Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wuri. Ismail yace, zan dawo da wuri insha Allah. Ya kalli mimi, khadija bari inje in dawo, ko kina son wani abu inzo miki dashi? Ta girgiza kai alamun a’a. Taci taci gaba da kukanta. Yace, shikenan sai na dawo. Yasa kai ya fice mimi ta qara sautin kuka. “yaya malam ya saba da ganin kukana, ya daina lallashi na ynxun. Yaya tace a’a bayason kukan ne, shiyasa. Kuma gashi inya lallasheki bakyayin shiru. Ai khadija a rayuwa in akace maka kayi haquri, to kayishi. Karka ce wai kai zakayi tayi, mai lallashinka sai ya gundira. Mimi tayi shiru. Can tace, Yaya wai kuma baku da ‘yan uwa ne? Tace me kk gani? Tace naga ku kadai ne kuke zuwa. Yaya Amina tace, muna dasu khadija, amma dai basu damu damu ba. Ni da Ismail ne muke uwa daya. Nan ta ba ta labarinsu. Bata 6oye mata komai ba game dasu. Mamaki ya cik mimi, tace dama ana samun haka? Ni kam kishiyar mama na har tafi mamana sona. Ynxun haka nasan tanaa cikin damuwa. Yaya Aminu tace, bana zaton akwai wanda zaifi uwa son ‘yarta. Khadija duk inda mahaifiyar ki take a ynxun tafi kowa tashin hankali, sai dai in qila ita mai kawaici ce. Soyayyar uwa da ‘ya na daban ne kinji. Amma zaki gane haka nan gaba. Mimi tace, ko qawayena sunsha fadamun haka, amma har yau ban gamsu ba. Yaya Amina tace, to ke dame kk dogara wanda har yasa kk ganin mahaifiyar ki bata sonki? Mimi tace, zan baki labari, saina qara jin sauqi, amma ina da hujjoji masu yawa. Shi kam Ismail har ya Sauka samansu, ya dauki hanyar fita, sai ya fasa, ya dawo ya nufi gurin saida magani domin ya amshi canjinsa. Tun kafin ya qarasa dan windon da zai amshi canjin nasa, sai ya jiyo muryar innar Zainabu tana cewa, ni kudina sun qare banida sauran ko na mota. Wani yace, ina ruwanmu da qarewar kudinku. Kuma bamu damu ku sai mata magani ba. Mu dai ku bamu kudinmu, ynxun da wannan abokin aikin nawa bai ganku ba, da ynxun kun gudu. Ismail ya qarasa gurin su daidai lokacin da innar su Zainabu take cewa, nima ba laifi na bane, Alhaji ne baizo ba. Dayan yace, ku kirashi a waya mana babu inda zakuje. Ismail ya miqa wa Mutumin hannu tare dayi masa sallama suka gaisa, sannan ya kalli Inna wadda tunda ta ganshi taji kunya matuqa, kamar tace, qasa bude in shige. Yace, inna lfy kuwa? Tace lfy qalau. Dayan yace, kawai inna ki fada masa gsky. Kanaji ko malam. Wannan matar tun ranar da suka kawo ‘yarsu aka bata gado, bata biya kudin gadon ba, sannan akwai cikon kudin magani, wanda zata bada ciko, amma taqi, kullum sai tace, sai alhaji yazo. Yau likita ya ba sallama kurum, sai dai wannan abokin aikin nawa ya ganta a bakin Gate zasu hau tasi. Kaga mu taja mana kenan, ace mu muka cinye kudin. Ismail yace, nawa ne kudin? Inna cikin kunya tace, umm ai da ma ka barshi kawai, Alhajin dama yayi tafiya ne shiyasa. Mutumin yace, inna ki bari kurum a biya muku. Ba wani Alhaji, kullum kina zaizo, amma shiru. Ya kalli Ismail, dubu biyar. In kuma za’a basu ragowar maganinsu, dubu shida da dari uku da saba’in. Ismail ya saka hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro ‘yan dubu dubu ya miqa musu dubu shida. Sannan ya ce, jiya canji na nawa na bari anan? Dayan yace dari bakwai da hamsin. Ismail yace, ku cire cikon ku bani sauran canjin. Kanta a qasa tace, an gode Ismail. Ta juya zata tafi, suka ce, ki tsaya mana ki amshi sauran magungunan da kuma takardar shedar biya. Ismail ya amshi canjin sa, sannan ya kalli innar Zainabu, “Allah ya qara sauqi” bai jira amsarta ba, ya wuce. Ita kuwa dama kunya ta hana ta amsawa. Zainabu ta nufo gurin, sbd itama tasa baki, ko zasu yarda za’a kawo musu daga baya. Sam basuga juna ba, saida suka zo daf. Itace ta soma ganinsa. Tsayuwar da tayi ne yasa shi ganinta. Tayi sauri ta juya baya. Ismail ya runtse ido ya bude. Gabansa yaci gaba da faduwa. Shima yayi saurin dauke idanunsa daga kallon bayanta. Da qyar yace, “yaya jikinki? Tace, da sauqi, cikin rawar murya dake dauke da kuka tayi magana. Yaya taka mai jikin? Ya dubi inda take, a ransa yace, ashe taji. A fili yace ta samu sauqi. Yaja qafafunsa wadanda sukayi masa nauyi yace, sai anjima. Ta bishi da kallo bayan ya wuce. Sam ta kasa ko motsi, sai kuka har innarta ta iso tana tambayarta lafiya? Zainabu tace, an cuce ni. Dajin haka innar tasan Zainabu taga Ismail. Cikin borin kunya tace, “kina ta an cuce ki. Matar mutum ai kabarinsa ko? Ki barshi a qaddara. Zaizo ya sameni shi kuma Alhajin. Ya sanni, ni walki ce ina daidai da qugun kowa. Zainabu dai bata tanka ba, sai ta fita abinta. Tunda suka koma gida ko yaushe Zainabu tana cikin qunci da kuka. Musamman da innarta ta fada mata cewa, Ismail dinne ya biya kudin gado. Innarta tanason Alhajin yazo ya biya kudin da suka kashe, indai yanason zama da Zainabu. Ita kuwa Zainabu ba haka nata tunanin yake ba. Jiran Alhajin takeyi. Ko nawa zai kashe, batajin cewa, zata koma gidan Alhajin. Ismail ya jima zaune akan katifarsa kafin ya tashi ya dauki bokitinsa ya nufi cikin gidan, suna ta nasu harkoki. Yayi sallama suka amsa sannan ya gaidasu, ya nufi dakin Inna, tana ta gyangyadi, ya gaida ta. Ta tambayi mai jiki, yace, da sauqi, tace kai dama ashe Yarinyar nan ba sonka takeyi ba? Ismail yayi murmushi, tare da cewa ai wannan ya wuce Inna. Ya miqe ya nufi bandaki. Tace, haka dai kk kullum ba’ajin cikinka. Jeka can ka qarata. Bayan ya fito ne yaga wata yayarsu tazo ya gaida ita, zai wuce, fatu tace, kin masa jaje kuwa? Yaya shafa tace, meya faru dashi? Fatu ta tuntsire da dariya. “huce haushi akayi masa da mace. Ashe bata sonsa ta gudu, sai kuma tayi hadari a hanya. Shafa ta kalli Ismail wanda shi yana daf da zaure tace, to ashe haka akayi Ismail? To Allah ya kyauta. Yace, Ameen tare da shigewa zauren. Ya gama shirinsa tsaf cikin yadi mai kalar sararin samaniya marar nauyi. Ya saka hula sannan ya feshe jikinsa da turarukansa na musamman da yake hadawa a gurin masu saida turaruka sannan ya fita ya nufi gidansu Mahmud don amsa kiran malam Aminu. Da Mahmud ya soma haduwa, sai dai irin fara’ar da ya gani a fuskar Mahmud din ta bashi mamaki. Yace, malam ko anyi maka baiko da rabi’atu ne? Mahmud yace, qila da hakan ne zaiyi wuya ka gane a fuskata. Gara ma inda ranar daurin auren ce. Ismail ya dafashi, to sanar dani mana game da farin cikinnan naka? Mahmud ya kama hannun Ismail. “Zomuje kaji daga bakin malam. Tunda na iya jure daren jiya dana samu labarin, na jure safiyar yau, to kuwa zan jure ynxun muje kaji da kanka. Na yafe goron albishir din. Cike da fara’a suka gaisa da malam yace, malam Ismail yaya mai jiki? Jiki da sauqi Alhmdlh. Malam yace, masha Allahu. Ka samu labari daga bakin dan uwanka ko? Cikin zaquwa yace, bai fadamun ba malam. Yace, inji daga gareka. “malam ya fadada fara’arsa, sannan ya kalli Mahmud dake zaune gefe, yana murmushi, ya maido da kallonsa ga Ismail, “Scholarship dinku ya samu. Shekaran jiya malam mukktar yazo ya sameni da batun. Don haka sai ku soma shirye-shirye, nan da wata daya Matsalarmu kudin da zakuyi amfani dashi. Ismail yayi mutuwar zaune, jinsa yake tamkar a mafarki. Wai malam madina yake nufi ko zariya? Da darsuwar wannan zargin, sai ya kalli malam. “Malam wai madina dinne? Malam yayi dariya, ka samu nutsuwa Ismail, madina ce zaku tafi, kaida dan uwanka. Saiku soma shiri, tare kuma da neman kudin da zakuyi ‘yan abubuwan daya kamata. Sam Ismael baisan lokacin daya rungume malam ba. Sunyi murna sosai harda sujjada don nuna godia ga ubangiji. Ismail ya soma tunanin wa zai soma fada mawa? Duk lokacin da wani abin farin ciki ko baqin ciki ya sameshi, sai ya tuna mahaifinsa, ‘yar qwalla ta taru a cikin idanunsa, amma sai ya daure ya cije. Yace musu bari yaje ya fadawa yaya Amina da mutan gidansu. Mahmud yace, to sai ya shigo anjima, a gaida ‘yar amana. Ismail yayi murmushi, “zata ji.” Sam ya manta da Damuwar Zainabu daya baro asibiti da ita. Saida ya idar da sallar azahar sannan ya nufi cikin asibitin, zuciyar sa fal da murna. Yana shiga yaya Amina tana nunke sallaya, ta idar da sallah. Ismail yana shigowa sai ya rungume ta, ta tsorata sbd bata ta6a ganin haka ba. Ya sake ta yana dariya, “naga kin tsorata?” Tace ai dole Ismail ban ta6a ganin haka ba. Yace, zamu tafi karatu madina, nida Mahmud. Yaya Amina ta sake rungume shi, cikin tsananin murna tace, Allah da uwana? Allah mun gode maka. Sai kuma ga hawaye suna zubar mata. Ya ciro hankici yana share mata hawayen. Ba ason kuka a cikin murna yaya, cewa zakiyi “Alhmdlhi llazi bini’imatihi tatimmussalihat. Ta maimaita abinda ya fada, sannan sukayi murmushi. Ta kalli mimi. Wadda take kallonsu, kinji ko khadija? Mimi tace, Allah yasa alkhairi. Ismail yace, Ameen. Sannan suka zazzauna yaya tace, to ya batun karatunka na nan? Yace yaya ai kuma ba wannan zancen. Tunanina ina zamu samu kudi sbd tafiyata da kuma sauran hidimomi. Yaya tadan yi shiru, can tace “to ko daura zamuje wajen su kawu a saida gonarmu ta gurin mamarmu? Ismail a’a yaya gonar fa ba ta ni kadai bace, gaki kuma kema mai buqata ce. Yaya tace, ko ni na siya da kudina bazan sadaukar maka da ita ba, balle gadonta mukayi. Haba dan uwana abin duniya fa na duniya ne. Ya kama hannunta “nagode yaya, Allah ya kaini lokacin da zanga nayi miki fiye da abinda kikai min. Tace Ameen Ismail, in jikin khadija ya qara sauqi sai muje dauran ko? Yace to hakan za’a yi. Dama basu san komai game da auren nan nawa ba. Sai kuma sai kuma ya kalli mimi, tunda ba wai lallai auren ya dore ba, mubarsu kawai. Yaya ta gane yana fadin hakane don kar mimi taci gaba da rikicinta. Kafin kwana goma labarin tafiyar su Ismail ya zaga dukkan ‘yan uwa da abokan arziki, sai murna akeyi wa Ismail da Mahmud. Mimi kuwa jiki ya soma sauqi, gashi tanacin abinci amma fa rabin abincinta kifi ne. Hajiya sauda ta shiga damuwa sakamakon rashin samun Ismail a wayarsa. Ynxun ma da take zaune saida ta dauko wayarta da zummar ta sake gwadawa, kamar wasa sai layin ya shiga. Cikin Jindadi tace, Alhmdlh. Lokacin Ismail yana zaune yana 6are wa mimi lemun zaqi, ya daga ne ya kalli mimi, wadda ta qosa tasha lemun. Yace, ina zuwa. Ya fita cikin sauri. Suka gaisa, sannan yace, hajiya kwana biyu? Tace layin ka baya shiga. Yaya mai jiki? Yace da sauqi sosai hajiya. Ina tsammanin matsalar ntwk ne, amma wayata a kunne take, kuma akwai charge. Tace sauqi na samuwa sosai ko? Ismail yace, tunda tana dai kar6ar abinci. Hajiya sauda tace, to mun gode Allah, sannan ina qara jaddada maka amanata, sannan ina qara baka haquri. Na sani zakaga abubuwa gurin mimi. Ismael yace, don wannan karki damu hajiya. Sannan ina godia kan kudin da aka turo. Tace, karka damu wannan ba wani abu bane. Zan sake turo ma wasu insha Allahu. Daganan sukayi sallama. Ya dawo ciki yaci gaba da 6are lemunsa. Sai da ya gama ne, ya kalli mimi tare da cewa,, qanwatah ga lemun. Fuskarta daure tace, bana sha. Sbd me? Ya tambayeta cikin sauri. Tace, saida ka gama yin wayar, sannan zaka 6are min, alhalin tun tuni nace zansha lemu. “cikin irin shagwa6arta data zame mata jiki tayi maganar. Sannan qasa qasa don ita mimi ko yaushe maganarta qasa-qasa ce. Ya matsa kusa da ita haba qanwatah waya nayi. Ta harareshi, bana son ana hada uzuri na dana wasu. Inka gama nawa sai kayi na kowa. Yayi ‘yar dariya sbd yadda ya lura itafa iyakar gskyrta take magana. Yace, shikenan ranki ya dade. Ko wane lokaci uzurinki zansa a gaba. Tashi kisha lemun to. Tace ya fita raina. Barci nakeso inyi ynxun. Ya kalli lemun na hannunsa, sannan ya ajiye ya gyara mata kwanciya, tare da cewa, ayi bacci lfy. Ismail shida yaya Amina sun tafi Daura sbd maganar saida filin mahaifiyar su na gado. Hannun Ramatu Nurse Ismael ya bar mimi. Domin yace, komai dare aranar zai dawo ba zai kwana ba. Mimi kam ko amsa shi batayi ba, lokacin da yake yi mata saiya dawo. Ya gama karantar halin mimi tsaf, dan zaman da sukayi tare, shirunta na nuna taji haushin tafiyarsa. Bai damu ba, nasa ganin tafiyar itace zata kawo masa qarshen tunanin, ina zai samu kudin tafiya jami’atul madina. Sun samu tarbar mutunci da qauna, kamar yadda aka san dangin uwa. Sannan sunyi murna dajin batun tafiyar Ismail qasa mai tsarki don yin karatu. Haka nan sun jajanta masa batun hadarin matarsa da suka basu labari. Sannan sunsha alwashin zuwa su dubata. Kawunsu yace, shikenan nan ma in za’a zo sai a taho da kudin tunda yau za’a sata a kasuwa. Qarfe takwas da rabi Ismail ya iso katsina, yabar yaya Amina a can zatayi kwana biyu. Ya nufi gida kai tsaye, yayi wanka yasa jallabiya mai ruwan siminti, sannan ya nufi asibiti. Sai da yayi mata tsarabar kifi, sannan ya qarasa asibitin. Kuka sosai ya sameta tanayi idanunta jajur. A rude yake tambayarta abinda ya sameta. Bata tanka ba. Yace, to ga gasasshen kifi na siyo miki, nasan zaki ci. Ya duba cikin kular da yaya ta dafo mata abinci kafin su wuce, ashe faten wake ne da kifi, amma bata ci ba. Ya dawo ya zauna bakin gadon. “Kar dai duk yau bakici abinci ba? Ta kalleshi idanunta jajur, “yau na yarda banida kowa, muryarta tana rawa irin na wanda ya gaji da kuka. Yace me akayi miki khadija da bana nan? Fadamin. Kuma karki sake cewa, bakida kowa. Gaki da ni, ga yaya Amina, muma da mu biyu ne, amma ynxun kinga mun qara mun zama mu uku. Mun tafi da tunanin ki. Ya warwaro tissue ya soma share mata hawayen. Sannan ya dauko kifin ya soma bata a baki sala-sala tare da jajjagaggen kayan miya. Taci sosai, sannan ya debo ruwa ya kawo mata, ya taimaka mata ta wanke hannu da kuma baki. Sannan yace khadija tunda ynxu kina iya zama zaki iya yin sallah. Ta 6ata rai. Yace wai meyasa duk lokacin da nayi miki zancen sallah, sai ki 6ata rai? Tace to yaya zan iyayin sallah a haka? Yace, zaki iya mana. Shi addinin musulunci sauqi ne dashi, ya nuna mana yadda zakayi ibada matsawar kana cikin hankalinka. Ita kuwa sallah sbd muhimmancinta, ko a filin yaqi anayin ta. Tace, ni ynxun dai ka barni barci zanyi. Ya ce, kinada yaqinin daga varcinnan zaki farka? Tayi shiru, yace bakida yaqinin cewa, zaki farka, kuma zaki iya farkawa ki ganki a kabari. Tace, oh Allah na, don Allah kabar zantukannan. Yace assha! Assha! Ina tsoron kar zuciyarki ta kamu da mugun ciwo, wanda batason ko kadan taji an ambaci Allah ko manzonsa, ko wani abu na addini. In hakane kuwa lallai kin daura qawance da shaidan, kuma yaci galaba akanki. “Don Allah ka barni mana! Ga mamakinsa, sai yaga ta soma kuka, shiru yayi, ransa 6ace. Lallai akwai matsala babba, akan zancen addini mimi ke kuka. A fili yace “akwai aiki!. Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba. Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin kashewa, ynxun dai fada min me za’a yi? Hajiya Nana tace, tsabar katan qamshi za’a hada masu fizgar hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. “kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan suka nufi gidan Na’ima. Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm. Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin gadon Na’imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, “ke da Allah natsu! Na’ima ta tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki. Nan ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin gidajenmu. Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace, kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du, yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija mana dariyar ‘yan baqin ciki. Da ma gashi jikin dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da hankali, suka fita, suka tafi. Sha biyu da kusan minti arba’in na dare lokacin ne Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa. Na’ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa kiranta. “Na’ima in na shigo sai na ci miki mutunci. Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da kallo tun daga qasa zuwa sama. ‘yar mitsilar rigar varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi. Cikin wata kidima ya rungume Na’ima a zaton ta abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi. Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni. Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na’ima tana kukan takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba. Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin kashewa, ynxun dai fada min me za’a yi? Hajiya Nana tace, tsabar katan qamshi za’a hada masu fizgar hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. “kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan suka nufi gidan Na’ima. Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm. Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin gadon Na’imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, “ke da Allah natsu! Na’ima ta tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki.Nan ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin gidajenmu. Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace, kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du, yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija mana dariyar ‘yan baqin ciki. Da ma gashi jikin dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da hankali, suka fita, suka tafi. Sha biyu da kusan minti arba’in na dare lokacin ne Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa. Na’ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa kiranta. “Na’ima in na shigo sai na ci miki mutunci. Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da kallo tun daga qasa zuwa sama. ‘yar mitsilar rigar varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi. Cikin wata kidima ya rungume Na’ima a zaton ta abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi. Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni. Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na’ima tana kukan takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. Na’ima tayi kuka, iya kuka cikin daren kafin varci yayi gaba da ita. Qarfe takwas ya farka. Halin daya ganshi ciki ya sashi kallon gefensa. Na’ima ya gani kwance cikin irin yanayin daya samu kansa. Ya soma tunanin da yaushe har tazo masa daki akai hakan? Ya dai iya tuno jiya sun samu matsala da Jennifer. Yarinyar daya kawo ta Abuja da kansa ya kama mata gida tana zamansa, ynxun kuma sai ta dinga munafuntarsa. Jiya yaje mata zuwan bazata sai ya sameta ta kawo wani gidan. Yayi mata magana tana fada masa cewa, itafa ba matarsa bace bare ya dinga yi mata dokoki. Yayi mata duka kafin ya baro gurin ta ya nufi club dinsu inda suke hadewa da abokansa suna shayeshayensu. Ya fada musu halin da yake ciki, nan suka bashi shawarar cewa, yasha mayensa ya manta da ita, ya daina zuwa ta gani in akwai wanda zai mata kwatankwacin abinda yake mata. Sha yayi sosai, don bai ta6a sha irin haka ba. Ko iyayensa basu san yana sha ba, domin baya sha da yawa. Ya kasa komai don haka suka kawoshi gida. Tuna hakan yasa shi gane cewa, maye ne ya suranta masa Na’ima a matsayin Mimi. Tsaki yaja sannan yasa hannu ya daddaka mata duka. Firgigit ta farka tana kallonsa, fuskarsa daure. Yace, tashi ki fita! Tace dama kai ka kawoni bani nazo ba. Ta soma kuka, yace ban tambayeki wani dogon zance ba. Nace dai ki fita. Na’ima ta saka rigar varcinta ta fita da kuka. Ya jima shiru yana takaicin faruwar hakan Tsakanin su, don bai tsara zaiyi hakan da ita ba. Amma sai ya miqe ya nufi bandakinsa. Na’ima ma bayan tayi wanka da sallah, ta koma ta zauna tanata tunanin yadda mijinta yake mutuwar son mimi. Kai ita da ta sani, da bata kawo kanta gurin son maso wani ba. Can ta miqe ta nufi kicin, yauma da kanta ta girka abinda zataci kifi ta gasa, irin gashin da Mimi kansa ayi mata. Na’ima ta dan iya girki, domin ko a gidansu tana shiga kicin gurin masu yi musu girki jefi-jefi. Ta gasa bread dinta, zata fito shi kuma zai shigo kicin din, ya kalli tiren hannunta, “bani kiyi wani! Bata musa ba, ta miqa masa don tanason su riqa ‘yar hulda ko yaya. Ta koma ta hado wani abin karin. Bayan ta karya ne ta shiga turare gidan da turarukan da aka kawo mata. “Yayi qamshi. Ya fada, duk da ba cikin walwala yayi maganar ba. Taji dadi, kuma taji mamaki. Don haka bayan fitarsa, sai ta dauko sauran abubuwan ta kama amfani dasu. A waya Abbas ya kira Usman, yana bashi labarin abinda ya faru a jiya. Usman yace, kai sakarai me nace maka? Ai na fada maka kawai ka more quruciyar Yarinyar kace a’a, to ynxun don ja nuna ma Jennifer kurenta kawai, ka share ta kaci amarcinka. Abbas yace, banason Yarinyar tayi tunanin cewa, ina sonta ne. Usman yace, ai ba wai zaka sakar mata fuska bane sosai. Ka gane? Abbas yace, shikenan zan kwatanta. Tun daga ranar Na’ima tadan samu sauqin mijinta. Zai sata ta dafa masa abinci, kuma zai kirata shimfidarsa. Amma ba wata soyayya, ko kulawa, ko hira ko sakin fuska. Abin da ta lura amfaninta kenan tayi masa girki, sannan yayi buqatarsa. Wani dare ya kirata a waya taje samansa. Ta sameshi a falo tace gani. Yace ki shiga mana. Kin tsayamin akai, sai kace wani sa’anki. Ranta ya sosu, tace, wai kai kana bani mamaki. Kana nema a gurina amma kayi ta dauremin fuska, kana fadamin abinda kk so. Yace kar ki kawomin raini. Ki wuce muje. Tace, ni varci nakeji, ta juya. Nan take ya kamota, saida ya mammareta, sannan yayi abinda yake so anan falon, ya kuma koreta zuwa dakinta. Zahiri baya sonta, amma abubuwan da take sha, da wanda take qamsasa jikinta suke fizgarsa gareta. Irin Rayuwar da Na’ima ke ciki kenan. Gashi danginsa sun tsane ta, musamman uwarsa wadda tace, Na’ima ta bada ita a gaban Qawayen ta. Zainabu kuwa tana can gidansu, saiga Alhaji ya diro da la’asar sakaliya. Yayi sallama

Chapter 20 of 32