Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 6
rigingimu za su balle a cikin gidan nan da cikin majalisata. Yaki zai barke za'ayi asarar miliyoyin rayuka da dukiya, kuma daya daga cikin ku ba zai sami damar gadona ba, face kun yi abu guda. Wannan abu kuwa shi ne ya zama wajibi a gareku ku 'ya'yana, wato ku takwas din nan ku yi shiri a ranar da aljalina ya Cika ku tafi izuwa Dajin Mutuwa, domin ku SamO wadansu abubuwa gudu uku wadanda da Su ne za ku hada wani magani wanda in dai kuka zuba shi a cikin kogin birnin nan ba za a yi tashin hankali ba, kuma ba za a yi asarar rayuka da dukiya ba, kuma tabbas sai daya daga cikin ku ya gajeni, Wadannan abubuwa uku da za ku samo a Cikin dajin mutuwa sun hada da hawayen wani tsohon rikakken kure, wanda ya shekara tamanin da bakwai a duniya, duk duniya babu wani kure mai karfi da shekaru tamkarsa. Abu na biyu shi ne za ku ciro kwayar idanun wani, batoyi, Wanda ya shekara dari da uku a duniya, Shi dai wannan batoyi girmansa yafi na gwiwa Sau goma kuma girman fukafukinsa guda ya ninka gangar, Jikinsá, Yana iya yin tafiyar kwana saba in, a sararin 'sama ba tare da ya gaji ba, kO ya bukaci abinci, ko ruwän sha. Idan ya fara fesar da wuta daga bakinsa sai ya kwana bakwai bai saurara ba. Kwayar idon nasa guda daya ce jal manne a tsakiyar goshinsa. Yanan ya surar giwaye goma da kafafuwansa guda biyu a lokaci guda ya kai su shekar ya'yansa su Cinye. Ya zama dole ku ciro kwayar idon wannan batoyi ku hada da wancan hawaye na tsohon rikakken kure. Abu na uku wanda shi ne na karshe dole ne ku samo ruwan wani koggi wanda ake kira Bahar Shufa adadin cikin salka guda. Kogin Bubar Sufa yana nan a can karshen Dajin Mutuwa. Asalin kogin mahada ce ta dukkanin tekunan duniya. Shi dai wannan kogi ruwan cikinsa ya kasance mai tsananin haske, kamshi, da dadin dandano. Komai dattin ruwa in dai aka zuba digo daya na ruwan Bahar Shufa a cikinsa sai ya tsaftace shi, kuma ya kashe dukkanin cutar da ke cikinsa. Idan mutum ya sha digo daya na wannan ruwa har abada ba zai sake jin kasala ba a jikinsa kuma zuciyarsa za ta zam fari kal ko yaushe ba shi babu bakin ciki ko da kuwa duniya za ta taru ta kishi. Yayin da kuka sami nasarar hada wadannan abubuwa uku kuka dawo gida tarc da Su shi kenan bukata za ta biya baya, kun zuDa abubuwan a cikin kogin birnin nan. Lokacin da sarki Sharudul Amman ya zo nan a Zancensa sai gaba dayanmu muka zazzaro Idanu, hankalin mu ya dugunzuma fiye da koyaushe. Babban cikin mu wato Mukairu ya dubi sarki a nutse ya ce, "Ya kai Babanmu hakika ka zo mana da babban al'amari wanda ya fi karfinmu. Shin ka manta ne cewa bokan da ya ZO mana ya ce ba a shiga Dajin Mutuwa yake, haka kiima shi ne dajin da ke dauke da dukkanin masifun dunIya. Ta ya ya za mu iya zuwa daji har mu iya samo wadannan abubuwa uku kuma mu fito daga cikinsa lafiya? wannan Lallai wannan daji ya ci sunansa Dajin Mutuwa. Koda mun sami damar shigarsu duk hallaka za mu yi dayan mu ba zäi dawo a raye ba. Gwara ma mu zauna a gida duk masifar da za ta zo ta Same Lokacin da Mukairu ya zo anan a zancensa, sai sarki Sharudul Amman ya ce, "Kaicon namiji matsoraci mai zuciyar mata. Ya kai Mukairu hakika ka tabbata ragon maza. Ina son ka sani Cewa matsoraci ba shi zama gwani, har abada. Kuma faduwar gaba asarar namiji ce. Bugu da kari ba a samun duniya a banza dole sai an sha wuya. Nima nan da kuka ganni akan karagar mulki ba a banza na samu ba, sai da na sha bakar wuya kamar ba zan yi rai ba. Ina son ku karfi zukatanku kusa a ranku cewa mai nema yana tare da samu, kuma da dai ku mutu ragwage gwara ku mutu a matsayin jasruma1 ko a tarihi ba a mantawa da ku ba. Idan ba ku manta ba aljani boka Sahibul Furrati ya ce ya zo ne ya bani gudunmuwa don kyautata bayana to ku sani ba komai ba ne gudunmuwar tasa face ya dauki alkawarin zai taimaka ya saku akan hanyar da za ku isa Dajin Mutuwa, amma fa ba zai ceci rayuwasr mutum daya daga cikin ku ba. Sai dai kowa tasa ta fusshe shi, amma duk da haka ya ce na shaida muku cewa wanda duk ya yi abu uku daga cikin ku lallai zai iya shiga Dajin Mutuwa ya fito lafiya. Abu na farko shi ne hakuri, na biyu rike gaskiya da amana. Abu na uku kaunar dan'uwa kamar yadda za ka kaunaci kanka. Wannan shi ne iyakar bayanin da zan iya yi muku dangane jinyarsa dare da rana. Duk sa'adda muka tuna cewa sa ura kwanaki kadan mu rabu da sarki har abada sai mu kama kuka, shi kuwa sarki sai va yi ta rarrashin mu yana ba mu baki gami da kara mana kiwarin gwiwa bisa jajurcewa wajen mu yi nemann samun nasara a tafiyar da za mu yi bayan aj alinsa. A ranar da kwanaki talatin suka cika cif sai rai ya yi halinsa, wato sarki Sharudul da Amman ya mutu. Nan take gida ya cika da koke-koke. Cikini kankanin lokaci labarin mutuwar sarki ya ba zu ko'ina a cikin birnin Farisa. Cikin kankanin lokaci babban birnin ya cika da jaina'a makil aka shiga jana' 1zar sarki Bayan an kammala bikin binne sarki sai dukkaninmu ya'yansa mu takwas muka taruu a waje guda inuka sa aka kirawo mana gaba daya yan majalisar kasar suka zo. lyayen mu mata kuma nan zaune a gefe guda. Bayan yan majalisar sun gama hallara sai Mukairu ya mike tsaye ya gaishe su, sannan ya sanar da su wasiyar da sarki ya bar mana ta batun tafiya, na zuwa Dajin Mutuwa don samo wadannan abubuwa guda uku masu wuyar gaske don don magance masifar da za ta barko kasar nan gaba, kuma a fitar da sarki daga cikin mu. Ko da gama wannan jawabi sa 'yan majalisar suka bushe da dariya gaba dayansu lokaci guda sunan cewa, ai wannan zanccn banza ne Yama za a yi a ce za mu iya zuwa dajin mutuwa har waninmu ya dawo a raye alHalin bokayen duniya sun tabbatar da cewa babu wani mahaluki da ya san inda Dajin Mutuwa yake, bare ma ya shige shi. Nan dai suka watse suka bar mu suna ta yi mana dariya. Tafiyarsu ke da wuya sai muka yi sallama da iyayenmu mata suna kuka, muna kuka. Muka rabu. Nan take muka kwashi guzurinmu kowa ya kama dokinsa ya hau muka bar cikin Farisa muka nausa daji ba tare da sanin inda muka dosa ba. Tun da muka fara tafiyar ko yaushe ina manne da dan'uwana Salkuf, ba ma yarda mu rabu. Su kuwa su Mukairu sai suka hada kansu su shidan suka ware daga cikin mu basa yarda mu jera tare. sai dai ya zamana cewa ko suna gabanmu ko kuma suna bayanmu. Haka kuma sai suka ki yar da mu ci abinci tare da su, kai ko hira ma basa yarda su yi tare da mu kuma ba sa kwanciya a kusa da mu a duk lokacin da muka yada zango. A takaice dai sun kyamace mu fiye da kima. Ganin yadda 'yanmunmu ke nuna mana tsana, sai hankalinmu ya tashi, muka rasa abin da ke mana dadi, amma haka dai muka rungumi kaddara, dan babu yadda za mu yi Sai da muka kwana arba'in da daya muna ta keta dazuzzuka ba tare da sanin inda muka dosa ba, kuma ba mu riski wani gari ba, haka kuma ba mu hadu da wani mugun abu ba. Da yammacin kwana na arba'in din ne muka iso wani surkuki mai wuyar wucewa. Shi dai wannan wuri ya cika manyan ramuka da manyan duwatsu wanda da kyar dawakanmu ke iya ketarewa. Ashe abin da ba mu sani ba shi ne wannan wuri wasu 'yan fashi ne ke amfani da shi wajen dana tarkon kama fatake. Sa'adda muka iso tsakiyar surkukin kawai sai muka ji mun rufta cikin ramuka damu da dawakanmu gaba daya. Kafin mu yi wani yunkuri an jefo mana wadansu raga ta lullube mu sai ga gungun wadansu yanfashi kimanin su dubu sun kewaye mu kowannensu na ruke da muggan makanai. Su dai dai wadannan 'yanfashi sun kasance karti majiya karfi masu girma da ban tsoro. Koda Suka kare mana kallo suka lura da irin tufafin da ke jikin mu, irin na sarauta da kuma dukiyoyin da muke dauke da su da guzuri mai yawa sai suka cika da farin ciki suka hau dariyar mugun ta. Ni da Salkuf sai muka kamu da tsananin tsoro jikin mu ya kama kyarma dama ga shi mu ne mafi kankanta, domin su Mukairu sun fi mu girma da rashin tsoro. Abin da yafi ba mu mamaki shi ne lokacin da yanfashin suka rutsa mu sai muka ga ko kadan babu alamar damuwa a fuskokin su Mukairu. Maimakon ma su tsora ta sai suka kama murmushi. Shi kansa shugaban yangashin sai mamaki ya kama shi ya ce, "Ku wadannan mutum shidan me kuke takama da shi har da ba za ku ji tsoran mu ba, kamar yadda yanuwanku su biyu suka firgita da ganin mu?" Ko da jin wannan tambaya sai Mukairu ya bushe da dariya ya ce, "Ai mu mun san ba ku isa ku yi mana komai ba, sai dai ku yi wa kannanmu. Kawai za ku bata mana lokaci ne a mu." banza kun ga tafiyar Gama fadin hakan ke da wuya sai su Mukairu suka bace bat da su da dawakansu da duk dukiyarsu ya zamana cewa saura ni dá Salkuf kadai a cikin ramin. Nan fa tsoro ya kama 'yanfashin da mu. 'Yanfashin suka ba zama neman su Mukairu a cikin dajin, amma ko duriyarsu ba su ji ba. Da suka gaji da nenman su sai suka dawo gare mu suka fito da mu daga Cikin ramin nan suka kwace mana dawakanmu da dukkanin kayanmu da guzurinmu. Kai hatta rigunan jikin mu sai da suka kwace, sannan suka daka mana tsawa muka firgice muka ruga cikin dawa. Hakan nan muka ci gaba da tafiya cikin tsananin takaici da bakin ciki ga shi kafafunmu ko takalma babu muka yi ta taka kaya da tsidau. Kafin ajima duk kafafun mu sun yi fatu-fatu da jini. Haka dai muka daure muka ci gaba da gaba tafiyar ba mu san inda muka dosa ba, kuma ba mu san yadda rayuwar mu za ta kasance ba. Idan muka tuno yadda 'yanuwan suka guje mu suka bar mu a cikin masifa don mu hallaka sai takaici ya turnuke mu mu kama kuka. Haka dai muka wanzu muna ta tafiya a daii har izuwa lokaci mai tsawo. A sannan ne yunwa da kishirwa suka kama mu ya zamana Cewa mun fara tafiyar sarsarfa muna yanke jiki muna faduwa. Nan fa muka hanga gaba da yamma, kudu da arewa, amma ba mu ga alamar abinci ba, ko ruwan sha. Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalin mu kenan don mun tabbatar da cewa in muka ci gaba da tafiya a haka tabbas za mu hallaka. Kawai sai muka kwanta kasa muka kurawa juna idanu muna zub da hawaye. Salkuf ya dube ni ya ce, "Ya kai dan' uwana idan na rigaka mutuwa a wannann wuri ka rungume gawata a jikinka har naka ajalin ya riskeka. Nima idan kai ne ka rigani mutuwa abin da zan yi kenan, domin kada wani abu ya zo ya raba mu. Fatana ko da tsuntsaye ne za su tsatstsage rhu uto su tsatstsage mu a lokaci guda" Yayin da na ji wannan batu sai na fashe da kuka na ce, "Ya kai danuwana me ya sa kake batun mi uwa tun a yanzu alhalin har yanzu muna iya yin numfashi kuma muna iya motsa idanuwanmu da hannayenmu Shin ka manta da wasiyar Babanmu ne? Lallai ya ce mu karfafi zuciyar mu da samun nasara bisa abin da muka fito nema. Har ko yaushe bana fitar da tsammanin cewa duk bala'in da muka shiga za mu fita daga cikinsa. Lallai mu rungumi hakuri, Juriya, gaskiya da amana da sannu za mu ga Waraka," Lokacin da na zo nan a zancenna sai na ga idanun Salkuf suna wurkilawa alamar cewa yana suma. Nan take na dimauce na mike zaune dakyar na rungume shi a kirjina na fasahe da matsanancin kuka ina mai cewa, "Kar ka tafi ka barni ya danuwana. Lallai idan ka mutu ni ma begenka ne zai kashe ni. Haka dai na wanzu ina ta surutai ina girgiza Salkuf wanda ya zautu har murya ta dashe. Daga nan kuma sai na ji jiri na diba na, take ji da ganina suka dauke ban san abin da ya biyo baya ba. Ba zat0, ba tsammani sai na farka na ganmu mu biyun kwance a kan jaki, mutum matashi na jan jakin, ya nufi wani kogon dutse. A wannan lokaci idanuna nan budewka da rufewa da kyar kuma ban daina jin jiri ba. wani Haka dai na saduda har wannan matashi ya isa damu kofar kogon dutse. Da zuwa sai ya wata mace tare da yarta kyakkyawar yarinya 'yar Klmanin shekara goma sha biyu, sun rugo gare mu. Da zuwansu sai matar ta dubi matashin ta ce, "Maigida wadannan samarin fa a ina ka samo su shin matattu ne ko da ransu" Matashin ya ce, "Ai da ransu, amma suna bukatar taimakon gaggawa. Ina tsammanin dai yan fashi ne suka tarba su, tausayın su na ji shi ya sa na yi tunanin ceton rayuwarsu kuma na kare musu kallo na fahimci cewa 'ya'yan manyan mutanene. Maza ku taimaka mini mu shigar da su ciki." Ba tare da gardamar komai ba, matar da 'yarta suka ciccibeni suka shigar da ni cikin kogon dutsen, shi kuwa matashin sai ya saba Sulkufa kafadarsa ya shiga da shi cikin kogon. Nan take suka kwantar da mu suka yayyafa mana ruwa muka farfado. Ko da ganin mun farfado sai matar ta dauko madarar shanu mai dumi a cikin koko ta ba ni na sha da yawa, sannan ta bai wa Salkuf shi ma ya sha ya koshi. Mu dai in ban da kallon su babu abin da muke yi muna masu mamakin yadda aka yi muka tsira da rayuwar mu. Bayan mun dawo cikin hayyacin mu matashin ya dube mu ya ce, Ya ku wadannan samari mene nc labar ku kuma wane tsautsayi ne ya shigo da ku cikin wannan daji mai tsananin hadari? Koda jin wannan tambaya sai na yi ajiyar zuciva na kwashe labarin mu kaf tun daga farko na zayyane masa tun daga lokacin da muka baro gida kawo Zuwa sa'adda muka fada tarkon 'yanfashi, yanuwanmu su Mukairu suka gudu suka bar mu. Sannan kuma na sanar da shi batun tafiyar mu izuwa Dajin Mutuwa don samo wadannan abubuwa guda uku kamar yadda mahaifin mu ya bar mana wasiya. Lokacin da na gama ba shi wannan labari sai muka ga ya kawo gwauron numfashi ya ajiye, sannan ya sake duban mu da kyau cikin nutsuwa ya ce, "Samari hakika kun sha wuya, to amma fa ku sani cewa wannan wuya da kuka sha ba komai ba ce face somin tab1 akan wacce za ku sha a nan gaba. Ni din nan da kuke ganina nna kasance maharbi kuma a cikin kogon nan aka haife ni, haka ma mahaifina har ma kakana. Wannan sana'a ta farauta na yi gadon ta ne tun Iyaye da kakanni, kuma sai da ya zama na cewa duk duniya babu wani mafarauci wanda ya fi kakana sanin sirrikan daji da kuma yawo a cikin dazuzzukan duniya, amma shi kansa ya taba ba ni labari sa'adda nake yaro cewar yana son ya je wani daji wanda ake kira Dajin Mutuwa, amma ya rasa a inda wannan daji yake, kuma ya ziyarci bokaye, sama da mutum dubu; amma bai Samu wanda zai iyà sa shi a hanyar da zai Je Dajin Mutuwa. Kamar yadda kuka ba ni labarin wadannan abubuwa uku da za ku samo a can ndajin mutuwa haka shi ma ya wasafa mini su. A fadarsa ya ce duk wanda ya mallaki wadannan abubuwa uku ya zuba su a cikin koko Suka gauraye ya kurba ko da makurwa daya ne sai ya zama mashahurin sarki, wanda ba a taba yin kamar sa ba a durniya. Atakaice dai ina tabbatar muku da cuwa akan wannar. buri na neman Dajin Mutuwa kakana ya hallaka, haka ma mahaifina. Ni kuwa ban yarda na bi ra' ayinsu ba, amma na dace da samun Sirrikansu na tsari da sanin sirrin daji, don haka na hakura na yi zamana a wannan daji tare da iyalina na gwanmace na yi ta Zama haka har karshen rayuwata. Wannan ita ce matata sunanta Sazira, wannan kuma yar mu ce ana kiranta da suna Amshira. Yaku wadannan samari ku sani cewa wannan aiki da ke gabanku daidai yake da tafiya neman jaki kara mai Raho, amma duk da haka ina mai kara muku kwarin gwiwa domin sa'a na ga mai rabo babu mamaki ku dace ku sami nasara. NI kam zan ba ku tawa gudunmuwar ta neman tsari daga sharrin 'yanfashi da muggan aljanu da kuma muggan dabbobin dawa. Haka kuma zan koyar da ku yadda ake ratsa daji a fahimce shi, don sanin sharrinsa da hadarinsa, amma dole ne ku zauna tare da ni tsawon kwana goma sha hudu, domin samun ilmin. Bayan nan zan rakaku har izuwa iyakar wannan daji inda na saba raka iyayena da suka shude, kuma inda mukan tsaya mu yi bankwana a duk sa'adda za su tafi neman Dajin Mutuwa." Yayin da muka ji wannan batu sai murna ta kama mu, mu ka yi ta yi masa godiya. Daga bisani sai na dube shi na ce,Yakai wannan mafarauci ka sani cewa ka gabatar da iyalinka a gare mu, kuma ka ba mu takaitaccen tarihinka da na iyayenka, amma har yanzu ba ka fada mana sunanka ba. KO da jin wannan batu sai ya murmushi ya ce, sunana Maruful Haz." DAJIN MUTUWA littafi na daya 1 Na Abdulaziz Sani M gini Typing - Shuraihu Usman Part 1D. Daga wannan rana muka zauna tare da Maruful Haz, kullum sai mun fita farauta tare da shi yana nuna mana Sirrin dajin, kuma yana ba mu sirrikan neman tsari iri-iri. Sannu a hankali muka kware a sanin sirrin daji, kuma muka sami tsari mai yawa. A cikin kwanakin goma sha hudun ne ni da Amshira yar Maruful haz'muka shaku ainun har takai cewa idan muka fita farauta ba ta iya cin abinci har sai ta jira ni na dawo mun ci tare, kai tun muna soyayyar sirrance a zuciyoyinmu har abu ya fito fili iyayen Amshira da danuwana Salkuf suka fahimci abin da ke wakana Da muka cika kwana goma sha hudu tare da mafarauci Maruful Haz, sai ya shirya mana guzuri isasshe ya ba mu sutura, takalma da makamai na kare kai, sannan ya ce mu tashi mu tafi ya yi mana rakiya izuwa iyaka. Yayin da Amshira da Sazira suka ga mun mike za mu tafi muna masu yi musu bankwana sai suka fashe da kuka, saboda shakuwa da kuma sabo. Amshira ta mike da sauri ta dubeni sosai muka kurawa Juna idanu muna zub da hawaye, har 1zuwa dan lokaci, Sannan ta ce"Ya kai masoyina ka yi Sani cewa babu abin da zai iya raba masoyi da masoyinsa a duniya face mutuwa. Zan kasance mai zuba ido da sauraren dawowarka daga yau har izuwa lokacin tsufana. Duk da na san cewa duk wanda ya tafi Daiin Mutuwa baya dawowa, amma ni ina sa ran cewa kai za ka dawo komai daren dadewa. Ka kasance mai ruke alkawari kada ka manta da ni har abada lalla ka biyo ta wannan daji ka daukeni ka tafi da ni kasarku, in dai ba ka rasa rayuwarka ba a can Dajin Mutuwa, domin na zamo abokiyar rayuwarka. Ka sani cewa nina anan dajin aka haife ni ban taba ganin wasu mutane ba a rayuwata face ivayena da ku Gashi jinina ya hadu da naka ina kaunarka, kamar yadda nake kaunar iyayena, don haka na san cewa idan babu su kai kadai ne za ka iya debe mini kewarsu." Yayin da Amshira ta zo nan a zancenta, sai na share hawayen idanuna na damke dubeta da kyau na ce, Ya ke masoyiyata kiyi sani cewa na dauki alkawari komai wuya komai rintsi, in dai ina numfashi a dorOn kasa komai dadewa sai na dawo nan na dauke Ki, mun tafi tare izuwa kasar mu. Haka dai muka yi bankwana da su Amshira muna kuka suna kuka, muka tafi muka bar su nan a tsaye bakin kogon dutse, tun suna hangenmu muna daga musu hannu har muka bace musu da gani. Shi kuwa maharbi Maruful Haz, sai ya ci gaba da yi mana jagora muka yi ta tafiya a cikin daji. Mu kwana nan mu tashi can har muka shafe kwana goma, sannan muka iSO iyaka. Da zuwa sai Maruful Haz ya tsaida mu ya ce, "To anan ne zan rabu da ku inan ma yi muku fatan nasara bisa wannan tafiya da ke gabanku, haka kuma ina dada yi muku tuni da ka da ku manta da kiiyaye abubuwan nan uku, wato; hakuri, juriya, gaskiya da amana. Sannan ko da za ku hadu da 'yanuwanku nan gaba ku so su kada ku saka musu da abin da suka yi muku a baya. Tabba in kuka yi haka za ku iya samun nasara bisa abin da kuka fito nema. Magana ta da ku ta karshe ita ce ina son na roke ku wata alfarma guda daya." Cikin muka dubi Maruful Haz, na ce, "Fadi bukatarka kowacce irii ce in dai muna da iko tabbas sai mun biya maka ita." Yayin da Maruful Haz ya ji haka sai idanunsa suka ciko da kwallah ya ce, "Ina son ku gafarce ni idan na saba muku a lokacin da na zaunan da ku, domin nasan cewa abu ne mawuyaci ku dawo ku riskeni a raye Koda ganin zubar hawayen Maruful Haz da kuma jin wannan batu nasa sai hankalin mu ya dungunzuma muma muka fara hawaye. Na dube shi cikin tsannanin tausayiu da damuwa na ce, "Ai mu a zamanmu da kai babu abin da za mu ce sai godiya. Kai kuwa menene dalilin da ya sa ka ce ba lalai ba ne mu dawo mu riske ka a raye ba?" Maruful Haz ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Dalilin da ya sa kuka ji na fadi haka shi ne idan har za ku sami nasarar shiga Dajin Mutuwa har ku fito lafiya a kallah sai bayan shekara goma. A yanzu haka wani boka ya tabbatar mini da cewa ba zan shekara goma ba a duniya. Lallai wannan shi ne ganina da ku na karshe. Ya kai Shafaru idan kun dawo daga Daiin Mutuwa a raye ka cikawa 'yata alkawari ka zo ka dauketa ka tafi da ita kasarku ta zamo abokiyar rayuwarka." Koda gama wannan jawabi sai muka rungume Maruful Haz gaba dayanmu muka fashe da kuka ina mai cewa, Lallai zan kasance mai cika alkawari." Sai da muka shafe sama da rabin sa'a a tsaye rukunkume da juna muna kuka, sannan muka rabu. Maruful Haz ya juya da baya ya tafi abinsa muma muka nausa gaba ba tare da sanin inda muka dosa ba. Haka dai muka ci gaba da tafiya a dajin kwana nan mu tashi can. Da yake wannan karon mun san sirrin daji ko kadan babu tsoro da fargabar komai a zukatanmu. Duk abin da muka gani akan hanya mun san irin abin da zamu iya haduwa da shi a wajen don haka sai mu dauki mataki. Kai ko rami muka gani mun san irin dabbar da ka iya buya a ciki, kuma ko tarko muka gani na yanfashi muna iya ganewa. Da yake ma muna tare da tsari mun sha giftawa ta gaban yanfashin amma ba su da ikon ganınmu saboda muna tare da wasu layun sihiri wadanda Maruful Haz ya ba mu. Kwanci tashi, sai da muka shafe kwana casa'in muna tafiya a daji ba mu hadu da komai ba, kuma ba mu ji ko duriyar yanuwan mu ba su Mukairu. A ranar da muka cika kwana casa'in ne muka hango wani tafkeken gida a tsakiyar dokar daji, wanda aka gina shi da zallan Jauhar. Koda ganin wannan gida sai muka cika da tsananin mamakin yadda aka yi aka yi shi kuma muka shiga tunanin mutane ne a cikinsa ko aljanu? Nan fa muka tsaya muna shawarar mu je ga wannan gaida ko kuwa mu ratse hanya mu kewaye shi. har ta kai mu da yin gardama ni ne na dage akan cewa sai mun je mun ga abin da ke ciki, shi kuwa danuwana Salkuf sai ya dage dage akan cewa lallai ba za mu je ba, don kada mu kai kan mu ga hallaka. A karshe dai sai na rinjaye shi da na ce da shi, "Kar ka manta fa cewa matsoraci ba shi zama gwani har abada." Yayin da Salkuf ya ji wannan batu, sai ya yi murmushi ya ce, Shi kenan na amince mu je kawai. Ba tare da fargabar komai ba na wuce gaba yana biye da ni har muka je bakin kofar gidan. wanda muka isketa a rufe. Kawai sai na kwankwasa kofar, shiru ba a amsa ba. Na sake kwankwasawa aka sake yin shiru. Na kama kofar na girgiza ta na ji ta a bame tam. Kawai sai muka ja da baya muka taho da gudu muka sa dukkanin karfin mu muka banke kofar da kafafunmu. Take kofar ta balle ta burma ciki kai tsaye muka kunna kai cin gidan. Da shigar mu sa muka yi arba da kwarangwal na sassan bil'adama a zube tsubi-tsubi. Al'amarin da ya firgita mu kenan, amma sai muka kanne muka ci gaba da tafiyar har muka iso kofa ta biyu. Ita ma wannan kofa a rufe take sai da muka banketa da karfi, sannan muka shiga cikin wani bangare dabam, inda muka iske dukiyar lu'ulu'u, zinare, jauhar,, yakutu, da murjan1, ga sunan kamar tulin duwatsu a banza babu mai tsaronsu. Nan ma sai muka cika da mamaki. Haka dai muka ci gaba da tafiya ba tare da mun taba komai ba, har muka iso kofa ta uku. Da zuwanmu bakin kofar muka jiyo koke-koke cikin murya irin ta mutane. Koda jin haka sai muka yi sauri muka barke wannan kofa muka afka ciki. Da shigar mu muka yi arba da 'yanuwanmu su Kumairu a daddaure cikin sarkoki suna ta rusa kuka. Gaba daya jikinsu ya sha dukan bulala ya farfashe sai Jini ne ke zuba. Dukkaninsu sun yi baki sun rame matuka, in ba don ma suturar da ke jikinsu ba, ba za mu iya gane su ba. Cikin matukar farin Ciki suka dube mu suna masu cewa, "Marhaban da ku 'yanuwa ku yi sauri ku kwance mu mu tsira gaba daya kafin maridan nan su dawo su iske

Chapter 3 of 6