kuma na ga Bose ta zo, ni daman ina gani na san abinda ka kulla. To ka yi a hankali mata sun fika sharri sau da yawa sai ka yi musu abu kana zaton ka ci Bulus, to wallahi ba ka ci ba, domin idan ka yi wasa sai ka yi amanta...". . Maganganun Sagir na ta kururuwa cikin kwakwalwarsa ya isa gidan. A motar Sagir ya zo gidan, domin gudun kada ya shigo motar haya ya bata lokaci har Rabi'at ta dawo ta sami Bose. Gashi kuma ya ce da ita ta dawo bayan magariba. Bakwai saura minti biyu kacal ya iso, yana zuwa ya yi fakin da motar Sagir cikin gareji kusa da tasa sannan ya nufi saman benen da gudu. "Bose Darling!". Ya kwalla mata kira shiru ta gaida kunnuwansa. "Bose kina ina ne!". ya sake kwalla mata kira shiru dai babu motsi. Abdul ya yi murmushi, ya san dole ne Bose ta yi fushi saboda barin ta da ya yi na tsawon lokaci. Ya nufi kofar dakin yana fito. Ya san dole ne su hau sama da Bose kafin ya shawo kanta. Ya tura kofar dakin. "Bose....". Ya yi shiru bai karasa ba cikin mamaki. Lafiya Bose ya Yaga Bose haka a kwance har yanzu..........????ACI BULUS - 7 . "Bose....". Ya yi shiru bai karasa ba cikin mamaki. Lafiya Bose ya ga Bose haka a kwance har yanzu, Abdul ya san cewa Bose gwana ce wajen barcin rana, amma bai yiwuwa ace har magariba tana kwance, abin mamaki kuma shi ne wai har da lillibe da wannan uban zafin. Abin na da ban mamaki. Tabbas Bose ba ta da lafiya. Abdul ya matsa bakin gadon sannan ya dan daki Bose a gadon baya. "Bose...bose tashi mana me ke damunki...?". Ya ji tsigar jikinsa ta tashi, domin lokacin da ya ke dukan bayanta, sai ya ji kamar ba jikin mace yake duka ba, domin abin da ya ke duka ya yi tauri da wuya a iya kiransa jikin mace, sai ya ji kamar yana dukan buhun siminti. Ya mika hannunsa sai ya ga kudaje sun yi sama buuu!! Mamaki da fargaba suka kama shi, sannan ne to ya ga wani bangare na mayafin ya rine da wani abu jajur kamar jini. Gaban Abdul ya fadi ras! Kwakwalwarsa ta kasa tunanin komai. Sannan sai ya yi ta yan maza ya yaye mayafin. Yawun bakinsa ya kafe cak kamar an tsotse. Cikin fargaba marar misaltuwa Abdul ya dubi kumburarriyar fuskar bose. Idanuwanta a jirkice, harshenta ya cika bakinta, idan ba don kayan da ke jikinta ba sai Abdul ya rantse da Allah ba Bose da ya sani ba ce. Abdul ba ya bukatar sake taba Bose domin ya tabbata gawa yake kallo. Ya yi ta yanmaza ya dafa jikinta sai ya ji ya yi sanyi karau kamar kankara, jikin ya sandare sandar-dar kamar itace. Abdul ya mike tsaye jikinsa na rawa kamar mazari, ya dubi fuskar gawar da ke kwance a kan gadon. Sai ya ji wani zazzabi- zazzabi yana neman rufe shi, Abu na farko da ya fara tambayar kansa shi ne wa ya kashe Bose. Rabi'at ta fado ransa, ya dubi agogo bakwai da mintina biyar. Kuma kowanne lokaci daga yanzu Rabi'at na iya dawowa. Abin daya kamata ya yi shi ne ya boye gawar kafin Rabi'at ta dawo. Da farko ya yi tunanin ya nemi taimakon yansanda, to amma sai ya yi tunanin me zai ce da su, shi kansa bai san abinda ya kashe Bose ba, shin idan ya kirawo yansanda za su iya yarda da cewa ba shi ya kashe ta ba kuwa. Tabbas ko sun yarda da labarin da zai ba su yanzu to za su ci gaba da bincikensu. Gabansa ya fadi ya tuno da hayaniyar da suka yia a daren jiya shi da Bose a (Rose Mary Club) abin da yansandan suke bukata su lankaya laifin kisan kan a kansa, shi ne su sami wata shaida da za ta nuna sun yi hargitsi shi da Bose. Tabbas daruruwan mutane sun ji Bose na ta fada cikin daga murya a daren jiya. Abdul ya share gumin da ke sartu daga goshinsa sannan ya nufi baki gadon. Ya zama dole ya boye gawar Kafin Rabi'at ta dawo. Dole ne ya boye gawar kafin ya yi tunanin abinda zi yi da ita. Sai dai kuma a ina zai boye gawar kafin ya yi tunanin abinda zai yi da ita. Sai dai kuma a ina zai boye gawar. A take a gurin amsar ta zo masa. Cikin but din motar sa. Ciccibo sandararriyar gawar mai nauyin tsiya yayi ya dora ta a kafada kamar tsani ya nufi kofar dakin. A daidai lokacin ne to aka kwankwasa kofar daki. Abdul ya yi sororo yana haki gawar a kafadarsa, "Wane ne ku,a, ya tambayi kansa, Rabi'at?" Aka sake kwankwasa kofar, Abdul ya jefar da gawar tim a tsakar dakin cikin kaduwa ya nufi kofar dakin ya bude. Nasir jakal ya yi murmushi sannan ya ce. "Me ka jefar ne haka na ji tim! Kamar buhun siminti? Abdul ya dubi Nasir (Jakal) Sororo cikin kaduwa yana son ya yi magana, amma yawu ya gama kauracewa bakinsa. "Shegen sama ina ka shiga ne kwana biyu?". Nasir yace yana murmushi sannan ya fara kokarin turar da Abdul ya kauce ya shiga dakin Abdul ya yi sauri ya sake bambanke kofar dakinda kafadarsa. "I...ina nan." Abdul ya sami kansa yana cewa Nasir ya dubi fuskar Abdul sai ya ga duk ta yi sharkaf da gumi duk a firgice. "To mu shiga daga ciki mana sai wani bambanke kofa ka ke yi kamar wanda ya ajiye wata uwa a ciki, ko Bose din ce ba ka so na gani a dakin matarka." Nasir Jakal ya yi murmushi. "Kai da Allah mu shiga ciki, na san fa tana nan, yanzu ma nemanta na zo, OJO ne ke son ganinta, da gaggawa shi ne yace da ni na nemo masa ita a duk inda take, to sai ya ce da ni wai duk idan ka ke ya san Bose tana nan domin ta ce da shi wai gurinka za ta zo." Duk maganar da Nasir Jakal ke yi, Abdul kawai jinsa yake yi cikin sa na kugi cikin tsoro da fargaba. Abdul ya dubi Nasir ya yi murmushin yake ya ce. "Kai dai ba ka da mutunci, wallahi yanzu kai har tsammanina ka ke zn kawo Bose dakin matata?". "Ai ba karamin aikinka ba ne." Jakal ya ce yana dariya kasa-kasa. "Nasan halin ka fa, malamin bariki, ai iskancinka ya fi da haka na san baka da kyau ne, na san idan ka yi niyyar kawota ma kana iya korar Rabi'atun tun da ba damuwa ka yi da ita..." "Kaga idan ka fara magana ka yi ta yi kenan kamar mai wa'azi sani kanka ne ina da guri-guri da dama da zan iya kai Bose ba tare da na kawo ta gida na ba to ka ga ni rabona da Bose ma ya fi kwana biyar." Murmushin da ke fuskar Nasir Jakal ya subuce sannan mamaki ya maye gurbin murmushin. "Haba Abdul kada ka raina min hankali mana, jiya ma fa da daddare kuna tare, kuma Ojo ya ce da ni gurinka Bose ta tafi, domin ba ta taba tafiya wani guri ba ba tare da ta sanar da Ojo ba. Amma yanzu don rainin hankali sai ka ce da ni wai kwananka biyar ba ka ganta ba, a'a kwananka dubu!". Abdul ya dubi Nasir cikin fushim domin ya fara isarsa, duk ya matsu ya bar gidan, domin ya san ba karamin hadari ba ne Nasir jakal ya ga gawar Bose dan kuwa yana iya tsorata ya tona masa asiri. "To shi Ojo ubanta ne da duk idan za ta tafi sai ta sanar da shi." Abdul ya ce. "Ba ubanta ba ne, amma ka san a harkar Zaman bariki ya fi ubanta, domin Ojo shi ne ya kawo Bose garin nan tun tana karama, shi ne ya daga ajinta a idon samari har ake warwasonta, ka ga kuwa ai dole ne duk inda za ta ta sanar da shi." Abdul ya kauce daga kofar dakin, sannan ya juya a hankali kamar zai shiga dakin sai kawai ya janyo kofar dakin garam! Ya rufe, sannan ya dubi Nasir Jakal ya ce. "Ka je ka ce da Ojo din. Bose ba ta guri na, idan ma tace da shi gurina ta zo to ka ce karya take kuma..." Nasir ya katse shi cikin fushi. "Ka ga Abdul ni ba yaro ba ne, tunda abin naka ya zama wulakanci shi ke nan, mene ne na boye-boye, ni yanzu har ni za ka kife da kwando don ka kawo karuwa dakin matarka, ashe kurarin da ka ke, na cewa kai ne malamin yan bariki ya zama shirme. Ni zan tafi kawai ka gane, daman na fuskanci a yan kwanakin nan tun da ka shigo cikin kudi ka ke wani neman dizdizga mutane, to idan kana ganin kudin ka muke bi an daina zuwa gurin naka, Ojo kuma zan ce da shi Bose tana gurinka amma ka hana ta zuwa." Kafin Abdul ya maida martani tuni Nasir Jakal ya juya cikin fushi ya nufi kasan benen daf! Daf!! Daf!!. Abdul na tsaye a bakin kofar benen yana duban Nasir Jackal har sai da ya fice daga gida. Abdul ya yi ajiyar zuciya a lokaci guda kuma ya sa gefen hannun rigarsa ya goge fuskarsa. Sannan ya juya a hankali jikinsa na rawa ya sake bude kofar dakin ya dubi gawar Bose kwance ta yi sandar-dar. Hanjin cikinsa ya yamutse, ya zama dole ya san duk yadda zai yi ya boye gawar kafin ya yi tunanin inda zai jefar da ita. Abdul ya sunkuya a hankali ya tallafo kan gawar ga mamakinsa sai ya ji hawaye ya fara sartu a kan fuskarsa, ya tuno irin zaman da suka yi da Bose, ya tuna sa'ar da suka fara haduwa da ita a Rose Mare Club duk cikin yan matan Abdul babu wacce yake kauna kamar Bose shin wa ya kashe Bose? Abdul ya tambayi kansa. Sannan ganin cewa bashi da amsar tambayar, sai ya sake ciccibar gawar ya dora ta a kafada ya tura kofar dakin sannan ya nufi kasan benen da gawar a kafada da kyar yake numfashi *** Garejin da Abdul ke ajiye motarsa kofa biyu ce da shi, a kwai kofar garejin ta waje wacce da ita ne ya ke amfani gurin shigar da motarsa idan ya dawo. Sai kuma kofa ta biyu wacce ita daga zauren gidan ta ke, wacce ta cikinta ne Abdul ke shiga garejin ta zauren gidan da ita ce Abdul ke amfani a duk sa'ar da zai fitar da motar daga gareji. To yau ma kuma sai gashi zai yi amfani da kofar garejin da ke zauren gidan sai dai wannan karon ba shiga zai yi ba ya bullo ta can ba DOMIN......ACI BULUS - 8 . Sai dai wannan karon ba shiga zai yi ba ya bullo ta can ba DOMIN kuwa ko ya shiga dole ne ya dawo ta inda ya shiga tunda kuwa dauke yake da gawa a kafadarsa Abdul ya sunkuya da kyar yana nishi, ya aje sandararriyar gawar a kan daben da ke zauren cikin gaggawa ya janyo kofar gidan ya rufe domin gudun kada Allah ya kawo wani bakon ba zata ya kama shi da gawar dumu dumu a hannu Rigarsa ta jike sharkaf da gumi ta kowanne bangare sai diga yake yi kamar kuturu A haka ya nufi kofar garejin da ke zauren cikin gaggawa ya bude ta sannan ya dawo ya sake sungumar gawar a kafada ya nufi cikin garejin Agogon da ke saman benen gidan ya buga kararrawar sa da ke nuni da cewa yanzu fa karfe takwas na dare Gaban Abdul ya fadi lokacin da ya ji kararrawar agogon tana ruri domin ya san ko wane lokaci daga yanzu Rabi'atu na iya dawowa tun da babu mamaki Rabi'at jira take sai an yi sallar Isha za ta dawo. Dole ne ya boye gawar cikin but din motar kafin ta dawo domin ya san indai har ya boye gawar a bayan motar to babu abinda zai hana shi fita cikin tsakar dare ya jefar da gawar daga nan kuma atunaninsa ya tsira kenan sai dai kuma ya dawo ya yi tunanin wanda ya kashe masa Bose..." Tunaninsa ya katse sakamakon duhun bakinkirin da ya mamaye shi a acikin garejin. A can wani bangare na Unguwar yaran makwabta suka dauki shewa (NEPA!!) Abdul ya yi gunaguni sannan ya ce kai Allah ya tsine wa (Nepa) din nan. Abdul ya sunkuya a hankali da nufin ya ajiye gawar sai ya ji ya dunguri bayan motar domin duhun ya hana shi ganin gabansa don haka, sai ya kintaci inda bazai sake cin karo da booth din motar ba ya kwantar da gawar domin ya sami damar laluben (Lighter) abin kunna sigarin sa da ke aljihunsa to amma sai ya ji ya sake dungurar bayan wata motar sannan ne to ya tuna da cewa ashe motoci biyu ne a garejin da motarsa da kuma motar yayansa. Don haka sai ya lallaba a hankali ya jingina sandararriyar gawar a jikin bangon garejin ya dafe ta da hannu daya sannan ya lalubi aljihunsa domin ya dauki (Lighter) din dazai kunna don ganin haske a daidai lokacin ne to ya ji kararrawar da ke zauren gidan ta dauki ruri. Gaban Abdul ya fadi tsoro ya kama shi sannan babu zato babu tsammani sai ya ji an fara bugun kofar gidan sannan sai wata murya ta biyo tana cewa. "Abdul! Abdul!!, ka bude mana." Ba muryar kowa ba ce muryar yayansa ce Cikin gigita sai Abdul ya saki gawar ta sulale ta fadi kasa tim! Sannan cikin gaggawa ya laluba aljihun wandonsa ya dauko yan mukullan motocin guda biyu Abdul ya kasa gane wanne ne dan mukullin motarsa a ciki domin duhun da ke garejin bai barin sa ya gani gashi kuma tsoro da fargaba sun hana shi ya yi amfani da hankalinsa don gane wanne ne dan mukullin motarsa daga cikin tunda ya saba rike shi. Aka sake buga kofar "Abdul". Cikin gigita sai Abdul ya zabi daya daga cikin yan mukullayen motar sannan ya jefa daya a aljihunsa, cikin gaggawa ya lalubi bayan but din daya daga cikin motocin biyu, tsoro da fargaba da kidimewa, sun mantar da Abdul bangaren da tasa motar take, to amma sabo da yana tunannin dan mukullin dake hannunsa na motarsa ne sai kawai ya lalubi wajen bude but din motar ya tura dan mukullin ciki, cikin sa'a sai ya ji dan mukullin ya shiga, Abdul ya murza dan mukullin sai but din ya bude. Ya juya da sauri ya yi lalube cikin duhu yana neman gawar sai ya ji hannunsa ya taba wani abu kamar kafar mutum, kuma ga alamu mutumin a tsaye yake, cikin fargaba sai ya yi sauri ya dauke hannunsa, sannan ya sake lalubawa sai hannayensa suka taba kan gawar Bose, Abdul ya tallabo kan Bose sannan ya dago ta sama da duk karfinsa ya jefa ta ciikin but din motar ya rufe, sannan ya ruga da gudu ya nufi zauren gidan yana zuwa sai ya bude kofar gidan ya dauka Rabi'at ce. A tsaye a kofar gidan, idanunsa boye cikin bakin tabarau, Sagir ne yayan Abdul. Abdul ya yi turus kamar wanda ya ga fatalwa. "Wanne irin iskanci ne haka zaka rufe kofa haka da wurwuri, kasan kuma zan zo na dauki mota ta, kai fa ka ce da ni yanzu za ka dawo, ka sa na yi ta jiranka, ban dan mukullin motata." Sagir ya mika masa hannu, sai a lokacin ne Abdul ya lura da cewa ashe dan mukullin motar da ya jefa gawar a but din ta har yanzu yana hannunsa, sannan kuma dan mukullin motar na sagir ne. Hantar cikin Abdul ta kada, ko shakka ba ya yi ya san ba a cikin but din motarsa ya boye gawar ba, a cikin but din motar Sagir ne "Bani mukullin mana sauri na ke yi." Sagir ya ce Abdul ya rasa yadda zai yi sai ya mika masa dan mukullin Sannan ya juya cikin sauri kwakwalwarsa duk ta rikice, ya bude masa kofar garejin ta waje, sannan sagir ya shiga garejin bai damu da duhun da ke ciki ba, yana lalubawa ya gane motarsa, ya bude ya shiga sannan ya fice daga garejin da gudu, bai ko damu da ya sake duban Abdul ba. Abdul ya yi sororo yana kallon bayan motar Sagir sa'ad da yake fita daga layin. Abin da Sagir bai sani ba shi ne Gawar Bose na kwance cikin but din motarsa. Abdul ya juya jikinsa na rawa ya shiga cikin garejin da niyyar ya rufe kokofin garejin kafin ya yi tunanin abin yi. Sannan ne to ya ji wani hannu ya sulalo ta cikin duhun daren ya dafa kafa darsa, Abdul ya juya a tsorace ya ce. "Wane ne?". Wata murya tace da shi. "Lallai Abdul ashe abin naka ya fara nisa haka, daga malamin bariki kuma ka koma kisan kai!".*** . Sagir ya ja birki a gaban yan samarin. Kayan marmari fal a kan teburin da ke gabansu, akwai ayaba, lemo gwanda, da Tufa kai har da biredi a can gefe guda to amma tufa din ita tafi daukar hankalin Sagir, domin ko sa'adda ya ke Amurka, babu abin da ya fi so a kayan marmari irin tufa. Sagir ya sauko daga motar. "Malam me ka ke so?". Wani saurayi fari mai fuskar dolaye ya tambaye shi. "Tufa." Abdul ya amsa kai tsaye. Bayan wasu yan dakiku, yaron ya zubawa Sagir Tufa din da ya saya cikin jakar leda, sannan ya nufi bayan motar da ita. Sagir ya bishi a baya ya bude masa bayan motar. Yaron ya daga jakar ledar zai sa a ciki, sai ya yi tsalle gefe guda cikin kaduwa. "Mene ne." Sagir ya tambayi yaron. "Leka ka gani." Yaron ya ce a tsorace, cikin mamaki sai Sagir ya leka but din motar. Hasken kwan lantarkin da ke makale a jikin rumfar kayan marmarin ya isa ya nunawa Sagir fuskar gawar Bose, idanunta a juye, harshenta a waje, sagir ya rufe fuskarsa cikin kaduwa. "Wayyo Allah!! Bose ce!!". . WAN NAN SHINE KARSHEN LITTAFIN ACI BULUS BOOK ONE ZAMU DORA DAGA LITTAFI NA BIYU . SAURAN samari ukun da suka rage a majalisar suka mike tsaye zunbur lokaci guda, "Mu tafiya zamu yi" wani daga cikinsu yace, Imran yayi frgigit daga cikin al'adar tunanin da ya sabawa kansa tun watanni shida da suka wuce. "Haba dai tun yanzu zaku tafi, ku bari mana su Ishaq su karaso." Wani dan gajere daga cikin samarin ya dubi Imran sannan ya girgiza kai yace, Zaman majalisar in babu hayaniya ba dadi, sai kaga duk anyi jugum-jugum kamar masu jiran sakamako". To ai shi yasa nace daku kuyi jiran su Ishaq su karaso, samari biyu daga cikin ukun suka yi gaba suka bar dayan tsaye akan Imran yana kokarin nuna masa cewa su fa basu iya zaman majalisa babu hayaniya, daman shine shugaban majalisar, to kuma shi yanzu gashi ya shiga halin kurame. "Idan anjima zamu dawo, kaga kafinnan majalisar ta cika, kaga kuma sai ka samu damar tunaninka a nutse ba tare da surutun mu sun dame ka ba." Kafin Imran ya sami ta cewa tuni daya saurayin daya rage a gurin ya dafewa sauran biyun da suka yi gaba baya. Imran yayi imani da cewa tunda Allah ya jeho dashi wannan duniya mai hargitsi iri- iri, bai taba ganin hargitsin rayuwa da tsananin tashin hankali ba irin na wadannan bakaken watanni shida kamar yadda ya kira su. Hakika rashin masoyi ba karamar masifa bane, domin rayuwa takan dagula tunani ya hargitse sannan kuma rashin nutsuwa da tashin hankali sukan yi hadin gwiwa su fada wa shi wannan gangar jiki daya rasa abin kaunarsa. Imran bai san da haka ba sai bayan daya rasa masoyiyarsa, sashen jikinsa a yadda ya kirata, Rabi'atu. Da farko da har Imran ya saduda, ya fitar da komai daga ransa, tun da dai ya tabbata babu makawa Abdul ne zai aure masa Rabi'atu, to amma fa da zarar anyi kiran sunanta, kai ko arubuce ya ga sunan, sai duk narkakkiyar kaunar nan mai azabar da zuciya ta dawo ta mamaye tasa zuciyar, akwai lokutan ma da har yakan guji bi ta guri indai har yana tsammanin za'a tuna masa da abar begensa domin tuna masa da ita shi yafi komai narka zuciyarsa a duniyar nan tun da dai ya tabbata ya rasa Rabi'atu har abada. Da yawa daga cikin abokan Imran sun dauka Imran ya kama hanyar zarewa ne, dan haka yake yawan tunane tunane, yayin da wasu kuma kadan daga cikinsu masana harkokin rayuwa kance Allah sarki Imran har yanzu dai yarinyar nan ce ke ransa, shi yasa yake yawan tunane-tunane. To koma dai me ne ne Allah ne kawai masanin halin da Imran ke ciki. "Imran" wata murya ta kira sunansa daga baya. Imran ya juyo a hankali ya dubi dogon saurayin dake tsaye yana..ACI BULUS - 9 . "Imran" wata murya ta kira sunansa daga baya Imran ya juyo a hankali ya dubi dogon saurayin dake tsaye yana murmushi kyakykyawa ne in banda sharbeben billen da ya mamaye rabin fuskar sa, babu abin da zi hana ya wuce a matsayin kwararren jarumi kyakkyawa na shekarar. Saurayin sanye yake da doguwar riga da wando na shadda launin toka kansa babu hula dogayen kafafun sa sanye cikin bakin takalmi Sannan a rataye a kafadarsa jakace katuwa irin ta matafiya launin kasa-kasa tana reto kamar mushen zakara jikin danga Sunana Abdussamad Dogon saurayin yace har yanzu dan saurayin murmushin nanan makale a kyawawan fatar bakinsa Imran ya dubi saurayin tun daga sama har kasa, irin duban da likita kan yiwa mara lafiya a duk sa'ad da yace wayyo cikina to amma har zuwa sa'adda idanuwansa suka zo ga takalman saurayin Imran bai gane ko wanene ba kai a iya sanin sa ma shi kan bai taba ganin saba Nasan cewa baka sanni ba nima kuma ban san ka ba don haka kada ka bata lokaci gurin tunanin sai ka gano ko ni wanene domin kuwa baka sanni ba Yayi shiru yana duban Imran sannan a hankali cikin sandar da ta yiwa hawainiya tazara da kadan sai ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya zaro farar Ambulan ya mikawa Imran "Gashi Saurayin yace "Wata ce tabani adireshin ka tace idan na karaso garin nan na baka wannan shine to da na zo gidanku yara suka rakoni nan Imran ya dubi dogon saurayin cikin mamaki sannan kuma lokaci guda ya fara tunanin anya kuwa kansa daya to sai dai kuma tun daga sama har kasa babu ta inda yayi kama da mai tabin hankali Wacece kuwa wannan ita batada suna? Imran ya bukata adai dai lokacin da hannun sa ya karbi wasikar Dogon saurayin ya shafi habar sa cikin kaguwa daya bar gurin. "Tace dani idan ka karanta za ka ga komai a ciki amma ni bata fadamin sunanta ba domin nima a tashar garin Dan'asi muka hadu da ita shine tayi ta yimin magiya tace don Allah nayi kokar na kawo maka wannan. "Malam yaya kam...manninta suke?" Imran ya tambaya a rude murmushin dake fuskar mutumin ya subuce sannan damuwa ta maye gurbin fuskar "Haba malam wacce irin tambaya ce wannan yaya za'ayi na tsaya kallon matar da ba maharramata ba kawai daga mun tsaya ta bani sako kaima ai kasan ba zai yiyu ba ina ganin idan babu damuwa to ni zanyi gaba domin motarmu tana tasha tana jirana don in banda sakon kama da babu abinda zai shigo dani cikin garin nan." "Mutumin ya yi shiru sannan sai yaci gaba da cewa, "Abin da na lura dashi kawai shine matar tana cikin wani irin matsananncin hali da bakin ciki domin baka ganta ba, dole ka tausaya mata." Kafin Imran ya farga mutumen ya juya gami da cewa "Sai anjima." "To na

Chapter 3 of 6