Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bakya sonshi toki shiga cikin gida ki dauko mana likkafani domin idan mun kasheshi mu sami abin jana'iza Raliya tace dasu a rude" "Na shiga uku!! Don Allah kuyi hakuri kada ku taba mun Rufa'i shi ne masoyina da zan aura" zan baku akwatin kudinku "ta fashe da kuka to sai dai kuma daga Raliya har jami'an tsaron da suke tare da ita" babu wanda ya daga kanshi sama akan wata itaciyar kadanya dake a kusa da kofar gidan saitin tsohuwar a kori-kura" Da ace wani a cikinsu zae daga kanshi sama da yayi nasarar hango ifiritan samari biyun dake a boye saman bishiyar tunda asuba" Gambo ne da abokin tafiyarshi Dumfama . ======>++++++^+++++<====== . Lokacin da Bilya da Aminu jangwarzo suka baro wurin Raliya sai suka koma bayan gari inda motarsu take" suka shiga suka zauna domin su sami nutsuwa su kammala hirarsu da suka fara a lokacin da suke tafiya akan hanyar Tun daren jiya suke ta nanata wannan magana" a halin yanzu dinma zamansu keda wuya sai bilya ya dubi aminu yace dashi Na fada maka tun jiya muddin...... . MUDDIN ME ? . KO SUMA YAUDARAR OGA KWAMISHINA ZASUYI ?RALIYA-15 . Bilya ya dubi Aminu yace dashi "Na fada maka tun jiya" muddin kwamishina ya dora hannunshi akan wadannan miliyoyin kudin to ba abinda zamu samu na dade da sanin halin kwamishina wajen hadama Aminu ya gyara zama yace dashi "Na fahimci wannan matsalar ni kaina Bilya Bilya yace "munyi dabara tun jiya bamu sanarwa kwamishina cewar mun kamo Rufa'i ba yayi kyau da muka ce dashi" bamu sami sa'ar ganin shi ba" kuma bana tsammanin zai gano inda muka boyeshi" Aminu yace "Ina fa zai gano tunda baiyi tsammmanin mun sake tunani ba" kawai da zarar ta bamu kudin tun anan mu raba kudin mu" kowa ya san inda zai nufa" domin kuwa na san kwamishina zaiyi kokarin baza yara su nemomu Bilya yayi dariya yace "Ina zai ganmu tunda dai ba kusa zamu tsaya ba" in dai Raliya ta amso mana akwatin kudin ina sa ran gobe kamar yanzu nakai kasar Colombia Acp Aminu yace "Ni kuma nakai kasar Japan ko kuma Indonesia tsofaffin biyu suka fashe da dariya hade da tafa busassun hannuwansu" wani ragon maza dake tsattsagar kan gero a cikin wata gona kusa dasu yayi saurin tashi a tsorace yana shirin bazawa aguje . =====**************************===== . Raliya tana zaune a kofar dakin kakarta tayi shiru tana tunani" tana faman hada biyu da biyu kuma babu shakka ta sami hudu a amsarta sai yanzu ta sake dawo da tunaninta na dalilin da yasa data sauka a mota jiya taji akwatinta ya kara nauyi" sai da badamasi mai amalanke ya taimaketa ya dauko mata daga bakin titi zuwa cikin kauyensu" bayan kuma tun daga cikin jami'ar Bayero har zuwa bakin titi inda ta tsaya ta shiga mota da hannunta ta dauko akwatiakwatin kacokan babu wani nauyi" . Sannan kuma bayan ta dawo gida a lokacin da Naziru ya matsa mata saita dauko mishi tabarau da tace ta sayo mashi tsarabar kano" Raliya tayi mamaki sosai da akwatin yaki budewa" bayan kuma a duniya tsawon shekarun da ta dauka da wannan akwati bai taba bata mata lokaci ba wajen rufewa da budewa ba" Raliya ta sake jin tsoro ya kamata" tabbas ba akwatinta bane" tace a zuciyarta" hakika misaya akayi min a mota" ba akwati na bane" to amma kuma babban abin takaicin shine tun jiya data ba Naziru akwatin domin ya kaiwa abokinshi Shegen Sama ya bude" bata sake ganinshi ba sai da daddare" data tambayeshi akwatinta ne yace da ita abokanshi sun sace akwatin daga yabar musu ajiya yaje zai dawo" da ace babu wannan sabuwar magana data taso" Raliya bazata taba damuwa ba don yayanta ya bayar mata da akwatin kayanta" A kalla tasan cewar tunda dai yanzu aure za'ayi mata zata sami wasu akwatinan da kuma wasu sababbin kaya na sawa iri-iri to amma kuma maganar wadannan mutanen da suka zo suka yi mata na tsabar kudi har Dala miliyan hamsin tayi matukar girgiza ta kuma dole ne ma ta sami Naziru suyi magana" domin kuwa bazata taba rufa mashi asiri ba" ita kuma su kashe mata masoyinta a banza Hakika sunyi dabara da suka kama Rufa'i domin kuwa akan Rufa'i zata iya zuwa ta nemo musu duk inda akwatinsu yake takai musu" . Raliya taso ace ta sanarwa mahaifinta wannan danyar magana domin asan halin da ake ciki a gidansu" to amma kuma sai daga baya ta gano cewar baiyana maganar ba abinda zai jawo sai tashin hankali Kuma bayan haka ma wannan wata magana ce ta sirri da ake yinta a boye" maganar Dala Miliyan Hamsin ba karamar magana bace" dole ne tayi taka tsantsan domin kuwa ba rayuwar Rufa'i kawai ke a cikin hadari ba ita kanta rayuwarta a halin yanzu yana cikin hadari" Domin kuwa idan har ta salwantar da akwatin kudin" to bayan sun kashe masoyinta Rufa'i itama bazasu barta haka nan ba" wannan wani abu ne da Raliya ta tabbatar kuma dole ne ta kiyaye Raliya tana nan zaune tana kissime-kissime mahaifiyarta tana dakin girki rufin jinka tana Fama da hayaki zuwa can saita ji fiton yayanta Naziru ya shigo gida yana wakar Bob Marley da gwarancin turancin sa yana sanye da kodadden wandonshi na tamfal kalar fatar jaki" da kuma wata jar riga ta saka wacce bai cika sata ba" sai yana jin tsiya Duk lokacin da Naziru yasa wannan jar riga ko magana bai cika yi ba a gidansu" don haka ne yasa da zarar Raliya taga yasa rigar itama take dauke mishi kanta" domin kuwa ya taba sa rigar daga kawai tace dashi "ina kwana" yayi kwallo da ita cikin tabo Mahaifinsu ya fito daga cikin daki a guje" ya rarumo iccen turken awaki ya wawukeshi suka Zuba a guje zuwa kofar gida Naziru bai sake dawowa gidan ba saida aka yi sati biyu To amma kuma a wannan karon duk da yake Raliya ta tuno wannan al'amari daya taba faruwa" sai taji bata fargabar tunkararshi da maganar akwatinta na jiya" zuciyarta tuni ta gama bushewa" domin kuwa an tabo wani bangare na ruhinta" an taba mata masoyinta Rufa'i . Ina Son ganinka yaya Naziru" akwai maganar da nakeso mu yi Naziru ya tsaya da fiton da yake yi" "wacce magana kikeso ki fada mun? Raliya ta sake kallon mahaifiyarta dake fifita wuta a murhu tace da Naziru" "Zanso mu shiga daki domin kuwa banaso kowa yaji abinda zamu tattauna Naziru" "Naziru yayi tsaki sannan ya duba wani kafcecen agogon dake hannunshi kamar ankwa" agogon yafi shekaru biyar da daina aiki" amma haka nan yake barazana dashi Yace da ita "lokaci yayi nisa" sauri nake yi zanje wani wuri ki bari mana saina dawo" Raliya tace dashi "kayi hankuri ka saurareni ba dadewa zamuyi ba" Naziru yabi Raliya suka shiga cikin dakin mahaifiyarsu" ya sake duban mushen agogon dake hannunsa" ya kosa ya tafi" domin kuwa tun jiya yakai tsohon babur dinshi gari ya sayar dashi naira dubu biyu" yana so ne ya samu isassun kudin mota ta yadda in ya bar gida zaiyi nisa ba tare da anji labarin inda yake ba Yanzun nan shirin tafiya yayi zuwa fadama" domin hako akwatin kudinshi ya gudu" yazo ne yayi wa cikin gidansu kallon yaushe gamo" da kuma wani guru da ya mance dashi a dakinshi maganin bindiga Da kuma wukarshi da yake daura ta a kwankwaso duk lokacin da zaiyi wata tafiya ta musamman gashi yanzun ya shigo kuma Raliya zata tsareshi da surutu" yace da ita a fusace bayan sun shiga dakin "Raliya wai wacce irin magana ce na fada maki sauri nake yi "Raliya ta tsaya a gabanshi suka hada idanu tace dashi babu alamar fargaba" Ina so ne kaje ka dauko min akwatin dana baka jiya" domin kuwa nima ba nawa bane" na wasu mutane ne da muka yi misaya a mota" akwai wani muhimmin abu dake ciki" Naziru yaji numfashin shi ya tsaya cak!! Yayi sororo a tsaye yana bitar maganar kanwarshi" sai kace ta yafa masa wuta a tsakiyar kanshi" wannan saurin canzawa da Naziru yayi a cikin dan lokaci kankani shiya sake tabbatarwa Raliya cewar da gaske Naziru ya bude akwatin yaga abinda ke ciki" kuma har Yanzu akwatin yana nan a wurinshi ya boyeshi" Naziru yace da ita a fusace "Na fahimci baki san halina ba Raliya" ban taba nuna maki bacin raina ba shiyasa baki jin shakkar tunkarata da maganganun da kike so" to na cinye akwatin bazan baki ba" in kina da abinda zakiyi kije kiyi "Raliya taji zuciyarta ta dauki radadi" ta tuno halin da masoyinta rufa'i yake ciki ta cewa Naziru "Zan so kasan cewar wannan akwatin dake hannunka daidai take da rayuwar masoyina Rufa'i kuma daidai yake da rayuwar wadansu mutane da dama bayan Rufa'i ciki har dani da kai da iyayenmu kasancewar ka bude akwatin tun jiya kaga abinda yake ciki" ina so ka canza niyyarka ta guduwa da wadannan kudade Naziru" domin kuwa koda ace ka tafi baza kayi nisa ba za'a cafkeka" domin kuma bakai kadai bane ke farautar wadannan kudin a duniya Akwai mutane da dama" kuma wasu daga cikinsu a yanzu haka sun zo nan garin suna nan suna lura da duk wani motsi da akeyi kuma sune suka sace min masoyina jiya" don haka kaje ka dauko akwatinsu in kai musu domin in amso Rufa'i kada su kashesh Naziru yayi makararriyar dariyar mugunta" yace da ita "Baki da hankali Raliya" ke yarinya ce karama baki san muhimmancin kudi ba a rayuwar Bil-Adama" da ace kin san yanda kudi suke a rayuwar duniya" bazaki taba tsammanin zan tausaya maki inyi asarar miliyoyin kudi domin ki amso masoyinki ba Don haka ina so ki san cewar akan wadannan kudin ban damu ba suzo su tafi dake da duk mutanen gidan nan" in suna bukata suzo su tafi da mutanen garin nan baki daya suyi garkuwa dasu bazan taba dawo da wannan akwatin ba" kiyi hakuri ki sake wani saurayin kanwata" Raliya taji hawaye sun zubo mata tace da Naziru kada kayi min haka Naziru" ka tausayawa rayuwata" ka duba halin da nake ciki" ka tuna cewar kudi komai yawansu zasu iya karewa" ni kuma 'yar uwarka ce bazaka taba samun kwatankwacina ba" bai kamata ace ka jefani acikin wannan masifar ba Naziru yaci gaba da murmushin mugunta yace "Baki san kudi ba Raliya" baki san zafin Farautar Kudi ba a duniya" yanzu a wannan duniyar kudi sune komai duk wanda kika gani su yake nema" idan baka da kudi a duniya ba abinda zaka iya mallaka" amma idan kana da kudi zaka iya mallakar komai in dai yana wannan duniyar" Raliya ta share hawayenta tace dashi "kudi bazasu iya mallaka maka wata kanwar ba idan bani a duniya" sannan kuma kudi bazasu mallaka maka wasu iyayen ba idan kaja aka zo aka karkashemu dasu baba da mama ko ka taba ganin wanda ya sayi "yan uwa da iyaye da danginshi dole ne ka tausaya mana Naziru" ka hakura da kudin nan idan kana da rabo saika samu wasu anan gaba Naziru ya murtuke fuskarshi yace da ita "kudi suna sayen duk wadannan mutane da kika lissafo Raliya" samun kudin sune masu wahala agareni Da Zarar.....RALIYA-16 . Naziru ya murtuke fuska yace da ita kudi suna sayen duk wadannan mutane da kika lissafo Raliya" samun kudin sune masu wahala a gareni" da zarar na mallakesu" ahannuna nasan inda zanje in sayi wasu 'yan uwan da duk wani mutum dana ke bukata a duniya" da Zarar na nema zan samu" ki dana batawa kanki lokaci Raliya" domin kuwa har abada bazan taba fitowa da wannan akwatin ba Naziru ya daga mata hannu wacce ke faman share hawaye "sai watarana kanwata ni zan tafi kada ki Zargeni kadan kenan daga cikin Laifin Kudi sune ke jawo mana rikice-rikice a duniya muke karkashe 'yan uwanmu ba laifina bane Naziru ya sakai ya fita daga dakin yana dariyar mugunta" cikin minti daya ya shiga dakinshi ya daura gurunshi da wukarshi a kwankwaso sannan ya fito cikin hanzari ya nufi bayan gari domin yaje fadamarsu ya hako miliyoyin kudin shi ya shiga uwa duniya Naziru yayi ajiyar zuciya sannan yayi murmushi KUDI Wadannan halittun da dan adam ya kirkiro a duniya sun dade suna bashi wahala" ya neme su sunki zama" to amma yanzu kam tabbas sun zo kuma bazai taba bari su sake kulle mashi ba Naziru baiyi nisa da fara tafiya ba ifiritan mutane biyu dake boye a saman bishiya kadanya dake akofar gidansu suka sauko cikin hanzari kamar kadangaru" suka bishi a baya" suna tafiya suna wasa da karfinsu a matsayinsu na tsofaffin 'yan dambe" . ======>+++++()+++++<======= . Har zuwa lokacin da Naziru Yakai fadama Zuciyarshi bata daina wasi-wasi ba domin kuwa shi kanshi abin ya bashi mamaki saikace amafarki Naziru ya tuno abokinshi marigayi Shegen Sama yana can karkashin kogi" yana rabawa kifaye da kwaduna abin kalaci" Naziru yayi murmushin samun nasara sannan ya tuno kanwarshi Raliya" bazai taba mancewa da Raliya ba aduk inda yake aduniya" domin ba ba don ita ba da bai sami wannan miliyoyin kudi ba Naziru ya isa gindin dorawarsu ta jiya" inda suka binne akwatin kudin shida abokinshi Shegen Sama nan da nan ya durkusa yasa gwiwoyinshi akasa ya fara kwakulo kasar sannu ahankali yana tureta gefe daya" sai kace wanda ke gino dankali" tsawon lokaci yana ta kwakulo ramin sai ya cimma jikin akwatin yana nan akafe a cikin ramin yadda suka barshi jiya Naziru ya karashe ture kasar yasa yannu biyu ya zaro akwatin daga cikin ramin duk kasa ta dambare a jikin akwatin" Naziru ya share ko ina sannan ya kurawa akwatin idanu yana murmushi Daga nan ina ya kamata ya nufa? ya tambayi kanshi kamata yayi ya fara kokarin barin wannan kauyen idan yaso ko ina yaje zai sami damar yin duk wasu shirye shiryen barin Kasar nan cikin kwanciyar hankali Naziru ya dauki akwatin ya rungume a kirjin shi zai motsa kenan ya tafi sai yaji wani bakon hancin bindiga yana asuwaki a gefen kunnenshi a lokacin ne yaji wata murya mai kama da fasasshiyar lasifikar rikoda tace dashi "Idan ka motsa daga inda kake ka lissafa kanka cikin wadanda kwanansu ya kare awannan safiyar Naziru yaji wani bakon hannu mai kama da bayan itace ya fado kan kumatunshi" sannan muryar dake gargadinshi taci gaba "yi sauri ka ajiye mana akwatin kudinmu bamu makara ba tun asuba muke tare dakai shashasha" . ======>++++()++++++<======= . "Mun dawo ne domin mu amshi akwatin kudinmu Raliya" dama mun sanar dake cewar Zamu dawo bada jimawa ba" shiga ciki ki fito mana da kudinmu ko kuma likkafanin jana'izar masoyin ki Rufa'i A.c.p Bilya ya dakawa Raliya tsawa dake tsaye tana kyarma tun lokacin da suka aika a kira musu ita" Raliya ta dubeshi a tsorace tana niyyar fashewa da kuka "Zan fada maku wurin da zakuje ku amso kudinku" suna wurin yayana yanzun nan ya fito daga cikin gida ya tafi fadama zaije ya tonosu yagudu Raliya ta saurara kadan sannan taci gaba "Don Allah kada ku taba mun yayana Naziru" ku amshi kudinku kawai" bani da wani dan uwa aduniya sai yaya na Aminu jangwarzo ya daka mata tsawa cikin sauri "Ina ne fadamar da ya tafi" yi sauri ki nuna mana" bama son bata lokaci Raliya ta nuna musu hanyar fadamar tana sheshshekar kuka" jami'an tsaron biyu suka garzaya a guje kamar ransu zai fita domin su cimma Naziru . =====>++++++*****+++++<======= . "Ka ajiye akwatin kuma bama son ka motsa" ko bakajin hausa ne? Dumfama ya sake dakawa Naziru tsawa" kamar harbin bindiga" bai san lokacin da ya saki akwatin ya fadi kasa Rambo dake rike da tashi bindigar yayi saurin dukawa domin ya dauke akwatin kudin. A daidai lokacin ne Naziru ya shammace shi ya matso da hannunshi daidai kwankwason shi ya Zaro sullubebiyar wukarshi" kafin Rambo ya dauke akwatin ya sake dawowa" sai yaji Dumfama" ya fasa kururuwa iyakar karfinshi" Bindigarshi ta fadi kasa" Rambo ya fasa daukar akwatin zai juyo da bindigarshi kenan ya harbi Naziru sai yaji wani abu ya toshe masa fuska kamar mota tabi ta kanshi ta wuce nan take shima ya fasa ihu ya zube a kasa tare da babban abokinshi . Abubuwa uku ne suka faru a lokaci daya Da farko Naziru ne ya juya kan wukarshi ya sokawa dumfama a tumbinshi sai da ta kusa nutsewa dukanta" sannan kuma yasa gindin takalmin shi ya naushi fuskar Rambo daga nan baya yayi hanzarin mika hannu ya sure akwatin kudin Naziru ya tsallake ifiritan samarin biyu dake kwance suna juye-juye" ya runtse akwatin akirjinshi da hannu daya" sannan ya gangara ta wata siririyar hanya dake cikin fadamar yaci gaba da gudu ya juyo fankacecen bayanshi" A daidai lokacin ne Rambo ya tashiya lalubi bindigarshi dake kasa" to amma kuma baya iya ganin komai sai wasu fararen taurari dake gada a cikin idanuwanshi" da kuma dan dishi dishin koren ganyayen dake cunkushe ako ina a cikin fadamar a cikin dan abinda ya gani ne kadan- kadan ya hango Naziru yana gudu dauke da akwatin kudin ya juyo bayanshi saitin inda Rambo ke zaune a kasa Rambo ya auna fankacecen bayan Naziru sannan yaja kunamar bindigar" tun kafin sautin bindigar ya bayyana daga can nesa Naziru yayi tsalle sama kamar an buga kwallon kafa" akwatin kudin ne ya fara dawowa kasa" kafin gawar Naziru ta Fado kanshi jini yana tsiyaya ta bakin shi kamar an bude famfon ruwa Rambo ya tashi da kyar da takarkara ya nufi inda akwatin kudin suke" da zuwanshi yana huci kamar maciji" har zai wuce sai yayiwa gawar Naziru kallon karshe" domin kuwa acikin shekaru fiye da goma wannan shine karo na farko" da ya samu matsala a wannan sana'ar tasu sannan kuma rabon da wani ya sami sa'a ya nausheshi tun a zamanin da yake dambe" to amma kuma wannan karon da ya dubi miliyoyin kudin dake hannunshi a cikin akwati saiya ji abin ya bashi sha'awa bai san lokacin da yayi murmushi ba. Domin kuwa ba wanda zai sami Dala miliyan hamsin a duniya kudi hannu" yayi tsammanin bazai sha wahala ba" Rambo ya koma inda abokinshi Dumfama yake kwance ya dafe cikin shi inda Naziru ya caka mishi zundumemiyar wukarshi" fuskarshi ta canza ta koma launin shudi-shudi" da kyar yake numfashi ya daga kanshi ya kalli Rambo wanda ke tsaye da Miliyoyin Kudin a hannun shi. A gaisheka namijin duniya" yace dashi yana numfashin karfin hali" da'ace yagudu ya sha da ba abinda zai hana in kashe kaina in huta da bakin ciki Dumfama ya dubi raunin dake dafe a hannunshi ya kalli jinin dake biyowa ta yatsunshi kamar ya matse ledar manja" ya lumshe idanunshi ya sake budewa sannan yace "yi sauri ka daukeni mubar nan abokina" yayi min rauni" ina bukatar agajin gaggawa Rambo yayi murmushi sannan yace da dumfama baka bukatar zuwa ko ina Dumfama zamanka anan zai fiye maka sauki Dumfama ya dubi abokinshi atsorace ban gane abinda kake nufi ba Rambo" yanzu fa ba lokacin wasa ba ne" na kosa muje asibiti jinina ya kusa karewa Rambo ya sake kankame akwatin kudin ya ce "Baka da hankali abokina" me yasa kake tsammanin zan iya rabuwa da wadannan Miliyoyin kudin ? Ka tayani Addu'ar neman sa'a zan tafi sai mun hadu adarussalam wannan itace ranar da zamu rabu abokina" na sami abinda na fito nema shekara da shekaru. Dumfama ya kalli Rambo cikin kunan rai. ka bani kunya Rambo" ban taba tsammanin akwai wasu kudin da zaka samu ka gujeni ba" banyi tsammani ba Rambo ya fashe da dariyar mugunta" "Ba'ayin amana da kudi abokina Miliyan Hamsin ba kudin da zaka bani amanarsu bane awannan duniyar" tun ina yaro nake Farautar Kudi shekaru ashirin kenan sai yau na same su Gobe zan gudu in tafi Kasar amurka kada ka damu abokina ko bayan ka mutu zan rika tunawa dakai" idan na gina kamfani sunanka zan sawa kamfanin" ai nayi maka halacci Dumfama" ko banyi maka ba abokina?" Rambo ya sake fashewa da dariyar mugunta sannan ya kankame akwatin kudin ya juya da sauri kamar walkiya ya bace a cikin fadamar Dumfama ya cije lebenshi a fusace" sannan ya dubi jinin dake zuba daga jikinshi" yasan cewar nan bada wani lokaci ba" jinin jikinshi zai kare ya mutu" a wulakance a cikin daji" sai yanzu Dumfama ya tuno irin barnar da yayi arayuwarshi" Ya taba jagorantar 'yan fashi sunje sun kashe kawunshi sun kwashe dukiyarshi" to menene don yanzu abokinshi yaci amanarshi ya gudu da kudin da suka farauto tare?" wannan kadan ne daga cikin halin 'yan adam. . Dumfama ya rarrafa yana cije lebe ya dauko bindigarshi data fadi cikin wani alayyahu" ya rike bindigar ya kura wa hancinta idanu tsawon lokaci a fusace yana neman abinda zai kashe a cikin wannan fadamar" domin ya huce haushin abinda abokinshi yayi mishi Yana rike da bindigar yana waige-waige domin yaga giftawar wani tsuntsu ya harbeshi su mutu tare" Cikin sa'a ya hangi wasu mutane sun nufo inda yake a guje" sanye da kayan 'yan sanda" Dumfama yayi murmushin farin ciki domin kuwa duk duniya bashi da wani abokin gaba irin 'dan sanda" ya dade yana shan duka ahannun 'yan sanda har karyashi sun taba yi a kafa lokacin da yana yaro" Dumfama ya saita bindigarshi ya auna wani kakkaura a cikin tsofaffin 'yan sandan biyu" ya dirka masa bindigar" Dan sandan yayi kuwwa sannan.......RALIYA-17 . Dumfama ya saita bindigarshi ya auna wani dan kakkaura a cikin tsofaffin 'yan sandan biyu" ya dirka masa bindigar" dan sandan yayi kuwwa sannan ya wuntsila ya fada cikin ciyayi abokinshi ya fashe da kururuwa ya tambayeshi "Bilya meya sameka? Dumfama dake boye a cikin ciyawa yayi murmushin mugunta" sannan ya auna goshin ragowar dayan daga nesa" A daidai lokacin da yaja kunamar bindigar ne kan dan sandan ya tarwatse kwanyarshi ta watse a cikin gonar tumatirin dake wajen lokacin da gangar jikinshi ta fadi gefe guda" ko sau daya bai sake motsawa ba Dumfama ya jefar da bindigar sannan ya saki hannunshi dake dafe da raunin da Naziru yaji mishi" ya yiwa sullubebiyar wukar kallon karshe wacce ke yashe a kasa tayi dama-dama da jini yana nan akwance a wurin yana haure- haure azaba" kafin mutuwa tayi awon gaba dashi har zuwa lokacin bai mance da babban abokin shi ba daya ha'ince shi Rambo . =====>++++++()+++++<======= . Rufa'i baisha wahala ba" wajen kwance igiyar dake daure a hannunshi ta hanyar kwana da yayi yana gwagwiyar ta da hakora" bayan ya kwance daurin da 'yan sandan sukayi mashi" sai yayi hanzarin kwance igiyar da suka zagayeshi da ita a jikinshi da kafafuwanshi kamar huhun goro Da kwancewarshi ya fasa tagar da wata kujerar katako daya dake cikin dakin" Rufa'i ya haura ta cikin tagar ya gudu yabar tsohon gidan da suka kawoshi suka kulleshi" har lokacin da ya nemi motar komawa kauyensu daga birnin kano yayi tsammanin 'yan yankan kaine suka kamashi Sai lokacin da ya koma gida ne ya rude da yasami labarin abinda ya faru a wurin masoyiyarshi Raliya" wacce take ta faman kukan farin ciki tun dawowarshi A ranar ba'a yi barci ba a kauyen Danmarke" domin kuwa an ga bala'in da ba'a taba gani ba" An tsinci gawarwaki har hudu" daya gawar Naziru ne babban dan ladanin garin" da kuma gawar 'yan sanda har biyu" tare da gawar wani bakin saurayi da ba'a san inda yake ba 'yan sanda sunyi iyakar kokarinsu wajen gwaje- gwaje domin su gano mafarin al'amarin to amma kuma da maganar taje kunnen kwamishinan 'yan sanda "Danmasani" sai ya gargadi jami'an dake da alhakin binciken ya tattara maganar yayi watsi da ita" cikin gaggawa" nan da nan aka kwashe 'yan sanda aka tafi dasu" tun daga nan ba'a san inda maganar ta nufa ba. to amma kuma da ace za'a tuntubi Raliya da masoyinta Rufa'i sun fi kowa sanin yadda al'amarin ya faru" sunyi shiru ne domin kuwa basa son wani abu ya sake kawo musu cikas a wannan lokaci nasu mai muhimmanci da zasuyi aure Bayan kwana biyu kuma hankali ya fara kwanciya" sai kuma wani masunci dake kamun kifi ya lalubo gawar wani saurayi a kasan kogin dake garin harta fara rubewa" bayan jama'a sun taru ne jingim a bakin kogin sai aka gane ko wanene Hashimu ne dan gidan malam makeri wanda matasan kauyen Dan marke ke kiranshi Shegen Sama A ranar kwana akayi ana kuka da Addu'o'i a kauyen dan marke" domin kuwa ba'a taba yin jana'iza har uku a jere a cikin kwana biyu ba sai a wannan lokaci babu wanda yasan dalilin faruwar wadannan munanan abubuwa" to amma kuma wasu mutanen dake kauyen acan cikin zuciyarsu farin ciki sukeyi" domin kuwa dama wadannan shakiyan samari biyu sun gallabesu. a satin ne aka tsayar da lokacin auren Raliya da masoyinta Rufa'i sha hudu ga watan sallah Babba . =====>*******************<======== . Kwana shida kacal da faruwar al'amarin kwamishinan 'yan sanda dan masani ya sami bakar takardar kora daga babban insifrktan 'yan sanda na kasa" jami'an tsaro da dama basuyi mamakin korar kwamishina da kuma yi mashi ritaya da akayi ba cikin gaggawa" Domin kuwa ya dade yana cin amanar aikin tsaro ta hanyar amsar cin hanci daga wurin rikakkun 'yan fashi da makami da kuma masu safarar miyagun kwayoyi A rana ta biyu da sallamar kwamishina" yaje wani gidan giya yasha yayi tatul da daddare" domin kuwa yawanci idan yana cikin bacin rai to giyar kawai yake sha yaji ta kwatar mashi da hankali bayan dare yayi nisa" saiya kamo hanyar dawowa gidanshi inda wata karuwarshi bose ke zaman jiranshi tsawon lokaci bata san inda ya shiga ba Danmasani yana cikin tafiya bai ankara ba wata katuwar motar daukar kaya ta shawo gangara aguje" babu fitila ko daya a gabanta" motar ta fada wani gargada tana sukuwa" cikin kosawa ta cimma tsohon najadun" Bai ankara ba sai yaji motar ta haye kanshi tana burari" yaji lokacin da katuwar tayar motar ta gaba ta haye kan ruwan cikinshi" daga nan kuma bai sake jin komai ba" sai radadin da ya mamayeshi a lokacin da kayan cikinshi sukayi falle-falle akan titi Alhaji Elbashir ya bude jaridar dake dauke da labarin mutuwar tsohon kwamishinan 'yan sandan" yayi dariya" sannan yace" yanzu na tabbatar na huce haushin miliyoyin kudina" banyi asararsu a banza ba Yana cikin doki ne

Chapter 6 of 11