Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
gode!" Imran yace a rude sannan sai ya bude jakar wasikar ya zaro farar takardar dake dauke da rubutu cikin siraran harrufa ya warwareta. Gabansa ya yi ras!!. A saman wasikar a rubuce jimla ce kamar haka. RAYUWA TA TSANANTA A GARENI MASOYIYAR KA RABI'ATU . Wani Sassanyan gumi ya fara barkowa tun daga tsakiyar kan Imran har zuwa gadon bayansa sannan lokaci guda kuma sai wani fitinannen kuda yayi wuf ya fada cikin kunnan sa, ya fara kuka Wurrrr!!!, Imran ya kai masa duka a fusace, kudan ya tashi sannan Imran ya mari kunnensa tas!.**** . ABDUL ya Juya firgigit a tsorace ya dubi duhun yana kokarin fahimtar daga inda yar siririyar muryar take fitowa. Adacan tun wani zamani daya shude, wayar wutar lantarki ta taba jan Abdul, a lokacin baifi dan shekara goma sha bakwai ba, a tunaninsa kuma a wannan lokacin baya tsammanin a duk duniyarnan akwai wani abu mafi girgiza mutum da tada hankali daya wuce wayar lantarki. To amma sa'ad da siririyar murya ta keto cikin duhun sai Abdul ya fara shakkar tunaninsa, domin duk irin abinda ake kira girgiza a wannan lokaci to Abdul yaga abinda yafi wannan ma, wani sassanyan gumi wanda yasha bamban da ruwan kankara ya fara sartu akan doronbayansa. "Wa...nene?" Abdul ya tambaya cikin raunanniyar murya. Shiru ba'a amsa ba, amma duk da haka Abdul yana iya jin hucin mutumin. "wai wanene anan!!" Abdul yace a fusace. "Nasir Jaka ne" siririyar muryar tace. "Shin baka gane muryata bane Abdul, ko kuma rashin gaskiyar mummunan aikin daka aikata ne ya fara tambayar ka tun yanzu." "Hantar cikin Abdul ta ya mutse, idanuwansa suka firfito waje, kamar zasu fado saboda kaduwa da abinda yaji daga bakin Nasir Jakal. "Ban...bangane abinda kake nufi da mummunan aikin da na aikata ba" Abdul yace muryarsa na rawa kamar gangar jikin rubabbiyar mota. "Da sannu zaka gane abinda nake nufi ko kuma ince dakai da sannu zan kara jaddada maka abin da kasan ka aikata, kai dai kawai shiga gaba mu koma daki domin aganina cikin duhu ba gurin harkar kasuwanci bane ko kuwa me ka gani Malamin yanbariki.?" A dai dai lokacin ne yaran unguwar suka dauki ihu "NEPA!! . Kafin kiftawa da bismilla zauren da kuma cikin garejin sun gauraye da haske. Abdul ya dubi Nasir Jakal tsaye yana yi masa murmushi, irin murmushin da jami'i mai horar da yan wasan kwallon kafa kanyi a duk sa'adda yaga yan wasansa sun lallasa abokan karawarsu da ci shida babu ko daya. Kadan ya rage Nasir Jakal ya fashe da dariya sa'ar daya dubi fuskar Abdul tayi sharkaf da gumi tana naso. . Abdul ya juya ya nufi cikin gidan gwiwarsa a sanyaye, yayi mamakin ta yadda akayi har gwiwowinsa suka iya daukar gangar jikinsa. Nasir Jakal ya bishi a baya, sannan ya dada da cewa. "Shin daman abin da naji dazu ka jefar Tim kamar buhun siminti gawar Bose ce, gaskiya fa shiyasa ka hanani shiga, to don ma Allah ya horemin tunanin jiran ganin kwakwaf, da badan haka ba, da KACI BULUS Malamin Bariki?*** . Bani na kasheta ba Nasiru, Wallahi bani na kashe ta ba, kasanni ai Nasir tun muna yara yaushe zan iya kashe koda kadangare ne da ransa ballanta na mutum." Abdul yace, muryarsa na rawa a daidai lokacin da suka zazzauna a kujerun dake dakin Abdul suna duban juna. "Nasan bakai ka kasheta ba Abdul" Nasir Jakal yace yana murmushi. Abdul yaji wani dadi ya lullube shi jin cewa Nasir jakal ya yarda bashi ya kashe Bose ba. "To amma kana tsammanin akwai alkalin duniyar da zai yarda ba kai ka kasheta ba, Nasan cewa tana cikin bayan motar yayanka Sagir, ina kallon sa'ar da duk kake kokarin jefata ciki. Ta hakan da kayi ba karamar dabara bace, sai dai kuma binda kawai zanyi ka shiga bala'i shine na tashi yanzunnan na bugawa yansanda waya na sanar dasu duk abin da ke faruwa, idan nace dasu Ojo ne uban gidan Bose ya turoni na kirawo ta babu abin da zai hana su yarda dani musamman ma idan su kayi bincike suka gane cewa a daren jiya kunyi fada kaca-kaca da Bose a (Rose mary Club) me kake ji zai faru, kana tsammanin idan yayanka yaga gawar cikin but din motar sa zai kyaleka, ko kuwa kana tsammanin yayanka bai san Bose yarinyar kace ba." Nasir ya danyi shiru yana duban fuskar Abdul, a yamutse, ga mamakinsa, sai yaga kusan shekaru goma sun karu akan hakikanin shekarun fuskar a duniya. Wani dunkulallen abu ya taho tun daga hanjin cikin Abdul har zuwa makogwaron sa ya tsayar da numfashinsa cak. "Haba Nasir Jakal" Abdul yace a shashshake. "Amma ai bai kamata kayimin haka ba, tun da kasan wani ne ya kasheta, kuma ko ni nakashe ta ai kai mai rufamin asiri ne Nasir, dan Allah ka taimakeni... Don Allah..." "Kada kayi kuka, ba tashin duniya bane yazo "Nasir yace yana murmushi.ACI BULUS - 10 . "Ni mai iya rufa maka asirine idan zaka rufa nawa asirin, ni mai iya taimakon kane idan kaima zaka iya taimako na, ina fatan zaka iya taimako na, ina fatan ka gane abin da nake nufi..." Abdul ya girgiza kai cikin rashin fahimta. "Abinda nake son ka gane shine, duk mutumin da ya taimaki mutum mai yansulalla kamar ka to babu abinda zai hana shima yasa rai da dan wani abin hasafi da zai magance matsalolin sa dasu." Nasir yayi shiru yana maida numfashin sa. "Kamar me kake so...nawa kake son na baka..." Abdul yace bakinsa na rawa. Nasir yayi murmushi. "Da kyau mutumina ashe dai kana ganewa. To ina ganin zan iya rufa maka asiri, zanyi shiru da bakina, zan kuma karbi aron motar taka nabi bayan Sagir domin ganin duk yadda za'ayi na dauke gawar kafin ya ganta a ciki, (Domin indai yaganta al'amura sun lalace gaba daya)." "Nawa kake so? Abdul ya sake tambaya, zuciyarsa ta fara tunani a halin yanzu. "Dubu dari biyu da Hamsin ma Kawai ta isheni". Nasir Jakal yace kai tsaye, "Dubu nawa!! Haba Nasir ai sunyi yawa, ina zan samo su ba ka ganin nima a jikin Sagir nake ci". "Idan sun yi maka shikenan, ban damu da yadda zaka bi ka samo su ba, kai kasan hanyar da zaka bi, ko kabi dare ko kabi rana dole ne ka bani dubu dari biyu da hamsin dina ko da kuwa hakan na nufin ka saida motar ka ne. Daman na dade ina tunanin ranar da zan jefa kugiyata a makwogwaron ka Abdul, domin tunda ka shigo gari kake yi min wani gani-gani to lokaci yayi da nima zan shigo gari, kasan daman sai ta hanyar wani wani yake arziki." Ya dan yi shiru ya maida numfashi san nan yaci gaba. "Zabi ya rage naka ko dubu dari biyu da hamsin, ko kuma kwalawa su cikama gida da bakaken kaya, "Meka ce malamin yan bariki?"*** . Zazzafan gumin dake kokarin shiga idanun Imran bai hanashi ci gaba da karatun siraran kalaman dake rubuce ajikin farar takardar ba. MASOYIYARKA RABI'ATU IMRAN Ina san ka sani cewa rayuwa ta tsananta a gareni, na shiga cikin dabaibayin sarkar bala'in da ban san mai fitar dani ba, sai subahanahu wata'ala. Ba ka ga irin halin dana shiga ba Imran bani da wanda zan fadawa sai Allah sai kuma kai Imran. Dan Allah kayi hakuri Imran da dukkan bakin cikin da ka sami kanka a ciki saboda ni, sanin kanka ne Imran bani da wani abin so sai kai, kai kadai ne kuma Imran har yanzu cikin zuciyata sanin kankane Imran ban taba iya son wani idan ba kai ba, amma idan kaddara ta fadawa abu sai kaga duk ya jirkice ya sauya kamanni tamkar yadda kalanzir kan sauya kammanin ruwa. Imran tun ranar da muka rabu da kai rabuwarmu ta karshe wani abu mai suna farin ciki bai sake zuwa zuciyata ba, ni kaina ban san abin da ya sameni ba, kawai dai na farka ina mai bakin cikin dukkan abinda nayi maka, wallahi ni kaina Imran bana ce ga abinda ya sani na auri Abdul ba, ya doke ni, ya azabtar dani, ya zagi iyayena, sannan daga karshe kuma yayi sanadiyyar da tilas badon na so ba na aikata wani mummunan al'amari, al'amari akan kuskure da idan ka jishi kai kanka sai ka kyamace ni. Kada incika ka da surutu Imran, domin tuni na riga na bar garin nan, bana jin kuma zan sake dawowa sai ko wani abu na kaddara ka yafeni ya masoyina Imran, dan Allah ka yafemin ni kam tawa ta kare, daman na rubuta maka wan nan wasikane domin kawai na nemi gafarar abin da nayi maka abaya. Nasan kai mai kaunata ne a kullum, to nima ina son ka sani cewa ko bayan raina bani da wani abin so sai kai, kayi hakuri Imran, Allah ya baka wacce ta fini, shikenan Imran dan Allah kaje ka nemar min gafara ga iyayena. Sai wata rana (Darling) sai wata rana . Wani zazzafan hawaye ya kwarara akan kumatun Imran sannan ya mike tsaye cikin kunan rai ya hada takardar a hannunsa ya dukunkunata kadan ya rage yayi jifa da ita to amma sai wata zuciya tace dashi kada ka jefar A hankali sai ya cusa takardar cikin aljihun wandonsa sannan ya juya a fusace ya nufi gida, abin kawai dake ransa shine yayi sauri yaje tasha domin ya sami mutumin nan daya kawo masa wasikar ya tambaye shi inda ya baro Rabi'atu duk da yake dai mutumin ya fada masa sunan garin to amma yana bukatar hakikanin inda suka hadu da Rabi'atu Dole ne yabi bayanta Imran yace da kansa *** . Abdul ya dubi Nasir Jakal a fusace yace, kana nufin yanzu ke nan tursasani zakayi ta dole na biyaka kudin?" "To kana da zabine taimakon ka nayi fa ko dai ka kawo ko kuma ka mika dan gajeren wuyanka ga jami'an tsaro ka tuna fa ko ba'a kasheka ba dole ne ka karasa sauran rayuwar ka a gidan maza Me yiwa ko za'a sake ka alokacin baza ka ganu ba saboda tsufa, kuma TSUFAN MA na banza domin kowa ya kalle ka yasan ba tsohon arziki bane". "To....to amma Nasir Jakal, wannan shine abotar da kake nufi ina laifin na..." Nasir jakal ya katse shi. "Kada ka batamin lokaci". Nasir yace, gami da mikewa tsaye sannan ya tura hannayensa cikin aljihun shudin (Jeans) wandon dake jikin sa. "Na gaji da ciniki, ka tashi kawai ka lalubamin karafana nasan a gida kake ajje kudadenka". Abdul ya mike tsaye jikinsa na rawa, ya dubi Nasir Jakal cikin takaici, akwai wani abu a tattare da irin kallon da yake yi masa, wanda shi kansa Nasir Jakal sai da yayi tsalle ya koma gefe guda domin a tunaninsa Abdul kutufo zai kawo masa, amma maimakon hakan sai Abdul ya wuce kai tsaye ya nufi can cikin dakin. Ba'a dade ba sai Nasir Jakal yaji wani sauti Zuuuu!!, kamar ana zuge zif din jaka, nan da nan yayi sauri ya nufi cikin dakin shima. Abdul yayi firgigit gami da daga kai yana duban Nasir Jakal cikin kunan rai. "wanne irin iskanci ne kuma haka, sai ma ka....biyoni" Nasir Jakal yayi murmushi sannan ya mika hannunsa ya dauke jakar daga cinyar Abdul yaleka ciki. Yawun bakinsa ya kafe lokacin da yayi ido biyu da wazobiyoyi fal a ciki sabbbi suna daukar ido, Nasir jakal ya zuge zif din jakar a hankali sannan ya dubi Abdul. "Nawa ne a ciki?" ya tambayi Abdul. Har yanzu busashen murmushin na nan a labban bakinsa bakikirin sabo da hayakin taba. "Ba....ba zai yiyu ka tafi ba Nasir, Naira Dubu Dari Uku da goma ne, sai dai mu raba walla..." "Kada ka bata numfashin ka a banza" Nasir Jakal ya katseshi. "Domin babu abin da zaai hanani tafiya dasu, kaga Allah ya taimake ka kenan ba sai ka sayar da motarka ba." "To....to amma ai ba haka mukayi da kai ba" Abdul yace, kamar ya fashe da kuka. "Kada kayi kuka Abdul, domin Dubu Dari Uku da Goma ba komai ba ce, indai har rabuwa da ita din na nufin ka tserar da ranka, amma duk da haka zan iya kyalema kudinka idan kana ganin sunfi rayuwarka, sai dai kuma sanin kanka ne babu abin da zai hana na rerawa yansanda wakata." . Nasir Jakal ya jefawa Abdul jakar kudin tim a kirji yana murmushi, sannan yace, "Sai ka zaba Abdul, tsakanin mummunan aski da sa kai a wuta, wanne ne yafi maka." Abdul ya mike tsaye a hankali jiki na rawa, bakinsa ma rawa yake, ya rasa abin dake yi masa dadi, bashi da mafita alokacin, yace cikin zuciyarsa, mafitarsa daya ce, shine ya mikawa Nasir jakar kudin, amma yasan tabbas sai ya rama rashin mutuncin da Nasir Jakal yayi masa. Abdul ya dauki Jakar wasarairai yana jujuyata a hannunsa kamar yadda sarkin fawa kan yiwa fatar da yake tsammanin akwai huda a jikinta. "Gashi nan Nasir, na gode da abin da kayi min, bazan manta da kai ba, yanzu kam kaci nasara, to amma fa kada ka manta ba kullum take salla ba, ba kuma kullum guda ba inji matar barawo, kaje ka, na gode, kuma kada kamanta, wallahi duk wanda ya hadiyi kibiya saita tsaya masa a wuya, zamu hadu dakai Jakal, kada kuma ka dauka KACI BULUS domin kowa yaci ladan kuturu dole ne yayi masa aski, kowa ya shaki barkonon tsohuwa dole ne yayi ruwan idanu." Shima sai ya jefa jakar gurin Nasir jakal, Nasir ya cafe jakar yana murmushi. "Kada kayi fushi Abdul Lamarin kasuwanci ne yazo da haka, nayi maka Alkawarin baka biya kudin ka abanza ba, yanzu nan zanje na dauke gawar daga bayan motar Sagir, zan jefar da ita inda mai yiyuwa sai an yi wata ma ba'a ganta ba, akwai kududdufi a unguwarmu." "Nasir yayi shiru gami da mika hannun sa gurin Abdul," "Bani dan makullin motar na bishi, tun kafin ya buda lamarin ya lalace baki daya". Abdul ya laluba aljihunsa ya sake jefawa Nasir dan mukullin motar. "Ka dawomin da motata gobe da safe, fice daga gidannan bana son kara ganin ka matsiyaci" Nasir ya fashe da dariya. "Kada kayi fushi Abdul babu abinda zaka iya, ka riga ka hadiyi fatsa ta, ta kuma kamaka a wuya, baka da damar kwacewa tunda dai kai karamin kifi ne, baka kai koda karfasa ba, balle tarwada." "Fice daga gidan nan." Abdul yace cikin karaji, tuni ya gama kulewa Nasir. "Tabbas....tabbas." Nasir Jakal yace, ya juya a hankali gami da yiwa Abdul murmushin karshe, sannan ya juya da gudu-gudu ya nufi kasan benen, koda ya tabbata ya fice daga dakin sai ya dada dacewa. "Abdul kayi kokarin taramin wasu kudin kafin wannan su kare na dawo." Abdul yayi sororo tsaye cikin takaici tuni ya fara tunanin hauhawar jini zaiyi.ACI BULUS - 11 . A daidai lokacin da wani agogo a can cikin daya daga cikin shagunan dake tashar motar ya fara rurin sanar da tuzuran dake barci a ciki cewa to yanzu fa karfe daya tayi, to a daidai lokacin ne kuma wata zungureriyar marsandi ta turo hancinta cikin tashar motar. Tana shigowa tashar sai duk sauran yantsirarun motocin suka zama wani abu daban, domin in har zaka hadasu da motar da ta shigo a yanzu, to baka iya kiransu da motoci, sai ko dai kace musu sunduki da taya, ko kuma kace dasu shankwalatin bangaro, kamar yadda ungulu ta kirasu. zungureriyar motar taja ta tsaya a hankali gaban teburi wani mai shayi da yafi kowa naci a cikin masu shayin garin dan'asi. Wasu al'majirai uku, da magidanta guda biyu suna zaune akan teburin mai shayin suna hira abinsu, ba tare da sun kula da duniya ba, babu abin dake damun su sai hirarsu, hakan nema yasa basu kula da shigowar motar tashar ba har sai bayan da hasken fitilar ta ya dallare idanuwansu. "Wane ne kuma wannan." Wani daga cikin mutanen ya tambaya, "Baka san wannan ba kai kana garin nan??" Mai shayin ya tambaya. "Aliyu Rashid kenan, tsohon kwamishina ne a zamanin janhuriya ta farko, baka san babansa bane, dangidan Rashidu baduku nefa, na nan garin," " to amma da yake nima inba karshen sati ba bana zuwa garin, ba dole ne ba na sanshi". Kofar motar ta bude Alhaji Rashidu ya fito Dogo ne kakkaura baki, mai gashin baki, a iya tunanin kuma wandada suka sanshi tun yana kwaminshina, ance ba'a taba ganin sa da wasu kaya ba inba farare ba. "Assalamu Alaikum." "Ameen Wa'alaikassalam" Mutanen suka amsa baki daya, sannan duk gurin suka yi tsit, irin shirun da kakanji a yayin da malami ya shigo aji yara suna surutu. Mai shayin ne ya fara bude shirun da cewa. "Alhaji barka da dare." "Yauwa mai shayi ya kasuwa, don Allah ko yarannan masu sai da fetur sun yi barci, wallahi maina kadanne, kuma gobe da sassafe nake son na bar garin nan," yace cikin sauri, "Wallahi Alhaji duk sun tashi amma bari inje shagon su dan'asabe ina jin shi baiyi barci ba, don naji hayaniyarsu dazu suna karta." "Yauwa da ka kyauta wallahi," Aliyu Rashid ya nemi guri kusa da mutanen ya zauna akan bencin. Tun kafin duwawunsa su taba bencin sauran mutane hudun dake zaune akai suka mimmike suka bar masa bencin shi kadai. "Kai...kai miye haka, ku zauna mana meye na tashi, ku zauna mana ko ni bakwa son ku yi hirar da ni." Mutanen sukayi yar dariya cikin jin kunya da nauyin sa, na mai hannu da shuni, sannan suka zauna, amma ba'a sami mai iya sake ce wa komai ba. Bayan wasu yan dakiku mai shayin ya bullo daga can cikin duhun dare daya mamaye tashar, a kusa dashi wani yaro ne dauke da gallan din man fetur guda biyu, ya kafa bututun ya zuba man a kansa, yana tafe yana wakar mai asharalle, bai damu da komai a duniya ba,**** . Acan wani bangare na tashar wasu runfuna ne, na masu sai da abinci da rana. Babu komai a cikin rumafar sai tebura da murahun karfe na dafa abinci. To amma sabanin sauran lokutan baya, a wannan dare ba tebura bane kawai a cikin rumfunan, a cikin su harda Rabi'atu kwance akan kwali, tayi matshin kai da jakar kayanta, idanunta sharkaf da hawaye tana tacin uban kuka. Tun sa'ar data iso garin take kuka, koda yake lokacin data iso garin bata bari mutanen dake tashar sun gane kuka take ba, domin in suka gane haka, suna iya yi mata tambayar yaya akayi aka haifi uwarki, Har sa'ar da duhun dare ya fara shigowa Rabi'atu bata gama yanke shawarar ta shiga garin ko kuma ta wuce ba, to amma ita a son samunta kamata yayi ace ta dada lulukawa can cikin uwa duniya, inda babu wani abu ma da zata sake gani daya shafi gida, balantana ma ya tuna mata da mummunan al'amarin da ya faru tamkar a mafarki. Lokacin da tazo garin, sai taga ba karamin kuskure tayi ba data baro gida bata nemi gafarar iyayenta ba, da kuma tsohon masoyinta Imran. To amma ai har yanzu bata baci ba tace da kanta, A lokacin ne ta bude jakarta ta dauko takarda da biro ta rubuta wasika zuwa ga Imran, sannan ta fara duba izuwa tsalibar fuskar da zata amincewa, domin bata sakon ta zuwa ga Imran, alokacin ne to ta hango Abdussalam, ba karamar magiya tasha ba, kafin ya amince da zai kai sakon. To amma har yanzu da take kwance cikin rubabbiyar rumfar tashar tana sharbar kuka, bata taba yarda da cewa alokacin wasikar ta sami Imran ba. . Wani dankararen bera ya bugo sufa daga cikin tarkacen rumfar ya fado a kan ruwan cikin Rabi'atu Tim! Rabi'atu ta mike zaune zumbur gami da yan addu'o'in da suka iya zuwa bakinta Ita kanta tasan ba karamin hadari zamanta a rumfar ke tattare dashi ba to amma ranta ya gama baci zuciyarta ta gama rudewa rayuwarta ta dagule tunaninta ya zama kankani hakanne yasa zuciyarta ta bushe daga duk wani abu na ban tsoro bata ma damu da duk wani abu da zai sameta ba A daidai lokacin da take kokarin turar da beran daga kanta ne to hasken mota ya dallare mata idanu Aliyu Rashid yayi mamaki domin ganin kyakkyawar fuskar zaune cikin tsohuwar rumfa cikin wannan talatainin dare fargaba da tsoro suka tattokare kirjinsa domin yasan babu mamaki ma matar aljanace ke son bude masa ido Tun yana yaro tun kafin ya bar kauye ya koma birni yasha jin mahaifinsa Malam Rashid baduku na fadin labarin wani abu wai shi fatalwa to amma a yadda yaji mahaifin nasa na fadi yasan wannan ba fatalwa bace sai dai ko aljana domin ance ita wai fatalwa ko yaushe cikin fararen kaya take Duk da irin tsoron dake kokarin cin karfin zuciyarsa hakan bai hanashi tsayar da motarsa ba gefen rumfar Ya dubi Rabi'atu ta cikin gilashin motar sai yaga ta daga hannunta ta kare fuskarta wanna ce tasa ya fara tunanin ba aljana bace mutum ce to koma dai menene, sai ya sauka ya gani, wa ya sani ma ko irin matan aljannunan ne dake auren mutane suna kawo musu daloli. Aliyu Rashid ya danyi wani murmushi, lokacin daya tuna makudan kudin da aka damfari abokinsa Alhaji Rabi'u Hamza, wai za'a aura masa aljana, mai kawo kudi. Kafarsa na rawa ya nufi gindin rumfar, fitilar motar a kunne take, tun kafin ya karaso gurin Rabi'atu ta lillube jikinta da hannun mayafinta. "Baiwar Allah me kike yi a nan ke kadai?" Aliyu Rashid ya tambaya muryarsa na rawa. Bata amsa ba sai ta fashe da kuka. A can wajen mai shayi, kuna sun zubowa gindin motar ido. Suna masu mamakin abin da ya tsaida. Aliyu Rashid gindin rumfar. "Kaga fa ina jin matar nan ce ta dazu, har yanzu bata bar tashar nan ba." mai shayin yace da wani magidancin dake rike da kofin shayi shi bai kai baki ba kuma bai ajiye ba hankalinsa ya tafi ga rumfar. "Wace ce kenan kake nufi." "Haba matar nan mana wacce nake ce maka tun dazu da yamma ta sauka amma duk an watse an barta." "Oh to, na tuna kwarai kuwa kuma kaga fa inajin irin korarrun karuwannan ne dake gudun shari'a daga burni zuwa kauye, su wai a tunanin su shari'ar baza tayi wani tasiri a kauye ba, to nan ma dai korar su zamu yi gayyar tsiya, arna a idi, shari'a dai Allah ya kawo, don haka ba ruwanta da birni ko kauye ko ina aiki zata yi." Mutanen suka fashe da dariya, sannan mai shayin yace, "Mai yiyuwafa, yallabai daukarta zaiyi Ya kai ta ina wani ya tambaya mai shayin yayi dariya ce Ashe kai har yanzu bakasan shugabanninmu ba kenan da mata ai kai irin abubuwan masha'a da suke aikatawa da mata sai abin da ka gani domin wallahi kashi saba'in da biyar daga cikin dari basu da aiki sai lalata da matan banza To Allah ya kiyaye Allah ya shirye su mu kuma Allah ya karemu Sauran suka ce Ameen-ameen To amma har yanzu idanun mai shayin bai bar gindin rumfarba In badon ba badon ba, da babu abin da zi hana shi zuwa ya leko abin da ke faruwa saboda tsabar zato *** Dogon Saurayin mai fuskar matsorata ya dubi Sagir a firgice saboda ganin abin da ya gani cikin bayan motar "Na shiga uku" Sagir yace a rude yana duban saurayin Sagir ya juya ya dubin inda sauran samarin masu saida kayayyakin suke tsaye Abinda ya bashi mamaki sai yaga ko kusa ko alama ma hankalinsu bai zo kanshi ba Sagir ya tara tunanin gaggawa a cikin zuciyarsa daga nan kuma ya gane hanya mafi sauki itace yayi sauri ya bar gurin tun kafin rudadden saurayin dake gabansa ya rusa ihun da zai janyo hankulan sauran mutanen dake can gefe guda Tunanin haka ne yasa Sagir ya mai da But din motar garam Ya rufe Sannan yayi sauri yace da yaron Koma gurin kayan ka kada kuma ka sake naji labarin a bakin wani inka sake ka fadawa wani sai na raba wannan dogon wuyan naka da gangar jikinka kai wacce ka gani a but din motar nan ma sai ta fika kyan gani Kafin dogon saurayin ya gama girgijewa daga kaduwar abinda yaji, tuni sagir har yafada cikin motar ya tasheta, ya juya kan motar ya ruga a guje ya koma ta inda ya fito hantar cikinsa na rawa Dogon saurayin yayi sororo baki bude yana kallon danjar motar har sa'ar data kule yayi ajiyar zuciya lallai duk yadda akayi wannan mutun irin yan mafiya dinnan ne da yake jin labarin masu yanka mutane suyi tsafi da gangar jikinsu.ACI BULUS - 12 . Lallai duk yadda akayi wannan mutun irin yan mafiya dinnan ne da yake jin labarin masu yanka mutane suyi tsafi da gangar jikinsu, yace da kansa yau Allah ya rufamin asiri, bari inyi shiru da bakina ko nasami damar ganin sallar badi. To amma can cikin zuciyarsa yasan dole ne ko ba dade ko ba jima sai ya labartawa wani labarin, kamannin gawar kuwa daya gani kwance cikin but din motar ba zai taba barin zuciyarsa ba, yayi mamakin in zai iya barci a ranar, kai me yiyuwa ma sai ya dade yana munanan mafarkai.**** . Ba karamin namijin kokari Sagir ke yi ba, don ganin ya dafe sitiyarin motar, domin tun daga dan yatsan kafarsa, har zuwa gashin kansa rawa suke, Abdul, me kuma Abdul ya zama? Me Bose ta yiwa Abdul ya kasheta? Me Abdul ke nufi da ya boye gawar Bose cikin but din Motata? Ashe yanzu duk irin abinda nake yiwa Abdul wannan shine abinda zai saka min dashi Haka yayi ta jerawa kansa tambayoyi iri-iri amma babu amsar koda ta farko balanta kuma ta karshe Adaidai lokacin ne to ya hango lambar motar Abdul, cikin hanzari ya zuro hannunsa ta cikin tagar motar yana yiwa Abdul alama da ya tsaya. Nan da nan motar ta rage gudu sannan a hankali ta sauka gefen titi, shima yayi fakin guri guda, sannan sai ya lankwasa kan motar ya koma can bangaren motar Abdul, yana zuwa ya taka burki kusa dashi ya tsaya, sannan Sagir ya bude kofar motar cikin fushi jikinsa na digar da gumi kamar ledar kankara. Sannan a hankali sai kofar motar Abdul ta bude, sannan dan kakkauran saurayin daya sanya shudin wando (Jeans) da farar riga ya fito. "Barka da war haka Sagir." "Ina zaka ne naga kana zuga wuta haka, kamar zaka birnin Caina?" Nasir Jakal yace yana busashen murmushin sa, Sagir ya dubi Nasir Jakal cikin kaduwa yace. "I....ina Abduul!" "Wallahi yana gida yana hutawa abinsa cikin nitsuwa da kwanciyar hankali" "Nasir Jakal yace, har yanzu murmushin na nan makale a fatar bakinsa. Akwai wani abu a tattare da murmushin da ya fara baiwa Sagir Tsoro, domin duk sa'ar da Nasir Jakal yayi murmushin sai ya dubi fuskar Sagir, sannan kuma ya dubi but din motar Sagir, to a wannan lokacin kuwa idan akwai wani abu da zai ta dawa Sagir hankali fiye da komai a duniyarnan to shine wani yayi kokarin koda taba but din motar ne. "Ab...Abdul...din yana gidane?" "Acan dai na baroshi" Nasir Jakal ya amsa kai tsaye, Sagir ya fuskanci idan ya biye ta wannan sakaran saurayin abokin Abdul dake gaban sa to ko shakka babu kwabarsa ruwa zata yi. Domin ya tabbatar nan ba da dadewa ba. Sandararriyar gawar dake but din motar zata fara wari. Kuma koma ba zatayi komai ba, to hadarin dake tattare da gawa a bayan motar mutum to bambancinsa kadanne da kuma ashana a gaban tankin fetur. "Sai ka dawo" Sagir ya ce a takaice. Kafin Nasir Jakal ya farga tuni Sagir ya shiga motar sa yana kokarin take totur. "Sagir!" Nasir Jakal ya kira sunansa, ba kiran sunan ne yasa Sagir sandarewa cikin fargaba ba, sai irin yadda muryar Nasir tayi kiran sunansa shiya sa shi fargaba, musamman da yaga har sa'ar daya shiga motar Nasir Jakal na nan tsaye bai motsa ba, hannunsa na hagun na saman motar Abdul abokinsa. Sagir ya dubi Nasir Jakal a firgice, kafarsa daya a cikin motar, daya kuma a waje, "Mene...ne?" Ya tambaya, cikin fargaba, bakin Nasir jakal ya sake washewa cikin sabon murmushi, Sagir ya kufala ransa ya baci, wai shin me zaisa wannan saurayin ya sashi a gaba haka ne yana tayi masa dariya kamar wani mahaukaci. "Kaga in baka da abin fadi ni zan tafi kaji ko!! Kada ka batamin lokaci". Sagir yace a fusace. Nasir Jakal ya fashe da dariya sannan yace. "Kada kayi fushi Sagir (Cool down) in bata lokaci kake gudu, ka gamu dashi domin kuwa ina ganin ba da bara bace ace ka ratsa ta tsakanin yansandan can na kan danja masu cakin din motocin mutane da wannan abin a bayan motarka." Sagir yaji kamar an sokeshi da mashi a kirji, "Me kake nufi!!" Sagir yace a rude cikin fusata, "(Cool down)" Nasir ya sake cewa a karo na biyu yana murmushi. "Kayi a hankali Sagir, ko so kake ka tara mana jama'a da wannan sandararriyar gawar yar budurwa dake but din motar ka?" . Mai shayin ya ajje kofin shayin dake hannunsa kwaf akan tsohon teburin dake lillibe da leda shudiya, gami da nazarin mutanen dake zazzaune akan dogon bencin mai kamar makara suna kukkubar ruwan shayin gami da zazzare idanu. Domin da yawa daga cikin kwastomomin da suke zaune gindin teburin shayin badon dadi suke sha ba, sai don sabo, wasu kuma a tunaninsu wai burgewace a ganka a garin Dan'asi da sassafe kamar haka kana shan shayi, koda kuwa dandanon shayin bashi da bambanci da ruwan gishiri da sukari. Bayan da mai shayin ya tabbata duk kusan kwastomomin dake gurin sun wadata da

Chapter 4 of 6