Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mamaci tunda dai ba addu'a 'ya'yanshi suka iya ba" noma kawai ya koya masu" kuma shi zasuci gaba da yi suna ajiyewa suna saran zaifi kowacce shekara tsada Lado yafi kowa jin dadin wannan mutuwa acikin 'ya'yan mamacin" domin kuwa raba gadon ke da wuya yaje ya sayo sabon babur (Jencheng) Sannan kuma duk ranar kasuwan garin idan ta Zagayo sai ya fitar da buhuna goma a cikin buhuna dari biyu da arba'in da ya samu anashi rabon" A cikin wata bakwai ya karar da buhunan ya kashe kudin baki dayansu" daga baya kuma yasayar da babur din da yake yiwa samarin kauyen barazana dashi" yawancin 'ya'yan Alhaji Hashimu sun fuskanci irin wannan matsalar" domin kuwa basu iya wata sana'a ba" gashi kuma wande ke matsa masu fita gona tun da Asuba ya fadi" suka shiririce suka kashe dan abinda suka samu na gado" wasu suka sayar da gonakinsu" masu motoci tuni sunci kasuwa a birni sun kashe kudin" Rayuwarsu ta kuntata" wasu suka fita birni neman kudi suna aikin wahala" wasu kuma suna sakin matansu" domin su ragewa kansu aiki" Abu daya lado ya bari bai sayar ba a cikin kayan gadonshi" wani gidan ne a kusa da kasuwar garin kuma shidin ma wani kansila dake a garin ya so ya saya mahaifiyar lado mai suna HAIRE ita hanashi sayar da gidan" Tace dashi. . .RALIYA-25 . Mahaifiyar Lado mai suna Haire ita ta hanashi sayar da gidan" tace sai tayi mishi baki idan ya sayar kuma lado yafi jin tsoron bakinta" domin kuwa wani abokinshi watarana sunje satar mangwaro a bayan gari yake shaida mashi cewar "Uba sai ya tsinewa danshi sau miliyan bata kamashi ba" Amma uwa data tsine sau daya to mutum ya shiga uku ya lalace Wannan shine ilmin da lado ke takama da ya sani" domin kuwa a karyar abokinshi da ya ruwaito wannan zancen shima yace a wajen wani malami yaji dake wa'axi a kasuwa don haka ya rike wannan gida nashi da mutunci wanda ke da dakuna uku da zaure hade da dakin girki da katanga" Duk da gidan kasa ne" anyi mashi rufi na Zamani" an buga kwano kuma anyi sili da wani kwali mai karfi" Anan lado yake zaune shi kadai tun rasuwar babansu" kuma anan suke wuni shi da manyan abokanshi biyu suna shaye-shaye" wato bala da bangis Sa talauci ya ishe su ne suna zaune aikin yi" sai suka fara yawon sata Da farko kananan sace-sace suke yi" to amma da suka ga wuyansu yayi kwari sai suka fara babbar sata wato kwace" da kuma fashi da makami" Duk da ana zarginsu da wannan hali" rana bata taba baci aka kamasu ba" Amma ana taka- tsantsan dasu a cikin garin" kuma 'yan sanda suna nan suna lura da duk wani motsi da sukeyi A wannan karon lado ya isa gida a guje dauke da miliyoyin kudin shi" bayan ya sami sa'ar tserewa 'yan sandan saiya fara tunanin inda zai boye kudin" Lado ya kulle kofa ya ajiye akwatin a kasa" ya durkusa hannunshi yana rawa ya sake budewa" Ba rufa ido bane kudi" Dalolin Amurka Sababbi!! Lado yasan cewar yana a cikin hadari" domin kuwa babu yadda za' ayi mutum ya tsinci irin wadannan makudan kudi ya boye su ya zauna lafiya" dole ne a tsananta bincike" kuma dole ne afahimci wanda ya same su indai zai fito dasu ya rika facaka a cikin al'umma Yanzu menene abin yi? Lado ya tambayi kansh" sai a lokacin ya tuno da abokan tafiyarshi su bala da bangis" A wanne hali suke ciki an kama su?" ko kuma suma sun gudu sun kai labari" Lado yasan cewar inhar 'yan sanda sun kama su" to shima asirinshi ya tonu" domin kuwa idan aka tuhume su dole ne su fadi sunanshi" kuma duk inda ya shiga za'a bishi akwakuloshii" Lado yaji tsoro ya kamashi" lallai zama bai ganshi ba" to amma kuma yaya zaiyi da wannan makudan Kudin ?" zai yiwu ace ya tafi dasu duk inda zaije" Akwai matsala babba" dole ne ya boye su kamar yadda yayi niyya tun farko" idan ya gudu ko awanne zamani" kuma komai dadewa idan yadawo zai iya dauko abinshi" ba tare da kowa ya sani ba" Lado ya mayar da akwatin ya rufe cikin sauri Zuciyarshi na bugawa aguje kamar tabaren injin nikan ruwa" A ina zai boye su?" Lado ya fara waige waige cikin dakin" babu wani lungu da zai boye su hankalinshi kwance" katifa daya ce shirgegiya wacce ta tsare rabin dakin" sai wata doguwar kujera wacce rigarta ta fara zazzarewa soson ciki ya fara lekowa waje" babu inda zai boye wadannan kudi ba tare da wani ya shigo bai gansu ba" Lado ya daga kanshi sama ya kalli rufin dakin" nan da nan yaji ya samu wajen boye su mai kyau" domin kuwa rufin sili ne kuma ba wani mai karfi bane sosai da zaiyi wahalar budewa" nan da nan ya hau kan kujera cikin sauri ya fara sa hannu ya banbanro siraran katakon da suka taba silin din" bayan ya banbaro layi uku sai ya jawo silin da tsiya ta bude guda biyu a cikin jerin gidajen rufin da aka yi da katako" Lado yayi sauri ya sauko ya kinkimo katon akwatin ya fara kokarin zirashi cikin ramin da yabude a cikin rufin dakin. Bayan ya tura akwatin da tsiya yana rufe idanu saboda kurar dake kakkabowa daga cikin silin din" tana zubo mishi a fuska" sai ya gyara katakon ya mayar da rufin yana tura kusoshin da hannu a cikin ramin su" Lado ya kammala gyara silin kamar bai boye komai aciki ba" yana yi yana digirgire akan kujerar da ya taka ya hau" bayan ya tabbatar komai ya gyara babu wanda zai shigo dakin ya fahimci akwai wani abu da aka boye" sai kuma ya fara tunanin abin da zai yi na gaba zama bai kamashi ba Domin kuwa yasan cewar inhar aka kama bangis da bala" ko kuma idan tsautsayi ya ratsa aka kashe su" to shima asirin shi ya tonu domin kuwa an saba ganinsu tare" kuma kowa yasan abokanshi ne" kuma abokin barawo barawo ne" Lado yaga cewar kamata yayi" yayi sauri yabar garin a cikin wannan dare" domin kuwa a kowanne lokaci bayan yanzu 'yan sanda zasu iya xuwa su kamashi in har sunci sa'ar kama Bala da bangis" Lado yayi sauri ya fito ya kulle dakin shi da kyau" sannan ya fice waje ya bude kofar gidan ya sake kulleta da kanshi" To amma kuma wurin zuwa mai sauki ne" komin dare ana samun mota" duk inda zaije indai har zai bar garin ya tserewa 'yan sanda" to komai yayi kyau" ko yasan lokacin da zai dawo a cikin wani daren" A wani lokaci idan kura ta lafa ya dawo ya bude silin ya dauki kudinshi" Lado yayi murmushin jin dadi" ya ya tuna cewar shifa yanzu miloniya ne Ya sake kallon gidanshi sau daya kafin ya tafi" Ya tuno mahaifiyarshi wacce tace saita tsine mashi idan ya sayar da gidan" hakika tayi gaskiya" domin kuwa da'ace ya ketare maganarta" ya sayar da gidan tuni da yanzu bai san wanda zai dankawa amanar wadannan kudin ba a duniya" Lado ya juya ya nufi tashar moto cikin sauri" yana bin lunguna da jikin gidaje don kada ya gamu da 'yan sanda ko kuma 'yan banga dake faturol din unguwar" yaje bakin titi kenan sai yaji an hura usur abayan shi" wasu 'yan sanda uku suka fara tsaya ya tsaya" Lado ya rude ya sheka da gudu kamar ranshi zai fita" ya fada kan titin bai tsaya dubawa ba" A daidai lokacin ne wasu motoci biyu da suka jero a guje suna tsere a cikin daren suka cim masa" motar dake gaba kirar (IBECO) wacce aka ciko ta fal da lodin albasa ita ta fara yin awan gaba da shi" ta jefar dashi can gaba kan titi" kafin direban ya taka birki ya kaucewa gawar shi" tuni har manyan tayoyin gaba sun haye han lado" Kafin tatoyi ashirin da biyu su gama sukuwa akanshi sanda motar ta wuce har sun nikeshi yayi falle-falle akan titin" motar dake biye a baya kirar (MAN) wacce ta dauko lodin awaki ta karashe dan abinda motar gaba ta rage" . Da safiya tayi sai da 'yan sanda bakwai suka yi minti goma" suna aikin banbare nama da kasusuwan lado wadanda suka kame akan titi" . =====>++++++++++++<====== . BAYAN SHEKARA SHIDA Raliya tana zaune a bakin kofar dakin ta" tana kallon wani dan tunkiya na makwabtansu da kullum yake shigowa sashin su yana cin kanzon abinci dake a bakin kwata" A halin yanzu da dan tunkiyar yake ta zagaye- Zagaye a cikin gidan bai sami kanzon komai ba" sai yayi tsalle sau biyu yayi kuka" sannan ya fita waje a guje" Raliya tayi ajiyar zuciya sannan tace a sanyaye" "muma bamu samu munci ba" ballantana har mu zubar kaima ka samu" Wannan yanayi na babu ya dade" kuma ya zama dan gari a wajen Raliya da mijinta Rufa'i Bana shekara shida kenan da yin aurensu" gashi har Allah yayi wa auren abarka Raliya ta haifi kyakkyawan yaro tun shekaru biyar da suka wuce mai suna Idrisu Gashi a halin yanzu ma wani cikin gareta har yakai wata biyar" to amma kuma ta bangaren rufin asiri" sai dai ayiwa Allah godiya" tun da dai akwai rai da lafiya" A halin yanzu da Raliya take a zaune tayi tagumi tana jiran mijinta rufa'i ya dawo da abin da zasuci" kusan karfe uku kenan na rana" amma kuma abin takaici har yanzu Raliya bata karya ba" Rabonta da Abinci tun daren jiya" gata da ciki to amma ya zatayi tunda babu?" Da a can da farko-farko idan basu sami abin jefawa a baki ba" saita aika gidansu a samo mata abinci" shi kuma Rufa'i sai ya zagaya wajen abokai ya zauna wanda ya dan sami sukuni ya fito da shi" su taru a ci" to amma yanzu abubuwan sun ishi kowa" Yanzu ana cikin tsakiyar rani ne" tsabar hatsi ta dami kowa" to wa zai jure kullum ya rika turo mashi yaro da kwano in ana gajiya ai dole ne yaji da wannan zaman babu na Raliya da Rufa'i Shiyasa take hakuri idan Rufa'i ya samo su ci" idan bai samo ba su hakura yunwa dai ba kisa take yi ba" sai dai asha wahala kafin a samu a ci" Dan su Idrisu ne abin tausayi" shi kuma yaje yawo" yana dai fita gidajen makwabta yana wasa da yara" yawanci acan yake samun nashi yadan ci a hannu a hannu ba yawa sai kaga har ya koshi" Rufa'i yana iya kokarinshi" yana noma kuma yana zuwa kwadago safiya da yammaci" to amma kuma da yake zama ne irin na karkara bai iya sana'a ba" dole dan abinda aka noma ko buhu arba'in ne ba inda yake zuwa" Baya kaiwa wata daminar yake karewa" idan babu lafiya ana bukatar magani dole hatsin nan da za'a sayar" idan sallah tazo a ciki za'a dauka ayi hidima ayi dikci aci nama" Idan dakuna suna bukatar gyara" ko kuma idan katanga ta fadi a ciki za'a dauka a sayar ayi gyara" Ga hidimar bukukuwa da haife-haife basa karewa" idan ana fadin gaskiya kuwa sai dole ne Rufa'i ya shiga tsomomuwa Zama ba sana'a ba dabara bace" Raliya ta dade tana bashi shawara ya kama sana'a Rufa'i ya kan daukar mata alkawarin zai duba ya gani" to amma abinka da mutumin da bai saba abu ba" koya fadi baya cikawa" don haka saita rabu dashi" yayi abinda ya gada kuma ya iya" Mutane suna mamakin wannan baiwar Allah gata 'yar boko kyakkyawa" amma ta hakura sai faman wahala take sha tare da wannan dan kauyen miji nata" gashi wasa-wasa har zata yi haihuwa ta biyu" Raliya bata damuwa domin kuwa tayi tawakkalin tun tana karama tayi amanna da cewar samu da rashi duk daga Allah ne" To me zai sa ta damu kanta" tun da dai mutum bai yiwa kanshi arziki idan suna da rabon jin dadi a duniya" to komai dadewa ai zasuji" don haka babu matsala" Allah yasan halin da suke ciki" kuma shine mai badawa" Don haka komai tsanani indai anyi hakuri to sauki zaizo Raliya tana zaune tana zaman jira" zuwa can sai taji sallamar Rufa'i mijinta" ya shigo cikin gidan, yana fara'a rike da.......... RALIYA-26 . Raliya tana zaune tana zaman jira" xuwa can taji sallamar Rufa'i mijinta" ya shigo cikin gida yana fara'a rike da leda a hannunshi na hagu" ya riko idrisu da daya hannun" Raliya ta amsa sallamar tace dashi "shi kuma wannan a ina ka tsinto shi" ina ta nemanshi zanyi mishi wanka tun dazu" Rufa'i ya saki hannun idrisu ya rugo a guje ya fada jikin uwarshi" Can nagan shi tare da yara a dandali suna guje-guje" ya zauna a gabanta yana murmushi da gani tasan cewar an dace" an samo abinci" to amma kuma ga alama bayan abinda ya shigo dashi a ledar akwai kuma wani albishir mai dadi da ya kosa ya sanar da ita" Rufa'i ya kwance bakar ledar Raliya taga shinkafa ce" yar gwamnati kwano biyu" da fakitin makaroni" da magi" ta rike numfashinta cikin mamaki" domin kuwa rabon da taga makaroni agidan tun tana amarya" sanda abubuwa na farko-farko" kafin gari yayi gari" Raliya ta tambayeshi "Rufa'i me yasa ka sawo shinkafa da makaroni" mu da muke neman masara da kubewa mushashshiya.....? "Rufa'i yaci gaba da yi mata murmushi" suka dubi juna yace "kada ki damu Raliya" in Allah ya yarda wahalar mu tazo karshe" wannan somin tabi ne" Raliya ta dubeshi cikin rashin fahimta" "Kamar yaya Rufa'i nifa ban gane ba" Rufa'i yayi ajiyar zuciya yace da ita" "Da na fita dazu na hadu da wani abokina dake birni" shine yazo ya shaida min wani abin farin ciki" wai yaso ya dauke ni mu rika sana'ar kifi tare" yana so in zama babban yaronshi" zai ajiye ni awani gari inda ake sayen kifi sosai" ya kafa min depot a can yana kawo mani kifin daga birni ni kuma ina sayarwa" to har mun gama komai shine ya bani dubu goma yanzu wacce zan samu mota mu kwashe kayanmu zuwa garin tare Raliya ta rike baki cikin mamaki" "Ina zamu zauna idan mun koma wani garin? Rufa'i yayi mata dariya" "Haba Raliya ga gidajen haya nan ba iyaka" yanzu aduniyar nan wanne gari zaka je ka rasa indai kana da kudi" wannan ba matsala bace zamu samu gida kada ki damu" Raliya sake cewa "to yaya su baba ka sanar da su sun amince kuwa?" Rufa'i yace "Na biyo ta gida na shaida musu halin da ake ciki kuma sun amince domin wannan abin karuwa ne" Raliya duk wanda ya sami labari dole ne ya tayani murna" Yanzu shiye-shirye zaka fara yi" yace jibi yake so mu koma can baki dayanmu" Raliya ta girgiza kai cikin wani sabon mamaki tace "Ai ni abin ne duk yazo mani a kurace wallahi" abu ba zato ba tsammani haka?" Rufa'i yaci gaba da murmushi" "Haka rayuwa take dama Raliya" Idan ubangiji ya nufe ka da samun wani arziki kana kwance abinka ba zato ba tsammani sai kaga yazo ya sameka" In Allah ya yarda wannan sana'a da Zamu fara ta kifi alheri ne" kuma wannan canjin gari da zamu yi mu koma wani garin shima duk alheri ne" bazamuyi dana sani ba" Raliya tayi saurin cewa "Allah ya sa haka" kuma Allah ya taimakemu" Ta zaunar da idrisu danta a kasa wanda yake ta kokarin taka gwiwarta ya kamo wani abu a jikin bango" daga baya ta sake tambayar Rufa'i "wanne gari yace zai ajiye ka inda zamu zauna ya rika kawo maka kifin kana sayarwa?" Rufa'i yace "Ba nesa bane nan ne kusa" yace mani kwanar tsamiya zamu koma" domin ana zuwa sarin kifi agarin kuma yace mani indai na kula to za'a sami riba mai yawa" Da ya ga kamar Raliya tana tunani sai ya sake cewa "ko baki taba zuwa kwanar tsamiyar bane Raliya shine fa wannan garin da aka taba yin wani shaharren manomi wanda duk jihar nan babu kamar shi" sunan shi marigayi Alhaji Hashimu MAI ABINCI HAR BAYAN RAI" . ======>++++++++++<======= . Sai da ya kwace fiye da minti biyar a tsaye a kofar gidan yana tunanin abinda zai fada mata wanda zai kwantar mata da hankali" Domin a yadda suka rabu da safe dazu da zai fita" yasan cewar in har a wannan karon ya shiga baizo mata da labarin sabon gidan da ya nema ba" inda zasu koma" to ba zasu kwana lafiya ba" Ya tsaya shiru yana sake-sake azuciyarshi" wani mutumi ya wuce shi a tsaye sau biyu yana mishi sallama" amma ko dago kai baiyi ba" Zuciyarshi tayi nisan zango" mutumin ya wuce saurayin yana mamakin abin da kesa mutane na dorawa kansu damuwa ba gaira ba dalili da ransu To amma kuma da'ace yasan abinda ke damun wannan saurayi mai suna ABASHE da bai ce hakaba" abashe matsakaici ne mai farar fata wanda ko ba fadawa mutum ba da ganinshi ansan cewar yaci kaji a duniya" to sai dai wannan tuni ya zama tarihi" domin kuwa a halin yanzun ba'a maganar kaza" shi bama ta abinci yake yi ba" ta muhalli yake yi" wannan wannan shine abinda ke hadashi fada kullum da matarshi. abashe haifaffen garin kwanar tsamiya ne" wanda ya dade da fita neman kudi ya dira birnin kano da sa'a A cikin shekara biyu yayi karfi a kantin kwari a dalilin wani ubangidanshi mai kirki da ya samu" wanda ya buda mashi kofofin samun arziki ba mugunta" da bakin ciki" karayar arzikin da ta samu ubangidanshi ne ya sa shima dole ya turgude suka fadi kasa tare da kwance uwa kwance" Gashi kuma kafin ayi haka Abashe ya auri wata yarinya 'yar birni kuma 'yar hutu wacce bata son hada hanya da wahala a rayuwarta" tun faruwar al'amarin mara dadi matar wacce bata fi shekara daya a hannunshi ba" mai suna KUBURA" ta fara juya mashi baya" bala'i na safe dabam" na rana dabam" ga kuma na dare" to amma baya tsayawa a gida kafin ta farka barci tayi bala'in safe" shi tuni yabar gidan yayi nisa baya dawowa da rana kwata-kwata" sai dai idan ya dawo da daddare ta zazzage mashi kwandon tsiyar da ta tara tun safe har daren" Ganin cewar zaman kano bana rago bane" dole ne a tashi a nema" kuma ganin yadda hanyoyi suka toshewa Abashe sai ya yanke shawarar daukar matashi su koma garin su kauyen kano inda ya baro" domin kuwa acan rayuwa da dan sauki ba kamar zama a birni ba ne" inda ko bola ka tara a cikin gida saika bada kudi an kwashe maka ita. Abashe ya daufi fiye da sati daya suna kai ruwa rana da kubura wacce ta tsaya kai da fara bazata bishi ba" sai dai in sauwake mata zaiyi" to amma da ya tsara mata dabararshi cewar Zuwa zaiyi yayi noma a gonar mahaifinsu na shekara daya kacal ya sayar da amfanin gonar su sake dawowa birni su sami jarin yin sana'a saita hakura amma da ganin yanayin fuskarta a sanda suka zo garin to an san cewar dole ce kawai ta kawo ta" kamar yadda kare yake fadi in ance dashi dan kauye Da yake babu sauran dakin da mace zata zauna agidansu Abashe" kuma koma akwai safayar daki" kubura tace bazata zauna a gidan su na gado ba" mai dauke da matan aure goma sha biyu" dakunan su a jere ciki daidai" bandaki daya dafa duka" da kuma dakin girki na kasa" Sai Abashe ya nemi gidan haya" a wani gida a bakin kasuwa na wani barawo da mota ta taba kashewa da daddare" an biyoshi mai suna LADO. . Tun wasu shekaru da suka wuce" dakuna biyu dake a gidan lado marigayin barawon" wani dan kasuwa ya kama su haya aka zuba farin wake aciki yana jira yayi tsada a kwashe asayar" saura daki daya kawai ya rage inda maigidan ya zauna" to amma kuma abin takaici silin dakin ya tuntsiro ya kusa ruguzowa" kamar an dora wasu kaya a ciki" Tun a ranar farko da wadannan ma'aurata suka tare a gidan matar ta fara balbala masifa" domin kuwa a cewarta dakin baiyi mata ba" gara tun da wuri su canza gidan" wannan silin idan ya fadowa mutum ai sai dai azo a ceci bawa bazan iya ba" kwanansu shida kenan a gidan" kullum maganar kenan guda daya" A rana ta hudu ne Abashe yace da ita Kiyi hankuri kubura na fadawa masu gidan wannan matsala kinsan mai gidan ya dade da rasuwa" wata mahaifiyarshi ke iko da gidan" kuma ta tsufa" bata da kudi" amma tace in gyara silin a cikin kudin da zamu biya na haya sai mu warware daga baya" kubura ta turo baki tace a fusace "Sam!! Bazan iya zama sai anyi wani gyara ba" Idan zakaje ka nemo mana gidan mutunci da Zamu zauna kaje ka nemo" idan kuma ba haka ba" to wallahi kaji na rantse maka zan hada inawa-inawa in koma kano" domin nifa dama matsamin kayi ba'a son raina nazo wannan kauyen ba ehee!! Ganin cewa allura zata tono garma" sai ya fara fafutukar nemo wani gidan" A halin yanzu anyi mashi alkawarin awashe gari yaje yaga gidan" sanna ya fadi mashi farashin yaji idan zai iya biya" to wannan shine abin da yake tunani a ranshi da ya tsaya a kofar gidan" yana tsara yadda zai fadawa rabin ran tashi" don ta fahimce shi" su samu dai su sasanta" domin masifar shi ma ta ishe shi. . Abashe ya shiga cikin gidan da zuwa bai zame ko ina ba" sai dakin wanda shine na karshe a jerin dakunan guda uku" ya sami kubura a zaune a bakin gadonta tayi shiru tana tunani" tana sanye da atamfa da kallabinta" tun kwalliyarta ta rana" fitilar kwai ta haske kakkausar fuskarta sai faman cika take yi tana batsewa" Abashe yayi mata sallama ko gezau bata yi ba" da yake yasan irin zaman da sukeyi" sai ya zauna a bakin gadon kusa da ita ya fara lallashinta Kiyi hakuri kubura indai akan wannan gidan ne komai yazo karshe" In Allah ya yarda gobe zamu tashi na sami wani gidan. Kubura taja numfashi mai tsawo tace dashi a fusace Dakata malam" kada ka raina mani hankali batun yau kake yi mani wadannan karairayin ba" Idan zaka bani takardata da arziki ka bani" Idan kuma so kake yi kabani da tsiya" to zamu zuba dani da kai mu gani" amma ni na gaji bazan iya ba" Abashe ya rage murya yace da ita" "Duk abin bai kaimu ga haka ba" kubura kin san ba'a zaune nake ba" ina iya kokarina akan neman gidan nan" kuma tunda an samu menene kuma da wani tsokano abinda ya wuce" daga gobe ta kare" kuma ki bari ki gani" Kubura ta dago kanta ta kalli rufin dakin" ya babbako har wani tozo-tozo yake yi" tace a fusace In ban da wulakanci da harkar karanta ace kamar ni da arzikina da mutuncina ka dauko ni ka.....RALIYA-27 . "In Banda wulakanci da harkar karanta ace kamar ni da arzikina da mutuncina ka dauko ni ka sakani a wannan dakin" silin ya lalace ba'a gyara ba" sai kura ke zubowa yau nayi shara takai sau talatin a dakin nan" Abashe ya sake cewa kiyi hankuri gobe iyanzu kina a wani daki in Allah ya yarda" Kubura tayi tsaki tace Ai kamata yayi ace tantabaru ke kwana anan" kai ni wallahi ko tantabarata bazan ajiye ta anan ba..... Ta sake hararar rufin dakin dama shi yafi komai tunzurata abinda wannan mata bata sani ba shine" wannan rufin daki yafi karfin matsayinta" Da ace za'a ciro abinda ke ciki wanda ya lalata silin ya kusa ruguzowa" Da ace duniya ta san komai ke a ciki a boye tun shekara shida da suka wuce" to ko shugaban kasa zaiyi fatan ya zauna a ciki" Abashe yace da ita a lokaci guda da ya bita suna kallon rufin dakin" "Ni kaina kullum na shigo dakin ina bakin cikin in kalli silin din nan ji har wani doro-doro yake yi sai kace katako ya balle a ciki" "kubura ta yatsine fuskarta sannan ta duba agogon dake manne a jikin bango" taga karfe sha daya na dare saura minti ashirin" ta matsa sosai kan gadonta ta jawo matashi daya ta jefa shi can karshen gadon kusa da jikin bango" sannan ta fara warware bargon dake cukuikuye akan gadon" Abashe dake zaune yana kallonta cikin damuwa yace "Haba kubura yau ma haka zakiyi min" kwanan mu wajen goma kenan fa a haka" ta kalle shi cikin raini" "me kake so inyi maka...?" Ganin wata masifar zata sake tasowa" sai ya rage murya yace da ita "A'a ba wani abu bane dama gani nayi ana zafi sosai" kuma naga zaki kwanta baki dan rage kayan jikinki ba" Ta sake taso mashi da fada tace "to banga damar cire kayan ba" idan kana da karfi kazo ka kamani da tsiya ka cire mani" ta murguda baki tana harararshi" sannan ta juya mashi baya ta kudundune jikinta duka a cikin bargo" har safiya tayi Abashe yana a zaune abakin gadon cikin takaici yana kallonta" . ======>++++++++++<======= . Anyi haka da kwana biyu Rufa'i ya tare da iyalanshi suka bakunci garin kwanar tsamiya" da yamma a cikin wata karamara akori-kura" ta debe su da kayansu" Lokacin da suka sauka a gidan wannan abokin Rufa'i wanda ya kawo shi garin don suyi sana'a tare" sai mutumin ya amshe su hannu biyu da yake dama ya dade da sanin maganar" yace dasu tun kafin su sauke kayansu daga motar" "Ai ba tsayawa bata lokaci za'ayi ba" sai mu wuce gidan da na samar maku" yana can kun baro shi a bakin kasuwa" mutumin ya shiga motar yana nunawa direban hanyar da zai bi tare da su Rufa'i har suka isa gidan hayar da ya samar masu" Ba wani boyayyen gida bane" gidan marigayi lado ne" dan fashin da mota ta kashe a titi" wadanda suka bi wata mai abinci har gidanta suka kasheta" wai ita hajiya tabawa" koda yake tuni an mance da wannan labari a garin" domin ba yanzu abinda ya faru ba shima Rufa'i bai sani ba" gida dai gida ne ko na wanene" kuma shi bako ne haya ya kama" kuma biya zaiyi" mutumin yacewa Rufa'i a lokacin

Chapter 10 of 11