Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
fara. "Mene ne kuma haka." Abdul ya tambaya cikin fushi. "Mai da wukar ango na amarya ba laifina bane ni dan aike ne." "Aiken me wane ne ya aiko ka." Nasir Jakal ya kanne ido daya ya ce cikin rada. "Tare muke da Bose." Abdul ya dafe kirjinsa cikin fargaba. "Kai da wasa ka ke." Nasir Jakal ya fashe da dariya. "Don ubanka ni abokin wasanka ne,, wallahi tare muke da ita. Kuma wallahi ta sami labarin aurenka." Abdul ya sake dafe kirji a karo na biyu. "Yanzu tana ina tana waje ne?". Jakal ya girgiza kansa. Sannan ya nuna kofar dakin da bakinsa. A lokacin ne to suka ji motsin tafiya kwas! Kwas!!. Kamshin turarenta ne ya fara sallama sannan sai Bose ta shigo. Doguwa ce farar Bayarabiya. Tana da kyawu irin nata, da kuma aji irin nata. Ita ce yarinyar da Abdul ya fi shakuwa da ita a duk cikin yan matansa na bariki, wadanda in har ma lissafin gaskiya za ayi bana dokin rano ba, to sun doshi goma sha biyu Bose ta dubi Abdul sannan Abdul ya dubi Bose. Ya yi murmushin karfin hali ya ce. "Bose manyan gari." "Haba Abdul, ina ni ina manyan gari, ai sai ku masu aure da tsakar rana, na ji an ce za ka yi aure gobe, koma a fada mana, shi ne na zo da kaina mu yi sallama." Ta bata fuska tana duban Abdul. "Haba Bose, ai dan zan yi aure ba wai yana nufin mun rabu da ke ba ne..." "Yi min shiru, munafiki, kana jin zan iya daukar tatsuniyar da kake rerawa shashashan abokan ka, wai auren rama wulakanci za ka yi, ai ba zai yiwu ba da ba ka sonta da ba za ka aure ta ba...". "Haba Bose ke wallahi..." Ta katse shi "Ka ga daga yau kada na kara ganin (Your ungly face) a cikin (Rose Mary Club) ba ni ba kai, muddin kuna tare da matar nan to mun yi hannun riga." Bose ta juya cikin fushi ta bar dakin tana sassarfa. Abdul ya dubi Jakal ya ce. "Manta da ita, sai na gama da wannan karamar yar iskar Rabi'atu, sannan zan koma ta kanta." Shi kansa bai gaskata abin da yake fadi ba.***** . Abdul ya karawa motar wuta ya nufo garejin a guje bai tashi tsayawa ba sai da ya zo daf da garejin motar sannan ya taka birki ku!!!. Kura ta tashi sama. Wasu daga cikin dattijai makwabtansa da ke hutawa a kofar gidajensu, suka dubi motar cikin kunan rai suka yi tofin Ala tsine. "Kai Allah ya shiryi wannan yaro, lallai duniya na rudinsa." Wani dan tankwararren tsoho mai kamar baka ne ke fadi. Tun sa'ar da Abdul ya tare a sabon gidanshi da matarsa Rabi'atu, mutanen layin suka daina kwanciyar dare, domin fargabar kada wata rana Abdul ya shawo giya ya bi ta kansu cikin tukin ganganci. Da zarar an jiyo sautin injin motar Abdul za ka ga kowa na kokarin janye kananan yara daga kan hanya, domin sun san Abdul kan iya banke yaro, ku yi magana kuma ya nuna maka iyakarku. Watanni shida kenan yau da daurin auren Abdul da Rabi'atu. Allah mai yadda ya so, wata daya kacal kawai da yin auren, sai Allah ya dawo da babban yayan su Abdul, Sagiru wanda ke karatu a kasar Amurka, ko da yake ya dade da gama karatun har ma ya fara aiki a can. Tun sa'ar da ya bar gida ya tafi karatu Amurka, bai taba zuwa, gida ko da da hutu ba, sai wannan karon. Yau kusan shekaru tara kenan, tun Abdul yana matashi. Zuwan yayan Abdul daga Amurka ba karamin alheri ya zamewa Abdul ba. Domin kuwa yayan Abdul ya je kasar Amurka da kafar dama, inda ya dawo da makudan masu gidan rana. Da zuwansa ya sayawa Abdul sabon gida ya sai masa mota (Honda), sannan ya bashi kudi ya ce da Abdul ga su nan na ka ne, ko ka juya su ko ka kashe kai kaso, in kuma ka so ma kana iya kashe su baki daya idan sun kare ka dawo na kara ma. Sagir ya fi Abdul ma lalacewa nesa ba kusa ba. Yau kusan watanni shida kenan Abdul yana fantamawarsa yadda ya so. Idan ya ga dama sai ya yi kwana biyu bai zo gida ba. Satin farko na Auren sa, shi ne kawai Rabi'atu za ta iya lissafawa a cikin ranakun farin cikinsu na aure, to amma a kwana na takwas. Da yin auren ma Abdul bai kwana a gida ba. A lokacin da aka daura Auren Abdul da Rabi'atu, da kwana biyu sai mahaifin Abdul wanda tsohon dan sanda ne, mai murabus, ya kira su shi da Rabi'atu ya ce yana son magana da su. Abdul da Rabi'atu suka zauna gaban sa kansu a sunkuye suna sauraron Dattijon. Insifecto S.B. Rabi'u, wanda shine sunan mahaifin Abdul, ya muskuta a kan kujerar da yake zaune sanna ya ce da su.......ACI BULUS - 04 . Kansu a sunkuye suna sauraron Dattijon. Insifecto S.B. Rabi'u, wanda shine sunan mahaifin Abdul, ya muskuta a kan kujerar da yake zaune sanna ya ce da su. "Abdul na gode wa Allah da ya shirya min kai, tunda gashi duk da surutun da mutane ke yi a akanka, wai ka ki aure kana yawon iskanci, hakan bai hana ka ba yau ka zabarwa kanka mata." Ya dan yi shiru sannan ya dubi Abdul ya ce "Ba kuma ka aureta ba, wallahi idan ka sake ka wulakantata tamu ce da kai na san halinka, Allah sa na ji labarin ka yi mata wani abu." Sannan ya dubi Rabi'a ya ce "Yarinya ki bi mijinki sau da kafa domin Aljannarki tana karkashin sawunsa, kada ki bata masa idan kuma shi ya sake ya bata miki to ki zo ki sanar da ni zan yi miki maganinsa. Ku tashi ku tafi Allah ya yi muku Albarka." Rabi'atu ta ce ameen. Abdul bai ce komai ba, domin ya san kamar ya saba ma abinda babansa ya gama wa'azi yanzu ne. Duk wannan ya faru ne watanni shida da suka wuce. Abdul ya tura kofar motar da karfi garam! Ya rufe sannan ya shiga cikin gidan cikin sauri tun daga tsakar gida ya fara kwalla mata kira. "Rabi'atu!!. Ina kike ne, wanne irin iskancin banza ne kuma haka kika bar famfo yana ta zuba shi kadai, ko kin dauka kyauta (RECA) suke bamu ruwan ba biya muke ba." Rabi'atu ta muskuta daga kan gadon ta tashi da kyar cikin kunan rai. Tun sa'ar da ta ji karar takun birkin motar Abdul gabanta ke faduwa domin ta san masifa ta dawo, kullum aikin kenan zagi na safe da ban na rana da ban, yau wata biyar kenan abin da ke kona mata rai a yau shi ne, tun da Abdul zai fita da safe ta ce da shi ba ta da lafiya tana son ya kaita asibiti. Yanzu zan dawo. Abdul ya ce da ita bai dawo din ba sai yanzu waje karfe biyar na yamma. Bayan kuma ya san juna biyu ne da ita. Cikin ya kai wajen wata uku a yanzu. Rabi'atu ta tashi da kyar ta leko ta tagar benen ta dubi Abdul ya yi tsaye a tsakar gidan yana ta masifa. "Au har ma leke na kike yi. Kin ma mai da ni abin kallo kenan, za ki sakko ne ko kuwa sai na hawo na turo ki da ke da koton cikinki na banza mai kamar kwarya." Rabi'atu ta bude kofar dakin numfashinta sama-sama, sannan ta rike kafar benen ta ci gaba da gangarowa kasa a hankali. "Idan kin ga dama sai ki kai min ruwan wanka." Abdul ya ce da ita a fusace lokacin da ta sauko daga kan benen. Rabi'atu ta rike kafar benen. Sannan ta dafe dan matashin juna biyunta ta cije baki ta ce. "Haba Abdul, kai yanzu ko tausayina ba ka ji tuna fa tunda safe nace da kai bani da lafiya amma ka share ni ka yi tafiyarka yawo sai yanzu ka ga dama ka dawo." "To idan na zauna aikin me zan yi miki, rashin lafiyar ki ba ta shafe ni ba ke ta shafa, in kin ga dama ki tafi asibitin ke kadai in kuma ba ki ga dama ba zauna ke ta shafa, babu abin da zai sa na dora ki gaban motata, da ciki tirtsi kamar kwarya sama-sama bai yiyuwa." Ya dan yi shiru yana dubanta duban wulakanci yana kada dan mukullin da ke hannunsa. "Za ki kai min ruwan wankan ko kuwa." Hawaye ya fara kwararowa a kan kumatun Rabi'atu. "Yanzu Abdul ka san cewa da shawa fa a bandakin nan, amma kuma dan wulakanci da rashin Imani ka ce wai sai na kai maka ruwan wanka." "Kin ga ba na son rashin kunya, kada kuma ki zage ni in ba so ki ke yanzun nan ba na tumurmusa ki ke da tulelen cikinki. In ba za ki kai min ba kawai ki ce ba za ki kai min ba. Kai wallahi na auro jaraba ni na rasa masifar ma da ta sa ni ma auro ki Rabi'atu." . Rabi'atu ta fashe da kuka cikin takaici ta kifa kanta a kan kafar benen, yanzu hannayenta na rike da kofar benen. . Abdul ya nufi inda take ya turar da ita sannan ya bi kan matattakala ya haye saman benen, ba a dade ba ya sauko daga kan benen daure da tawul iya kirjinsa ya shiga bandakin. Mintuna bakwai ya gama wankan ya sauya kaya sannan ya sauko daga kan benen yana takawa daidai. Har yanzu Rabi'atu na dafe da kafar benen tana kuka. "Ki tabbata kafin na dawo kin dafa abinci, in kuma ba haka ba sai na lahira ya fi ki jin dadi, kina ji ko!". Ya buga mata tsawa. Ba ta dago koda kan ta ba, ballan tana ta dube shi, Abdul ya matso inda take cikin fushi sannan ya hada da dankwalin kanta da gashin kanta ya rike sannan ya fizgota, ta ci karo da kirjinsa, Rabi'at ta kwalla kara saboda azaba. "Wayyo Allah! Don Allah ka sake ni Abdul zaka ji min rauni...za ka ji min rauni Abdul don Allah ka bari." "Ai gara in ji miki raunin, tun da na yi miki magana kin share ni kina ji ko!". Ya sake buga mata tsawa. "I... Ina ji dan Allah ka sake ni Abdul dan Allah." Abdul ya hankadata gaba ta fadi a kan tafukan hannayenta tana kuka. Abdul ya fice yana murmushin jin dadin ya fara ramawa. Sannan ya shiga motar ya tada ita ya taka ta da gudu ya nufi kan titin da zai kai shi (Rose Mary Club) shin ko Bose kuwa tana nan ya tambayi kansa. Rabi'atu ta tashi cikin tsananin azaba ta daddafa kafar benen ta koma dakinta. Ta fada kan gado ta fara kuka. Ta yi kuka ta yi kuka har hawaye ya kare a idanunta, sannan sai ta lumshe idanunta ta Dulmiya cikin kogin tunanin mutum daya a rayuwarta, wanda ko a da, kuma har a yanzu shi ne kawai ta taba kauna. "IMRAN". Ta kira sunansa a hankali, a tunaninta kiran sunan nasa na iya sanyaya mata zuciya.**** . Hannayensa na cikin aljihunsa, sanye da bakin tabarau, karan sigari (Rothmans) na cin wuta a makale tsakanin fatar bakinsa. A haka Abdul ya shiga (Rose Mary Club) kusan duk wani matashin birni mai ji da yan kudi bashi da wani wajen shakatawa da ya wuce (Rose Mary). Tun sa'ar da ya shiga (Club) din yake hange- hange ko zai hango Bose, amma ko keyarta. Yau (Club) din ya cika tab, duk kusan teburan da ke cikin (Club) din dauke suke da Jama'a, da yawa daga cikinsu suna kora ruwan bagaja. Abdul bai kula da su ba, domin muddin zai zauna a gurin to dole ne shi ma ya dan kora, tunda shi ma yanzu ya dawo ruwa, kudi sun dawo da shi. Abdul ya juya ya dubi bayansa, inda ya ji hayaniyar dariyar mutane, wani tsohon Bayerabe ne ya sha giya ya ke ta shirme. Tsohon Bayeraben ya ja da baya taga taga kamar zai fadi sannan ya zazzaro idanu ya ce. "Can I see the light...". Mutanen da ke zaune kusa da teburin da Bayeraben ya ke suka fashe da dariya, sannan tsohon Bayeraben ya sake ja da baya ya ce. "I Can .... See...the light". Aka sake fashewa da dariya. Wasu karti su uku masu mummunar fuska kamar an sassakota daga itacen marke suka shigo (Club) din kamar an jefo su, sannan suka cakumi tsohon suka yi waje da shi. A daidai lokacin ne to Abdul ya hango Bose ita kadai zaune acan kuryar Club din. Abin mamaki kuma shi ne ita kadai ce zaune a kan teburin, kwalbar coke da kuma kwalbar giya biyu a gabanta. Abdul ya nufi gurin yana murmushi. Bose ta yi sauri ta mike tsaye lokacin da ta hango Abdul ya nufo ta. "Kada ka zo min nan wallahi kada ka maso inda na ke ba ruwa na da kai." "Ni kuwa halina da ke ke nan wallahi baki jin lallashi, yanzu Bose haka za mu yi da ke, ki tuna fa yau zuwana gurin nan goma sha daya ban ganki ba, amma duk da haka yanzu ma bayan na ganki za ki kore ni, haba Bose, Sisiliya ba ta fada miki ba ne na zazzo nemanki." "Ina ruwa na ina ma sau dubu ka zo nan kai ta shafa. Ka share kawai malam ka ji ko Bose ta yi maka nisa ga ra ma ka bar gurin nan tun wuri kada saurayina ya ganni da kai ya saye ka." Ki shi ya tokare kirjin Abdul da kyar ya ke numfashi. "Haba Bose yanzu haka za mu yi da ke, ki tuna fa irin rayuwar da...". Ta katse shi. "Abdul, ka yi min shiru bana son jin muryarka, ka kuma ishe ni da surutu, ya kamata ka kyale ni haka na sha iska, ka nace min ka nace min kamar (Chewing gum). Ka koma mana can gurin matar ka wacce ka ke so ni mene kuma na nemana, wato sai da ka gama soyayyarka da matarka, sannan ka dawo gurin banza Bose wacce ka raina. To koma can gurin matar ka da ka dawone KACI BULUS ? To Allah ya kiyaye. Abdul ya rasa abinda ke yi masa dadi, hakika yana masifar son Bose, ba zai iya rabuwa da ita ba. "Sai an jima"....ACI BULUS - 05 . Allah ya kiyaye. Abdul ya rasa abinda ke yi masa dadi, hakika yana masifar son Bose, ba zai iya rabuwa da ita ba. . "Sai an jima". Bose ta ce da shi. Sannan ta juya ta fara tafiya. Sannan ne to Abdul ya kula da cewa ashe duk Club din an yi shiru su ake sauraro. Kafin ya farga Bose ta yi tafiyarta, tana rangwada kamar reshen bishiya Acan wani bangare na (Club) din wani dan giya ya fashe da dariya sannan ya ce. "Allah ya tsinewa marar zuciya, ina ma ni ta yiwa." Abdul ya ji shi amma bai ce komai ba, sai kawai ya zauna kan teburin da Bose ta bari, ya sa giyar a gaba ya yi ta sha sai da ya yi tatul sannan ya kifa kansa a kan teburin cikin takaici. karfe biyu na dare Bose ta dawo (Club) din, Babu kowa sai Abdul shi kadai, sai kuma mai kula da (Club) din. Bose ta kama kafadar Abdul sannan ta ja shi zuwa dakinta da kyar yana tangadi. A dakin nata ya kwana a ranar. Da safe bayan ya wartsake, ta kawo masa karin kummalo, bayan ya gama sai Bose ta ce da shi. "Abdul kana sona?". "Haba Bose, ai kema kin san ina sonki". "To, indai gaskiya ne, kana sona ka jira ni, yau da yamma zan zo gidanka mu yi soyayyar mu a gaban matarka, idan ka yi haka to, ka nuna min lallai kana kaunata". Abdul ya dubeta cikin zumudi, sannan ya ce. "Ai wannan mai sauki ne." "Ai ba shike nan ba." Abdul ya dube ta ya ce "Sai me kuma?". Bose ta dafa kafadarsa, sannan ta rungume shi ta ce. "Abdul ina son bayan haka kuma ka saki matarka saki uku, sai mu koma kamar yadda mu ke a da, za ka iya?". "Wannan mai sauki ne Bose domin abin da na ke niyya kenan." Bose ta yi ajiyar zuciya sannan ta dada da cewa. "Ina son sai ka zane ta ciki da baya kafin ka sake ta". Abdul ya gyada kai, cikin amincewa. Bose ta dada kankame shi tana cewa. "Bani da wanda ya fi ka Abdul." . KASHI NA HUDU (4) SHAFI NA (30) _____________________________ Hasken ranar da ya yi wa kansa hanya ta tsakanin labulen tagar dakin shi ya fara dumama fuskarta, sannan kuma sautin. Kararrawar agogon ta fara ruri karfe takwas na safe. Rabi'atu ta yi mika a hankali gami da salati ga shugaban talikai sannan ta bude idanunta. Ta zuro kafafunta a hankali daga kan gadon, sannan ta gangaro daga kan benen zuwa tsakar gidan ta shiga bayan gida. Bayan yan mintuna ta dawo ta sa madubi a gaba tana kallon fuskarta. Abin da ta gani a jikin madubin ba karamin razanata ya yi ba kyakkaywar fuskar doguwa ma'abociyar annuri da tattausan Murmushi wacce a kullum Rabi'atu kan yi alfahari da ita, duk ta yamutse ta yi duhu, idanunta duk sun koma cikin loko. Rabi'atu ta yi sauri ta daina kallon madubin jikinta na bari. Ba zata iya jure ganin kamanninta ajikin madubin ba. Ta juyo a hankali ta fada kan gadon a rigingine sannan ta dafe dan matashin juna biyunta ta fara kuka cikin boyayyiyar murya, ba ta damu ba da ta yi yan shafe- shafen da mata suka saba yi idan sun fito daga wanka ba, domin a yau ba za ta iya ganin kamanninta jikin madubi ba. Tunanin Imran ya sake fado mata, tunanin ranar da ya zo gidansu ana sauran kwana daya kacal a daura mata aure. "Yanzu Rabi'atu shike nan mun rabu kenan duk soyayyarmu ta tashi a banza?". "Gaskiya...Imran...sai dai hakuri ka je ka nemi wata, Allah ya hada ka da wadda ta fi ni amma ni kam na yi maka nisa, sai dai ka rungumi kaddara domin gobe war haka an daura aurena da Abdul." Rabi'at ta fashe da kuka a kan gadon, lokacin da ta tuna irin yadda Imran ya fara zubar da kwalla a gabanta saboda kauna. Shin da Imran ta aura kuwa anya zai yi mata haka? Abubuwan da suka fara a yammacin jiya suka fara dawowa zuciyarta, ita daman tun sa'adda Abdul ya fice daga gidan ta san da wahala idan zai dawo ya kwana a gidan. Ko ina yake yanzu ta tambayi kanta. Sannan kamar amsar tambayarta sai aka banko kofar dakin da karfi kamar iska ta turo ta. Rabi'atu ta yi firgigit cikin fargaba ta tashi zaune sannan ta yi ido biyu da shi. Abdul ne tsaye yana dubanta, idanunsa jajur kamar garwashin wuta. "San..nu da zuwa." Ta ce da shi cikin tsoro kirjinta na dukan uku-uku. . Gabanta ya fadi domin ba irin turaren da Abdul ya saba fesawa ba ne, kuma ko da Abdul zai sake sabon turare to ta san zai yi wuya ace ya sayi turaren mata, Rabi'atu ta shaki kamshin turaren. Tabbas turaren mata ne, gumi ya fara sartu a kan dogon wuyanta, sannan a hankali sai ta nufi kofar dakin tana matsawa kusa, kamshin turaren na kara bugun hancinta. Lokaci guda sai kawai Rabi'at ta ji ta daina tsoron ko zata sami Abdul ciki, abin da kawai take so shi ne ta shiga dakin ta ga abinda ke kamshin turaren. Don haka sai kawai ta tura kofar dakin, sanan ne to ta ji kamar an soka mata kibiya a kirji. Rabi'at ta yi turus tana duban doguwar arniyar da ke kwance a kan gadonta daga ita sai siket, gashin robar da aka yi wa Bose kari da shi ya warwatsu a kan matashin kan. Bose ba ta ma san abinda ake ba. Barcinta take cikin kwanciyar hankali. Rabi'at ta ji wani abu ya tokare makogwaronta, sannan ta ji idanunta sun fara dusashewa. Cikin fushi sai ta matsa kusa da Bose ta sharara mata mari tas!!. Bose ta yi firgigit cikin razana kadan ya rage ta fado daga kan gadon. "Abdul me nene...haka." Sannan sai ta yi shiru lokacin da ganinta ya dawo sosai. Bose ta dubi Rabi'at tsaye ita ma Rabi'atu ta dubi Bose. "Ai sai ki tashi ko, tunda ba gadon ubanki ba ne." Ga mamakin Rabi'at da kuma karin haushi sai ta ga Bose ta yi murmushi sannan ta sauko daga kan gadon ta ce. "Sannu da zuwa Rabi'at daman ke nake jira ki dawo."*** . Yan matan biyu suka dubi juna, alamun tsana karara a fuskokinsu. "Kin mare ni kin ji dadi, sai dai ina son ki sani cewa baki ci bulus ba, wallahi sai na rama, sannan kuma na lugwigwita cikinki, idan kika yi wasa sai kin haife dan yanzun nan ko da lokacin haihuwarsa bai zo ba." Bose ce ke fada tana zazzare idanu. "Karya ki ke yi arniya ba kece Allah ba." Rabi'at ta ce a tsorace, tana ja da baya. Rabi'at ta san cewa idan ba dan juna biyun dake jikinta ba babu yadda Bose za ta yi da ita, to amma a yanzu idan ta biye mata tana iya halakata. Bose ta kaiwa Rabi'at cafka da karfin gaske kafin Rabi'at ta janye jikinta Bose ta rike mata riga. Rabi'at ta kawo mata duka, Bose ta kare sannan ta sa hannu ta mangare Rabi'at a fuska, sannan ta hankada ta zuwa kofar dakin. Rabi'at ta kwalla kara cikin tsananin ciwo, ta fada da baya ta yi zaman yan bori a kofar dakin kafin ta tashi Bose ta yi tsalle ta fada a kanta. "Sai na ci ubanki kafin Abdul din ya zo, shi ma kuma idan ya zo nasa shi ya kara miki." Rabi'at ta yi yunkurin tashi sai Bose ta mai da ita. Cikin Rabi'at ya motsa, ta ji numfashinta ya fara yin sama- sama. Ta sake yunkurawa, suka mirgina zuwa wajen kofar dakin da haka da haka har suka zo daf da kofar bene. Bose ta sa hannu ta shake Rabi'at. "Ina karfin naki yake yanzu, bari na kashe ki kafin ya zo, sai ya binne ki." Bose tace. "Rabi'at ta san cewa idan ta sake Bose na iya halakata, ita kuma ta san a haka bata iya fada da Bose, don haka sai ta ga abinda ya dace shi ne ta yi kokarin ture Bose daga kanta, sai ta yi kokarin sauka daga kan benen, ta san ko da Bose ta bita kasa, tana iya yin ihu a cece ta. Wannan shi ya sa Rabi'at ta tattara sauran karfinta guri guda, da kyar ta ke numfashi sannan ta yunkura da karfin gaske ta jefar da Bose gefe guda. Bose ta mike cikin gaggawa da nufin ta sake turmushe Rabi'at, Ashe ba ta sani ba, kafarta a daf da matattakalar benen na farko take. Rabi'at ta yi kokarin tashi zaune, sannan ta mike tsaye cikinta rungume da hannayenta, ta nufi matattakalar benen, sai Bose ta tsare hanyar. "Babu hanyar gudu yarinya, yau zaki fada musu sai na ga ta rashin kunya." Bose tace. Rabi'at ta yi kunan bakin wake, ta nufi inda Bose ta tare da gudu-gudu. A tsammaninta Bose zata kauce ta bata hanya tunda ta san a daf da matattakalar benen take. Yunkurin da Rabi'at ta yi sai ya zamo na kaddara, domin Bose bata dauka kafafunta suna daf da zamewa ba. Rabi'at ta bangaji Bose da gefen jikinta. Sannan ne to kafar Bose ta zame. Bose ta yi kokarin rike kafar benen sai dai kuma ta makara. Ta kwalla kara a sa'adda ta wuntsula kasan benen ta fado da ka a tsakar gidan. A nan ta baje wanwar kamar yartsanar roba. Jikin Rabi'at na rawa ta sauko cikin fargaba ta taba Bose a kafada. "Ki...ki tashi mana." Tace muryarta na rawa a tsorace, sannan ne to jini ya fara zubowa ta bakin Bose idanunta sun birkice. Rabi'at ta fashe da kuka, ta yi kisan kai tabbas ta yi kisan kai. Duk da yake ba ta taba ko da kusantar gawa ba, to amma ta taba ganin yadda idanun Balaraba kanwarta suka birkice a lokacin da Allah ya yi mata rasuwa, Rabi'at ta sake taba jikin Bose, sai ta ji jikinta ya yi lagwaf-gwaf kamar jikakken tsumma. TABBAS TA MUTUACI BULUS - 06 . TABBAS TA MUTU*** Rabi'at ta mike a hankali ta dubi hannunta sai taga jini. Hanjin cikinta ya yamutse kamar za ta yi amai Abu na farko da ya fara zuwa zuciyarta shi ne ta nemi taimakon mutane Sannan sai ta tuna Idan ta kirawo su ta ce da su ta kashe mutum Tasha jin labarin cewa duk wanda ya kashe mutum kashe shi za a yi ta sha ganin lokacin da ake harbe yan fashi da makami a talabijin tare da wasu masu laifin kisan kai Babu abin da Rabi'at ta tsana a rayuwarta irin ta buda talabijin ta ga ana harbe barayi To kuma yau sai gashi ita ma ta kashe mutum yanzu ita ma kashe ta za a yi Tsoro da fargaba suka rikita kwakwalwarta gaba daya ta rasa ma me za ta yi sannan sai wani tunani ya fado mata Tunanin shi ne ai babu wanda ya san ta shigo gidan duk inda Abdul yake a yanzu ta tabbata zai yi tunanin ba zata dawo ba sai bayan magariba to idan haka ne kuwa abinda za ta yi shi ne ta hada yan kayanta ta bar gidan idan Abdul ya dawo sai ya san yadda zai yi da ita Sai dai kuma ta sha jin labarin kwazon yansada waje binciken kisan kai ta sha jin cewa zai yi wuya ka yi kisan kai irin wannan ba tare da an gano ka ba Rabi'at ta fashe da kuka duk duniyar ta yi mata kuna Ita kam yanzu ta san rayuwarta ta zo karshe ina amfanin auren Abdul ta tambayi kanta yanzu mene ne amfanin auren mutumin banza irinsa ita kanta sai yanzu ne take mamakin abinda ya sa ta aure shi KADDARA ta amsawa kanta Sannan lokaci guda sai ta ji wata irin mummunar tsana ta shiga zuciyarta, babu abin da ta tsana a yanzu irin Abdul, dama shi ta kashe, ta huce bakin cikin da ya kulla mata, amma duk, da haka....zan rama tace cikin kuka. Sannan ne to ta yanke shashashar shawarar da ta dada jefa ta cikin masifar baki daya. Rabi'at ta lallaba a hankali ta nufi zauren gidan ta janyo kofar ta sa sakata, sanan ta dawo tsakar gidan ta dubi gawar Bose yanzu kam ta san babu tunanin kowa ni zai shigo gidan ya kama ta dumu-dumu da gawa. Yanzu abinda ya rage mata shi ne ta mai da gawar bose saman benen. A nan ake yinta lokacin da ta fara ciccibar Bose sai ta ji kamar dan da ke cikinta zai fasa ya fito saboda nauyi. Rabi'at ta ajje gawar jikinta na rawa, sannan ta zauna dirshan a tsakar gidan tana mai da numfashinta, a lokaci guda kuma tana tunanin hanyar da za ta bi ta hau da gawar sama, sannan ne to dabara ta fado mata. Ta tashi da kyar ta nufi saman benen, ta dauko tabarma, sanan ta dawo, ta warware tabarmar, ta kama kafar gawar ta janyota kan tabarmar, sannan ta nannade gawar a ciki. Ita kanta abin na bata mamaki irin yadda take wasa da gawar babu tsoro ko fargaba. Abin da ba ta sni ba, shi ne tsananin bacin rai, da kuma tsattsauran ra'ayin ramuwar gaiyar da ke zuciyarta su suka dakushe dukkan tunaninta na hankali da kuma tsoro dan haka take jujjuya gawar babu fargaba, Hakika abin na da mutukar mamaki ace mace kamarta tana jujjuya gawa yadda ta so. Bayan da Rabi'at ta gama nannade gawar Bose cikin tabarmar sai ta ruga dakin ajje kayan girke-girke, ba a dade ba ta dawo da doguwar igiya ta roba fara, sannan ta sa igiyar ta daure tsakiyar tabarmar don kada ta warware. Sai dai kuma tsayin gawar ya fi tsayin tabarmar, hakan shi ya sa kan Bose da kafafunta duk a waje suke gangar jikin tane kawai a tabarmar. Rabi'at ta dan dafe cikinta yayin da ta ji ya motsa mata, ta dan dakata ta huta sannan sai ta kama kafafun gawar ta fara ja, tana hawa benen da baya a hankali a hankali tana tafiya tana hutawa a haka har ta kai karshen benen. Mintuna biyar da faruwar hakan Rabi'at ta mai da gawar Bose kan gadonta, ta kwantar da ita sannan ta dora kan gawar kan matashin kai, ta janyo mayafi ta rufe gawar. Sannan cikin gaggawa ta harhada yan kayan da take jin za su yi mata amfani ta zuba su cikin jaka. Ta dauko jakar kudinta ta lissafa, tana da naira dubu biyar cif-cif, sun ishe ni na bar garin, ta ce cikin zuciyarta, sannan ta nufi

Chapter 2 of 6