Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ DAJIN MUTUWA littafi na daya 1 Na Abdulaziz Sani M gini Typing - Shuraihu Usman Part 1A. Awasu shekaru da dama da suka A shude a birnin Farisa anyi wani mashahurin sarki mai suna Hamaru ibini Salkuf. Sarki Hamaru ya wadata da dukiya mai tarin yawa gami da karfin mulki domin a wannan lokaci akwai sama da manyan garuruwa gudu dari bakwai a karashin mulkinsa. Haka kuma yana da karfin mayaka bisa dalilin haka ne ma dukkanin kasashen duniya ke shakkar sarki Hamaru kuma ake yi masa biyayyar dole da girmamawa. Kash, duk wannan dukiya, daukaka da mulki na sarki Hamaru sai suka zamo a banza tunda sun kasa share masa hawaye bisa abin da ya addabi rayuwarsa wato matsalar rashin haihuwa. Sarki Hamaru na da matan aure a kallah guda arba'in da duriya kuma tun yana saurayi dan shekara ashirin da biyu yayi auren fari amma har shekara saba'in bai samu haihuwa ba, wannan matsala ba karamin jefa sarki tayi ba cikin mugun bakin ciki. Babu irin kokarin da sarki Hamaru baiyi ba wajen neman maganin haihuwa a wajen likitoci da bokaye amma ba'a Samu dace ba duk sa'adda sarki Hamaru ya tuno da wannan matsala sai bakin ciki ya taru yayi masa katutu a zuciya harma ya boye kansa ya kama kuka. Ana cikin wannan hali ne wata rana wani bakon boka waishi Shamakalu ya sauka a birnin Farisa a cikin gari ya zamana cewa ya zo da abubuwan al'ajabi wadanda suka firgita jama'a domin kuwa yana iyayin abubuwa da dama wadanda ake ganin cewa har abada ba za su yiyu ba. Abu na farko da yayi wanda ya baiwa kowa matukar mamaki shine akwai wata tsohuwar rijiya a tsakiyar birnin wacce ta gagari a budeta a debi ruwanta saboda tarewar wasu bakaken aljanu a cikinta. Sai da ya zamana cewa an gine rijiyar an kangeta, amma ko kusa da wajen mutum ya je sai dai a dauki gawarsa, kai hanyar da ta doshi wajen ma ba'abi sama da tsawon shekaru talatin amma a ranar da boka Shamakalu ya sauka ya banke kofar ginin, kuma ya bude murfin rijiyar da karfin sihirinsa ya fatattaki duk bakaken aljanun da ke wajen ya debi ruwan rijiyar ya sha ya shayar da dokinsa Harma ya mayar da dakin rijiyar masaukinsa wato ya rinka kwana a cikin dakin da rijiyar take. Ko da faruwar wannan al'amari nan da nan labarin Shamakalu ya cika gari sai ga jama'a nata bulbulowa daga ko ina birni da kauye suna zuwa neman biyan bukata. Duk wanda ya zo da larura ta rashin lafiya sai Shamakalu ya debi ruwan wannan tsohuwar rijiya ya bashi ya ce ya sha. Ai kuwa da zarar mutum ya sha ruwan sai ya warke daga cutar nan take ko da kuwa ya shekara dari a cikin larurar. Babban abin al'ajabi na biyu da Shamakalu yayi shine akwai wata sihiratacciyar Damisa wacce kullum daren duniya tana yawo a cikin birmin Farisa. Duk wanda tsautsayi ya sa ya yi arba da ita sai ya zama gawa ko kuma ya hauka ce ko ya zama makaho ko ya nakasce. a daren da Shamakalu ya shiga wannan birni yayi arba da sihirtacciyar damisar suka yi gumurzu ya kamata da hannunsa sai gashi tayi ladaf yana sarrafata tamkar karen farauta ya zamana cewa ko da yaushe tana durkushe a gabansa har ma yana umartarta da yi masa wasu aiyukan. Ita dai wannan Damisa duk mutumin da bai haura shekara saba'in ba bai san farkon baiyanarta ba a Birnin Farisa sai dai kawai ya taso ya ganta ko ya ji labarinta Damisar takan fito ne kullum da tsakiyar dare kuma idan tayi haniniya sai an jiyo sautin haniniyar a ko ina cikin birnin kuma duk wanda ya ji haniniyar sai ya firgita ainun wasu ma asalin kamuwa da gudawarsu kenan. Daga ranar da Shamakalu ya dira ba'a sake jin haniniyar wannan Damisar ba sai ga shima ana zuwa kallonta a banza da rana tsaka ana ta al'ajabi. Lokacin da sarki Hamaru ya sami tabbacin wadannan abubuwan al'ajabi wadanda boka Shamakalu ya yi sai ya aikamasa da dukiya mai yawa kuma ya gaiyaceshi izuwa fadarsa domin ya gabatar da bukatarsa a gareshi. Yayin da yan aiken sarki suka jewa boka Shamakalu da wannan sako sai yaki karbar wannan dukiya kuma ya ce da su su koma ga sarki su shaida masa cewa shi baya karbar kyauta ko sadaka haka kuma baya zuwa wajen mai neman biyan bukata sai dai a zo wajensa. Nan take Shamakalu ya yi tsafi sai dukiya ta baiyana ninkin wacce sarki ya aiko masa da ita. Kawai sai ya báiwa 'yan aiken sa ya ce ku debi wannan dukiya na baku ita kyauta domin ni ba'a zuwa wajena a tafi hannu banza face an sami karuwa. Cikin tsananin farin ciki da rawar jiki 'yan aiken sarki suka kwashe wannan dukiya suka yi ta dogiya sannan suka yi sallama suka tafi. Lokacin da 'yan aiken suka koma fadar sarki Hamaru suka kwashe labarin duk abin da ya faru tsakaninsu da boka Shamakalu suka zaiyane. Sai ran sarki ya baci zuciyarsa tayi bakinkirin ya fusata ainun. Nan take ya tuno da karfim,mulkınsa da kuma darajarsa a idanun duniya amma ya za'ace boka guda daya ya shigo har cikin birninsa ya nuna masa gadara. Nan take sarki Hamaru ya ce "A shirya dakarun yaki mutun dubu su je su fatattaki wannan boka daga birninsa da karfin tuwo." Ko da jin wannan danyen hukunci sai fadawan sarki suka shiga rarrashinsa suna bashi baki da kyar ya amince cewar a aikawa da boka Shamakalu wasika cewar sarki na bukatar ya kwashe komatsansa ya bar masa bininsa Salin'alin ba da tashin hankali ba. Nan take aka rubuta wannan takarda kuwa sai aka rasa wanda za'a baiwa takardar ya je ya kaiwa boka Shamakalu domin duk wanda aka baiwa daga cikin bayin sarki sai ya kama kuka yana neman ayi masa uzuri don kada ya je fushin boka Shamakalu ya tabbata akansa. Yayin da aka rasa wanda zai kai wannan takarda sai sarki ya ce "aje kurkuku a fito da wani mutum waishi Shafaru a bashi takardar ya kai in ya so duk bala'in da zai same shi ya same shin kuma da zarar ya dawo a sake damkeshi a mai dashi kurkukun a kulle." Asalin Shafaru kanine ga mahaifin sarki Hamaru kuma shine ya cancanta ya hau karagar mulki bayan mutuwar mahaifin sarki Hamaru amma saboda kasancewar Hamaru sadauki kuma azzálumi sai ya kama Shafaru ya kulle shi a kurkuku kuma ya kori iyalansa daga cikin gidan sarauta ya zamana cewa suna walagigi a gari basu da makwanci basu da cin yau bare na gobe, ma'ana suka wulakanta suka zama Almajiran dole domin an rabasu da dukkanin abin da suka mallaka. A halin yanzu Shafaru ya shekara ashirin da daya a cikin kurkukun kuma tunda aka kulleshi dai dai da rana daya bai taba fitowa ba kuma bai sake saduwa da iyalansa ba. Shafaru na da mata guda daya da kuma 'ya daya wacce sa'adda aka daureshin bata wuce shekara uku ba a duniya ana kiranta da suna Humaila. Mahaifiyar tata kuwa sunanta Amshira. Wani babban abin takaici shine ba'a taba barin Humaila da Amshira sun ziyarci Shafaru a gidan kurkuku ba. Duk sa'adda suka je ganinsa sai a koresu ayi musu mulakanci, wani lokacin ma har dukansu ake yi a fatattakesu. Da farko sa'adda Humaila take yarinya karama kullum sai Amshira tayi bara ko kuma tayi aikatau sannan suke samun abin da za su ci, kuma komai ruwa komai rana sai dai su kwana a kwararo ko a cikin rami sun sha jin giftawar sihirtacciyar damisar nan daf da su amma wani iko na Allah tsautsayi bai sa ta taba ganinsu ba amma duk sa'adda Humaila ta ji haniniyar damisar sai ta kwana bakwai tana a mai da gudawa, dakyar take samun lafiya. Lokacin da Humaila ta fara zama budurwa, kyawunta da na siffarta suka fara baiyana sai azzalumai suka fara kawo mata farmaki don suyi lalata da ita. Da kyar Amshira ta rinka kwatarta. Ba shiri suka nemi aikatau a gidan wani attajiri har ya basu makwanci a cikin gidansa. Shi dai wannan attajiri yana da mace guda daya amma daga ranar daya kyallara ido ya ga Humaila sai kwadayi ya kama shi don haka wata rana matarsa bata nan ta tafi ganin gida sai ya ribaci Humaila har ta debo masu ruwa takai masa cikin turakarsa. Da shigarta cikin turakar ya faki ido ya ga babu kowa a kusa sai ya shiga ciki ya mai da kofa ya rufe, kawai sai ya afkawa Humaila suka kama kokawa ya na son yayi lalata da ita da karfin tsiya. A wannan lokaci Amshira na can a cikin dakin da aka basu tana ta sharar barci bata san abin da ke wakana ba. Yayin da attajiri ya ga ya kasa biyan bukatarsa sai ya mangare Humaila ta fadi kasa a galabaice, har ya yunkura zai afka mata ashe hannunta ya kai kan wata wuka cikin zafin nama ta dauki wukar ta soka masa a ido , take attajiri ya kurma ihu, jini kuwa ya kama bulbula daga cikin idon nasa. Kafin bayin gidan Su iso tuni Humaila ta ruga dakin da mahaifiyarta ke kwance, cikin rudewa kuma ta na kuka ta tashi mahaifiyarta ta sanar da ita duk abin da ya faru tsakaninta da attajiri. Yayin da Amshira ta ji wannan batu sai ta ce da ita. "Shin wani ya ganki lokacin da ki ka fito daga dakinsa?" Humaila ta ce "A'a kafin bayin gidan su kawo masa dauki tuni ta rugo nan." Amshira ta ce "Da kyau yata kinyi farar dabara, ki kwantar da hankalinki babu inda Zamu tafi har sai. dare yayi sannan mu hada namu ina mu mu sulale." Wannan shine abin da ya faru tsakanin Humaila da mahaifiyarta Amshira. 'al'marin attajiri kuwa lokacin da ya kurma ihu sakamakon wukar da Humaila ta caka masa a ido jini na ta zuba sai ga bayin gidan sun rugo da gudu izuwa cikin turakar tasa. Da zuwa suka iskeshi shi kadai yana ta birgima a kas yana ihu, cikin gaggawa suka sa tsumma suka daure idanun don tsaida jini sannan aka ruga aka kirawo mai magani yayi masa magani. Nan da nan 'yan'uwa da abokan attajiri suka cika gida. Yayin da aka tambayeshi yadda wannan al'amari ya faru sai ya ce "Ai bisa tsautsayine ya zame ya fada kan wannan wuka ta cike a Idanunsa." Dalilin da yasa kuwa yayi wannan karya shine zai ji kunya idan matarsa da jama'a suka ji cewa yar almajira ya farwa ta yi masa wannan aika-aika. Nan dai aka yi ta yiwa attajiri jaje bisa rasa idonsa guda da yayi. Lokacin da labari ya riski matarsa sai ta baro gidansu da sauri tana kuka ta zo ta kama aikin jinyarsa. Yayin da dare ya raba sai Humaila da, Amshira suka hada yan komatsansu suka sulale suka bar gidan. Da fitowar sai suka wuce kai tsaye izuwa gidan wata tsohuwa da ake kira Shabiratu. Tsohuwa Shabiratu ta kasance dillaliya a gidan sarki kuma shekarunta a kallah za su kai casa'in da motsi, ita dai Shabiratu ta kasance mace mai tausayi da taimakon ma kaskanta. Humaila da Amshira sun saba da wannan tsohuwa tun suna kwana a kwaroro kuma tasha yi musu tayin Su koma gidanta da zama amma sai suka ki saboda gidanta a kusa da inda Tsohuwar rijiyan nan take mai kwankwamai. Duk da cewa akwai tazara mai dan yawa tsakanin gidan Shabiratu da wannan rijiya su Amshira na matukar jin tsoron zuwa. Da yake masu iya magana sunce idan kaga ki gudu to sa gudu ne bai zoba kuma abin da ya koro bera daga rami ya fada wuta, ya fi wutar zafi. Tabbas Su Humaila sun san cewa idan suka ci gaba da zama a gidan attajiri tabbas sai ya jefa rayuwarsu a cikin bala'i bisa wannan rasa ido guda da yayi. Haka kuma indai zai gansu a wani wurin ma ba zai kyalesu ba. Bisa wannan daliline suka yi tunanin cewa dole ne su nemi wani gida inda zasu buya. Da suka yi dogon tunani sai suka ga cewa ai basu da wani zabi face su tafi gidan tsohuwa Shabiratu. Cikin tsananin razani da fargaba kuma jikinsu na kyarma suka tunkari gidan tsohuwa Shabiratu. Abu nafarko dai suna tsoron gamuwa da sihirtacciyar damisa sannan kuma suna shakkar bin wannan hanya wacce zata nufi inda muguwar rijiya take. Haka dai suka kama hanya a cikin daren suka yi ta tafiya har suka iso kofar gidan tsohuwa Shabiratu cikin sa'a bá tare da sun hadu da komai ba. Da zuwa sai suka buga kofar gidan sau daya. Bisa mamaki sai suka ji muryar tsohuwa Shabiratu tana mai cewa Wanene nan yake buga mini kofa da wannan tsohon dare?" Cikin murya mai rawa. Amshira ta amsa ta ce "Ni ce almajira Amshira tare da 'yata Humaila. Yake dillaliya kiyi mana rai ki bude mana mu shigo." Ko da jin wannan batu sai dillaliya Shabiratu ta mike da sauri ta fito daga cikin dakinta taje ta bude kofar gidan. Amshira da Humaila suka shige ciki sannan ta mai da kofar ta rufe. Shabiratu ta yiwa su Amshira kallon tsaf ta fuskanci cewa lallai suna cikin tashin hankali kawai sai ta jasu izuwa cikin turakarta tayi musu shinfida ta ce su kwanta suyi barci bata bukatar ta ji komai da ga bakinsu sai gobe da safe. Cikin tsananin murna suka kwanta suna masu yi mata godiya. Ita dai ba tace da su uffan ba har barci ya kwashesu. Ita kuwa Shabiratu bata sami damar rintsawa ba sai gefin Asubahi. Yayin da Amshira da Humalla suka farka daga barci sai suka tashi suka wanke jikinsu, sannan suka kama share-share da gyaran gida. Kafin Shabiratu ta farka daga barci sun gama kintsa gida har ma sun dafa abin kalaci. Gamawarsu ke da wuya sai tsohuwa Shabiratu ta farka koda ta ga yadda suka gyara gidan har ma suka dafa abinci sai farin ciki ya lullubeta, al'amarin da ya janyo idanunta suka ciko da kwalla ta fara zubar da hawaye koda ganin haka sai hankalin su Humaila ya dugunzuma, cikin matukar damuwa Amshira ta dubi tsohuwa Shabiratu ta ce ya ke wannan dillaliya ki gafarcemu idan wanan aiki da muka yi miki ya bata miki rai. Sa'adda Shabiratu ta ji haka sai ta yi murmushi ta ce ai ko kadan ba ku 6ata mini ba, asalima tsananin farin cikine ya sani zubar da wannan hawaye. Ku sani cewa ni din nan da ku ke ganina bani da kowa a garin nan asalina ma a yaki aka samoni a matsayin ganima, tun ban fi shekara hudu ba, a duniya. Ban san iyayena ba kuma bansan dangina ba. Na girma a matsayin baiwa daga baya maigidana ya yantani bayan na tsufa ina yi masa bauta. Ban taba yin aure ba kuma ban taba haihuwa ba. A rayuwata wani bai taba kula da makwanci na ba ko yayi mini wata kyautatawa ba makamanciyar wannan da kuka yi mini yanzu. A salima dai tun da na shigo cikin gidan nan kimanin shekaru arba'in baya ban taba kwana tare da kowa ba a cikinsa face ku din nan. Lokacin da na farko daga barci naga kun share mini gida, kun gyara mini shimfida kuma kun dafa mini abinci sai na aiyana a raina ina mai cewa ina ma ace ku dangina ne na jini da ban mutu da takaicin rashin yan uwan ba a duniya. Sa'adda tsohuwa Shabiratu ta zo nan a zancenta sai tausayinta ya kama su Humaila suka rungumeta su duka suka fashe da kuka har izuwa lokaci mai tsawo. Bayan sun nutsu ne suka kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsu da attajiri suka zaiyane mata. Ko da ta ji hakan sai itama ta kamu da tausayinsu ta ce da su daga yau zata boyesu a cikin gidanta har izuwa ranar da mai rabawa zata rabasu wato mutuwa. Haka dai suka ci gaba da hira har Ashmira ta baiwa tsohuwa Shabiratu labarin rayuwarsu kaf har da batun daure mijinta Shafaru a kurkuku saboda rashin adalcin sarki don kawai ya hau karagar mulki. Ashmira ta sanar da Shabiratu cewa tun Humaila na da shekara uku a duniya aka daure Shafaru gashi har ta cika budurwa amma basu sake ganin Shafaru ba, basu sani ba ma ko yana raye ko ya mutu. Yayin da Shabiratu ta ji wannan batu sai tausayi ya turnuketa ta sake rungume Humaila da Ashmira a kirjinta ta fashe da kuka tana mai cewa kuyi hakuri ku rungumi kaddara lallai daga yau zan rukeku tamkar 'ya'yana. Daga wannan rana Amshira da Humaila suka ci gaba da zama tare da tsohuwa Shabiratu cikin jin dadi da kwanciyar hankali tamkar ya'yanta na cikinta. Da yake Shabiratu na hulda da gidan sarki sai tayi ta bincike cikin hikima har ta so labarin cewa Shafaru na nan a raye a kurkuku Nan fa tayi ta kokarin ta sadu da shi amma sai abu ya faskara domin sarki ya sa doka mai tsanani akansa ba'a yarda kowa ya ziyarce shi ba a kurkukun. Ranar da sarki zai sa a fito da Shafaru daga kurkuku domin a bashi wasika ya kaiwa boka Shamakalu sai tsohuwa Shabiratu ta sami labari a lokacin da ta je gidan sarki. Nan da nan kuwa ta garzayo da sauri ta dawo gida ta sanar da su Amshira cewa yau ne ranar da za'a fito da Shafaru amma ga dalilin fito da shi don kawai a bashi wasika ne ya kaiwa boka Shamakalu saboda an rasa wanda zai kai wasika kowa na tsoro saboda duk wanda ya kai wasikar da wuya ya rayu. Ko da jin wannan batu sai hankalin Amshira dana Humaila ya dugunzuma suka fashe da kuka saboda sun san cewa shi kenan har abada ba za su sake saduwa da Shafaru ba. Amshira ta dubi Shabiratu a lokacin da hawaye ke ta kwarara a idanunta ta ce"Ya ke uwata kin sani cewa fitarmu daga cikin gidan nan ni da yata abu ne mai mugun hadari domin idan har attajiri ya ganmu zai iya sawa a biyo dare a hallaka mu kema kuma mu shafa miki kashin kaji. Ina mai neman alfarma guda daya a wajenki, ina son na baki wannna sarkar da ke wuya na, duk yadda za'ayi ki baiwa Shafaru wannan sarka ya gani kafin ya kai wannan wasika izuwa gidan boka Shamkalu tun da dai ta kofar gidan nan zai wuce. Idan ya tambaye ki ina ki ka sami sarkar ki ce da shi kina tare da mai ita kuma ta ce kiyi masa albishir cewa yarsa humaila na nan a raye ta zama budurwa cikin koshin lafiya. Ki gaya masa cewa kada ya bukaci ganinmu har sai idan bai rasa rayuwarsa ba bayan saduwarsa da boka Shamakalu." Ko da gama wannan jawabi sai Amshira ta cire wata sarka dake wuyanta wadda aka yi ta da zallan jauhar. In banda wannan sarka babu wani abu mai daraja wanda Amshira ta mallaka a duniya kuma duk da irin talaucin da suka Shiga a baya da fatara bata taba tunanin ta siyar da sarkar ba. Kullum tana 6oye sarkar don kada ta bata ko a kwance, duk sa'adda ta dubi sarkar sai ta tuno da mijinta Shafaru sa'adda ya daura mata sarkar a wuyanta ranar da aka daura musu aure. kawai sai tayi ta zubar da hawaye. Yayin da tsohuwa Shabiratu ta karbi wannan sarka daga hannun Amshira sai ta danketa da kyau ta ce Na rantse da darajar furfurar dake kaina duk wuya duk rintsi ko zan rasa rayuwata sai na sada wannan sarka ga mijinki a gobe idan za'a wuce dashi ta kofar gidan nan don zuwa gidan boka Shamakalu." Kashe gari kuwa tuni labari ya cika gari cewa yau ne za'a fito da Shafaru daga kurkuku domin a tusa keyarsa ya kaiwa boka Shamakalu wasikar raddi ta sarki. Ko da jin wannan labari sai mamaki ya kama jama'a domin babu wanda yayi zaton cewa har yanzu Shafaru na nan a raye. Kafin a kulle Shafaru a kurkuku ya kasance mutum mai farin jini, suna da daukaka a cikin birnin Farisa fiye da kowa saboda tausayinsa da kuma taimakonsa ga talakawa gami da rashin girman kansa a matsayınsa na dan sarki. Hakika a wancan lokacI jama'a sun so ya ya zama sarkinsu amma sai gashi an nuna fin karfi wato dan wansa ya karbi karagar da karfin tsiya. A lokacinma sai da talakawa suka yi zanga-zanga amma ko da sarki Hamaru yasa aka rinka kamasu ana gana musu azaba sai kowa ya noke aka dai na zanga-zangar Sa' adda mutane suka sami labarin cewa Shafaru na nan a raye kuma yau ne za'a fito da shi sai jama'a suka cika da dumbun farin ciki DAJIN MUTUWA littafi na daya 1 Na Abdulaziz Sani M gini Typing - Shuraihu Usman Part 1B. aka yi ta fitowa daga cikin gidaje ana jeruwa akan hanya don kawai a ga Shafaru, Manyarn mutane kuwa masu shekaru suka yi ta bayar da labarin Shafaru ga yan baya wadanda basu san shi ba. Na da nan kaunar Shafaru ta cika zukatan matasa da yara fiye da yadda manya ma ke kaunarsa. Nan fa garin gaba daya ya hautsine da ambaton Shafaru duk inda mutum ya wuce sai dai ya ga jama'a sun fito sunyi dandazo. Tun daga bakin kofar kurkukun garin wanda ke can bayan gari har izuwa cikin garin inda gidan boka Shamakalu ya ke mutane sun jeru a sahu dama da

Chapter 1 of 6