Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
mu." Mu dai ba mu tsaya jiran komai ba sai muka kwankwance su. Da kyar suka iya taka Rafafunsu muka fice gaba daya daga cikin gidan muka nausa da gudu cikin daji ba tare da sanin inda muka dosa ba. Sai da muka shafe sa'a uku muna gudu a daji, sannan muka iso bakin wata korama. Anan ne muka tsaya gaba dayannmu muna haki. Bayan kowa ya sha ruwa ya wanke jikinsa sai muka bude jakarmu ni da Salkuf muka dauko abinci mai yawa muka bai wa su Mukairu. Ko da karbar abinci sai suka dasa masa wawa tamkar a ajiye gafiya a tsakiyar karnuka. Haka dai suka yi ta cin abincin wannan nan ture wancan, tamkar sun shekara ba su ci ba. Bayan sun nutsune hankalinsu ya dawo jikinsu sai muka kwashe labarin mu muka muka raiyane musu, tun daga lokacin da suka gudu suka bar mu a tarkon yanfashi kawo izuwa sa'adda muka hadu da su. Ko da jin wannan labari na mu sai dukkaninsu suka fashe da kuka, suna masu neman gafarar mu bisa abin da suka vi mana kuma suka yi ta yi mana godiya, da muka ceci rayuwarsu a yanzu. Nan take Kumairu ya shiga ba mu na su labarin bayan rabuwar mu, inda daga karshe ya shaida mana cewa wasu maridai ne ma'abota karfin damtse da karfin sihirin tsafi suka kama su suka kai su wannan gida suka daure su kullum sai sun yi musu bulala ashirin-ashirin kafin su fita daji farauta. Al'adar wadannan maridai shi ne cin naman mutane, amma idan suka kama mutum sai su daure shi su yi ta zane shi kullum har tsawon kwana arba'in sannan su kwance shi su gasa shi su cinye. Lokacin da maridan suka kamo su Mukairu suka zo da su wannan gida sun iske cewa akwai wasu mutanen a daure kamar su wadanda kwanaki Kadan ya rage musu a cinye su. Ai kuwa da Kwanakin suka cika a gaban su Mukairu aka gashe mutanen aka cinye su. Mukairu ya ce, "A yau din nan da kuka zo kwanan mu talatinda tara, ana yi mana bulala kullum ma'ana a gobe ne za a gashe mu a cinye. In da ba ku zo yau ba kun cece mu da tabbas gobe za a gama da mu." Koda jin haka sai muka kankame su Mukairu muna masu taya su farin ciki da suka kubuta daga hannun wadannan mugayen maridai masu cin naman mutum. Bayan an gama wannan tattaunawa muka yanke shawarar mu tashi mu ci gaba da tafiya don ba mu sani ba ko maridan nan sun biyu sawun mu. Nan take kuwa aka kama hanya aka yi ta tafiya ba tare da sanin inda aka dosa ba. Mu kwana nan, mu tashi can muka wanzu muna ta tafiya a daji har muka sake shafe kwanaki ashirin da tara, amma ba mu sake saduwa ba da wani mugun abun. A ranar kwana na ashirin da taran ne muka shigo cikin wani irin daji mai ban tsoro dominya tara manyan tsaunika, dogayen bishiyoyi da manyan duwatsu. Haka dai muka yi ta ratsa wannan daji har tsawon sa'a uku ba mu ga karshen ba. Al'amarin daya dugunzuma hankalin mu kenan. Kwatsam muna cikin tafiyaa sai muKa ga wasu irin halittu suna saukowa daga sama kamar tsuntsaye bila adadin babu iyaka. Kafin mu yi wani yunkuri halittun sun yi mana kawanya babu damarguduwa ko neman matsera. Kawai sai su Kumairu suka dafa wani kambu dake jikinsu take suka bace bat, muka neme su sama da kasa muka rasa, sai dariyarsu muka ji Suna ta kyakyatawa. Su ka bar mu nan tsaye mu biyu kacal a tsakiyar halittun masu siffofin aljanu. Nan fa muka yi ta matsa layun nan na iikin mu wadanda Maruful Haz ya ba mu, don mu bace, amma sai abu ya faskara. Muna ii, muna gani halittun nan suka kama mu suka tashi da mu sama, sai da suka kai mu can saman wani tsauni mai tsakanin tsawo Sannan suka dirga damu a gaban wani kerarren gida, wanda aka yi shi da zallan zubardaji. Da Zuwa sai kofar gidan ta bude da kanta aka shigar da mu ciki, sannan kofar ta rufe kanta. Nan fa aka yi ta tafiya da mu har tsawon sa'a biyu Sannan muka iso wata wangamemiyar fada wani karaga zaune akan wata shirgegiyar basamuden aljani ne mai mummunar siffa. Aljanin na da rafkeken kai mai kama da na alade. Hannayensa da kafafunsa irin na biri ne. Jelarsa kuwa katuwa ce kuma doguwar gaske duk jikinta kahonhona ne. Girman farcen hannunsa guda ya kai na hauren giwa. Koda aka zo damu gaban aljanin sai ya sa aka zaunar da mu bisa wasu kujeru manya aka dauremu tamau, da sarkoki.Aljanin ya dube mu ya fashe da mahaukaciyar dariya mai kama da tartsatsin aradu, sannan ya ce da mu. "Marhaban da shaidanun bil'adama masu Son shiga cikin gonar Sirrin mu. Ku yi sani cewa ni ne boka Shukurul Akwar, wanda ke kiwon tsohon kure, na Dajin Mutuwa. Bincike ya nuna mini cewa za ku je Dajin Mutuwa ku zamo sanadin mutuwar wannan kure nawa, wanda na shekara tamanin da bakwai ina tsumashi a cikin tsumin tsafina. Lallai ruhina na tare da ruhin wannan kure idan kuka hallaka shi tamkar kun hallaka nine don haka gwara ni yanzu na fara hallaka ku don an ce ka kashe makashinka kafin makashinka ya kashe ka." Lokacin da Shafaru ya zo daidai nan a labarinsa ne rana ta fadi, gari ya soma yin duhu, don haka sai boka Shamakalu ya daga masa hannu ya tsaida shi ga barin zance mai dadi. Boka Shamakalu ya dubi dakarun sarki Hamaru wadanda suka zo da Shafaru ya ce, "Ku koma ga sarkin ku ku ce da shi Shafaru ya kawo mini wasika kuma na ji abin da ke cikinta. Ni boka Shamkalu na ce ba zan bar birnin Farisa ba, kuma ba zan yi wa Shafaru komai ba. Duk abin da sarki zai yi sai dai ya yi kuma ba zan fadi komai ba, sai gobe bayan Shafaru ya gama bayar da wanan labari da bai karasa ba, don haka yanzu na umarci kowa da ya tafi izuwa gida in ya so gobe da safe a dawo nan don jin cigaban labarin Shafaru. A halin yanzu zan ruke Shafaru ya kwana tare da ni." Ko da gama fadin haka sai boka gama fadin haka Shamkalu ya nunan sarkokin da ke jikin Shafaru da danyatsa guda duk suka tsinke suka fadi kasa, sannan sai ya kama hannunsa ya ja shi iZuwa cikin wannan gida nasa inda rijiyar kwankwamai take. Koda faruwar haka sai jama'a suka watse kowa ya kama gabansa. Yayin da boka Shamakalu da Shafaru suka kadaita a cikin wannan gida sai Shamakalu ya yi tsafi take wata aljana ta bayyana ya sa ta ta yi wa Shafaru aski ta gyara fuskar nan tasa ya yi kyau, sannan ta yi masa wanka. Aka kawo tufafi mai kyau aka ba shi ya sanya, aka sa masa turare mai kamshi. Sannan aka kawo masa abinci iri-iri sama da kala goma irin na sarakai aka ba shi ya ci ya koshi. Rabonsa da shiga irin wannan ni'ima shekara ashirin da daya kenan. Bayan ya sami nutsuwa sai boka Shamakalu ya dube shi ya ce, "Yakai Shafaru ka yi sani cewa har abada danuwanka sarki hamaru ba zai taba kaunarka ba, kuma hankalinsa ba zai taba kwanciya ba face ya ga baka numfashi a doron kasa. Ina so ka sani cewa shi makiyı har abada makiyi ne, kuma ba zai fasa farautar makiyinsa ba, in dai yana rage. Yanzu zan baka wani labari wanda zai tabbatar maka da gaskiya ta." Boka Shamkalu ya yk gyaran murya ya fara bayani kamar haka: A wani bangare can na duniya akwai wata rana da wani abokin gaba ya tsira da kyar daga hannun abokan gabansa, bayan sun kusan hallaka shi ya tsere akan dokinsa yayi ta gudu a daji cikin halin suma har ya isa nahiyar da ba ta su ba, dokinsa ya yarda shi a gabar wani kogi inda ya samu ya farfado. Farfadowarsa ke da wuya sai ya jiyo motsin tafiya daga cikin wadansu bishiyoyi. Cikin matukar karfin hali ya daga hannunsa na dama ya dora shi akan kufen takobinsa duk da ya san cewa ba zai iya kodá zare takobin ba. Sannu a hankali motsin tafiyar ya kara yawa har ya fara jiyo sautin murya. Koda ya gane cewa muryar ta mata ce sai hankalinsa ya dan kwanta, domin ya san cewa ba abokan gaba ba ne suka biyo bayansa. Ba zato, ba tsammani sai ga yanmata guda bakwai dauke da tuluna sun iso wannan kogi da nufin dibar ruwa. Koda suka yi arba da Wannan mutum da kuma dokinsa a cikin kogin Suka ga jini na malala akan ruwa sai suka rafka ihu suka yarda tulunan na su suka juya da baya da gudu. Sai da suka yi nisa sannan suka tsaya Suna haki daya daga cikin su wadda ta kasance Kyakkyawar gaske ta gaban kwatance ta dubi Sauran ta ce da su. "Wai shin ku menene dalilin wannan gudu na mu, ca nake mutumin da muka gani a cikin rafin can ba zai iya cutar da mu ba, ku dubi halin da yake mana ba mamaki ma yanzu in muka koma mu tarar ya mutu. Yanzu shi kenan mun hakura da debo ruwan kenan?" koda jin wannan batu sai jikin ragowar yan matan yayi sanyi wadda ke kusa da ita ta ce "haba ishmira shin kin manta ne akwai yan sumame da yawa a nahiyarnan ta mu?babu mamaki mutumin da muka gani a kwance ba shi kadai bane akwai yan uwansa a labe sun dana mana tarko." Ishmira tayi murmushi ta ce " ai kuwa in dai akwai wasu a laben ba zamu iso nan batare da sun cimmana ba. nikam ba zan koma gida ba babu ruwa, lallai sai na koma rafinnan wacce taga zata iya ta biyoni, wadda bazata iya ba ta tafi gida" ishmira na gama fadin haka ta juya da baya ta nufi hanyar rafin, ragiwar yan matan bakwai sai sukayi kasake suna kallon juna, wata matsoraciyar gaske wadda ake kira banisa ta zura a guje zuwa cikin kauyensu lokacin da su ishmira suka dawi bakinrafin sai suka iske wannan mutum a cikin kogin kamar yadda suka bar shi dazu. Gashi dai tsamo-tsamo a cikin ruwa yana numfashi da kyar, amma ya kasa motsi. Ishmira ta kare masa kallo ta ga ashe saurayi ne kyakkyawa, wanda bai fi shekaru ashirin da shida ba, ga shi da kira irin ta sadaukai, kuma babu alamar kamanin mugunta a fuskarsa. Koda ta gama wannan nazari sai ta ruga cikin ruwan sannan suka yi kama-kama ita da sauran yanmatan suka dora shi akan dokinsa. Daga nan kowacce ta cika tulunta da ruwa. Ishmira ta kama linzamin dokin yana kwance a kai taja suka yi gaba izuwa cikin gari. Sai da suka yi nisa da barin rafin, sannan suka fuskanci cewa Banisa ba ta tare da su. Ishmira ce ta fara tambaya, Ko akwai wanda ya ganta?" Badura wadda ta kasance babbar cikin su ta ce, "Ai sarkin tsoron tuni ta ruga gida." Gaba dayansu suka bushe da dariya. Daga nan suka ci gaba da tafiya, suna ta hirar su har da batun wannan bako da suka tsinto a kogi har suka iso cikin kauyen Madinatul Asmal. Madinatul Asmal karamin kauye ne na ma'abota addinin Musulunci a cikin yankin kasar Turkiya. Shi dai wannan kauye haramtacce ne ga sarki Sharmuzul Bazabur wanda ke mulkin birnin Turkiya, domin asalin kauyen an kafa shi ne sa'adda sarki Sharmuzul Bazabur ya hau kashe tsirarun Musulmai wadanda ke zaune a cikin birninsa. Bisa dole suka yi hijira suka koma cikin daji har suka gia wannan karamin kauye, wanda gaba dayan mutanen cikinsa ba Su wuce mutum dubu biyu ba. Shugaban wadannan mutanen kauye wani bawan Allah ne dattijo, dan kimanin shekaru tamanin da doriya ana kiransa da suna Abul Ishmira, wato mahaifin wannan kyakykyawar budurwa wacce ta dauko bakon mutum daga rafi. In ba don karfin addu'a ba, da tuni sarki Sharmuzul Bazabur ya hallaka mutunen wannan kauye, domin har yau har gobe kullum yana turo dakarunsa, suna zuwa farautar wannan kauye, amma duk sa'adda suka iso sai Su ga kauyen ya zama kogi gaba dayansa, kuma ko tsuntsu ba sa gani a wajen Al'amarin da ya jefa sarki Sharmuzul Bazabur cikin matsanancin bakin ciki kenan, domin boka Asimul Abaru ya tabbatar masa da cewa idan har wadannan mutane suka ci gaba da rayuwa to tabbas wata rana za su zamo sanadiyar rushewar mulkinsa, da kuma addinin su na tsafi. Bisa wannan dalili ne sarki Sharmuzul Bazabur ya tsananta farautar makiyansa wato mutanen kauyen Madinatul Asmal, kullum dare da rana. Mutanen birnin Madinatul Asmal sun kasance masu gaskiya, amana da jin kan juna; don haka kowa a garin yana jin dadin zama tare da tafiyar da rayuwarsa cikin in dadi da kwanciyar hankali. Gaba daya mutanen kauyen maza da mata, yara da manya kowa ka gani akwai wata laya daure a wuyansa. Ita dai wannan laya babu komai a cikinta face sunayen Ubangiji tsarkaka na ismil A azami. Babban Malamin kauyen wanda ake kira Sheikh Huzaif bin Kasim shi ne ya raba wadannan layu iya adadin jama'ar kauyen. Kuma ko yau aka haifi Jariri sai an karbo wannan laya a wajen Huzaif an sa masa a wuya. Wannar laya ta kasance tsari ga jama'ar wannan kauye, domin idan suna tare da ita, babu wani tsautsayi da ya isa ya hau kansu. Da yake Banisa ta riga su Ishmira isa gida tana zuwa ta kwashe labarin duk abin da ya faru a rafi ta sanar da jama'ar gari. Ai kuwa nan take aka taru gaba daya a kofar gidan su Ishmira aka yi Cincirindo anan jiran dawowar su Ishmira daga rafi. A wannan lokaci Abul Ishmira da Sheikh Huzaif na zaune a can gefe guda suna tattauna al'amarin inda Abul Ishmira ya dubi Sheikh Huzaif ya ce, "Yakai babban malami shin yanzu menene abin yi? Za mu zauna ne mu ci gaba da sauraro ko kuwa za mu bi bayan yaran nan ne don mu tabbatar da lafiyarsu? Yayin da Sheikh Huzaif ya ji wannan tambya sai ya yi murmushi, sannan ya ce, "Haba Abul Ishmira yanzu ashe har zuciyarka na tunanin wani abu zai samu 'ya'yanmu? Shin ka manta ne cewa suna tare da kariyar Allah. Ina tabbatar maka da cewa idan har suna tare da layunsu babu abin da zai same su. Gama fadin haka ke da wuya aka hango su Ishmira a tare Sun nufo kauyen. Ishmira ce akan gaba rike da linzamin doki, Akan dokin bakon saurayi ne kwamce magashiyan. DAJIN MUTUWA littafi na daya 1 Na Abdulaziz Sani M gini Typing - Shuraihu Usman Part 1E. Koda ganin haka sai hankalin Abul Ishmira ya tashi, ransa ya baci ya dubi Sheikh Huzaif ya ce, "Yakai babban malami ka yi sani cewa 'ya ta karya dokar kauyenmu, lallai hukunci ya tabbata a kanta, tun da ta dauko bako ta shigo da shi." Sheikh Huzaif ya ce, "Kwarai ta karya doka, to amma sai mun ji dalilin ta na karya dokar sannan mu yi mata hukunci daidai da hujjojnta, idan ma tana da hujja mai karfi ba za a hukuntata ba, sai dai mu dauki mataki daidai da tsarin rayuwammu Yana gama fadin hakan ya mike tsaye ya ce, 'Ka zo da ishmira gidana da yammaci domin mu zauna gaba daya da sauran malamai domin magance wannan matsala. Na umarceka da kada awulakanta wannan bako da ta zo da shi. A ceci rayuwarsa a yanzu a yi masa duk abin da ya kamata kafin shi ma mu yanke hukunci a kansa." Abul Ishmira ya sunkui da kai kas ya ce, Haka za a yi ya babban malami." Nan take Sheikh Huzaif ya tafi izuwa gidansa. Ganin tafiyar tasa ne ya sa jama'a suka watse, kowa ya kama gabansa, aka bar Abul Ishmira da matarsa Falira Su kadai a tsaye Suma sauran kawayen Ishmira sai suka rarrabu kowacce ta tafi gidan su. Cikin alamaun tsoro Ishmira ta karaso gaban iyayenta rike da dokin bako, kuma ga tulun ruwa a kanta. Kanta na sunkuye, kirjinta na dakan uku-uku ta tsaya a gabansu. Bisa mamaki sai ta ga mahaifiyarta ta karbi tulun da ke kanta, shi kuwa Abul Ishmira sai ya dauko bako daga kan dokin ya ratayo shi a kafadarsa ya nufi cikin gida. Koda ganin haka sai ita ma Ishmira ta ruga cikin gidan tana ma murna. Abul Ishmira bai sauke bako a ko'ina ba sai a cikin turakarsa. Nan take ya hada magani kala biyu na sha, da na sha fawa ya kimtsa bako. Ishmira ce ma ta talmaka masa wajen hada magungunan. Jim kadan sai bako ya farfado ya dawo cikin hayyacinsa. Koda ganin haka sai Abul Ishmira ya umarci Falira da ta kawo dafafiyar madarar shanu. Take ta cika aiki. Abul Ishmira ya shayar da bako wannan madara a koko da hannunsa. Bayan ya gama shan madarar sai ya kwantar da shi akan gSaboda hunturin sanyin da ke hadawa a wannan lokaci. Shi dai bako har yanzu bai ce da kowa kala ba, sai dai kawai ya kalli wannan ya dubi wancan, yana dan murmushin karfin hali. Jim Kadan kuma sai barci ya kwashe bako. Abul ishmira ya dubi Falira, sannan ya dubi ishmira ya ce, "Kada ku tashi bakon nan har sai ya farka da kansa. Ke kuma Ishmira ki sani cewa da yammac za mu je gidan babban maiami ni da ke, domin ki kare kanki bisa karya dokar mu Koda jin haka sai idanun shmira suka yi tsuru-tsuru ta kasa cewa uffa. Falira ta yi ajiyar Zuciya Cikin yanayin damuwa, sannan ta dubi Ishmira ta ce, yake yata ke kuwa saboda me ki ka yi wannan gangani alhalin kin san doka ce mat tsauri a garin nan ki shigo da bako?" Ishmira ta sunkui da kanta kas cikina alamun nadama, idanunta suka ciko da kwallah ta ce, "Ku gafarce ni ya ku iyayena ku yi San cewa ni kaina ban san yadda aka yi ba zuciya ta rudeni na aikata wannan laifi. Tabbas yanzu na yi nadan a amma hakikannin gaskiya tausayi ne yà sa ni na aikata hakan kuma gani na yi ado, sannan ya lullube shi da bargo babu kamanni na rashin gaskiya ko zalunci a fuskar wannan bako shi ya sa na taimake shi. Falira ta yi ajiyar zucoya ta ce "Ai shi kenan je ki karasa mini aiyuka a cikin gida." Nan take Ishmira ta wuce cikin gida. Da La'asar sakaliya Ishmira da mahaifinta suka tafi izuwa gidan babban malami Sheikh Huzaif. Da zuwa suka shige ciki inda suka isa wani babban falo wanda babu komai a cikinsa face shimfidu na fatar dabbobin dawa. Zaune a kan shimfidar Sheikh huzaifa ne yana sanye da fararen kaya, kuma ya nada gajeren rawani a kansa. Sheikh Huzaif ya kasance mutum mai matsakaicin kaurin jiki, gami da faffadar fuska. Yana da farin gemu, farin saje. Kai duk inda ake neman kwarjini in aka ga Sheikh huzaif an samu. Shekarunsa sun haura casa'in amma kuma bai kai dari ba. Zagaye da shi wasu malamai ne dattija Su goma sha daya, wato shi ne cikon na goma sha biyu. Koda isowar Abul Ishmira da yarsa gaban su Sheikh Huzaf sai suka zauna a gefe daya bayan sun yi sallama an amsa musu. Ishmira ta sunkui da kanta kas ta yi shiru kamar ba ta da rai dama ta sha lullubi kuma duk jikinta a rufe yake. Zuciyarta kuwa sai bugawa take yi da karfi, saboda tsoron irin tambayoyin da za a yi mata yanzu da kuma rashin sanin irin hukuncin da zai biyo baya bisa laifin da ta aikata. Dadin dadawa kuma ba ta taba shigowa wannan gida ba a cikin irin wannan hali na tuhuma bisa laifi. Bayan an yi gaisuwa irin ta addinin Musulunci tsakanin Abul Ishmira da su Sheikh Huzaif sai shiru ya biyo baya, tsawon yan dakiku. Daga can sai daya daga cikin dattawan ya yi gyaran murya, sannan ya dubi lshmira ya ce, "Yake Ishmira shin za ki iya yi mana ce, bayanin abin da ya faru gare ku ke da kawayenki yayin da kuke je rafi diban ruwa?" Ishmira ta hadiyi miyau, sannan ta fara bayani cikin rawar murya har sai da ta zayyane komai dalla-dalla, ba ta boye komai ba. Koda ta gama jawabi sai wani dattijan daban ya sake tambayarta ya ce, "To menene dalilin da ya sa kika dauko wannan bako mutum tare da dokinsa kika taho da shi cikin gari alhalin kin san cewa aifi ne a tsarin dokokin mu?" Ishmira ta amsa wannan tambaya da irin bayanin da ta yi wa mahaifiyarta. Koda jin wannan batu sai gaba dayan dattijawan suka yi shiru, suna kallon Ishmira kawai kamar suna tunanin wani abu har izuwa wani dan lokaci kuma suka yi ta kallon junansu tamkar suna zance da idanu. Daga can sai sheikh Huzaif ya yi gyaran murya ya dubi Ishmira ya ce da ita. "Hakika kin zo da hujja mai karfi, to amma duk da haka sai kin fuskanci hukunci, domin kin karya doka. Hukuncinki shi ne za a tsare ki tsawon kwana uku a gida ba tare da kin fita ko ina ba, ya zamana kullum daga safe har izuwa faduwar rana babu abin da kike face karatun alkur'ani mai girma." Koda jin wannan batu sai fuskar Ishmira ta fadada da murmushi, saboda murnar jin saukin hukuncin da aka yi mata. Nan take ta yi godiya, sannan ta mike ta tafi gida da sauri zuciyarta cike da farin ciki. Da zuwa Ishmira gida ba ta tsaya ko'ina ba sai cikin turakar, mahaifinta inda ake ajiye bako. Da shigartka cikin dakin ta iske bako a kwance kamar yadda ta tafi ta bar shi, kuma har yanzu barci yake bai farka ba. Ishmira ta kurawa fuskar bako idanu, nan take ta ji ta fara Jun Kaunarsa a ranta sai ta yi sauri ta kau da kanta ga barin kallonsa, sannan ta yi sauri ta fice daga dakin. Abin da ba ta sani ba shi ne mahaifiyarta Falira na rakabe a can gefe daya tana kallonta, kuma ta ga sa'adda Ishmira ta kurawa bako idanu tana ta kallonsa. Al'amarın da ya bai wa Falira matukar mamaki kenan, domin ba ta taba gani wani da namiji da ya taba burge Ishmira ba, sai wannan bako. A cikin gaba dayan 'yanmatan dake cikin wannan kauye na Madinatul Ansal babu wata budurwa mai kyau da farin jinin Ishmira. Kusan duk samarın garin sun nemi soyayyarta, amma taki ba su hadin kai, al'amarin da ya fusata mahaifinta kenan, har ma wata rana ya ce da ita me take nufi da kin fitar da gwani daga cikin samarinta, ko kuwa tana nufin ba za ta yi aure ba ne, har abada, A lokacin ne Ishmira ta ce ya kai abbana ka yi sani cewa ina son na yi aure amma sai na ga saurayin da ya kwanta mini a rai, ka yi hakurI a yanzu, domin duk samarin da ke gari nan banga wanda na ii ina so ba. Abul Ishmira ya daka mata tsawa ya ce ai wannan maganar banza ce, ya za ai a ce duk yawan samarin garin nan baki ga wanda kike so ba. To yaushe ne kuwa za ki ga wanda kike so alhalin baki basa shigo mana, kuma muma ba ma zuwa ko'ina." Ishmira ta ce,"Ya kai Abbana ka sani cewa na yi istahara an nuna minj cewa nan da wani lokaci kadan Allah zai kawo wanda zan aura har cikin garin nan. Ni dai abin da nake so da kai shi ne ka ci gaba da rike alkawarin da ka yi mini tun iya yarinya cewar ba zaka aurar da ni da ba sai ga zabina." Da wannan kalami ne jikin Abul Ishmira ya yi sanyi. Daga wannan rana bai kara yi mata maganar aure ba, kawo I yanzu. Kashe gari da Asuba bayan an idar da sallar Asuba sai Abul Ishmira ya shigar da Ishmira cikin wani daki ya zaunar da ita, sannan da ya kawo Alkur'ani ya ba ta ya ce, 'Sai ki kama karatu, don amsa hukunci. Na hore ki da kada ki saurara face kina da bukatar abinci ko zuwa kewaye har izuwa faduwar rana." Ishmira ta karbi Alkur'ani fuskarta cike da murmushi ta ce, 'An gama ya Abbana." Nan take ta kama karatu cikin zazzakar muryarta mai dan karan dadin sauti. Shi kuwa Abul Ishmira sai ya tafi turakarsa ya zauna ya ci gaba da lazumi har gari ya waye, sosai rana ta hudo. A lokacin ne Farila ta shiryo abincin kalaci ta kawowa Abul Ishmira ta ajiye a gabansa. Har ta juya za ta fita sai ya kira Sunanta ya ce, "Ina labarin bakon mu shin ya farka daga barci ne?" Farila ta ce, 'Ya farka, amma da kyar ya iya mikewa zaune." Ya yi magana kuwa, kuma ya ci abinci?" "Ko kala bai ce ba, amma ya ci abinci dan kadan shi ma sai da aka dura masa a baki. Babban abin da ya bani mamakı a gare shi shi ne na ga yana ta kallona yana zub da hawaye, kuma yana ta kallon yanayin gidan nan. Babu yadda ban yi ba da shi akan ya yi mini bayanin dalilin zubar hawaye a idanunsa amma ya ki yai magana. Koda jin wannan batu sai Abul Ishmira ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, 'Kada ki kara tambayarsa komai, zai fi kyau mu ci gaba da Jinyarsa har izuwa tsawon kwana bakwai mu gani wata kila sai ya warware sosai, sannan zai iya yin magana idan har shi ba kurma ba ne." Daga wannan rana Farila ta ci gaba da jinyar bako tamkar dan cikinta, bayan ishmira ta gama horon karatun Alkur'ani na kwana uku sai ta karbi aikin jinyar bako ta ci gaba da yi masa hidima ya zamana dare da rana suna tare babu abin da ke raba su face kwanciyar barci. A yammacin rana ta shida ne Ishmira ta samo sanda ta bai wa bako ya rike sannan ta kama kafadunsa ta tashe shi tsaye ta umarce shi da ya dogara sandar ya yi tafiya. Da kyar da sidin goshi yana zufa ya daga kafarsa guda ya yi taku uku. Saboda tsananin zafin da yake ji a kafar tasa sakamakon raunikan jiki har sai da ya kurma ihu, sannan ya sulale kasa zai fadi. Ishmira ta rugo da gudu ta ruke shi, sannan ta zaunar da shi akan kujera, suka kurawa juna idanu tana mai matukar tausayinsa. Al'amarin da ya jefa shi cikin mamaki kenan, domin har kwalla ce ta zubo mata. Ishmira ta yi murmushi a gare shi ta ce, "Ka yi hakuri dole ne ka daure ka ci gaba da jarraba tafiya, in ba haka ba kuwa jijiyoyin kafar taka za su lalace, su daina aiki. Daga yau kullum za ka dunga yin tafiya taku uku." Bako ya jijiga kansa cikin alamun amincewa gami da yin murmushin yake. Kamar yadda Ishmira

Chapter 4 of 6