Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sanda domin a nemo musu JARMAI babu wanda yayi ma wani mgana" domin kuwa tunanin wadannan makudan kudi ta gama rudasu" kowanne yana tunanin abinda xae fara yi da xarar kudin sun xo" suna cikin tafiya ne a mota xasu dawo gida" sai ACP aminu ya bugi kafadar abokin aikinshi bilyaminu yace dahi" mutumin naga kayi shiru ne! Tunanin me kake yi?" Bilya yayi ajiyar xuciya" "tunanin wadannan kudin nake yi" Ina ta lissafa abubuwan da xanyi dasu ne" "Wata xuciyar tana raya min inje kasar rum in gina kamfanin karafa acan" "Amma kuma nafi so in koma kasar japan in hada hannun jari da wani kamfanin kera bindigogi" . ACP Aminu yace dashi" "Ni kuma tuni na yanke shawarar komawa kasar swizilan in gina otal nawa na kaina" Daga nan kuma ni da wannan kasar har abada Allah ya rabani da talauci" 'yan sandan biyu suka fashe da dariya lokaci guda" abinda basu sani ba shine tuni har kwamishina ya gama shirya irin kisan da xaiyi musu a boye" da xarar kudin sunxo hannunshi" . ======>*****^*****<======== : "SURI?" Raliya ta tambayi mutumin cikin mamaki" ya akayi kasan kawata suri malam?" jarmai yayi mata murmushi yace" "masoyiyata ce" bata taba baki labarina ba?" RALIYA ta girgixa kanta alamar bata taba ji ba" Hakika wannan xobe dake a yatsanta suri ta mallaka mata shi a daren jiya domin ta rika tunawa da ita" gashi yanxu kuma ta hadu da masoyin suri a mota kuma ya gane xoben shi" daya ba masoyiyarsa" RALIYA ta tuno maganar da sukayi ita da suri a yammacin jiya inda take shaida mata cewar" AKWAI WANI SAURAYINTA RIKAKKEN BARAWO MAI SUNA JARMAI raliya taji gabanta ya fadi ta dafe kirjinta" a tsorace sannan ta sake kallon Jarmai wanda ke xaune a cikin fasinjojin motar yana yi mata murmushi" taji tsoro ya kamata" to amma kuma da yake taci sa'a ta kusa sauka daidai hanyar da xa'a bi a nufi kauyensu bata damu ba" Jarmai ya mayar da hankalinshi a wajen nashi tunanin da yaga raliya bata son hirar" domin kuwa shima yana da nashi tunanin da ya dame shi a xuciyarshi" to akalla dai yanxu yana kyautata xaton yayiwa kawunshi Elbashir nisa" domin kuwa koda ace Elbashir ya sanarwa 'yan sanda" bazasu taba kawowa a ransu cewar xai gudu ya boye a wani kauye ba" xasu bishi can wani waje ne inda suke tsammanin ya nufa" kamar tashar jirgin sama" "to amma kuma gashi ya shammacesu ya dauko murgugujen akwatinshi wanda ya cika FAL da miliyoyin kudi na dalar amurka" ya shiga motar haya xaije wani kauye ya labe sai kura ta lafa" sannan sai ya biyo dare ya dawo ya dauki masoyiyarshi suri su gudu da kudin su" Jarmai yayi murmushin farin ciki da ya tuna irin holewar da xaiyi a duniya da wadannan kudi bai san cewar suri ta gama shirya hanyar da xata bi tayi mashi wayo ba ta amshe akwatin ta gudu da kudin ba" . SURI tana can makaranta tana ta duba agogo tana tsaki" domin kuwa ta kosa taga Jarmai" ta kosa ta amshe kudin ta koma garinsu ta dauke tsohuwar kakarta gurguwa su gudu xuwa wata duniya inda xasu more kudinsu hankalinsu a kwance ba tare da 'yan sanda sunbi sawunsu sun takura musu ba" . Motar taci gaba da sheka gudu akan titi" xuwa can RALIYA ta hango lambar kauyensu dake a bakin titi an rubuta DAN MARKE nan da nan tayi sauri ta taba yaron dake gyangyadi" "Akwai wajen lambar can! Akwai......." Yaron motar ya cewa direban cikin sauri" "In kaje Dan marke akwai mai sauka" Motar ta fara saranda nan da nan ta silale ta tsaya a saitin hanyar kauyen su RALIYA" wasu matan fulani su hudu sun dauko koren nonon suna ta sauri sun kama hanyar kauyen" A kusa dasu kuma wani saurayi ne ya tasa manyan shanun huda a gaba sun dawo daga aiki duk ya jike da raba a kafafuwan wandonshi da ya yage" raliya tayi ajiyar xuciya domin kuwa taga gida" tayi sauri ta fita daga motar bayan yaron ya bude kofar" ya nufi bayan motar cikin sauri domin ya bude ya dauko mata akwatinta Jarmai ya cewa raliya "sai anjima 'yan mata" idan kin ga suri kice ina gaisheta" RALIYA tayi banxa dashi domin kuwa ta tsaneshi duk ta kosa dama ta sauka su rabu" yaron motar ya ajiye mata akwatin a kasa" ya rufe bayan motar ya dawo a guje ya shiga direban ya ja motar suka tafi" yaron motar ya daburce bai san akwatin da ya ciro ba a cikin kwatinan biyu" domin kuwa irinsu daya" wannan ba matsalarshi bace" yace a xuciyarshi sannan yaci gaba da gyangyadin shi motar tana ta sheka gudu RALIYA ta gyara lullubinta da tsohon gyalenta" sannan ta dauki akwatin domin ta kama hanya ta nufi kauyensu" to amma kuma ga mamakinta sai taji akwatin yayi mata nauyi jigim! Sai kace an xuba mata duwatsu a ciki" ta yunkura dakyar ta raba akwatin da kasa" sannan ta fara tafiya dashi batayi nisa ba ta tsaya domin ta huta" me ya sami akwatinta kuma?" RALITA ta tambayi kanta" to amma kuma watakila laifinta ne domin kuwa yunwa take ji bata karya ba ta fito daga makaranta" gashi yanxu daukar akwati xai gagareta" RALIYA tayi murmushi tace a xuciyarta"Dana sani dana tsaya na karya domin kuwa suri ta gama abinci" to amma kuma ta kosa ta dawo gida taga masoyinta rufa'i RALIYA tana kan tafiya ne da kyar dauke da akwati" sai ga wani mutum makwabcinsu mai suna malam Dan kano" ya taho da amalanken shanu yana turata da hannunshi" ya cewa raliya "yan makaranta an dawo ne?" Raliya ta...RALIYA-07 . Yan Makaranta An Dawo Ne? "RALIYA ta gaisheshi cikin ladabi ya amsa" ganin tana ta fama da katuwar akwatin sai ya mayar mata ya dora akan amalanken ya tura mata" Raliya tayi mashi godiya tabi shi a baya" suna ta sauri" suna wuce manoma a gonakin dawa da masara" suna ta faman aiki" Raliya taso ace ta rage kudi a hannunta data ba mutumin ko naira ashirin ne" domin kuwa ya taimaka mata wajen daukar mata wannan akwati mai nauyin tsiya" to amma kuma bata da sauran ko kwabo a hannunta" su kenan ta bada su kudin mota" to saidai kuma da ace raliya zata bude akwatin da mutumin ke tura mata data sami kudin da xata bashi lada masu yawa" Abin da raliya da mutumin basu sani ba" shine wannan akwatin dake gabansu ba tsummokara da littatafai bane a cikin shi" Dalar amurka ne har kimanin miliyan hamsin" . =====>******^*******<===== . FARAR motar tana cikin tafiya da fasinjojinta guda shida sunyi shiru" ba zato da tsammani sai suka ji jiniyar motar 'yan sanda a bayansu" direban ya kalli madubin motar yaga bakar motar yan sanda ta cika Fal da kwalawa suna rike da bindigogi" nan da nan ya rage gudu daya ga 'yan sandan suna tsayar dashi" Tsayawar motar keda wuya" sai motar 'yan sandan taci taya a bayanta" 'yan sanda shida suka firfito a gurguje suka xagaye motar suna xare idanu" Jarmai dake xaune yayi mutuwar tsohuwa domin kuwa yasan cewar asirinshi ya tonu" shiyasa suka biyoshi" Yaron motar ya bude kofar motar" 'yan sanda suka leka ciki biyu daga ciki suka cakumo Jarmai kamar dan wake a lokacin ne wani dan sanda ya bude bayan motar ya sungumo akwatin ya kankame ta yana ta baraxana da bindigar dake a hannunshi" wani a cikin 'yan sanda ya dakawa Jarmai tsawa" "wannan shine akwatin?" Jarmai ya girgixa kai "yace shine" 'dan sandan yasa gindin bindiga ya kwada mishi a gepen bakinshi" hakora uku suka yi tsalle suka fito waje" wata mace dake a cikin motar ta rusa kururuwa" Jarmai ya xube kasa yana shure shure" jini yana kwararowa ta bakinshi da hancinshi" nan da nan suka tattarashi suka hada da kawatin suka nufi cikin motarsu" ba laifin su bane" domin kuwa tun cikin daren an basu umarni in har sunga Jarmai kada suxo dashi da kamanninshi" su canxa mashi halitta yadda ko uwarshi ta ganshi baxata iya ganeshi ba" To amma kuma har 'yan sandan suka ja motarsu sukayi kwana suka tafi bata Jarmai suke yi ba da yake kwance magashiya" ta akwatin kudin suke yi dake a tsakiyar su" domin kuwa su kansu basu yarda da junansu ba" suna jin tsoron kada wani a cikinsu ya harbesu ya gudu da miliyoyin kudin shi kadai" Da ace xasuyi karambanin bude akwatin da sunsha mamaki domin kuwa xasuyi nasarar tsintuwar littatafan karatu da kuma rigunan mama da tsofaffin takalma . =======>*****^*****<====== . Kauyen dan marke wanda yake da nisan kilomita daya da rabi daga bakin titi" yana cikin karamar hukumar garun malam" dake a jihar kano" dan marke kauye ne dake da dimbin tarihi domin kuwa akwai tsofaffin dake a raye a cikinshi" wadanda suke ba yara tarihin kafuwar wannan kauye" tun xamanin mulkin mallakar turawar ingila" kafin a sami yancin kai" ALLAH ya albarkaci kauyen dan marke da manyan manoma na rani da kuma na damina" kusan a kowanne yanayi mutum ya shiga cikin kauyen da wahala ya sami mutane a xube suna xaune" koda yaushe mutane suna gonaki da kuma fadamu" Akwai kuma masu xuwa kamun kifi" domin kuwa a xagaye da kauyen dan marke manyan koguna ne da ba'a taba ganin sun kafe ba atarihin da za'a iya tunawa" Kasancewar yankin karkarar da kauyen dan marke kewaye yake akwai yalwatacciyar ciyawa a gepen fadamu rani da damina" shiyasa fulani suka kafa rigaye jefi-jefi a kusa da kauyen" wannan ya sake taimakawa maxauna yanki yajen samun isassun dabbobi da kuma samun takin gargajiya da arahar nono da man shanu" . Duk da wannan albarka da ubangiji yayiwa yankin karkarar na samun abubuwan dogaro da kai" hakan bai hana samun matasan dake xaman kashe wando ba" tun sape har xuwa dare" naziru yana daya daga cikin irin wadannan hatsabiban matasa majiya karfi dake a kauyen dan marke" wadanda sau daya idan za'a yi fada tsakanin fulani" makiyaya da kuma manoman kauyen dan marke su Naziru ake sawa a gaba" suyi ta ife-ife da makamai a hannu" domin kuwa duk cikin samarin dake wannan kauye babu wanda ya kama kafar Naziru " wajen hatsabibanci da kuma son tada xaune tsaye" Mahaifinshi malam muntari shine ladanin dake kiran sallah a kauyen" sannan kuma shine na'ibin babban limamnin dake yankin karkarar" kowa yana ganin mutuncinshi badon halin 'ya'yanshi biyu sun bayar da shi ba" Malam Muntari shine mahaifin Naziru da kuma raliya 'yar makaranta" da Naziru da kanwarsa raliya sunyi matukar yin kaurin suna a wannan gari nasu" Naziru yayi bakin jini ne badon komai ba saboda kowa yana da labarin baya xuwa gona domin taya mahaifinshi aiki". Sannan kuma jifa-jifa na cewa wai ya fara shan taba" a tarihin kauyen dan marke ba a taba samun wani saurayi da ya taso yasha taba ba sai akan NAZIRU" . Yawancin matan garin har gargadin 'ya'yansu sukeyi idan sun dora masu talla" ko Naziru ya kirasu zai saya kada su sayar mashi" suce an hanasu" Akwai wata mata dake dorawa 'yarta tallar tubani da manja" wacce Naziru ya kira yarinyar ta ya sayi kwano biyu" da matar ta sami labari" da kyar makwabta suka xo suka cece yarinyar" matar tana ta jibgarta tana cewa" "kullum idan zata fita saina ja mata kunne" ko hanya ta biyo taga Naziru tayi sauri ta shige wani gidan sai ya wuce" amma shine ya kirata taje har ya sayi tubani ya taba min kwano" Ance saida matar tayi kwana bakwai tana wanke kwanonin da tokar makaranta da kuma kasar masallaci kafin a sake xuba abinci a ciki" saboda Naziru mai shan taba ya taba kwanonin da hannunshi" . Ita kuma RALIYA an tsaneta ne a garin saboda tayi shirgegiya amma kuma mahaifinta yaki aurar da ita" tsararrakinta sun haifi 'ya'ya hudu xuwa biyar" shiyasa da xarar ta dawo hutun makaranta matan garin xasuyi ta gulmace-gulmace" wadansu suna cewa ai anji labarin tana da wannan ciwon na kanjamau da ake kwasowa a birni" wadansu kuma sunce duk wata sai an xubar mata da cikin shege" To amma kuma a bangaren malam muntari" shidai yasan hakika yana da matsala babba a bangaren danshi Naziru" kuma shidin ma ba'a xaune yake ba" duk sati sai ya sa an sauke mashi Ashafa" sannan kuma yana da wata bara daya sa ana rubuta mishi ita kafa saba'in duk karshen wata yana tsare Naziru yana sha domin a samu ya daina wannan lalata da ya sawa kanshi" ta barin suma akai da kuma shaye-shaye da xuwa bakin rapi suna yin karta shi da lalatattun abokanshi" Sannan kuma malam muntari ya sami wani lakani a wajen wani bafillatani wande ake barbadawa a tsire aba yaro ya cinye tsiren a xaune" a cewar bafillatanin komai ibilishin da yaro ya xama indai aka barbada garin sau biyu" to an sami sauki har abada" sai ya koma waliyyi" Malam muntari ya barbada wannan magani a tsinkayen tsire yafi sau goma koda yaushe ya kira danshi Naziru saiya zare mishi idanu yace ya xauna ya cinye tsiren" to amma kuma har yanxun babu alamar nadama" Naziru sai kara gaba yake yi" maimakon yayi dan dama dama" ko sati biyu ba'a yi ba ya saci wata tunkiya tun daga lokacin malam muntari ya fara karaya da lamarin Naziru domin kuwa hatsabibancin shi ya wuce duk inda ake tsammani" To amma kuma a game da raliya yarshi wannan sai dai ayi mashi sam barka" domin kuwa bai taba kamata da wani laifi da zaice mata tir ba" ta tsare mutuncinta tana karatunta" kafin ta kammala kuma ta fito da masoyinta ayi mata aure" A ka'ida a kowacce safiya idan an tafi gona" Naziru tare da shakiyan abokansa su SHEGEN SAMA basu da wani aiki saisu nufi bakin kogin dake bayan garin su xauna a gindin wani mangwaro su nada mandula su sha suyi karta" kamar kullum a karon bayan duk mutane sun tafi gona" sai Naziru ya hau tsohon babur dinshi (SUZUKI) wanda ya taba yin gobara ya kone" idan zai tada babur din saiya xungura shi a guje sannan sai yayi tsalle ya haye" gashi kuma babur din bashi da salansa idan ya fara burari sai yaran kauyen suyi ta koke-koke" wasu kuma suna shigewa gida a guje" domin kuwa kafin a saba da babur din a lokacin da Naziru ya fara tadashi a kauyen mata duk suka bi suka rude suna salati" sun dauka cewar girgixar kasa ake yi" NAZIRU ya xungura babur din a guje yayi tsalle yasa giya" amma kuma a wannan karon baici sa'a ba" haka yayi ta dama dashi har yakai bakin kogin" yana sanye da kodadden wandonshi na sojoji daya fashe a gwiwa" da kuma bakar riga wacce ta dauki shekara biyu bata ga ruwa ba" in aka dauke ruwan saman da ya jikata bara" Naziru bazai taba mancewa da wannan rigar ba" domin kuwa a caca ya ciwota tare da wani takalmi" Bayan yaje bakin kogin bai iske abokan shekiyancin shi ba" sai yayi fushi ya gunguro babur din ya kamo hanyar dawowa gida" yana cikin gungura babur din" sai kuma wata xuciyar ta raya mashi cewar ya sake jarraba tayar dashi me yiyuwa yaci sa'a ta tashi" Naziru ya ingixa tsohon babur din a guje" sannan yayi tsalle yahau yasa giya" babur din ya sarke da ihu" saida tsaunukan garin suka amsa kuwwa" sannan ya cilla da shi a guje Naziru ya nufi gida yana murxa babur din" A daidai lokacin da yake kan tafiya ne kafin yasha kwana ya shiga garin" wasu bakin mata tsofaffi sun biyo ta hanyar xasu nufi wani kauye" suna tafiya suna labarin jirgin da suka sami labari ya fado a birnin kano a watan da ya wuce" wanda ya kone gidaje da mutane bil adadin" sai kuma sukaji rugugin wani abu ya tunkarosu kamar zai tsaga kasa" saboda tsananin burari nan da nan tsofaffin matan suka juya cikin kauyen a guje domin kuwa sun dauka cewar jirgin ne irin wanda suke jin labarin ya fado a kauyen a halin yanxu" Matan suka watsar da kullin kayayyakin su . . . .RALIYA-08 . Matan suka watsar da kullin kayayyakin su daya kakkaura ce mai kiba" daya kuma doguwa ce dakayar take iya tafiya" to amma kuma da sukaji burarin yana kara matsowa kusa dasu" nan da nan suka xage dantse doguwar ta wuce kakkaurar tayi mata nisa" ita kuma kakkaurar tana biye da ita tana salati" domin kuwa sun gama tsinkewa mutuwa ce ta zo . Suna cikin gudu suna numfashi sai suka ci karo da wasu mata su uku dauke da tuluna" sun debo ruwa a wata rijiya" matan suka tsaya tambayarsu a tsorace" ganin tsofaffin sun wuce su a guje kamar iska suna haki sai matan suka ajijjiye tulunansu suka rufawa tsofaffin baya" wadanda aka tserewa sunata ihu suna cewa a jira su" A dai dai lokacin ne wani dan koli dake bin kauyuka da keken shi yana tallar 'yan kunne da sarka ya shawo kwana da tsohon keken shi" ba zato da tsammani sai yaci karo da mata ridi-ridi su biyar suna cin gudu" dan kolin yayi iyakar kokarin shi domin ya tsayar da keken amma yaki tsayawa" gashi kuma ya jiyo karar wani abu shima kamar jirgin kasa ya biyo matan" nan da nan yayi tsalle ya jefar da keken yabi matan a baya yana nannade malum-malum dinshi data dabaibayeshi a kafa . Mata biyar da Dan koli suka keto kauyen danmarke a guje kamar sunga mutuwa" wani mutum da ake cewa tsalha mai jaki" ya hawo wani tsohon jakinshi mai shegen gardama" ganin mutane suna cin gudu" sai ya kada kan jakin domin su koma gida" amma kuma jakin ya ruga guje" ya tunkari inda burarin nan ke tasowa" wanda ba'a san ko menene ba" ganin haka sai yayi tsalle ya sauka daga kan jakin ya dawo baya ya rufawa matan baya suka yi cikin gari raf! Raf!! A guje Bayan sun kai bakin dandalin garin ne sai suka ji shiru rugugin ya wuce" tsofaffin biyu suka fara tsayawa suka dafa bangon wani gida" suna share zufa" matan dake biye dasu da dan koli da kuma tsalha mai jaki suka cimmasu" kakkaurar tsohuwar ta dubi ragowar abokan tseren tace dasu" "Sannun mu jama'a barka da arziki Dan koli yace" "Lallai Allah ya auna mana arziki sannunmu" malam tsalha ashe haka wannan al'amari yafaru" Malam tsalha ya mikawa dan kolin hannu suka gaisa" ragowar matan uku masu tuluna suka fara yiwa juna jaje Matan makeri sannunmu da tsira" wata a cikinsu tace "Barka dai matar mai unguwa sannunku" "wannan bala'i dame yayi kama a duniya?" tsalha mai jaki ya cewa dan koli" "wai me ya faru ne dan koli ni nayi tsammanin harin da akace jaji bush zai kawo shine suka jeho mana nakiya anan kauyen" jiya matata taji ana fadi a rediyo? Dan koli ya share zufa yace da malam tsalha" "Eh, to nidai na taho naga wadannan mata suna gudu" ina jin maganar dai kenan koba haka akayi ba? Ya tambayi matan biyar" matan makeri tace" muma dai mun debo ruwa ne" muka ci karo da wadannan tsofaffi suna gudu" mun tambayesu ko lafiya basu ce mana komai ba" shine muka biyo bayansu Dan koli ya bata rai yace" Zancen banza kenan" kawai kuma daga ganin mutane suna gudu sai ku kama yi" to ku baba me kuke yiwa gudu?" Doguwar tsohuwar tace" "mu baki ne muna tafiya ne zamuje kauyen kwananduke" daga magaji wando muke" shine sai muka ji karar wani abu kamar na jirgin sama zai fado" to munji labarin abinda ya faru a birni kwanan nan shine mukayi ta kanmu" . Malam tsalha yayi tsaki yace da tsofaffin" "Amma wallahi kun cucemu tsohuwa" haka kawai daga kunji karar wani abu sai ku kama gudu" Yanzu haka ma babur din yaron can NAZIRU dan gidan mai kiran sallah kuka ji" Dan koli yace" "shine mana!! Kawai kunja mana tashin hankali muna gudun banza ni banma san inda na ajiye keken kayana ba" Ya wuce gaba yana zage-zage" afusace ya koma inda ya baro kekenshi" malam tsalha yabi bayanshi yana share zufa" yana ta tsaki domin kuwa matan sun gama bata mashi rai" Matar mai unguwa ta shiga gaba suna ta fada domin su koma su dauki tulunansu" "wannan sakarcin ma dame yayi kama a duniya" indai lalatar Naziru ne wanene bai saba dashi ba a wannan kauyen" haka yake tada wannan babur din ya tsorata mana yara" kuma kawai ku da girmanku sai ku kama cin gudu?" Kakkaurar tsohuwar tace a fusace "to mu ina xamu sani tunda mu baki ne?" kawai muna cikin tafiya malam" sai muka ji abu ya taho rugu-rugu ba arxiki" ina xamu tsaya kawai-kawai ya cim mana? matan suka yi ayari suka koma suna ta musayar maganganu" malam tsalha mai jaki bai waiwayi inda jakinshi yake ba" da xuwanshi saiya shige cikin gida" domin kuwa ranshi ya riga ya baci" Duk lokacin da ranshi ya baci haka kawai sai yaji yana jin gudawa ya shiga cikin gidan a fusace yana ta xupa" matanshi suka fara tambayarshi abinda ya faru" ko daga kai baiyi ya kallesu ba" yayi sauri ya wawuri buta ya fada bayi" da shigarshi ya turo kofar ta rufe a fusace" . =====>******^*******<====== . NAZIRU ya shiga cikin gidansu" yana gangara babur dinsa" da shigarshi ya hango kanwarshi Raliya ta dawo tana xaune a kasa da kakarsu tare naziru ya jingine akwalar babur dinshi" sannan ya nufi wajen kakarsu da kuma Raliya yana fara'a "yan makaranta yaushe aka dawo ne?" Raliya tace dashi "tun daxun na dawo yaya Naziru" ina ka shiga ne?" Naziru yace da ita yana shafa tarin sumarshi" "Na dan fita nan bayan gari ne" yaya karatun naku Raliya?" "kafin tabashi amsa ne kakarsu tace dashi" "An fita yin sana'ar da aka sabo ko?" ai kai dai wallahi Naziru har abada baxaka rika jin magana ba" Naziru yayi saurin canxa hirar domin kuwa yasan halin kakarsu idan ta fara yi mashi bambami sai ta wuni bata gaji ba" "Raliya ina fatan dai a wannan karon kin cika min alkawarina" tuntuni nasha tuna miki idan xaki dawo ki sayo mani tabarau irin mai dan fadin nan" irin na SHEGEN SAMA abokina" Raliya tayi murmushi" "Ban mance ba yaya Naziru" tace dashi sannan takai ganinta inda ta jepar da akwatinta tun dawowarta anan ta sake shi a tsakar gida" 'ya'yan awakai suna ta hawa kai suna tsalle bata damu ba" domin kuwa tasan cewar ba wata tsiya ke a ciki ba" daya wuce tsummokara da littatafan karatunta" yaunxun nan da xarar ta gama hutawa dama take so ta amshi kudi a wajen mahaifiyasu taje ta sawo omo tayi sukola Raliya ta cewa yayanta Naziru Yana cikin akwati ka bari sai anjima idan na bude sai in baka yanxun nan xan tashi" dama in ciro kayana wanki xanyi" Naziru ya bata rai yace da ita" "sauri nake yi tashi ki bani yanxu Raliya" wajen abokina zan tafi Shegen Sama yana can gida yana jirana" kakarsu dake sauraronshi tace" "kadai xama sangwamemen katon banxa Naziru" ace kai ba xaka tsinanawa kanwarka komai a duniya ba" sai dai ita ta samu ta baka kaji kunya kayi girman kwabo" naziru yayi dariya ya cewa kakarsu" "In banda abinki kaka menene to don taxo mini da tsaraba" Daga birni fa take" tinda mu muna nan a kauye" ai yakamata ace ta danyo mana siyayyar birni" nima idan aurenta da rufa'i ya tashi ai dole ne inyi mata Raliya taji farin ciki ya lullubeta" data ji Naziru ya ambaci sunan masoyinta Rufa"i da shigowar ta ta aiki wani yaro domin gidan su domin a sanar dashi cewar ta dawo" amma kuma taci rashin sa'a Rufa"i ya tafi gona tunda safe sai ya dawo " Anjima nan zaizo ya sameta su raba dare suna hirar yaushe gamo" Raliya ta tashi cikin tsananin farin ciki domin ta dauko wa Naziru tabaronshi data sawo mishi a kano" ta ciro dan makullin akwatin ta kori awakan dake xaune akai ta daga akwatin tsaye ta fara kicin kicin budewa" Raliya ta dage tana dama da akwatin ya budu amma kuma yayi gam yaki budewa" wannan abu ya bata mamaki" daxun nan tahi akwatin ya kara nauyi data sauko a mota" yanxu kuma gashi ya kulle tayi-tayi ya bude yaki budewa" anya kuwa wannan akwatin shine nata? Raliya ta tambayi kanta cikin fushi" Naziru dake a tsaye yana jiranta ta bude ta ciro mishi tabaronshi yace da ita" "kawo mabudin mu gani don Allah" sai kace wani aiki?" Raliya ta mika mashi mabudin yayi nashi kokarin amma akwatin yake buduwa" kakarsu dake xaune tana yagar rama tace" "to wai dole sai an bude" a hankura mana sai an huta xuwa anjima" wannan naci har ina?" bana son kana takurawa yarinyar nan Naziru" kai baka san ka girma ba wallahi" Naziru ya hauri akwatin cikin fushi da gwandolarshi" "Duk bukulunka saina sai tabarau yau akwati" yace yana xaro idanuwa" sannan ya dauki akwatin da hannu daya yace da Raliya" "Kada ki dama Raliya bari inje dashi wurin abokina Shegen Sama yana da karfen bude kwatuna" idan ya bude kwadon sai in dawo miki dashi ki ciro ki bani" Raliya tace dashi" "ba komai yaya Naziru kaje dashi ku bude" Naziru yayi waje da akwatin kakarsu tace" "wannan masifar naci naka Allah ya rabamu da irinshi" Naziru ya fito daga cikin gidansu" Abokinshi Shegen Sama wanda suke takadarcinsu tare" kamar Naziru dashi a gidansu" su biyu ne dama suka gagari kowa a kauyen danmarke" to amma kuma har dama-dama Shegen sama shi ance yana xuwa gona idan ta raya mashi" to sai dai kuma ko sati daya ba ayi ba daga kawai mahaifinsh yace ya daina kawo mishi tuwo tunda bayason xuwa aiki" kishiyar mahaifiyarshi ce keda aiki" data gama abinci bata sa mishi ba" saida ya bari babanshi ya fita masallaci ya fada cikin dakinta" yayi mata dukan tsiya da bel" tsawon lokacin mahaifinshi yayi yana tsine mashi albarka" Naziru ya sami shegen sama a xaune akan gungume a kofar gidansu yana hamma" shegen sama gajere mai fadin kirji kamar kofar gareji" yana da murgujejen kai da kuma faskeken tafin hannu kamar faranti" yana sanye da kodaddun kaya irin dan madina" wanda ya zazzare ya koma kamar kyallen tatar koko Naziru ya kunduma mashi zagi tun kafin ya karasa wajen shegen sama. . ZANSO KUYI HANKURI SHAFIN DA NA SHIGO YANA DA MATSALA" BANA GANE RUBUTUN" AMMA SHAFI DAYA NE KAWAI" . Ayarin 'yan sandan da suka kamo jarmai suka ci birki a daidai ofishin ACP Aminu jangwarxo" tsayawarsu keda wuya suka fito dashi nannade da ankwa a hannayenshi tare da murgujejen akwatin kudin...RALIYA-09 . Ayarin 'yan sandan da suka kamo jarmai suka ci birki a daidai ofishin A-C-P AMINU JANGWARZO" tsayawarsu keda wuya suka fito da shi" nannade da ankwa a hannayenshi tare da murgujejen akwatin kudin" Dan sandan da yake dauke da akwatin sun shashi a tsakiya rike da bindigogi" domin kuwa suna fargabar wata kila yana da layar bata" Da shigarsu ofishin jangwarzo suka sameshi tare da A-C-P bilya" 'yan sandan suka sara ma tsofaffin sannan babban cikinsu yace "An gama aiki yallabai gashi nan mun kamoshi a motar haya xai gudu xuwa wani kauye" ga akwatin da ya sato A-C-P Jangwarzo yayi saurin amshe akwatin a hannunsu" sannan ya daka masu tsawa yace" "ku daukeshi ku kaishi gidan tuhuma ku kulleshi" kada a bari wani ya kusanci inda yake har xuwa nan da lokacin da xan baku umarni nan gaba" 'Yan sandan suka cakumi jarmai wanda bakinshi ya karkace ya koma gefe daya" yana ta xubar da jini" kamar gilmawar walkiya" nan da nan har sunyi ciki dashi sun bace" tsofaffin 'yan sandan biyu suka kalli juna cikin tsananin murna" sannan suka fice da sauri domin su kaiwa kwamishina ya bude ya basu nasu kason" Cikin minti uku har sun garxaya a mota sun sami dan masani yana ta kai da kawowa a wani kebantaccen gida na sirri da ya ce su sameshi acan idan sun amso akwatin kudin" Yana tsaya yana kallonsu suka tunkareshi da akwatin suna fara'a ganin haka saiya shiga cikin wani daki na sirri" tsofaffin 'yan sandan suka bishi ciki suka sameshi har ya xauna akan kujera ya dora hannuwanshi akan teburin dake a gaban kujerar fara'a akan fuskarshi da kuma murnar ganinsu" "Me kuka tsaya jira tun daxun ina xama jiranku?" Dan Masani ya tambaye su yana shafa bindigarshi dake a boye a kugunshi domin ya tabbatar tana nan" sai jangwarxo yace "mun sami matsala ne a wurin nemanshi" domin kuwa da farko tashar jirgin sama da kuma na kasa muka tura yara su nemoshi" sai daga

Chapter 3 of 11