Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
hagu an bar hanya a tsakiya wacce Shafaru zai bi don kowa ya ganshi. Lokacin da labari ya riski sarki cewa mutanen garin da sun rude da kaunar Shafaru kowa na son a fito dashi a ganshi sai hankalin Hamaru ya dugunzuma ya fara tunanin kada fa mutane su kawo matsala bisa wannan wasika da ake son lallai Shafaru ya danganata ga boka Shamakalu. Lokacin da fadawan sarki suka fuskanci haka sai wazirinsa wanda ake kira Hannamu ya dube shi ya ce"Haba ranka ya da de yaya kai da ka ke da dakaru har zaka yi shakkar wani abu, abin da za;ayi kawai a fito da dakaru su jeru a layi a gaban jama'a tun daga bakin kurkukun har izuwa kofar gidan boka Shamakalu duk wanda ya kawo rudani a kaddamar da shi kawai." Ko da jin wannan batu sai murna ta kama sarki Hamaru ya ce "Kwarai kuwa ka zo mini da mafita." Nan da nan cikin kankanin lokaci aka baiwa dakaru umarni suka fito cikin shiri suka jeru a layi kamar yadda aka tsara. Al'amarin da ya tsorata mutanen gari kenan kowa ya shiga taitayinsa. Bayan an gama wannan shiri sai aka tura aje a fito da Shafaru da ga cikin kurkuku. Sarki ya bada umarnin a daurawa Shafaru sarkoki a wuya da hannu da kafafu don tabbatar da tsaro ka da ya sami damar guduwa har sai ya kai wannan wasika zuwa ga boka Shamakalu. Ai kuwa haka al'amarin ya kasance sai gashi an fito da Shafaru a daddaure cikin sarka ana jansa da karti har yana faduwa, sannan a tasheshi ana dukansa da bulala su kuwa mutanen gari sai yi masa jinjina suke, wasu na Zub da hawaye don kaunarsa da tausayinsa. wannan lokaci tsufa ya riski Shafaru da kyar ma yake tafiya kuma fuskarsa ta cika da gashi da gemu tai buzu-buzu. Kafin a fito da Shafaru tuni tsegumi ya isa cikin kurkukun cewa so ake a hallakashi ta hanyar bashi wasikar raddi wadda zai kaiwa boka Shamakalu kuma shi ma Shafaru ya ji wannan batu amma ko kadan bai damu ba domin dama rayuwar duniyar ta isheshi saboda bakin cikin halin da ya tsinci kansa a ciki na wulakantashi da akayi a matsayinsa na dan sarauta aka kulleshi a kurkuku har tsawon shekaru ashirin da daya kuma aka raba shi da iyalansa wadanda ya kasance kullum a cikin begensu dare da rana kuma bai san a halin da suke ciki ba a yanzu walau suna raye ko sun mutu. A kullum ma dai Zuciyarsa tafi aiyana masa cewa ba sa raye wata kila tuni sarki Hamaru yasa an hallakasu. Sa'adda aka fito da Shafaru daga kurkuku da kyar ya iya bude idanunsa saboda rabonsa da ya ga hasken rana yau shekara ashirin da daya kenan, sannu a hankali ya samu ya bude idanun sarai. nan take aka kawo wasikar raddi aka danka masa a hannu, sannan aka tusa keyarsa aka fara tafiya da shi yana faduwa ana dukansa da bulala yana mikewa da kyar. Tun daga nesa tsohuwa Shabiratu da su Humaila suka juyo hayaniyar jama'a na karuwa alamar cewa an kusa isowa kofar gidan Shabiratu da Shafaru. ko da jin hakan sai Shabiratu ta mike da sauri ta kimtsa ta dauki wannan sarka da Amshira ta bata ta nufi kofar fita daga cikin gidan kawai sai ta ji Amshira ta kira sunanta, cikin mamaki ta waigo ta ga ashe da Amshira da Humaila duk kuka suke yi. Ko da ganin haka sai hankalin Shabiratu ya tashi ta ce. "Ina dalilin wannan kuka naku alhalin ina gabda cika muki burinku Amshira ta goge hawayen idanunta ta ce "Ya ke wannan tsohuwa mai jin kai kiyi sani cewa ba wani abu bane ya samu kuka face tunanin abu biyu. Abu na farko shine idan muka rabu da ke yanzu bami san irin halin da zaki shiga ba domin aikin da muka baki na tattare da hadarin gaske. Tabbas mun shaku dake ainun har muna Ji a ranmu kamar ke jinin muce. Hakika rashinki a tare da mu zai iya haifar da mummunan bakin ciki a gare mu. Abu na biyu shine muna mutuwar son mu sake ganin fuskar Shafaru a karo na karshe, tunda mun sancewa wannan wannan ce kadai damar da muke da ita tà ganinsa a rayuwarmu. Sa'adda Amshira ta zo nan a zancenta sai tausayinta ya turmuke tsohuwa Shabiratu nan take ta ji kaunar su Humaila ta karu nin kin ba nin kin a cikin zuciyarta bata san sa'adda hawaye ya zubo mata ba. Cikin matukar tausayawa ta dubi Amshira ta ce Abin da za'ayi ku rufe fuskokinku da mayafi ku bar idanunku kadai a waje sai mu fita tare ku tsaya a cikin jama'a domin kuma ku ga Shafaru amma fa kada ku kuskura wani ya shaidaku domin tabbas nasan cewa har yanzu attajiri Abaiwu ibin Affan har yanzu ba zai fasa farautar ku ba. Na san halinsa mutum ne mai riko da neman daukar fansa. tabbas wannan ido guda da ya rasa sai ya nemi ramuwa a kansa." Amshira ta ce Lallai zamu kiyaye Nan da nan Amshira da Humaila suka mike da sauri suka dauki bakaken mayafai suka rufe jikinsu gaba daya har da 'fuskokinsu, in banda idanunsu babu abin da ake gani sannan sai tsohuwa Shabiratu tayi musu jagora suka fita kofar gida suka tsaya a cikin cinkoson jama'a yayin da hayaniya ta yawaita ana ta kallon hanya don ganin karasowar Shafaru. Duk inda mutum ya duba dakaru ne a tsaitsaye suna ta tura mutane baya da karfin tsiya, wani lokacin ma har dukan mutane ake amma saboda nacin mutanen kowa yaki gusawa saboda burin shiga gaba don ganin fuskar yarima Shafaru. Yayin da su tsohuwa Shabiratu suka ga wuri ya cika makil da jama'ą ana ta turmutsutsu babu halin su ratsa su shiga kan gaba inda zasu iya tsayawa su ga Shafaru sai hankalinsu ya dugunzuma suka rasa abin dake musu dadi. nan fa suka tsaya suna tunanin mafita domin basu da karfin da zasu iya kutsawa su shiga gaba. Suna cikin wannan tunanin ne dabara ta fadowa Shabiratu. Nan take ta kira wani babban badakare ta jashi gefe daya ta kawo dinare mai Yawa ta bashi ta ce bukatarta kawai yasa a buda musu hanya su Uku su sami damar tsayawa akan gaba inda za su yi arba da Shafaru. Yayin da badakare ya ga Wannan dukiya sai ya rude ya cika da murna, nan take ya karbe dinare ya Boye jikinsa ya ce. An gama wannan aiki ku biyoni a baya. Ko da suka iso cikin jama'a sai badakare ya daga bulala ya sa duka bisa dole aka dare aka bashi hanya ya wuce da su Shabiratu har ya kaisu kan gaba suka sami wuri suka tsaya. Faruwar hakan ke da wuya sai ga Shafaru an taho da shi duk jíkinsa a daure da sarkoki ana jansa yana tafiyar tatata saboda gajiya da tsufa. Yayin da Humaila da Amshira suka hango shi sai suka kura masa idanu suna masu zub da hawaye. Amshira ta ce da Humaila "Yake 'yata tabbas wannan shine mahaifinki wanda aka rabaki da shi tun kina da shekara uku a duniya. Ni kam banyi tsammanin cewa zan sake ganinsa ba a rayuwa ta, lallai masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce mai rai baya fitar da rai ga samun rabo. Duk wannan bayani da Amshira ke yi ashe wani munafukin bawan attajiri Abairu ibini Affan waishi Kumaz na tsaye daf da su yana sauraro. Ko da ya ji haka sai ya sulale ya ruga can inda Abairu yake ya sanar da shi cewa ga Amshira can da'yarta Humaila ya gansu a tsaye suna son ganin Shafaru. Ko da jin wannan batu sai murna ta kama Abairu. Cikin hanzari ya tura aka kirawo masa wasu hadimansa mutum biyar ya ce suje tare da Kumaz ya nuna su Humaila. Duk yadda za'ayi su yi ta bibiyarsu har dare yayi sannan su kamosu a sirrance su kaisu can gidan shakatawarsa na bayan gari. Nan take Kumaz ya jagoranci wadannan hadimai su biyar suka tafi Izuwa can kofar gidan tsohuwa Shabiratu inda ya baro su Amshira. Kash wani akasi da aka samu shine lokacin da su Kumaz suka iso kofar gidan Shabiratu sai suka iske cewa tuni a lokacin an iso da yarima Shafaru dai dai wajen don haka wajen ya dada hargitsewa har ma an cakuda maza da mata. Haka kuma mata masu bakaken mayafai suna da yawa a wajen kuma duk sun rufe fuskokinsu don haka sai Kumaz ya kasa gane su Humaila daga cikin wadannan mata. Yayin da Humaila taga an zo za'a gifta da Shafaru ta gabanta sai kawa ta kai hannu ta dafa kafadarsa. Ko da Shafaru ya ji mace ta dafa shi sai ya juyo ya dubeta. Nan take kuwa suka kurawa juna ido, ya tsaya cak a wajen yana kallonta cikin tsananin mamaki domin ya ga cewa idanunta iri daya ne dana matarsa Amshira. bugu da kari sai ya ga hawaye na zuba a idanunta al'amarin da ya jefashi cikin wasu- wasi kenan ya ce a ransa anya kuwa wannan ba yata bace Humaila? Har ya bude baki zai yi magana da ita sai dakaru suka ingizashi gaba, nan fa yayi ta waigenta ita kuwa tayi ta daga masa hannu tana mai ci gaba da zub da hawaye. Shafaru yayi ta daddagewa yana son ya dawo da baya amma sai dakaru suka rufeshi da duka suka yi gaba da shi da karfin tsiya. A wannan lokaci Amshira na can gefe guda mutane sun bamban keta bata sami damar ganin fuskar Shafaru ba. Ko da ta fahimci cewa anyi gaba da shi sai ta fashe da kukan bakin ciki. Ana cikin wannan haline tsohuwa Shabiratu tayi fitar burgu cikin shammace ta ruga kan Shafaru. Ai kuwa tana zuwa gabansa sai dakaru suka rufeta da duka har sai da suka kaita kas. Nan da nana ta kama aman jini, cikin tsananin karfin hali da kama zafin nama ta danko hannun Shafaru ta danka masa sarkar nan ta matarsa ya karba ba tare da kowa ya lura ba. A lokacinne aka dauke Shabiratu ranga-ranga aka fitar da ita daga cikin jama'a aka je aka wullar da ita can waje daya tana numfashi da kyar alamar cewa abu ne mawuyaci ta rayu. Lokacin da jama'a suka ga dakaru sun yiwa tsohuwa Shabiratu laga-laga sai wuri ya sake hautsinewa, jama'a suka firgice aka kama guje-guje da iface-iface Da yake Humaila taga sa'adda aka je aka wullar da tsohuwa Shabiratu sai ta ruga inda take ta ciccibe ta goyata a baya ta shige da ita cikin gida. Shigarsu ke da wuya sai ga Amshira ta biyo bayansu ta rufe kofar gidan. Cikin dimauta da kuka suka je suka kwantar da tsohuwar Shabiratu akan Shimfidarta suka fara yunkurin yi mata magani don tsai da jinin dake zuba a hancinta da bakinta. A wannan lokacin idanun tsohuwa Shabiratu suna budewa da rufewa da kyar. Amshira ta dubi Humaila ta ce "MAza ki je ki dafa ruwan dumi ki kawo mini gami da kyalle maikyau. Humaila ta yunkura da nufin tafiya cika wannan umarni sai tsohuwa Shabiratu ta riko hannunta ta budi baki da kyar ta ce "Ka da ku wahalar da kanku domin bakin alkalami ya riga ya bushe, tabbas ba zan tashi ba mutuwa zanyi. Ni kam yanzu zan mutu da farin ciki idar da sakonku ga yarima Shafaru domin tabbas na bashi wannan sarka ya tafi da ita a hannunsa. Ko da Shabiratu ta zo nan a zancenta sai tayi tari ta tofar da jini al'amarin da yakara dugunzuma hankalin su Amshira Su ka kara fashewa da kuka. Amshira ta rungume Shabiratu a kirjinta tana mai cewa "Ya ke abar kaunarmu saboda me zaki tafi ki barmu. Yanzu In babu ke ya zamu yi da kadaici?" Sa'adda tsohuwa Shabiratu ta ji wannan tambaya såi tayi murmushi karfin hali ta ce "Ya ku masoyana ina yi muku albishir da cewa jiya da daddare nayi mafarki. A cikin mafarkin an nuna mini cewa zaku shiga cikin sabuwar rayuwa ta jin dadi da kwanciyar hankali a nan gaba. Humaila zata zamo matar sarki mijinki Shafaru zai fito daga kurkuku kuma zai zamo, daya daga cikin manyam birnin Farisa. Tabbas nayi imani da wannan mafarki don haka ina neman alfarma guda biyu rak a wajenku bayan mutuwata. Alfarma ta farko itace ina son idan na mutu ku haka mini kabari na a cikin gidan nan ku binne ni sannan idan kuka sami matsayi ku mayar da gidanan nawa makabarta kuma kada a binne kowa a cikinsa face wanda ya kasance maraya ko mara dangi kamata. A yiwa makabartar lakabi da makabartar Shabiratu. Alfarma ta biyu itace ina son ku rinka ziyarar kabari na ko da sau daya ne a shekara don tunawa dani. Da wannan kalami nake muku ban kwana ina mai yi muku fatan mafarkina ya tabbata gaskiya. Ko da Shabiratu ta zo nan a zancenta sai numfashinta ya sake sarkewa. Nan take jikinta gaba daya ya sandare, idanunta ya kafe ta zama gawa. Ko da ganin haka sai Amshira da Humaila suka kankame gawar suka fashe da matsanancin kuka. Ba su gushe ba suna wannan kuka har sai da rana ta fadi sannan suka tashi suka haka kabari a cikin gidan suka binne tsohuwa Shabiratu sanan suka zauna suka ci gaba da kuka suna begenta. A wannan rana dai yadda suka ga rana haka suka ga dare kuma ko ruwa ba su sa a bakin su ba. Wannan shine abin da ya faru a gidan tsohuwa Shabiratu bayan an wuce da yarima Shafaru izuwa gidan boka Shamakalu. Al'amarin Hadiman attajiri Abairu kuwa tunda wuri ya hargitse Kumaz ya kasa gano su Amshira sai suka yi ta kai kawo da duru-duru a wajen har izuwa lokacin da kowa ya watse aka barsu su kadai a tsaye. Nan fa hankalinsu ya -dugunZuma suka rasa abin yi, bisa dole suka koma wajen attajiri Abiru suka sanar da shi halin da ake ciki. Yayin da Abiru ya ji wannan batu sai ya harzuka zuciyarsa ta kama tafarfasa ya mike tsaye ya kama zagayale yana mai tunanin abin da ya kamata yayi. Daga can sai ya tsaya cak ya dubi hadiman nasa sannan ya janye kyallen da ya rufe idonsa guda wanda ya tsiyaye ya ce. "Na rantse da darajar wannan 1do nawa wanda na rasa duk ta dalilin Amshira da 'yarta Humaila duk inda suka shiga suka buya a cikin garin nan Sal na zakulosu na dauki fansa akansu. Tabbas Sal nayi lalata da Humaila sannan na kwakule mata idanunta biyu da wuka tanaji tana gani. Ita kuwa Amshira kisangilla zan yi mata na tsira mata mashi daga kasanta sai ya bullo ta ta bakinta." Ko da gama wannan jawabi sai ya ya dakawa su Kumaz tsawa ya ce Ku tafi ku ci gaba da bincike duk wanda ya gano inda wadannan makiya nawa suke zan bashi ladan rakuma dubu da dinare dubu dari." Ko da jin wannan batu sai su Kumaz suka rude suka bazama izuwa cikingari. Lokacin da aka ci gaba da tafiya da yarima Shafaru izuwa gidan boka Shamakalu sai aka ci gaba da dukansa da bulalai ana tusa keyarsa. In ya fadi sai a tasheshi da sauri yaci gaba da tundashi, jama'a kuwa suka biyo ba'yan dakarun da ke tafe dashi du, ba a dadi tamkar mutanen garin ne kaf za suyi hijira. A haka dai aka iso har kofar gidan boka Shamakalu, wannan shine tsohon ginin nan inda sihirtacciyar rijiya take. Da zuwa kofar gidan sai aka iske boka Shamakalu a tsaye ya ruke kugu da hannayensa biyu fuskarsa a murtuke abar ban tsoro. Tsaye daf dashi sihirtacciyar damisar nan ce tana gurnani. Ko da jama'a suka yi arba da boka Shamakalu da kuma wannan damisa sai suka firgita aka ja da baya ana rakabewa saboda kwarjinin Boka Shamakalu da kuma mummunar siffar wannan damisa, sukan su dakarun da suka zo da Shafaru basu san sa'adda suka saki Shafaru ba suka ja da baya suka yi cirko-cieko jikin su ya kama tsuma. e Yayin da yarima Shafaru ya tsinci kansa a gaban boka Shamakalu sai ya nufeshi gadan- gadan ba tare da tsoron komai ba ya mika masa wannan wasika ta raddi ya ce. masa "Ya kai wannan bakon ga takarda daga sarkina ya umarceni da na kawo maka, ina mai rokonka da ka sauke dukkanin fishinka akai na bayan ka karanta wannan wasika amma kada ka taba lafiyar sarki Humaru domin ya kasance da ga dan'uwana marigayi sarki salkuf." ai Lokacin da boka Shamakalu ya ji wannan batu na Shafaru sai ya cika da tsananin mamaki ya dubi Shafaru ya ce "Saboda me baka son na hukanta sarki Hamaru alhalin ya kasance babban makiyinka a duniya, ka tuna fa cewa shine ya raba ka da iyalinka ya daureka a kurkuku har tsawon shekaru ashirin da daya, kai ne ka cancanta da zama sarkin Farisa amma sai ya karbe mulkin da karfin tsiya, shine ya jefa iyalinka cikin mugun hali suke kwana a kwaroro tsawon wannan shekaru kuma suka yi ta fama da yunwa da kishirwa. Har a yanzu suna nan a cikin rayuwar kunci da fargaba har ma ana farautar rayukansu. Ya kai Shafaru kasani cewa ni boka Shamakalu na san komai na dangane da rayuwaka bisa abin da ya faru a baya dama wanda zai faru nan gaba. Wannan wasika daka bani ba komai bane a cikinta face sakon sarki na cewar na hada komatsena na bar masa garinsa saboda gadarar da na nuna masa. Ka sani cewa idan ina son na maishe da kai sarkin farisa yanzu take zan iya. ldan kana son na kamo sarki Hamaru na hallakashi a gabanka zan iya. Haka kuma zan iya sadaka da iyalanka yanzu yanzu amma sai ka amsa mini tambayar da na yi maka dazu cewar me yasa baka son na taba sarki Hamaru? Yayin da boka Shamakalu ya zo nana a zancensa sai idanun Shafaru suka ciko da Kwallah ya sunkui da kansa kasa sannan ya bude tafin hannunsa ya kurawa sarkar Amshira idanu yana mai zub da hawaye. Daga can sai ya daga sarkar sama yana mai yiwa boka Shamakalu nuni da ita sannan ya ce Ya kai wannan boka mai daraja kayi sani cewa asalin wannan sarka ta mahaifin sarki Hamaru ce wato dan'uwana marigayi sarki Salkuf. Hakika Hamaru ya ci darajar wannan sarka shi yasa har abada ba zan so ya shiga masifa ba. Abin da zan gaya maka yanzu labarine mai tsawo amma zanyi kokari na gajerce shi domin sai ka saurari labarin sannan zaka gane dalilin da yasa nake kaunar sarki Hamaru duk da cewa shi baya kaunata ko kadan a zuciyarsa. Asalima bashi da abokin gaba sama da ni. Yayin da boka Shamakalu da sauran Jama'ar gari sukaji wannan batu saijikin kowa yayi sanyi aka yi tsit ana sauraron labarin da Shafaru zai bayar. Shafaru yai gyaran murya ya fara bayani kamar haka: Kimanin shekaru arba'in baya sa'adda mahaifinmu sarki Sharudul Amman ke mulkin birnin Kisra ya kasance yana da matan aure guda biyu kacal a duniya. Matarsa ta farko ana kiranta da suna Husaira kuma sai da suka shekara goma sha hudu da yin aure sannanya auro uwata wadda ake kira da suna Shabila kafin uwata ta zo Husaira ta haifi yaya Shida kuma dun son kasance maza, a shekarar da uwata ta zo sai suka sami ciki a tare ita da Husaira kuma suka haifi 'ya'ya maza a rana guda. Da ranar suna ta zagayo sai aka sawa dan Husaira suna Salkuf ita kuwa mahaifiyata sai aka sawa danta suna Sahfaru, wato dai a wannan lokaci Husaira na da 'ya'ya bakwai ita kuwa mahaifiyata tana da da daya kacal wato Sahfaru. A kwaná a tashi sai muka taso kai daya ni da Salkuf muka cika shekara goma sha biyar. A wannan lokaci ni da Salkuf mun shaku ainun ko yaushe muna tare dare da rana bama rabuwa. Kai sai da takai cewa Salkuf ta tattaro kayansa gaba daya daga dakin mahaifiyarsa ya dawo gaba dakin mahaifiyata domin ba zai iya yin barci ba idan bana kusa dashi. Wannan Zumunci da shakuwa da ke tsakanina da Salkuf sai suka zamo abin bakin ciki a wajen Husaira da sauran ya'yanta domin babu yadda ba su yi ba akan su rabamu amma abu ya faskara. Yan'uwan Salkur sun sha yi masa duka da zaba mai tsanani akan ya daina hulda da ni amma sai ya kasance da su in dai kuna sonku rabani da Sahfaru sai dai ku kashe ni. Bisa dole suka hakura suka kyalemu muka ci gaba da zumuncinmu. Yayin da tsufa ya sake riskar mahaifinmu SOsai sai kishin dake tsakanin uwata da uwarsu Salkuf ya yawaita har ya zamana cewa Husaira ta tsanemu kamar yadda ta tsani mutuwarta don haka sai ta fara tunanin hanyar da za tab1 ta shafemu a doron kasa. Duk sa'adda Husaira ta shirya wani makirci a boyc don ta hallakamu sai Salkuf ya zo a sirrance ya sanar da mu abin da ta shirya don haka shirinta sai ya wagatse. Al'amarin da ya kan jetata Cikin matsanancin mamaki kenan abin da ta kasa ganewa shine Salkuf yana labewa ya saurari duk abinda suke kullawa ita da 'ya'yanta ba tare da sun sani ba. Mahaifinmu sarki Sharudul Amman ya kasance a cikin dumbin farin ciki bisa ganin yadda muka hada kai muka so juna ni da Salkuf don haka ne ma ya kauna ce mu soSai fiye da sauran ya'yan Husaira ya zamana cewa ya jamu a jikinsa fiye da su domin ko yaushe mua gabansa. Ana cikin wannan hali ne cutar ajali ta kama sarki Sharudul Amman, yayin da yya fahimci cewa tabbas wannan cuta tasa ba ta tashi ba ce sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abin dake masa dadi a duniya domin ya tabbatar da cewa duk ranar da ya mutu ni da Salkuf da mahaifiyata sai mun dandana kudarmu. Bisa wannan dalili ne ya shiga tunanin hanyar da zaibi ya kubutar da rayuwarmu daga cikin wannan fargaba. Wata safiya ni, Salkuf da mahaifiyata muna zaune a cikin turakar sarki yayin da yake kwance cikin jinya muna kuka saboda a ranar Ciwonsa ya tsananta sai ga sarkin gida ya shigo, da zuwa sai ya fadi ya ce da sarki ga wani bakon boka ya zo kuma ya ceyana da muhimmiyar magana da kai. Ko da jin wannan batu sai ranmu ya baci domin mun gaji da zuwanbokaye barkatai saboda babu wanda ya 1ya share mana hawaye. Cikin fishi mahaifiyata ta dubi sarkin gida ta ce "Ka je ka sallameshi kawai domin bashi da. ... DAJIN MUTUWA littafi na daya 1 Na Abdulaziz Sani M gini Typing - Shuraihu Usman Part 1C. Wani amfani ga sarki runda kafin ya zo duou Sun zo." koda da jin wannan batu sai sarki ya budi baki da kyar ya ce "A'a ba za ayi haka ba. A KOwane mutum da irin baiwarsa, a kyale wannan bakon boka ya shigo mu ji abin dake tafe da shi." Nan take sarkin gida ya mike tsaye ya fita waje a lokacin ne kuma Huraisa da 'ya'yanta su shida suyka shigo cikin turakar suna muzurai da hararar mu. Da zuwa sai suka sami wuri suka zauna suka kama kukan munafunci su duka har Huraisa na cewa ai basu san cewa jikin sarkii yayi tsamari haka ba. Dama can basu damu da rashin lafiyar sarki ba burinsu kawai ya mutu babban dansa wanda ake kira Mukairu ya hau karaga. Jim kadan da fitar sarkin gidan sai gashi ya dawo tare da bakon boka wani mtumi mai tsananin kwarjini wanda ya kasance dogo mai matsakaicin kaurin jiki. Duk jikinsa gashi ne kuma babu komai a jikinsa face walkin fata dami da guraye da kambunan tsafi, ko takalmi babu a kafarsa. Yana da kananan idanu gami da faffadar hanci da kuma karamin baki, fuskarsa na cike take da gemu da kasumba shekarunsa sun haura na sarki Sharudul Amman, amma abin mamaki shi ne yana yana jin karfin jikinsa tamkar na saurayi matashi. Da shigowar bakon bokan sai ya risina ga sarki Sharudul Amman ya ce, "Gaishe ka ya kai sarkin adalci, kai ne sarkin da babu kamarsaa fagen talakawansa. Ka yi sani cewa na dade da yin hakuri, tausayi da taimako ga nazari a kanka bisa wannan dalili ne na Zo maka da wata muhimmiyar gudunmawa." Sa'adda sarki Sharudul Amman ya ji wannan batu sai ya dubi boka a nutse ya ce, "Kai kuma waye, daga inan ka fito?" Koda jin wannan tambaya sai bokan ya yi murmushi ya ce, "Sunana Sahibul Furrati kuma na fito ne daga Dajin Mutuwa." Yayin da muka ji haka sai kowa ya cika da mamaki. Sarki ya sake duban boka Sahibul Furrati ya ce, "Shi ne Dajin Mutuwa? Sahibul Furrati ya ce, "Shi ne dajin da ba wani mahaluki da ya taba rayuwa a cikinsa face ni kadai. Shi ne dajin da ba a shigarsa a fito lafiya, kuma shi ne dajin da ke dauke da dukkanin magungunan Cututtuka na duniya kaf face cuta daya wato mutuwa. Shi ne dajin da babu wanda ya san ainihin inda yake face ni kadai, kuma shi ne dajin da ke dauke da dukkanin masifun duniya. Yakai wannan sarki ka yi sani cewa 1dan zan yi maka bayanin abin da ke cikin wannan daji sai mu kwana arba' in ina jawabi ban kare ba. Yanzu dai ba abin da ya kawo ni kenan ba. Na zo ne na gabatar da gudunmuwata a gareka, don kyautata bayanka, amma ba zan iya baka gudunmuwar ba face na kadaita da kai ya zamana babu kowa a cikin dakinan daga kai sai ni, kuma babu mai 1ya jin abin da zamu tattauna. Koda jin haka sai sarki ya dube mu gaba daya ya ce, "Ku tashi ku fita ku ba mu wuri." Nan' take uunianirmu muka mike muka fice. Fitarnu ke da wuya sai boka Sahibul Furrati ya dubi kofofin dakin da tagogin sa da idanunsa. Take suka rufe kan su ruf. Caba dayanmu sai muka tasru a kofar turakar sarki a gefe gudu muka yi cirko-cirko Laura iiran boka Sahibul Furrati ya fito, sannan mu shiga mu ji abin da suka tattauna a bakin sarki. Sai da muka shafe sa'a uku cur a tsaye muna jira, sannan muka ga kofar dakin ta bude boka Sahibul Furrati ya fito yana mai yi mana bankwana, amma bai dubi fuskar kowa ba a cikin mu sai ta Salkuf. Kawai sai ya yi murmushi a gare shi ya dafa kafadarsa, sannan ya wuce abinsa. Cikin sauri mu duka muka ruga izuwa cikin turakar sarki. Da shigar mu sa muka iske shi a zaune cikin annushuwa tamkar bai taba yin cuta ba. Al'amarin da ya matukar ba mu mamaki kenan, muka zazzauna muna masu kura masa idanu. Sarki Sharudul Amman ya dube mu daya bayan daya cikin alamun takaici da damuwa kawai sai idanunsa suka ciko da kwallah ya fara zubar da hawaye, sannan ya ce, "Yaku ya'yana da matana ku yi sani cewa wannan bako da ya ziyarce mu yanzu ba mutum ba ne kamar mu, aljani ne. Tabbas ya ba ni labarin duk abubuwan da suka faru a rayuwata tun daga sa'adda uwata ta haife ni kawo iyanzu kuma tabba a cikin labarin na sa babu kuskure ko guda daya. Baya ga wannan ya sanar da ni cewa idan na mutu

Chapter 2 of 6