Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ACI BULUS - 01 . (c) Nazir Adam Salih . . "Ni ban ce da ke mummuna ne ba. Yana da kyau daidai gwargwado. Abin dai kawai da nake so da ke shi ne ki bambance tsakanin karya da gaskiya." yan matan biyu suka dubi juna na dan lokaci. Sannan wankan tarwadar ta dubi farar ta ce. "Me kike nufi ne Asma'u? Ni fa na kasa gane wannan soki burutsun naki. Ban san abinda imran yayi miki ba bakya son sa". "ba wani haka bane Rabi'atu. bawai bana son sa bane. Abinda nake so ki gane shine duk son da nake masa bai kai wanda nake yi miki ba. Ke kawata ce tun muna yara. Dole ne na shawarce ki ga bin duk abinda nake ganin ya dace ki bi domin amfanin kanki haka ma na hane ki ga barin duk abinda nake ganin zai cutar da ke". Asma'u ta yi shiru tana maida numfashin ta san nan ta dubi Rabi'atu ta ce. "Yanzu ke kina tsammanin imran zai iya auren ki kuwa? Dan makaranta ne fa, karambani ne kawai irin na yaran samarin nan mayaudara, yanzu ke in banda lalacewa ina ke ina kula wani imran, wanda ba shi da wani (hope) a rayuwa, ba fa dole bane in ya gama makarantar ma ba ya sami aikin da zai iya rike ki, kuma kina nufin yanzu jiransa za ki yi har sai ya gama karatun kuwa me kike nufi?". Asma'u ta dubi Rabi'atu, sannan Rabi'atu ta dubi Asma'u ta girgiza kanta cikin damuwa. "Asma'u, ina son ki sani cewa idan har babu wata mafita, to dole ne na yi jiran nasa har sai ya gama domin Allah ne mai komai, bana jin zan iya zama da wani da namiji in ba shi ba, domin shi na ke so kuma na tabbata shima yana kaunata tsakani da Allah." "Kin dai bani kunya wallahi". Asma'u ta ci gaba da cewa. "Amma kina da aiki, sai ki yi ta jiran nasa gani ki ka yi za ki iya idan kikayi wasa kuma, wallahi sai ya gama makarantar ya sauya wata budurwar kinga daga nan sai ki hakawa kan ki kabari, ki shiga a binne ki tunda kuwa kin ce baki iya zama da kowa sai shi, to idan ya mutu fa yaya za ki yi...". "Ba zai mutu ba Asma'u, kinga ya ishe ki, wane irin fata ne kuma haka na mutuwa." Ama'u ta fashe da dariya, har da kyakyatawa. * "Iye!! Harma wani kare shi kike yi, ke dai wallahi har yanzu bagidajiya ce, sau da yawa ki kan bani mamakin abinda kika gani a jikin Imran kika like masa haka kamar cingam, ga wani can kullum yana fama da ke amma ko gaisuwa kin ki tsayawa ku yi". "Kina nufin Abdul?". Rabi'atu ta tambaya. "Ashe kina iya ma rike sunan sa daman da gangan ki ke walakanta shi saboda Imran...". "Kin ga ni ba wulakanta shi nayi ba, ke wallahi Asma'u kin cika sharri." "Ah! To sharri ne, in gaskiya ne to idan ya zo yau a kula shi mana kamar kowa." Asma'u ta yi shiru, gami da yar boyayyiyar atishawa, sannan ta dada da cewa. "Rabia'tu ya kamata ki yi wa kan ki fada ya kamata ki daidai ta tsakananin Imran da Abdul, na sha fada miki Abdul din nan so yake ya aure ki, duk da yake dai shima ba wani hali yake da shi sosai ba, amma shi yana da (hope) domin ina tabbata miki da cewa nan da wata hudu zai shi go gari. Amma ke kin nace wa Salula, tsammanin warabbuka wai malam ya ki noma don zakka. Wallahi Rabi'atu duk cikin samarinki babu wanda ya ke sonki da aure kamarsa, ke ce dai ba ki sani ba, kuma kin ki ma ki saurare shi ballantana ki gane manufarsa. To kanki, ni dai shawara na ke baki ba wai don Abdul dan'uwana ba ne, ni dai kawai ina ganin kamar shi ya dace da ke." Asma'u ta mike tsaye ta gyara daurin zaninta sanan Asma'u ta mike tsaye ta gyara daurin zaninta sanan ta ce. "Ni zan tafi, amma don Allah Rabi'atu idan Abdul ya zo gobe ki saurare shi, bai dace ba a ce kina share shi a gaban Imran, ke baki san halin samari ba ne, wallahi in kika sake Imran ya gane kina kaunar shi kin gama yawo. Ke ko irin gwajin nan ma kin ki ki yi masa irin wanda ake yi dan ki gane ko yana kaunar ki ko baya yi. Share shi za ki yi na kwanaki biyu sai ki gani, idan ya share ki ya ki ya lallabe ki to wallahi ba kaunar ki ya ke ba." * "Kai Asma'u ke kuwa kamar shedaniya. Ai ni wallahi da kyar zan iya yiwa Imran haka, domin tsoro nake kada ransa ya baci kuma ina kaunarsa kinsan....". "To shike nan daman shawara ce, tunda kuwa kin ki sai ki je ki yi ta zubar da mutuncin naki gabansa." Asma'u ta ce cikin fushi. Rabi'atu ta dubeta ta ce. "Ke kuwa abina da ke kenan wallahi saurin fushi ni ban ce ba zan dauki shawarar ki ba, ai ciwon ya mace na ya mace ne." "Ashe dai kin gane yar gari. To tunda dai kin fara gane abinda nake nufi daga yau sai Abdul ba Imran ba kayansa." "A'a... Shima zan ke kula shi ai ba...". "Ba cewa nayi ki daina kula shi ba, amma abin da za ki yi masa shine kafin ki kula shi sau daya ki kula Abdul sau bakwai, kin gane ai . "Na gane." Rabi'at ta ce, zuciyarta na wasuwasi, anya kuwa za ta iya yiwa masoyinta Imran haka, sun dade da shi kuma ta san yana matukar kaunarta kamar ya hadiyeta, a kullum ba shi da wani zance sai na ya aure ta, to amma ta kance da shi da sauran lokaci, to kuma sai gashi katsam wani yana shirin faruwa anya kuwa za ta iya. "Ni zan tafi, sai jibi zan dawo na ji yadda kuka yi da shi Abdul din." Sannan ta dubi Rabi'atu ta yi murmushi lokacin da ta nufo kofar dakin Rabi'atu, na biye da ita a baya. "Ko ke fa Rabi'atu, amma a ce kyakkyawa kamarki ta rasa wanda za ta kula wai sai wani marar mamora, wai Imran, ni wallahi har kunya nake ji naga ya zo gunki zance a tsohon keken nan mai kamar dokin kara." Yam matan biyu suka fashe da dariya. Rabi'atu ta kaiwa Asma'u duka a baya. *** * Abdul ya shafi gashin bakinsa sannan ya sake kallon fuskarsa a cikin madubi, a kalla dai shekarunsa basu nuna ba karara a fuskarsa, in ka dauke jajayen idauwansa kiri-kiri da su babu wanda zai iya zata ya kai shekara talatin da bakwai a duniya. Abdul gajere ne wankan tarwada, zai yi wuya ka iya karanta abin da ke kunshe a zuciyarsa ta hanyar duba fuskarsa. Domin in har da fuskarsa za ka yi amfani to kana iya zabarsa a matsayin babban limamin masallacin unguwarku, amma a zuci, zai baka mamaki, domin an dade a duk fadin unguwar ba a sami cikakken dan bariki ba kamarsa, kwararre ne wajan kora ruwan bagaja, sannan kuma kartagi ne gurin caca, sai dai yanzu ana iya cewa sambarka ya dan shiryu, tunda dai ya daina caca da shan giya, abu daya ne kawai bariki ta barshi da shi, shi ne neman mata, wanda abin ya zame masa kamar jaraba, hakan shi ya sa shi shantake kafafu, ya ci gaba da tafka aikin masha'a. To kuma katsam, sai abin hangen mata, ya hango masa Rabi'atu. Tun sa'ad da ya dora idonsa a kan ta ya dauki aniyar ko ta yaya sai ya mallake ta, kai ko da auren ta nema yana iya yi. Shi kansa abin yana bashi mamaki ba don komai ba kuwa sai don tun da yake a rayuwarsa bai taba tunanin aure ba, kai shi a tunaninsa ma mata irin na aure ba su san mene ne rayuwa ba. Katsam rana guda Rabi'atu ta sauya tunaninsa, tun da ya ganta ya ke fatan mallakarta, bai damu ba da cewa Rabi'atu tana da wanda ta ke kauna tun kusan shekaru hudu da suka wuce, ya san cewa ko da na ci da bin malaman tsibbu sai ya yi nasarar mallakarta. Ba karamin girgiza ya yi ba, lokacin da ya ga ya gama nacin duk a banza, Rabi'atu ko kallo bai isheta ba, gashi kuma kullum sai masifar kaunarta ce ke shiga zuciyarsa, hakan shi ya sa shi yanke shawarar da bai taba tsammanin a da zai yi ba. Lokacin da Abdul ya fuskanci ya gama duk abin da zai iya yi, ya kuma gama kaskantar da kansa gare ta amma sam abin ya ci tura, kuma abin bakin ciki ma shi ne kusan duk sa'ad da ya je gurin Rabi'atu, ba za ta tashi wulakanta shi ba sai a gaban Imran wannan abu ya kona masa rai matuka. "Sai na rama, wallahi sai ta san ni ta ke yiwa haka". Abdul ya yi wa kansa alkawarin hakan. Kusan malaman tsibbu goma sha biyar ya baiwa kwangilar Rabi'atu, yau ne kuma ranar da aikin ya kammalu, dan haka lokacin da Asma'u ta zo ta ce da shi ai yau mutuniyar sa wato Rabi'atu ta ce ya je, sai farin ciki ya lullube shi domin ya san malamansa sun cimma nasara. Sai kuma ta je gidan za ta gani. Ya ce da kansa sai na gana mata irin azabar da ta gana min. Abdul ya mike tsaye ya janyo farin kambas dinsa daga karkashin gado ya sa, sannan ya gyara shimfidar gadonsa ya matsa gaban madubi ya sake gyara gashin bakinsa, sannan ya gyara shimfidar gadonsa, ya sake matsawa gaban madubi a karo na biyu ya gyara gashin bakinsa, sannan ya yi wa kansa murmushi, a daidai lokacin da aka turo kofar dakin babu sallama, a ka shigo kai tsaye. "Some body got to die!!" Mai shigowar ne ke fadi cikin shakakkiyar muryar da kan iya tsorata yara a tunaninsa, wai waka yake yi. Abdul ya juya cikin sauri suka yi ido biyu da Nasiru jackal. Nasiru jakal shine babban abokin Abdul tare suke sheke ayarsu a doron kasa. "Ina kuma za ka na ga kana wani shirye shirye, ba dai wajan mara kunyar yarinyar nan za ka koma ba?". Abdul ya yi murmushi sannan ya ci gaba da goge takalminsa da wani farin tsumma. "kai ma ai ka sani". "Na san me, kana nufin gurin nata za ka koma kai fa wallahi kamar kare ka ke baka da zuciya, Haka kawai za ka bar wata yar cilikowar yarinya karama tana juya ka yadda ta so kamar wata waina, idan ba ka sa ni ba Abdul bari yau na fada maka, duk abokanmu sun tsane ka saboda wannan yarinya, kai ba aurenta za ka yi ba, to mene ne na nace mata, sanin kanka ne ba irin matan mu bace to kuma mene ne na bata lokacinka." "wa yace maka ba aurenta zan yi ba." Abdul ya katse shi. Nasiru Jakal ya dube shi sororo sannan ya ce. "Amma kuwa ka hadu da wahala, kuma ka bani kunya, kana nufin kenan ka jefar da kambunka, yanzu a kan wannan yar cilakowar zaka wani...ACI BULUS - 02 . Kana nufin kenan ka jefar da kambunka, yanzu a kan wannan yar cilakowar za ka yi wani abu wai shi aure?" Abudul ya yi murmushi sannan ya dubi jakal ya ce "Dan haka ko yaushe nake son ka rika girmamani, a matsayina na Malaminka a harkar bariki, Abinda na ke son ka gane shi ne a duk sa'adda ka nemi mace iya kokarinka, amma taki ka, ta kuma nuna maka matsayinka a gaban wani karamin kwaro, to kada ka ce za ka yi fushi domin idan ka yi fushi ka rabu da ita, ta gama da kai domin ta bata (record)". Abdul ya dan yi shiru yana mai da numfashi sannan ya ciji fatar baki ya ce da jakal. "Abin da ake yi musu shi ne, sai ka lallaba su su zo hannunka, kada ka yi fushi duk irin wulakancin da za ta yi maka sai ka daure ka nace kota halin kaka sai ta zo gurinka. Da zarar ta zo sai ka nuna mata kai ka fita iskanci! Sai ka ribanya abin da ta yi maka sau biyu." Abdul ya dubi Jakal yana murmushi sannan ya ce. "Wallahi, idan Rabi'atu ta zo hannuna sai na ribanya wulakancin da ta yi min sau babu iyaka...". "To kai da kake ta wannan shirmen ta zo hannun naka ne? jakal ya tambaye shi. Abdul ya fashe da dariya. "Shi ya sa Jakal akullum nake yi ma ka kallon dabaibayi duk da yake kai kana yi min kallon turke. To bari in fada maka Rabi'atu kamar ta zo hannuna ne." "Ta yaya bayan ko kula ka bata yi?". Nasir Jakal ya bukata "Yanzu kuwa za ka gani". Abdul ya amsa, sannan ya durkusa karkashin gadonsa ya janyo wata tsohuwar jaka ya bude ta, daga cikinta ya fiddo da wata kwalba fara mai dauke da garin wani magani bakinkirin, sannan ya dan bubbuga gindin kwalbar a gefen katakon gadonsa. Wani farin hayaki ya yi tsiri sama daga cikin kwalbar, ya hada wani dan karamin gajimare a sararin samaniyar dakin. Nasir Jakal ya yi tsalle gefe guda cikin fargaba. "Kada ka ji tsoro Jakal wannan gwaji ne kawai na yi maka yanzun nan zan bunne kwalbar, daga nan kuma sai gurin Rabi'atu, ina tabbatar ma ka da cewa binne kwalbar nan, kamar binne soyayyar Rabi'atu da Imran ne, soyayyar su kuma daga yau sai dai tarihi." Abdul ya sake murmushi a karo na biyu, lokacin da ya dubi fuskar Jakal ya yi sharkaf da gumi, kamar ya yi ido biyu da fatalwa. Za ku gani jakal, ba ku na yi min dariya ba ku da (Friends) abokai, wai har ma kin rakani kuke yi gurinta wai kada ku wulakanta to ai shike nan, wannan shi ne bambancina da ku a harkar bariki, ku ci gaba da dariyar ku ku na ji kuna gani ZAN CI BULUS ku na shirme." Ya fashe da dariya, sannan ya nufo kofar dakin kwalbar, har yanzu farin hayakin bai daina fita daga cikin kwalbar ba. Nasir Jackal ya bi shi da kallo. Tabbas ya yi gamo da aljannu ya ce cikin zuciyarsa. * PART (2) PAGE (17) ________________ Imran ya daga kansa sama yana duba izuwa ga wani dan kankanin tsuntsu mai doguwar jela, launin rawaya da shudi. Tun sa'ad da suka zauna gindin bishiyar tsuntsun ke ta rera wakoki cikin wani irin yare da Imran bai iya ganewa. Imran ya so ya tashi tsaye daga kan kujerar da yake zaune domin kawai ya karewa tsuntsun kallo, to amma irin Halayyar da Rabi'at ta zo masa da Ita a yau bai bari Imran ya kula da dan tsuntsun. Bishiyar da suke zaune a karkashinta ita ta fi kowacce bishiyar inuwa da kyawawan furanni a duk fadin farfajiyar gidan su Rabi'atu. Imran ya muskuta daga kan kujerar sannan ya zaro wani farin kyalle daga aljihunsa ya goge gumin da ke kwararowa tun daga goshinsa har zuwa gadon bayansa. Imran ya dawo da hankalisa kan Rabi'atu wace ke zaune a kan kujerar dake gabansa kanta a sunkuye tana wasa da ganye a hannunta. "Me ke damun ki ne yau Rabi'atu, ni na ga duk hankalinki baya gurin nan." Rabi'atu ta dube shi ta tabe bakinta ta dauke kanta gefe guda. "Ni babu abinda ke damuna." "Babu abinda ke damunki, amma kike irin wannan tunane-tunane haka?". "Ba komai wallahi, don kaga na yi shiru, kawai dai na...". Ta karasa abinda take son fadi a ciki. Imran ya dubeta cikin damuwa ya ce. "To ai gani na yi tun da muka fara hirar nan baki fadi jimla ta kai goma ba, sai dai kawai in na tambaye ki ki bani amsa. "Ni kawai babu abinda zan ce ne, idan akwai abinda zance ai da na fada." Ta tabe baki ta sake sunkuyar da kanta kasa ba tare da ta dube shi ba. "Abin ne yau ya ke bani mamaki Rabi'atu, kin ga da idan na zo, ki kan yi kokarin fadin duk kalmar da za ta faranta min rai. Wasu lokutan ma ko magana ba kya bari na na yi sai dai na yi ta sauraron muryarki abar kaunata. Amma yau na rasa abinda ke damunki." "Idan ka san haka ne kuma mene ne na damun kanka, ni nace da kai babu abinda ke damuna, amma kai sai mita kamar maroki." Imran ya dafe kirji cikin kaduwa, ba abinda ta fadi ba ne ya sa shi kaduwa, irin muryar da tayi amfani da ita tafi sashi kaduwa. "Ra.. Rabi'atu me ki ke yi min irin wannan maganganu, don kawai na tambayi abin da ke damunki." Ya dan yi shiru yana sauraron ko za ta ce wani abu, to amma bata ce uffan ba. "ko kin fara gajiya ne da ni Rabi'at." Wannan ya sa ta daga kai ta dube shi sannan ta yi far- fari da fararen idanunta ta tsuke baki ta ce. "kai ka sani ni dai ba a bakina ka ji ba. Bai kuma dace ka fadi haka ba, domin sanin kanka ne duk cikin samarina babu wanda nake kauna sama da kai ko karya ne Imran?". Imran ya rasa abinda zai ce saboda kaduwa tunda suke da ita ba ta taba fadin sunansa haka ba kai tsaye. Sai dai ko idan ba ya gurin. "To shike nan Rabi'atu...ni daman abin da nake gudu shi ne yin soyayya bisa takurawa." "ASSALAMU ALAIKUM." Aka yi sallama Gabadayansu suka dago kawunansu Suna masu duba izuwa inda aka yi sallamar. "Asma'u manyan gari." Rabi'atu ta ce. "Oh! Rufa min asiri, manyan gari ai sai su Imran." Asma'u ta ce tana dariya. Sannan ta dubi Imran ta ce. "Malam Imran Ina wuni?". "Lafiya lau, Asma'u." Ya amsa. Asma'u ta dubi Rabi'atu sannan ta ce da Imran. "Don Allah in babu takurawa bari in dan gana da ita mana minti biyu." "Ah! Haba Asma'u babu komai ku je mana." Imran ya ce yana murmushi. Abin da bai sani ba shi ne Asma'u tare suka zo, da mutumen da zai kawo karshen soyayyarsu da Rabi'atu, sannan kuma murmushin da ya gani a fuskar Rabi'atu lokacin da take tarbar Asma'u shi ne murmushi na karshe da zai sake gani a fuskar abar kaunarsa, wacce a kullum ita ce a ransa kuma abin da yake fatan ya zauna tare da shi har iya tsawon rayuwarsa, to amma ba haka kaddarar ta kasance ba. Rabi'at ta bi Asma'u a baya Imran yana kallonsu, bai sani ba ashe kaddara ce ke tafe da abar begensa.***** * Imran ya dubi agogonsa ga mamakinsa sai ya ga kusan mintuna ashirin kenan da tafiyarsu Rabi'atu. A dai dai lokacin da ya fara tunanin ko lafiya ba su dawo ba, sai ya hango Rabi'at ta nufo cikin lambun. Bayan yan dakiku ta karaso ta tsaya a gabansa kikam kamar tabarya ba ta ce da shi komai ba. "Zauna mana." Ya ce zuciyarsa kamar ta fashe saboda bacin rai. "Gaskiya Imran sai dai ko ka tafi ka dawo domin yanzu akwai abinda zan yi don haka ma kaga na dade, kar ka ce na wulakanta ka." Imran ya mike tsaye cikin bacin rai, sai dai duk abin da ke faruwa bai bari ba ya nuna a fuskarsa. "Sai yaushe kenan." Ya tambayeta. Ta dubi tafukan hannayenta sannan ta ce cikin gadara. "Rana ya ta yau ko, sati daya kenan." Imran ya ji kamar ya yanke jiki ya fadi. "Haba Rabi'at, yanzu ashe har kina iya jure sati guda baki ganni ba? Lallai kaunar ki tana da rauni a kaina, ni wallahi ban iya sati guda ban ganki ba." "Haba dai, bayan kullum muna tare, dan yau kawai haba ai ka manta kawai rana ya ta yau sai ka dawo wallahi zamu yi wani biki ne dan haka na ce maka sai bayan sati daya ba na son ka zo ne ka tarar bana nan ko ina wani aikin "To amma Rabi'atu ace duk cikin kwanaki bakwai din ki rasa wata rana guda da za ki saurare ni? Ta tabe baki sannan ta dan yi taku biyu gaba kamar za ta tafi ta ce To ai shike nan tun da baka yarda ba ni zan tafi sai ka zo din." Kafin ya gama jin abin da ta fada tuni ita ta yi nisa ta nufi katon falon gidan da ke fuskantar Lambun. Imran ya bita da kallo cikin kunan rai ga mamakinsa, sai ya ji hawaye ya fara sartu a kan kumatunsa, ya yi sauri ya goge fuskarsa da kyallen da ke hannunsa. Ya juya a hankali ya dago tsohon kekensa da ke jingine a jikin daya daga cikin bishiyoyin lambun, sannan ya tura a hankali ya nufi kofar da za ta fita...ACI BULUS - 03 . . Ahankali ya dago tsohon kekensa da ke jingine a jikin daya daga cikin bishiyoyin lambun, sannan ya tura a hankali ya nufi kofar da za ta fitar da shi waje. Da ya san abinda ke faruwa a kusa da shi, dan wasu tattaki kawai to da sai ya fadi ya mace don bakin ciki. A tsaye a jikin gilashin tagar falon suna lekensa Asma'u ce da Rabi'atu. Asma'u ta yi murmushi ta ce cikin dariya. "Sangali kenan, kin ji kuwa yadda keken ke kara kamar injin nika." Rabi'atu ta sunkuyar da kai zuciyarta ta dan sosu da ta ga Imran ya fice daga cikin lambun jikinsa a sanyaye. Ta girgiza kan ta cikin fargaba, anya kuwa za ta iya yiwa Imran haka. To amma duk wannan tunanin kafin Asma'u ta kai ta ne ta yi ido biyu da Abdul wanda ke can zaune a babban falo. Yana jiran ta kawo masa Rabi'atu.**** . "Wallahi Rabi'atu babu abin da na fi kauna a duk fadin duniyar nan da ya wuce ace yau na aure ki, idan har zan samu hadin kanki to a shirye na ke da a daura mana aure cikin satin nan ma idan kin so." Abdul ne ke magana cikin kwararriyar muryarsa ta mayaudara. Kusan sa'o'i hudu kenan yana ta shirya wa Rabi'atu laccar shaidan. Tuni Asma'u ta dade da tafiya, amma kafin ta bar gurin sai da ta tabbatar da Abdul ya shiga har cikin gidan ya gai da mahaifiyar Rabi'atu, watau Hajiya Ramatu. Sannan ta juya ga Rabi'atu ta ce da ita cikin rada. "To inji dai mai kyau, ba na tafi na bar ku ba, saura ki wulakanta shi, kin ga dai auren ki ya ke son yi ba wasa ko wata shiririta ba. Don haka sai ki zabi abin da ki ka ga ya fi miki, ni dai ina baki shawarar da ki zabi Abdul, domin wallahi idan kika sake ki ka zabi Imran kin yi ta banza, kuma Wallahi ya ci Bulus, mutumin da ko aikin yi bashi da shi ina shi ina kin kimar kyakkyawa kamar ki, ina zai kai ki da uwarsa zai hada ki." Da haka Asma'u ta bar Rabi'atu da Abdul. Rabi'atu ta dago kanta a hankali ta dubi Abdul. Dan gajeren mutumin da ke gabanta ba wani abin zo ku gani ba ne, babu ma ta yadda za ka iya hadashi da ko wanne bangare da Imran, to amma ga mamakin Rabi'atu, lokacin da ta kalle shi sai ta ji haka kawai tana son ta aure shi, ba dan kuma wai don tana sonsa ba ne, ta san babu wani da namiji da take so a duniya da ya wuce Imran, to amma kuma sha'awar ta auri Abdul din na nan na karuwa a zuciyarta, ita kanta ba ta san dalili ba, don haka lokacin da Abdul ya dago kansa a hankali ya dube ta ya ce. "Za ki iya aure na kuwa". Sai kawai ta sami kanta tana mai cewa. "Me zai hana." Abdul ya yi murmushi domin ya tabbata malamansa sun gama aikinsu. Shi kansa ya san bai yiyuwa ace Rabi'atu ta so shi cikin dan kankanin lokaci haka kuma wai har tana son ta aure shi. Abdul ya mike tsaye. Sannan kuma domin ya kara tabbatar da nasarar malaman tsibbunsa sai ya ce da Rabi'atu. "Sai kuma yaushe." Ta dube shi cikin rudewa ba ta san lokacin da za ta ce da shi ba. "Ko yaushe ma ni ina nan." wannan shi ne farkon faruwar dukkan wani abu da ya biyo baya, tun daga ranar Rabi'atu ba ta sake kula Imran ba KADDARA TA RIGA FATA******** . Saura kwana daya kacal a daura auren Rabi'atu da Abdul Ba karamar kaduwa abokansa suka yi ba lokacin da suka ga lokaci guda Abdul ya juya hankalin Rabi'atu kansa, sannan lokacin da ya fara raba katin gaiyata, sai duk suka sallama masa, sun san tabbas Abdul shugabansu ne a harkar mata, sai dai abu daya suka zuba ido su gani shi ne yaya za ta kare tsakanin Abdul da Rabi'atu, domin kowannensu na tattare da masaniyar Abdul zai auri Rabi'atu ne domin kawai ya rama wulakancin da ta yi masa Karfe hudu na yamma. Abdul ya dauko turare daga cikin akwatin kayansa, ya fara yiwa rigarsa feshi, sannan ya juyo cikin gaggawa, da nufin ya fice daga dakin. Gidan su Rabi'atu ya nufa domin yin hirar karshe wacce daga ita kuma sai ko a dakinta. Idan ta ganni kenan Abdul ya ce cikin zuciyarsa. Sannan ya yiwa kansa murmushi ya yi kwafa. Rabi'at! Kin gama yawo yarinya. Yau kin fada babban tarko. A daidai lokacin ne aka kwankwasa kofar dakin sannan aka fado dakin kai tsaye babu sallama. Nasir jakal ne, daga shi sai yar singileti

Chapter 1 of 6