Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
ruwan shayin, wadanda da yawa daga cikinsu duk manoma ne da leburori, wadanda kuma sukayi imani da cewa wai ruwan shayin maganin basir ne, sai ya juya a karo na farko ya dubi kyakkyawan saurayin dake tsaye a gefen teburin shayin tun kusan mintina biyar da suka wuce yana jiransa. "Uhm Hum! Malam me kake so, sai hakuri fa, kasan in mutane sukayi ma yawa sai ka rasa ma mezakayi". "Tabbas" Imran ya amsa, gami da nazarin tauyayyiyar riga dake jikin mai shayin daya tabata rabonta da ganin ruwa tun na daminar bara." "Daman dan Allah wata mace nake tambaya wacce nake tsammanin ta sauka a garinnan jiya, ban sani ba don Allah ko kai kaga inda tayi tunda kai anan kake sana'arka." imran yayi shiru yana jiran amsar mai shayin tuni gumi ya fara sartu bayansa me yiyuwa ko dan saurayin hantsin ranar daya fara dukan bayansane, babu mamaki kuma shirun da yaga duk jama'ar dake gurin sunyi suna saurarensa ne ya sashi diga ta baya kamar ledar ruwan sanyi. "Ih to, bana ce ban ganta ba, hakan kuma bana na ganta ba." me shayin yace yana kifkifta idanu kamar birdiddigi." "Domin Allah ne yasan yawan matan da suka sauka a garin nan jiya, koda yake mafi yawa daga cikinsu karuwai ne masu gudun shari'a daga birni zuwa kauye, to amma zai yi wuya na iya tantancewa ko wacece takan daga ciki tunda dai ni ba kai bane, kuma bansanta ba, sai yanzu kai daka zo min da tatsuniyar." "Farace doguwa mai kauri amma ba sosai ba, ina tsammanin kuma tana dauke da jaka." imran yace yana duban maishayin gami da addu'ar Allah sa yaga Rabi'atun. Mai shayin ya daga kansa sama yana tunane tunanen karya, domin kuwa ya tabbata matar da Alhaji Rashid ya dauka ce jiya da daddare. "To, in banda abinka ai duk kusan matan da jakunkuna suke zuwa, to amma... uhm" Ya sake yin shiru yana tunanin karya. Sannan yaci gaba da cewa, "Ina ganin naso naga wata mace jiya mai kama da wacce kake siffantawa, sai dai kuma ita waccen din wani mutum ne ya dauke ta a mota jiya da daddare, to amna kayi sa'a dannan garinne sai dai kuma a cewarsa yau zai bar garin da sassafe domin ma'aikacin gwamnatine a can birni." Me shayin ya washe baki cikin abinda yake tsammanin wai murmushi ne. "Ai kaima naga hala daga birnin ka fito ko, bari in kwatanta maka gidan kaje, ko Allah yasa ka dace, idan itace to shikenan idan kuwa ba ita bace to kana iya dawowa sai a sake bincikawa gurin yan yuniyon din can na tsangayar arewa, mai yiyuwa su sun ganta. "Yar uwarka ce ne?" *** . "Da...daga nan shine naga ni...ba...bazan iya zama ba su kashe ni da wannan cikin dake jikina shi...shine na gudu." Rabi'atu ta fashe da kuka lokacin da ta kawo karshen labarin. "Daina kuka yarnan kin ji, dena kuka in Allah yaso babu me tabaki, ai ba da gangan kika aikata ba, kaddara ce." To amma duk da hakurin da mahaifiyar Aliyu Rashid ke baiwa Rabi'atu, itama hakan kuma bai hanata zubar da hawaye ba cikin tausayawa. Aliyu Rashid ya girgiza kai cikin tausayin abinda yaji daga bakin wannan kyakkyawar mace, abinda ya kasa fahimta shine, soyayyar ta tsakanin Imran da Abdul, domin acewarta, Imran take so, kuma tace bata taba son wani ba sai shi, hakanan kuma iyayenta basu takura mata akan dole sai ta auri wanda bata so, to idan hakane kuwa menene dalilinta na auren Abdul, Babu amsa, kuma har yanzunnan daya sa Rabi'atu a gaba cikin tausayi, bai zo koda kusa da amsarba. A cikin katon falon mahaifiyar sa suke zaune, lokacin da ya dauketa a daren jiya sai yaga babu abinda zai iya yi da ya wuce ya dauketa ya kaita gidansu wato inda mahaifiyarsa take, idan gari ya waye sai ya tambayeta labarinta, domin da ganinta kai ka san tana cikin tashin hankali mara misaltuwa, wani kuma abin bakin cikin ga al'amarin da tausayi shine juna biyun dake jikinta. Aliyu Rashid yasha karanta labarai na ban tausayi, to amma bai taba ganin abin tausayin da yafi na Rabi'atu ba, koda yake lokacin da ya karanta littafin WANA KAMA har kusan hawaye ya sashi, to amma kuma wannan wani lamarine na labari, ba kamar....ACI BULUS - 13 . Koda yake lokacin da ya karanta littafin WANA KAMA har kusan hawaye ya sashi to amma kuma wannan wani lamarine na labari ba kamar wannan ba da yake faruwa a zahiri Agogon dake makale a babban falon Wanda a da can na mahaifin Aliyu Rashid ne tun kafin ya rasu ya dauki ruri karfe tara da rabi na safe "To yanzu dannan me ka ke gani zamuyi da yarinyar nan, kaga dai halin data ke ciki kuma kune a birni ban sani ba ko akwai abinda zaka yi ka taimaki wannan yarinya Mahaifiyar Aliyu Rashid take fadi Aliyu Rashid yayi shiru yana tunani na tsawon lokaci sannan yace "To, Inna wannan abu dai ba abune mai sauki ba domin abu ne da ya shafi kisan kai to amma dai gaskiya daya ce kuma Allah yana wajen mai gaskiya, ina ganin abinda zan iyayi shine zanyiwa lauyana maganar, ina ganin idan har yarinyar nan zata kai kanta ga hukuma ta baiyana duk abinda ya faru to in Allah yaso sai kaga ta kubuta, tunda dai tsaron kanta tazo yi tsautsayi yafada a kanta, da yayi sanadiyyar da yarinya ta zame daga benen ta fado, kinga kuwa..." . Sallamar da aka kwalla a waje ita ta katse kalaman Aliyu Rashid, mahaifiyarsa ta mike tsaye sannan ta fice daga falon ta nufi tsakar gidan. "Wai ana sallama da mai gidannan." Wani almajiri mai yagagen gajeren wando kamar siket yace. "wane ne kuma yake son ganin mai gidannan." "Nima bansan shi ba wallahi, amma dai ina ganin kamar daga birni yake, yaron yace yana soshe soshe kamar zai yaga rigar, "Bari to in kirawo dannan ya gano ko wanene". Ta juya da sauri ta shiga falon. "Ina zuwa Rabi'atu" Sannan ya fice daga dakin. Aliyau Rashid ya dubi kyakkyawan saurayin dauke da jaka, sannan kuma babu alamar kwanciyar hankali ko farin ciki a tattare da yanayin kyakykyawar fuskar. "Kaine kake son ganin mai gidannan?" "Nine wallahi, Alhaji barka da asuba." "yauwa barkan ka dai an tashi lafiya." "Lafiya lau." Saurayin ya amsa sannan sai yaci gaba da cewa. "Daman tambaya na zoyi don Allah ko zaku taimakeni, wata mata ce yar uwata data gudu daga gida jiya, ta zo garin nan, to shine na biyo sahunta, da na zo tasha ne aka kwatantamin gidan nan aka ce dani me yiyuwa zaku taimakamin domin wai jiya anga wani mutum ya dauki wata mata bakuwa wanda kuma akace anan gidan yake ban sani ba ko kaine?" Aliyau Rashid ya dubi saurayin cikin mamakin irin yadda gumi yake zuba kamar ruwan sama yace. "Me yiyuwa nine, me yiyuwa kuma bani ne ba, ni dai abinda nasani kawai shine jiya na sami wata mata da daddare tana barci a rumfar tasha, shine na tausaya mata naga kuma ya dace na taimaketa da gurin kwana shine to na kawota su kwanta tare da mahaifiyata, domin ni bama anan nake da zama ba, iyalina suna birni, nan dai zuwa nake yi lokaci-lokaci kamar karshen sati na gaida mahaifiyata da sauran yan uwana." "To Alhaji don Allah ko zan iya ganin waccen din, babu mamaki itace wacce nake nema"Imaran yace kirjinsa na bugawa. "Eh to, amma bana tsammanin itace, domin ita wannan bata ce dani tana da wani dan uwaba." Aliyu Rashid yace yana duban fuskarsa. "Me tace dakai tana dashi." Aliyu Rashid ya danyi murmushi sannan yace da Imran " haba Malam kana ganin ya dace na sanar dakai sirrin wani?" "Bai dace ba," Imran yace da Alhaji Rashid. "Amma don Allah Alhaji idan babu takurawa ko zaka taimakeni kace da ita Imran ne a waje yake san ganinta, idan kuwa tace bata sanniba to bani bane." Wani kuda yai tsalle ya fada kunnen Aliyu Rashid ya fara yi masa zuza a kunne Zuuu!!, hakan shiya hada da wur-wur din da kwakwalwarsa keyi tana kokarin tabbatar da abinda yaji." "Me...Imran kace". Aliyu Rashid ya tambaya bakinsa na rawa, kallo daya Imran yayiwa fuskarsa ya tabbata Rabi'atu ce a gidan." "Imran nace, kace da ita tsohon saurayinta ne." "Shigo daga ciki." Aliyu Rashid yace. "Imran, sannu Imran kaji wallahi an cuci wannan tsohuwar budurwar taka." Aliyu Rashid yace yana girgiza kai. Acan wani bangare na kofar gidan, wani mai tallar alewar dinya ya girgiza kai cikin mamaki domin jin wata siririyar murya tana shashekar kuka a cikin gidan yallabai Aliyu Rashid. "Lafiya kuwa gidan Yallabai?" Me alewar ya tambayi kansa, to sai dai kuma babu amsa sai tarin kudaje bataliya guda dake kokarin dauke farantin alewar.*** . . "Ni ban....ban...san abinda kake magana ba" Sagir yace cikin firgita muryarsa na rawa. "Kafini sainin abinda nake magana akai, ina ganin kuma ba dabara bace kaci gaba da batawa kanka lokaci da wannan kayan gawar a bayan motarka ba." Nasir Jakal yace yana murmushi sannan yaci gaba da cewa "Ni mai taimakon mutane ne...... Sagir, ni mai iya taimakon kane na jefar da gawar inda bazama a taba iya ganinta ba Domin nasan a tunaninka yanzu kokwanto kakeyi ka koma gidan Abdul ka tambaye shi dalilin da yasa gawar ta shiga but din motar ka to bari kaji Sagir idan ka yaudari kanka kabi ta hanyar nan kashinka ya bushe domin jami'an tsaro suna nan suna cakin din motocin mutane duk da yake dai ba dole bane su buda but din motar to amma zaka iya caca da hakan in zaka iya to ga hanya nan a dawo lafiya Nasir jakal yayi nuni da hannunsa zuwa kan titin yana murmushi a dai dai lokacinne agogon dake jikin motar Abdul ya buga karar goma sha daya na dare Sagir ya dubi Nasir Jakal a kideme cikin rashin fahimta duk ya rudashi hakika kuma ya gama tsorata "To...to yanzu me kake son muyi?" Sagir ya tambaya bakinsa na rawa "Ina ganin Dubu Dari Uku ta isa ta kula da dukkan wata wahala da zansha gurin jefar da gawar." Nasir Jakal yace a sanyaye yana murmushi. "O ho! Daman abinda kake nufi kenan!!" Sagir yace a fusace "Kusan haka nake nufi Sagir kuma gaskiya ina mai fargabar baka da wani zabi da ya wuce ka shiga motar ka mu koma gidan ka ka biyani karafana ni kuwa nayi maka Alkawari zan jefar da ita inda ba za'a taba ganinta ba in kuwa kaki shawarata to ina mai fargabar baka da zabi domin (Simply) ina iya kirawo kurtun dansanda yanzunnan ince dashi ya bude bayan motarka ban yarda da kai ba shin ya zaka so hakan?" Sagir ya dubi Nasir Jakal cikin takaicin, to sai dai shi ba kamar Abdul bane domin kwakwalwarsa tana tunani fiye da kima." "Mu tafi to" Sagir yace Da nasir. "Amma fa indai na baka kudin dole ne ka jefar da gawar "Tabbas-tabbas." Nasir Jakal yace cikin mamakin ganin yadda Sagir ya amince nan da nan. Mintuna goma sha daya kacal sunzo gidan su Sagir. "Ina zuwa" Sagir yace da Nasir Jakal, bayan duk sunyi fakin da motacin a kofar gidan, Nasir Jakal yabi Sagir da kallo cikin mamaki anya kuwa Sagir ba yaudarar sa zai yi ba, shifa abin ya fara bashi mamaki, haka a saukake kamar shan ruwa, tabbas kam akwai wani abu a tattare da lamarin da kesa gaban Nasir Jakal faduwa To amma lokacin da Sagir ya fito daga cikin gida dauke da bakar jaka, duk sai Nasir ya manta da fargabar sa "Gasu ni na gama sai...sai gareka" Sagir yace yana rawa da muryarsa. "Nasir Jakal ya dubi Sagir yace. "Sai ka bani makullin motarka, ni zan tafi, ga mukullin motar Abdul nan ka kai masa motarsa ni kuma gobe da safe zan dawo maka da taka motar idan na jefar da gawar". "yaushe zaka jefar da gawar?" Sagir ya tambaya. "Yau din nan da asuba." "To shikenan, don Allah Nasir ka rufa mana asiri kada kowa yaji zancen nan kaga dai ni bani na kasheta ba kuma..." "Kada ka damu". Nasir jakal ya katse shi, "Ka dai zauna kayi ta addu'ar Allah sa kada na dawo neman karin kudi." . Kafun Sagir ya tanka tuni Nasir ya fada motar Sagir ya tayar sannan ya fice daga layin da gudu ba tare daya damu daya kunna fitilar motar ba, sha daya da minti ashirin a lokacin. Sagir yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi danjar motar yayi murmushi cikin duhun daren sannan yace. Shege ACI BULUS in kasan wata baka san wata ba karamin macuci." . Abdul ya dubi Sagir a fusace cikin fushi mai tsanani yace. "Yanzu kana nufin kaima wannan dan iskan bai barka haka ba, sai da ya karbi wani abu daga gurin ka." "Ni ba wannan na tambayeka ba, na dai baka labarin ne domin in nuna maka abin da kajefa ni aciki, kai dan uwanane Abdul, duk abin da ya sameka kamar ni ya samu, ina son kasanar da ni abin da yasa ka ai kata wannan kisan kai..." "Wallahi bani bane, Allah kuwa, ni na fada maka ina baro wajen zaman makoki nazo na sameta kwance a kan gadona a mace, Allah bani na kasheta ba." Sagir ya dubi Abdul cikin mamaki, domin a yadda yaga alamun dake fuskarsa ya tabbata bashi ya aikata laifin kisan kan ba, "To wa ya kasheta, Abdul". sagir ya tambaya. "Ni ma shine nake fatan Allah ya sanar dani, wallahi ban sani ba." Samarin biyu sukayi shiru na kusan mintuna uku suna duban juna kowa na kokarin fahimtar abin dake gudana a zuciyar dan uwansa batare da sun cimma nasara ba. Sannan ba zato ba tsammani sai Sagir yace "Ina Rabi'atu?" Wani abu kamar kibiya ya soki zuciyar Abdul sannan yawu ya kauracewa bakinsa In banda yanzu da Sagir ya tambaya kwata-kwata shi a gurinsa Rabi'atu ba'a ma hallice ta ba Bala'i da tashin hankalin da ya shiga a cikin sa'o'i kusan biyar din da suka wuce su suka dauke kusan ko wanne tunani daga zuciyar sa sai na fuskar gawar Bose. . "Ba...bata dawo ba tunda ta fita "Kana nufin tunda ta fita da rana bata dazwo ba dubi fa yanzu shabiyun dare saura minti uku "Wallahi...bata dawo ba ni kuma duk mutuwar nan ta baba da kuma ta Bose dana tarar itama a mace gami da wannan dan iskan daya damfare mu su suka rudani na manta da ita." Yayi shiru yana...ACI BULUS - 14 . "Wallahi...bata dawo ba, ni kuma duk mutuwar nan ta baba da kuma ta Bose dana tarar itama a mace gami da wannan dan iskan daya damfare mu su suka rudani na manta da ita Yayi shiru yana duban Sagir amma Sagir bai ko kallo shi ba yace "Ina ganin ta dawo gidannan Abdul amma ka tambaya a makwabta me yiytuwa akwai wanda yaga dawowarta Abdul ya mike tsaye zumbur cikin fushi jikinsa na bari "Wallahi banyi tunanin haka ba kana nufin ita ta kashe Bose." "A'a ni bance da kai haka ba." sagir yace a tausashe kamar yadda liman kanyi yayin radawa jariri suna a kunnensa "Amma ba abin mamaki bane domin ka san mata abin tsoro ne musamman ma idan ta sami Bose adakinta kwance abin da daman nake guje maka kenan gashi kuma ina mai fargabar..." Babu zato babu tsammani sai Abdul yayi wuf, ya fizgi dan mukullin motar dake hannun Sagir ya ruga da gudu ya nufi kasan benen "Abdul!!" sagir ya kwala masa kira cikin kaduwa "Abdul ina zaka miye haka!" Baiko juyo ba balle ma ya kalle shi Sagir ya taso shima da gudu ya biyo bayan Abdul. To sai dai kuma ya makara domin kafin ma ya gama saukowa daga kan benen sautin injin motar Abdul ya cika shirun dake daren lokacin da Sagir yazo kofar gidan tuni motar Abdul ta harba da gudu kamar kibiya Sagir ya dubi danjojin motar biyu cikin kaduwa baki bude ba'a dade ba suma suka saje da duhun dare Sagir ya daina ganin komai sai duhun dare. Adaidai lokacin ne wani agogo mai rurin tsiya a makwabta, ya fara garam! Garam!. Karfe goma Shadaya na dare kenan a gogon Najeriya kamaru da Ghana. *** Dattijuwar Matar ta dubi Rabi'atu sannan kuma ta daga kanta a dai dai lokacin da taji motsin shigowar su Aliyu Rashid, sannan ne to shima Imran ya shigo dakin. A cikin dan lokacin sai duk dakin akayi shiru ana duban Imran, Sannan kwatsam sai Rabi'atu ta ganeshi bata taba tsammani ba shine mutum na karshe da take tsammanin zata gani a gurin "Imran" Rabi'atu ta kira sunansa sannan sai ta fashe da kuka me tsananin gaske. "Rabi'atu...daina kuka don Allah gani nazo duk abin da zai sameki sai dai ya same mu tare." "Hawaye ya fara zuba akan kumatunsa. . "Babu abin ma da zai sameku in Allah yaso." Aliyu Rashid yace. Cikin tausayi yana duban yaran biyu. A daidai lokacin ne Rabi'atu ta dafa cikinta tana cizon baki. Da farko da sun dauka zuwan Imran ne to amma can sai ta fara kuka mai tsanani tana nishi. "Wayyo...Imran....cikinq ciwo" "Rabi'atu menene kuma!!" Imran ya tambaye ta a rude. Bata amsa ba tuni ta fadi a tsakar dakin tana murkususu. Mazan biyu tare da mahaifiyar Aliyu Rashid suka mike tsaye lokaci guda suna kokarin fahimtar Abinda ke faruwa. Mahaifiyar Aliyu Rashid ce ta kama kafadarta sannan ta tabota tana salati. "Lah'ilah ha illallah, ni yasu na shiga uku wannan yarinya kuma me..." Tayi shiru bata karasa fadi ba saboda abin da ta gani mai kamar jini yana sartu kan kafafunta. "Yi sauri maza mu kaita cikin mota, ina tsammanin juna biyun dake jikinta ne ya sami matsala me yiyuwa zubewa zaiyi." Kafin ta rufe bakinta Aliyu Rashid ya ruga da gudu katuwar babbar rigar dake jikinsa tana daukar iska kamar kumbo a folo minti daya kacal ya dauke shi ya fito da zungureriyar motar daga cikin gareji. "Ku...ku kamota mu kai...ta ciki" yace dasu Imran da mahaifiyarsa da ke tsaye carko-carko kamar zakaru suka dubi Rabi'atu kwance tana murkususu. Imran ya cicibeta su kuma suka bishi a baya har sa'ar da ya kwantar da ita a bayan mota, Imran bai daina zubar da hawaye ba. Allah ka ceci ran yarinyar nan, Allah-Allah ka bata Lafiya yayi addu'a cikin zuciyarsa. Sannan ya shige gidan gaba na motar, ita kuma mahaifiyar Aliyu Rashid ta shiga gidan baya domin tana kula da Rabi'atu. "Wan...ne asibiti zamukaita" Aliyu Rashid yace a takaice gami da kunna injin motar. Gaban imran yafadi domin jin cewa za'a maida Rabi'atu inda ta gudo. "Amma...ina ganin ai da wani garin muka wuce tunda dai ga halin da ake ciki kada muje... Aliyu Rashid ya katse mahaifiyarsa ta hanyar daga mata hannu. "Kada ki damu Inna, domin ina ganin wannan itace damarta ta kubuta tunda dai kina ganin gashi yanzu in ba wani ikon Allah ba barin cikin zatayi sakamakon dukkan da Bose tayi mata. Ni ina ganin kamata yayi idan Allah ya kaimu birni na ajje ku a asibitin na wuce kai tsaye wajan jami'an tsaro na basu gaskiyar labarin, domin irin wannan gara ma ka fadi gaskiya ko kuma wayonka ya janyo maka matsala shin yanzu zata tabe ne har abada tana gudun boye kanta? . Ya sawa motar giya sannan ya tuka da gudu suka nufi birni. To sai kuma abin da Allah yayi. Imran yace cikin zuciyarsa. Har suka fice daga kauyen garin Dan'asi idonsa rufe suke yana ta sake-sake a zuciyarsa. *** Dan tsinken dake nuni da adadin manejin motar ya haura a hankali har izuwa kan dari da casa'in, da yawa daga cikin yantsirarun motocin da dare yayi musu akan titin sukan ringa sauka daga kan titin su bashi guri ya wuce baki bude. To amma duk hakan bata dami Abdul ba, domin ko manejin motar baya kallo balantana ma ya lura da irin gudun da yake. Burinsa daya a wannan lokacin ya kai ga Unguwar su Rabi'atu lallai ko shakka babu indai ya tabbata Rabi'atu ta halaka Bose, to shima kuwa zai halakata, idan kuwa ba haka ba to sai yayi mata dukan da me yiyuwa a asibiti zata karasa. Lallai Rabi'atu! Ya sake nanatawa cikin zuciyarsa, yanzu in ban.... . Tunaninsa ya katse a daidai lokacin daya hango jerin manya manyan motoci a gabansa, motocin katako ne guda uku, sannan acan gefensu kuma motar yansanda ce bakikirin da ita kamar kurtun tawada, idan ba dan hasken fitilar motar ba babu ta yadda za'ayi Abdul ya iya ganin motar a cikin duhun daren saboda bakinta. Yansandan biyar dake ta fama da binciken kola da manya manyan motocin da ke dauke dasu, suka hangi mota ta nufo su gadan- gadan kamar Alburushin bindiga. Acikin yan dakikun da abun ke kokarin faruwa babu abinda Abdul bai yi ba domin ganin ya rage gudun motar to sai dai kuma kaddara ta riga fata. Ya taka birkin motar gaba daya tayoyin motar sukayi kara kuuuu!! Sannan tayoyin motar na gefen hagu suka daga motar ta wuntsula sau biyu a sararin samaniya sannan ta sake direwa ta nufi inda yansanda ke tsaye gindin motocin katakon. Yansandan biyar sukayi tsalle gefe guda, hular daya daga cikinsu ta tashi sama kamar filfiluwa. Ba'a dade ba motar Abdul ta karaso gurin da gudun sa gashin jiki mimmikewa ta daki motar katakon garam!, sannan ta nannade kamar alkaki atake a gurin wani bangare na motar ya fara cin wuta, gangar jikin motar katakon dake dauke da kwalayen madara da buhuhuwan Omo, ya tuntsure, gami da danne karan motar dake can sama donono kamar biri, shi ya fara shekawa barzahu kafin Abdul ya biyoshi a baya. . Jama'ar da akayi hadarin a gabansu, suka dubi motar a rude suna salatin da ba karewa, ba'a dade ba sai yansandan da suka watse da gudu suka sake haduwa a gurin ana kokarin fito da dan sauran abin da ya rage na daga gangar jikin Abdul. Lokacin da aka fito da gawar sai duk yansanda da mutanen dake gurin suka dauke kawunan su a firgice da abin da suka gani. Sajan Danlami ya dubi Abdul wanda duk da yake kafafunsa biyu sun rabu da gangar jikinsa, amma har yanzu yana numfashi sama-sama, ba karamin mamaki yayi ba lokacin da Abdul ya bude idanu, yace su kirawo masa Sagir. To amma kafin ma yakara fada masu adireshin tuni ya mutu a hannun sajen Danlami. Sajen Danlami ya dubi rattakakkiyar gawar sannan ya mike tsaye ya bugawa mutane tsawa subar gurin, koda ya mike tsaye daga kan gawar sai yahango jerin gwanon motoci makil akan titin duk sun yi fakin suna kokarin ganewa idanuwansu hadarin.ACI BULUS - 15 . Sagir ya tashi firgigit a rude. Da farko da ya dauka mafalki yakeyi, domin tun sa'ar da Abdul ya fice da gudu a mota ya dawo gidan ya zauna, yana jiran Abdul ya dawo, duk kuwa da cewa bai san inda Abdul din zashi ba, to amma yasan koma ina ya tafi nan da karfe dayan dare zai dawo. Sagir ya dade a zaune yana tunane tunane, abinda ya kamata suyi idan Abdul ya dawo, yace da kansa sai suyiwa wancan dan iskan sharin da har abada bazai kara marmarin ya damfari wani ba. Nasir jakal yace dashi da asuba zai jefar da gawar, to indai kuwa hakane abin kawai da za'ayi shine ya chuna masa yansanda su cafke shi da gawar dumu-dumu a hannu. To sai dai kuma motar sa domin ba dole ne yansanda su so jin abinda ya kawo matarsa hannun Nasir Jakal. Yana wannan tunanin barci ya sace shi zaune kan kujera. Kansa a kife a kan teburin cin abincin dake dakin Abdul, Don haka lokacin da agogon dakin ya dauki jiniyar bugun karfe daya sai ya tashi firgigit, domin a tunaninsa asubace tayi, to sai dai kuma banda karan agogon acan wani bangare kuma kararrawar dake kofar gidan ce take ta faman ruri kamar zata fasa kwakwalwarsa. Sagir ya tashi a rude ya nufi kasan benen, wanne irin iskanci ne haka kuma Abdul yakeyi, in banda ....tunaninsa ya katse, ai kuwa idan Abdul ne ba zai tsaya waje yana danna kararrawa ba, to in kuwa bashi bane wanene to cikin wannan dare haka, Sagir ya bude kofar sannan yayi turus kamar wanda aka rutsa da bindiga yansanda biyar, gami da na cikon shidan mai murdadden gashin baki kamar igiya suka dubi Sagir suna muzurai. "Ka ne Sagir?" "Eh ni...ne" Sagir yace yana wasiwasi, amma in kuwa Abdul ne ya tura masa.... "Kaine Yayan Abdul?" Gaban Sagir ya fadi lokacin da yaji tambayar. "Eh nine". Sagir yace. Sannan ne to suka bayyana masa hadarin. Sagir ya dubi yansandan a rude yace. "Ab...dul ya mutu!!" "Tabbas, kana iya zuwa gobe da safe ka dauko shi yana mutuwaren asibitin garin nan." "Ku shigo ina son magana daku". sagir yace yana zubar da hawaye." *** Bakar motar yansandan ta shigo cikin asibitin a hankali, sannan kuma kurtun dansanda dake tuka motar yayi mata matsugunni karkashin daya daga cikin bishiyoyin da tafi kowacce inuwa a harabar asibitin. Kofar motar ta bude, sannan yansanda takwas suka fito, Sagir na tsaye a tsakiyarsu, kansa babu ko hula, hakanan idanunsa a kukkunbure, takalmin dake kafarsa ta hagun bashi bane a kafarsa ta dama, rigarsa duk ta cukwikwiye kamar wanda aka kwato ta daga bakin saniya. Yansandan takwas da Sagir suka nufi bangaren da mutuwaren asibitin take, yayin da majinyata dake zazzaune a gindin bishiyoyi suka bisu da kallo baki bude, Kai kace wasu halittu na daban suke kallo wadanda sam ma ba'a wannan duniya suke ba. Hakika Sagir ba karamin tashin hankali yasami kansa a cikiba. Domin a zamansa da yayi a amurka, yasha ganin mutane iri daban-daban da Allah ya jarabta da masifu iri-iri, to amma babu wacce tayi kama da tasa. Gashi dai cikin yan sa'o'i kalilan, ya rasa mahaifinsa ya kuma rasa kanensa, wannan abu da ciwo yake, to sai dai kuma babu yadda ya za'ayi abin da Allah ya kaddara sai dai addu'a. . Tun karfe tara na safe suka so suzo, to amma saboda cukucukun Kama Nasir Jakal da yansanda suka yi shiya kawo suka yi shiya kawo suka makara. Ba karamin girgiza yansanda suka yi ba lokacin da Sagir ya basu dukkan labarin abin da yafaru tun daga farko har karshe, basu bar gidan ba sai karfe biyar da rabi, acikin daren ake kawo yansanda sukayi ta gwaje- gwajensu na al'ada idan anyi kisan kai a guri. Acewar insifecto Ja'afar, wanda yai kisan shekararsa talatin da doriya yana aikin dansanda tunda yake bai taba ganin kes, mai abin mamaki irin wannan ba sai sau daya, shima wannan wata matace ta kama mijinta da karuwa a daki, to amma ita wannan mata wuta ta banka musu gaba daya suka kone suna barci Akan dole suka taho da Sagir mutuwaren badan komai ba kuwa sai dan ya tabbatar da gawar idan ta Abdul ce. To amma a gurin Sagir yaso ace bai ganshi ba, domin idan ya ganshi a halin tagayyara tunanin na iya makalewa a zuciyarsa, har zuwa karshen rayuwarsa Adaidai lokacin da yansandan da sagir ke kokarin tsallake wata magudanar ruwa dake rufe a harabar asibitin sai wata farar mota zungureriya taja ta tsaya a dab dasu Ba'a dade ba wani mutum sanye da babbar riga kai babu hula ya fito sannan wani kyakkyawan saurayi ya biyo bayansa suka bude bayan motar wata mata dattijuwa ta fito sannan sai suka janyo wata mace ranga-ranga suka nufi cikin asibitin da ita Daga inda suke suna iya jin nishin yarinyar sama sama Yansandan suka ci gaba da tafiyar su domin su ganinsu wannan ba wani sabon al'amari bane balantana ma yasa su tausayi. To amma basu fi taku uku-ukuu ba, sai duk suma suka tsaya, saboda ganin Sagir yayi turus yana duban mutanen dake dauke da yarinyar. "Me ya faru kuma?" Insfecta Ja'afar ya tambayi Sagir cikin gwarjejiyar muryarsa. Sagir bai amsa ba sai yaci gaba da kallon matar da ake dauke ranga-ranga. Sannan sai yaji gabansa ya fadi, lokacin da ya dubi fuskarta sai yaji yawun bakinsa ya kafe, numfashin sa na neman kauracewa huhunsa. Ko shakka baya yi RABI'ATU ce. Wani kuma abu daya kara bashi mamaki shine dogon saurayin, tabbas ya sanshi, to amma kuma ya kasa tuna inda ya taba ganinsa. Nan da nan Sagir ya juyo a gigice. "Yal...labai ga....tacan". Duk sai yansandan suka juyo lokaci guda suka dubi Sagir, saboda jin abin da yace." "Wa cece?" Insfecta Ja'afar ya tambaya. "Rabi'atu! Mana matarsa da nake baku labarin ita muke zargin ta kashe Bose...gatacan za'a shiga asibiti, babu mamaki juna biyunta ne ya motsa akan hanyarta ta gudun kisan...." Kafin Sagir ya karasa yansandan sun juya da gudu gudu sauri sauri sun nufi cikin asibitin wajen inda akayi da Rabi'atu. Wata yar siririyar malamar asibiti mai wuya kamar lilo tayi tsalle gefe guda ta basu guri suka wuce kusan suna fareti. "Na shiga uku ! Yau kuma me zan gani haka" ta tambayi kanta.ACI BULUS - 16 . <<<<< KARSHE 🔚 >>>>>>> . Agogon tangamemen falon karbar baki dake asibitin ya buga karfe uku na yamma. "To kungani ba laifinta bane, indai kuka duba lamarinnan." Aliyu Rashid yace da Insefecta Ja'afar. Kusan sa'o'insu uku kenan cikin dakin suna ta jujjuya maganar. Ba karamar kaduwa Aliyu Rashid yayi ba, lokacin da yaga yansanda sun zagayesu. Lokacin da suka ce dashi wanan matar suna zarginta da laifin kisan kai, sai yaga babu abinda yafi daya wuce ya bayyana musu gaskiyar al'amarin. Bayan da likitoci hudu suka hau aikin ceton ran Rabi'atu, sai insefecta ja'afar ya aje kurata uku domin suyi gadin dakin da Rabi'atu take, sannan kuma yace da sauran kurata ukun suje can su jirasu a gindin mota, shi kuma da sajen Danlami suka wuce zuwa dakin karbar baki inda suka fara sauraron labarin daga

Chapter 5 of 6