Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
ta fada haka al'amarin ya kasance domin kullum sai ta taimakawa bako ya taka sawayensa. Tun yana yi da kyar da ciza lebe, har ma ya zo ya daina dogara sanda ya fara tafiya tatata, tamkar kankanin yaro mai koyon tafiya. A hankali kafafunsa suka warke sarai ya zamana yana iya tafiya sosai. A ranar da ya kwana goma sha hudu ne ya samu cikakkiyar lafiya, har ma ya kece da gudu a harabar gidan Abul Ishmira, sannan kuma ya dauko takobinsa ya kama wasa jini da ita, yana bai wa kansa horon yaki. A wannan lokaci Ishmira, Farila da Abul Ishmira na zaune a gefe daya suna ta kallonsa kawai cikin tsananin mamaki, domin ba su taba ganin mutumin da ya iya sarrafa takobi ba kamarsa, sannan ga shi da iya yin tsalle-tsalle da yin alkafira a sama tamkar tsuntsu mai fukafukı. Rayan bako ya gaji da bai wa kansa horon fada da takobi sai ya zauna ya yi shiru, ya shiga tunani. Koda ya yi nisa a cikin tunaninsa sai ya fashe da kuka. Al'amarin da ya matukar bai wa su Abul Ishmira tausayi da mamaki kenan. Farila ta dubi Abul Ishmira ta ce, "Ya kai mijina yanzu me zai hana mu tambayi wannan bako labarin sa, tabbas wannan kuka da yake yawan yi akwai dalilinsa." Abul Ishmira ya dubi Farila cikin alamun karayar zuci ya ce, Ya za a yi mu ji bayani daga bakin wanda bai taba magana da mu ba, tsawon kwana goma sha hudu? Ina kyautata zaton wannan yaron kurma ne." Koda gama fadin haka sai Ishmira ta mike tsaye ta tafi ga bako kai tsaye, su kuwa su Farila sa suka bi ta da kallo kawai. Yayin da Ishmira ta iso daf da bako sai ta zauna gabansa suka dubi juna sannan ta ce, "Zuciyata da idanuna ba su gamsu cewa kai kurma ba ne. Ya kai wannaan bako ina son ka budi baki ka ba mu labarinka idan har baka kasance mai butulci ba bisa ceto rayuwarka da na yi daga can bakin kogi na kawo ka nan. Sa'adda Ishmira ta zo nan a zancenta, sai bako ya sa hannu ya share hawayen idanunsa, Sannan .ya budi baki ya ce, 'Sunana Umairu bin Azwaba. Na kasance da ga sarki ham na birnin Mazdur guda daya cal tilo a duniya. Yake wannan budurwa ma'abociyar kyawu ki yi sani cewa labarina yana da tsawo kuma akwai abin tausayi a cikinsa, amma duk da haka zan yi kokari na gajarce muku shi kafin na fara baku labarina ina son na fara da yi muku godiya bisa ceto rayuwata da fatan zan zamo mai amfani a gare ku, ko kuma na yi muku sakaiya wata rana." Kimanin shekaru ashirin da biyu baya sa'adda ban fi shekara biyar ba a duniya. Na taso a cikin gata, jin dadi da walwala kasancewata dan sarki guda daya tilo a wajen mahaifina, sarki Ilham. Mahaifina da mahaifiyata suna matukar sona, kuma duk abin da na furta ina so in dai akwai shi a cikin duniyar nan sai sun ba ni shi. Sarki Ilham na da karfin mulki da kuma tarin dukiya mara adadi. Babu abin da ya ke so a rayuwarsa face adalci da zaman lafiya, domin ya kasance mai tausayi da taimako ga talakawansa. Wannan halaiya ta sa ce ta sa ya sami farin jini mai yawan gaske a wajen jama'ar birnin Mazdur har ta kai cewa ko da wasa mutum ya zagi sarki ko ya aibata shi take za a yi masa rajamu. Duk inda sarki Ilham zai je ina tare da shi, kai ko kwanciyar barci. Kai ko kwanciyar barci, tare muke sai dai mahaifiyata ta dauke ni daga kan kirjinsa ta kai ni dakina ina ta barci ban sani ba. Shakuwata da mahaifina ta wuce duk yadda mutum zai tunano, domin ina farkawa da safe Sunansa nake fara ambato, Da zarar na bude ido na ga baya kusa da ni sai na ruga turakarsa na riskishi. Nan zan zauna mu ci abinci tare ya yi mini wanka, ya sauya mini tufafi, sannan shi ma ya je. ya yi wanka ya kintsa mu tafi fada tare. Wani abin al'ajabi kuma shi ne ni da mahaifina kamar an tsaga kara ne, in ba don ni yaroba ne shi kuma babba da sai a ce Hassan da Usaini ne. Gaba daya mutanen kasar mu ma'abota addinin bautar dutse ne, kuma duk shekara mu kan je bayan gari mu. taru a gaban wani katon dutse, wanda har yau ba a sami wani dutse mai girma ba kamarsa a duniya. Muna kiran wannan dutse da suna Gaubul Sabar. A bisa al'adda duk shekara idan muka je gaban wannan dutse gaba dayanmu muna yin Sujjada ne a gare shi babu wanda zai dago kai ya mike tsaye har sai sarki ya bada umarni. Shekarar da ba zan taba mantawa ba ita ce shekarar karshe wacce muka ziyarci Gaubul Sabar. Bayan mun yi sujjada a gare shi izuwa tsawon yan dakiku sai mahaifina sarki llham ya mike tsaye yä umarci jama a da su mike. Koda muka dago da kawunan mu sai na ga mahaifina na zub da hawaye, al'amarin da ya razana ni kenan, kuma ya firgita dukkanin jama'ar birnin Mazdur. Cikin matukar damuwa mahaifiyata ta matsa kusa da shi ta kama hannayensa ta ce, Yakai sarki mai adalci ka yi sani cewa hankalin jama arka ya dugunzuma saboda ganin zubar hawaye a idanuka domin sabon al'amari ne a gare mu baki daya. Tun da ka hau kan karagar mulki sama da shekaru ashirin duk shekara sai mun zo nan mun yi bauta tare da kai, amma ba mu taba ganin ka yi kuka ba, sai yau. Ina dalilin wannan kuka na ka?" Yayin da sarki llham ya ji wannan tambava sai yà sake fashewa da matsanancin kuka. al'amarin da ya kara karya zukatanmu kenan, har nima na ruga gare shi na fada kan kirjinsa ya rungume ni yana mai dada ci gaba da kukansa. Da kyar mahaifiyata ta rarrashe shi ya daina kukan. Bayan ya nutsu sai ya kama kallon jama'arsa daya bayan daya, yana kwallah. Daga can sai ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Ya ku jama'ar birnin Muzdar kun sani cewa duk shekara idan muka zo nan mai girma Gaubul Sabar yana fada mini abubuwan da za su faru gare ku a cikin shekara walau na alheri, ko na tsiya. Sannan ni kuma na sanar da ku. Haka ne ko?" Jama'a suka amsa gaba daya, "Haka ne ya sarkin mu mai adalci." Sarki Ilham ya ci gaba da cewa, "To yau ma kamar ko yaushe mai girma Gaubul Sabar ya yi mini ishara bisa abin da zai samemu Ku yi sani cewa ya gaya mini cewa a wannan shekara wata babbar masifa za ta afko mana wacce za ta zamo sanadiyyar mutuwarmu gaba daya, face mutum daya daga cikin mu wanda bai sanar da ni ko wanene ba. Za a rushe wannan kasa tamu, a kone gidajenmu, a malale birnin mu da Jininmu yadda har abada ba za a tuno da ire-iren mu ba. Mai girma Gaubul Sabar ya tabbar mini da cewa ba zai iya ceton mu ba, daga wannan masifa idan ta zo mana, amma ya ce wannan mutum guda daya wanda zai tsira a cikin mu komai daren dadewa zai dawo wannan birni namu ya kafa sabon gari kuma ya mulke shi. Wannan masifa tabbas tana nan tafe, kuma za ta zo mana ne a lokacin da ba mu sani ba, amma lallai za tazo ne. a cikin daya daga cikin lokuta uku. Ko dai ta zo a farkon shekara ko kuma a tsakiyar shekara ko a karshe." Sa'adda sarki Ilham ya zo nan a zancensa sai jama'a suka rude, wasu suka kama ihu, wasu Suka kama koke-koke, kai wasu ma tsalle da birgima suka yi ta yi, kamar sun zautu. Masu nutsuwa ne suka hau rungumar yanuwa suna hawaye da jimami cikin tsananin bakin ciki. Daga wannan rana mutane suka rasa sukuni, a cikin birnin Mazdur, har ma wasu suka fara hada nasu-inasu da nufin yin hijira. Koda sarki ya sami labarin abin da ke faruwa sai ya tara jama'ar birnin kaf ya sanar da su cewa ko da fa mutum ya yi hijira ba zai tsira ba, daga wannan masifa domin duk inda ya je bai isa ya tsira ba, sai masifar ta riske shi. Koda jin wannan batu sai hankalin jama'a ya kara dugunzuma fiye da da can, kuma aka rungumi kaddara bisa dole saboda an san cewa sarki ilham bai taba yin karya ba, kuma duk abin da ya fada yana tabbata a iya tsawon shekarun mulkinsa. Haka dai jama'a suka Ci gaba da rayuwa cikin fargaba, zullumi da tashin hankali. Tsananin fargabar tasa wasu ma suka dunga kamuwa da cuta. Abu dai kamar wasa farkon shekara ya shude lafiya lau babu abin da ya faru. Ai kuwa da shekara ta zo tsakiya sai fa jama'a suka dada firgicewa, musamman a ranar cikar watanni shi da na shekarar. A wannan rana har dare ya raba kowa na cikin gidansa a zaune duk an kulle kofofin gidaje, masu kuka na yi masu addu'ar ban kwana na yi. Lokacin da dare ya raba sosai ina kwance akan kirjin mahaifina ina ta sharar barci sai mahaifiyata ta shigo cikin turakar ta riskemu. A wannan lokaci mahaifina ko rintsawa bai yi ba, idanunsa na zubar da hawaye ya kura mini ido yana shafa gashin kaina. Ko da mahaifiyata ta data ganshi cikin wannan hali sai hankalinta ya dungunzuma ita ma ta fara kuka. Cikin karfin hali ta zo daf da shi ta zauna, suka dubi juna, sannan ta ce, Ya kai mijina ina dalılin zubar wannan hawaye a idanunka a yanzu? Ka yi sani cewa a iya rayuwata ta Zama da kài wannan ne karo na biyu na taba ganin hawayenka." Sarki Ilham ya yi ajiyar zuciya ya ce.Yake matata a bar begena dare a rana shin ba ki ji Wata irin iska mar şanyi ba, tana kadawa a çikin wannan dare" Mahaifiyata ta ce, "Kwarai kuwa ina jin Wannan iska a Yanzu haka." Shin ba ki ga mikiyoyi ba a sama suna shawagi?" Ta ce, Kwarai kuwa na gan su. Sarki lham ya ce, "Ki yi duba i zuwa waje ta cikin ta ga abin da kika gani ki zo ki da ni." Koda jin haka sai mahaifiyata ta ruga gaban ta gar dakin ta dube ta ta leka. Cikin razani ta rugo da baya ta fadi gaban mahaifina ta ce, "Na ga bishiyoyi na rangaji tamkar za su tunbuko daga cikin kasa kuma na ga koramai da fadamom Suna fantsama kamar za su Cinye birnin nan." Sarki Ilham ya fashe da kuka ya ce, "Duk wadannan abubuwa da kika gani ba komai ba ne face alamomi na zuwan masifar da za ta shafe mu. Tabbas wannan masifa za ta zo mana ne a gobe da sassafe. Ba wani abu ba ne ya sa kika ga ina kuka ba face bakin cikin zamu mutu tare da wannan da na mu Umairu wanda ya kasance karamin yaro dan shekara biyar. A rayuwata ta duniya ba ni da burin da ya fi bayan raina Umairu ya gaje ni, ga shi kuma zan mutu tare da shi, shi kenan ba za na bar baya ba. Ko na mutu babu wanda za a kalla a tuna da ni duk da cewa na yi suna na shahara a duniya. Ki dubi dukiyar nan da na mallaka haka za mu tafi mu BArta a banza." Sa'adda sarki llham ya zo nan a zancensa sai mahaifiyata ta fashe da kuka ta rukunkume shi, al'amarin da ya janyo na farka daga barci kenan a razane. Koda na' ga iyayena na suna kuka sai nima na kama kukan aka rasa wanda zai rarrashi wani a tsakaninmu. Daga can sai na daina kukan na dubi mahaifina na ce DAJIN MUTUWA littafi na daya 1 Na Abdulaziz Sani M gini Typing - Shuraihu Usman Part 1F. Ya kai Abbana ka ce akwai mutum daya da zai tsira daga wannan masifa, to wai shin wanene wannan mutum kuma ta ya ya zai tsiran?" Koda jin wannan tambaya sai mamaki ya kama mahaifina ya kura mini idanu kawai. Daga can sai ya ce, "Ya kai dana ka yi sani cewa mai girma Gaubul Sabar bai sanar da ni kowanene ba, amma ya gaya mini cewa wannan mutum zai tsira ne ta hanyar buya a cikin wani karamin dutse wanda tsawonsa da fadinsa bai wuce kamu uku ba." Na sake tambayarsa cikin yanayin mámaki na ce, Ta ya ya mutum zai iya shiga cikin dutse alhalin ba kofa gare shi ba?" Mahaifina ya ce, "Da ikon mai girma Gaubul Sabar hakan za ta faru." Da wannan faruci sarki llham ya tsuke bakinsa ya kara rukunkume mu a kirjikinsa, ni dai ban san sa'adda barci ya sake sace ni ba. tsananin rugugin rushewar gidaje, ihun mutane da girgizar kasa ne ya farkar da ni daga barci. Ina bude idanu na ji an sunkuce ni an yi jifa da ni sama, tamkar an cilla takarda, sai gani a can kololuwar sama kai ka ce daga cikin baka aka harba ni. Koda na leko samą sai na ga wadansu irin halittu masu tsananin muni da ban tsoro sun cika birninmu gaba daya. Su dai wadannan halittu babu abin da mutum zai iya siffanta su face dodanni. Idan suka kama mutum sai dai ka ga sun sa hannu sun yaga shi tamkar sun ya ga tsumma ko takarda. Nan fa jini ya rinka fantsama da malala. Ina can kokoluwar saman na hango sa'adda wani mugun dodo ya kama uwata da ubana da yanyatsu bibbiyu kawai sai ya wangame katon bakinsa ya Cusa kawunansu ciki ya gutsure ya taune. Ganin wannan al'amari ne ya sa na suma a sama. Ban san abin da ya Ci gaba da wakana ba, sai bayan na farfado kawai sai na tsinci kaina a cikin dutse a rufe ruf, kuma ga shi babu wata alamar kofa ta fita daga cikin dutsen. Wani abun mamaki kuma shi ne ta cikin dutsen ina iya hango gaba dayan cikin bimin mu tamkar a cikin gilashi nake. Babu abin da idanuna ke gani face tarin gawargakin mutanen birnin mu duka, ga jininan yana malala yana gudu a kan kasa kamar cibiyar ruwa ta balle, su kuwa dodannin nan sai kaiwa da kawowa suke suna ta dube-dube ko su ga wani sauran me rai, amma ba su ga Kowa ba. Babu abin da ya fi ba ni mamaki, face dutsen da nake ciki a tsakiyar wadannan dodanni yake dan mitsitsi, a gabansu, amma sam ba sa iya ganina. Kuma babu wanda ya shuri dutsen, ida ma suka zo Wucewa ta kansa sa dai na ga su daga kafa sun shallake shi. Koda na dubi yawar gawarwakin al'ummarmu kuma na tuno da irin kisan gillar da aka yi wa iyayena sai na fashe da kuka na kama ihu a cikin dutsen, domin a lokacin gaba daya rayuwar duniya ta fita daga sha'awa ta. Burina kawai dodannin nan suji ihuna su fito da ni daga cikin dutsen su kashe ni. Amma sai duk ihun nawa ya zamo a banza, domin babu wanda ya ji kuma babu wanda ya ganni. Bayan kamar rabin sa'a sai na ga dodanin nan sun daga wata bakar tuta wadda a jikinta akwai hoton zanen farin hankaka, kawai sai suka kama tsalle da gurnani, mai nuna alamun samun nasarar yaki. Ba zato, ba tsammani kuma sai na ga wani aljani yana saukowa daga can sama sai kada manyan fukafukansa yake. Zaune akan aljanin wani gabjejen mutum ne bisa kujerar zinare, sanye da kayan sarauta, kuma fuskarsa a rufe da hular karfe, ba a ganin komai na sa face idanunsa, hancinsa da bakinsa. A jikin kirjin rigarsa, akwai wannan hoton zanen farin hankaka. Koda aljanın ya sauka kasa, sai wannan sarki ya dubi gabas, da yamma, kudu da arewa. Bayan ya ga fululun gawarwaki sai ya bushe da mahaukaciyar dariya, cikin tsananin farin ciki. Lokaci guda ya daina dariyar ya dubi dodannin nan ya ce, "An gaishe ku manyan dakaruna, tabbas yau kun hutasshe ni yin farautar makiyana, domin kun kashe babban abokin gabata, kun rushe mulkinsa kun shafe jama'arsa, daga doron Kasa, don haka kun goge dukkan bakin cikin rayuwata." Yana gama fadin hakan ya sake bushewa da dariyar mugunta. Shi kuwa aljanin da ke dauke da shi sai ya bude fukafukansa ya tashi da shi sama ya lulaka cikin gajimare. Har suka kule a sama ban dainan jiyo sautin dariyarsa ba. Har vau, har gobe na haddace sautin muryarsa da sautin dariyarsa ba zan taba manta su ba Bayan bacewar sarkin ne wadannan dodanni ma suka yi sahu-sahu suka kama hanya suka bar cikin birnin namu. Sai da sa'a uku ta shude sannan suka gama fita daga garin, saboda tsananin yawansu haka kuma ban daina hango su ba sai bayan wata sa'a ukun. Bayan bacewarsu ne dutsen da nake ciki ya tsatstsage ya fashe na fito daga ciki. Ai kowa ina fitowa na ruga izuwa inda gangar jikin iyayena ke zube ba kawuna na fada kan su na yi ta shara kuka. Sai da na jima a haka, sannan na mike tsaye na ja gangar jikin na su izuwa cikin irin wutar da ta kone gidaje na jefa su ciki. Nan take na ji zuciyata ta kekashe na daina jin tsoron komai. Kawai sai na kama tafiya na bar cikin birnin na nausa jeji na yi ta tafiya babu abin da ke fado mini a rai face tunanin daukar fansa. Duk sa' adda na runtse idanuna sai dai na ga hoton zanen farin hankaka kuma sai na dunga jin muryar wannan azzalumin sarki a cikin dodon kunnena gami da sautin dariyarsa. Daga wannan rana na zamo tamkar dabba domin abani da gida sai daji, bani da yanuwa sai dabbobin dawa bani da abina sai yayan itatuwa da kuma naman da na iya farautowa. tun ina shekara biyar din na iya farauta a daji kuma na iya boya a duk sa'adda naga abin tsoro ya zamana ina kwana akan bishiyoyi kamar dan biri. Sai dana shekara goma acikin irin wannan rayuwa sannan wata rana na hadu da wani mafarauci mutum mai kirki wanda ya tafi dani izuwa gidansa inda matarsa ta rukeni tamkar dan cikinta a cikin wani daji daketa yamma da wani. Babban birni da ake kira madarul Aswar. Sai da na shekara uku a gidan wannan mafarauci ba taba shiga cikin birnin madarul Aswar dani ba. Haka kuma bai tab6a tambayata labarina ba kuma nima ban taba tambayarsa nashi labarin ba da kuma dalilin zamansa a cikin wannan daji. A zaman da mukayi ya koya min farauta ainun kuma ya bani sirrikan tsafi da yawa domin na kare kaina bisa mugun abu. Katsam sai wannan mafarauci ya kwanta cutar ajali al'amarin daya dugunzuma hankalina dana matarsa kenan muka rasa abinda ke mana dadi a duniya. Magani kuwa babu irin wanda bamu yi nema ba mün bashi amma duk a banza. Daga sannan kullum muke fita farauta na nemo abinda za'a ci a gidan mafarauci har tsawon kwana arba'in Hakika a wannan lokaci na tsinci kaina a cikin hadari da mütukar damuwa saboda sabon da nayi da maigidana kasancewar yana debe min kewa kuma na daukeshi tamkar mahaifina. Wata rana na dawo daga farauta cikin tsananin farin ciki sakamakon samun nasarar kamo Barewa da gada sai na iske matar mafarauci zaune a gaban maigidanta wanda ke kwance tana ta sharar kuka, shima kuma hawaye na zuba a idanunsa. Al'amarin daya tayar da hankali na kenan na yarda abin farautar tawa na ruga garesu da zuwa sai na durkusa a gaban maigidan nawa na kama kuna sannan na kama hannayensa na ruke nace yakai Abbana ina dalilin zubar hawaye a idanunka? Shin ka fidda rai da sanmun lafiya ne? A rayuwarka? Ni Kama nayi imani cewa in dai da rai'akwai rabo. Bisa mamakI sai na ga fuskar mafarauci ta fadada da murmushi daga bisani kuma sai ya fashe da kuka ya ce, "Ya kai dana ka yi sanin cewatabbas wannan cuta tawa ba ta tashi ba ce, ita ce ajalina. Ba komai ne ya sa ka ga muna wannan kuka ba ni da matata face za mu rabu a lokacin da ba mu samu damar cika burın rayuwar mu ba. Wannan buri kuwa shi ne na samun da wato magaji wanda muke sa ran nan gaba shi ne zai zamo sarki a wancan babban bimi na Madarul Asuwad. Ko da mafarauci ya zo nan a zancensa, sai na kara cika da mamaki na ce, "Ya kai Abbana ya za a yi dan ka ya zamo sarki alhalin bai gaji sarauta ba?" Mafarauci ya yi tari har sau uku, sannan ya ce, "Ya kai dana Umairu ka yi sani cewa sarkin da ke mulki a wannan birni na Madarul Aswad a yanzu kanina ne uwa daya uba daya. Sunansa Zalulu bin Asmar, ni kuma sunana Hulairu bin Asmar. Tsakanina da shi bambancin shekaru biyu ne kacal. Tun da muka taso muna yara halayenmu suka bambanta, domin ni na kasance mai hakuri, tausayi da jin kai. Shi kuma sai ya zamo mai taurin ka, azzalumi da bakar zaciya. Bisa wannan dalilina mahaifinmu sarki Asmar ya kaunace ni fiye da Zalulu, kuma tun muna yaran sarki Asmar ya tabbatar mini da cewa nine zan gaje shi Koda dan uwana Zalulu ya fuskanci cewa lallai in dai mahaifinmu na raye ba zai taba yin sarautar birnin Madarul Aswad ba, sai hankalinsa ya dungunzuma ya shiga tunanin hanyar da zai bi ya yi maganin wannan matsala. Ita ma mahaifiyarmu wacce ake kira Hasmira ko kadan ba ta kaunar Zalulu saboda mugayen halayensa da taurin kansa na kin jin magana. Akwai wata rana da ta rufe shi da fada akan wani laifi da ya yi na zaluntar wani bawa kawai sai ran Zalulu ya baci ya zagi mahaifiyarmu. Nan take kuwa ta daga hannu ta shara masa mari, ta sake daga hannun da nufin ta kara masa marin sai ya yi wuf ya kauce ya ce, "Akul kika kuskura kika kara marina. uwata ki yi sani cewa na rantse da darajar karagar gidan nan daga yau da ke da ubana kun daina zama matsala a gareni. Na san bakwa kaunata kun fi son danuwana Hilairu kuma shi kuke so ku bai wa mulkin kasar nan. To 1na tabbatar muku da cewa wannan mafarki na ku ba zai taba tabbata ba. Ni kam na hakura da ku a matsayin iyaye tuni zuciyata ta aminta da cewa ni maraya ne. Wannan gani da kika yi mini a karshe a yanzu shi ne zai zamo gani na karshe a rayuwarki. Tabbas in kuwa kika sake ganina a rannan za ki mutu." Zalulu na gama fadin haka ya juya ya fita daga gidan sarautar. Daga wannan rana ba mu sake jin duriyar Zalulu ba, har tsawon shekara uku, kai ko wanda ma ya ji labarinsa ba mu samu ba. Rana daya aka wayi gari sarki ya kamu da matsananciyar rashin lafiya.Nan da nan likitocin sarki suka taru a kansa suka yi ta aikin su suna bincike. Yayin da bincike ya yi tsamari sai aka gano cewa guba guba aka bawa sarki a cikin shayi ya sha kuma ba wani ba ne ya yi wannan barna ba, face mai dafa masa abinci wani mutum wanda ake kira Mahakuf. Asalin Mahakuf bawa ne wanda ya yi zamani da kakanmu, kuma ya zauna da shi bisa gaskiya da amana, don haka nema mahaifinmu sarki ASmar ya yarda da shi dari bisa dari ya amince da shi a,matsayin mai data masa abinci. Koda aka gano cewa Mahakuf ne ya zubawa sarki guba a shayi, sai fadawa suka ce a tafi da shi filin fada a sare masa kai. Duk da cewa sarki Asmar na cikin matsanancin hali sai ya budi baki ya ce, kada aje a kashe Mahakuf a zo da shi yanzu gabansa tukunna. Nan take aka zo da Mahakuf a daure wani irin cikin sarka aka gurfanar da shi. Cikin matukar kunya Mahakuf ya sunkui da kansa kas ya kasa hada idanu da sarki. Shi kuwa sarki Asmar sai ya dago kai da kyar ya budi baki cikin dauriya yana mai duban Mahakuf ya ce, Ya kai amintaccen bawana kai kuwa wane laifi na yi maka wanda ya cancanci wannan horo mai tsanani a gareni har ka nemi rayuwata? Ni dai na san cewa a iya zamana da kai ban taba ha'intar ka ba, kuma ban taba cutar da kai ba. A sanina a duk duniyăr nan, kai ne mutum na daya wanda nafi aminta da shi, asalima da kai nake shawara bisa dukkan al'amurana. Babu wanda ya tamkarka. Na baka amanata, ka ba ni taka. Me ya sa yanzu ka Ci amanata alhalin kai yardajjene, kaSan sirrina har a wajen mahaifinmu?" Sa'adda sarki Asmar ya zo nan a zancensa, sai bawa Mahakuf ya fashe da kuka ya ce, "Ya kai sarki mai adalci ka yi sani cewa wannan barna dana aikata ba a son raina ba ne an yi mini dole ne. Kuma ba wani ba ne ya tursasani ba na aikata hakan face danka Zalulu. Ka yi sani cewa tsawon shekaru uku da bacewar Zalulu tun a sannan ya sace dana Imal yaro dan shekara bakwai, wanda shi kadai gareni a duniya. Zalulu ya yi garkuwa ne da dana Imal a matsayin idan ban zuba maka wannan guba ba, Zai kashe shi. Tsawon shekaru ukun nan kullum da daddare sai Zalulu ya turo an sace ni cikin dare an kaini can wani daji in da ya kafa sansani na mayakansa yan tawaye kimanin su dubu dari biyu da doriya. Anan ne ya boye dana Imal. Kullum idan aka kai ni sai ya sa an yi mini bulala ashirin, sannan kuma ya fito da dana ya nuna nmini shi ya ce in dai ban aikata abin da yake s0 ba, a bakacin ransa. Kullum idan aka dawo da ni gida sai na yi ta kuka, saboda na san cewa ba zan iya cin amanarka ba." Ko da Mahakuf ya zo nan a zancensa sai ya tube rigarsa, nan take aka ga tabon bulalu a bayansa rudu-rudu. Gaba daya fadawan da ke wajen sai da tausayi ya kama su saboda ganin yadda aka yi kaca-kaca da bayans tsoho Mahakuf mutumin da ya fi shekaru casa'in a duniya. Mahakuf ya share hawayensa ya ci gaba da bayani ya ce, "Ya kai sarki mai adalci ka yi sani cewa Zalulu bai ba ni gubar da zan zuba maka a shayi ba, sai da shekaru ukun nan suka cika, wato kwanaki uku da suka gabata, A ranar ne ya ce da ni lallai a gobe da safe yake son na zuba maka wannan guba idan kuwa na ki lallai zan tsinci gawar dana Imal a kofar gidana da yammacıi. Kuma a lokacin ne ya tabbatar mini da cewa lallai idan har ka sha wannan guba ba za ka wuce kwana uku ba, a duniya. Wannan shi ne dalilin da ya

Chapter 5 of 6