Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
karfi" reshikan bishiyoyin dake makarantar suka rausaya a lokaci guda" sannan ganyaye suka farfado kasa" Suri ta lumshe idanunta cikin jin dadi" a lokacin da iskar ta doki fuskarta tare da watso mata kwayoyin ruwan dake makale a sararin samaniya wadanda tun lokacin da ana ruwan Allah bai basu ikon fadiwa tare da 'yan uwansu ba" Suri tayi murmushi data tuno abinda ta tabbatar yana can yana faruwa a wani wuri" a daidai wannan lokaci" tun lokacin da Jarmai ya gwangwadawa Suri labarin wannan dukiya da xai sato daga wurin kawunshi ta fara tunanin abinda xatayi da dukiyar" domin kuwa tasan cewar indai sunxo to sun xama nata har abada" ta riga ta gama shirya duk yadda xatayi ta yaudari masoyinta Jarmai ta kwace dukiyar ta gudu da ita cikin uwa duniya" Daga nan ba wanda zai sake jin duriyar inda take" sai dai in ana labarinta idan ta fara gina kampanoni" tasan cewar mutane da dama xasu tsananta binciken yadda akayi ta xama biloniya tun tana budurwa ko karatu bata gama ba" tace a xuciyarta" Idan na sami kudin dole ne ayi shakkar tabani" suri ta sake murmushi" Dole ne suri ta riga girmama kudi da dala a duniya Domin kuwa taci bakar wahala a rayuwarta kamar 'yar mahauniya" tun lokacin da aka yaye ta a hannun wata azababbiyar kakarta ta girma" wacce kullum idan xa.ayi lissafin gaskiya bana dokin rano ba" to sai ta lakada mata shegen duka sau bakwai ko sau tara a rana" kuma ba wani laifi ma take yi ba" laifin dai kenan idan ta dora mata talla bata sayar ba" kuma a kullum kakar suri takan dora tukwanen shinkafa gudu uku manya-manya kamar mai saida kan awaki" Haka suri ta rika daukar su a bangaji daya bayan daya" duk sai sun kare" Idan dare yayi aka xo kan lissafin ribar da aka ci" kullum kafin suri ta kwanta barci sai kakarta ta nemi lafiyayyen itace tayi mata dukan ala-tashemu lafiya" domin kuwa a ka"ida indai akayi lissafi ba.a ci ribar jaka uku ba" to suri ta banu ta lalace" . SAI lokacin da ta samu ta gama sakandire ta shiga jami'a sannan ne Allah ya raba suri da masifar wannan kaka tata" domin kuwa tun lokacin da ta kawo karpi suka fara sa"insa da tsohuwar" Watarana suri ta koma gida hutu daga jami'a tayi xanxaro da jaket mai ruwan kasa" wadanda samarinta na jami'a 'yan duniya suke saya mata" xaman ta keda wuya" ko ruwa bata sha ba" sai kakarta ta nufi murhu ta fara neman itatuwa tana cewa" "Ai naji dadi da wannan hutu da kuka samu suri" dama duk na kosa ki dawo wallahi" haka nan nake xaune ba cas ba as" tun da kin dawo da wuri yanxu bari in dora maki shinkipa ko tiya hudu ne" tunda rana tayi" ala bashi gobe sai mu tashii da shiri" mu girka shinkafa tiya takwas wake tiya uku" SURI tayi banxa da tsohuwar tana ta kicin kicin ragar shinkafa" bayan taci aikinta ta gama shinkapa ta nuna cike da tukunya" sai kakar suri ta leka daki" ta sameta tana duba alban din hotunan da suka yi ita da kawayenta da kuma samarinta a jami'a" kakarta ta daka mata tsawa tace" "ke nake jira ga shinkapar can xan kwashe" so nake kiyi hanxari shinkafar tayi rana in kinje can saiki ci taki" SURI tayi murmushi sannan tacewa tsohuwar" "kaka ai wannan xamanin kuma ya wuce" yanxu ni 'yar jami'a ce ba 'yar sakandire ba ce!" Tsohuwar ta matso kusa da ita ta rike kugu tace" "suri ubanki nace" ko bakya jina" nace ubanki!!" wato har kin fara koyo fitsara daga xuwanki jami'ar ?" to bara in fada maki" wallahi tallahi ko ferfesa kika xama a gidan nan sai kin daukar min tallata" xaki tashi kije ki nada gammo ko saina ci ubanki?" Suri ta sake yin murmushi sannan taci gaba da bude alban din hotunanta" bata ko daga kai ta kalli tsohuwar ba" kakar tace" "Au! To nasan abinda kike so" kin rabi da samu ne shiyasa" tayi sauri ta fita waje ta nufi inda take ajiye itacen konawa" ta xabo wani mukeken faskare tana ta sumbatu tana ce" "Ina amfanin abaka rikon maraya" tun kina jaririya da iyayenki suka yanke jiki suka fadi" shegiya nina daukoki ina ta wahala dake" wato yanxu kin girma kin shiga jami.a" shine xaki yi min ixkanci" to baki isa ba yarinya" Tsohuwar ta fada cikin dakin rike da faskarenta" suri ta mike a fusace ta rike itacen a lokacin da tsohuwar take shirin kawo mata duka tace" "Gaskiya fa kaka wallahi baxan yarda kullum kice xaki rika dukana kamar kin sami jaka ba" yaya kawai na girma zaki rika takura wa rayuwata" yakamata ki rika wayewa" ki gane cewar da fa" ba yanxu bane" Tsohuwar ta xaro idanu cikin mamaki tace" "Ni ai banyi ilmi ba" bansan komai ba sai talla da duka" kuma tunda kince min kin girma kin wuce duka da talla" to mu xuba ni dake shege ka fasa" dan halak sai yanka" Tsohuwar ta kama jikarta da kokawa kici-kici" da yake irin mutanen da ne" tasha sauyoyi da jike- jike tana nan garas da karfinta" ta dauki suri ta buga da kasa" ta shake mata wuya da kumbunan hannunta" Da suri taga tshohuwar xatayi mata lahani" saita xame jikinta" sannan ta tashi ta ruga a guje ta nufi kofar gida" tsohuwar tabi ta a guje cikin tsautsayi sai taci tuntube da tukunyar miya a kafafuwa ta fadi ta sake wuntsilawa" kakar suri ta fara kururuwa mutane suka shigo suka kawo mata dauki" bayan an duba tane aka ga ta karye guri biyu a kafarta" ta dama sannan ta goce a hannunta na hagu" Tun daga wannan rana ta xama gurguwa" kuma tun daga nan suri ta sami sauki" dole sai dai ita ke dawainiya da ita" shiyasa suri take bin samari 'yan duniya suna kashe mata makudan kudi" rabi tayi hidimar karatunta" rabi kuma ta aikawa kakarta gurguwa wacce ke xuwa yawon bara da sanda" . A halin yanxu da suri take tsaye a saman benen cikin duhu" tana shakar daddadar iska mai cike da kamshin damina" kuma mai sanyaya xuciya" saida ta tuno da axababbiyar kakarta dake acan gida tana yawon bara" daga gobe kakarta ta daina xuwa bara" suri tace a xuciyarta tana murmushi a bayyane" domin kuwa gobe ne xan xama miloniya" daga ni har dangina mun gama shan wahala a rayuwarmu ta duniya" Allah yasa Jarmai yayi nasara yaxo mana da kudin" . Suri ta bar jikin karpen benen cikin fara.a ta nufi dakinsu ita da Raliya" da kuma wata iyamura mai suna MARY Da xuwa ta sami Raliya xaune gaban kyandir din dake a jikin teburin karatun su" ta bude wargajejen akwatinta mai taya baki" tana ta kimtsa kayanta a ciki wasu ma basu bushe ba" haka nan take ta faman cusasu" suri ta matsa kusa da ita" ta dafa kafadar Raliya tace-; "Allah sarki kawata" shike nan xaki tafi ki barni" Raliya tayi murmushi" sannan ta dubeta" "Kada kidamu suri" tace da ita" sannan ta dauko wata rigar mama ta jepa a cikin akwatin kayanta" wata rana ai xamu sake haduwa" in dai bake ce kika jepar dani ba" Suri tace "Baxan taba jepar dake ba Raliya" duk da yake xan xama miloniya baxan mance dake ba" da karpe nawa xaki tafi goben?" Sammako xanyi tun da sassafe" Raliya tace da suri" sannan ta koma kan littatafanta dake xube akan katifarta" suri ta dafa kawarta sannan tace da ita cikin murmushi... . . LOADING PAGE 04RALIYA-04 . "SAMMAKO xanyi tunda sassafe" Raliya tace da suri. Sannan ta koma kan littatafanta dake xube akan katifarta" suri ta dafa kawarta sannan tace da ita cikin murmushi" "zuwa lokacin kudina sunxo" in da rabonki kema xan dan yaga maki ko dubu dari ne" kawata ko kuwa me kika gani?" Raliya tayi tsaki" sannan ta debo littatafan ta xuba a akwatinta" . =======>*******<======== LOKACIN da abokan Elbashir suka shiga cikin falon ne" suka same shi a tsaye!! "ku nake ta xaman jira" tun daxun. Na dauka cewar baxa ku sami xuwa bane" Daya daga cikin bakin uku ya hade fuska yace" "Haba Alhaji me xai hanamu xuwa kuwa?" maganar kudi ba maganar wasa bace" yi sauri ka fito mana dasu kowa ya dauki kasonshi" Elbashir ya dubi fuskokinsu yaga ko wanne a murtuke yake basa fara'a yasan cewar tuntuni tun lokacin da suka mara mishi baya ya wawuro wadannan kudade" dama suna xargin da wahala idan bai ha'incesu ba a wurin kasafin da xa'ayi to amma kuma da ace ma anan kadai abin xai tsaya to da da sauki" "Ina fatan dai ba wanda yasan wannan magana" domin kuwa wannan sirrine tsakaninmu mu hudu" wani mai katon kai a cikin bakin yace a fusace" "Haba Alhaji sau nawa xakayi mana wannan tambayar?" kada ka daukemu kananan yara mana" duk duniyar nan wa xamu fadawa irin wannan sirri mai girma" yanxu maganar kasafi takawo mu" ka gaggauta don mu gama da wuri kaga dare na kara yi" Elbashir yayi murmushi" maimakon ya shiga cikin dakin ya kinkimo akwatin kudin" sai suka ga ya tafa hannayenshi fas!! Bakin suka dubeshi a tsorace cikin rashin yarda domin kuwa sun san cikakken ibilishiii ne" yanxu haka wata makarkashiya yake so ya kulla musu" kafin su san me yake faruwa ne" sai suka ji karar harbin bindiga a bayansu" mutum biyu a cikinsu suka yi koli-koli a cikin falon suka fado kasa cikin jini ko shurawa basu yi ba" dayan kuma yana inda-inda a rude" sai wani harsashi ya sheko a guje ya fada cikin malum-malum din da ya jibga" ba wanda yasan inda harsashin ya nufa da gana nan" sun dai ga mutumin yayi tsalle ya hadu da bango" daga nan wurin yayi tsit kamar anyi ruwa an dauke" gaba daya mutanen sun tafi barxahu" . A gaisheku jarumai" Elbashir yace da ifiritan samarin biyu wadanda ke tsaye a bakin kofar falon" bindigogin su na fitar da tiriri" suka matso xuwa cikin falon" suka dubi gawarwakin mutanen da suka kashe" Mai bakar rigar yace a fusace" "Akwai wani aikin da xamu sake yi maka kuma Alhaji? Elbashir yace dasu" "Ina so ku kwashe su ku sakasu a mota" nabar muku su kyauta idan kuna so" Nidai ku kwashe min su daga nan" Amma ku tabbatar kun batar dasu ta yadda har abada baxa a gano su ba" bayan kun gama sai ku dawo in sallameku ragowar kudinku" Nan da nan Ifiritan biyu suka fara kinkimar gawarwakin bakin da suka kashe daya bayan daya" suna kaisu cikin motar da suka xo da ita" awaje" . Wadannan ifiritai biyu da basu dauko rayukan mutane a bakin komai ba" suna da tarihin rayuwarsu kamar yadda ko wanne dan adam yake da nashi tarihin" Matsalar kawai itace su nasu baiyi kama dana sauran mutane dake a duniyar mutanen kirki ba" Mai bakar rigar wacce ke da hoton damisa a baya" sunanshi DUMFANA" mahaifiyarshi ce kawai data rage masa a duniya" ita kadai tasan sunanshi na gaskiya" ita ma kuma rabon da ta sakashi a idanunta bana shekara goma sha biyu (12) cif-cif" tun wani ciwo da yayi a wajen yawon duniyar shi aka mayar dashi garin su" bayan ya warke sai ya sake baxama ya fito" tun lokacin bata kara jin duriyar shi ba" don haka babu wanda xai ce yasan sunanshi" . Shi kuma dayan mai shudiyar singileti sunanshi GAMBO" amma kuma shi a iya cewa sam barka ansan sunanshi na lakabin rana wato DANLITI saidai kuma idan mutum ya shekara yana neman shi indai ba Gambo yace ba" to da wahala ya samu wanda xaice ya sanshi" Wannan shakiyan samari guda biyu abokan juna ne na GANI KASHE NI" domin kuwa a wajen yawon dambe suka hadu" daga sana'ar dambe kuma sai suka koma satar kekuna" Bayan nan sunyi sana'o'i da dama" daya bayan daya dukansu na alatsine da tir!! Daga bisani ne suka ci birki a guda daya wato sana'ar kisa da gangan" Idan kuma sun dauki lokaci mai tsawo basu sami wanda xa'a kawo su kashe ba" sukan tuna baya suje suyi fashi da makami" . GAMBO DA DUMFANA" suna kammala kwashe mushikan barayin" suka xubasu a mota suka tuka a cikin daren suka tafi" su kadai suka san inda xasu kaisu su watsar" Elbashir yayi ajiyar xuciya daya ji sun tafi da motar" ya shiga cikin daki ya jawo bakar akwati mai tayoyi wacce ke cika FAL da makudan kudin" ya xauna dirshan a falon kamar dan shayi" ya bude akwatin a tsanake ya dubi sababbin dalolin amurka suna ta sheki a ciki" Yayi murmushin farin ciki" domin kuwa duk duniya shi kadai yasan wannan lamarin a halin yanxu babu wanda xai tona mashi asiri" Elbashir yayi jugum a xaune yana kallon kudin" alokaci guda yana tunanin abubuwan da xaiyi dasu a duniya" . Abu na farko daya fara xuwa mashi a rai shine.....RALIYA-05 . RALIYA ta shiga cikin motar ta xauna tare da sauran fasinjojin" yaron ya shigo ya rufe kofar direban yaja suka tafi" Ga al'adar xaman mota ba wanda ya damu da wani" fasinjoji ne duk da raliya baya a gaba biyu na a kujerar tsakiya" mutum hudu sun warwatsu" a sauran kujerun baya" kowa yana ta tunanin da ya dameshi" kamar yadda raliya ta dukufa yin nata tunanin" bayan ta ciro kudin mota ta bayar" Ba a fi minti biyar ba da fara tafiyar su ba sai wani fasinja ya sake tare su cikin sauri" yana sanye da gajerar riga da wando mai ruwan kasa" yana dauke da nashi murgujejen akwatin a hannunshi" yaron motar ya bude kofar bayan motar ya tsaya" Sannan ya bude but din motar yakai hannu ya amshi akwatin fasinjan" da farko mutumin bai so ya bashi akwatin ba" domin kuwa yafi so ko ina xai xauna ya kasancee tare da akwatinshi domin kuwa ba abin wasa bane a ciki" to amma don kada mutane su xargeshi saiya mikawa yaron motar ya saka a cikin but din motar" tare da akwatin Raliya wacce xata koma kauyensu" shi kanshi yaron motar saida abin ya bashi sha'awa daya ga an jera Akwatina biyu irin su daya a bayan motar" kowanne yana ta sheki ajikinshi an rubuta (Japan Express ) . Yaron motar ya dawo cikin motar ya xauna" direban yaja suka tafi" wannan fasinja daya shigo motar yanxu" mai akwati irin na raliya 'yar makaranta" akwai alamar damuwa mai yawa a tare dashi" domin kuwa shima tun sanda ya shigo yayi tagumi" motar tana tafiya yana ta faman waige-waige sai kace yana tsammanin wasu suna biye dashi" TO amma kuma idan ma har yayi wannan xato ba laifi bane domin kuwa shi kanshi yasan cewar ya kinkimowa kanshi uwar rigima" wacce idan ba wata kwakkwarar sa'a ya taka ba" to xai yi wahala idan bai bar baya da kura ba" mutumin yayi ajiyar xuciya sannan ya dubi budurwar dake xaune kusa dashi mai yiwuwa irinshi ce" duk abin duniya ya isheta" to amma kuma matsalarta tasha banban da irin nashi" gashi dai sun shigo mota daya" sannan kuma akwatinan da suka shigo dasu cikin motar duk irinsu daya" amma kuma basu damu da suyiwa juna magana ba" Lokacin da mutumin ya dubi yatsun Raliya ne sai yaga wani xobe a dan yatsanta wanda yayi kama da xoben da ya taba ba masoyiyarshi dake jami'a baiyi kawaici ba saiya tambayeta cikin tausasa murya" "Yan mata ina kika samu wannan xuben don Allah?" Raliya ta dube shi a karo na farko tun shigowarshi cikin motar" sannan tace dashi cikin mamaki" "Kamar yaya ina na samu wannan xoben" malam wannan wacce irin tambaya ce haka?" RALIYA tayi tsaki sannan ta kawar da kanta xuwa wani bangare tana kallon bishiyoyin dake wucewa a gepen titi" domin kuwa tasan cewar dama akwai irin wadannan mutanen masu karambanin yiwa 'yan mata magana a mota" Gashi kuma ita ba a irin wannan surutun da ita in har tahau mota to da xarar ta biya har a sauka ba wanda xaiji muryarta" Ralita tayi tsammanin mutumin ya rabu da ita" to amma kuma xuwa can sai taji ya sake yafitota a hankali" lokacin da ta juyo ne a fusace ta dubeshi sai ya dukar da kanshi kusa da kunnenta yace da ita" "Kiyi hankuri 'yan mata dama ba wani dalili yasa nayi maki wannan tambayar ba" ina da wata masoyiyata ce dake jami'a wacce na taba bata irin wannan xoben" sunanta SURI ni kuma sunana JARMAI" . ======>*****()******<======= ALHAJI ELBASHIR ya dauki tsawon lokaci akwance bai san inda kanshi yake ba" jinin dake xubowa kadan" kadan" daga cikin raunin dake a kanshi ya gangaro yana malala a fuskarshi" bayan ya kwashe kwararan awoyi biyu a haka" xuwa can sai numfashinshi ya dawo" sannan ya fara motsa yatsun kafarshi da kuma hannayenshi" ya dauki lokaci mai tsawo yana haka kafin ya fara yunkuron tashi ya xauna" Duk wannan abu dake faruwa hankalin Elbashir yana kan akwatin kudinshi da ya bari a bude a tsakar falon" har xuwa lokacin da ya tuno cewar an sami akasi wata matsala ta faru" bai amince da xargin da yake rayawa a ranshi ba na tunanin wani ya shigo ya tafi da akwatin" Yasan cewar hakika an shigo bai sani ba" kuma ya tuno cewar an kwada mashi wani abu mai kamar karfe akai" to amma kuma duk da wannan yana saran idan ya farfado xai laluba yaji ba su" to tabbas dole ne ya amince da xargin da baya so" wanine ya shigo yayi awon gaba dasu" wanda kuma idan har haka din ta kasance to dole ya dauki mataki kwakkwara" Elbashir ya samu da kyar ya tattara karfinshi wuri guda" ya fara kokarin tashi ya xauna" to amma kuma juya tana dibarshi" da xarar ya kusa xaunawa sai kuma ya koma ya sake faduwa yaraf! Sai kace yasha barasa" Bayan yaga wahala yana kokartawa" xuwa can saiya samu sa'a ya xauna" tun baya iya ganin komai sai duhu" har ya share fuskarshi da hannun rigarshi" sannan ya fara ganin abubuwa dake a cikin dakin" to amma kuma cikin rashin sa'a sai yaga wayam" babu katon akwati" nan da nan sai yaji gabanshi ya fadi" ya sake waigawa ko ina a cikin falon" babu akwatin kudi ba dalilinshi" "DALA MILIYAN HAMSHIN" shinkenan sunbi ruwa" Amma kuma dole ne ma ya nemo su ko ina suka shiga a duniya" Elbashir yace a fusace" ko xan rasa raina saina dawo da abina!" ya karashe maganar cikin daga murya" Yana nan cikin falon yana ta surutai shi kadai saiya kai ganinshi xuwa tsakar dakin inda yayi male-male a lokacin da hadarin ya faru" Elbashir yaga wani dan mabudin mota a kasa akan darduma" nan da nan yayi hanxari yakai hannunshi ya dauki mabudin" dubawarshi keda wuya sai yaga hoton Jarmai a cikin gilashi a baya kuma hoton wata budurwa ne" to amma kuma bata hoton budurwar yake yi ba" Ganin hoton Jarmai da yayi shiyafi komai tayar mishi da hankali" domin kuwa a halin yanxu ya tabbatar da abin da ya faru ko shakka babu Jarmai ne ya shigo yayi mishi wannan muguwar ta'asa" "JARMAI..!!!" Elbashir ya tambayi kanshi cikin mamaki" bai taba tsammanin Jarmai yasan da wannan sirri ba" na wadannan makudan kudi da suka sata daga gwamnatin tarayya" Gashi yanxun ya biyo sawunsu kuma yayi nasara" tabbas Jarmai ne ya shigo ya doke shi" ya dauke akwatin kudin ya gudu abinshi" Tun Jarmai yana karami Elbashir ke rike dashi" wannan ya samo asali ne a lokacin da yayar Elbashir mai suna LANTANA taxo ta sameshi da maganar hatsabibancin da danta Jarmai yake yi mata" baban Jarmai ya dade da mutuwa yabarta da rigima" mahaifiyar Jarmai ta kaishi karatun allo can wani gari mai nisa" domin ta huta da axabarshi" acan makarantar ko sati ba'a yi ba jarmai ya rotsa kan almajirai uku da allo suna fada" da malamin yasa a kamo shi ne ya gudu" akasa ya dawo gida bayan ya kwana biyu yana tafiya" A ranar da ya dawo ya kwashe tiramen xannuwan mahaifiyar shi Lantana ya sayar yaje aka cinye kudin a wajen caca" Da Lantana ta kwashe duk wannan labari ta shaidawa dan uwanta Elbashir sai yace ta kwantar da hankalinta xai yi mata maganin Jarmai zai daukoshi su xauna tare" tun daga wannan lokaci shekaru ashirin kenan xuwa yanxu" Jarmai yana hannun Elbashir " ya sashi a makaranta tun yana karami amma yaki karatu" ganin haka saiya mayar dashi boyi-boyin gidanshi yana aikenshi wurare daban-daban" yana taka tsan-tsan da halinshi" Daga lokacin da Alhaji Elbashir ya fara xama da wannan hatsabibin da nashi Jarmai ya kamashi da laifuka da dama" kadan daga ciki sun hada da dauko matan banxa yana kawosu gidanshi" da kuma shaye-shayen kayan maye" To amma kuma duk wadannan laifuka basa damun Elbashir " abban abinda ya tsana a rayuwarshi ta duniya shine ayi mishi sata" daka daukar mashi kwandala daya ya gwammace kayi tatul da giya kaxo ka xaxxageshi kayi ta kwara mishi amai a jikinshi" shiyasa suka dade tare da Jarmai basu bata ba shekara da shekaru" domin kuwa Jarmai baya daukar mashi ko anini" idan yana son kudi yakan xo ya tambayeshi" To amma gashi yanxu ba xato ba tsammani Jarmai ya sake hali" ya fara sata gawurtacciya" babu mamaki dama can kwanton bauna yayi" hakika ya shammaci kawunshi Elbashir to amma kuma baiyi nasara ba" Elbashir yace a xuciyarshi" xan nemoshi duk inda ya shiga" ya daga mabudin motar a saitin fuskarshi ya dubi hoton Jarmai cikin tsananin fushi kamar ya jawoshi a cikin hoton ya kashehi" yace dashi cikin kunan rai a bayyane" "Asirinka ya tonu munafuki" saina kamaka duk inda ka shiga" kuma saika dawo min da kudina" DALA MILIYAN HAMSIN" baxa su taba kubce mani ba"! Saina ganoka yaro" . Elbashir ya mayar da numfashi sannan ya shiga cikin wani daki dake jone da falon" da shigarshi yakai hannu inda wayarshi ta sadarwa take akan wani teburi karami" ya danna lambobin wayar" sannan ya saurara yana rike da hannun wayar a kunnenshi" xuwa can ya fara magana a fusace" "Hello! Nine Alhaji Elbashir "Yi maxa ka kira min kwamishinan 'yan sanda kace nine ke magana" akwai muhimmiyar maganar da xamu tattauna dashi" "Zuwa can Elbashir ya dakawa wanda suke magana tare tsawa sai da dakin ta masa kuwwa" "Yayi barci?" kace a tasheshi babu lafiya ne" bana so kana bata min lokaci" A daidai lokacin ne akayi walkiya mai haske a sararin samaniya" sannan akayi tsawa" yayyafi mai sanyi ya biyo bayan haka" . =======>******^*****<====== . Kwamishinan 'yan sanda C.P RAIYANU DANMASANI yana xaune yana fuskantar mataimakan aikinshi su biyu sun yi mishi tsuru" suna sauraron abinda xaice dasu" domin kuwa tun lokacin da ya buga masu waya a gidajensu yasa matansu suka tattashesu a cikin wannan talatainin dare yace su hanxarta xuwa su sameshi yana a gida yana jiransu" Sun san cewar babu lafiya inma kuma da lafiyar to akwai wani babban al'amari daya faru mai Zafi-zafi wanda yake bukatar jan damarar yaki" Kwamishina 'Danmasani dogo ne dan kimanin shekaru hamsin a duniya" fuskarshi ta fara tattarewa kadan" sannan kuma furfura ta fito jefi-jefi a cikin sajenshi da kuma tumbujejen gashin bakinshi" kullum kanshi a aske yake kamar tulu" tun lokacin da yana karamin ma'aikaci yana matukar alfahari da..............RALIYA-06 . TUN lokacin da yana karamin ma.aikaci yana matukar alfahari da jajayen idanunshi dake boye a cikin loko kamar idanun maciji" da kuma faskeken hancinshi da ya tsare rabin fuskarshi" sau da yawa idan ya hade fuska ya kalli mai laifi" tun kafin yace wani abu wasu ke fara kuka" domin kuwa har gara mutum ya hada idanu da namijin zaki a daji da ya hada ido da DAN MASANI . Mataimakanshi biyu da yafi shakuwa da su A.C.P AMINU JAN ZAKI" da kuma ACP BILYA dukan su suma tsofaffin Ma'aikatane da suke dade suna shan damara tun a xamanin yakin basasa" Har yanxu a ckinsu babu wanda ya mallaki abinda ya wuce gida da kuma tsohuwar mota banda motar ofishi da ake xuwa da ita a daukesu" har gara kwamishina yana da 'yan kadarori da ba'a rasa ba" to amma kuma idan aka kwatantasu da hidimar da yake yi da bila'adadin 'yan'yanshi sai dai ayi hamdala amma kuma baxa ace an samu yadda ake so ba" Kwamishinan 'yan sanda ya dubi fuskokin mataimakanshi dake xaman jiran yace dasu wani abu" ya gyara xama sannan yace" Nasan cewar xakuyi matukar mamaki a dalilin wannan kira da nayi maku" wata magana ce ta taso mai girma a tsakanina da ku" Ina so ku tattara hankalinku wuri guda" domin kuwa mun sami dukiya mai yawa wacce xata amfanemu da 'ya'yanmu da jikokinmu har karshen rayuwarmu Amma sai kun bani goyon baya" mun hada kai sannan xamu cimma wannan dama data fado hannunmu" Tsofaffin 'yan sandan sukayi saurin gyara xama da sukaji maganar da kwamishina ya fada" nan da nan suka girgiza kawunan su domin su karfafa mashi gwiwa yaci gaba "Yanxun nan bada dadewa ba" kwamishina yaci gaba" Alhaji Elbashir ya kirani a waya" har nayi barci yasa aka tasheni" dana dauka ne yake sanar dani gaskiyar abinda ya faru a tsakaninshi da wani dan uwanshi" wani yaro mai suna JARMAI Elbashir ya sanar dani cewar Jarmai ya sace mishi kudi har dala miliyan hamsin" ya gudu dasu a cikin daren nan" ya sanar dani ne domin mu taimaka mishi cikin gaggawa a samu a kamo barawon tun kafin yabar garin" yace zai bamu ladan dala miliyan daya" idan har muka taimaka mishi muka kamo Jarmai Tsofaffin dake sauraron kwamishinan suka kalli juna cikin murmushi" domin kuwa ladan aikin yana da yawa" akalla zasu sami kudi mai tsoka ACP Aminu jan Gwarzo yace cikin doki" "Ya kamata mu gaggauta mu kamo barawon domin kuwa dala miliyan daya kudi ne masu yawa yallabai ACP Bilya yace" "Kwarai kuwa yallabai indai xai cika mana wannan alkawarin lallai ya kamata mu kokarta mu kamo barawon cikin hanxari" Kwamishinan 'Dan masani yayi murmushii sannan ya dawo cikin kankanin lokaci ya murtuke fuskarshi" mataimakanshi biyu suka yi ajiyar zuciya" domin kuwa murmushinsa yafi xama abin tsoro fiye da abin sha'awa yawancin murmushin yafi kama da yanayin da xaka gani a fuskar busasshen tsohon da aka tsirawa allura . Har yanxun baku fahimci inda bayanina yasa gaba ba" kwamishinan yace dasu" wadannan kudi da yake so mu kwato mishi kada ku taba tsammanin idan suka xo hannunmu xamu mayar masa" domin kuwa shima ba nasa bane" kuyi tunani xaku fahimci abinda nake nufi" a ina Elbashir xai samu dala miliyan hamsin a kasar nan"?" Nasan cewar shima sato su yayi a asusun matatar man fetur yana so ne mu rufa mashi asiri da xarar kudin sunxo hannunmu sun xama namu wannan rabo ne daga sama ya fado a hannunmu" Tsofaffin 'yan sandan suka dubi junansu" cikin tsananin rudewa da murna" domin kuwa indai har abinda kwamishina ya fadi gaskiya ne" to hakika sun gama hayewa" kwamishina yace dasu" "Ina so kuyi hanxari kuje can ofis ku sami yara hudu ko biyar na amana wadanda xasu yi mana wannan aikin" ina so kafin nan gari ya waye su nemo mana shi Jarmai din" suxo mana dashi nan" kun ga da xarar sun kamo mana shi sai mu amshe kudin mu boyeshi a inda baxai kara fitowa ba har abada" balantana ya tona mana asiri" kun ga sai mu kasa wannan kudi kowanne a cikin mu ya adana abinshi domin akwai hadari idan muka ce xamu kai banki" yafi kyau musan inda xamu boyesu a gidajenmu" ko me kuka gani?" . Wannan haka yake yallabai" suka ce a lokaci guda a cikin biyayya" a cikin dan lokaci kankani har sunyi sharkaf da xufa duk da yake cewar yayyafi akayi a waje" nan da nan suka tashi a cikin daren suka baxama domin xuwa ofishinsu su nemi 'yan sandan da xasu yi masu wannan aikin cikin gaggawa" Har xuwa lokacin da tsofaffin 'yan sandan suka tura rundunar 'yan

Chapter 2 of 11